AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 8 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

AUREN KWANGILA BOOK 4 CHAPTER 8 BY SUMAYYAH ABDULKADIR

Www.bankinhausanovels.com.ng 

Ai ba ta san lokacin da ta juyo ba ta mike zaune. Ni kuma in zauna da wa??”

Cikin tsakiyar idanunta ya dube ta kai tsaye. Da da wa ki ke zaune a gidan nan? Ban yi zaton kin san da mutum a cikin gidan ba?

Mikewa ta yi ta diro daga gadon ta nufi wardrove ta soma kwaso kayanta, cikin rishin kuka ta ce. Wallahi ba zan zauna ba, ko dai kafata kafarka, ko ka sa ni a jirgi in koma gida. Yanzu ne na yarda da duk abin da Mammah ta ke fada. How sure am I yanzun kana sona? Zuciyata ta zarme na ki yarda da ita, bayan na san duk duniya ba wanda ya kai ta sona! Na yarda da dadin bakinka, da kalaman ka na yaudara, na yarda duk abin da ka ke fada da zuciya daya. Da na san haka kake da ban zo ba.Kaicona! Da na yarda aka maida auren nan!! ..…Auren da tun fil azal nasan bani da gurbi a cikinsa..!!!”. Ta sulale a kan gwiwoyinta rungume da rigarta a hannu, ta sa kuka mai cin rai.

Ba ta san yaushe ya taso daga gefen gadon da yake zaune ba. Ta dai ganshi yana ciro wasu daga cikin kayanta wadanda ta ke watsawa a jaka. Fita ya yi da su bai ce mata komai ba. Wannan ya fi komai kara bakanta mata rai; shirun da ya yi mata. Zama ta yi a wurin ta saki kukan gabadaya. A can dakinsa shi kuma da ya hada kayanta da ya debo da nasa ya rufe jakar ci gaba ya yi da sabgoginsa, amma duk sai ya ji ya kasa sukuni, maganganunta sun taba shi, ya kuma yardar wa kansa hukuncin nasa ya yi tsauri fiye da laifin da yake ikirarin ta yi masa. Ga wata irin soyayya da ke cinsa a zuci. Yau Hafsat din ce matsayin matarsa ta hakika a dakin aurensa babu zancen yarjejeniya, amma ya tsaya yana wahalar da su dukkansu a banza. Ita ta kasa ganewa lallashi yake so. So yake ta lallashe shi, ta yi admittingda kanta ta yi masa laifi, amma ta ki yin hakan. She only insist on ba ya sonta. Murmushin takaici ya yi, ya tabbata in zai iya buda mata son ta gani ba ta da fadin zuciyar da za ta dauki nauyin rabin sa.

Duk yadda ya so ya yi bacci a wannan daren ya kasa. Hafsat ce a cikin apartment dinsa, amma wai ya raba daki ba ma makwanci da ita ba. Tana can tana kukan bakin cikinsa, yana nan soyayyarta na neman hallaka shi. Abin da ya dade yana jiran samun yancinsa shi ne a hannunsa amma ya jefar. Ya tuna yadda yake hana idonsa barci yana rokon Allah ya dawo da ita cikin rayuwarsa ya gyara kuskuren da ya yi, Ubangiji maji rokon bayinSa Ya amsa masa a lokacin da bai zata ba. Anya wannan gabar da ya kulla da ita don kawai ta kashe masa waya tana so ta yi jarrabawa ba butulci ya yi wa Ubangiji ba?

Wani irin tausayi da kauna suka taru suka dabaibaye shi. Soyayyar da ke dankare a zuciyarsa ta yi ta kawata su. Tsohuwar ajiya ta soma bankadowa tana fiddo kanta. Tsayawa ya yi yana karbar isowarsu daya bayan daya cikin zuciya da ruhinsa. Yayin da gangar jikinsa ke musu masauki a muhallin da ya dace da kowannensu. Kafin ya mike ya shiga toilet dinsa da zummar yin wankan da ya zame masa jiki kafin ya kwanta, ya sanya Pajamas samfurin‘FENDI ya soma cumbing kanshi, gashin ya yi tudu kadan don ya kwana biyu bai yi saisaye ba. A yau bayan CreedAventus da ya lura Hafsat na matukar so, ya samu kansa da fesa wasu turarukan da bai taba fesawa ba. Ya kalubalanci zuciyarsa dalilin yin hakan?Dalilin fesa turaren da bai taba amfani da shi ba?Wanda ya tabbatar ya fi Creed aminta zuciya da sanyayata.Sai zuciyar ta ce. Because you want to please her. Kuma dai ai yau kake Abdulazeez angon Hafsah in an bi salsala; wadancan watannin da kwanakin har sama da shekara sun shude a banza ne.

Ita kuwa Addar bayan ta gama kukanta ta gaji sai ta mike kanta na sarawa saboda kukan da ta yi. Wanka ta yi ta dauro alwala. Abayar sallarta ta sanya da hijabi ta feshe su da turaren ibadarta wanda ta tanada kawai don sallah. Nafilfili ta ke yi tana kai karar Abdulazeez a wurin Allah. Ba muguwar addua ta ke masa ba, ita kadai ta san me ta ke roka, wani sirrin na zuciya ne. Ashe da gaske wasu tun kan su tashi daga sujjadarsu Allah yake amsa musu bukata??? Hafsat ba ta san hakan ba sai yau, domin kuwa cikin sujjadarta ta ji budewar kofarshi da shigowarshi. 

Hasken da ta bari ya fara ragewa ya sanya dim-light ba ta kara jin motsinshi ba. Ta dauka ma fita ya yi, ashe cikin duvet dinta ya shige bai kara motsin da za ta san yana dakin ba. Har wajen biyun dare agogonsu na can Hafsat na nafilfilunta. Abdulazeez bai katse ta ba, yana fama da zuciyarsa. Amma da ya hangota ta cikin kankanin hasken fitilar ta daga hannuwa biyu tana addua, tashi ya yi da sauri ya sauko daga gadon ya sunkuce ta suka koma tare. Kinsan Allahyarinyar nan ki bar ni haka! In ba kuma rokon Allah ki ke ya zauta ni ba. Inna zauce kin fi kowa asara.In kuma wuta ki ke roka min to ki sani ni ne mai kai ki wuta ko aljannah, ba ki isa ki kai ni ba!.

Hijabin ya zare cikin nutsuwa ya yi gefe da shi, amma ya rasa yadda zai yi ya zare abayar bai san ta ina ta bi ta zarga ta ba. Sumbatarta ya soma yi ta hanyar da yake ganin shi ne kadai samun rangwamensa wato intensely kamar wannan ne karo na farko da ya taba samun damar hakan.Hafsat ta zama mute wuta da gudun jini suka dauke mata, saboda kusan a cikin shock ta ke da wannan sudden reactiondin nasa ba ta gama tantance a halin da dukkaninsu suke ciki ba, ganin alamarin ta ke kamar gizo irin na mafarkanta.

 Abdulazeez ya zame mata hawainiya mai rikidewa duk kalar da yake so a gareta, a kuma lokacin da ya ga dama. Haka za ta bari ya yi ta tamaula da emotion dinta duk yadda yake so? 

Wata zuciyar ta ce Kada ki zama mai butulci ga Ubangijinki Hafsah! Wanda ya amsa duainki tun kafin ki dago daga sujjadah, Ya kawo miki Abdulazeez din har makwancinki a tafin hannunki. A lokacin da ki ka riga ki ka fidda rai. Yau dai for the first time, let your hearts have the freedom it wants.

 Lokacin ya zo daidai da sanda Abdulazeez ya samu nasarar amshe abayar bakidaya daga jikinta. Hafsat ta runtse idanunta lokacin da ta fahimci yau babu sauran hijabi tsakaninta da Abdulazeez, ita ce ranar da yake gaya mata cewa “it will be a day inhistory.Ranar da za ta zama shi ya zama ita, ranar da zata zamanto babu sauran kunya ko shamaki a tsakaninsu. Hawayen da ta ji suna fita a idonta ita ta san na farin ciki ne, kuma na tsoro da fargaba duk a lokaci daya. Daga ita har shi sababbi ne a cikin alamarin wanda hakan ya janyo wa dukkaninsu rawar jiki na ban mamaki da neman taimakon dan uwansa. Lokacin da mai faruwar ta faru Hafsat ta san ba ita kadai ba, shi ma Abdulazeez din ya sha wahala. Duk da sanyin garin amma gumi suke. Shi kansa ya yi mamakin dauriyar da ta yi domin ba ta yi kukan nan nata wanda gari banza yinsa ta ke kamar ba gobe ba. Bai juya mata baya ba kamar yadda maza da yawa ke yi a irin wannan lokacin, shi a lokacin ne ma ya sanya ta a jikinsa sosai, physique-chestdinsa ya zame mata mahuta, wurin maida numfashi da sauke ajiyar zuciya. Cikin daruruwan kalaman da ya gaya mata a wannan ranar ban da albarka da ya sanya mata ba ta rike ko daya ba. Saboda ta yi amanna da cewa, shi kansa ba’a hayyacinsa yake fadarsu ba, to don me za ta kama su? Ai gara ta bari a gaya mata wadanda za ta iya yarda da su a lokacin da ya dace.

Duk wani taimako da mace ke bukata a wannan ranar Abdula
zeez ya yi wa matarsaHafsat, wankan ma shi ya yi mata tana kunkunin ta data saba tana ba ta so amma bai saurare ta ba. Shi ya gyara gadon da komai na dakin ya ba ta kayan da ya ga dama ta saka. T.Shirt dinsa ce da wandonsathree quater wai haka yake son ganinta, in ka ganta cikin kayan sai ka yi dariya duk da dai shi ma ba kauri ne da shi har can ba, amma ya fi ta girma da tsayi sosai. Ya ciccibota ya aza a kan ruwan cikinsa ya dora kanta a kan kirjinsa ya ja quilt ya rufe su iya kafada. Sai rufe idanunta take wani abu da ake kira (ta baya ta rago) kunyar bata zo wa Hafsat ba sai wannan lokacin.A lokacin da Abdulazeez ya karbe komai da ya saura a tsakaninsu, ta dawo cikakkiyar Mrs Barrister Abdulazeez Hamzah Atiku. 

Wani matsayi, wani da-kace, wani buri, wani fata, wani kintace, wani mafarki data dade tana yi.Fuskarta ya tallabo da tafukansa ya dube ta ya ce complains time wato (lokacin korafi).

Samun kanta ta yi da jin kunyar Yayan nasu fiye da kowacce rana a tsayin rayuwarsu.

Yo wane complains gare ni bayan ka karyata komai?

 Zancen zuci Hafsat ke yi ba ta san cewa a fili ta ke yi ba!.

Murmushi ya yi ya kankame ta sosai yana dariya mara sauti.

Hafsat ni ban karyata ki ba!.

Rufe idonta ta yi da hannayenta tana shirin guduwa daga saman ruwan cikin sa ya damko ta. Ya juya kwanciyarya koma shine a sama, dogon karan hancinsa na gugar nata ya soma magana cikin sanyin murya.

 Cikin korafinki ban karyata ko daya ba, amma ina so ki maimaita min su yanzu, zan iya ba ki amsa. A dazun na rasa amsar ba ki, saboda ni kaina ban yarda da kaina ba da hukuncin da na dauka a kanmu tun zuwanki. Amma yanzu Im ready to answer you daya bayan daya.

Hannunta ya ji cikin sumar kanshi, cikin jin kunyar kalaman da ta fada masa dazun ta ce. Ni fa abin da ya wuce bana iya dawo da shi Yaya Azeez, bacin rai ne.

Saboda ke ma ba ki yarda da kanki kan abin da ki ka fada din bane Hafsah”.

“Na roke ka don Allah a bar maganar nan sosai take cakude yatsunta cikin sumar kansa duk dai don ta samu ta mantar dashi munanan kalaman data san ta yi amfani dasu gareshi cikin bacin rai.

Ta ya ya zan bar wadannan zafafan korafin naki ban ba ki amsar da ta dace da ke ba?Capital NO Addah Hafsat. Kin ce bana sonki, Mammanki ta gaya miki bana sonki. Hafsat Mammanki ba ta yi min adalci ko kankani, me ya sa ba ki gaya mata ke ma kin fi son bokonki a kaina ba? 

Saboda wannan banzan bokon ki ka kashe min waya mai nuna ba ki da lokacina sai kin gama da abin da ya fi miki ni muhimmanci, sannan za ki saurare ni. Ni da yake ke ce a gabana nawa karatun nake ajewa gefe in samawa zuciyata salama in ji muryarki;it doesnt change the fact that you are not with me but ithelp me a little to feel youbesideme.(Hakan baya canza  gaskiyar cewa bama tare, amma yana taimakamin in ji ki a kusa da ni ko yaya ne). Hafsat ki ka yanke min wannan jin dadin ki ka sanya ni cikin ukuba. Ita Maman naki da nake roko ta hada mu ta ce ba dai da wayarta ba tunda ta ba ki wayarki. Hafsat wannan bai ishe ta ta gane ni na damu da ke ba, ke ba ki da lokacina sai na abin da ba zai amfane ki ranar gobe kiyama ba? Along the way kuma ta ke fada miki bana sonki? Ko kuwa baya ba ta taba canzawa ku a gurinku? Hafsat bari in gaya miki wani abu wanda na lura har yau baki sani ba. 

Ban taba kin ki a zuciyata ba dai-dai da rana daya, saboda ina son Mamanki (Habibah), ta so ni, ta kula da ni kamar dan cikinta. A garin hidimta min ta fadi har hakan yayi sanadin nakudar haihuwarki lokaci bai yi ba. Kullum na tuna wannan ranar zuciyata tana raurawa. Mammah ta yi min tayin aurenki ne at a very wrong time bayan na yi wa Muazatu alkawarin aure. Wani irin so na yi wa Muazatu mara tushe don ni kaina in za a kashe ni kan in fadi dalilin son da nake mata ba zan iya fada ba. Daga baya bayan na zauna da ke na kuma rabu da ke na gane ba son Muazatu nake ba infatuation ne. Ke din dai dana ki kwantar da hankalina a kan ki ke zuciyata ke yi wa so na hakika.

 Kin ce zuciyarki ta zarme, ta zarme da yawa akaina, ta yarda da duk abinda na fada bayan ba gaskiya na fada ba. To Hafsat letthis heart know thatAbdulazeez bashi da kalaman sake maimaitawa don ta yarda dashi but he is morethan zarmewa a kanta. And I thank her (the heart) for this abundance love for me. And I promised eternal love for her alone. Zan kasance mai yi mata uzurin da ban iya yi mata ba, zan so ta fiye da yadda ta so ni, zan kula da ita fiye da yadda zan kula da kaina. Zan ci gaba da ba ta farin ciki fiye da wanda ta bani a daren yau Jumaah ashirin gawatan Fabrairu a birnin NewHaven din Connecticut. A yau ina rokonki Hafsat ki yafe min sabon Ubangijin da na ja ki muka aikata a matsayina na mai hankali da sani fiye da ke (yarjejeniyar aure) wanda haramun ne kuma ta wata fuskar yaudara ne a shariance .

 Bayan Mammah ta hana ki komawa aurena na na sha wahala kafin Baffa Atiku ya yarda su maida aurenmu. Sai da ya zaunar da ni ya ba ni fatawa ta ilmi inda na fahimci ba karamin shirme muka aikata ba. Godiya ta daya ga Allah da na yi gaggawar maida ke dakinki kafin ki gama iddah, yau da ban san makomar rayuwata ba in Mammah ta aura miki wani. Wanda na tabbata da na yi wannan kuskuren hukuncina gareta kenan.

Suhaanah Im sure da hakan ta faru zan iya haukacewa. Ya mannata a kirjinsa sosai tana jin yadda zuciyarsa ke bugawa da sauri-da-sauri. Tsigar jikinsa na tashi,  cikin sanyin murya ta ce.

Ni fa tun a lokacin duk da ba wanda ya gaya mini zuciyata ta gaya min ba abin kirki muka kulla ba, kuma ya zama yaudara ga Mammah.

.Daina tuna min Suhaanah kin ji? Ihate myself ranar da na dawo na tadda Mammah a gadon asibiti. Ya Allah kada ka maimaita min wannan ranar, ke ma ki yi ta istighfari kamar yadda har gobe ban daina ba.

******

Washegari sun gama shirinsu tsaf na tafiya Texas. A jaka guda suka hada kayansu kala bibbiyu. Tare suka yi breakfast wanda Abdulazeez ne ya girka, ya kuma ba ta magani (pain reliever) da Panadol,ko kitchen din ya hana ta shiga. Tafiyar ma ba don ta zame masa dole ba ya ce da ya fasa, sabida duk da tana dauriya don kada ya barta ita kadai ya gane bata jin dadin jikinta, duk da ta gasa jikinta yadda ya kamata da taimakon sa. A cewar Abdulazeezyana son honeymoon-time dinsu ya kasance cikin New Haven Towers kawai. Ita kuma ta ce tana so ta je Texas din, ko ba komai za ta bude ido. Ta kuma labartawa Mammah garuruwan da ta gani a kan hanya.

Ko kuma don ki samo mata dan Texas ba? Mammah is eager to grab hergrandson from you shi ya sa ta kasa hakuri in dawo ta turo min ke nan.

Wata uwar harara ta suburbuda masa tamkar idanun sa fado. Dariya ya yi ya fizgi jakar kayansu ya janyo hannunta yana fadin. Ni da wannan kallon da ake kashe ni da shi ma za a barni in hada assignment din nan?Anya ba a daki za a kulle ni ba sai na samar da baby din nan?

Fisge hannunta ta yi, ta yi gaba cikin fushi. Ya sake riko ta a bakin kofa ya kankame ta. Neman bakinta yake tana kaucewa, amma sai da ya yi nasarar samun shi ya biyar da shi yadda yake so. Daga zaman da ya yi da ita zuwa jiya ya fahimci wannan shi ne weaknessdinta. She enjoys it ko cikin fushi take…. Amma ita kam duk yadda ta so ta fahimci nasa har yau ba ta yi nasara ba. A da ta dauka kissing dinne, a jiya kuma ta ga ba haka bane. Its beyond that…. Abdulazeez is indescribable! Ga saurin fushi, ga wahalar saukowa, in yana yi da kai ya fi kowa saukin kai, in ba ya yi da kai ya fi kuturu ban haushi. Gwani ne kuma sadauki a fannin nunawa matarsa soyayyah!!!

Sun bata lokaci sosai kafin su bar gidan, duk kwalliyar da aka yi sai da aka bata ta aka sake wanka da sabon (dressing). Wanan karon sauri ta yi kafin ya gama abin da yake yi ta sauka kasan gininsu tana jiransa don kada ya kara bata musu lokaci. Ta lura shi soyayyar ta fi masa komai muhimmanci a halin yanzu, duk wani abin da zai yi ya biyo bayanta (soyayyar). He had achieved a lot in life itace kawai bai samu ba. Don haka yanzu da ya same ta bai dauketa da sauki ba. Bata taba ganin mutum serious a kan abin da ya sa gaba irinsa ba. Itama soyayyar seriousness yake bata na gasketare da bat
a dukkan hakkokinta.

Tana wannan tunanin ta ji hannunsa cikin nata. Ta daga fararen idanunta ta dube shi, ya yi kyau cikin sabon dressing din da ya sake fiye da na dazu. Riga ce short-sleeve fara tas an yi rubutun kamfanin Nike a jikinta, trouser dinsa baki sidik shi ma ya fito ne daga Nike’. Farin cambas ya daura a kafarsa shi ma dan gidan Nike, sumar kansa ta kwanta luf sai sheki ta ke, he looks so much like his father. Ta ce a ranta, sai dai shi din cike yake da tarin kuruciya cikin thirtieth dinshi. Ba ta da maaunin da za ta iya dora kiyasin matsayinsa a zuciyarta wanda ya rubanya ya hauhawa sau sabain daga jiya zuwa yau.

“Lets go Mrs. Thinking. Tukunna ma tunanin me ki ke yi na dade a gabanki ba ki sani ba?

Tunanin ina ma zan iya in gaya wa Mommah abin da ka ce, ta san cewa ba ta yi maka gwaninta ba.

Dariya ya yi, ya sha gabanta. Kada ki jawo abin da zan rungume matata a bainar jamaa Hafsah!A duniya akwai Uwa mai tausayi da jin qai irin tawa?She is like mother Terasa!(A humanitarian). Ta kawo min matata a lokacin da ya fi dacewa in a very silent and tranquil environment free from all worries andstresses. Salute to your Mommah! Just tell her I love you and Im making this to you practically and you are responding to the practice tooyadda ya kamata!.

Ta zaro ido, sannan ta kai hannu  ta rufe idanunta, ta mayar dasu ta toshe kunnuwanta biyu.

 Yaya Azeez zan koma gida ka tafi kai kadai. Zaka dode min kunnuwa.

To ki koma mana? Nan garin mata da yawa sai wadda na zaba daga farare zuwa bakake, kuma yadda ki ka maida ni yanzu ba zan iya kwana ni kadai baHafsat. Sai yanzu na san na yi asara mai yawa, wai har shekara da rabi abinda nayi tamissing kenan! Oh me!!!. Ya fada cikin jinjina lamarin da takaicinsa a fili with exclamation.Yana so ya kallo tsakiyar idanunta don gano reaction dinta amma ta ki hakan, tafiyarta kawai take kanta tsaye kamar ta fishi sanin hanya. Wani dan kishin-kishin abunda ya fada a sama na sukarta, kalamansa na gaba kuma suka danne kishin suka suka sanya mata jin kunya, don haka kishi da kunya ne suka taru suka lullube ta suka hanata magana taki yarda ta kalleshi. A gefen titi suke tafiya suna zantukan nan. Abinki da inda ba ruwan kowa da kowa. Ya sakeshan gabanta ya baro jakarsu a baya.

 Hafsat haka mukai ta asara??? Duk yadda ta so daurewa tare da boye fuskarta sai da ta yi dariya mara sauti, sannan ta juya ta janyo  jakarsu da ya bari abayata yi gaba ta barshi. Da sassarfa ya cimmata ya riko hannun damanta har sai da jakar hannunta ta sabule ta kusa faduwa kasa. Sake maimaita tambayarsa yayi shi lallai sai ta bashi amsa zaa cigaba da tafiyar. Dakatawa tayi tana  russunar da gazing dinta daga duban kwayan idanunsa,sannan cikin jin nauyi da sanyin muryarta tace.

“Yanzu dai a kan titi muke Yaya Azeez, kaga an fara kallonmu, reserve your quations sai mun je Texas. Suka hau taxi zuwa filin jirgin kasan Amtrak.

Train suka bi mai zuwa Texas (Dallas) kai tsaye daga NewHaven County, duk station din garin da aka tsaya don daukar fasinja da saukewa sai Hafsat ta tambaye shi sunan garin ya gaya mata. Sun wuce garuruwa daban daban kafin daga karshe jirgin ya tsaya a Dallas(Texas), fasinjoji suka fita, hatta handbag dinta shi ya karba ganin alamun gajiya da ji ga tarin zaman jirgin kasaa tare da ita. A cikin filin jirgin ya saya mata lemo Pepsi mai sanyi da ta ce tana so. Yana fadin wannan shin last timeda zaki sha pepsi dinnan naga kina son ta, tunda kika zo kike shanta kullumbayan cutarwa suke yi. Ba don a jigace take ba har bata son magana da ta ce dashi ba gara ni ba? Kaima ka daina shan Coca-Cola duk uwarsu daya ubansu daya. Kamar ya ji ta, ko da yake Abdulazeez reads her mind easily ta dade gane hakan, wisdom dinshi har tsoro yake bata. Sai cewa yayi nasan motsin da kikeyi da baki ai, ko ni da kika ga ina shan Coca-Cola tozero sugar ce. Sukazauna a karkashin wata rumfaya jirata ta sha, sannan suka fito inda za su samu abin hawa. Da wayarsa ya yi amfani wajen samo hotel mafi kusa da kotun da zai yi abin da ya kawo shi. Ya gaya wa mai motar inda zai kaisu suka shiga suka tafi.

Karamin daki ya kama musu ciki daya (falle daya) kwana biyu, ya sa katin a kofar ta bude ya shigar da jakarsu. Ta bi shi a baya ya maida kofar ya rufe. Hafsat tsaye ta yi a jikin kofar tana kakabin yadda za ta rayu daga ita sai Abdulazeez a wannan dan karamin dakin, shi kansa gadon bai fi mutum daya ya kwanta a kanshi ba. 

Da ta sani ta hakura ta zauna a NewHaven kamar yadda ya ce da farko, to in za ta canza kaya ko shi zai canza ya za a yi kenan? In za su yi wanka fa? Ta kasan ido ya dube ta yana zaune gefen gadon yana warware igiyar cambas dinsa, abinki da Lawyer nan da nan ya gano abin da ta ke tunani. Murmushi ya yi ya ci gaba da cire takalminya zare socks, sai da ya gama tsaf sannan ya dago ya dube ta a kaikaice.

Akwai wani dare da ya saura ne da Jemage bai gani ba???”

Ban gane abin da ka ce ba, waye jemage? Ta amsa innocently.

Mikewa ya yi ya tako har inda ta ke kyawawan tafukansa na mannnewa akan marblesya tsaya a gabanta, space din da ke tsakaninsu ba shi da tazara, hannayensa biyu ya dora a kafadunta, daya a kafadar  hagu daya a ta dama. Ya rage tsawonsa suka yi kai daya sannan ya dube ta cikin idanunta da shanyayyun idanunsa,fitarnumfashinsu na sarkewa dana juna.

 Da na sani Hausa na nema miki a jamia Hafsah.

Murmushi ta yi kumatunta suka lotsa sosai. Itama Hausar karantarta ake yi??

Kwarai kuwa, yadda ake karanta Geography.

Ya sa hannu ya soma warware mata lullubin dake kanta, ya saki mayafin a kasa, ya kai hannu kan hudar karan hancinta da barimar danyen gold yar kankanuwa ta dade da samun muhalli yana mai zagaye barimar da dan alinsa.Yana daga abinda yake so a kawatacciyar fuskarta maabociyar zati da kamala wannan hular hancin,sai kuma ya zarce da hannun  damansa saman kanta ya shafo kwantaccen gashinta mai santsi da sheki tun daga farkonsa har karshensa.Sannan ya hada mikakken karan hancinsu wuri guda ya soma magana cikin wata irin kasalalliyar murya. 

Mommanki ba ta gaya miki daga ranar da ta aura min ke mun zama sirrin juna ba? Ba ta gaya miki mun zama marufar asirin juna ba? Ba ta gaya miki mun  zama abu guda ba babu sauran boye-boye ko kunya a tsakaninmu? Na dauka kunyar ta kare daga jiya Hafsah?Amma na gani cikin kwayar idanunki kina kokonton zama da ni Abdulazeez a dan tsukukun daki???”

Dariya ta yi ta somakokarin sunne kanta cikin jikinshi. Ba dama tayi magana cikin ranta sai Abdulazeez dinnan ya karanta? Bai bata damar hakan ba (buyan) ya dago fuskarta yana so su hada ido ta rufe idon da azama.Thelong eye lashes…. suka bi idon suka kwanta luf; wani abu da ya dade da lura da cewa yana tsananin fizgar zuciyarsa zuwa gare ta ya sumbaci idanunta ko bai niyya ba. Fuskarta ya saka cikin tafukansa ya ce.

 Kina min wannan lumshe idon Hafsat, za ki bari in yi assignment dinnan kuwa?

Babu kuzari a cikin muryarsa a lokacin da yake fadin hakan. Bude idanun nata ta yi da sauri. Ni fa ba lumshe ido nake ba,ido ne bana so mu hada.

Saboda me toh? Hafsah in ba ki kalle ni ba wa za ki kalla? Ko ni in ban kalle ki ba wace pretty face zan kalla haka?

Murmushi ta yi sosai da jin kalamansa. Don Allah ka je ka yi assignment dinka.Ina so ka ci maki da yawa kafi duk abokan aikin ka cinyewa.

Dariya ta ba shi sosai, wai cinyewa kamar wani abinci.Ya janyo ta sannu a hankaliya rungume tsantsan a jikinsa, ya ce. Ashe kina sona haka da yawa Hafsat? Me ya sa ba ki gaya min ba tun muna gidanmu? Saidai ki dinga ga kallon hoto na a waya a cikin duvet?

Hannuwanta ya ji ta zagaya a bayansa ta rike shi gam-gam itama. Saboda na san ba ka sona lokacin Yaya Azeez, kaga fadar ba abinda zata sauya sai ma dai ta lalata komai,kuma ko na fada babu amfani tunda sakina za ka yi ka auro Muazatu.

Lumshe idanunsa ya yi, kansa a kafadunta, idanunsa a rufe yana shakar daddadan scent din gashinta, ya ce.

Kin san wani abu?

Aah.

Ban yi wa Muazatu irin son da nake miki ba Hafsat. Ko kusa da juna basu je ba. Ni dai kawai in aure ta shi
ne babbar damuwata, wata damuwa data tsaya ta tokare a raina. Abin da nake ji kawai shi ne sai na aure ta ne zan samu kwanciyar hankali da nutsuwa, ko hannunta ban taba shaawar in kama haka kawai ba. Hirarrakinmu babu bond babu ties irin wanda nake ji in ina hira dake kamar zan zauce.Hirarrakinmu sun fi yawa a kan karatunta, rayuwarta da alamuranta. And I respect her Dad (ina girmama Babanta), wannan shi ne tsakanina da Muazatu Rufai which is totally opposite to your case.

Hafsat tun daga ranar da ki ka sa ni a gaba kina tambayata wai ‘sex is not allowed in Nigeria na fahimci you are very very innocent, your heart is soft and freshbabu komai a cikinta sai tarin tsabta da kuruciya. Ranar da na yi rashin lafiya ki ka kula da ni na kara fahimtar zuciyarki mai kyau ce, kuma kin san hakkin abokin zamanki duk da kuruciyarki ko da bana dadada miki. I cannont recall when I started touching you and how,but your protest….???Hummm! Ya fahimtar da ni kin kulle wani abu a ranki a kan zamanmu, kin fara sanin ciwon  kanki wanda a da ba ki sani ba. Kina kullace da ni akan wasa da rayuwar ki, kuma a shirye kike da ki yi fighting dina for your rightda na danne a kan wata. Tun daga lokacin Hafsat na soma tsoronki, na fara shiga taitayi na, na kuma fara sansano wata rana na zuwa da ke din nan da nake rainawa za ki juya duniyata idan ban yi da gaske ba. 

Ban fita daga wannan taraddadin ba na soma hada jiki da ke ba tare da zuciyata ta yi shawara da ni akan hakan ba . Hafsah ba zan iya hakan da macen da bana so ba. Inada kyama inada tsantseni.Im very sensitive and cautious ga inda zan kai hannu na balle jiki na. Your protest brought a number of sleepless nights to me!!! Ba zan iya gaya miki halin da na shiga ba saboda a lokacin na yi zargin kin fara sona kamar yadda na samu zuciyata da hakan ina karyatawa da gangan, za ki bari mu mori auren ko ya ya ne, soyayya ta sa a manta da kwangilar har sai lokacin ta ya zo. Sai kika nuna min kin san abin da ki ke yi, wanda hakan ya sa ni jin kunyarki, ya kara miki kimaa idanuna. Ya tattaro miki daraja mai yawa, na zo ina tababar yiwuwar rabuwar nan. Na shiga tsaka mai wuya, ga alkawari ga soyayyar gaskiya ta huda ni. A lokacin na yardar wa kaina na zalunce ki da wannan contract da na jefa mu a ciki, amma na rasa hanyar fita. I then concluded in fita daga sarkakiyar da na jefa kaina daga baya in dawo da ke mu gyara aurenmu ba tare da kowa ya ji ba. 

Lokaci ya yi min halinsa ko in ce Allah bai barni na yi yadda na ga dama da rayuwarki ba, sai da Ya hukunta ni, Ya dandana min azabar subucewarki daga hannuna. A karo na biyu ina rokonki ki yafe mini domin hakika na zalunce mu bakidayanmu..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *