AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 4 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

                    Www.bankinhausanovels.com.ng 

Dauke wayar ta yi daga kunnenta na dan lokaci, tana mai karbar tasirin kalaman a cikin kowacce gaba ta gangar jikinta. Isthis what is calledLOVE? And the feeling of having it in return? In hakanshine soyayya ta hakika, to hakika ba abin da ya fi ta dadi da sanya nutsuwa a zuciyar dan Adam. Allah ya sani tana son Abdulazeez! Wayar ta mayar kunnenta, abin mamaki he is still onthe call.

Ya ce, Hafsa bude kunnenki ki ji

Kalaman da yake fada mata sun yi mata nauyi a cikin kwanyarta, wanda ya kai ta ga janyo hijabinta ta rufe fuskarta bakidaya kamar yana ganinta.

Mammah ta ba ta waya ne dama don Danta Abdulazeez ya kashe ta da dadadan kalamansa, ko don ya hana ta bacci da manyan maganganun sa? Ya yi formatting brain dinta ya zuba sababbin abubuwa da ba ta san da su ba a duniyarta?

Kin yi alkawarin duk ranar da muka hadu babu kunya? Kin yi alkawari it will bea day in history? In kin yi wannan alkawarin zan barki ki kwanta Hafsah kuma zan yarda in zauna!.

A yadda ta matsu da ta samu shakar numfashi yadda ya kamata, ba alkawarin da ba za ta iya yi masa ba yanzu. Don haka ta ce ta amince.

Ya ce, Then a good night kiss, irin na Rockview.

Wannan karon Hafsat ba ta da mafita banda ta kashe wayarta jin numfashi na neman fin karfinta. The Rockview memories overwhelmed her!Ita kadai ta ke murmushi mai zurfi bayan kashe wayar.

                  

Washegari sai da ta makara, makara ba yar kadan ba. Ana gab da rufe exam hall. Yau kam ta sa a ranta za ta kashe wayarta kafin ta kwanta. Abdulazeez a shirye yake da ya jawo mata dako (carry over) wanda ba zai taya ta wajen sauke shi ba. He is already what he wants to be in life! Ba ta tsammanin don ta zama mai (spill over) yana da damuwa. She is a goal oriented like him. After all zai iya jiranta ta gama su dora a inda suka tsaya tunda an sakar musu mara yanzu babu tunani da fargabar ranar karewar KWANGILA!

Kin kunna wayarta ta yi har bayan kwana biyu. Dawowarta kenan yau ta shiga dakin Mammah don ta sanar da ita ta dawo. Tana shiga ta ce. Kin ga Allah ki kunna wayarki ko wannan dan Anacen ya shafa man lafiya. Ina dalili zaabi a uzzire ni? Ni kuma ba zan ba ki tawa ba kamar yadda ya bukata, don ban ga dalili ba.

Murmushi ta yi ta juya ta fita a ranta tana fadin, Mammah kyale Yaya Azeez kawai. He just want me to score zero, ko in cika musu answer sheet da ABDULAZEEZ DAKATA .

Alhamdulillah! Yau Hafsat-Suhaana ta zana last paper dinta. Ta gama zangon farko na year 2, sun samu hutu na tsayin sati hudu, idan sun dawo za su shiga zango na biyu na (level two). Ta yi baccinta yau ta hantse har da munshari.

******

Gaisawa suka fara yi ita da Hajiya Halima matar Controller, sannan Mammah ta fadi makasudin kiran nata, Ki turo min babarbariyar da ki ka turo ta yi wa Hafsat gyaran amarci Fannah takeko wa? Daga gobe zuwa jibi don Allah Maman Saadiyyah.

Toh!Tantabara sarkin soyyyah! Tsohuwar zuma ce ta tashi za a yi wa formerAmbasada gyara?Ko kuwa Hafsat ce ta haihu har zata koma babu gayyatar suna?

Ko daya. Addar nake so a kara gyara min kawai, ta koma masha Allah fiye da gyaran farko.

Dariya sosai Anty Halima ta yi. Ka ji uwa, kuma surukar zamani, wato a gyare miki yarki Abdulazeez ya sha shagalinsa!”

Salati Mammah ta saka tare da runtse ido. Ni Hajiya Halima yaushe za ki girma ne? Yau in da ni na ce zan yi ki ce na addabi tsoho, na ce a yi wa yara shi ma ya zama abin magana?

Sosai Halima ke dariya, To ita Hafsat har yau ba bayani ne? Ana neman shekara ta biyu fa.

Ki sanya su a addua komai sai Allah ya nufa.

Haka ne. Inj Hajiya Halima, Kada ki damu, Hafsat sai ta koma tamkar jiya aka kai ta. Zan yi magana da wadda ta yi mata na aure goben nan zan sa a kawo ta, ta zo Abuja yi wa yar Captain Bakari, kin san auren ya zo.

Au abin ya zo? Zumunci na da Haj. Munira ya yi rauni ne, tun dawowarmu nan ban samu na ziyarce ta ba, kuma ba ni da lambar wayarta, bana jin ta san mun dawo ma, ta zo wajena a Belgium da suka kai dansu karatu can. Tun daga nan ba mu kara haduwa ba.

Haka suka yi ta hira irin tasu ta aminai, sai da Hafsat ta shigo ta gaya mata ta yi baki, sannan suka yi sallama.

Mammah ta yi shiri kamar yadda ta saba duk dare ta nufi turakar maigidanta. Prof. Dr. Hamzah Dakata, agogo sarkin aiki wanda a gida ma ba ya hutawa. Bautawa aikinsa yake da karfinsa, lafiyarsa da lokutansa har zuwa lokacin marking takardun dalibansa yake yi. Hajiya Maryam ta zauna a gefensa, sassanyan turarenta ya bugi hancinsa, dole ya aje biro ya dube ta da sassanyan kallo, Maryama Amarya, kuma uwargidan Hamza Atiku ya aka yi ne?

Dariya ta yi ta juya masa idanu, Zuwa na yi neman alfarma, a yi wa Addah visa ta tafi America.

Hannayenta biyu ya riko cikin jin dadi domin hakika ta yi masa ba-zata. Bai zaci za ta barta haka da wuri ba duk da ya san za ta barta din, Sun samu hutun ne?

Eh, na sati hudu. A yi da gaggawa don ta samu ta yi ko sati uku ne. Jikinshi ya janyo ta yana fadin, Mairo yar albarka, na gode, nagode!.

Hajiya Maryam ta san Ambassador yana son Abdulazeez tun yana karami, amma ba ta kara sakankancewa da kaunar ba sai yau. Tukwicin soyayya mai yawa ta karba, har da kujerar makkah. Ya ce dukkansu su je su yi umrah, Suhaana ta tafi wajen mijinta sun dade rabonsu da Saudiyyah.

Don haka gabadaya gidan ba wanda ba a hada da passport dinsa ba. Haleem ne ya kai Hafsat yin tata visar babu wani cikakken bayani, shi Daddy yasa yayi processing visa din kagin su mika, duk da shima bai san me iyayen nasu suke shiryawa ba, an umarce shi ne kawai da ya ciccikeapplication din ya hada da informations din Abdulazeez wandaDaddy ya shi ya kuma ya kaita thumbprint. Daga nan ya mika nasu wajen yin na Saudiyyah. 

A ranar mai gyaran jikin ta zo da yamma ta fara yi mata. Ta soma ba ta wasu abubuwa na ci da sha, a take ta tuno farkon aurenta, ta kuma tuno Daada, the same da abubuwan da ta dinga ba ta da za ta dawo daga Jimeta tana zubawa a shara a boye. Zuwa yanzu kuma ta yi wayon fahimtar mene ne su da amfaninsu ba kamar lokacin aurenta ba. To ita da ba ta da mijin amfanin me za su yi mata? Daada ta ce na gyaran aure ne.

Kwanaki hudu ta diba tana zuwa ta ce ta gama, sai wanda ta ba ta ta ce ta ci gaba da sha da kanta da turare na tsugunno. A washegari Mammah ta ce ta shirya za ta je Yola ta kwana biyu tana dawowa za su yi tafiya. Ta yi murna sosai, she cant wait to see Daada , Malam Babba, Abba, Imamu and co. Usman ne ya kai ta filin jirgi ya yankar mata ticket-to Yola da yar kankanuwar trolley dinta, wadda ta zuba kaya saiti uku kacal, tana rataye da matsakaiciyar handbag(vintage) da takalmin ta mai tsayin dunduniya.Sanye da wani tattausan leshi ruwan zuma da aka yiwa dinki (fitted gown)ta rufe jikinta da yalwataccen mayafi kalar kayan jikinta. Idan ka kalle ta ba za ka iya jurewa ba sai ka waiwayo ka kara sabida kyan da ta yi. Kwarjini na zuba, haiba da kamala na magana da kansu. Hafsat Hamza Atiku Dakata kenan. 

Wadda bullowar iyaye da kakanni na jini bai sa ta sauya identity dinta ba. Wanda
kowa ya santa da shi yake kuma tubuce a takardun karatu dana haihuwarta. Ba zai ma sauyu ba, ko zai sauyu babu mai canzawa, (not even Dr. Bashar), ga kuma AURE da ya kara tiding dinta ga wannan identity din na wannan family mai albarka. A cewar Dr. Bashar.Su din a cikin rayuwarta ba komai bane facestrangers. Ta kara rike su, ta kaunace su cikin amana, ta zauna da su saboda Allah, mutane irinsu tsiraru ne a cikin alumma.

Imamu ne ya zo daukarta a filin jirgi. Murna kamar su hadiye juna. A kind of brother-and sisters love mai karfi ne a tsakaninsu, fiye da Abdurrahman da Yaya Modibbo. Kai tsaye DEMSAWO suka nufa. Malam Babba na lazumi yana hadawa da gyangyadi a falonsa, Hafsat ta lallaba ta zauna ta jawo tarin gemunsa. Firgigit ya bude ido sai ganinta ya yi a gabansa kamar a mafarki. Mutsittsika ido ya yi ya tashi zaune, Hansatu an onbo (ke ce kuwa)?

Ba wai don ta ji fulatancin ba fahimtar abin da ya ce kawai ta yi, Ni ce nan, ko ba ka soganina ba in koma?

Hannunta ya riko ta ga alamun rauni a tare da shi ba kamar zuwansu Abuja ba.

Ya ce, Wane ni in ce ki koma? Murna na yi sosai da ganinki, kwanan nan ban cika lafiya ba, bana iya cin abinci, sau uku ana yi min karin ruwa, amma yau jikin da dan dama-dama. Jabbama-jabbama! (lale-marhabin), ya ya iyayen naki da Abdulazizua Turai? Dazun nan muka gama waya da shi, yau kwana uku a jere kullum sai ya bugo ya ji ya jikin nawa, dan arziki irin albarka.

Hafsat ta ji jikinta ya yi sanyi. Ita yau ta mance kwana nawa rabon da ta yi magana da shi balle common gaisuwa, ta ji shi din wane hali yake ciki saboda bokonta. Sai dai fa yana manne cikin kowanne bugun zuciyarta. Ta sa a ranta yau da kanta za ta kira shi ta wanke laifukanta, ba ta samu nutsuwa ba sai yanzu, zuwanta Jimeta ya kara jefa ta cikin nishadi. Ta san ita yau mai tarin laifuka ce a wajen Abdulazeez, wanda ba shi da gaskiya ma yana fushi a kai, balle wanda ya san an aikata masa shi ne da gangan?

Daada ce ta daga labule ta shigo da sallama tana dauke da karamar kwarya an rufe da faifai, ga ludayin duma bisa, da alama fura ce ko farau-farau ta kawo wa Malam din. Nuru a bayanta, ta kusa tsorata da ganin Hafsat, wadda a yau ta rikide mata Habibanta sak! Babu wanda ya gaya musu zuwanta, Imamu kawai ta yi wa waya, shi ma don ya dauko ta filin jirgi ne. Yana ajiye ta a nan babban gida ya juya ya ce zai kai ma Abba motar ne, su koma gida tare.

Hafsatu an on (ke ce?), ko kuwa Habibana ce ta dawo? Ta fada cikin raunin murya.

Hafsat ta mike ta karbo furar daga hannunta ta ajiye wa Malam, sannan ta kamo ta suka zauna. Gaishe ta ta soma yi sannan ta ce, Yi hakuri Dada, ban gaya muku zan zo ba, Mommah ma na hana ta gaya muku. Ina so in muku ba-zata, za mu yi tafiya ne duk gidan shi ne ta ce in zo in muku sallama.

Wurin Abdulazeez? Malam ya yi saurin tambaya.

Dan jimm! Ta yi kafin ta ce, Gaskiya Mommah ba ta gaya min ba, kuma bana jin wajensa ne, don bai dade da tafiya ba ai.

Suka shiga hirarrakinsu, Nuru na fadin, an je Abuja ba da shi ba yana makaranta, shi yana so ya je ya ga gidanta. Ta ce masa insha Allahu idan sun dawo za ta shirya masa zuwa Abuja. Nan da nan labarin zuwan Hafsat ya isa kowane sako na gidan, aka soma aiko mata da akusan abinci daga sassan matan su Yaya Tijjani, daga nan suka koma dakin Dada. Sai da ta yi sallah ta sake wanka sannan ta ci abinci. Cikin tarin abinciccikan kala-kala dashishi da miyar taushe wadda ta ji manshanu da naman rago ta zaba, wanda Sahura matar mai bin Habiba a haihuwa ta aiko. Sosai ta ji dadinshi sai santi ta ke zuba wa Daada. Ba ta tashi a wurin ba Mammah ta kira Daada tana ji tana fada mata ta iso lafiya. Suka yi magana wadda ba ta jin me Mamman ke cewa ta ga dai Daada na dubanta, sannan suka yi sallama.

Da ta gama cin abincin daki-daki ta shiga ta gaishe su, kowa a gidannan kamar ya hadiye ta, ta dawo suka ci gaba da hira da Daada wadda nan da nan ta ga ta shiga hada saiwoyi da hakukuwa iri-iri tana damawa da nono ta gama ta bata, ta kuma kasa ta tsare sai ta sha a gabanta. 

Amma dai Daada kina ganin yadda na ci abinci na koshi ko? Idan na shanye wadannan abubuwan har kofi uku ai sai in yi amai ko?

Daada ta daure fuska ta ce, O yara reta yahugo jemma a yara reta (To shanye rabi, zuwa dare ki sha rabi). Yadda ta ga tsohuwar ta tsume fuska ta san ko ta kara musawa ba yarda za ta yi ba, haka ta daure ta sha rabin. Duk da ranta ba ya son bauri, ga na Daada ya fi na Mammah rashin dadi.Da daddaren kuma wasu kananan yan shila guda biyu ta dafa mata kafin ta ci abincin dare. Hafsat kamar ta yi kuka, ta ce. Da na sani ma ban zo ba, ni tunda nake a rayuwata ban taba cin yayan kaji ba!

Daada ta ce. Ni kuma in bi ki da su har gidanku ba!

Tana cikin ci Abbanta ya yi sallama, har kofar dakin Daada, kamshin turarensa har ciki. Ya sha farar shadda, ya dora hula zanna bukar.Sardidin bafillace maabocin kwarjini da kamala. Nan ta samu hanyar gujewa yan shillan Daada don kuwa mikewa ta yi tana Abba-Jabbama.

Dariya ya yi ya ce, Fulfulde sai dan gado! Daada kina kokari fa waje koyawa Gaaji gida Ya shigo daga ciki. Daada na shimfida masa darduma.

Ture kwanon Daada ta yi ta koma wurinsa kamar ta shige cikinsa don So. Hira suke yi a kan karatunta da mutanen Abuja. Ya ce ta tashi su tafi gidansa gobe ta dawo. Daada ta ce. Aah.

Rokon Daada ta shiga yi ta barta ta je, Aunty Kubra ba za ta ji dadi ba ta zo garin ba ta je gidanta ba, amma Daada ta ki. Ita haka kawai ba ta son Kubran ta ankare da kakkarfar soyayyar da Dr. Bashar ke yi wa Hafsat, zuciya ba ta da kashi, duk da Kubran ba ta da aibu amma an ce ido guba ne. Tashi ta yi ta bar musu dakin, ta kuma ce da Abban akwai magani da Hafsan ke sha shi ya sa ta ce ba za ta samu zuwa yau ba. Amma gobe Imamu ya zo da yamma in Abban ya koma gida ya kaitata dawo da daddare tunda jibi da safe za ta koma. Abban ya gamsu da bayaninta. Duk da ya so su raba dare suna hira ne. Komai nata irin na Habibah ne, hatta muryarta wanda shi kadai ya san abin da hakan ke darsawa a zuciyarsa, sannan wata irin kauna yake yi wa yarinyar fiye da ta dukkan yayan da ya rayu da su har girmansu.

Abban na yin sallama da su ya fita, Daada ta janyo akushin da ta ture na yan shillah ta dangwara mata, Ya mu pat (cinye du).

Sai da ta cinye ta bar mata kasusuwan sannan ta shafa mata lafiya.

Da ta yi shirin kwanciya ta yi ta kiran layin Abdulazeez ba ta same shi ba, wayar ba ta shiga sam. Ko dai a kashe ta ke, ko kuma ya daina amfani da layin. Ta shiga damuwa ba yar kadan ba, ta dauki rashin kyautawar duniya ta dora wa kanta. Da za ta iya da ta tambayi Mammah, amma ko kusa ta san ba za ta iya ba. Ismaeel ne last hope dinta. Shi kuma ta san ta sake ta tambaye shi lambar Yaya Azeez sai ta gwammace kida da karatu. Sai ya shekara yana kasa ta a faifai. Haleem bako ne, a wajenshi ya kamata ta nemi lambar mijinta? Ai sai ya ga rashin hankalinta. Gara-gara Usman ba shi da matsala. Shi din ta kira, amma cikin rashin saa ya kashe wayarsa ya kwanta, dole ta hakura sai dai fa kafin wayewar gari har wata yar rama ta yi saboda damuwa.

Da safe ta je gidajen yan uwa tare da Nuru autan Daada, har gidan Yaya Modibbo, daga can suka wuce gidan Abbanta, Imamu na shirin zuwa dauko ta sai ga su sun shigo. Da mamaki ya ce Nuru wa ya kawo ku?

Dariya ta yi ta ceDan sahu, keke-napep mai dadin hawa fiye da mota. Tana gwada dadin ta hanyar kada yatsunta kusa dakunnuwanta, ya gane yau dai cike take da farin ciki mara misaltuwa. Dariya ya yi, ya ce. Ok, how do you feel it?

Ta ce, Dadi sosai-sosai, ko ta ina iska na buga ka. Ai ina hawa a Kano idan muka je kallon hawan sarki da sallah tare da yayan Aunty Murja.

Ta shiga ba shi labarin yadda suke zuwa Kano kallon durbar tun suna kanana. A nan falon suna ta hira Abba da Anty Kubra suka dawo suka tadda su. Abdurrahman a bayansu. Aunty Kubra ta yi ta ina ta-ka-sa-ka da ita, Imamu ya ce, Abba yau Kawu Nuru a dan sahu ya yi ta yawo da Ghaaji a Jimeta.

Abba ya ce. Nuru me ya sa?

Nuru ya ce. Ita ce ta dage, Daada ta ce ta jira Imamu ya zo ya kaita koina ta ki, zan maka waya ma ta kwace wayar.

Hafsat ta cuno baki irin na karshen shag
waba. Kuma shi ke nan ni ba zan dana ba Abba? A Kano ma in mun je Mommah ba ta barina, ni kuma ina so Abba.

Da sauri ya ce. Shi kenan Ghaaji, itsok, dama ina tsoron kar ki fado ne tunda baki saba ba, da anan ki ke ko kuma da ba a hana amfani da shi a tsakiyar Abuja ba da na saya miki wallahi.

Ta ce Ka saya min ka ajiye min a gidan nan, in na zo  a dinga kai ni unguwa.

Imamu ya harare taAmma dai ba ni ne direban ba ko?

Waye kuwa in ba kai ba?

Haka suka yi ta hira cike da kaunar juna har dare. Aunty Kubra da mai aikinta suna kitchen suna shirya musu abincin dare. Abdurrahman ya ce, 

“I will call Abdulazeez and tell him ya koyi tukin dan sahu da zarar ya dawo.

Dariya aka saka har Abban, sai wajen goma na dare Imamu da Abdurrahman suka maida ita Demsawo, Nuru a can ya baro ta tun magriba ya koma gida.

Dakin Mallam ta nufa suka sake sabuwar hira, a daren kuma suka yi sallama ya kawo adduoI masu yawa ya bata, ya ce ta rage barci ta yi amfani da rabinsa wajen neman kusanci ga Ubangiji da neman yardarsa da rokon soyayyar Ubangiji daga mijin aurenta. Duk son da miji ke miki ki hada da neman soyayyarsa wurin Ubangiji. Ta Ubangijin ita ce wadda ba ta da karshe, lokaci, yanayi, tsawon zamani ko yawan shekaru ba ya canza ta. Kullum sabuwa dal take komawa. Kada ki kwanta ki ce ai ke mijinki na sonki shi kenan, wannan kuskure ne babba. Kada ki nemi soyayyar miji a wuin kowa ki nema a wurin Allah, a cikin sujjadah da tahiyarki. Tashi ki je ki kwanta, Allah ya hada mu da alkhairi.

Kamar jiya, yau ma ta yi trying wayar Abdulazeez (not reachable). Haka ta hakura ta kwanta zuciya na zugi. Ta tabbata lafiya yake, har ta soma tunanin ko ya yi barring number dinta ne, don kuwa in har ta ji daidai dazu Malam ya ce sun yi magana, kamar ta ce ka ba ni lambar, amma ta yi kawaici ta kuma rufa wa kanta asiri ta yi shiru. Ta san halin tsohon nan sai ya binciki dalili. To ta ce masa me? Ni ce na daina magana da shi don ina jarabawa shi ne shi ma ya daina kirana ko me? Ita a kan kanta ta ji uzurin nata invalid wanda zai lalata shirin da ke tsakaninta da Malam Babbah har ta bar Jimeta.

Ta yi shirin tafiya, ta yi sallama da kowa. An fidda jakarta mota, Imamu na mota yana jiranta. Ta shiga turakar Malam su yi sallama ta karshe. Dattijon na kishingide a kan buzunsa ya tada kai da tum-tum ya yafitota da hannu. Ta karasa gefensa ta zauna, wani qoqo ya janyo da ke rufe a gefe da fai-fai ya bata, ya ce ta shanye. Rubutu ne an barbada wani koren magani a kai (ganyen magarya). Sai da ta shanye ya ce mata, Tsari ne, ba mutum ba ba aljan ba, insha Allahu.

Sannan ya kira sunantada nasabar jikinsa yadda bai taba yi ba. 

“Hafsatu yar Habibah jikar Hashim Babbah!!!

Dagowa ta yi da sauri jin wadannan tarin sunaye da yau Malam ya kira ta da su. Murmushi ya yi ya karbi qoqon hannunta ya ajiye, sannan ya ce.

 Kin san me ya sa na kira ki yau ta bangaren mahaifiyarki?

Girgiza kai ta yi, ya ci gaba, Saboda in tunasar da ke wani abu wanda ya kamata ki ke tunawa. Ambassador Hamza da maidakinsa Maryama ba su diga miki jinin haihuwa ba, amma tunda ki ke kin taba jin labarin ko katari da mutane irinsu?

Da sauri ta sake girgiza kai, Ko a labarin hikaya, musamman yadda zamani ya koma yanzu rikon dan wani naka ma ya koma sai yadda hali ya yi balle Da irinta a gare su. Duk da tana tune da yadda shi kansa Daddy ya kasa karbarta cikin ahalinsa a shekarun kuruciyarta sai daga baya, amma duk da haka dole a sara masa. Ya yi abin a jinjina masa cikin rayuwarta, musamman sunansa da ta ke bearing har gobe. Mammah kuwa ai fadin karimcinta wani abu ne da ba zai taba yiwuwa ba. Malam ya yarda ta ankara da abin da yake so ta ankara da shi a lokacin, sai ya warware gundarin abin da yake dunkulewa.

A ganinki da me za ki saka wa wadannan mutanen Hafsatu? Ko da da kwatantawa ne?

Girgiza kai ta yi cikin sanyin jiki alamar ba ta sani ba.

Ya ce, Sun dauki Dansu mafi darajar girma da kima a gare su sun aura miki. A lokacin da suke da tabbacin ba ki da kowa. Ba su da tabbacin halaccin samuwarki.Kin kasance mai kaskantaccen matsayi a garesuIn ke mai halacci ce da me za ki saka musu a halin yanzu da wannan Da tsaya tsayin daka ya nemo miki jininki a duniya ya damka ki gare su? Mahaifiyarshi ta yi fito-na-fito da shi don ya rike ki da daraja?

Hawaye Hafsat ta soma yi tana girgiza kanta, tana da amsar amma ji ta ke in ta fade ta ta yi kadan, gara ta bari Mallam din ya bata da fadi…Sai dai da za ta iya da ta ce da kakan nata…

In zan iya zan goya shi kullum! In zan iya zan daukaka darajarsa fiye da ta kowa cikin rayuwata In zan iya zan yi ta yi masa biyayya daga fitowar rana zuwa faduwarta a kan dukkan umarninsa. Zan yi ta yi masa addua a bayan dukkan sallar farillah ta In yi ta rokon Allah Ya yarda da shi, Ya buda masa, Ya kare shi daga duk wani abin ki,Ya sanya shi ya zamo miji a gareni har a aljannah!!!”.

 Amma ji ta ke in ta fadi hakan Malam zai ce ya yi kadan, don haka ta ba shi dama ta hanyar cewa ba ta da idea a kan hakan. Hawayen wata sabuwar kaunar ABDULAZEEZda bata taba ji bana malala a kan kundukukinta.

Sai ki rike musu shi da amana, ki so shi da tsarkakkiyar zuciya. Ki ba shi soyayya fiye da wadda suka ba ki. Ki zama garkuwa a gare shi daga aikata ZINA da sauran ayyukan alfasha. Ki zame masa sanyin idaniya ki kawo madauwamin farin ciki a rayuwarsa ki zamo masa bango, a lokacin da yake bukatar jingina. Ki yi masa biyayyah a kan kowanne umarninsa muddin bai saba wa iyakokin Ubangiji ba. Hafsatu ki nuna musu ke yar halal ce wadda ta san halacci da alherin da anka yi mata. Ba kuma ki da hanyar nuna hakan sai ta hanyar aurenki da Dansu, da irin rikon da za ki yi wa auren da mai shi. Na barki da wannan, ki kara fadada shi, haske kawai na ba ki, ki yi amfani da ilmin da Allah ya ba ki ki yi su a aikace. Tashi je ki. Allah Ya yi wa rayuwa albarka!.

Har suka zo filin jirgi Hafsat kuka ta ke yi, kukan da Imamu bai san dalilinsa ba. Ya dauka na kewar mutanen Jimetan ne, ya rarrashe ta har ya gaji ya rabu da ita. Ita kadai ta san me ta ke ji a zuciyarta, Abdulazeez kawai ta ke son gani, da wata irin soyayyamai yawa. She only wants to see him beside her at every blink of an eye (so kawai take ta ganshi a gefenta, cikin kowanne kiftawar ido) she wants to feel herself in his arms like before,and tell him how much she love him abubuwan da ta ke ji a lokacin masu yawa ne da harshe ba zai iya bayyanawa ba. Babban tashin hankalinta ba ta san yaushe za ta ganshi ba ya ce zai zo ta ce aah ya ce su yi magana su debe wa juna kewa, shi ma ta ce aah. Har ya gaji da bibiyarta ya yi barring dinta. Me ya sa wasu lokutan mu ke yin mistakes wanda bamu daukesu komai ba, kuma  ba ma sanin kuskure ne sai daga baya???

Cikin wannan halin Hafsat ta sauka a Abuja. Zuciyarta ta kara raunata da ta hango Maryam Dakata da kanta ba sako ba! Haleem ya kawo ta filin jirgin Nmadi Azikwe tana jiran isowarta kamar wadda ta dawo daga wata kasa. Ai tana isa gare ta cikin reception(she cannot control her tears). Fuskarta Mammah din ta saka cikin tafukan hannayenta tana tambayarta ko lafiya?, Kukan da ba ta san dalilinsa ba.

 To ko a sake yankar tikiti a koma Jimeta ne? 

Ta fada cike da damuwa.

Hafsat sai ta rungume ta cikin kuka ta ce. Ba fa Jimeta zan koma ba

Dariya ta yi ta riko hannayenta suka nufi mota, To ko in bude ciki ki koma???”

Haleem dake bayansu haushin maganganun su da shagwabar Hafsat ya ishe shi, ya karaso ya sha gabansu.

 Mammah, kin san Allah yarinyar nan don ta ga ba ki da babya gabanki ne ta ke miki shagwaba, she better brings you a baby soon ko yaya Azeez ya kara aure. Yayi maza ya koma bayan Mammah.

Wata harara ta juya ta galla masa, kuma har zuciyarta zancen ya mintsine ta. Gwalo ya yi mata ta bayan Mammah wadda ta hau shi da fada tana fadin ita ba ta son expensive joke haihuwa kuma ta Allah ce. Ita ma ta faki idon Mamman ta yi masa gwalo ga hawaye shabe-shabe a idonta,maimakon ta ba shi haushi sai ta ba shi dariya. Ba zai iya tuno yanayin kwayar idanunta ba sanda ya ce “Yaya Azeez
ya kara aure!.

Azumi na ta oyoyo da dawowar Hafsat, ta cika ta da abinci kala-kala. Ismael ya ce, Ina tsaraba?

Tulin kayan da Daada ta hado wa Mammah ta nuna masa. Da kanshi ya hau budewa yana ware komai gefe, akwai kindirmo sabo fari sol a cikin sabuwar farar jarka, akwai sabuwar ‘maasa da kuli’ fal a leda, su ya kinkima ya yi kitchen da su ya bar sauran tarkacen a nan, sai Azumi ce ta kauda su ta kai wa Mammah komai inda ya dace, Ismael ya ciko plate da maasa da kuli ya zo falo yana ci kenan Usman ya shigo, Shagali! Yar fillo ina nawa?

Yamutsa fuska ta yi, 

Ni ba yar fillo ba ce.

Ya ce, O.k Toh  Lemme say Jimeta Lady a zamanance. Yayi???.

Kafin ya rufe baki Baba Azumi ta kawo masa nasa Masan shake taf da plate.Bayan kulin ta yanka cabbage da cucumber akai. Da godiya ya karba ya ce. 

Baba Azumi, Allah ya nuna min aurenki!

Me za su yi ba dariya ba har ita din. Azumi ta rangwadar da kai ta ce, Mujaddadi (Usmanu) mai babban suna, burina in ga naka kafin in ga nawa. Ya ce, Insha Allahu har liki zan miki wajen dinner.

Mammah ta shigo falon tana fadin Hafsat ta je ta kwanta ta huta, kuma su daina kwarzabar mata Azumi. Baba Azumi ta ce, Jin dadina da farin cikina in gansu haka dukkaninsu a gabana muna hirarmu, ina tuno kuruciyarsu ta Jeddah da Beljiyan.Rai ne, watarana babu shi!.

                      *****

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *