AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 7 BY SUMAYYAH ABDULKADIR
Dumi ya ji a bayansa wanda ba ya ko tantama hawayen Hafsat ne. ba tun yau ya lura ba abu kankani ke sanya ta kuka. Abu kankani ke karya zuciyarta. To yanzu sabida Allah cikin labarin zuciyarsa da yake ba ta me ye abin kuka? Dago ta ya yi daga jikinsa ya soma dauke mata hawayen da bakinsa.
Alfarma ta karshe da na ke nema ki yi min Suhaanahdont ever talk about Muazatu again, shes a bygone in our life,she exists only in our past; our destiny to be tormented by.Lets create our peaceful present and abright futuretunda ita din ta zame mana ciwo. Yo ciwo mana?
Duk wani abu da zai sa ka fita hankalinka ka kasa gane abu mai kyau da mara kyau kuma ka kasa bin iyayenka akansa ai ya zama ciwo. I dont want to recall the moment I put you in trouble with your mother (bana son tuna lokacinda na sanya ki a matsala da Mamanki ) saboda hoton Muazatu a falonki. Ranar nan na ji kunyarki mai yawa na muzanta, na kirga ta cikin tarin uzururrukan da ki ke yi mun. Imsorry Hafsah once again, ni na kasa yi miki uzuri ko daya. You received a weird welcome from me.
Dariya ta yi ta zame daga jikinsa ta zauna a gefen dan tsurut din gadon don kafafunta sun gaji da tsayuwa, da alama shi Yaya Azeez tsayuwa ba ta gajiyar da shi sai kace soja. A kalla sun kwaso mintuna sittin a yadda suke. Cikin shagwabar da ba ta san ta yi ba ta ce.
Kuma sannan ka yi barringdina ba, na kasa kiranka.. na kusa mutuwa sabida damuwa da rashin jin muryarka!”.
Kusa da ita ya zo ya zauna kafada-da-kafada, ya juyo yana kallonta da kyawawan idanunsa.Fuskar sa kawai ta bayyana dadin da kalaman ta suka yi masa baka da zuci. She loves him to such an extent amma ta hadiye. Ta iya controlling kanta a kullum. Hannayenta ya kama ya rike gam! Cikin nasa.
Saboda ki dandana abin da ake dandanawa in mutum na son magana da matarsa ta hana shi. A duniya ina da rival irin karatunki Hafsah? Im very-very jealous of it. Ya fada yana kaurara very-very din wanda ya fito tun daga karkashin zuciyarsa. Hafsat me za ta yi in ba dariya ba? Ban da an an kashe deal din Muazatu kuma ta yi masa alkawarin ba za ta kara zancenta ba, da ta ce wani abu akai. Kafafunsa ya mayar kan tafukan kafarta ya sarkesu cikin na juna ya kumatake susosai da yatsunsa, ya fiddo fararen idanunsa a kanta cikin damuwa.
“Tell me please. Ni da bokon nan naki wa ki ka fi so? Na san da Allah ya ba ku damar aure fiye da daya da mu biyu za ki aura ni da shiIm sure. Ya karashe kalaman da karyayyen sauti. Ta sunkuyar da kai ya dago fuskar ta. “You are to look directly into my eyes and answer me Hafsah(cikin idanuna za ki kalla ki amsa mini).
A yadda Hafsat ke jin zuciyarta tun daga lokacin da ta fara hankali a gidan Abdulazeez, ta fara bambance me zuciyarta ke ji a kansa, ta fara sanin darajar aure da martabarsa; to tun a lokacin ta riga ta mika wuya ga cewa; za ta iya hakura da komai in dai za ta tsira da shi!!! Idan ta ce komai tana nufin KOMAI!!!
Ciki kuwa har da nemo mata biological parents dinta. Ta ji cewa za ta iya rayuwa a doron kasa ko babu kowa in dai yana tare da ita. Yau da ya yi mata wannan tambayar sai ta samu kanta da kasa cewa komai. A ganinta kalaman will not be enoughto express her inner feelings wani lokacin shiru ya fi faida a inda babu gamsasshiyar amsa.
Maimakon hakan, sai ta fada jikinsa da karfi ta wani irin cukwikwiye shi tamkar zata shige cikin tsokar jikinsa. Yana iya jin karfin matsar da ta yi masa da iyakacin karfinta kamar zata balla shi. Har sai da ta kai shi ga fadawa saman dan gadonsu akan bayansa sabida bai zata ba jinta kawai yayi. Ta bishi ta turmushe tana tumurmusa ta koina. Dariyar da bai shirya yi ba ce ta kufce masa.
Meye haka Hafsat? Karya ni zaki yi?
Nasa rukon da ya yi mata in returnya kuma jirkita ya maida ta upside-down(is beyond herwords to express the tightness). Hakannan ya sanya ta yin nadamar gwada masa karfi don nuna inner expressions dinta. Bata da idea na yadda zata nuna din kuma tana so ya fahimta. Wani riko ne da ko jiya bai yi mata kwatankwacinsa ba. Amma can kasan zuciyarta ta sa a ranta za ta jure goman wannan a kowacce rana…… in dai hakan zai sa Abdulazeez ya rayu da ita ita kadai! Cikin kunnenta ya rada mata, a lokacin da ya dawoABDULAZEEZ dinsa maimakon mijin HAFSAH! .
“Addah Hafsatuh,kin kusa balla ni fah! Yarinyar nan karfi gareki dama??In shi ki ka aura, ai ba za ki so ki balla shi ba;Im very sure lallaba abinki za ki yi ta yi ku tsufa kuna morar juna cikin lallaba tsufanku da tsohuwar soyayyar ku.
Ta dubeshi cikin takaicin abinda yake fadidaga cikin duvet dinta data cukwikwiye ita kadai ta hana shi (dama ta saba) ta bata fuskatace.
Bokon? Bokon zan aura Yaya Azeez?”
Ya dago fuskarta cikin tafukansa yana jan tsinin karan hancin ta da yatsun sa biyu,wata halitta guda daya da tafi komai burgeshi da jan hankalinsa a fuskar matarsa Hafsat (dogon karan hancinta). Kallonta yake deeply tamkar ya hadiye ta bakidaya don SO. Cikin imitating(kwaikwayon) yanayin da ta yi maganar yace.
“To ni Abdulazeez damainada wani rival dina duniya bayan shi ne? Kar fa ki manta har kwana kike raba mana ni da shi, kada wani ya shiga na wani, ke ga mai maza biyu, in ban yi kishi da Bokon ki ba Hafsah da wa zan yi a duniya???”
Hannu ta kai ta dafe goshinta.
Na rantse Yaya Azeez da kai mace ne da mun shiga uku saboda mita. Oh ni Hafsatu yar Habibah jikar Hashim Babbah! Da na san abinda kashe wayar nan zai jawo min kenan da banyi shi ba. Juya mata baya yayi yana so yayi dariya. Amma ya hadiye don ya san ta tsani hakan, ta sake jawo shi da karfi ta baya jikin ta yana dan rawa.
Yaya Azeez babu wani duvet din? Na rufa da wannan amma kamar da zanin atamfa na rufa ban daina jin sanyin ba. Ta fada kamar zatayi kuka kuma sosai da gaske bilhaqqi sanyin take ji,tsigar jikinta har tashi take yi duk da ta rufa din ta kuma handame abin rufar ita kadai ta hana shi.
Juyowa yayi ya kama duvet din yana kokarin janyewa ta rike gam-gam. I cant do without It, don Allah ka bar min nikadai.
Rausayar da kai yayi yana mata wani irin kallo wanda daga jiya zuwa yau ta gama sanin maanar sa tsaf!Idanunta sukayi kwalkwal amma ta riga tayi alkawarin juriya ga alamarin nan no matter what in dai zata tsira da shi!!! Ga mamakinta bayan ya raba ta da duvet din maye gurbin sa yayi a hankali in a way that is unusual to her.Hakan yasa rawar da jikin nata ke yi da tashin tsigar jikintaya ragu.
Relax Addahh,ni ba na jin sanyi,balle in kwace miki abin rufar ki. Andits not what you are anticipating Baby….
Sabuwar hanyar samar da HEAT kenan wadda tafi dukkan duvets dinki. You have me now……no need of your quilts daga rana irin ta yau. Ya hade bakunansu wuri guda kamar yadda ya hade jikkunansu, hannunsa cikin sumar kanta yana fadin.
Jaruma, kuma matsoraciya Hafsatu matar Barrister Abdulazeez Hamzah Atiku!.
Murmushi ta hau yi irinna karkashin zuciya. Tana mai kara nitsewa a cikin jikinsa. Wani identity data dade tana kwadaitawa zuciyarta a farke ko a mafarki. Yau gashi ya fito kai tsaye daga bakin mamallakin sa.
“The heat is uniq
ue, so its provider!
Magana take a zuci cikin lumshe idanu tana kara rungumeshi tsam, batasan cewa a fili take yi ba.Shima murmushin yayi yace mata a cikin kunnuwanta.
“TheMammahs patient is also unique too. I love herso much Hafsah! And the word LOVE is not enough!It can only make a comparison. Allah ya kara miki lafiya!!!
******
Wannan assignment dai da kyar aka yi shi sharp-sharp a washegari, sai dai su kansu sun san ba za su ci makin yadda Hafsat ta yi fata ba. In aka ce ya samu C to sunyi kokari. To duka an cinye lokacin a soyayya da wani irin honey moon mai ban mamaki a dan tsukukun dakin (ta bakin Abdulazeez) dake cikin hotel din WyndhamDallas birnin Texas. Tunda suka shigo hotel din nan sau biyu ya fita ya je kotun, daga safe zuwa yamma, ya harhada abinda ya kawo shi ya rubuta yayi typing acan.Abinci daga hotel din suke order a shigo musu da shi.
Ranar litinin suka koma NewHaven suka ci gaba da rayuwarsu mai tsafta da ban shaawa, wadda soyayya da kauna yar usulisune jigonta.Hafsat tarairayar Abdulazeez ta ke kamar ta maida shi cikin kirjinta, tareda kinkimar duk wasu bukatun rayuwarsa da dukkan iyawa da jarumtar da bai taba zato ba. Abdulazeez kula yake da Hafsat kamar yadda yake kula da bugun zuciyarsa. Duk wani abin bukatar diya mace ya kaita ya saya mata. Ya sayawa Mammah tsaraba sosai. Akwai sanda suka shiga wani shagon kayan sawa ya ga tana diban T.Shirts da Trousers masu kyau na maza tana faman gwadawa da jikinsa tana jefawa a kwando, ya ce.
Ban gaya miki bana bukata ba ne? Tsaraba kawai nace kiyi ba ruwan ki da ni. Da na zo na sayi kaya masu yawa wasu ko taba su ban yi ba har yau. Ba tare da ta kalle shi ba ta ce. Ba fa kai nake sayawa ba Malam . Haleem nake daukarwa!.
Dariya ya yi da ya tuno wani zuwa da ya yi Jeddah Haleem din ya faki idon Mammah da Baba Azumi ya danne ta yana kirbarta tana ta zabga ihu, shi ya daga shi daga ruwan cikinta. Ta sha wahala iri-iri a hannun Haleem, amma duk gidan har gobe ba wanda ta ke so kamar shi.
“Shine kuma kike gwadawa da ni? Ai na fishi tsaho? Kuma shi mai kiba ne. Ki hada da Usman ko banza ya sha jigilar kai ki makaranta ya dauko ki, a lokacin da aka sanya ni a makarantar Mammah,kuma dai yana son ki kullum mukayi waya sai ya tambayi lafiyarki.
Dariya ta yi jin abinda yace wai (makarantar Mammah) ta ce, He is the first in the list, na saya mashi a Texas, shi da Hamma Imamu.
Ya ce, Abba fa?
Kai ma ka san ba ya saka kananan kaya.
Ki saya masa wani abun to, ga agoguna ga takalma?
Waya ta fiddo ta kira Imamu ta tambaye shi lambar kafar Abbansu, sannan ta dauka mishi takalma kafa uku da tsadadden agogon POLO. Ya ce hatta Malam da Daada sai an yi musu tsaraba. Dariya ta yi ta ce, ita ba ta ga abin da ya dace da su a nan ba, ya bari in ta koma gida za ta saya masu.
Ya ce, Wallahi ko ki ma Ismael tsaraba ko na gaya masa kin ware shi, kin maida shi saniyar ware. Ta zumburo baki, tace ba abinda zan saya da sunansa, ina kaiwa zai gayamin bakar maganar da sai tayi shekara tana damuna.Ka manta sanda yace nikazama ce, don kawai ya rako Mammah ban yi wankan safe ba, zai aura maka yar gayu. Murmushi Abdulazeez yayi yana tuno ranar shima, abubuwa da yawa sun faru a ranar very bitter and sweeteralso,ya kada ya raya ta ki, sai ya fiddo waya ya kira Ismael.
Ishma, Hafsat ta yi wa kowa tsaraba ban da kai saboda laifuffukanka masu yawa ne.
Ismael yayi dariya ya ce ya ba ta wayar. Da farko tace bazata karba ba sai ta ga rashin kirkinta, shi Abdulazeez Ishma ne nasa yafi shiri dashi a kan sauran duk da shine sakonsa. Karba tayi tana hura hanci, ita ga wadda zaa bawa hakuri. Ismael yayi gyaran murya sannan yace,
“Addah meye na daukar zafi da ni haka? Da zaki yiwa kowa tsaraba banda ni?Ni fa ko da na ce zan aura wa Yaya yar gayu, in kin mutu nake nufi!.
“……Insha Allahu Wasila ce za ta fara mutuwa kafin ni…..
Abdulazeez ya fizge wayar jin ana zancen mutuwa ga Hafsat ta fara hawaye a tsakiyar shago. Ba ta hango komai sai ranar da za ta mutu ta bar Abdulazeez kamar yadda Ishma yayi mata fata, ya manta da ita ya auri watanta. Ta karbe duk wannan soyayyar da yake gwada mata wadda daga ita sai Allah sai shi suka san yadda take. Hannunta ya kama suka bar shagon bayan ya biya su kudin kayan da suka dauka. Sannan ya kira Ismael suna cikin taxi don komawa gidaya soma sauke masa fada da bacin rai mai tsanani, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. “Daga yi maka abin arziki Ishma, wai ni babba inaso in gyara muamalar ku dana lura bata da dadi duk da na san kai ne ba ka da gaskiya? Ashe girma na bai isa yayi amfani ba Ismael?” Ya karasa cikin kwantar da sauti.
Ismael dariya yake yiko a kwalarsa ya ce, Ai ba za mu taba shiryawa ba sai ranar da ta daina shagwaba da kazanta a gidan miji.
A karshe gajiya ya yi ya rabu da shi, saboda ya fara sa masa ciwon kai. Haka Allah ya yi shi(very annoying). Hafsat kuma ba ta daina kuka ba har suka je gida, kayan ma duk shi ya kai mata daki. A kujerar falo ta zube tana ta sharar ido. Sunkuyawa ya yi a gabanta bayan ya fito daga dakinta ya juyo mata bayansa….
She wonder what he is going to dohaka sunkuye a gabanta duk da hawayen da ta ke yi. Hau bayan nan Hafsat in goya ki, yi maza ki riga yayan Abdulazeez hawa, in mutuwar da ya ke ambato ta zo ta ganki a bayana za ta ji kunyar dauke ki ke kadaita barni. Sai ta hada mu mu biyun ta dauka.
Da gudu ta haye bayan nasa ta kwanta, ta sarkafo hannayenta a wuyansa ta rungume shi tsantsan,kukan ya rikide ya koma dariya. Sosai ya bata dariya.
Ba mutuwa nake gudu ba Yaya Azeez, yadda za ka manta da ni ne idan na mutun kayi aurenka.
Shi ne na ce mu makale juna kawai mu zama kamar alkaki, yadda za ta ji kunyar dauke ki ta bar ni. Har a lahira ina rokon Allah ya zaba min HAFSAT-SUHAANAH matsayin matata a gidan aljanna, na yi miki alkawarin ko Hurul-eeni ba zan roka ba!.
Sosai ta manne a bayan nasa tana wani irin blushing da bata jin ta taba yin irinsa a rayuwarta, wanda ke fitowa tun daga karkashin zuciyarta. Hakika kalamansa sun ratsa har tsakiyar ruhinta sun haifar da farin ciki da annashuwa marar misali. Tuni ta mance da shirmen Ishma ta rungume mijinta. Rokon Allah ta ke cikin zuciyarta ya biye bakin Abdulazeez Dakata. Ya sa in mutuwa ta zo ta dauke su tare, in ya so su bar ma Mammah yayansu ta goya. Cikin wannan nishadin suka shige bedroomdinsu ba sa ganin kowa da komai a gabansu da bayansu sai junansu
******
Tun Hajiya Maryam na kidayar kwanakin dawowar Hafsat tana jiran Abdulazeez ya kira ta ya ce rana kaza za ta taso, har lissafin ya subuce mata. Hafsat dai tunda ta saka kafa kasar America Abdulazeez ya raba ta da wayarta. A cewarsa gabadaya lokacin nasa ne, sai ya yi covering shekarar da ya yi asara har da doriyar watanni biyar a banza,cikin yan satittikan da suka zamo nasa. Sati uku suka cika, aka shiga na hudu, shi ma ya kare aka shiga na biyar Abdulazeez bai da niyyar maido mata Hafsat ta koma makaranta. Ta yi fadan har ta gaji kullum da uzurin da zai bayar.
Uzuri na karshe da ya ba ta shi ne, Hafsat ba ta jin dadi yana tsoron sako ta a jirgi ita kadai, a bari zuwa wata mai kamawa sai ya yi kokari ya kawo ta da kansa, ko kwana biyu ne ya yi ya koma. Dan jim! Mammah ta yi kafin ta ce, Me ya same ta?
Cikin damuwa ya ce, Ni ma ban sani ba, ba dama ta dora girki dai sai ta yi amai, wai ba ta son kamshin abinci. Idan na siyo ma bata ci ba tare da ya dawo ba. Snacks kadai da Pepsi ke zama a cikinta…
Bai karasa ba ya ji Mammah ta kashe wayar, sai da gabansa ya fadi, cike da tsoron ko wata mummunar cutar ce da bai sani ba ya fadi symptoms dinta? Ya juya ya dubi Hafsat din wadda ke kwance a dandaryar marbles kamar wadda tayi wata uku tana jinya, damuwarsa ta kara nunkuwa. Ya ce, Don Allah Hafsat ki yarda mu je asibiti, na yi miki alkawarin ba zan yarda su yi miki allurar ba, kuma ki tashi daga tayal din nan sanyinsa zai cutar da ke.
Kukan da ta kwana tana yi ta ci gaba, da kyar in ba mutuwar da Ismael ya yi mata fata ce ta iso ba, ba tare da ta ga Da
nta da Abdulazeez ba. Yau kwananta biyar cikin wannan halin ta ki yarda su je asibiti, honeymoon ya guntile ya koma jinya. Ta yi-ta yi ya sa ta a jirgi ta tafi ya ki, shi a wahale ita a wahale, yana cutuwa ta fannin karatunsa sosai, ita kuma ba abin da ta ke tsoro a duniya irin a huda jikinta da allura, ta san yadda ta ke vomiting din nan abu na farko da asibiti za su yi mata shi ne, saka drip. Ya taso daga inda yake rubutu cikin system dinsa ya dago ta daga tiles din ya hada da jikinsa. Sai kawai ta fasa kuka tana fiffizgewa, ita dai ya kyaleta ta fi jin dadin can. Zama ya yi a kasa ya rungume ta kamar shi ma zai yi kukan. To ni ki kwanta a kaina duk yadda ki ke so, kiyi birgima kiyi ta kukan yadda yayi miki, amma ba zan iya kallonki kwance a kasa ba sanyin nan na huda jikin ki.
Zamewa ta yi ta koma inda ya dauko ta ta yi kwanciyarta ta juya masa baya. Abdulazeez ya rafka tagumi ya soma tunanin ko dai ya yi musu yadda suke so ne ita da Mammah ya maida ita gida? Duk da cewa zamanta tare da shi as a patient nauyi ta zame masa, musamman yadda karatunshi ya dau zafi a wannan dan tsakanin, ya fiye masa rashinta cikin gidan sau dubun dubata duk da yanzu babu abin da ta ke tsinana masa sai aikin kwashe amai da gogewa da ya hau kansa. Wanka ma shi yake mata, abinci sai dai ya sayo ita kuma ya sayo mata snacksda pepsi amma wallahi hes enjoying this new life fiye da farkon zamansa a gidan shi kadai.
Sai dare ya samu wayar Mammah, da sauri ya amsa a lokacin yana kan hanyar komawa gida ya fita sayo harpic na wankin toilet dinsu. Muryoyinsu su biyu ya ji ita da Daddy, da alama a handsfree suke magana, Daddy ya ce, Kana jina ko Abdulazeez?
Ya ce, Ina jinka Daddy.
Mammah ta ce, Kai kadai ne?
Ya ce, Eh, a titi ma nake.
Daddy ya ce, Ka je ka kira hospital din su zo su tafi da ita da kansu, kada ma ka tsaya a wajen ta ganka. Idan ta samu karfin jikinta ka sako ta jirgi ba abin da zai faru insha Allah.
Cikin damuwa ya ce, To Daddy.
A tare suka hada baki, Yauwa Abdulazeez Allah ya yi muku albarka.
Ji ya yi damuwarsa ta tafi gabadaya, ya amsa da karsashi, Ameen-ameen Daddy, ameen Mammah.
Hafsat na kwance ya shigo ya ce, Tashi ki shirya za mu yi baki yanzu.
Bata fuska ta yi zai katse mata kwanciyar jin dadinta ta kan marbles wanda ya fi komai dadi a gare ta yanzu. Da ya ga tana bata masa lokaci ya shiga ya dauko mata doguwar abaya da mayafinta kawai ya ciccibo ta ya hau saka mata, sai cin fushi ta ke tana mita.
Wadanne irin baki ne tun ina da lafiyata ba su zo ba sai yanzu da na koma gawa ta ki rami?
Dariya ya yi, ya ce, Ashe kin iya Hausa kike cewa baki iya ba?
Ta zumburo baki ya kama lebunan da yatsunsa biyu, Ki yi a hankali da ni kada na karasa gawar, kin ga ina tausaya miki kwana biyu, to ki lallaba ni in ci gaba da daga miki kafa har ki warware in koma angwancina.
Rufe idonta ta yi da tafukanta, Yaya Azeez ka dinga jin kunyata mana, ni fa kanwarka ce.
Hannayen da ta rufe idon da su ya dauke, ya dube ta cikin ido ya dage girarshi sama ya ce, Really?
Neman wajen boyo ta koma a jikinsa, shi kuma ya ki yarda da hakan, wai lallai ta dube shi cikin ido ta maimaita ita kanwarshi ce ba matarshi ba. Suna wannan diramar suka ji kararrawa. Mayafin ya dauko ya nannada mata a ka ya taimaka mata ta mike, Mu je mu bude musu, ga su nan sun iso.
Har takalami ya dauko mata. Cikin mamaki ta ce, To ka je ka bude musu mana? Na sani ko da maza?
Hannunta ya ja zuwa bakin kofar yana fadin, Aah mata ne.
Mata! Ta fada in exclamation! Tuni ya gano inda ta nufa, kawai ya yi dariya ya bude kofar. Hafsat ta yi arba da kyawawan matan turawa guda biyu, amma dai da fararen kayan maaikatan jinya a jikinsu. Wani murmushi suka kashe ta da shi, kowacce ta kama hannunta daya suka yi gaba da ita zuwa farar ambulance din da suka zo a cikinta. Ta waiwaya hagu da dama babu Abdulazeez babu alamarsa, ya gudu ta inda ba ta sani ba. Ta so yi musu gardamar kin shiga motar, ta ga za su gwada mata karfi duk da dai lallashinta suke yi, amma fa ba ta ga za su yarda da abin da ta ke so ba. Sai tsintar kanta ta yi a wani kyakkyawan asibiti.
Abin da ta ke gudun shi aka fara yi mata, tana kuka tana komai. Ta sha allurai kala-kala, kulawa dai zallah kamar tana gaban Mammanta. Zuwa washegari dai kam da kanta ta nemi abinci white rice and stew, haka suka kawo mata. Lallabata suke kamar kwai in ta tambayi mijinta su ce sai ta daina kukan allura za su barshi ya zo. Kwananta uku ta samu karfin jikinta sosai, haraswar ta tsaya, sai mugun cin abinci kamar tashin hankali. Magungunan da za su kara mata karfi da lafiya suka bata suna kara jadda mata ta dinga sha kullum kuma ta dinga kula da kanta. A daren ranar suka sallame ta, ba ta ga Abdulazeez ba sai lokacin. Bai ce komai ba ya kamo hannunta yana sakar mata wani irin murmushi, suka shiga taxi ta kai su gida.
Suna shigowa falo ya wani irin juyo ya sure ta bai dire ta a koina ba sai dakin barcinsu. Ba don kar ya saukar mata da hajijiya ba juyi yake so ya yi ta yi da ita. Idanu ya zuba mata kamar zai cinye ta. Kafin ya mirginota ta dawo samansa, ya ce, Kin san wani abu?