AUREN KWANGILA BOOK 2 CHAPTER 9 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
MUN TSAYA
za ka fadi gaibu kuma Ubangiji subhana ya hana amfani da zato, domin zunubi ne. Zaman tare shi kadai yake proving who that person is (wane ne wannan mutum din). Abdul’azeez kishiyar yadda ta dauke shi yake a bangarori da dama, barshi dai da ra’ayin rikau irin nasa, ta kira shi odd, ta kira shi stranger , ta kira shi weird ….amma ashe mutum ne mai matukar kirki, kuma mai sanin yakamata. Masanin sirrin zamantakewa. Kokari yake daga jiya zuwa yau ya Sa ta sake da shi ta daina wannan dari-darin da ta ke yi da shi. Sai dai ya manta cewa, duk wani abu da aka san yana da karshe to ba za’a zira jiki a cikinsa ba. In yau sun yi musabaha gobe kuma sai Yayan musabaha ko Babanta??? Jingine ta ke da kofa idanunta a rufe tana wannan tunanin. Ta tuno da abincin da ta shirya
ZAMU TASHI
masa. Da gudu ta bude kofar ta fito ta sungumo basket din ta bi bayansa. Shi har ya isa ga motar ya bude zai shiga. Yaya Azeez!”. Ta kira sunansa tun daga nesa. Waiwayowa ya yi ya kuma dakata da shiga motar har ta karaso. Kujerar baya ta bude ta sanya basket din, ya shiga motar ya tashe ta. Kanta ta zura ta window din side din da ya ke ta soma magana cikin sanyin muryarta. Na san ka dade da daina tafiya da abincina ofis. Ban sani ba ko abokanka ne suka ce babu dadi? In hakan ne dalili ba zan ji haushi ba tunda na san ba kwarewa nayi ba. Amma yau ka yi min alfarma ka ci ko babu dadin, saboda ba ka da lafiya. Bai kamata ka zauna da yunwa ba har sai ka dawo” Idanu ya zuba mata, ya kasa cewa komai. Ta ja da baya tana waving dinsa. Ya ja motar jikinsa a
sanyaye tare da daga mata hannu ya fita daga get din gidan nasa. Www.bankinhausanovels.com.ng
Sai zamansu ya dauki wani sabon salo mai ban sha’awa. Kowanne kokari yake ya kyautatawa dan uwansa iyakar iyawarsa. Tun daga ranar Abdul’azeez bai kara girki da kansa ba, girkin matarsa Hafsat yake ci safe da rana da daddare. Da safe zai tafi da shi, da rana zai turo a daukar masa, da daddare za su zauna su ci tare a ‘dining’ ko a dakinsa. In ba shi da ayyuka da yawa su yi hirar mutanen gidansu ko ya ba ta labarin shari’u iri-iri da suke yi a kotu. Ya kan gaya mata cewa, ‘rape case’ wato lamarin fyade ya fi yawa yanzu a kotunan Nigeria. Bai san me yasa society dinmu ta cire imani da tausayi ta koma haka ba, watakila rashin aure ga matasa shine dalili. A wani bangaren kuma in an duba yadda abin yake filla-filla ba rashin auren bane masifar karshen zamani ce. Rannan yana bata labarin wata shari’ah ta fyade da suka yi sai wani abu ya fado mata a rai, ta gyara zama ta hau bashi labari inda tace. Ka ga sanda muke Brussels, akwai wani malamin mu Belgian ya kan gaya mana each kind of sexual act is not a crime in their country except rape in dai mutum ya girma , ya wuce shekaru goma sha takwas. They teaches this as sex education. Dana dawo Nigeria na kara hankali sai na fahimci cewa karya suke yi, every sexual act is prohibited, not only rape. Ba tare da kowa ya fahimtar da ni ba”.
Abdul’azeez rubutu yake yi, amma abin da ta ke fada sai ya dauki hankalinsa sosai. Me ake da makarantun nasara? Hasbunallahu wani’imal wakeel ya ce cikin ransa. Dakatawa ya yi da rubutun ba tare da ya dago ya dube ta ba. How do you came to know that? (Ta ya ya ki ka fahimci hakan)?” Ya tambaye ta, cikin kokarin danne kaduwarsa. Sake gyara zama ta yi, ta soma bashi labari. A secondary school dinmu ta ST. Barchman’s College a ajinmu akwai wani yaro Bature Fayol da wata yarinya Jessica, a gaban kowa suke kissing. Ban saba ganin wannan al’adar ba a inda na baro (Jeddah) don haka hankalina ya tashi na gayawa class master dinmu don ya hana su. Sai ya tara mu duka ya ce, “‘ They are not committing a crime, since it’s not a rape . Amma yanzu shekarunsu sun yi kadan su dinga aikata hakan su bari sai sun gama ‘high-school’. Na so in gaya wa Mommah a lokacin na ji tsoro sanin cewa muddin taji wannan maganar sai ta cire ni daga makarantar, ni kuma inason Www.bankinhausanovels.com.ng makarantar saboda na saba da ita. Amma na sa a raina abin da malamin nan ya fada ba gaskiya ba ne, wannan aiki ne na arna marassa addini da tarbiyya. A Belgium ba wani abu ba ne a wurinsu ko a hanya za ka iya ganin suna kissing, masu aure da marasa aure.
Da muka dawo Nigeria sosai na ga bambanci mai yawa. Ban ga mata na rungumar maza ba wai don ana goodbye , ban ga ana kissing a kan titi ba. Abubuwan da na saba gani duk bana ganinsu a nan. Ko masu aure ban ga suna yi ba. I then concluded that; things like that are not accepted here in Nigeria and hence, it’s a crime in Islam and culture daga manya har yara, masu aure da marassa aure”’.
Abdul’ azeez gumm! Ya yi, ya ki ba ta amsa. Haka ne ko ba haka ne ba?” Ta tambayeshi curiously . Daurewa yayi yace da ita. “Ban sani ba Suhaanah , tunda dai kin ga ni ba ni da mata”. Ya amsa a gajarce, cikin son a bar zancen. Da sauri ta ce. “Ba ga ni ba???” Dariya ce ta kama shi amma ya gintse, saboda yadda ta fadi maganar kanta tsaye kuma innocently . Hafsah matar wucin gadi ce ke”. Mene ne wucin gadi?” Ina nufin……. temporary ”.
“Ok, na fahimta. Mu matan wucin-gadi ba a kiranmu matan aure?” “This is beyond my knowledge Hafsah. Da na san kina da baki da Law na zabar miki’.
An tabo hirar da ta ke so (karatu) tuni ta manta da waccan.” Au, ba law ka zabar min ba? Mommah ta yi tsammanin hakan”’Girgiza kai ya yi, “Ba law na cike miki ba, career din da ya fi dacewa da ke ne. Tashi ki je ki kwanta kin dame ni, kada gobe ki makara a kicin, kuma ki hana ni fita sai kin gama. Yau saura kadan ki sa a zane ni” Dariya ta saka ta mike tana fadin, “Zan so ganinka Justice yana zane ka”. Murmushi ya yi ya ce mata, “Sai dai in tafi da ke a zane mu tare, tunda ke ki ke makarar da ni da tambayoyin ki kamar supervisor . Night !”Ya kada mata yatsu. Ya maida kai kan aikinsa, lokaci zuwa lokaci yana tariyo hirarsu a ransa. SeX iS a crime in Nigeria… all kind of sexual acts are prohibited in Islam and culture daga manya har yara, masu aure da marassa aure……. ” . Sai dariya ta kama shi ya yi murmushi, cikin ransa yana fadin “In mun rabu kin sake aure za a sha kallo a gidanku ke da ‘future husband’ dinki . Tunda kin haram ta komai. Www.bankinhausanovels.com.ng
A wannan dan tsukin sun zama abokan juna, ko ciwon kai ta ke sai ta gaya masa ya ba ta magani. In shari’a ya yi, sai ya gaya mata yadda ta kaya. In zai shiga kotu sai ya kira ta ya gaya mata ta yi masa addu’a, he don’t want to be a loser ! In ya yi nasara sai ya gaya mata “….successful as always” addu’arta ta karbu. Ta shirya in ya dawo su je Dominic ta ci Pizza ta sha ice-cream ladan addu’ arta. Fitarsu ta biyar kenan zuwa (Dominic) hakan ba karamin faranta ran Hafsat yake ba. In ba ya nan tana tare da su Mammah a waya. Ko ta dauko Alqur’ ani tayi ta tilawa da sauran littattafanta. Baba Azumi ma ta dawo daga Sokoto duk sanda Mammah ta kira ta, ko ita ta kira ta za ta hada su su sha hira. Haka kawai zai ce kada ta yi abincin dare in ya dawo za su fita su ci a Chinese restaurant ko KFC. Don haka a wannan dan tsukin Hafsat ba ta da damuwa ko cikin cokali. Ranar wata alhamis ya shigo mata da (past quastions and answers) na Jamb ya ce ta duba ranar asabar zai kai ta ta zana. An tura ta wata makarantar sakandire ta gwamnati a nan Abuja inda za ta zana jarrabawar. Ta dukufa karatu ba ji ba gani duk da a wurinta da matsayinta na dalibar (ST. John Barchman’s College) wannan ba wani karatu ne na a zo a gani ba. Da yake asabar ce ba aiki, tun bakwai da rabi ta shirya ta fito tana tsumayinsa. Da ya fito ya ganta idonta luhu-luhu ya tabbatar masa ko isasshen barci ba ta yi ba. Tausayi ta ba shi sosai, kowanne dan Adam da abin da ake jarrabtarsa da so, shi Mu’azatu yake so, Hafsat kuma karatun boko ta ke so. Yana rokon Allah ya cika mata burinta, shi kuma Ya ba shi ikon zama tsanin cikar wannan burin.
Da suka isa ya nuna mata inda za ta fito ta zauna ta jira shi idan sun gama. Sai da ta shiga ajin zana takardar ya ga shigar invigilators sannan ya bar makarantar zuwa gidansu. A can ya karya kumallo ya tadda Mammah da Baba Azumi na shirye-shiryen tarbar Isma’el da Usman. Sun kasa zaune sun kasa tsaye. Ya tambayi Mammah karfe nawa za su sauka?
Ta ce, “Nan da awanni biyu”. Ya kudure a ransa zai ba da mamaki ba tare da ya yi shawara da Mammah ba. Kafin azahar ya koma, ta gama papers dinta tsaf ta fito. Inda ya nuna mata ta jira shi ta nufa kai tsaye, ta samu wani benci ta zauna. Tana nan zaune tana kallon shige da ficen mutane wasu a kafa, wasu a motoci. Kamar daga sama ta ji muryar namiji yana yi mata sallama. Da sauri ta juyo, kallo daya ta yi masa ta gane fuskarsa, a kusa da ita ya zana papers dinsa, zai girme mata sosai don zai yi shekaru ashirin da uku. Dauke kanta ta yi ta amsa_ sallamarsa. Karshen bencin da ta ke zaune ya zauna, Www.bankinhausanovels.com.ng
“Kin riga kowa submitting wannan ya nuna kin shirya wa jarrabawar nan sosai’”’In magana fa ta karatu ce Hafsat ba ta shariya. Harararsa tayi.
“OBJ questions din ne sai an yi wani shiri?”
Murmushi ya yi, ya ce, “A wajenmu ‘yan Nigeria sai an yi, don ke da ganinki ‘Afro-Arabian’ ce (‘yar Africa da surkin larabawa)”. A nan kuma shiru ta yi masa. Wace Uni za ki?” Ban sani ba wallahi, ba ni na cike ba”.Haka ya yi ta janta da hira, wani ta amsa wani ta share shi don ba ta ga dalili ba, kuma ba ta iya wulakanta mutane ba. Tun daga nesa ya hango Hafsat a inda ya ce ta zauna, amma abin mamaki tare ta ke da wani a benci daya. Hafsat murmushi ta ke yi wani irin murmushi da ya ba shi mamaki, kuma saurayin yana magana, wani irin kyau ta yi masa da hand bag dinta a kan cinya. Amma tsaya… wane ne wannan saurayin na kusa da ita? Me ye alakarsu da har ta ke sakar masa wannan murmushin a matsayinta na matar aure? Ba ya tsammanin ko su Isma’el tana yi wa wannan murmushin (A idonsa fa). Girarsa ta tattare ta hade wuri guda, cike da mamakin yadda yake tsaye a gefensu zaune cikin mota, amma ba ta ma ganshi ba. Wayarsa ya dauka ya kira numbarta don ga dukkan alamu ba su da niyyar rabuwa ko zai kwashe awanni yana jira. Yana kallon sanda ta bude jakarta ta dauko wayar ta kara a kunnenta. Muryarta mara amo mai tsananin taushi ta fito tar-tar ta speaker din wayar a jone ta ke da aux na motar. Bai amsa sallamarta ba ya yi shiru kawai yana jinta. “Yaya ka iso? Ban ganka ba. Kana ina?” Sai kuma ta fara juye-juye alamun tana nemansa. Tana ganin motar ta ce da matashin wani abu, sai gani ya yi ta tashi, shi ma ya biyo ta sun nufo motar tare, amma ba ta sake cewa komai ba. Daga inda yake ya fahimci saurayin ne yake ta magana ta yi masa shiru, inda ya fahimci ta gane shi ne ya zo shiyasa ta kama kanta, kuma ta gane shirun da ya yi mata yana da ma’ana. Har suka karaso idanunsa a kanta bai dauke ba, ta bude kofar tare da sallama ta shiga ta zauna. Www.bankinhausanovels.com.ng
Zai iya rantsuwa ko ‘shopping mall’ yarinyar nan za ta shiga sai ta yi sallama, daya daga cikin kyawawan dabi’unta da ke burge shi kenan. Amma yadda ta jefa shi cikin matsanancin bacin rai yau bai jin ko kallon fuskarta zai iya yi balle amsa sallamarta. Ba ta dauke hannunta daga gama rufe kofar motar data yi ba, ya yi mata giya ya fizge ta da wani irin gudu kamar zai tashi sama da su. Sun hau titi sosai sun kama hanyar cikin gari, so ta ke ta ce ya rage gudun babu fuska, hasalima ba ta taba ganin fuskarsa haka kamar hadari ba, takurewa ta yi a kujerarta ta hade jikinta wuri guda ta yi shiru. Abin kirkin da ya yi niyyar yi mata yau yake so ya fasa, wata zuciyar na tausarsa. Ya karya kan motar ya hau titin da zai kai shi unguwarsu Asokoro. Kamar daga sama Hafsat ta tsinkayi muryar Abdul’ azeez a cikin kanta, cikin yanayi mai boye halin da zuciyar mutum ke ciki.
Waye shi?” Ya tambaya a matukar gajarce. Ba tare da ya dauke kansa daga titi ba, kuma ba tare da ya dube ta ba. Ta murza yatsun hannunta cikin junansu, sannan ta ce, “Ni ma ban sanshi ba’.
Muryarta ta nuna zullumin da ta ke ciki irin na guilty conscious. Bai sauya daga yanayin da yake ciki ba ya ci gaba da tambaya. “Ba ki sanshi ba ki ke hira da shi kina matar aure? Ba ki sanshi ba murmushinki ya zama mai arha a gare shi? For Allah’s sake me ya hada ki da saurayi Suhaana? Wace irin hira zai miki har ya samu murmushinki haka?” Dagowa ta yi ta kalle shi. Har zuwa wannan lokacin idonsa na kan titi. Ya ci gaba da magana cikin bacin rai amma wannan karon kamar cikin lallashi. Www.bankinhausanovels.com.ng
“Aure kowanne iri ne yana da martaba da mutuncinsa. Kuma kin sani wannan auren yana da limit kina da enough time da in maza dari ki ke son kulawa a nan gaba za ki yi. So please kar ki kara, bana so. I repeat it, bana so! Kada ki ba da kofar da za a fahimci irin zaman auren da muke yi”. Sai ta yi shiru tana kallon hanya cikin mamakinsa. Ta yi rantsuwa ta daina sanya al’amarin Mu’ azatu a ranta, sannan shi din ba abokin sa-insar ta bane, amma da ta ce ashe babu dadi! Maganarsa ta karshe ta yi mata ciwo wai ta bari sai aurensu ya kare ta kula maza dari in tana so. Ita daa rayuwar da ta yi cikin turawa ma ba ta sanya kanta cikin sha’anin maza ko ya ya yake duk da cakuda suke karatu saboda yadda Mammah ke kwabarta a kullum, sai yanzu da ta ke da sunan matar aure? Ita bata san wani murmushi data yiwa saurayin ba, watakila gizo ne idonsa yayi masa. Hasalima duk maganar da yake mata daga eh, a’ah ba abinda ta ce. Tana hango shi kuma ta bar wajen.
Ta fassara maganganunsa da cewa; Aurensa da ta ke tare da shi a yanzun kawai yake karewa martabarsa, ba ruwanshi da duk irin rayuwar da za ta yi a gaba, koda kuwa ta karuwanci ce, to kula maza dari (100) ai yana nufin karuwanci.
Ji ta yi idanunta sun cicciko da kwallah. Amma ta yi kokarin maida ita. Ta koma ta jingina da kujera ta rufe idonta ba tare da ta ce da shi komai ba. Ba ta bude idonta ba lokaci mai tsawo, sai da ta ji ya ja birki ya kashe motar. Sai dai da ta bude
idon maimakon ta ganta kofar gidanta, sai ganinta ta yi a kofar gidan iyayensu (gidansu).
Duk wani bacin rai nemansa ta yi ta rasa. Da sauri ta dube shi kamar ta rungume shi. Ya wani hade rai ya matse gira ya dauke kai daga kallonta. Murmushi ta yi ta soma kicin-kicin bude kofa amma ta kasa. A marairaice ta dube shi kamar za ta yi kuka.
“Wallahi in ki ka fito da hawaye juyawa za mu yi. Mu jera mu shiga a tare, in mun je falo ki zauna kusa da ni, kada ki yi hannu da Haleem balle Isma’el. In na kula ki, ki ba ni attention , kin san Mammah proffessional ce wajen karanto psychological moves din kowa cikin ‘ya’ yanta, don haka ki nutsu”.
Ita dai burinta ya bude mata kofa ta ganta a falon gidansu, don haka da gaggawa ta amsa. Sai da ya gama yangarsa da noke-noke da nemeneme cikin motar na babu gaira babu dalili, zuciyarta kamar ta fito ta bakinta don takaici, sannan ya bude kofofin motar. A tare suka fito tana so ta shiga da sauri, amma dole ta jira shi ya zagayo suka jera.
“What a perfect match ?” Www.bankinhausanovels.com.ng
Abin da Isma’el ya fada kenan wanda suka fara tozali da shi a cikin falon yana cin abinci yana zaune a dandaryar kasa. Haleem, Usman, Mammah, Daddy, Ramadan da Sha’aban da Farhan ‘ya’yan Uncle Abdulkareem wadanda su ma gidansu a nan Abuja ne unguwar Maitama, suna hade a makeken family dining din gidan suna cin nasu abincin. Tare da su aka je aka dauko su Isma’el daga filin jirgi. Hafsat kasa jure wannan tafiyar da Abdul’ azeez ke so su yi ta yi, ana shigowa falon taku dayabiyu ta sheka da gudu ta rungume uwarta, uwar da babu kamarta a duniyarta, wadda ta fi dutsen sapphire daraja a gare ta. Hajiya Maryam Hamza Atiku.
“Lallai ma, wato duk cikar mu nan Mammah kadai ki ka yi kewa?” Inji Auta Haleem. “Kyale ta Brother, ni sau daya ta taba kirana a waya, ni in na kira ta a ce na aje voicemail. I’m sure kullum tana kiran Ishma”. Cewar Usman wanda ba su cika shiri ba, shi halinsa ma daban ne da na kowa a gidan, bai cika shiga shirgin mutane ba hatta iyayensa sai dai su neme shi, irin mutanen nan ne masu kamewa, shi dai bar shi ya fuskanci karatunsa ya fiddo (CGPA) mai daraja.
“Wai ni yarinyar nan ta ke kira ‘bachelor’ Mammah saboda ta riga ni aure kamar ba a hannuna ta soma ta-ta-ta ba”. Cewar Isma’el. WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG
Haka kowannensu ke jifanta da korafinsa, ita dai ta yi shiru ta dora kanta a kafadar Mammah sai murmushi ta ke yi. Tana binsu da idanun kauna daya bayan daya. Mammah wadda farin cikinta ya kasa boyuwa ta ce, “Kai ku kyale min yarinya ina dalili? Daga jarabawa ta dawo ko hutawa ba ta yi ba”.
Ta ja mata kujerar kusa da ita ta zauna, ta tsugunna ta gaida Daddy wanda ke magana da Abdul’azeez tun shigowarsu. Sosai ya amsa ya na suruka, na rabin jiki ga Abdul’ azeez dan da bai da kamarsa. Hatta sauran ‘ya’ yan sun san haka sai dai su yi hakuri, duk wani Da ya biyo bayan Abdul’azeez a wajen tsohon Ambassada Hamza Atiku. Ta gaida su Farhan sabida duk yayyenta ne, Farhan sa’an Abdul’azeez ne, karatun likita yake yi ya kusa kammala wa yanzu haka. Sha’aban sa’an Ismael ne. Ramadan ya girma Haleem kadan. Duk a Australia suke karatu.
Sai ga Baba Azumi ta bullo daga corridor din kicin tana dauke da katon din ruwan sha mai sanyi na FARO. Da Hafsat ta fara tozali fuskarta ta washe, bakinta ya fadada, ta rasa dalilin wannan gashin kuma na Hajiya Maryam, wai ba za su je wajen Hafsat ba sai ta shekara a gidan miji, ga shi ai su sun kasa jurewa sun zabi mai fishshe su. Tunda sun zo ai ba za ta kore su ba. Oyoyo da ‘yar Baba, oyoyo da ‘yar Mammah, lale da amarya mai abin mamaki”.
Turbunewa Hafsat ta yi tana cuno baki, “Da na zo da kaina Baba Azumi? Wai kema har da ke Baba, ba kya nemana… kin manta da ni…”Ina kaka za ta manta da babbar jikanyarta? Wane mutum!!!”
Gabadaya aka yi dariya, sabida irin yadda ta jinjina girman al’amarin. Hafsat ta karasa gare ta ta rungume ta. I missed you so much Baba…”
Baba Azumi na jin turanci sama-sama ta ji abin da Hafsat ta ce. “Kin yi fari, kin yi kiba, Babban Yaya ya iya kiwo. Mu ma mun yi kewarki ‘yar Mammah, kullum ma muna yi (kewar)”. Ta fada tana bubbuga bayanta. Da kyar Baba Azumi ta samu Adda ta sake ta.
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG