AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 6 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Bayan sallar isha Mammah ta tadda Hafsat a dakinta, kayanta ta ke gyarawa cikin wardrove wadanda ta dawo da su. Janye ta ke da akwatuna biyu masu matukar kyau. A tsakar dakin ta zube su ta ce ta bude ta duba wanda bai mata ba ta aje a bayar a Kano. Dinkuna ne yan uban-ubansu daga atamfa, leshi, material zuwa ready made na voils din zamani da mayafansu. Hafsat ta hau dagawa cike da shaawa ba wanda ba ta ji ba ta so ba, amma don kada ta yi hadama sai ta ce a raba biyu a bayar din. Mammah ta ce.
Dama mace tana kyautar da manyan kayan lefenta?? Cikin kayan lefen da kuka tsibe a Sun-City’ ne nasa aka dauko min na tsince manyan na bayar aka dinka miki.
Kunya ta ji, ta rage murnarta a kan kayan, ita ta manta da wasu kayan lefe. Mammah ta juya ta fita tana fadin ta je Daddy na kiranta.
Tsallake komai ta yi ta yafa yalwataccen mayafi ta nufi sassan Daddyn.
Da sallama ta shiga, Yau wace rana Daddy ba ya aiki a takardu, News yake kallo? Hafsat ta ce a zuciyarta.
Amsa sallamarta ya yi, ya kuma umarce ta da ta zo gefensa ta zauna. Abin da ya kara mata jin nauyinsa don ba za ta iya tuna rana ta karshe da ya ce ta zo kusa da shi ta zauna ba. Cikin matsanancin ladabi ta bi umarninsa, sannan ta gaishe shi. Ta lura yau Daddy cikin faraa yake sosai, ya ce, Suhaanah an gama jarabawa lafiya, sai hutu ko?
Murmushi ta yi, ta ce, Ai hutun ba yawa Daddy, har mun ci sati daya.
Gyada kai ya yi, ya ce, Mammanki ta gaya miki za ki bi mijinki ki karasa hutun tare da shi?
Da sauri ta dago sai kuma ta tuna da wa ta ke magana, ta yi maza ta sunkuyar. Mafarki ta ke ko idonta biyu? Ko dai cikin mafarkanta ne masu nuna mata Abdulazeez a dan tsukin wadanda suka zame mata jiki a yanzu? Ajiyar zuciya ta sauke a hankali, kafin ta girgiza kai ta ce masa.
Aah, ba ta yi min zancen ba.
Cikin kulawa ya ce, To sai ki je ki hada abin da za ki bukata, Im sorry you areto fly alone (ke kadai zaki tafi), na san za ki iya. A rage cost din dan rakiya, mu ma kuma za mu tafi umrah gabadaya duka a goben, amma za ki riga mu tashi. Za mu tashi Saudiyyah karfe biyu na rana, ke kuma za ki tashi zuwa America sha biyu na rana. Ungo nan. Ya miko mata passport dinta da tickets a tsakiyarsa. Jiki a sanyaye Hafsat ta karba ta yi godiya, za ta mike ya ce, Kada ki damu direct flight na nema miki har can babu (transit) kina sauka kuma zai dauke ki, ya san lokacin tasowarki da sauka. Duk da haka ki kunna wayarki da zarar kin sauka.
Hafsat ta rasa a wane yanayi ta ke jin kanta, farin ciki ko taradaddi? A haka ta isa dakin Mammah. Daga bakin kofa ta rabe kamar mara gaskiya. Mammah ta yi kamar ba ta ganta ba, ta ci gaba da gyara kayanta cikin closet dinta. A ranta ta ce, Gulmar banza, bayan ji ta ke kamar ta goya ni.
Hafsat ta gaji da tsayuwa don kanta ta karaso ciki, a gefen gadon Mammah ta zauna ta dukar da kai. Ba ta ce mata komai ba yau za ta ga karshen fillanci. Ita da kanta shirun ya dame ta, ta motsa bakinta amma ta rasa jumlar da za ta hada wadda za ta bada maana. Tausayinta da kaunarta suka cika zuciyar Hajiya Maryam, irin macen da ta ke yi wa yayanta fata da buri kenan, mace mai kawaici, addini da alkunya. Yanzu fatanta yana kan Ismael da Usman Abdulazeez ya gama dacewa.Sai dai ga dukkan alamu burinta a kan Usman da Haleem zai cika, Ismael kam ya ce sai irin wadda yake raayi shi ba Yaya Azeez ba ne. A wannan karon ta sanya a ranta ba za ta takura wani a cikinsu ba kada a zo a samu irin matsalolin da aka samu a na farko ba don Allah ya nufa auren rayayye ba ne, kuma aka yi saa suka kaunaci abin daga baya. Da saki uku Abdulazeez ya yi kuskuren yi ba ta san ya za ta yi da kayan nadama ba, da kallon Hafsat a gabanta matsayin bazawara a shekarunta da ko ashirin ba su kai ba.
Don haka tsakaninta da yan baya addua ce da fatan alkhairi babu tursasawa. Yanzu kam hankalinta ya kwanta, zuciyarta cikin farin ciki ta ke da wannan buri da Allah ya cika mata na sanya Hafsat-Suhaana cikin ahalinta, tsatsonta, jininta, kuma uwa ga jikokinta na farko. Su Ismael su yi yadda suke so za ta bi su da addua.
Karasowa ta yi gabanta ta cire mata tagumin da ta yi. Hafsat ta dago ta dubi Mammah, sai ta ji hawaye sun ciko idanunta. Ba ta san ta ina za ta fara cewa za ta yi kewarta ba. Ji ta ke kamar yanzu ne karo na farko da za ta bar gida zuwa gidan miji kamar ba a yi hakan a baya ba, kamar ba yan satittika aka ce ta je ta yi ba! Kamar idan ta tafi ba za ta dawo ba take ji!!! Ba ta yi aune ba sai hawayen suka balle. Salati Mammah ta yi duk da a hankali ne, ta ce, Ko ba kya son zuwa ne Addah? In ba kya son zuwa babu komai, ki yi zamanki har ya dawo, amma sai dai ki tafi Kano tunda ba a yi visar Saudiyyah da ke ba, Azumi ma Sokoto za ta.
Hawayen ta share da sauri, Aa, Mommah. Murmushi ta yi, da ma tsokanarta ta ke yi don ta ji cikinta ne. Ta ce To ai kukan da ki ka zo ki ka tasa ni a gaba kina min sai ki tada min hankali, in ba hakan ba ne mene ne?
Hawayen ta ke ta gogewa da gefen mayafinta. Mommah, ina tunanin yadda zan zauna a wani wuri babu ke ne.
Dariya ta yi. Da ki ka zauna a gidanki tsayin shekara da watanni ni na taya ki zama? Ki sa a ranki kamar unguwa ki ka je ki ka dawo, za ki dora daga inda ki ka tsaya. Sai dai wannan zaman zai kasance ba irin na baya ba. Shi wannan akwai focus, kuma komai ki ka yi a cikinsa kin yi ne don neman aljannah. Wancan kuwa na sabo ne babu lada a cikinsa sai alhaki. Ku rike istigfari koyaushe ki bi mijinki ku zauna lafiya. Gidana babu space na yaji tunda wannan karon ba ni na tursasa ku zama da juna ba,don haka bazan yi tolarating kowanne nonesense daga dayanku ba. Ku yi hakuri da juna tunda kun ce kun ji kun gani kuna son zama da junanku, sai a yi zama na soyayya da amana. Tashi ki je ki hada abubuwan amfaninki. Kayan da ki ke amfani da su duk ki barsu ki yi amfani da sababbin da na baki. Mu kwana lafiya.
Hafsat na shirya kayanta cikin babbar jaka tana hawaye. Haka kawai maganganun Mammah ke shawagi a kanta. Wadanda ke nufin wannan karon za su yi zama ne ita da Abdulazeez irin na kowadanne maaurata babu interference na iyaye. An ce kuma cikin zaman aure akwai kalubale mai yawa wanda duk son da ake wa juna sai an yi hakuri. Daya zai iya bata wa daya rai kuma dole ya yi hakuri. Ga Abdulazeez mutum mai wuyar shaani, abu kadan zai nuna ransa ya baci. Tana rokon Allah ya ba ta nasara cikin zama da shi ya dinga sassauta zuciyarsa a kanta.
Salisu direban Daddy shi ya kwashi dukkan jamaar gidan da kayayyakinsu a washegari zuwa filin jirgin saman Nmadi Azikwe. Ismael da Usman ne suka yi ta yi mata shige da fice na awo da immigrationcheck har ta shiga jirgi da kayanta bayan sun yi bankwana da juna.Ba ta dade da shiga jirgi ba su ma aka fara screening din kayansu. A kan idonsu jirginta ya keta hazo ya lula cikin sararin samaniya.
A lokacin ne Daddy ya fiddo waya ya kira Abdulazeez ya gaya masa tasowar Hafsat da lokacin da za ta sauka. Yadda ta ji maganar bagatatan haka shima ya ji. Amma ya yi kokari ainun ya rike kansa da reaction dinsa, ta yadda Daddyn bai gane yadda ya karbi zancen ba. Ya ce masa dai insha Allah zai je ya dauke ta a kan lokaci, sannan ya kara da godiya. Daddy ya juya ya ce da m
atarsa.
Kamar bai yi murna ba!.
Mammah ta ce.
Itama ai ba ta yi murnar ba, har da kuka, Oho su suka sani!.
*****
HADUWAR AMARYAR DA ANGON!
Jirgin Egypt Air ya sauke Hafsat-Suhaanah a birnin NewHaven din Connecticut da misalin karfe bakwai na dare agogon kasar Amurka. Jamiar da Abdulazeez ya zo, wato (YALE UNIVERSITY) tana cikin New-Haven din jihar Connecticut. A sannu ta biyo bayan jerin gwanon fasinjojin da ke saukowa daga matattakalar jirgi rataye da jakarta louis Vuitton a kafadarta ta dama. Bakar abaya ce a jikinta ta nade kanta da dan mayafinta. Fuskarta ce kawai a waje, ta yi fayau sabida baccin da ta sha a jirgi. Takalmin kafarta mai tsayin dunduniya ne siririya wadda ta daure igiyoyinsa a idon sawunta. Saukarta a sararin airport din Bradely International Airport ya tuna mata da abubuwa da dama; rayuwarsu a Belgium da kewayenta, bambancin ba mai yawa ba ne da nan.Amma in ka dubi tsakiyar idanunta za ka hango yar kankanuwar damuwa makale kyawawan idanunta wadanda bacci ya canza musu launi.
Shin Abdulazeez ya san da zuwanta? In ya sani da yardarsa aka turo ta? Shin wace irin tarba za ta samu daga gare shi? Ta yi masa wani alkawari mai girma da yau ce ranar cika shi Alkawarin cewa duk ranar da suka hadu; babu kunya a tsakaninsu….. And It will be a day in history! Yau ga ranar ta zo, amma ta zo a wani irin jirkice; Abdulazeez din yana fushi da ita.
A yayin da tata zuciyar ke cike taf da alamura masu wuyar fassaruwa;so much love, so much affection, so much devotion, so much emotion, so much respect for him and so much many more things!!!Ina ma ana dawo da hannun agogo baya? Da ta yi rewinding ta goge duk wani laifi da Abdulazeez ke ganin ta yi masa! Bata yi da gangan don ta bata mishi rai ba. Bata dauki hakan laifi bane sai da ya nuna bacin rai akai. Ina ma ya kasance cikin mutane masu saurin yi wa abokan rayuwarsu uzuri kamar yadda kullum ita ta ke yi masa? Da Allah kadai ya san muhimmancin ranar yau a gare su.
Duk da dare ne amma koina haske yake da fitilu masu tsananin haske wadanda ko allurarka ce ta fadi za ka duka ka dauki abarka ba da wuya ba. Kanta tsaye ta ke tafiya janye da jakarta bayan ta dauko ta daga kayan da jirgi ya sauke. Kujerun da matafiya ke zama don jiran masu daukarsu ko hutawa ta nufa ta zauna da jakarta a gabanta. Alal hakika ta gaji tibis, kwanciya kawai ta ke son yi a lallausar katifa, ba ta tare da yunwa don ta ci abinci a jirgi, abincin ma na mukami domin kuwa a first class seats ta zo. Tunanin ta inda za ta ga Abdulazeez ta ke yi cikin dubban mutanen nan farare, jajaye da bakake. In bata yi kuskure ba tace har da shudaye da koraye. Ta tuna Daddy ya ce ta kunna wayarta. Tana laluben wayar cikin jakarta ta ji an zauna a gefenta. Kafin ta dago Creed Aventus ya ziyarci hancinta da karfinsa. Kafin ta farfado ta ji muryarsa mai amo da karsashi (husky) cikin kunnuwanta.A yayin da ya rankwafo sosai daidai kunnen nata har tana jin sanyin numfashinsa.
Welcome to New Haven!!!”.
Abinda Ya rada mata kenan. Muryar ta kara gardi da dadin sauraro fiye da koyaushe. Ko kuwa ita kadai ta ji hakan? Bazata iya cewa ba! Lumshe idanunta ta yi, kafin a hankali ta bude su tarr a kanshi. Dauke kansa ya yi ya dubi wani gefen daban, We can go (zamu iya tafiya).
Wani irin kallo ta bi shi da shi kasa-kasa, zuciyarta na melting. Ya kara tsawo fiye da wanda ta san shi da shi, ya yi wani irin fresh ya saje da black-Americans din da ke giftawa jefi-jefi. Sai dai kuma ya yi musu zarrah kasancewar shi akwai hasken addinin musulunci a tare da shi da cikar zati da kamala. Wadanda suka samar da wani irin kwarjini a tareda shi. Sanye yake da dogon wando da riga Long-sleeved(Burberry Hartford) ruwan makuba. In ta ce;he is handsome is not enough to convey thehandsomeness, ta san hakan tun tana karama da ta ke ganinsa a gidansu a Jeddah. Ta kuma sha fadin hakan a zuciyarta cewa ya fi duk yan gidan kyau mai daukar hankali, sai dai kuma duk sun fi shi kirki. Har gobe hakan ne a wurinta, sun fi shi saukin kai da dadin muamala, ya fi su Psychological Charisma.
A haka ta mike cikin sanyin jiki, za ta ja jakarta ya sanya hannu ya dauka, suka jera zuwa harabar airport din inda motocin haya suke jiran fasinja. Tun kamin su karasa wani siririn bature ya iso gare su ya karbi trolley din daga hannunsa yana tambayarsu inda za su je. Hannunta ya kama ya rike cikin nasa suka shiga farar taxi din mai matukar lafiya da sabunta. Sai da suka fara tafiya Abdulazeez ya ce da shi.
NewHaven Towers!.
NewHaven TOWERS, gidan bene ne mai kunshe da gidaje masu yawa(apartments)da mafi yawan daliban Yale ke zama, ana kiran daliban Yale University da (Yalies).Apartmentsdin ba iri daya ba ne, ya danganta da yadda ka ke so, single room, onebedroom, two bedrooms ko three bedrooms. Suffofin New Haven TOWERS sun hada da proximity ga jamiar Yale, wuraren siyayya, wuraren cin abinci, libraries, museums, parks da duk wasu ababen dabe kewa da dalibin Yale zai buka. (New Haven Towers) yana nan a Downtown na birnin NewHaven County. Idan aka ce Downtown ana nufin mahada ko cibiya ta kasuwanci, aladu da tarihi, siyasa da Geographical heart. Sau tari downtown’ synoymous ne da (CBD) na kowanne gari, wato Central Business District ko kuma a kira downtown da city-center ya fi saukin fahimta.
Abdulazeez Dakata na zaune a two bedrooms apartment a cikin New Haven Towers’. Daga (New Haven Towers) a kafa yake takawa zuwa makaranta kullum sabida bauchi nisa (trackable distance) ne. Da taxidin ta sauke su a daidai kofar shiga ginin TOWERS din shi ya dauki jakar ta har handbag dake hannunta suka hau ta lifter. A kofar apartment dinsa ya ciro makulli a aljihunsa ya bude, jakarta ya fara shigarwa sannan ya ba ta hanya. Sai wani dauke kai yake yi ya ki yarda su hada ido. Wucewa ta yi ciki ta samu lallausar kujerar wadataccen falon ta zauna, sannan ta warware lullubin kanta ta shiga karewa falon kallo. Matuka tsarinsa ya ba ta shaawa, komai neatandclassycikin tsari irin na bature, a can gefe study-table ne, manya-manyan littattafan law sun cinye filin tebirin sai inda zaa aje littafi ayi rubutu kadai suka bari. Ga study light mai ban shaawa komai na falon har labulaye brown da milk ne (ruwan kasa da ruwan madara). Akwai talabijin ta jikin bango, amma da alama ba’a kunnata sam. Kujerun wasu yan gujib-gujib na leathermasu tsananin taushi kalar su ruwan madara zallah. Daya daga cikin dakunan barcin guda biyu ya shiga bata kara ganinsa ba.
Ranta ya soma baci da wannan tarba da Abdulazeez ke mata, a kalla ya nuna mata dakin da za ta shiga ta sauke lalurorinta, ko ba zai yi mata magana ba. Idonta ta ji ya kawo ruwa da ta tuna salloli uku ne a kanta, ta taho tun daga Nigeria har America saboda shi, amma daga sannu da zuwa ko sannu ba ta kara samu ba. Tana wannan tunanin ya fito daga dakin da alama wanka ya yi, ya yi sallar magriba da isha a gefe duk tana zaune. Sannan ya sake komawa dakin ya sauya kaya ya fitohar da takalmi a kafarsa alamar fita zai yi. Kallonta ya yi da mamakin har yanzu tana a inda ya barta? Kamar ya wuce ta, sai kuma ya iso gabanta ya tsaya, sanyin turaren wankan sa na dunhillduk ya cika mata hanci.
Dakin ma sai na ce ki shiga za ki shige shi? Ai kuwa kina da aiki kuma zaki kwana anan wajen tunda ba ni na gayyato ki ba. Ya sa kai ya fice abinsa.
Ci gaba da zaman ta yi tana shaqar bacin rai, daga bisani ta ji fitsari na neman kwace mata. Dole ta mike ta suri jakarta ta murda dakin da ke daura da wanda ya fito. A nan ta lura ya ajiye mata trolley da tun shigowarsu ba ta ga inda ta yi ba. Kofa daya ce tal a cikin dan kyakkyawan dakin barcin wadda ta san toilet ce. Can ta nufa da hanzarinta, fitsari na barazanar zubo mata.
Sai da ta yi shi ta samu saida. A gurguje ta daura alwala ta fito ta kintaci gabas ta nada mayafinta ta tada sallah. Sai da ta rama sallolinta a nutse sannan ta kara da shafaI da wutiri ta mike ta soma rage kayan jikinta don ta shiga wanka. Wanka ta yi sosai da ruwa mai dumi don garin akwai sanyi duk da bai yi nisa ba, nisan d
a zai soma zubar da kankara. Tana wankan ta ji motsinsa a dakin da rufe kofarsa.
Da ta gama wankan sai da ta leko da kanta ta tabbatar ba ya dakin, sannan ta fito gaba-gadi. Ledoji ta gani ya ajiye mata guda biyu wanda ko ba ta bude ba bata raba daya biyun abinci ne. Ga lafiyayyen kamshi na tashi. Kwalliya ta tsaya ta yi sosai da daya daga cikin dinkunan da Mammah ta yi mata na wani material light bluemai santsi, an yi masa doguwar riga fitted gownda aikin duwatsu a gaban rigar sosai, ta murza daurin kai kamar mai shirin zuwa dinnerparty. Ta sa dankunne da sarka deep colour na material din na dutsen (cubic zirconia). Ba ta shafa jambaki ba, sai ta yi amfani da wet-lips mai taushi da kamshi. Har za ta zauna ta ci abincin ta ga gara ta je falo ta ci a can?Na me za ta kunshe kanta a daki don maigidan ba ya maraba da ita? Ai gara ta je ya yi ta ganinta tana harkokinta, in zamanta ya takura masa ya maida ita gaban iyayenta.
Falon ta fito rike da ledojinta, akwai dining table a gefe mai cin kananan kujeru uku, amma ba ta hau ba, tsakiyar rug ta baje ta fiddo kazar Kentucky Fried Chicken da chips da gwangwanin pepsi mai sanyi har guda biyu ta hau cin kayanta hankali kwance.
Zaune yake a study-table yana rubutu, wando ne three quarter a jikinsa da farar singlet ko sanyi ba ya ji. Tun fitowarta yana hankalce da ita ta gefen idanunsa, yana kuma ci gaba da hada assignment dinsa duk a lokaci daya. Ganin alamarin yake kamar a mafarki, yau ga shi ga Hafsat matsayin cikakkun maaurata a KARO NA BIYU! Its indeed a day in history wadda ba zai taba mantawa ba. Godiyarsa ga Ubangijin halitta wanda ya halatta AURE ya kuma halicci SOYAYAYAH ba za ta taba gushewa ba. Sosai yake enjoyingsharetan da yake yi musamman ganinyadda damuwarta a kan hakan ta fito karara. Dazu yana kallonta har kananan hawaye ta yi saboda bai nuna mata dakin kwana ba. A ransa ya ce.
Ashe babu dadi?
Da ta gama cin abincin ta nufi kofar da ta gane kitchen za ta kai ta, murmushi ta yi tana bin madafin da kallo. He still cooks. Ta fadi in a whisper (cikin rada).A shara ta zuba ledoji da kasusuwan kazar da ta ci ta wanke hannunta a sink da sabulun wanke hannu.Kawai sai ta hau gyara kitchen din. Kitchen ne na zamani, amma ya hadu da girkin namiji. Komaiout of order sai dai babu kofi ko kwanon da bai wanke ya killace ba ya rufa farin tawul akansu. Ta bude firji da freezer yana da kayan abinci daidai cikinsa. Da gani ba kullum yake yi ba, sai a (leisure time) dinsa.
Falon ta dawo ta nemi kujera ta zauna ta zuba tagumi. Wannan karon ya gama rubutun ya koma typing dinsa cikin laptop dinsa. Kamar bai san da zaman mutum a falon ba, zuciya ta soma zo wa Hafsat wuya duk kuwa da cewa ba halinta ne fushi ba. Ta ga in ta ce kuka za ta yi ta yi kan wulakancin Abdulazeez ta fadi ba nauyi. Gara ta dinga damunsa yadda zai yi gaggawar maida ita gaban masu kaunarta.
Mikewa ta yi ta isa ga T.V ta hau kokarin jona ta, ko banza ta samu abokin hira kada bakinta ya soma ciwo.
Cikin saa kuwa ta hada ta, ta dauki remote tana neman tashoshi, ta dire a bollywood wato tashar fina-finan India ta saka murya sosai suna ta raye-rayensu. Duk yadda ya kai da son ci gaba da abin da yake yi, hakan ya faskara. Hayaniyar ta dame shi, shi tunda ya zo bai taba jona T.V ba. Tsaki ya yi ya daga murya yadda za ta ji ya ce.
Please ki kashe. Banza ta yi amsa kamar ba ta ji ba. Tasowa ya yi a fusace ya je ya kashe ya koma ya ci gaba. Mikewa ta yi ta je ta sake kunnawa ta dawo ta zauna. Ba ta gama zaman ba ta ganshi a gabanta, cikin bacin rai ya ce.
“Are you here to disturb me (kin zo ne don ki dame ni)?
Hafsat ba ta taso ta ga ana tsiwa a gidansu ba, sannan ba ta cikin halayenta, amma yau ta yadda komai hali yake yi, kuma in ka ce ba za ka iya abu ba, to tabbata condition din bai same ka ba. Domin samun kanta ta yi da mayarwa Abdulazeez martani cikin launin nata bacin ran.
Kana iya mayar da ni inda na fito, tunda zama na takura ne a gare ka!.
Da sauri ya amsa.
Da ni na kawo ki? And I think you have your return tickets in your handbag?(Na yi zaton kina da tikitin komawarki a jakar ki?)”
Duk dauriyarta sai da hawaye suka silalo ta mike ta nufi daki. Kayanta ta jawo ta soma dannawa da ma ba ta jera su a wardrove ba suna cikin trolley din. Wadanda ta fitar da ta yi wanka ta ke dannawa, ta zuge ta saka hijabin sallarta. Keeeeeeeyyyy! Haka ta janyo jakarta ta tadda shi a falon yana ci gaba da aikinsa. Gabansa ta isa ta tsaya fuskarta babu ko digon hawaye ta goge su tsaf a daki.
Na fito Yaya Azeez, kai ni airport.
Da farko ko dagowa bai yi ba. Shi kansa ya san yanzu kam ba daidai yake typing dinsa ba. Yana yi ne kawai kada tasan ta birkita nutsuwarsa. Dagowa ya yi ya dube ta cikin ido da shanyayyun idanunsa.
Ki ka taho tun daga Nigeria ke kadai sai zuwa Airport ne zai gagare ki???”
Dauke idanunta ta yi daga kallon cikin idonsa sakamakon wani maganadisu da ke fita daga tsakiyar idonsa, yana shiga natamiraculously. Ba abin da za ta iya karantawa cikinsu a wannan lokacin ban da rashin damuwa da lamarinta. Gefen hijabinta ta kai ta rufe fuskarta ta soma kuka. Tashi ya yi tsam da takardunsa da laptop dinsa ya shige dakin kwanansa.
Sai da ta yi mai isarta sannan ta bai wa kanta hakuri ta koma dakin da kayanta. Ba ta da kudi a hannu, amma tana da credit cards’ har biyu. To amma ta koma gida ta ce wa Mammah me bayan ta gama gargadinta gidanta ba space na yaji? Babu kawo kara, su je su zauna su yi HAKURI da juna, to ko wannan shi ne hakurin da ta ke ikirari?
Haka ta kwana bacin rai da sake-sake. Amma da yake akwai gajiya sosai a tare da ita ba ta san yaushe wani wahalallen bacci ya yi awon gaba da ita ba, har sai da ta makara sallar asubahi.
Washegari ba ta tashi ta tadda shi a gidan ba, ya wuce makaranta tun bakwai na safe. A gefen filonta ta ji motsin takarda. Zarota ta yi ta duba,
“You can use thekitchen.
Jefar da takardar ta yi a fusace ta mike ta yi toilet.
Ba ta shiga kitchen din ba sai wajen sha daya na safe. Bakin shayi kawai ta dafa don ba ta jin za ta iya sanya wani abu a cikinta saboda haushin mai apartment din nan. Da rana ma kwai ta dafa guda biyu da indomie noodle guda daya ta ci jin hanjin cikinta na rawa da karkarwa. Ta yi niyyar dafa masa abinci ta tuna Abdulazeez fa in yana wannan fushin nasa maras dalili ba ya cin abincinta, wahalar banza za ta yi ya zo a kan idonta ya tsallake nata ya nemi abin da zai ci. Ba shi ya dawo gidan ba sai da yamma niki-niki da ledoji. A kitchen ya zube su ya wuce ta a falo tana kallo ya shige dakinsa.
Kwanan Hafsat uku kenan a America amma ba abin da ta gani sai bacin rai da damuwa. Abdulazeez ya zube mata komai na ci da na amfani, amma ban da kulawarsa wadda ita ta fi bukata fiye da komai. Duk ta wani rame sabida damuwa da rashin cin abincin kirki. Shi da kansa ya soma damuwa da ramar da ta ke yi din, wanda ya san shi ne sila. Ya soma saukowa ko ba komai ya san ya rama, ta dandani irin abin da ya ji a lokacin da ta yanke communication a tsakaninsu a lokacin da ba ya bukatar komai sai kulawarta.
A sanda ya soma saukowa a sannan ne ya lura ita ta hau ingarman dokin fushi. Sai ya janye saukowar suka ci gaba da zama a haka. Sai dai wannan karon in ta yi girki yana ci, ko ba komai ya yi kewar abincinta yadda ba zai iya bayyanawa ba.
A haka suka share sati daya, a karshen satin tafiya ta kama shi kan wani assignment dinsa zuwa Texas (The Supreme Court of Texas), ga shi ba ya so ya shiga sabgarta ganin yadda ta ke a kan tsininta. Abincin ma yau ba ta dafa da shi ba, daidai cikinta ta dafa ta shige daki. Ba zai kuma iya tafiya ba tare da ya sanar da ita ba, haka ya wuni da wannan damuwar. Tunda ta zo kuma bai hada mata layin waya ba, amma shi yana magana da su Mammah a Saudiyyah. Ya gaya musu ta zo lafiya bai san me ya sa ba ta kira waya ba tunda ta zo, amma lafiyarta lau. To su ma they are busy da ibadah ba wanda ya damu da rashin kiran nata tunda shi suna jinsa.
A daren ranar bayan ya hada yan kayan da zai yi amfani da su na kwana biyu, wato asabar da lahadi sai
ya fito ya nufi dakin nata.
Sanda ya murda kofar ya shiga tana kwance a gadonta tana lazumi. Sosai ya tsaya yana kallonta, abu biyu ne ya dauki hankalinsa, ramar da ta yi da hawayen da ta ke zubarwa. Jikinsa ya ji ya yi wani irin sanyi, ya shigo dakin gabadayansa ba tare da ya zo da niyyar hakan ba. Lokaci na farko da ya soma zargin kansa da rashin kyautawa kan abin da yake yi tun zuwanta.An rabo ta da kowa nata an turo ta wajenshi, amma tukwicin da zai yi wa iyayensa kenan?Wadanda ba su bukaci ko kwandalarsa cikin tafiyarta ba sai don su faranta masa. Amma ita har yau ba ta yi hankalin ta yi wa mutum laifi ta san ta yi ba, har ta nemi sulhu kan laifinta? Sai ma nasa laifin ta ke gani, wannan shi ne a doke ka a hana ka kuka.
Haka ya daure duk wani bacin ransa da laifin da ta ke ganin nasa ne ya ya zauna a gefen gadon daura da kafafunta. Rana ta farko da ya shigo dakin har ya zauna tun zuwanta. Dauke idonta ta yi daga kansa ta juya bakidaya daya barin ta ci gaba da sharar hawayenta. Ya ji haushin abin da ta yin, amma ya hadiye ya ce.
Ki juyo mu yi magana, tafiya zan yi ta kwana biyu Im going for some assingments to Texas.