AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 1 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
A ganinta hakuri da biyayya shi ne abin da ya kamace su daga ita har shi. Duk abinda hakuri bai bayar ba rashinsa ma bazai taba bayarwa ba! Hafsat dai sai dago kanta ta yi daga tunaninta ta gansu a harabar Rockview Hotel Abuja.
Kallon tsoro ta fara yi masa, amma ya ki ko ya dubi inda ta ke. Tana nan zaune ya je ya dawo ya bude kofar side dinta, jakarta ya fara daukowa sannan ya ce,
Mu je daga ciki.
A raunane ta ce Yayan Haleem,Hotel? Hasken fararen idanunta kadai da yadda ta wargazasu a kansa, suka gusar da duk wani tension da yake ciki. Yadda ta yi maganar ya kwaikwaya. To ko mu ma yan abin nan dinne ne?
Tsoron zuciyarta ya ninka na farko ganin Abdulazeez na nade hannun suit dinsa da zummar daukanta a gaban mutanen da ke shige da fice. Sauri ta yi ta fito, kiris ya rage ta fashe da kuka ta wuce gaba ta barshi a baya. Sai da suka shiga reception ta dakata har ya cimmata don batasan ina zata nufa ba, hannunta ya rike suka wuce cikin lifter. Suna shiga lifterta kwace hannunta ta harare shi ta gefen ido. Jinjina kai yayi, ya ce.
Ki harareni yadda kike so. Za ki yi bayani ne Hafsah.
A ranta ta ce Allah na kowa ne, tuni ya riga ya zame min gata.
Katin kofar ya sa a jikin kofar kawai ta bude,ya bata hanya ta wuce tukunna ya mayar ya rufe sai faman cin magani take yi. Fuskar nan kamar kunun kanwa sabida kirnewa. In ma ya lura to ba abinda zai iya tasiri bane akansa a wannan lokacin. Tun daga bakin kofar Hafsat ta gane yau ta shigo wata koma da taimakon Allah ne kadai zai fitar da ita. Ta san dai ya yar da jakarta da ke hannunsa a muhallin da bata tantance ba. Ya kuma raba ta da mayafi da dankwalin kanta cikin wata irin nutsuwa. Idanunsa na fidda wani chemistry zuwa cikin nata mai bayyana intent and in depth sorrow din da ya kasance ciki na rashinta lokaci mai tsawo. Sauran alamuran da suka biyo baya sun fi karfin ta iya bayyana su; Is a kind of gentle romance wanda ba ta taba sanin akwai irinsa a duniya ba. Tashin hankalinta ragagge ne sanin cewa she is safe a yau kam. Kwananta biyu da karbar bakonta kuma a iya saninta na addini da na boko mace mai alada miji ba ya kusantarta.
A yadda ya santa da tsoron ta shiga hannunsa ya yi mamaki da yau ba ta tsorata sosai ba, karewa ma she contributed a lotdonganin ya samu nutsuwar da bai da ita,wanda hakan ya zo masa kamar a mafarki. Don haka duniyar da suka fada mai nisan zango ceda ta shallake tunanin su. Sai da komai ya kankama ya gane Hafsat shigo-shigo ba zurfi ta yi masa (abun mata ce a jikinta). Alamarin da ya jefa shi cikin wani hali wanda ita kanta sai da ta tausaya. Gefen gadon ya koma ya zauna ya dafe kansa da ke tsananin ciwo hade da ciwon mara mai tsanani da ya bakunce shi, kodayake ya dade yana damunsa a kwanakin nan tun dawowarsa gidansu da Hafsat din da yake yawan gani kodayaushe tana gilmawa ta gabansa. Itama Hafsat din shiru ta yi, tayi tsuruu a gefensa kamar wadda ta yiwa sarki karya. Tana farin ciki da kubutarta, amma hakika tausayin Abdulazeez ya mamaye farin cikin. Ya cancanci samun farin ciki komai kankantarsa a yau daga gare ta. Duk da tana da tabbacin ko lafiyarta kalau ba za ta amince ba.
A hankali ta iso inda yake zaune a gefen gadon kafafunsa a kasa, ta kwantar da kai a bayansa. Cikin sanyin murya ta ce,
Im sorry.
Bai ce mata komai ba, wayarsa da ke ta kuwwa a kan bedside din ya dauka. Ya yi sliding kiran ya amsa.
Tunda ka san ba halina ba ne in zo in kuma fitan, kasan ina da uzuri ne. Ya jefar da wayar ya janyota ta dawo jikinsa. Wani irin kallo yake binta da shi da sai da ta kasa jurewa ta rufe fuskarta da hannunta daya.
Dole ki rufe fuska tunda kin san kin yi nasara a kaina, Mammah ta san haka ki ka girma kuwa Hafsah? Ita kullum tana miki kallon babynta a Jeddah acikin incubator? Anyway I appreciate, and I must thank Hafsah for this great moment.
Wata irin kunya da ba ta taba ji ba a rayuwarta ita ta lullube ta a wannan lokacin. Mikewa ta yi tana kumburi irin na nade tabarmar kunya.
Please Yaya Azeez mu bar wajen nan, ba mutuncinmu ba ne.
Ni mutunci na ne. Ya fada bai da alamar tashi sai wani lafiyayyen kallo da yake ta binta da shi.
Abubuwanta ta soma tsincewa a dakin wadanda yayiwa fatalin Allah-tsine, ta daura kallabinta ta yafa mayafi ta juya masa baya. Dariya ce ta kama shi ganin zip din rigarta ta baya bakidayaa bude, ya ce. InnaHafsatu saura zip din.
Hannu ta kai ta shafo wajen. YaIlahi! Wata harara ta juyo ta zuba masa tamkar idanun sa fado.Tasowa ya yi cikin takun nutsuwaya iso gabanta, idonsa kan bakin data ke ta turowa gaba.
“Lemme help…..(bari in taimaka).
Ta zumburo baki tareda ja baya. Bana so, ka bari!. Ya daga hannuwa sama daga taimako? Da na sani na yi shiru Mammanki ta gyara miki da kanta. Ya fada yana ja da baya cikin hadiye dariya.
Kansa ta yi da wani sabon kuka da ya zo mata nan take kamar mai shirin rufeshi da duka, data tuno rashin kyautawar data yiwa Mammah. Ya kuwa yi mata wata irin kyakkyawar runguma ya hade bakunansuin no space measure.Hawayen ya shiga daukewa…, ko kadan bai barsu sun sauko kan kundukukinta ba…. Komai ya dawo sabo kamar baa yi shi ba. Hafsat ta tausayawa kanta a wannan rana don har azahar Abdulazeez bai barta ta huta ba,amarcinsa yake yiiri-iri kamar babu gobe. Sai da ya samu relief daga tsofaffin damuwoyin sa da suka dade yana fama da su a kan Hafsah sannan da magiya da roko har da hawayenta ta samu ya amince zai maida ita makaranta.
Test dai har biyu ta yi asararsu, amma Abdulazeez ya ce mata ladan da ta samu ya ishe ta shiga aljannah. In dai miji ke wa matarsa sanadin shiga aljannah, yau ya daga mata ta shiga cikin aminci Ud-khuluhaabissalaam!. Ya fada da larabcin da har yau bai manta ba. Wanda yasa Hafsat tuno birnin Jeddah with nostalgia.
Suna hanyar NILE ya na tuki, batareda ya juyo ya dube ta ba yace,
Karfe nawa za a dauke ki?
Ciki-ciki tace. Sai 5pm Mommah za ta zo.
A gaban department dinsu ya ajiye ta, kafin ta fita ya rike hannunta. Ta juyo ta dube shi idanunta narai-narai, sunyi wani irin maiko da kyalli, wani yanayi da yake matukar son gani cikin idanunta,a zuciyarta ta ce, “Oh ni! Me kuma ya saura?
“Take a look into my eyes Hafsah! Will you now believe it if I say I really love you?(kalli cikin idanuna Hafsah, yanzu zaki yarda dani idan nace ina matukar sonki?
Daga masa kai ta yida sauri sabida a kagare take data fita, sama-sama ma taji me yake cewa, hankalin yayi gaba, bata son a ja zancen da tsawokada wani tsautsayi ya gifta Mammah ta zo da wuri, ya cika hannun nata don ya fahimci yanayin da take ciki. A zuciyarsa yana jinjina kaunarta da uwarta da gudun zuciya irin nata, wani alamari da shi yanzu anzo gejin da bazai iya ba.Mammah ta kure duk wani hakuri da kawaicinsa.
Na gode Hafsatu, me ki ke so in ba ki? Ban taba ba ki komai ba.
Murmushi ta yi har hakoranta suka bayyana, Zo in rada maka.
Ya kuwa sunkuyo da kunnensa daidai bakinta. Keep loving me till eternity!.
Kafin ya farfado daga duniyar shaukin da kalamanta suka jefa shi ta dauke jakarta ta fice. Rufo masa k
ofar ta yi, ta yi waving dinsa sannan ta juya da dan gudu-gudunta ta barshi da murmushi. Ya dade bai iya tuka motar ba, sabida wata irin kasala da ta bakunce shi. Tana cikin rukunin matan da yake fatan samu a rayuwarsa, har fiye da yadda yake burin samun. Ashe baa judging mace a fannin auratayya da zurfin ilmi, yawan shekaru da wayewa? Halitta ce kawai ta ubangiji. A yau ya kara cursing perceptiondinsa.
Sai laasar ya koma office. A nan ne ya tadda dalilin kiran da su Barrister Abdallah ke ta masa yana kashe musu waya. Abin alkhairi ne ya same su su goma a ofishin. Takarda ce ta fito ta tura su karo karatu (L.LM) daga (Federal Government) zuwa Amurka wanda zai dauki tsayin shekara daya kacal.
Kowa a cikinsu murna yake, ban da Abdulazeez Dakata, sannan tafiyar za ta kasance wata mai zuwa, lokacin da suke da shi na shirye-shirye kadan ne.
Shi tun tali-tali kasashen turawa ba sa cikin yan kayansa. Baida shaawa a kansu. Yana da burin tafiya (L.LM) ko ba su tura su ba amma accross Nigeria. Duk wani pride dinshi yana kasar haihuwar shi. Ko zuwa graduation din Ismael da Usman a kan dole ya je saida Daddy ya nuna bacin rai. Don haka su ESQ Ahmad sun yi mamakin ganin babu wani farin cikin abin a tare da shi, da suka dame shi da tambayar dalili ya ce ba damuwar kowannensu ba ne.
Karfe biyar na yamma Hafsat ta fito daga dakin karatu ta doshi inda Mammah ta yi parking tana jiranta. Ta bude ta shiga suka yi wa juna dan murmushi kafin Hafsat ta ce.
Yaya B.P din Mommah? Hope doctor bai ce yana sama ba?
Ta tuka motar suka fita daga parkinglot ta hau kwalta sosai, sannan ta juyo ta dubi Hafsat fuska ba walwala. Yaya test din?
Shaf! Ta manta da zancen wata test duk da Mami ta gaya mata an yi, kuma ba ta samu halin taimaka mata da ko attendance ba, lecturer din ya kasa ya tsare. Inda-inda ta hau yi saboda a rayuwarta bata saba karya ba. Karya wani abu ce da Mammah ta rayu tana gaya mata mai yin ta dan wuta ne. Amma hakika yau zatayi karya ga Mammah, a inda bata da mafita.
Au… am, Eh….test din.. test din ba wuya sosai. Ta samu kanta da fada cikin daburcewa. Wanda ko daga yanayin data yi maganar ya gama fallasa ta. Sabida abune da baa raine ta da shi ba take kuma feeling guilty na yinsa tun kan a gane ba gaskiyar ta fada ba.
Abin da ba ta sani ba tunda ta shigo motar jikinta kamshin Abdulazeez yake yi. Duk cikin yayanta ba mai amfani da wannan turaren sai shi, ya dade da kame komai nasa, sannan ita Hafsan bata fesa turare in za ta fita. Bayan haka Salisu ya koma ya tadda ta a asibiti da wuri, ta ce ya aka yi ya yi sauri haka? Ya ce ai sun hadu da Barrister ne ya ce ya koma shi zai kai ta. Ta rasa me za ta yi wa Salisu ta huce don haushi da takaicinsa, don haka uffan ba ta ce masa ba.
Wani abun personal ne, kuma shi Salisu ya kwana da sanin waye Abdulazeez a gidan, kuma ya san Hafsat wace ce a gare shi. Ko babu aure ya isa ya hana Abdulazeez tuka Hafsat? Don haka ta kowanne bangare ta mishi uzri, amma za ta yi maganinsu. Kanta na bisa titi tana tuki.
A ajandar AUREN KWANGILAr naku, har da cewa bayan ya maida ke makarntar, ya kuma kore kin, zai dawo kuma daga baya ya hana ki karatun?
Hafsat ta ji numfashi ya dauke mata na dakika biyu. Tayi kokarin hadiyar miyau amma makoshinta taji ya bushe kyamas.
Wannan test din guda biyu, kin rubuta su ko ba ki rubuta su ba? Ta sake fada cikin son controllingtsananin fushin da yake yunkuro mata. Wani tashin hankali ya ziyarci Hafsat, sai ta ke ganin ai kamar Mammah ta ga komai ma a kan idonta. Sunkuyar da kai ta yi, wata matsananciyar kunya da guilty conscience na lullube ta. Mammah ta yi kwafa, bata kara magana ba haka Hafsat din, har suka isa gida. Ta kasa daga kai balle ta dubi Mammah.
Suna zuwa gida Mammah sassan Daddy ta wuce ita kuma ta yi dakinta, bakin gado ta nema ta zauna a kasalance ta yi tagumi, ba ta da kalmar kare kanta yau a wurin Mammah, a kan-kanta ba ta da bayanin da za ta yi mata don ta yarda da ita, ta yarda ba da son ranta ba ne ta bi Abdulazeez, tana kan biyayyarta, ya fi karfinta ne da duk wani kokarinta na tsayawa a bangaren Mammah, sannan zuciyarta mai tsananin laushi ce a kansa sai dai idan ba su kebe ba.
Ba ta dade da shiga falon Daddy din ba Dr. Hamza ya fito daga bedroom dinsa ya ganta a falon a zaune. Kallo daya ya yi mata ya fahimci ranta a matukar bace yake, kuma ba abin da ke bata ranta a dan tsukin sai lamarin Abdulazeez da Hafsah! He is tired of all these yau zai kawo karshen komai.
Tun kafin ya zauna a kujera ta soma.
….Daddy ni fa na gaji da zaman Abdulazeez a gidan nan, ina tufka yana min warwara, sabida ya mayar da ni marainiyar wayonsa. Na samu matsala ban samu kai Addah makaranta da kaina ba, na tura Salisu ya kai ta, ya tare su a hanya ya dauke ta tun safe har yamma ban san inda suka je ba. Tana da test har biyu bai barta tayi ba.
Ya sake ta kamar yadda ya yi wa kansa alkawari, kun mayar da aure ban hana ba don an fi karfina,nace kome sai sanda na ga dama kun amince.To binbinin na menene?Karatun ma marufar asirin diya mace ba za ta tsira da shi ba tunda bata da soyayyarsa? Bana zalunci, bana goyon bayan yinsa! Ka ja masa kunne wannan ya zama na karshe da zai kara shiga harkar Hafsat.
Iyakar bacin rai ran Dr. Hamza ya baci, amma ya yi kokari matuka ya daidaita muryarsa yadda bacin ran bai fito a cikinta ba. Ya lalubi kujera ya zauna.
Da izinin wa ki ke zirga-zirgar tukin mota kai Hafsa makaranta da dauko ta? A kan karan-kanki kina tuka mota ki je unguwa?
Ta yi shiru ba amsa. Wani irin nutsatstsen murmushi ya yi ya dube ta sosai.
Akwai mai zalunci ma irinki a duniya?
Zaro idanunta tayi baki daya a kansa, bai damu ba da yadda tayin ya gyada kai cikin karfafa ingancin furucinsa,ba tare da ya bata damar cewa komai ba ya cigaba.
Yara na son junansu kin dage sai kin raba su. Ba kya tukin mota amma saboda kiyi zalunci kin jureshi yanzu. Ita Hafsan ki tambaye ta mana da wadanne kafafun ta fita daga motar ta bi shi? Ko aka ya dauke ta ya canza mata mota? Ita da bakinta ta gaya miki sun je wani waje ba makarantar ba ko kuwa kwakkwafinki na balai?
Kin san Allah Maryama! Ki fita daga idona in rufe. Daga yau ban yarda ki kara tuka mota ba. Ban yarda ki kara kawo min zancen Hafsat da Abdulazeez ba in ba na alheri ba. Tunda ke ba kya afuwa. Shin da Allah ba ya afuwa a gare mu ga tarin laifukanmu, da mun kawo yau ne? Shin ke ba za ki yi afuwa ga dan cikinki ba ko don kwadayin rahmar Allah a gare shi? Ya biki, ya biki, ya biki har kin kai shi gejin da zai soma fandare miki. In bai saci matarsa daga wajenki ba, da ki ka bi ki ka kankane masa, zina ki ke so ya je ya yi ko me?
Please ina son kadaici, hayaniyarki ciwon kai ta ke sa mini, ba don na tsufa ba da na dauko budurwa sabida tension dinki a kwanakin nan da ke neman nima ya hauhawar da jinina. Ko ba komai na san in na dawo zan samu mai yi min sannu da zuwa. Saboda auren yayanki duk kin lalata kyautatawar da ki ke yi wa naki auren. Don Allah je ki daga cikikiyi hayaniyarki ke kadai.
Rai bace ta wuce ta bar dakin, ta sanya kai za ta fita, Abdulazeez na sanyo dogayen kafafunsa zai shigo saura kadan su yi karo. Da sauri ya ja baya ya ba ta hanya. Mugun kallon da ta jefa masa sai da gabadaya hanjin cikinsa suka hautsina. Ya tabbatar ta bare da shi ne, amma da wuya in Hafsat ce ta fada mata laifin nan da ya yi mata. Salisu ya fado masa a rai. Ya yi catching breath dinshi sharplysannan yayi saranda ya shiga falon Daddy. Yana shiga shi ma bai barshi ya zauna ba ya soma karbar nasa rabon don bai gama hucewa ba.
Kai da uwarka so ku ke ku kwantar da ni ko? Ina lallaba tsufana cikin koshin lafiya shi ne abin da ba kwa so ko? Tunda ta fada maka abin da ba ta so ka bari mana har sai ta sauko? Ka san dai ba za ta dauki matarka ta aura wa wani ba ko tunda ka maida ta? To gajen hakurin na mene ne? Ka ba ta lokaci mana tunda ka san yadda zuciyarta ta ke kamar ta kuturwa ba mai sa ta ba mai hana ta? Not even her mother! Idan ka kawo ni bango ni ma korarka zan yi daga gidan nan….
Shi dai ya zauna a kan kafafunsa ya nutsu yana sauraro. Sai da ya gama tsaf sannan ya kwantar da kai da murya ya soma ba shi hakuri. A karshen ban hakurin nasa yace.
Kuma Daddy ba wani waje na kaita ba banda makaranta…….
Dr. Hamza ya kara harzukowa cikin hargagi ya ce.
Na tambaye ka? Na ce tambayarka na yi? Ko bangon duniya ka kai ta ina ruwana ba matarka ba ce? Im talking about your mother, dole ka guji bacin ranta idan kana so ka wanye lafiya.
Hakuri ya ci gaba da bayarwa sai da Daddyn ya ce ya ishe shi, ya tashi ya ba shi wuri sannan ya mike. Sai kuma ya dawo ya zauna ya fiddo takardun sponsorship dinsu na tafiya karo karatu ya karasa a hankali ya aje masa a kan tebir. Ya shiga yi masa bayanin komai. A karshe ya ce.
Amma Daddy ni na yanke shawarar ba zan je ba, zan koma Ibadan na yi.
Wata harara Dr. Hamza ya watsa masa, Ibadan? Aah ODUDUWA! Wallahi ka ji na rantse ka tafi karatun nan ka gama, salon ka je ka kara lakewa wata yar Attorneys din ko dangin Yarbawa? Su baka surkullensu cikin abinci kazo ka daga mana hankali? To ka sa a ranka cewa, in ka ga ba ka tafi karatun nan ba, bana numfashi ne.
Jikinsa ya yi sanyi kalau, ya kasa tashi. Bakinsa ya shiga motsawa alamar akwai sauran magana a bakinsa. Daddy ya harare shi.
Me ya rage kuma?
Sunkuyar da kai ya yi, cikin fargaba ya ce,
Dama wai cewa zanyi wai…. ko in yi visa da Hafsat?
A nitse Ambassador Hamza ya dube shi, can kasan zuciyarsa tausayi ne fal! A hankali ya furta.
Ita kuma nata karatun fa?
Abdulazeez ya ji duniyar kanta ta tsaya masa cak! Da ya san abin da karatun nan zai zame masa kenan da baa fara shi ba. Shi ba abin ya ce zai nema mata wani a can ba shekara daya kacal zai yi. Ci gaba ya yi da zama ba shi da niyyar tashi. Tausayi ya cika zuciyar Dr. Hamza, daurewa kawai yake yi. Ganin Abdulazeez ba shi da niyyar tashi, kuma ana ta kiraye-kirayen sallar magriba ya ce da shi.
Idan zuwa lokacin uwarta ta sauko, zan duba possibility na zuwanta wajenka hutu har ka kammala, ka fada musu su fito mu yi sallah.
Godiya ya yi sosai, sannan ya bar dakin. Tare suke yin sallar magriba da isha wani lokacin in har dukkansu suna gida.
Saboda kunyar Mammah yau Hafsat kasa fitowa ta yi daga daki tun shigewarta. Abincin dare ma Baba Azumi ce ta kai mata.
Washegari Hafsat ta shirya tana jiran fitowar Mammah ta sauke ta. Shiru-shiru ta ji babu ko motsinta a gidan. Dole ta yi gammon kunyarta ta fito zuwa kicin. Baba Azumi ce kadai tana ta aikace-aikace, ta gaishe ta sannan ta tambaye ta Mammah, ta ce ita ma yau tun safe bata ganta ba kuma Daddy ya jima da fita.
Juyawa ta yi zuwa dakin Mammah, a darare ta yi sallama ta shiga. Fitowarta daga wanka kenan tana shiryawa. Gaisheta ta yi, ta amsa ba yabo ba fallasa, wannan ya ba ta karfin gwiwar cewa.
Mammah, dama na jiki shiru ne, na leka kicin Baba Azumi tace ba ki fito ba.
Ki je ku tafi da mijinki, nawa mijin ya hana ni kai ki.
Dan jimm! Ta yi, jin kamar cikin gatse ta fada, ta yi kasa da kanta, Ki yi hakuri Mammah abin da ya faru jiya wallahi….
Addah! Did I ask anything?
Ta girgiza kai tare da hadiyar miyau, mukut!Mommah to ai na ga kamar….kamar kin yi fushi ne?
Murmushin takaicinsu su duka biyun ta yi, sannan ta dube ta. In ba so ki ke yau ma ki bata min rai ba to ki wuce ki neme shi ku tafi. In kun ga dama ku wuce gidanku daga can. Im just trying my best to protect your dignity,in kuma kwato miki darajar ki da ya bi ya wulakanta sabida wata mace yar uwar ki da bata fi ki komai ba, amma na lura aikin banza nake yi. Adda kina da wayonki dana ke ganin baki da shi, tunda har kinsan ki yimin karya sabida Abdulazeez. Don haka bana cikin shaaninku, ku barni in yi alamuran gabana.
Kukan da ba ya yi mata wuya ta soma, Mammah ko ta kula, ta ratseta ta wuce zuwa closet dinta, kaya ta saka ta fito ta wuce ta gabanta ta bar mata dakin.
Makarantar da ba ta je ba kenan saboda rashin dadin zuciya. Inda Allah ya taimake ta ma ba su da gwaji, kuma lacca daya gare su. A yinin ranar bakidaya Mammah ba ta shiga harkarta ba, Azumi kadai ke kula ta, ita ma ta lura yau ta yi tsami tsakanin Mammah da yar gaban goshinta. Amma an ce fadan da babu ruwanka dadin kallo gare shi balle irin nasu, da in ka sake ka shiga koda da ba da hakuri ne kai ne da shan kunya.
Washegari bayan ta shirya ko breakfast ta kasa, labewa ta yi jikin tagarta sai da ta ga ficewar Abdulazeez daga parking space na gidan. As usual cikin shigarshi da ke tafi da imaninta;dark grey suit da farin tie a wuyansa rike da black robe dinsa da wig a hannu, ya bude mota ya shige. Ya ajiye su a kujerar gefensa ya gyara tie din wuyansa ta hanyar sassauta shi, sannan ya kunna motar.Har ya bar gidan a kan idonta.
Ajiyar zuciya ce ta subuce mata, ba ta da idea na yadda ta yi kewarsa cikin kwanaki biyun nan. Mayafi ta yafa kalar atamfar jikinta ta dauko handbag dinta ta fito. A kicin ta tadda Mammah da Azumi ta gaida su. Azumi ta amsa, amma Mammah ciki-ciki ta amsa. Cikin marainiyar murya don Mamman ta ji tausayinta, ta ce,
Mammah ko Illaila yana nan? Zan je na roke shi ya kai ni makaranta.
Kamar ta rabu da ita, sai kuma ta ce, Ke ma kin san bacci yake, amma ai kina ji shi wannan din mai sammakon ya fita ko? Me ya sa ba ki fito da wuri kin bi shi ba?
Shiru ta yi, a ranta ta ce. Don kar in kara laifi. Sai ga Usman ya shigo, Mammah yake nema. Ya dube ta ya dubi Mammah da ke cin magani.
Ya aka yi ne senior Sis?
Mammah ta ce, Ka sauke ta makaranta in hanyar za ka yi.
Ya fada mata sakon da ya kawo shi, ya ce su je ya kai ta.
Kwana uku Usman ke kai ta makaranta ya dauko ta, ta ki yarda ta hadu da Abdulazeez ma, duk dai don kada ta kara laifi a wurin Mammah. Shi din kuma isvery busy shirin tafiyarsu kain da nain shi da colleaguesdinsa, wataran har tara na dare yake kaiwa bai dawo ba sabida cuku cukun visar su. Mammah ta san da zancen tafiyar, sai dai ba wanda ya ji ta bakinta a kai, ta ce da Daddy da ya gaya mata zancen Allah ya bada saa.
A cikin ranta damuwa ce tsantsa, kada kuma wannan karon ya je ya kwaso mata soyayyar baturiya.
Zuwa wannan lokacin ta sallama, ta hakura ta yi niyyar amincewa ta maida Hafsat gidanta bayan ta gama jarrabawar karshen semesterda za ta fara sati mai zuwa, sai kuma ga wannan zancen tafiyar ya taso.
Sati daya bayan haka suka wayi gari da baki na ba-zata, Malam Hashim Babbah Jimeta, uwargidansa Daada Zainabu da kafatanin iyalinsa maza da mata, masu aure da marassa aure. Wannan tafiya takakkiya ce ta godiya daga wannan zuria mai albarka zuwa zuriar Maryam Dakata da maigidanta tsohon Ambassador Hamza Atiku. Daga nan Abuja, Kano za su wuce gidan marigayi Malam Abdullahi Dakata. Daddy ya san da zuwansu don yana office Malam ya kira shi ya gaya masa tahowarsu, ya kuma kira Mammah a take ya gaya mata. Nan da nan ta sa maaikatan gidan maza na waje su bude sashen baki su gyara duk da kusan koyaushe a gyare yake. Ita da Baba Azumi kuma suka shiga kitchen. Hafsat tana makaranta sai gefen maghriba ta dawo. Tun daga gate ta fahimci gidansu a cike yake, motocin buses(Yola Express) har ukku, tana kuma iya shaida motar Babanta Sienna da motocinsu Uncle Sagir data Modibbo. Tun Usman bai gama daidaita parking ba ta fice saura kadan ta fadi. Shi ya biyo ta da jakar hannunta cikin gidan.