AUREN TAGWAYE CHAPTER A
.
*Amincin Allah ya tabbata ga wad’anda zasu karanta wannan labari nawa dama Wad’anda basu samu damar karantawaba ina maku fatan Alkhairi akodayaushe*
~Note~
*Wannan labari ‘kir’kirarane banyi dan wani ko wataba, ko satar fasahar wani saboda haka duk Wanda/wacce taga yazo dai-dai danata abune yazo d’aya sai ha’kuri*
.
“Hassana waike bazakiyi sauri mutafiba ke kullum idan mutum yahad’a abu dake sai ranshi ya 6aci, yanzu dan Allah so kike daddy yadawo yahanamu fita, kuma sanin kankine muddin idan banje *Dinner* d’innan ba zuby bazataji dad’iba kinsanfa bikinnan na best friend d’inta ne, kuma ta gayyacemu ba dad’i mu’ki attending.
Cikin sanyin murya wacce aka kira Hassana take magana “Haba Hussaina nifa wlh banison wannan abun dakikeyi, ke shikenan koda yaushe da an gayyaceki ferty kin dinga ‘kyarma kenan kamar wacce aka gayyata zuwa aikin hajji.
Magan-ganun Hassana suka ‘kara harzu’ka Hussaina cikin bala’i da d’aga murya take cewa “dallah malama kada ki gayamin magana, ke dama duk wata harka ta wayewa baki santaba, idan bazakiba basai kin gayamin maganaba kawai ki zauna a gida, haka zaki ‘kare, kullum kitchen.
Zama Hassana tayi bakin gado tare da cire mayafin data sanya, “nikam bazaniba kitafi kawai sai kindawo, ni dama wlh hankalina be kwanta da tafiya wannan *dinner* d’inba kiduba agogo yanzufa ‘karfe bakwai da rabi na dare.
Jin Hassana tace bazataba yasa Hussaina zuwa kusa da ita ta du’ko dai-dai fuskarta har numfashinsu na gauraya dana juna, sannan tafara magana cikin sanyin murya.
“Haba my sweet sister, plz ayimin ha’kuri kinsan bazan iya tafiya batare dakeba……
Ringing d’in wayarta ya katseta da maganar datake, da sauri tasa hannu ta d’auko sunan Zuby tagani yana yawo kan screen d’in wayar da sauri ta danna OK tare da karawa a kunne.
“Hellow Zuby ya?
A d’aya 6angaren zuby ta amsa
“Haba ‘kawata me kike har yanzu baki fitoba, halan wannan sister taki ce take maki kofsi.
Hussaina kallon Hassana tayi sannan tace “a’a yanzu zamu taho, tare da itama zamuzo.
“Dan Allah kuyi Sauri.
“Owk kawai Hussaina tafad’a tare da tsinke kiran.
A Falo suka tarad da momynsu tana kallon tashar sunnah TV, cikin ladabi sukaje gabanta Hassana tace “Momy zamu tafi.
Momy ta kalle yaran nata daga sama har ‘kasa babu wata shiga ta aibu tattare dasu, atamface suka sanya d’inkin Riga da zani pieces, sai wadataccen gyalen da suka yafa.
“To amma kada Ku wuce ‘karfe tara kunsan dai tara da rabi dadynku yake dawowa gida, Momy tafad’a tana ‘karemasu kallo,
Hussaina ce tayi saurin cewa “kada kidamu Momy Tara a gida zatayi mamu.
Hassana tace “insha Allah Momy munyi maki wannan al’kawarin.
“To shikenan kuje Allah maku Albarka
Tare suka amsa da Ameen sannan suka fice daga gidan.
.
Suna fita get sukayi ‘yar tafiya kad’an sukasamu napep suka fad’a masa inda ze kaisu.
.
Lokacin dasuka ‘karaso had’addiyar Hotel d’in da’ake gudanar da *dinner* d’in kai tsaye suka nufi hall d’inda suka tabbatar da nanne ake farty saboda mutanen dasuka hango ciki.
Suna shiga lokacin Zuby na zaune suna labari itada wani boy friend d’inta wanda tadad’e da afkawa kogin ‘kaunarsa tasha nuna masa haka amma ya’ki yagane dan kwata- kwata Zuby bata cikin tsarin kalar yan matan dayakeso kawai dai yabarta a matsayin Friend.
.
Cike da farinciki Zuby ta tarbo ‘kawarta Hussaina, ko kallan Hassana batayiba, Hassana ma nunawa tayi batasan da zaman wata halitta wai ita zuby ba, dan ita dama tun can jininta be had’u dana zuby ba.
Guri suka samu suka zazzauna kan kujerun dake Jere a hall d’in.
Zuby ta kalli boy friend d’inta sannan takira sunansa “Hafiz, ga ‘kawayena danake gayama ‘yan biyu ne, wannan itace Hussaina wannan kuma itace Hassana tafad’a tana nuna Hassana yayinda itakuma ta kauda kanta gefe dan ko kad’an ita batason a had’ata da wani namiji barantana kuma har suyi wata magana, shiyasa kodayaushe Hussaina da Zubby suke kiranta bata wayeba.
Haka suka zauna zuby sai wani shishshigema Hafiz takeyi tanata mashi surutu, shikuma kwata- kwata hankalinsa be kanta, tunda su Hassana suka shigo idanunsa suke kan Hussaina, yariga yagama fad’awa kogin ‘kaunarta, wanda zuby bata lura da hakanba, amma ita Hussainar ta dad’e da d’agowa dashi kodan yanda dasun had’a ido yake sakar mata wani tsadadden murmushi, dama gashi kyakkyawa ajin farko, take itama Hussaina taji takamu da sonshi.
Wani irin kid’ane ya tashi lokacin da Mr DJ ya kunna Speaker’s d’insa, wayyo jikin zuby har 6ari yake, dama haka take mayyar rawace duk sun dad’e da sanin haka saboda haka basuyi mamakin hangonta tsakiyar fage ita kad’ai tana caskad’ewaba, ba kunya take rawar sai wani kaso shoki takeyi….. _Lol_
Lokacin Hafiz yasamu damar yima Hussina magana, “Ya kike ‘yan mata, wayyo wani iri Hussina taji a jikinta lokacin da ta tsinkayi muryar Hafiz a kunnenta, a zuciyarta tace “Wow fantastic, nice voice, Ashe dai yanda yahad’u hakama murayarsa ta had’u gaskiya gayen yagama had’ewa.
Lokacin Hafiz yasake magana karo na biyu batare da Hussaina tabashi amsar ta farkoba, “idan bazaki damuba kisakamin numberki ko bayan kin koma gida sai muyi magana,
Ba musu ta amsa tasakamai numberta, sannan ta mikamar wayar dayake Hafiz gogaggen d’an duniyane gurin amsar wayar saida yahad’o da hannunta, suduka wani irin shock sukaji lokacin da tattausan hannuwansu suka had’u dana juna, kasa sakin hannunta Hafiz yayi sunkai kimanin minti biyu a haka sai itace tayi ‘karfin halin zare hannunta daga nashi, kashe mata ido yayi tare da sakar mata wani ‘kawataccen murmushi.
Duk abinda sukeyi Hassna batasaniba duk da guri d’aya suke zaune, hankalinta nakan wayartane tana chat a wani group na Zee Mmn khady me suna *Ciwon Ya mace* tanajin dad’in group d’in sosai yanda ake bada shawara me kyau da kuma yanayin abubuwan amfani da ake turowa, ba kamar kuma Had’in kai da ‘yan group d’in suke dashi, duk da yanda takejin dad’in chat da *Mmn Ummi da Ameeno, Mmn Ramadan da rukky abdull* hakan behanta duba lokaciba dan kada suyi dare basu koma gidaba, dan yanzuma data duba ‘karfe takwas da rabi, tasama ranta takwas da minti arba’in zasu koma gida.
Muryar Hussaina ta tsinkaya “Hassna dan Allah aromin wayarki zanyi kira, bansan credit d’ina yakareba, ba musu Hassana ta mi’kamata “amma gaskiya dakin gama wayar zamu tafi saboda tara takusa kuma kinsan Al’kawarin da muka d’aukoma momy,
“To kawai Hussaina tace, tawuce tanufi gunrinda akayi parking d’in motoci kamar tana wayar gaske.
Dai-dai motar da Hafiz yafad’amata nan ta tsaya, jingina tayi da motar idanunta akan wayarta.
Tashi Hafiz yayi yabi bayanta, Hassana na kallo amma bata kawo kome a rantaba, iatadai fatanta kawai idan Hussaina tagama wayar datadawo sutafi gida
.
Bud’e motar Hafiz yayi gidan baya suka shiga, kasancewar motar tanada ba’kin glass bazeba wanda ke waje damar ganin nacikiba dukda dama gurin akwai duhun dare,
Ac Hafiz ya kunna musu, take motar tad’au sanyi tare da wani daddad’an ‘kamshi
Zaune suke gaf da juna har jikinsu na had’uwa dana junansu, Hafiz ne yafara magana cikin kwarewa da gogewa na yan duniya “Babyna ammafa kin had’u kinganki kuwa kamar matan hurul’ayni, wani ‘kawataccen murmushi Hussaina tayi tare dasa hannunta tarufe fuskarta, duba Hafiz yakai kan shantala-shantalan yatsun hannunta wanda yake d’auke da awarwaraye da wani had’adden zobe na azurfa, hannu yasa Yakama hannun nata yamatse a hannunsa, sannan yafara wasa da zoben “kai amma ring d’innan yayimin kyau babyna, amma set ne tare da sarkarki koh?
Yafad’a tare dakai hannunsa kan wuyanta yana wasa da sarkarta, lokacin yagama kashema Hussaina jiki yanda yake shafar wuyanta, ko magana bata iyawa sai maida numfashi datake d’aya d’aya, hakan yabashi damar yin ‘kasa da hannunsa zuwa cikin rigarta yafara wasa da breast d’inta, wani irin yarrrr taji ajikinta, saboda ba’kon Al’amarin daya risketa yau, domin Hafiz shine mutum na farko daya fara yimata irin wannan wasan, suna soyayya da Jabeer amma koda wasa beta6a kai hannunsa kan jikintaba, “hakan yana nufin jabeer be iya soyayyabane ko miye….
Tana cikin wannan tunanin taji Hafiz ya rungomota yahad’ata da jikishi, yana rad’amata kalmar “I love you a kunnenta, cikin kasalalliyar murya tace “mee too my Dear,
“Wow nice my Baby, Hafiz yafad’a tare da had’e bakinsa da nata yacigaba da kissing d’inta.
Dare yafara Hankalin Hassana ya masifar tashi dan tanemi Hussaina ko’ina a cikin hall d’in da wajen hall d’in amma bata gantaba, duk tabi tarud’e, gashi Zuby tunda tashiga fagen rawa batako wai-waiyesuba barantana ta tambayeta kotasan inda Hussainar take gashi tatafimata da waya barantana takirata.
Komawa tayi kan kujera ta zauna tayi tagumi hannu bibbiyu,
Can Hankalin Zuby yayo kan inda tabarsu Hussaina amma batagansuba sai Hassana wacce tahad’a hannuwa biyu ta tallabe kumatunta kwalla suncika idanunta, da sauri zuby takaraso inda take “Ke ina ‘yar’uwarki? Hassana batajitaba dan tayi nisa cikin tunanin irin hukuncin da daddy ze yanke masu idan yadawo ya tarar da basunan, batakaran suba ranar momynsuma bazata fitaba dan dady mutumne me zafi tsaye yake kan tarbiyar iyalanshi.
Ta6ota zuby tayi “tambayarki nake ina Hussaina?
Sai lokacin tadawo daga tunanin datake “nima wlh ita nake nema dan Allah ki kiramin ita da wayarki danni tatafi da tawa wayar.
“To ina Hafiz? Zuby ta’kara jeho mata wannan tamabayar
“Kinga ni dukansu bansan inda sukeba, nidai dan Allah ki taimaka ki kiramin Hussaina mutafi gida.
Take zuciyar Zuby tabata akwai wata kulalliya tsakanin Hafiz da Hussaina, idan kau hakane lallai Hussaina tad’auko ruwan dafa kanta.
Wayarta ta fiddo daga cikin poss tafara lalubar number Hussaina, kusan kira takwas zuby tayima Hussaina no answer, hakan ba ‘karamin ‘kular da ita yayiba, batako kalli Hassanaba tabar gurin tana cika tana batsewa.
Ganin dare na’karyi yasa Hassana tambayar wata budurwa kusa da ita “dan Allah ‘karfe nawa?
Duba wayar tayi “karfe tara da Monti takwas tabata amsa a ta’kaice.
Cike da rud’ewa Hassana tatashi tafita harabar hotel d’in Allah ya taimaketa lokacin wani me napep ya sauke wasu, tagayamshi inda ze kaita, saida suka d’au hanya tafara tunanin inda ‘yar’uwar tata tashiga “Toni yanzu mezanfad’ama Momy idan aka tambayeni Hussaina, wasu hawaye suka gangaro kan kumatunta.
“Allah sa dai tana lafiya duk inda take.
Tana cikin wannan tunanin har suka iso ‘kofar gidansu batamasan sunzoba saida me napep yace “hajiya mun isofa sannan ta sallameshi tafita daga napep d’in.
Jiki a sanyaye tanufi gidansu, ahankali ta kwankwasa megadi yabud’emata bayan yatambayeta tagayamashi itace.
Ahankali tashiga gidan da sallama Momy tagani zaune tayi tagumi koba tambaya tasan jiran dawowarsu takeyi, ganin Hassana yasa Momy sauke wata ajiyar zuciya, “Alhmdlh ina ‘yar’uwar taki take?
Hawaye yacigaba da zuba daga idon Hassana batare databa Momy amsar tambayar datayimataba, cikin tashin hankali Momy ta’karaso inda Hassana take takama kafad’unta “ina take nace? Ko wani abu ya sameta? Kifad’amin……
Ganin hankalin Momy yatashi yasa Hassana goge hawayenta “bawani abu yasametaba kawai na nemeta bangantaba, kuma gashi dare yayi…
“Subhannallah Momy tafad’a Allah sa dai lafiya, kin kira wayarta? “Nima wayata tana hannunta.
Hankali tashe Momy tasa wayarta takira Hussaina itama no answer aka gayamata kamar yanda duk wanda yakira ake gayamai, saida tayi kira kusan na goma sannan Hussaina ta d’auka cikin kasalalliyar murya tafara magana dan lokacin tana jikin Hafiz yagama rabata da rigarta yana ‘ko’karin ciremata breziya,
Cikin fad’a Momy tace “dan Ubanki kiyi maza ki dawo gidan tun kafin dadynku yadawo, batajira me Hussaina zatafad’aba Momy takashe wayar
Lokacin sukajiyo horn d’in motar Alamar dawowar me gidan, cikin tsananin tashin hankali Hassana tafara magana “Momy dadyne yadawo nashiga ukku tafad’a tana yarfe hannu.
Da sauri Momy tace “maza ki shige d’akinku kada yazo yaga batanan, Dan batakaran itadayi laifinba mu kanmu sai rayukanmu sun 6aci.
Da sauri Hassana tashige d’aki, zama tayi bakin gado tayi tagumi hannu bibbiyu tana tunanin ‘yar’uwarta.
Hassana na daga d’akinsu taji shigowar daddy wani mummunan fad’uwar gaba taji, tanajin lokacin da Momy kemasa sannu da zuwa, yana zama ba abinda yafara tambaya sai “Ina yarannan suke? Cikin inda-inda Momy tabashi amsa “uhm am suna d’akinsu ko Alh….
Kwalamasu kira yashigayi “Hassana….Hussaina….
Hassana naji tayi saurin Amsawa “na’am…
“Kuzo nan ina nemanku “to ta amsa jiki na kyarma tasako d’an karamin hijab d’inta ta fito, durkusawa tayi gaban daddy “gani daddy tafad’a tare da sunkuyar da kanta ‘kasa gabanta sai dukan tara-tara yake.
“Ina ‘yar’uwar taki? Daddy ya tambaya, “im ahm….uhmmm tafara inda-inda tarasa wace amsa zata bayar domin kare ‘yar’uwarta shiru tayi tana wasa da yatsun hannunta.
Tsawa daddy ya kwatsa mata “ke…. Ba magana nike dakeba ina ‘yar’uwarki nace? Jiki na ‘kyarma tafara magana tana d’an ja da baya dan taga yanda daddyn nasu ya zuciya a lokacin ze iya mazgeta, “daddy munje walimar bikin wata ‘kawarmune shine dazan taho nayita nemanta bangantaba shine nikuma nataho,
“Owk good hakan yayi kyau, shine ita ta zauna dan bata tsoron fushina, aiko ranta inyayi dubu a gidannan yau sai ya 6aci, kallon Momy yayi “kekuma kinsan bata dawoba amma ko ajikinki saboda baki damu da tarbiyar yarankiba ko “haba Alhj ya zakace bandamu da tarbiyarsuba, wlh tun d’azu nake faman kiran wayarta sai tacemun gatanan to ya kakeso inyi? Ko zuwa zanyi intaho da ita,
“A’a ba tahowa zakiyi da itaba, idan bakije kika taho da itaba nizan taho da ita dakaina, yafad’a yana nuni da ‘kirjinshi da hannu.
Bejira abinda zatafad’aba ya zari cable d’in jikin tv yafita zuwa harabar gidan,
Me gadi na hangoshi tafe yataso da sauri “Sannu da fitowa Alhj, “yauwa mal bala, abinda kawai ya furta kenan sannan yafita daga wajen get d’in gidan ya tsaya ya maida hannuwanshi duka baya, yafara safa da marwa yana jiran yaga ta ina Hussaina zata 6ullo, tsawon kimanin minti goma sha biyar yana zarya gurin Amma bako Alamarta, mal bala me gadine ya le’ko cikin girmamawa yafara magana “Alhj lafiya kuwa naganka haka kamar hankalinka a tashe?
“Mal bala yarinyarnan ni zata rainama hankali ni zata maida mutumin banza cikin garinnan, da darajata da ‘kimata ace wai har kamar ‘yanzu ‘karfe goma da minti ashirin da takwas yarana suna gantali a gari.
Mal bala yace “amma Alh ai naga kamar sundawo ko? “Gudace tadawo yanzu jiran dawowar d’ayar nake.
“To Alhj Allah maidota lafiya, Allah sa duk inda take tana lafiya.
Komawa mal bala yayi daga ciki ya zauna kan d’an bencinshi, yanda hankalin Alhj yatashi shima duk sai yajishi cikin damuwa, saboda Alhj mutum ne harda rabin mutum.
Da misalin ‘karfe sha d’aya saura minti goma, lokacin Alhj yagaji da zarya tsakanin wajen get d’in gidan zuwa cikin gida, yana zaune kan bencin mal bala, tsayuwar mota yaji dai-dai get d’in gidansa da sauri Alhj ya mi’ke le’kawa yayi lokacin Har Hussaina tafito daga motar me motar yayi gaba abinsa,
Momy kuwa da Hassana suna cikin gida hankalinsu a tashe, Hassana banda kuka ba abinda takeyi.
Hussaina kuwa bayan Hafiz ya ajiyeta ya wuce sai lokacin wani mugun tsoro ya dirar mata cikin zuciya, jikinta yafara ‘kyarma, hankalinta be ‘kara tashiba saida taduba agogo taga ‘karfe sha d’aya na dare, ahankali tafara buga get d’in gidan, da sauri mal bala yazo ya bud’e mata tana Shiga,tafara tafiya da sauri tana wai-waye saida tazo gab dashiga falon gidan ta tsaya tacire takalminta dan kada ajiyo ‘karar tafiyarta, ri’ke takalmin tayi a hannu sannan tatura ‘kyauren falon ahankali.
Jitayi an sha’kota ta baya a firgice ta juyo, ido biyu sukayi da daddy beyi wata-wataba yafara zabga mata cable wayar dake hannunsa nan tafasa ‘kara tana ihu, amma daddy be sauraramataba, tsulamata wayar yakeyi iya ‘karfinshi, mommy da Hassana suna daga falo sukajiyo ihunta, wani sabon kuka ya kwacema Hassana cewa take “Momy dan Allah ki taimaki Hussaina kiba daddy ha’kuri kada yajimata ciwo, kallonta Momy tayi cikin nuna rashin halin damuwa tace “koma miye ita tajama kanta ‘kara yadaketa gobe bazata ‘karaba.
Da gudu tashigo falon kamar wacce aka jeho, bayan Momy tanufa tana kuka ta ‘kan’kameta “wayyo Momy dan Allah ki taimakeni wlh bazan ‘karaba,
6an6areta Momy tayi daga jikinta tare da barin gurin tana cewa “lokacin dakikayi rashin jin naki kinyi shawara dani, dan haka kada ki nemi taimakona can ki ‘karata jiki magayi, shigewarta tayi d’aki ta maida ‘kofarta tarufe, wani irin kuka Hassana tafashe dashi ganin momy batada niyyar baiwa dady ha’kuri shikuma beda niyyar hakura, rugowa tayi tari’ke hannun daddy tanamashi magiya “dan Allah daddy kayimata ha’kuri bazata ‘karaba, a harzu’ke daddy ya hankad’ar da Hassana gefe guda yacigaba da suburbud’ar Hussaina, suduka suke kuka suna bashi ha’kuri amma beko sauraresuba saida ya tabbatar Hussaina ta daku sannan ya rabu da ita yanufi d’akinshi yana huci yana cewa “gobema ki kara tafiya ki wuce magrib baki dawo gidaba wannan kad’an nayima shashasha kawai.
Kama hannunta Hassana tayi suka nufi d’akinsu, da kyar Husaina take tafiya saboda ba ‘karamin duka tasha hannun daddynsu ba,
Zaunar da ita Hassana tayi bakin gado tana sharar kwallah, tace “kinga abinda nake gujemaki koh, ba irin neman dabanyimaki gurin *dinner* d’innan ba amma ban gankiba, wai ina kikajene?
Cikin dasashshiyar murya Hussaina tace “uhm yanzu banida lokacin dazanbaki wannan amsar,
Toilet Hassana tanufa batare data ‘karama Hussaina wata maganaba ruwan d’umi tahad’amata tarakata har toilet sannan tajawo mata ‘kofar, haka tayi wanka ta gargasa jikinta bayan tafito Hassana tasa Robb ta shafemata jikinta sannan sukabi lafiyar gado, kowace tayi shiru kamar me bacci a zahiri amma kowace da tunanin datake cikin zuciyarta, Hussaina tunanin Hafiz ne fall cukushe a zuciyarta, “lallai Hafiz ya iya soyayya, yanzu nagane jabeer ba kome ya iyaba a fanni soyayya sai dai kullum idan yazo yakamayimani nasiha da sauransu, nikam nafison namiji d’an life Wanda yasan takan love, gaskiya akwai sakal kan maganaraurean da jabeer dan ni yanzu babu namijin danake muradi a rayuwa kamar Hafiz, dan Abinda ya faru tsakaninmu yau yasa naji bana bukatar kowane namiji sai shi.
Hassana kuwa tunani take shin ina ‘yar’uwarta tashiga har takai wannan daren bata dawo gidaba, Allah sa dai Hussaina bata biyema samarin shahoba, mayaudara “Hmm tafad’a shiyasa niko Alama bana harkar samari.
Da haka ta gyara kwanciyarta bacci yayi awon gaba da ita.
6angaren dady kuwa bacci gagaran idanunsa yayi tashi yayi ya zauna gefen gado ya zabga uban tagumi, zuwa can kuma yami’ke tsaye yafara safa da marwa cikin d’aki, “lallai dole inyi saurin yima tufkar hanci, saina tashi tsaye kan tarbiyar yaranan, saboda zamaninnan yanzu saika haifi d’a baka haifi halinsaba. Kusan raba dare daddy yayi yana tunani.
** ** ** **
Washe gari zaune suke kan dining suna breakfast bakajin motsin kome sai ‘karar plate da cokulla, kowane ka kallah cikinsu rai a dagule dakuma tunanin abinda yafaru jiya.
Bayan sun kammala daddy yayi gyaran murya “kunajina? Suduka suka jiyo suka kalleshi, “tunda abin naku yazama lalata inaso insanar daku na soke maganar makarntar dazakuje *AMUSLIM COMMUNITY SCIENCE &TECHNOLOGY FUTUA* daga yau kucireta a ranku kuduka aure zanyimaku, ke Hassana inaso kifito da miji nanda wata d’aya, ke Kuma Hussaina ya watsamata wani matsiyacin kallo “kigayama jabeer inason ganinshi, wani irin Fad’uwar gaba Hussaina taji dajin dady yace yana neman jabeer, sadda kai tayi ‘kasa “daddy nifa mundad’e da 6atawa da jabeer.
Shiru daddy yayi yana kallonta, toki fiddo miji nanda wata d’aya, idan kika wuce iya adadin kwanakin dana ebar miki zand’au duk matakin danaga ya dace.
Mi’kewa yayi tare da d’aukar jakarsa ta zuwa office sannan ya kalli Momy “maganar fita kuma daga yau nakasheta idan sunbar gidannan a tabbatar islamiyya zasu, yana gama fad’a yasa kai yafice
*Bayan sati d’aya*
Hassana da Hussaina sun daina fita konan da can kullum sai dai idan zasu islamiyya, maganar fitar da miji kuwa kullum sai daddynsu ya tinasar dasu,
Yauma kamar kullum zaune suke kan had’addun kujerun dake zagaye da babban falon gidan, Hassana ta kalli Hussaina, “nikam sister inaso muyi wata magana dake,
“Ina jinki Hussaina tafad’a,
“Wai meyasa kikacema Abba kun 6ata da jebeer Alhalin ba abinda yashiga tsakaninku,
Murmushi Hussaina tayi sannan ta d’au ‘kafa d’aya ta d’ora kan d’aya tana girgizawa “ba wani dalili kawai tsuntsun ‘kaunarsane ya canja she’ka.
Tana fad’in haka ta maida hankalinta kan wayarta wacce suke chat itada Hafiz suna tattauna yanda za’ayi su had’u dan tun ranar da daddy yahanasu fita tasanar dashi, shikuma kullum sai yakirata yakai sau goma yanamata magiya akan dan Allah tayi dabarar dazasu had’u koda na minti biyar ne.
Sauke ajiyar Zuciya Hussaina tayi, tace “amma Hussaina idan kikayima jabeer haka kinci amana, kinriga kinsan irin so da ‘kaunar dayake nunamaki, zeyi wuya kisamu namijin daze soki kamar jabeer.
“Ba wani wuya, Hussaina tafad’a saboda nadad’e dasamun wanda ya mayemin gurbinsa, cike da mamaki Hussaina ta kalleta wannan wanene wanda yayi ‘karfin halin raba Zukatan dasuka dad’e suna maradin zama abu guda,
“Murmushi Hussaina tayi tare da mi’kewa tsaye tayi taku biyu zuwa ukku sannan tajuyo ta kalli Hassana wacce kebinta da ido tana jiran jin amsarta “Ba wani bane kinsanshi, Hafiz Wanda muka had’u dashi gurin *dinner* itama Hassana mi’kewa tayi ta isa inda Hussaina take cike da mamaki “indai Wannan Hafiz d’in kike nufi wlh inabaki shawara da kada kiyi sakin na hannu kamun na guje danni wannan Hafiz d’in da kike gani kwata-kwata be kwantamin araiba da ganinshi yafi kama da yan abi yarima asha kid’a,
Hannunta takai kan kafad’ar Hussaina ta dafata “sister iname baki shawara kada kibari jabeer ya su6uce maki dan samun namiji kamarsa a wannan zamanin sai antona……
“Ke dakata, hussaina tafad’a cikin d’aga murya, kada ki kawomin ‘kabli da ba’adi nace banison jabeer idan ke kinasonshi ki aureshi mana wani yahanaki, “Hmm aini tun farko bani yace yansoba, amma in bancin haka banga abin ‘ki gareshiba.
“Mtsswww, Hussaina taja wani dogon tsaki sannan tanufi bedroom tabar Hassana nan tsaye cike da mamakin hali irin na ‘yar’uwarta.
Hussaina kuwa tana shiga d’aki kiran Hafiz yashigo wayarta, cike da farinciki ta d’auka bayan ta sumbaci wayar dan a kullum ‘karajin son Hafiz takeyi cikin zuciyarta.
“hellow babyna,
“uhm my dear ya kake tafad’a cikin shagwa6a.
“Eh to gaskiya ba lafiya…
“subhannallah meyasameka tafad’a tare da gyara zamanta.
“kin’ki muhad’u dan baki d’auki son danikemaki a bakin komeba.
Wata nannauyar ajiyar zuciya ta sauke “Haba my dear dan saboda wannan zakace bakada lafiya, indai wannan ne ka kwantar da hankalinka yau idan nafito islamiyya zamu had’u.
“Wow babyna amma naji dad’i, ‘karfe nawa kuke fitowa?
‘Karfe hud’une mukoma shidda, kaga wannan lokacin ya ishemu mud’an gaisa.
“Eh to hakane amma kinsanfa nayi missing d’inki sosai.
“Hmm sai munhad’un kawai tafad’a
“Owk bye “muaaah yasakar mata wani kiss ta wayar sannan ya tsinke kiran, wani dad’i taji ya ziyarci zuciyarta rungume wayar tayi cike da Farin ciki, harta ‘kosa Hud’u na yamma tayi sufita zuwa islamiyya.
.
Da misalin ‘karfe hud’u saura minti goma Hussaina tagama shirinta tsaf na islamiyyah cikin uniform kalar ruwan ‘kasa,
“Kallon yar’uwarta tayi wacce ke ‘ko’karin d’aura farin d’an kwali, tace Hassana kiyi sauri kinga bana bu’katar zuwa a makare, kallo kawai Hassana tabita dashi “Tofah yau kuma kece me cewa bakison makara ince kullum saina gama shiryawa sannan inyi zaman jiranki,
“Naji dan Allah yanzu dai kitaho mutafi kina ‘kara tsyar damu, ……
Dai-dai lokacin kuma wayarta tayi ringing dubawa tayi jiki na kyarma takai dubanta ga Hassana wacce tagama shirinta tsaf tana jiran sutafi.
Sunan Hafiz tagani yana yawo kan wayar, dama kuma kobata dubaba tasan shine dan tsakanin ‘karfe ukku da Rabi zuwa yanzu ‘karfe hud’u yayimata kira yakai tara,
“Hellow yanzu zamu fito daga gidan, tafad’a tana kallon Hassana ta wutsiyar ido,
“To babyna dan Allah kiyi sauri wlh na matsu na ganki dan bakisan yanda nakejibane shiyasa kikai har yanzu baki fitoba.
“Sorry dear ina hanyafa nace ka saurareni mana.
“To shikenan ina gurinda nagayamaki,
To sainazo tafad’a tare da kashe wayar.
Tana juyowa suka had’a ido da Hassana saida gabanta yayi ‘yar ‘karamar fad’uwa saboda kallon tuhumar dataga tana mata.
Nunawa tayi kamar batasan kome kenanba tace “muje ko kada mu makara naga yau baki bu’katar muyi latti,
“Owk muje to.
Haka suka jero gwanin ban sha’awa kome nasu iri d’aya ga tsananin kamanni dasuke farinsu d’aya tsawonsu d’aya haka zubin jikinsu d’aya, suna matu’kar kamanni wanda hakan kesawa mutane da dama basa gane Hassana basa gane Hussaina, hatta da iyayensu basu cika ganesuba saita gurin halinsu daya bam-bamta.
A falo suka tarar da Momy, cikin ladabi suka isa gabanta “Momy mutafi islamiyyah
“To Allah bada sa’a Yakuma tsareku, Allah yayimaku Albarka, Adawo lafiya.
Amsawa sukayi da Ameen sannan suka fice, suna fita sukasamu me napep suka gayamashi sunan islamiyyar daze kaisu,
Sun fara tafiya Hussaina ta Kalli Hassana tace “sister dan Allah kiyimin taimako d’aya sonike inje gidansu zuby kuma kinsan gida baza’abarni infitaba inaso me napep ya saukeni acan sai awuce dake islamiyya idan antaso kimin waya sai muhad’u mutafi gida.
Da Hassana kamar bazata Aminceba saikuma tace “to shikenan Amma dan Allah kada ki wuce lokacin tashinmu islamiyya, kinsan dai daddy ba sauki.
“InshaAllah kinamin waya zanzo, “to shikenan.
Hassana aka fara saukewa islamiyya sannan aka wuce da Hussaina unguwar Barhim dake wajen Gari, dai-dai inda Hafiz yagayamata yananan nan kuwa tasameshi.
Tana fitowa daga napep ta hangoshi tsaye jikin motarshi ya hard’e duka hannayenshi a ‘kirji, sanye yake cikin bakin wando, da yellow riga, sai ba’ka’ken takalmi, sannan ya d’ora wani ba’kin glass Wanda ya’kara fitowa da ainafin kyawunsa.
Yana hangota yafara jefarta da ‘kawataccen murmushinsa, itama maida mashi martani tayi harta isa gurinshi suna musayar murmushi.
“Welcome babyna yafad’a tare da rungumata a jikinshi, saurin tureshi tayi tana waige kada ace mutane suna kallonsu. *{Hmm Hussaina kenan idan mutane basu ganinku ai Allah yana ganinku}*
“kada kidamu babyna ba mutane sosai a unguwar, kodama wani yaganmu ba wanda ze shiga harkarmu, amma tunda naga kamar kina tsoro shigo daga ciki, “dadai yafi, tafad’a
Sannan yabud’emata motar tashiga shima yashiga.
.
Wani d’an sandane ya kalleta Wanda da Alama shine babbansu yace “miye sunanki?
Jiki na kyarma tabashi amsa “Hussaina,
“Ke yar gidan wacece kike yawo da wannan daren?
“Uhm wlh yalla6ai ba yawo nikeyiba, hasalima ni bansan ya’akayi nafito daga gidaba.
“Shut up, yafad’a cikin d’ga murya, ke muzaki rainama wayo, irinki-irinki mungamu yafi a ‘kirga, hadama wad’anda sukafiki iskanci.
“waye zefitodake daga gidanku batare da izininkiba, kada kimanta cikin Halin da aka kamaki na maye koshima bakisan ya’akayi kikayi shaye-shayen ba?
“Wlh yalla6ai bansha komeba na rantsema da Allah,
Tassss saukar wani lafiyayyen mari taji a kumatunta wanda wannan d’an sandan ya d’auketa dashi, marinda saida ya gigitata saboda tsananin azabar tafin hannun d’an sandan ba ‘karamin kato bane.
A ‘kufule yace zaki fad’amana ke ‘yar’waye kokuwa saina sa6amaki.
Cikin tsananin gigicewa take magana “zanfad’a…. Zanfad’a wlh.
“Oya ina saurarenki d’ansandan yafad’a tare da tsareta da manyan idanunsa masu ban tsoro.
“Ni Yar gidan Alhj Mansir company ce.
“What? ‘Dan sandan yafad’a tare da mi’kewa tsaye.
“Karya kike yafad’a tare da nunata da yatsa, duk fad’in garinnan waye besan Alhj Mansir kamfaniba, mutumin kirki me halayya ta kwarai ace ke yarsace kina wannan munanan halaye.
Kuma ba wannan ba iya saninmu Alh Mansir bayada wasu ‘ya’ya sai yara biyu yan tagwaye.
“Yan la6ai wlh nice ai mune yan tagwayen Nice Hussainar dan Allah Ku taimakeni Ku maidani gidanmu.
“Sajen Habu, dan sandan yakwalama wani daga cikin yansandan kira.
Da sauri d’ansandan ya iso gabanshi ya ‘kame tare da saramashi.
“Maza a fiddo mota yanzu zamuje gidan Alh Mansir kamfani “yes sir yafad’a saida ya’kara saramashi kafin yafita zuwa ma’ajiyar motocin.
Dare ya tsala misalin ‘karfe biyu na dare motar yan’sandan tayi parking bakin get din gidansu Hussaina, nocking sukayi lokacin mal bala yana kwance cikin d’an karamin d’akinsa yafito da sandarsa a hannu yana tamabayar “waye? Hussainace tayi magana “nice mal bala, “kece wah? Ya tambaya.
“Nice Hussaina.
“Husssaina da wannan daren subhanallah bud’e ‘kofar yayi ahankali yana le’kowa yayi ido hud’u da ita da ‘yansanda biyu tare da ita.
Da Sauri Hussaina tashiga gidan ‘yansandan suka take mata baya, a harabar gidan suka tsaya “kishiga kiyimana magana da mahaifin naki.
Bata ko sauraresuba tayi cikin gidan da gudu,
Lokacin Daddy,Momy da Hussaina suna Zaune a falo, Momy sai Addu’a take Allah maidomata da ‘ya lafiya a Zuciyarta tana cewa “danasan haka zata kasance daban amince da fitartaba.
Hassana kuwa kuka kawai takeyi, yayinda dady Zuciyarsa tagama ‘konewa jiyake inama yaga Hussaina yanzu Allah kad’ai yasan irin dukan dazeyimata.
Begama wannan tunaninba yaga anturo ‘kofar falon, mikewa yayi da sauri dan ganin me shigo masu gida da wannan tsohon daren, ido Hudu sukayi da Hussaina saurin isa yayi Inda take a zuciye ya dun’kule hannu yakaimata wani mugun naushi sannan yasa ‘kafa ya hard’ota.
Fad’uwa tayi ‘kasa tana maida numfashi sama-sama ko kukanma yakasa zuwamata saboda tsananin azabar datake ciki.
Dukda haka Daddy beyi ‘kasa a gwiwaba gurin ciro cherger wata fitila dake jikin soket yarin’ka tsulamata, sai lokacin tasamu damar fasa ihu tare da d’aukewar numfashinta ta sulale ‘kasa sumammiya.
Ganin tafad’i yasa Momy ‘karasowa gurin tana kuka “innalillahi Alhj miye haka kake shirin kasheta, kabari mana kaji ta bakinta, “Bazanbariba da bata fitaba da hakan be faruba, kuma ko mutuwa tayi bani nadamar kasheta saboda da inyi mugun gani ‘kara narasata baki d’aya.
Hassana kuwa ganin ‘yar’uwarta kwance ba Alamar rai tattare da ita yasata rud’ewa tafito zuwa harabar gidan dagudu tana kuka, ganinta yasa ‘yansanda sukayi saurin tarbarta a tunaninsu Hussainace saida suka kula da kayan jikin wannan basubane jikin wacce suka kawo yanzu “ke lafiya suka shiga tambayarta, a gigice take nunamasu cikin gidan tana cewa “daddy yakasheta, ya kashemin ‘yar’uwa.
“What suka fad’a tare da abkawa cikin gidan baki d’ayansu..
.
A gigice Momy tabi Hassana da kallo tare da ‘yan’sandan dake tare da ita.
“Hassana Kina Haukane, mahaifin naki kika kirama ‘yan sandan.
Cikin muryar kuka Hassana tace “Wlh momy bani nakirasuba ina fita nagansu a harabar gidannan.
Kallonsu daddy yayi a gadarance yace “waya kawoku gidana, kuma da izinin wah kuka shigo har nan? Yafad’a yana nuna inda suke tsai-tsaye.
“Babban cikinsune yayi magana “Sunana inspeter Sabi’u wale, mune wad’anda suka kawo wannan yarinyar gidannan bayan mun tsinceta cikin halin maye, bayan ta dawo hayyacinta mukayimata ‘yan tambayoyi shine tasanar damu kaine mahaifinta shine muka kawota, muna tsaye a haraba munajiran tayimana magana dakai shine mukaga wannna tafito tana fad’in a taimaketa ankashemata ‘yar’uwa shine dalilin dayasa muka shigo domin gudanar da aikinmu kamar yanda doka ta tanada.
“Owj naji duka bayaninku nagode, inaso kutafi kawai ni zan iya solving kowace matsala tagidana batare da wani yasamin hannuba nagode da taimakon dakukayima ‘yata.
“Muma mungode Alhj Amma dan Allah ari’ka kai zuciya nesa, saboda gudun danasani….
Sai a hanzarta a kaita asibiti suka fad’a suna kallon Hussaina dake kwance bako motsi.
Bayan fitar ‘yansandan momy ta kalle daddy Wanda yaketa mazurai da Alama har ‘yanzu zuciyarsa bata gama hucewaba,
Hussaina kuwa har ‘yanzu tana kwance batasan inda kanta yakeba, momyce tamatso inda take ta tallabo kanta ganin ba alamar rai tattare da ita yasata fashewa da kuka, “Dan Allah Ahj mukaita asibiti kada tamutu…..
“Tamutun mana, yafad’a cikin d’aga murya.
Sannan yayi ‘kasa da muryarshi yana cewa “ba inda zan kaita na kwammace inrasata baki d’aya da mugun halin datake Neman jefa kanta.
Tajamani abin fad’i a gari, yana gama fad’in haka yashige d’akinshi ya maido ‘kofa yarufe.
Cikin kuka Momy ta kalli Hassana tace kawomani ruwa.
Da sauri Hassana ta d’ebo ruwa cikin cup takawo, amsa Momy tayi tashiga kwarama Hussaina a jiki amma ko motsi batayiba saida ta zubamata a fuska sannan tayi firgigi ta tashi ta ‘kan’kame Momy tana fad’in dan Allah kibashi ha’kuri wlh bazan ‘karaba.
“Ke Hussaina kitsaya mana, ki nutsu nace ba daddynku bane nice Momy
‘Kara ‘kan’kameta tayi tana fad’in “wayyo Momy wlh bazan ‘karaba kigayamashi na tuba.
“Cikin tsawa Momy tace “dallah ni sakeni tare da tureta daga jikinta, kinsan kina tsoro kikaje yawon har kika kai wannan lokacin baki dawoba, itama tana gama fad’in haka tayi tafiyarta d’akinta tabar Hussaina nan tana kuka itada Hassana.
Hassanace tamatso kusada ita takama Hannunta ta mi’kar da ita tsaye suka nufi d’akinsu.
Koda suka shiga d”akin zaune sukayi jugum-jugum suduka suna sharar kwallah.
Ita Hassana tana kukan halinda ‘yansandan nan suka fad’i sunkama Hussaina na maye.
Itakuma Hussaina tana kukan yaudara da Hafiz yayimata har yayi nasarar rabata da budurcinta.
Wasu sabbin hawaye suka zubo a kuncinta.
Hassana ta kalleta tare dasa hannunta ta sharemata hawaye
“Dan Allah ‘yar’uwata naro’keki ki gayamin gaskiyar inda kikaje har kikakai wannan lokacin baki dawo gidaba, kuma da gaskene abinda ‘yansandan nan suka fad’i na kamaki dasukayi cikin halin maye?
Tana gama fad’in haka ta tsareta da idanu tana jiran jin amsar dazatabata “Hmm ko d’aya Hassana wlh bansha komeba, kuma ni ba inda naje nasan dai naje asibiti kamar yanda na tambayi momy zanje kuma ta amincemin, ana gaf da magariba nabaro asibitin ina tsaye inajiran abin hawa wani me mota yatsaya gabana yaro’keni da inshiga yaragemin hanya nikuma ganin ina sauri yasa na Amince nashiga motar to shinefa daganan ban ‘kara sanin abinda yafaruba saida na tsinci kaina yashe a titi, wannan shine gaskiyar abinda yafaru.
Hassana najin haka ta ‘kara fashewa da kuka tare da rungume ‘yar’uwarta tana fad’in “sister Allah yasa da rabon sauran shan ruwanki a duniya, ya Allah na godema daka kwatomin ‘yar’uwata daga hannun muyagun mutane.
Hussaina kuwa dad’i taji har cikin ranta dan ganin Hassana ta yarda da ‘karyar data tsaramata, a zuciyartama cewa tayi aiko gobe idan daddy da Momy sun tuhumeni abinda zan fad’amasu kenan, da haka suka kwanta bacci yayi awon gaba dasu kowace da tunani barkatai a zuciyarta.
*Washe Gari.*
Koda suka tashi bayan sunyi duk abinda yadace na gyaran gida, komawa sukayi d’aki sukayi wanka wasu dogayen riguna suka sanya masu kyan gaske tare da ‘yan ‘kananan hijab.
Lokacin Momy tagama had’a break fast zuna zaune kan dining tana zubama daddy kasancewar tara hartayi yana sauri yafita office saboda yanada ayyuka da dama a can.
Jerawa sukayi gwanin ban sha’awa suka nufi inda iyayen nasu suke sannan suka zazzuna bayan sun gaishe da iyayen nasu.
Hussaina sai sunne kai takeyi alamar rashin gaskiya.
Bayan sunkammala breakfast ne daddy ya kalli Hussaina tare da d’dd’aure fuska kamar beta6a dariyaba yace “inaso kigayamin gidan ubanwa kikaje jiya.
“Uh…im asibiti naje ganin mamar ‘kawata.
“Da izinin wah kika fita?
Kallon Momy tayi suna had’a ido Momy ta watsamata wata muguwar harara, ba shiri ta saddar da kanta ‘kasa, tayi shiru.
Dadyne yacigaba da magana “koma waye ya d’aure maki gindi a gidannan kike Neman lalacewa tonidai ba agabana ba, kuma yau basai gobeba zan d’auki mataki kanki dan bazan zauna ina kallonki kijamin surutu a gariba, yana gama fad’in haka ya d’auki jakarsa yafice daga gidan ranshi a matu’kar 6ace.
.
Daddy ne Zaune office d’insa yahad’a hannu bibbiyu ya buga tagumi ba abinda yake tunani sai irin rayuwar da Hussaina take neman jefa kanta,
Mi’kewa yayi tsaye ya maida hannuwansa duka biyu baya tare da fara zagaya office d’in yafara zancen zuci “yanzu wane mataki yakamata in d’auka dan ganin nayima tufakar hanci bata war-wareba, yau kimanin shekara ishirin ina tarbiyantar da yarannan amma lokaci d’aya suna nema su bijiremin, komawa yayi kan kujera ya zauna tare da maida kanshi sama ba abinda yake tunani sai abinda ‘yan sandan dasuka kawo Hussaina gida suka fad’i na cewa sun kamata cikin Halin maye, wato rayuwar dazata jefa kanta kenan, wadda daga haka mutum ze iya aikata kome hatta da kisan kai mashayi na iya aikatawa batare da shakka ko shayin irin hukuncin daze biyo bayaba.
“Assalamu Alikum, da sallama jabeer yashigo office d’in hannunsa d’auke da wasu files-files, jin shiru ba’a amsa sallamar ba yasa ya’kara yin wani sallamar karo na biyu, nanma shiru daddy be amsaba dan yayi nisa cikin tunanin dayake, guri jabeer yasamu ya zauna tare da ajiye files-files d’in kan tebur d’indake gabanshi da d’an ‘karfi yanda daddy zeji karar ajiyewar. Hakan kuwa ya maidoshi daga dogon tunanin dayake ya d’ago da kanshi ya kalli jabeer “Ah jabeer badai har kagamaba, “eh nagama gashinan saura wad’annan files d’inne sunada ‘yar matsala akwai takardun da babu aciki, yafad’a yana ware wasu files guda biyu gefe.
“Owk to ba Matsala idan na duba zanyima magana sai a gyara, “to kawai yafad’a tare da mi’kewa ze fita daga office d’in harya kai bakin ‘kofa daddy yayi kiransa “jabeer, cikin girmamawa jabeer ya amsa tare da dawowa ya zauna,
Saida daddy yayi shiru na kimanin minti biyu kafin ya sauke ajiyar zuciya “Jabeer dama inason magana dakai “to Alhj Allah sa dai lafiya,
“Eh to lafiya lao, kan maganar Aurenka da Hussaina kanasonta kuwa har yanzu?
Cike da jin kunyar tambayar da daddy yayimasa ya amsa da “eh.
.
“To bakada matsala inaso da anjima bayan sallar azahar kataho da magabatanka da shedu koda basu wuce mutum gomaba, nima zan sananar da ‘yan’uwana za’a d’aura aurenku kaida ita, bani bukatar kome naka sadaki kawai zaka taho dashi naira dubu hamsin,
Kada kayi mamaki kan wannan abin dana aiwatar akwai dalilin yin hakan Wanda nasan koda kaji dalilin na tabbata bazaka’ki jininaba,
Jabeer dai shiru yayi yana sauraron Alhj cike da mamaki a zuciyarshi yana cewa “wannan shine ikon Allah me tsaida wando koba zariya, kome wannnagaggawar take nufi Allahu wa’alamu.
Haka ya kauda kowane tunani cikin zuciayrshi yayima daddy godiya sannan yakoma office d’inshi.
Koda ya koma tunanin dai yahanashi sukuni saboda haka rufe nashi office d’in yayi Yakama hanyar gida.
*Waye Jabeer*
.
Jabeer Suleman shine asalin sunanshi Haifaffen garin katsina, Alh sule tankuri shine mahaifinsa sai mahaifiyarsa Hajiya sa’ada sunada rufin asiri Bakin gwargwado amma ba’a kiransu masu arziki, su biyu iyayensu suka haifa dagashi sai ‘kanwarsa Nusaiba wacce akwai tazara sosai tsakaninsu dan ahalin yanzu nusaiba bata wuce shekara sha shidda zuwa sha bakwaiba yayinda jabeer yakeda talatin da d’aya.
Tun yana d’an shekara sha bakwai mahaifinsu yarasu lokacin mahaifiyarsu na d’auke da ‘karamin cikin nusaiba bayan rasuwar mahaifinsu da wata bakwai ta haifi nusaiba, haka sukacigaba da rayuwa yau da dad’i gobe babu, yayinda mahaifiyarsu ta tsaya tsayin daka dan ganin jabeer yayi karatu, da kyar da sud’in goshi sukasamu ya kammala karatunshi a F.C.Ekatsina kasancewarshi hazi’ki yasa yasamu sakamako me kyau amma dukda haka samun aiki yayi wahala kusan shekara biyu yana neman aiki besamuba, kwatsam rannan yaji ana Neman ma’aikata a Company Alhj mansir badan yasa ran zesamuba yaje yayi interview cikin ikon Allah kuwa saiga sunanshi cikin wad’anda aka d’auka aiki, sunyi matu’kar farinciki shida mahaifiyarshi da ‘kanwarshi, ranar dazefara zuwa aiki mahaifiyarshi tayimashi nasiha me ratsa jiki akan ri’kon amana da gaskiya, sannan tabishi da addu’ar samun s’a.
Bayan wata shidda dafara aikinsa Alhj mansir yalura da Halin gaskiya da ri’kon amana na jabeer hakan yasa yajawoshi jiki tare da ‘karamashi matsayi a office d’in Wanda a halin yanzu shine mataimakin manager company.
*Masu yimin magana ta prvt najina dasukayi shiru kwana biyu Dan Allah kuyi hakuri na rashin ganin reply d’ina naga sa’konku saidai be karantuwa kasancewar nasake download whatapp ne nagode da kulawarku.*
.
Saboda haka cike da tunani barkatai jabeer ya isa gidansu, ‘kanwarsa Nusaiba yafara gani zaune falo tana kallon wani Indian film me suna salam namaste, da sauri ta tarbeshi tanamashi sannu da zuwa, bayan ya amsa d’akinsa yanufa ya ajiye jakarsa sannan ya dawo falon, har yanzu dai nusaibar ce ita kadai a falo tambayarta yayi “ina mama?
“Tana bedroom,
“Owk kawai yafad’a tare da nufar ‘kofar dazata sadashi da d’akin kwanan mahaifiyar tashi, da sallama yashiga d’akin zaune ya isketa gefen gado hannunta ri’ke da waya da Alama waya tagama, kallonshi tayi bayan yasamu guri ya zauna kan bedsite “a’a jabeer yanaganka kadawo tun yanzu ko mantuwa kayine?
“A’a mama ba mantuwa nayiba wani babban Al’amari ya maidoni Wanda ni kaina ya d’auremin kai,
“Wannan wane Al’amarine tafad’a tare da maida duka hankalinta gareshi,
“Watako yanzu danaje office shine Alhj yakirani yake cemin inje insanarda magabatana kuma inbada kud’in sadaki naira dubu hamsin yau ze d’aura aurenmu da Hussaina.
“Alhamdulillahi mama tafad’a tare da d’aga hannuwanta sama tana godema Allah, kai Amma naji dad’i wannan abu ai abun farincikine dama kullum Addu’ata be wuce inga aurenkaba, Allah sanya Alkhairi yabaku zaman lafiya.
“To amma mama kina ganin babu wata matsala, “wace matsala haba jabeer me kanema karasa inaji kadade da kammala gidanka, kuma Hallacin da Alhj mansir kamfani yayimana ai kobakada kome yace ka auri d’iyarsa ka aureta kazubama sarautar Allah ido dan nasan baze barka hakaba,
“To mama Allah dai yasa haka shine mafi alkahiri,
“Ameen haka nikeso naji kana fad’i.
Daga nan yafita zuwa d’akinshi ya canja kaya sannan yakoma yayima mamarsa sallama tare da sanar da ita zeje ya d’auko mutum ukku dangin babanshi sannan mutum ukku a dangingin ita mamar tashi, fatan Alkhairi tayimashi sannan yafita.
⏱. *Misalin ‘karfe 3:00pm*
Aka taru a masaalacin dake ‘kofar gidan Alhj mansir mutane ‘kalilan suka sheda d’aurin auren Jabeer Suleiman tankuri da Amaryarsa Hussaina Mansir kamfani, bisa sadaki dubu hamsin.
Bayan ankammala Alhj mansir yasa aka gabatarma duk mutanen dasuka halarci d’aurin auren abun lasawa take away akayima akaiyma kowane suka wuce suna sanya Albarka.
Bayan ankammala wannan daddy yashiga gida da sallama, su duka falo ya taraddasu zaune Momy ce ta amsa sallamar, Hassana tace “daddy sanu da dawowa “yauwa ya amsa,
Hussaina kuwa daddy nashigowa jikinta yafara kyarma dan wani masifaffen tsoronshi takeyi, cikin muryar tsoro tace “d…dad…daddy sannu da zuwa.
Wani matsiaycin kallo ya watsamata sannan yawuce d’akinsa batare daya amsa sannu d’inda tayimashiba.
Can bayan kimanin minti baiyar yafito ya kalli Hussaina “ki shirya yanzu inaso zan fita dake kuma minti talatin nabaki, kinajina “inaji daddy tafad’a tare da mi’kewa tanufi d’akinsu jiki na kyarma.
Daddy kuwa fita yayi harabar gidan, waya yakira jabeer “ya masu aikinnan sun kammala kuwa,? Ya tambaya
cikin ladabi jabeer yake magana “Eh Alh sunyi kusan minti sha biyar ma da gamawa.
“Sun had’a kome dai yanda yakamata ko?
“Eh sun had’a kome 2 bedroom ne da falo 2 sai kitchen ba abinda ba’a zubaba na bu’kata.
“Owk to anjima ka shiryar tarbar Amaryarka,
Kasa magana jabeer yayi saboda kunyar Alhj yakeji sosai.
“Basu dad’e da kammala wayaba wata had’addiyar mota tayi parking ‘kofar gidan sannan wasu maza suka ri’ka jido akwatina suna shigowa dasu saida suka shiga da guda goma manya- manya, sannan sukayima jabeer bayani Alhj mansir yace akawo kayan amaryane.
Mamakine yahana jabeer magana danshi harga Allah yayi niyyar had’a wannan kayan Amma Alhj yahashi had’a kome.
.
Da misalin ‘karfe biyar na yamma Hussaina tafito cikin shiri sanye take da riga da zani d’inkin simple atamfar brown colour haka takalmin ‘kafarta yayi kala da kayan jikinta sai ‘katuwar hijab data sanya, ahankali take takowa hartazo gaban dadynsu cikin ladabi tace “na shirya daddy
“Owk muje ko, yafad’a yana nunamata ‘Kofa.
Ganin tana tafiya Ahankali kamar kazar da Kwai yafashemawa a ciki yasa daddy yayi gaba ya zauna a mota yana jiran fitowarta.
Fanin fitarsa yaba Hussaina damar yin magana “Momy wai ina zamu?
Momy tace “kin tambayi kaza hanyar rafi…..
Ni kaina da kike gani bansan meke wakanaba nidai kawai abinda nasani naga tunda Alhj yatashi yau yaketa hidima ko zama yaci abinci beyiba.
Hassana dake zaune tace Allah dai yasa Alkhairi ne, ni kaina ina mamakin yanda daddy yace Hussaina ta shirya su fita batare daniba, Alhalin nasan ko’ina tare muke zuwa.
Momy tace “to wannan abu dai Allah kad’ai yasani, kiyi sauri kibishi kada kuma yaga kin 6atamai lokaci.
Juyawa tayi tafita daga falon batare data ‘karayin wata maganaba.
A mota ta iske daddy zaune yana jiran fitowarta, gidan gaba tanufa da niyyar tashiga harta kama murfin motar zata bud’e daddy ya watsamata wani matsiyacin kallo “koma baya.
Jiki na ‘kyarma takoma ta bud’e bayan motar tashige, sannan daddy yatayar da motar Malam bala yabud’emasu get yana d’aga masu hannu suka d’au hanya sannan yamaida get d’in yarufe Yakoma kan d’an bencinsa ya zauna yana cewa “gaskiya Alhj ya iya maganin d’an iska, wato yarinyar nan wlh da Alhj beyi saurin Aurar da itaba saita d’aukomar abin kunya. Kodayake bansaniba shin itace koba itabace oho nikam bani ganesu, radio shi yajawo ya kunna yacigaba da sauraron abinshi.
Daddy kuwa ba inda ya zarce da Hussaina sai unguwar dutsin safe malali Quarter’s inda nan tangamemen gidan jabeer yake, bakin get yayi horn da sauri megadi ya bud’e mashi ciki yashiga ya ajiye motarshi inda aka tanada dan ajiye motocin, fitowa yayi sannan ya umarci Hussaina data fito itama, ba musu tafito tunda suka shigo take yaba kyan gidan, saikuma yanzu ta’kara ganinshi sosai tsarin gidan ya burgeta, a zuciyarta tace “nan kuma ko gidan waye? Amma ko gidan abokanin daddy ne bamu ta6a zuwaba, kuma sabodame daddy yaza6i yazo dani ni kad’ai banda Hassana Alhalin duk inda zamu tare muke tafiya da ita……
Daddyne ya tsinkemata tunanin datake ta hanyar cewa “shigo mana.
Ba musu tabi bayanshi wata ‘Kofa yabud’e wacce tasadasu da babban falon gidan me d’auke da maka-makan kujeru irinna zamani a tsakiyar falon gefe kuma kan wani step kujerun dining ne da ‘katon table d’insu, daga gaba kuma inda suke facing wata ‘katuwar TV ce plasma ma’kale jikin bangon sai manyan speaker’s (Home theaters) gefensu kuma wasu kyawawan flower’s ne masu d’aukar ido, duka kayan falon sun kasance purple colour hatta da pentin d’akin kalarsa kenan,
Daddy yace “to Hussaina wannan gidan da kike gani bana kowa bane face gidan mijinki……
Dammmm gabanta yayi wani mummunan fad’uwa da sauri tad’ago ta kalli daddy ganin ba wasa tattare dashi yasa tamaida kanta ‘kasa gabanta nacigaba da fad’uwa.
Daddy yacigaba da magana “naza6i na aurar dake dakijawomin abin kunya, saboda nan shine gidan aurenki, ki zauna kibi mijinki kiyi mashi biyayya Aljannarki tana ‘kar-kashin tafin ‘kafarsa idan kinbishi kisamu idan kuma kin baud’e wannan kuma Allah yasan hukuncin daya tanadar maki.
Saboda haka iname umartarki daki zama me biyayya a gareni ni mahaifinki dakuma mijinki ki zauna lafiya.
Nan daddy yayimata nasiha me ratsa jiki kafin yayimata bankwana ya ajiyemata bandir d’in kud’i yan dubu yace “saboda idan kina bu’katar wani abu bance ki matsama mijinkiba,
Bayan tafiyar daddy kasa tashi tayi daga inda yabarta, tunani take “wannan wane irin aurene daddy yayimin kamar auren wasa, to wai yaushema aka d’aura auren? Kuma waye mijin? Ina daddy yasamu mijin daya yarda da aure cikin kwana d’aya tak? Haka tagama jerama kanta tambayoyi amma batada amsarsu kuma batada Wanda ze amsa mata, hakan yasa tafashe da wani irin kuka, tana cewa “shikenan yanzu nasan daddy baya ‘kaunata menayi….menayi daza’a yankemin wannan hukuncin.
.
Kuka take iya ‘karfinta babu me rarrashinta sai da tayi me isarta sannan ta tashi falo na biyu tashiga wanda shima yaji set d’in kujeru da kayan kallo amma sai dai shi bekai na farkon haduwaba shikuma kome nacikinsa green colour ne, tsayawa tayi ta’karemashi kallo sannan tanufi wani d’akin nan kuma bedroom ne wanda aka zubama kaya yan Dubai ba ‘karamin kyau d’akin yayiba, fitowa tayi daga nan tanufi gudan d’akin ahanakali tatura ‘kofar tashiga nan ma karo tayi da wani ‘kawataccen d’akin kwana shikuma duka kayan yan Nigeria ne aka zuba amma harma sunso Sufi na Dubai d’in kyau.
Bayan tabi ko’ina na gidan ta’karemar kallo dawowa tayi a bedroom ta zauna tsakiyar gadon tare da rufe fuskarta da hijab d’inta, take tunanin Hafiz ya dirar mata a zuciya, wani irin kuka tafashe dashi a zuciyarta tana cewa “yanzu shikenan anrabani da Hafiz mutumin danafi so nafi ‘kauna akan kowane namiji, bazan iya zaman aure da kowane namiji ba bayan Hafiz yazanyi da rayuwata, haka tacigaba da kuka tana zancen zuci.
“Yanzu ni waye wanda daddy yaza6amin anya zan iya zama dashi, ita ko kad’an bata kawoma ranta jabeer ne wanda aka d’aura mata auren dashiba.
Zaune take tabuga uban tagumi hannu bibbiyu ba abinda ke mata yawo a kwalwa sai kalar salon soyayyar da Hafiz ke nunamata, yanzu shikenan anrabamu baze ‘kara shayar dani zumar ‘kaunarsaba.
Mi’kewa tayi tsaye kamar wacce aka tsikara “baze yiyuba tafad’a a zahiri bazan iya rabuwa bada Hafiz ba ko ana ha maza ha mata, Hafiz shi kad’aine namijin dazan aura in kasance cikin farin ciki, ko waye wannan yayi gan-ganci daya yarda da aurena, tabbass zesan abinda ya auro ya kawo gidanshi.
********
Momy da Hassana kuwa tun bayan fitar daddy da Hussaina suketa sa’ke-sa’ke da kwancewa sun rasa ina daddy zashi da Hussaina batare da yar’uwartaba Alhalin shine yasaba masu da duk inda zasu tare suke tafiya.
Da sallama ya shigo falon suduka binshi sukayi da ido ganin yadawo batare da Hussaina ba,
Momy ce tayi ‘karfin halin tambayarsa “Alhj ina Hussaina take naga ka dawo kai d’aya kuma bayan tare kuka fita.
“Tana gidan mijinta, yabata amsa a takaice sannan yawuce d’akinsa, binshi tayi daga baya zuciyarta cike da mamaki.
Hassana dake zaune tanajin abinda daddy yafad’a itama tashi tayi tanufi d’akinsu tana cewa “innalillahi wa’innalaihirraji’un “Gidan miji…. tafad’a cike da mamaki, yaushe aka d’aura auren sister bamu saniba dan gashi alamu sun nuna itama momy batasan da zancen ba,
“Ya salam tafad’a tare da dafe kanta da hannu biyu dataji yana saramata kamar ze rabe biyu, fad’awa tayi kan gado tana zubar da hawaye.
: Cike da 6acin rai momy take magana “haba Alhj ban fahimce inda zancenka yadosaba.
Juyowa daddy yayi ya kalleta tare da yin wani murmushi, sannan yace “baki bu’katar in maimaita maki abunda nafad’a d’azu saboda inada tabbacin kinji kome nafad’a.
“Lalai Alhj yanzu ka tabbatar min da baka ‘kaunar Hussaina akan me zakayimata irin wannan hukuncin, aure cikin kwana biyu kamar auren d’iyar kara, haba Alhj kuma amatsayina na mahaifiyarta yaci ace nasan da maganar amma bansaniba kuma banida labari kawai saika tafi da yarinya kace wai wani ka kaita gidan miji, gaskiya ni ban yardaba kawai kafad’amin inda d’iyata take inje in d’aukota idan kai baka sonta ni ina sonta, duk wannan maganganun da momy keyi tanayinsune cikin 6acin rai da d’aga murya.
“Dakata Maryam, daddy yafad’a cikin d’ga murya “wannan auren na d’aurashi kuma yariga ya d’auru ba wanda ya isa ya war-wareshi, ince idan yarinyar nan ta jawo mana abin kunya zagin daza’ayimin baza’ayimaki rabinshiba, saboda haka nariga na yanke hukunci idan kinji hukuncin danayimaki bemakiba zaki iya kama gabanki hanya a bud’e take yara kuma nawane inada iko akansu.
Tunda daddy yafara fad’a momy ke kallonsa cike da mamaki a zuciyarta tace “lallai Alhj da gaske yake kuma ba wasa tattare dashi dole nima inbi ahankali.
Cikin langa6ar da kai momy tamatso kusa da daddy ta dur’kusa gabansa “Haba Alhj meyakai na 6acin rai haka, indai kan wannan maganar ne inshaAllah kome ya wuce Allah sa haka shine mafi Alkhairi a rayuwar Hussaina, itakuma yar’uwarta Allah kawomata miji na gari.
“Ameen daddy ya amsa tare da shigewa toilet ya watsa ruwa sannan ya d’auro Al’walar magrib dan lokacin sallar yayi.
Itama Momy d’akinta tanufa ta d’aura Al’wala ta kabbara sallah bayan tagama ta dad’e kan abin sallar tana kwararo addu’a ga yaranta.
.
Zaune take cikin d’akin tarasa mekemata dad’i a duniya, wayarta ta Dauko sunan zuby ta lalubo sannan ta danna kira, bugu d’aya zuby ta d’auka.
“Hellow ‘kawata kin 6oye kwana biyu.
“Hmm kedai bari kawai zuby idan ana sallah ba’a magana.
“Banganeba ‘kawata wani abune yafaru dake?
“Abubuwa da dama sun faru dan ahalin yanzu wayar nan damuke dake ina gidana.
Saurin tashi zaune zuby tayi daga kwancen datake “bangane gidankiba ‘kawata, gidanki ko gidanku?
“Hmm gidana dai dan daddy yamin aure kuma yau natare.
“Aure kuma Hussaina, to waye angon zuby ta tambaya gabanta na dukan ukku-ukku kada Hussaina tacemata Hafiz ta aura, idan ko haka ta kasance da ba abinda ze hana abkuwar ‘karamin ya’ki tsakaninta da Hussainar.
Hussainar ce tadawo da ita daga duniyar tunanin data lula,
“Wlh nima har yanzu bansan ko waye mijin ba, amma inaso kizo gobe,
“To shikenan ‘kawata zanzo amma wane unguwane?
Nan Hussaina tabata full address sannan sukayi sallama kowanensu ya tsinke wayar.
Zuby kuwa tashiga tsananin rud’ani, tashi tayi tsaye tafara kai komo cikin d’akin “tabbass idan har tunanina ya tabbata Hussaina Hafiz ta aura tofa sainayi yanda nayi narabasu koda kuwa ta Hanyar salwantar da rayuwartane, inason Hafiz ina ‘kaunarsa bazan juri ganinshi tare da wata maceba bayan ni, wasu zafafan hawaye suka zubo daga idonta tasa hannu ta goge,sannan tanufi lokar dake jikin gadon d’akin tasa hannu ta fiddo kwalbar kodin ta tuttule a bakinta ta shanye sannan tafad’a gado tana mayarda numfashi kafin bacci yayi awon gaba da ita.
: Hussaina kuwa cigaba tayi da bin d’akin da kallo kad’an-kad’an takai dubanta ga ‘Kofa tana jiran ganin shigowar angon nata.
Ringing d’in wayarta tajiyo da sauri tasa Hannu ta d’auka dan tana tunanin zuby ce takirata kozata gayamata wani abu amma sai ganin sunan Hafiz tayi 6aro-6aro yana yawo kan screen d’in Wayar, sai da gabanta yayi mummunan fad’uwa bin wayar tayi da kallo har kiran ya tsinke sake kira akayi karo na biyu nanma batayi gigin d’aukaba dan ganin kiransa kayar mata da gaba yakeyi, duk dahaka beha’kuraba ya’kara kira karo na ukku hannunta na rawa ta daure ta danna OK tare da karawa a kunnenta batayi maganaba sai shi yafara magana.
“Hellow babyna kina lafiya?
Shiru tayi duk illahirin jikinta kyarma yake dan jin muryar Hafiz kad’ai jefata yake cikin wani yanayi me wuyar fassarawa.
Magana ya’karayi karo na biyu “hello babyna ko bakyajinane.
Sannan ta daure murya can ‘kasa-‘kasa tace “ina jinka.
“Amma kuma kikamin shiru, kinsan kuwa yanda nadamu dake, kinsan halin dana fad’a na rashinki danayi kwana biyu……
Cikin d’aga murya da masifa Hussaina tafara magana “dakata Hafiz bakada wani dad’in baki dazakayimin bayan ka cuceni ka cuci rayuwata karabani da abinda duk wata mace take ta’kama da tin’kaho dashi a duniya.
Amma bakome ba laifinka bane laifinane dana d’auki yardata nami’ka maka d’ari bisa d’ari, gashi yanzu ina gidan mijina banida wata daraja da ‘kimar daze kalleni da ita.
Dakata Hussaina nifa bangane inda maganganunki suka dosaba,
“Tunda ka yaudareni ka kaini gidanka da sunan zan gaisheda hajiyarka ashe da wata manufar ka kaini danka ketamin haddi…….
Jitayi ana doka sallama daga falo hakan yasa tayi saurin kashe wayar baki d’aya ta turata ‘kar’kashin filo, sannan tayi saurin janyo hijab d’inta tarufe fuskarta dashi.
Jitayi annufo d’akin datake hakan yasa fad’uwar gabanta ya yawaita,
“Assalamu Alaikum warahamatullah, yafad’a tare da ‘karasowa cikin d’akin ya zauna bakin gado.
Koda jin muryar kunnenta ya tabbatar mata da tasan me wannan muryar jin ‘kamshin turarensa yadaki hancinta ya’kara tabbatarmata datasan kowaye,
Saurin bud’e lullu6in datayima fuskarta tayi dan tabbatarma idanunta abinda take tunani.
Tana bud’ewa kuwa sukayi ido hud’u da jabeer, a firgice ta nunashi da hannunta tana fad’in “Jabeer dama Kaine mutumin dayaimin yankan ‘kauna, karabani da Wanda nakeso, kasa daddy yayimin aure irinnan d’iyar wasan yara aure cikin kwana biyu, bayan nadad’e da sanar maka inada wanda nakeso bakaiba, to ina me tabbatarma saikayi danasanin aurena dakayi, idan kayine dan farincikin rayuwarka nikuma ka ba’kantamin rayuwa to wallahi kaima ze zama ba’kin ciki a gareka.
“Haba hussaina banyi haka dan in ba’kantamikiba, kuma da banisonki bazan aurekiba inaso ki d’auki wannan a matsayin ‘kaddarace agaremu kuma muyi fatan Allah sa tazamar mana Alkhairi a rayuwarmu.
Wani irin kuka tafashe dashi dan tunawa datayi batadafa wata daraja da ‘kimar da sauran mata keda ita barantana tayima jabeer wula’kancin dataga dama abinda yafi kawai tabada kai bori ya hau, sannan tayi biyayya ta zauna lafiya ko Allah zesa yarufamata asiri, goge hawayenta tayi tace “to Allah shigemana gaba kuma Allah tabbatar mana da Alkhairi cikin wannan zama namu.
Jabeer ya Amsa da Ameen har cikin ranshi yaji dad’i da kuma mamakin saukowar Hussaina haka
.
Daga nan ya umarceta dasu gabatar da sallah su godema Allah kamar yanda addini ya tanada, ba musu tanufi toilet ta d’auro Alwala sannan shima ya Shiga ya d’auro tasa Alwalar suka gabatar da sallar nafila, bayan sun kammala ya dad’e yana kwararo masu addu’oi kafin su shafa.
Sannan ya d’auko ledar daya shigo da ita ya ajiye tsakiyar carpet d’in dake malale a bedroom d’in, da kanshi yanufi kitchen ya d’auko masu palate da cup, gasashiyar kazace guda ukku yabaje kan tire tare da fresh milk da lemun 5alive.
Juyowa yayi ya kalli Hussaina wacce take takure duk tabi ta raina gaskiyarta binshi kawai take da kallo, a zuciyarta kuwa tunanin abinda ze biyo baya takeyi bayan Jabeer ya kusanceta yajita ba cikakkiyar budurwaba, wasu guntayen hawaye suka zubo a idonta tayi saurin sa bayan hannunta ta goge batare da jebeer d’in ya luraba.
Jabeer d’inne ya maidota daga dogon tunanin datake ta hanyar matsowa kusa da ita “bismillah gimbiya saurautar mata nasan dai kinajin yunwa yakamata ace kinci wani abu kafin ki kwanta.
Kad’a kai tayi kamar ‘kadangaruwa “a’a ni banajin yunwa.
“Ban yardaba gaskiya da ganin wannan cikin ya dad’e rabonsa da abinci, yafad’a tare dakai hannunsa kan cikinta.
Ture hannun nashi tayi “nifa banajin yunwa,
“To naji bakijin yunwa amma ban yarda ki ‘ki cin komeba, kawai dai inajin sarautar takice ta motsa, uwar gida sarautar mata, yafad’a cikin tsokana.
Hannu yasa ya yago naman yanufi bakinta dashi da niyyar yabata tayi saurin kauda kanta,
“Haba Hussaina bekamata ace kin’ki kar6ar komeba idan kikayi haka nikam bazanji dad’iba, dan Allah badanniba ki taimakamin ki kar6a.
A hankali ta juyo yafara bata abaki saida ya tabbatar data ‘koshi sannan yazubo fresh milk nanma da kyar ta shanye cup d’aya.
Shima sama-sama yaci naman kajin sannan yakora da lemu, d’akinsa yanufa yacire kayan jikinsa yafad’a toilet yashe’ka wanka.
Hussaina kuwa tana ganin fitarshi tanufi wadrope tana bud’ewa taganta ma’kare da kaya, batayi mamakiba dan daddy yafad’amata babu abinda ba’a tanadar mata a gidan ba.
Wata fitinanniyar rigar bacci ta d’auko wacce zamu iya kira akwai ya babu, ta sanya sannan tabi duk illahirin jikinta ta feshi da sassayan turare, sannan tabi lafiyar gado tayi kwanciyarta batare data rage Hasken d’akinba kuma tayi hakane dan tanajin tsoro ganitake kamar idan ta kwanta a duhu-duhu wani abu ze sameta tasaba kullum tanajin motsin Hassana kusa da ita, yau gashi zatayi kwanan kad’aici dan taga Alamar Jabeer banan ze kwanaba tunda gashi yatafi gudan d’akin yabarta, da wannan tunanin bacci 6arowa yayi awon gaba da ita.
Sanye yake da best da short niker, farare ‘kal jikinshi sai tashin ‘kamshin turarensa yake me suna *story of love* yanufi d’akin.
Ganin d’akin da haske ya tabbatar mai da Hussaina batayi bacciba, da sallama yashiga jin bata amsaba yasashi dubawa kobata d’akinne, can ya hangota kwance kan lafiyayyen gadonta tanata sharar bacci hankalinta kwance, karsa shiga yayi cikin d’akin sannan ya maida ‘kofar yarufe, kafin ya isa gareta ya’karemata kallo, yanda rigar baccin jikinta take sharara ba abinda be bayyanaba na surar jikinta, take yaji wata matsananciyar sha’awarta ta kamashi rage Hasken d’akin yayi tare da kunna masu fitila me sau’kin haske, ya haye gadon ya rungumota gaba d’aya jikinsa.