AUREN KWANGILA BOOK 3 CHAPTER 15 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Www.bankinhausanovels.com.ng
Mun tsaya
tunda shi yana da Mu’ azatu. Ita kuwa ba ta da mai damuwa da ita ta wannan fannin wanda zai tsaya ya lallasheta in ta sha dukan. Kafin ta kai kofar Abdul’azeez ya riga ta, ya kuma murza ‘key’ din da ke jiki. Hannu ta dora a ka za ta zuba ihuya toshe mata baki da hannun daman sa ya janyo ta tana tirjewa har gefen gadonta. A jikinsa ya zaunar da ita, ya dauko shayin ya kai bakinta. Turewa ta yida karfi tana kokarin mikewa har da zabura,da haka duk suka zubar da ragowar shayin a jikkunansu. Ga shayin da sauran zafin sa sosai amma ba ta wannan take ba. Ta yi wuf ta mike jin Mammah na buga mata kofa, iyakar rikicewa Hafsat ta rikice, iyakar rudewa ta gama rudewa, tashin hankali baro-baro ya bayyana a fuskarta.
dawo ya zauna ta yi saurin matsawa.
“Wallahi ita nake so sau dubu ba kai ba, kuma wallahi na fi ka saninta, har yaushe ka zauna da ita? Kullum gudunta ka ke, sai yanzu rana tsaka bayan ka gama wulakanta ni ka zo ka ce za ka shiga tsakaninmu? Ka tafi ka auri Mu’azatunka tunda tace bazata hakura ba ka kyale ni da Mammah nah”.
Babu damuwa ko kadan a tattare da shi ya ce. “Duk na ji, kuma na yarda kin fi ni saninta.Amma maganar na wulakanta ki ni ban santa ba.Idan kuma akwai wata rana da hakan ta faru a zamanmu ki gaya min ita, na yi kuskure na yi saki, kuma na ce na mayar a gaban kowa in ga wanda ya isa ya ce bai maidu ba. Sannan ta wani bangaren I might not call it a mistake ; da yardarki aka yi shi (sakin) saboda ba ki san daraja ta ba, kin fi son boko a kaina.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Na ba ki bokonki nace ki tsufa kina yi karewa, yanzu kuma ki fi kowa daukar zafi wai an sake ki? To an sake kin, kuma an ce an mayar da ke sau saba’in in kin isa ki ce babu auren kwatakwata damuwar ki ce. Na ba ki minti talatin ki yi wanka ki yi min kwalliya, you are looking shabby, ki sama min abin da zan citunda kin zubar min da tea kuma Mammanki ba bani za ta yi ba tunda Azumi ba ta nan”.
Ya mike ya yi ficewarsa ya barta nan a zaune kamar an kafe ta. Ashe gaskiya ne da ta ke ji ana fadinwai maza ba su da kunya? Sai dai wasu daga cikin kalamansa sun tsaya mata a rai, ta nutsu tana analysing (duba su filla-filla) tana dora su a sikeli na hankali da adalci…. Ba ta san darajarsa ba! “ She is after her studies morethan the marriage itself”. Da yardarta aka yi saki, aka yi con
dawo ya zauna ta yi saurin matsawa.
Www.bankinhausanovels.com.ng
“Wallahi ita nake so sau dubu ba kai ba, kuma wallahi na fi ka saninta, har yaushe ka zauna da ita? Kullum gudunta ka ke, sai yanzu rana tsaka bayan ka gama wulakanta ni ka zo ka ce za ka shiga tsakaninmu? Ka tafi ka auri Mu’azatunka tunda tace bazata hakura ba ka kyale ni da Mammah nah’.
Babu damuwa ko kadan a tattare da shi ya ce. “Duk na ji, kuma na yarda kin fi ni saninta.Amma maganar na wulakanta ki ni ban santa ba.Idan kuma akwai wata rana da hakan ta faru a zamanmu ki gaya min ita, na yi kuskure na yi saki, kuma na ce na mayar a gaban kowa in ga wanda ya isa ya ce bai maidu ba. Sannan ta wani bangaren I might not call it a mistake ; da yardarki aka yi shi (sakin) saboda ba ki san daraja ta ba, kin fi son boko a kaina.
Na ba ki bokonki nace ki tsufa kina yi karewa, yanzu kuma ki fi kowa daukar zafi wai an sake ki? To an sake kin, kuma an ce an mayar da ke sau saba’in in kin isa ki ce babu auren kwatakwata damuwar ki ce. Na ba ki minti talatin ki yi wanka ki yi min kwalliya, you are looking shabby, ki sama min abin da zan citunda kin zubar min da tea kuma Mammanki ba bani za ta yi ba tunda Azumi ba ta nan”.
Ya mike ya yi ficewarsa ya barta nan a zaune kamar an kafe ta. Ashe gaskiya ne da ta ke ji ana fadinwai maza ba su da kunya? Sai dai wasu daga cikin kalamansa sun tsaya mata a rai, ta nutsu tana analysing (duba su filla-filla) tana dora su a sikeli na hankali da adalci…. Ba ta san darajarsa ba! “ She is after her studies morethan the marriage itself”. Da yardarta aka yi saki, aka yi con Www.bankinhausanovels.com.ng
tract , aka shirya komai aka tsara shi daidai da burin kowannensu. Kamata ya yi yanzun da ya yi nadama ya yi damarar gyara kuskurensa ta ba shi goyon baya su hadu su gyara kuskurensu tare, su nemi afuwar iyayensu game da yaudarar da suka yi musu a sirrance hadi da yafiyar Allah na saba masa da suka yi da gangan. Adashin karkacewa daga umarnin Ubangiji da suka yi ne saboda son zuciyoyinsu suke kwasa gabadayansu a yanzu. Ko wannan soyayyar dake cin zukatansu azaba ce mai zaman kanta. Sannan takunkumin Mammah ma kadai punishment ne mai cin zuciya. To amma anya zabar farin cikinsu ita da shi a kan biyayyar Mammah abu ne da ya kamata daga gare ta? Butulcewa umarnin ta wani abu ne da ya kamata ta aikata cikin hankalin ta? Ta tabbata ta kuma amince duk abin da Mammah ke yi tana yi ne don ta daidaita rayuwarta, tana yi ne for her own well-being da kwato mata darajarta. Tana yi ne don ta samu eternal farin cikin aure da rayuwa mai inganci har karshen rayuwar ta.
Hakika takasance mai matukar rauni kwarai a kan Abdul’azeez da soyayyar sa. Kada ta manta Mammah ta yi musu aure cikin mutunci, ta so su zauna da juna cikin aminci su kaunaci juna da zuciya daya, amma suka hadu ita da shi suka yaudare ta, Eh, yaudara mana? They blackmailed her! She didn’t deserve such a betrayal! Dagakowannensu . Kuka sosai ta soma yi, ta mike ta isa ga closet dinta tana canza kaya, ko dankwali ba ta tsaya dauka ba ta nufi dakin Hajiya Maryam.
Da rabe-rabe a jikin bango ta shiga dakin, guilty conscience na abinda ya faru na dibanta duk da ta san ba laifin ta bane amma ita Mammah ai bata san haka ba, fuskarta fal hawaye ta shiga dakin. A gefen gadonta ta same ta tana waya, kallo daya Mammah ta yi mata ta dauke kanta, ta ci gaba da maganar da ta ke yi. Ta lallaba ta isa ga gefen kafarta ta zauna tana ta share hawaye.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Ta fi minti goma sha biyar tana magana a waya inda ta fahimci da Auta Haleem ne, tana shirya masa zuwa hutu daga Sweden karshen watan nan. Da ta kammala tana ji suka yi sallama, ta ce “ Love you too Haleem”’.
Ta ajiye wayar tana shirin mikewa don ta bar mata dakin Hafsat tayi maza ta rike kafarta tana kuka. “Don Allah Mammah ki yi hakuri ki saurare ni, ba ni na kira shi ba, bansan sanda ya shigo ba, kawai ganinsa na yi a kaina na zo zan fita ya rufe kofar. Mammah in kin yi fushi da ni ina zan sanya rayuwata in samu irin sanyin da nake samu a tare da ke?”
Janye kafafunta ta yi, amma ta koma ta zauna, ta ce. “Za ki samu a wurin mijinki,wanda ba kya son bacin ransa, mijin da ya yanke igiyar aurenki ya watsar, ya ce wata mai aji yake so ba ke ba. “Yar masu kudi mai zurfin ilimi. You are unbelievable Hafsat! Sau nawa za mu yi wannan maganar? For the first time na fara shakkarki, don kin canza daga Addah ta da na sani, tunda har za’a iya hada baki da ke a yi wasa da hankalina. Naji komai na abin da kuka kulla kada don ban yi miki zancen ba ki dauka ban ji ba”.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Karshen tashin hankali Hafsat ta shige shi, kukan ma ta neme shi ta rasa. Ba ta taba zaton al’amarin zai yi girma haka a zuciyar Mammah ba, da ko kusa ba ta sanya kanta a ciki ba. Ba ta san sakin wani abu ne special ba, a lokacin tana
ganin all a woman wants is knowledge (abinda diya mace ke bukata shine kawai ilmi), kuma Mammah ta hana ta, ta ce AURE shine gaba. Tana so ta ga ‘yan uwanta na jini,tanaso ta ga wanda ya diga jini ya haifeta, Mammah ba ta taba damuwa da hakan ba. Bata so ma ayi mata zancen. Ba ta so ta takura mata da ta nemo mata danginta za ta ga kamar ta raina kulawar da suke bata ne.
Abdul’azeez ya zo kamar daga sama ya ce zai yi mata duk wadannan abubuwan cikin sirri, kuma cikin dan lokaci kalilan. All he need in return shi ne ta amince za su rabu bayan shekara daya! Dokinta ga hakan, enthusiasm dinta ga son zuzzurfan ilmi, rashin sanin me auren kansa ya kunsa, da rashin sanin cewa ‘SAKI’ shi ne babban koma baya ga rayuwar diya mace, da rashin sanin cewa babu mai iko da zuciyarsa sai Ubangijin da ya halitta masa ita, su suka taru suka kai ta ga amincewa ga bukatar Abdul’azeez Hamza Atiku,ba wasa da hankalin Hajiya Maryam ba, ko nufin yaudara a gare ta.
Maryam din data rayu shekaru goma sha takwas da doriya against all odds don tserar da rayuwarta tun tana cikin kwalba (incubator).Ta zabi Da mai sunan Da a cikin ‘ya’yan ta ta aura mata,ba tareda la’akari da nata matsayin ba, duk don ta samar da kyakkyawar rayuwa a gareta a shekarun girma bayan wadanda ta samar a shekarun kuruciya.
Hafsat ta ga ba ta da mafita a yau ban da warware wa Mammah komai, wannan Mammah din da ba ta da kamarta, yadda komai ya faru da
Www.bankinhausanovels.com.ng
dalilin amincewarta.
“It happened on 31 St september a studyroom da ki ka ce in je mu gana for the first time…….
Tiryan-tiryan ta gaya mata komai, har irin zaman da suka yi a gidansu a ‘Sun-City’. Amma da ta zo inda suka soma ‘having physical contact’ sai ta ke kaucewa. Ta kare da cewa.
“Ban taba sanin yana da kirki ba sai da na zauna da shi, abubuwa da yawa da na girma ina gani a tare da shi, sai na tadda su akasi ga tunanina. Ko a cikin mutane shi na daban ne. Yana da qualities da za a so shi a kansu ba tare da amincewar zuciya ba; he is genius, he is unique.
Ya tabbatar da kasancewarsa mai gaskiya da rikon amana a kan Mu’azatu. Ya tabbatar shi mai muhimmanta alkawari ne akaina da Mu’azatu. Duk alkawuran da ya daukar min ya cika min. Sai na ga bari ni ma in taimake shi ya kai ga samun wannan burin nasa guda daya. He used to say;he has only one weakness… shi ne soyayyar Mu’azatu. Mommah in na ce sai ya ci gaba da zama da ni bayan duk wannan halarcin da ya yi min, shi kada ya auri wadda yake soya samu farin ciki na zamo cikin masu son kansu da yawa. Bayan Annabi SAW yace imanin mu baya cika har sai mun so wa ‘yan uwanmu abinda muke so wa kanmu.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Nima ba da son raina ne aka yi sakin ba, but a iyaka tunaninsa a lokacin (it’s the only solution), kuma na ji ciwo sosai a zuciyata yadda bazan iya kwatantawa ba Mammah. Ki tambayi Dada I became unconscious na lokaci mai tsawo lokacin da na tsinci takardarsa cikin jakata. A lokacin ne na gane yanzu ba karatun nake bukata ba while it is too late, akwai wani abu wanda ya fi shi muhimmanci ga diya mace wanda ni na rasa a halin yanzu….”. (Sai bayan ta fadi hakan kuma ta ji kunya sosai, watairin kunyar Mammah da bata taba ji ba tsayin rayuwar ta, ta ga kamar ta ce ne da Mamansa tana sonsa indirectly ) bayan ba haka take nufin fada ba”.
Mammah ba ta nuna a kage ta ke da son jin karshen bayanin nata ba. Amma jin ta yi shiru ta kasa ci gaba sai ta fahimci kalmomin bakinta sun kare. Kallonta ta ke tana jin tausayinta da jin son ta sosai yana karuwa a ranta. Hafsat din kanta na kasa. Maryam Dakata ta kira sunanta cike da kulawa.
A hankali ta dago amma ta kasa kallon kwayar idanunta, sai yanzu ne ta ankara da irin kalaman da ta ke bulbularwa ba tare da tunanin wa ta ke gaya wa su ba. Ta gama fallasa asirin zuciyarta ba da saninta ba. Ta gaya wa UWA tana cikin soyayyar Danta a fakaice, wannan abin kunya da me ya yi kama??? Kanta ta kara sunkuyarwa tana jin tamkar ta ce da kasar ta tsage ta shige. Mammah ta fahimci halin da ta ke ciki, murmushi ta yi ta ce.
“Ni na nutsu na saurare ki, amma ni kin ki saurara ta. Tambaya biyu kawai nake son in yi miki, in ki ka amsa min su genuinely na daina shiga tsakaninki da mijinki kuma a yau dinnan zan tattaraki in maida ke dakinki don na Jura kun
fi kusa, kun wuce da tunanina……”. “Mommah ba haka ba ne, ni wallahi…..” Ta
fada kamar za ta yi kuka, amma ta kasa karasawa.
Mammah ta riga ta gama fahimtar tana son Abdul’azeez yanzu, ina za ta kai wannan kunyar?
“Addah yau suruka na zame miki? To idan na koma suruka ina za ki nemo uwa? Ke ki ka zauna da ni a lokacin da shi yake nesanta kansa da ni. Ke na sani a matsayin ‘ya ba shi ba. Ban zaci aurenki da shi zai sa ki canza min matsayi ba. Tashi ki je in kin shirya magana da ni a matsayin UWA kya dawo, amma yau suruka ki ke kallona”.
Murmushi ta yi har sai da kumatunta suka lotsa ciki sosai. ““An-ti Ummeeee…”. Wato Ke uwata ce .(Yau aka tuno larabcin Jeddah).
Kallonta Hajiya Maryam ta yi a tsanake, ta tabbatar ta samu nutsuwa sosai sannan ta ce. “Naji duk bayaninki kuma na fahimce ki. Tambayoyi biyun da zaki amsa min properly sune; How sure are you (ta ya ya ki ka tabbatar) yanzu yana sonki so na haqiqa? How sure are you ya daina son ita waccan din ko ya fasa aurenta acan gaba, idan kika koma gidansa?”
Shiru ta yi don ita kanta ba ta sani ba. Abin da ta sanin shi ne zamanta da shi a yadda suke a gidansu ko babu soyayyar ya fiye mata wannan zaman gashin kumar da ake musu a yanzu. She can’t get into his mind (bazata iya shiga zuciyarsa ba balle ta gano wadannan amsoshin). Zuciya abin sirri ce. Sai dai abu guda da ta ke da tabbaci shi ne, ba zai taba yi mata karya ba. Karya is out of his ‘vocab bank’ (vocabulary bank).
“Sannan kuma ita zuciyar ai tana canzawa Mammah, kamar yadda komai na duniya ke iya canzawa. Nima ai da ba son nashi nake ba.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Lokaci daya na tsinci kaina dumu-dumu a duni
yar da in ba shi ba zan iya rayuwa ba. Sannan yana da damarkarin mata biyu ma bayan ni da Mu’azatu. Mammah ta duba wannan mana ta yi masa uzuri”. Sai dai ko giyar wake ta sha ta san itama ba za ta iya yi wa Mammah wannan bayanin ba. Zai bayyana gare ta cewa ta makance a son mijinta, wanda a zahiri hakan ne. Ta yadda bata ji bata kuma hango komai sai na yadda zata koma rayuwa da shi.Saidai fa bazata taba zabar sa akan Mammah ba koda son ne zai yi ajalinta. Gara ta zuba ido ta bar wa Allah al’amarinsa, ta bar Mammah ta yi hukuncin da ta ke ganin shi ne daidai. Duk son da ta ke masa ta san bai yi na wanda ita da ta haife shi take masa ba. Idan so cuta ne, to hakuri da biyayyar iyaye maganin komai ne.
“Kina iya tashi ki je ki yi wanka mu yi shirin dora ‘lunch’. Ranar da ki ka samu amsa ga tambayoyina ki zo ki goya mijinki ku koma gidanku. Kuma ki tabbatar kin nemi wani abu kin ci. Silly girl kawai’”’.
Sum-sum-sum ta fice kanta a kasa. Mammah ba ta bi ta kanta ba, ta fito falon. Abdul’azeez ne da Usman, Isma’el ya fita. Hira suke amma tana shigowa falon suka yi shiru. Fuska dinke ta wuce su zuwa part din Daddy. Ta same shi yana ta aiki cikin projects din dalibansa na PhD, kasancewar yau ba zai shiga jami’a ba.
Tana shigowa ta soma korafi ko gaisawa ba ta bari sun yi ba. Ya kasa fahimtar daya kwakkwara cikin complains din nata. Abu daya ya fahimta; Abdul’azeezya bar mata gida ! Ya zo ne kawai don ya takura wa Hafsat ya zuge ta ta ki yi mata
biyayya. Kansa ya mayar kan abin da yake yi ya ci gaba, amma ya kasa fahimtar komai saboda ta dame shi da korafin ta. Dakatawa ya yi ya cire medicated lenses dinsa, ya dau waya ya kira Abdul’azeez ba tareda sanin yana cikin gidan ba, ko mintuna uku bai yi ba ya shigo, wannan karon ya sauya kayan jikinsa da alama wanka yayi a lokacin da itada Hafsat suke heart-to-heart talk dinsu. Shirt ce fara sol ‘long-sleeved’ mai rubutun ‘Nordstorm’ da ruwan tokar trouser ajikinsa. Ya yi kyau sosai kuruciyarsa ta fito fili. Yana ganin yanayin Mammah ya san kararsa ta kawo. Daddy tun kafin ya zauna ya ce dashi. “Me ka yi mata?”
Sunkuyar da kansa ya yi ya ce “Daddy a sanina babu komai. Na dai kwaso kayana ne kawai na dawo nan, saboda matsalolin da nake fuskanta na zama ni kadai da na abinci da tsabtar gidan kansa. Sanda nake dawowa daga office na gaji, abinci kawai nake bukata kuma babu. Sai dai in kara bata lokaci in yi express da kaina shi ma kuma wani lokacin gajiya ba ta barina sai dai insha coke in kwanta. In na ce sai na tsaya na biya na saya sallar magriba za ta wuce ni. Ka san kuma mutum da ya saba komai a yi masa, sannan the house is somehow dirtyalways ”. Ya fada cikin muryar da dole a ji tausayinsa amma banda Hajiya Maryam.
Www.bankinhausanovels.com.ng
Dr. Hamza ya ce. “Ki barshi ya zauna mana? A kanki yake zaune? Ga mari ga tsinka jaka?”
Cikin mamakin abin da ya fada ta ce, “Haka ma za ka ce? Wace jakar na tsinka masa?”
“To in dai gidana ne na ce ya zauna, ki gode Allah da ya ba ki shiryayyun ‘ya’ ya a wannan za
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG