AUREN TAGWAYE CHAPTER B KARSHE
Cike da farinciki suduka suka fad’a kan kujera, Hussaina ta kalli Hassana wlh sister na d’auka bazakizoba harna fara cire rai,
“Injiwaye inanan tafe ai,
“amma naji dad’in zuwanki wlh, dariya Hassana tayi “lallai sister aurennan ya kar6eki kinga kuwa yanda kikayi kyau kikayi wani fresh, kamar kinje wata ‘kasar Honey moon, dariya Hussaina tayi tare da kaimata duka cikin wasa “kai sister bakida dama, nidai yanzu bari nafara kawomaki lemu kisha idan kuma kina bu’katar abinci ga kitchen nan zaki iya shiga ki girka dan kema gidankine, bata jira jin abinda zata fad’ba tanufi kitchen tabud’e fridge domin d’aukoma sister dinta lemun.
Bayan shigarta kitchen kuma idon Hassana ya sauka kan jakar dake gefen Hussaina ajiye, hannu tasa ta d’auko jakar tare da zuge zip d’in ganin kayan sawa cikin jakar dakuma yan abubuwan bukata yabata mamaki, bata kai ga rufe jakar ba Hussaina ta dawo d’akin d’auke da lemu da cup d’in glass a hannunta ta ajiye gaban Hassana.
Kallonta Hassana tayi sannan ta tambayeta “sister wannan kayanfa na waye? Matsowa Hussaina tayi ta kar6i jakar ta rufe ta ajiye gefe sannan ta zubo lemun a cup ta mi’kamata “kar6i sister kisha zanyimaki bayanin kona miye….
Ba musu Hassana ta kar6i lemun ta shanye sannan ta kalli Hussaina “uhum ina jinki.
Cikin muryar Neman Alfarma Hussaina tafara magana “dan Allah sis wani taimako nakeso kiyimin wanda duk duniya nasan ba wanda zeyiminshi sai ke.
Cike da mamaki Hassana ke kallonta “ina sauraronki sister wane taimakone wannan?
Matsowa Hussaina ta’karayi kusa da ita “ba wani abu bane me wuya inaso ki zauna a gidannan a matsayina…..
“What? Hassana tafad’a tare da mi’kewa tsaye “me kike cewa sister ban fahimci inda zancenki ya dosaba, kama hannunta Hussaina tayi tare da maidata kan kujera ta zaunar da ita “plz sister ki saurareni mana nasan zaki fahimci inda zancena ya dosa.
“Ina jinki Hassana tafad’a tare da bin yar’uwar tata da kallo.
Hussaina tacigaba da magana “kamar yanda nafad’a inaso ki zauna a gidannan a matsayin nice, ba dad’ewa zakiyiba kwana biyu kawai zakiyi, kuma ni zaki taimaka.
“Kamar ya in taimakeki wannan abinda baze ta6a yiyuwa bane yaushe za’ace wani yayima wani zaman aure, aurefa ba abin wasa bane.
“Hmm sister dan Allah ki taimakamin inshaAllah ba abinda ze faru kuma ba Wanda ze gane, sanin kankine babu Wanda ke bam-banceni dake, ko Momy da daddy suna ban-bancemune ta gurin halayyarmu amma bata kamaninmuba.
“Dakata sister duk ba wannan ba, shin idan na zauna gidannan amatsayinki kekuma ina zaki?
“Yauwa sister tambayar dayakamata kiyimin kenan.
“Wata ‘kawatace zatayi aure shine ta gayyaceni to na tambayi jabeer ya Hanani kuma yace idan nasake tunkararsa da maganar ze gayama daddy, to nikuma yanda nike da ‘kawar tawa yawuce ace ta gayyaceni bikinta banjeba,
“To shine kuma baki iya zuwa rana d’aya ki dawo?
“Baze yiwu inje rana d’ayaba saboda ba nan garin bane.
“Wane garine? Hasana ta tambaya.
“Yar Kaduna ce, kuma kinsan nisan katsina zuwa Kaduna, kuma daga can Abuja zamu kai amarya kinga dole inkwana biyu.
Tana kaiwa nan a zancenta wayarta tashiga ringing tana dubawa taga sunan Hafiz gabanta yayi mummunan fad’uwa da kamar bazata d’agaba ganin Hassana ta tsareta da ido yasa ta d’aga “Heelow dan Allah kiyi Ha’kuri bani nacemiki zanzoba to yanzu haka wayar damuke ina hanya. Bata jira me Hafiz ze fad’aba ta tsinke wayar.
“Kinganiko sister wallahi tund’azu takemin waya, Amaryar cefa.
Hassana cikin sanyin jiki tace “shikenan na amince zan Zauna amatsayinki “Amma ba nan gizo ke sa’kar ba ya zamuyi da daddy da Momy kinsan dole zasu nemeni……
Saurin katseta Hussaina tayi tare da dafa kafad’arta “indan wannan kada kidamu, ni zantafi da wayarki zan barmiki tawa koda su daddy sunkira nasan bayanin dazanyimasu.
“To shikenan Hassana tafad’a, kawai dai ta amince da bu’katar ‘yar’uwar tata badan komeba sai dan taga yanda ta masifar shiga damuwa, amma can ‘kar’kashin zuciyarta cike take da tsoro da fargabar abinda suke shirin aikatawa.
Nan Hussaina ta ‘kar6i wayar Hassana ta kwafi Number Hafiz tasaka a wayar Hassana, wacce ke wayarta kuma tasata blacklist tare dayin delete d’in number daga wayarta sannan ta baiwa Hassana wayar.
Nan ta d’auki jakarta sukayi sallama da Hassana tatafi, tana fita takira Hafiz da number Hassana tafad’amashi tana hanya kuma idan ze kirata da wannan number ze kirata dan tabar waccan a gida.
Love u all my Fan’s 💃🏻 shoki 🏊🏻♀😏
[1/17, 9:19 AM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace* 👩🏻
Page………………….28
Gabanta yashiga dukan tara-tara a zuciyarta tarin’ka tunanin taya zatayi zaman aure da mijin ‘yar’uwarta, bayan ba mutuwa tayiba, kuma ba rabuwa sukayba, lallai Hussaina tasakata matsala sai yanzu takejin dama bata amince da ‘kudirintaba, amma yanzu aikin gama ya gama dole ta zauna tarufama ‘yar’uwarta asiri har lokacin dazata dawo, da wannan tunanin taji ana kiraye-kurayen sallar magrib saboda haka da sauri tanufi bedroom tashiga toilet ta d’auro Al’wala ta kabbara sallah, bayan ta idar da sallar ta dawo falo tsayawa tayi tana tunanin yanda zata fara aiwatar da ayyukan gidan dan da Alama Hussaina duk yau bata gyara gidanba,
Sharar falon tafarayi, tare da yin mopping, sannan tasaka wani ‘karamin towel me haske ta goge TV, center table, dakuma dining da sauran guraren da yakamata a goge, bayan ta kammala nan takoma bedroom, ta gayara tashare tare da canjama gadon bedsheet, lokaci guda gidan yayi fes kamar bashiba, freshner ta d’auko me dad’in ‘kamshi ta feshe ko’ina hatta da toilet saida tagayara ta fesa freshener abin gwanin sha’awa gidan sai yakoma kamar wani Sabin kaya aka zuba saboda tunda yake Hussaina bata ta6a gyarashiba, kullum saidai ta 6ata.
Bayan ta kammala wannan kitchen tanufa nanma tsayawa tayi tana tunanin me zata dafa, dan tasan duk inda me gidan yake yana gab da dawowa duk da batasan lokacin dawowar tasaba, ta dad’e haka daga ‘karshe ta yanke shawarar dafa abu mai sau’ki dan dare yafara gashi anata kiraye-kirayen sallar isha’i.
Jalouf d’in kus-kus ta dafa wanda yaji kayan lambu da kayan ‘kamshi, sannan tayi amfani da tsoka nama zallah ta yankata ‘kanana aciki yanda ze zamana duk lokacin da wanda zeci ya ebo yakai baki ze had’o da naman, dayake kus-kus ne cikin minti ashirin ta kammala dahuwar ta juye a flask, tare da had’a zo6o had’add’e shima sai ‘kamahin flavour yake ta jera kan dining.
Bedroom takoma tafad’a toilet ta she’ka wanka, bayan tafito bata wani 6ata lokaci gurin yin kwalliyaba lotion kawai ta murza tare da ‘yar hoda sai man le6e, wadrope tanufa ta d’auko wani had’adden less d’inkin Riga da siket ta sanya, wow kayan kuwa sun masifar kar6ar jikinta kamar dama dan ita aka d’inkasu, duk wata sura ta jikinta ta bayyana.
Zama tayi falo tare da jawo wayar da Husaina ta barmata tashiga danne-danne, tana dubawa tashiga inbox bataga komeba, sannan tashiga chat nanma ba kome, dan Hussaina batabar komeba saida tayi delete, dan kada Hassana taga halin datake ciki.
** ** **
Daddy ne ke safa da marwa hannunshi ri’ke da waya yanata try number Hassana amma sai acemai switch off, abin na matukar bashi mamaki gashi kuma har ‘karfe tara na ‘ko’karinyi bata dawo gidaba, Momy kuwa hankalinta yayi ‘kololuwar tashi “innalillahi Alhj yanzu ina yarinyar nan tashige, anya kuwa lafiya dan bata ta6a yimana hakaba,
Juyowa daddy yayi ya kalleta shima Hankalinsa a tashe, yace “ni kaina ina mamakin hakan dan Hassana yarinyace me matu’kar tsoro da kiyaye fushinmu amma yau ace tawuce ka’idar dana gindaya mata,
Momy wacce idanunta suka fara kawo kwallah tace bari inkira number Hussaina inji idan Hassana ta taho, wayarta ta d’auko ta lalubo sunan Hussaina tanata ringing ba’a d’agaba dan ganin sunan Momy a wayar ba ‘karamin d’aga hankalin Hassana tayiba, dan tasan duk yanda akayi yanzu itada Daddy sunacan hankalinsu yatashi na rashin dawowarta gida, bata d’aga wayarba saida kiran Momy na hud’u yashigo sannan ta d’auka ta dannan OK tare da karawa a kunnenta saida ta dai-daita nutsuwarta sannan tace “Assalamu Alaikum.
A d’ayan 6angaren Momy cikin 6acin rai tace Hussaina kina ina inata kiran wayarki har kusan sau hud’u baki d’agaba.
Ba ‘karamin fad’uwar gaba Hassana tayiba, tare da daburcewa dan gani take kamar Momy zata iya ganeta.
“Uhn ah am…. Dama bani kusa da wayar ne sai yanzu naji.
“To dama tambayarki zamuyi shin Hassana ta taho gida kuwa.?
“Eh tataho momy ai tun d’azu ta taho tace daddy yace kada ta wuce ‘karfe shidda kuma biyar da rabi tabar gidannan.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un Momy tafad’a tare da fashewa da kuka, tama manta ko tsinke kiran batayiba, Hassana kuwa tsayawa tayi ri’ke da waya a kunnenta tana sauraren yanda Momy ke kuka tana gayama daddy cewa “tun ‘karfe biyar da rabi Hassana tabaro gidan Hussaina.
“Subhannallah Daddy yafad’a tare da cewa Allah bayyana mamu ita a duk inda take.
Tsinke kiran Hassana tayi tare da sake kiran Momy, ringing d’aya ta d’auka, Nan Hassana ke tambayar “Momy wai meke faruwane, naji kinkira kintambayeni nabaki amsa kuma kinsa salati.
“Hussaina ‘yar’uwarki Hassana har yanzu bata dawo gidaba kuma munkira wayarta switch off,
“Innalillahiwa’inna’ilaijirraji’un Hassana tafad’a tare da fashewa da kuka, kafin ta tsinke kiran.
A tunanin momy Hassana tana kukane saboda 6atan ‘yar’uwarta.
Itako Hassana kukan nadama da ba’kin cikin halin dasuka jefa iyayensu takeyi, sai yanzu take datasanin yarda da kud’irin ‘yar’uwarta.
Love u all my Fan’s 💃🏻 shoki 🏊🏻♀. 🤒
[1/22, 6:47 AM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace* 👩🏻
Page………………….29
Zaune take kan d’aya daga cikin kujerun dake zagaye da falon ta buga uban tagumi hannu bibbiyu, ba abinda take tunani sai halin da iyayenta suke ciki,
A zahiri tayi magana “nidai bari inkira Hussaina tadawo gidanta nikuma inkoma gida in fuskanci kowane irin hukunci daddy zeyimin koda kuwa zefi na Hussainar tsanani, dan bazan iya zama cikin tunani da fargaba ba.
Wayarta ta jawo talulobo sunanta ta danna kira amma kuma cikin rashin sa’a sai akacemata wayar akashe, “ya salam tafad’a tare da d’ora hannu bisa kai nashiga ukku, tafad’a tare da mi’kewa tsaye “kodai inyi tafiyata idan tadawo tamasu bayanin inda taje, “kai bazan iyayima sister hakaba, muddin nasan daddy yaji labarin tayi wannan tafiyar kasheta kad’ai ne bazeyiba….
Wayyo ni Hassana ansakani tsaka me yuwa tafad’a tare da komawa ta zauna kan kujera jiki duk ba lakka.
Horn d’in mota taji gabantane yayi wani mummunan fad’uwa da sauri tanufi window tad’ga labulen tare le’kawa, me gadi ta hango yana ‘ko’karin bud’e get, bayan ya bud’e motar jabeer tashigo duk kan idon Hassana yayi parking sannan yafito hannunsa d’auke da jakarsa, da sauri takoma ta zauna sannan tayi ‘ko’karin dai-daita nutsuwarta dukda mummunan fad’uwar gaban datakeyi.
Da sallama yashigo falon, Hassana na Zaune jikinta sai kyarma yake tana tunanin wace irin tarba zatayima mijin ‘yar’uwar tata, da kyar tasamu ta dai-daita nutsuwarta tare da mi’kewa ta dur’kusa ta kar6i jakar hannunshi tana mashi sannu da Zuwa, jabeer kuwa tsananin mamakine ya lullu6eshi yayi tsaye inda yake yakasa motsawa yayinda itakuma Hassana ta dad’e da shigewa d’akinsa domin ajiyemar jakarsa.
Murmushi yayi a Zuciyarshi kuma yace “ikon Allah, yau kuma ni Hussaina kema wannan tarbar, bin ko’ina na falon yayi da kallo ya ganshi fes-fea ba kamar yanda yasaba ganinshiba kullum kace-kace, sannan tunda yashigo daddad’an ‘kamshin girki dana freshner sun had’u sun dakar mai hanci, lumshe idonshi yayi tare dayin wani guntun murmushi sannan yanufi d’akin dai-dai Hassana itakuma zata fito daga d’akin kad’an yarage suyi karo da juna Hassanar tayi saurin ja da baya duk tawani daburce “um ga ruwan wanka can nahad’ama “To, kawai jabeer ya iya amsawa dashi tare da binta da kallon mamaki sannan ya wuce Zuwa toilet d’in, tana ganin shigarsa tayi saurin zuwa wadrope ta fiddo mashi ‘kananan kaya marar nauyi tare da ajiyesu gefen gado sannan tafita zuwa falo.
: Yana fitowa daga wankan yayi tozali da kayan da Hassana ta ajiyemai murmushi yayi saida ya murza mai sannan ya d’auki kayan ya sanya tare da feshe jikinsa da daddad’an turarensa, sannan yafito zuwa falo, zaune take kan kujera da waya hannunta tund’azu number Husaaina kawai take try amma switch off, dan tunda jabeer yadawo hankalinta yayi matu’kar tashi jikinta keta kar-karwa tsoronta d’aya kada jabeer yagane ita ba matarshi bace.
Da sauri ta tashi tana mashi sannu da fitowa, tanufi dining ta zauna sannan ta kalleshi “bissmillah mana tafad’a tare da gyaramashi kujerar daze zauna, ba musu yazo ya zauna yana binta da kallon mamaki danshi har yanzu abubuwan dake faruwa ganinsu yake kamar a mafarki wai yau shine Hussaina ke tarairaya haka lallai da walaki amma koma miye ba yanzu yakamata in tambayetaba.
Yana cikin wannan tunanin harta zubamar abincin ta ajiye gabanshi sannan itama ta zuba nata, haka suka faraci dad’in abincin na ratsa jabeer har tsakiyar kanshi, a zuciyarshi yana cewa “yaushe rabon dayaci abinci me dad’in haka kullum yana hanyar zuwa restaurant,
Da misalin ‘karfe tara da rabi na dare suna zaune falo kowanensu yayi ahiru wani Indian film suke kallo a tashar zee cinema, da Alama film d’in yayima Hassana kyau dan ta maida hankalinta kaf kan film din, yayinda jabeer bacci yacikamar ido, sai hamma yake d’aya bayan d’aya tasowa yayi daga kujerer dayake yazo inda Hussaina take zaune Yakama hannunta “Taso muje mu kwanta, wani mummunan fad’uwar gaba taji tayi saurin kwace hannunta Daga nashi tace kaje ina zuwa saina ida kallon wannan film d’in.
Juyawa yayi ya kalli TV cike da mamaki dan yasan Hussaina bata ta6a yimar musuba idan ya umarceta dasu kwanta, kuma da kallo be dametaba, da wannan tunanin ya wuce d’aki yayi kwanciyarsa kasancewar akwai gajiya jikinsa bacci yayi gaggawar d’aukarsa.
Love u all my Fan’s 💞💘💞💕💖😘
[1/26, 10:09 AM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace* 👩🏻
Page………………….30
Husaaina kuwa bayan ta isa gidan Hafiz, cike da murna da jin dad’in zuwanta ya tarbeta, tana isa takira Zuby a waya, ringing d’aya zubyn ta d’auka dama jiran kiran takeyi.
“Hellow ‘kawata Zuby tafad’a cike da ‘kagara taji abinda Husaainar zata fad’a mata.
“Kawata naji dad’in shawarar da kikabani dan yanzu haka ina tare da mutumin,
Dariya zuby tayi a ranta tace “Zaki gane kurenki zaki gane da zuby kike magana.
Amma a zahiri sai tace “ai dama nagayamaki hakan kawai zakiyi kije inda ranki keso kiyi ko kwana nawa kikeso batare da wata matsala ba.
“Ai shiyasa nake masifar sonki ‘kawata Hussaina tafad’a.
Zuby tace “ai nima banida kamarki shiyasa kullum nakeson ki kasance cikin farin ciki, da haka sukayi sallama, kowace ta ajiye wayar
Wata mahaukaciyar dariya zuby tayi tare da tafa hannu ” yarinya kinshiga tarkona kad’an yarage in cimma manufata akanki,
Wata sabuwar dariya ta’kara kafin tasha mur kamar bata ta6a dariyaba “Hussaina ina me tabbatar maki yanda kika baro gidan jabeer kin barshi kenan Har abada.
Hussaina kuwa bayan sun gama waya da zuby toilet tashiga ta she’ka wanka, bayan tafito tabi jikinta da lafiyayyen lotion dinta tashafa kayan jikinta ta maida sannan tadawo falo ta zauna tana jiran shigowar Hafiz dan bayan sallar isha’i yafita yo masu take a way.
Be dawo gidanba sai ‘karfe tara da rabi lokacin Hussaina nadai zaune kan kujera a falo sai hamma take jerawa d’aya bayan d’aya, ga yunwa na addabarta ga kuma wani irin bacci dake fizgarta
Da sauri Hafiz ya isa gareta tare da ajiye ledar dake hannunsa gabanta, “sorry babyna na dad’e ko? Ya tambaya yana kallonta yanda take lumshe idanu da Alamar jin bacci tattare da ita.
“Uhm, kawai tace tare da ‘Kara gyara zamanta kan kujerar datake, “sorry sorry babyna tafad’a tare da nufar kitchen, bayan yan mintoci ya fito hannunsa d’auke da plate da cukulla da cup’s, gabanta yazo ya ajiye sannan yazuba masu abincin, da sauri Hussaina ta fara ci saida taji tayi dam sannan ta kora da lemu, toilet tanufa ta wanke bakinta tadawo kan kujerar datake tad’an kishingid’a cikin mintina biyar bacci yayi awon gaba da ita.
Hafiz Kuwa bayan shima ya kammala cin abincin tattara plate d’in yayi da cup’s ya mayar kitchen sannan ya wuce bedroom yafad’a toilet yashe’ka wanka yana futowa ya shafa cream wasu tare da feshe jikinsa da turare, jikinsa sanye yake da vest da shortnicar falo yanufa har yanzu Hussaina na kwance inda yabarta kan kujera sai sharar baccinta takeyi,
Tsayawa yayi kanta saida yakaremata kallo, take wata matsananciyar Sha’awarta ta d’arsu a zuciyarsa ahankali yakai hannunsa jikinta yafara shafata yana mata irin salon dayasaba tayar mata da hankali.
Can cikin bacci taji ana ta6ata saurin bud’e ido tayi tare da saukesu kan Hafiz dake aikamata sakon wani shu’umin murmushi, ture hannunshi tayi daga jikinta “miye haka kake shirin aikatawa kasanfa da da yanzu ba d’aya bane, yanda nasaki jiki dakai a da nabaka duk abinda kakeso yanzu baze yuyuba.
Hafiz yad’an 6ata rai “Haba babyna sabodame zaki hanamin kanki?
“Saboda kwakwkwaran dalili, Hussaina tabashi amsa.
“Inaga babu wani dalili dazesa ki hanamin wannan lallausan jikin naki me tarin ni’ima, a da kika amince dani baranrantana kuma yanzu da kome zamuyi baza’a ganeba kawai ki amincemin mu shana, yafad’a tare da jawota jikinsa ya matseta gam.
*sai kunyi ha’kuri da typing saboda ‘yar matsalar da wayana ya samu koda aka gyara sai naji duk ta canjamin typing d’inma baya sauri*
Love u all my fan’s 💃🏻 shoki 👄🍭
[1/26, 3:05 PM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace* 👩🏻
Page………………….31
®TALANTED WRITER’S GROUP (T.W.G) 📝
Saurin tureshi tayi daga jikinta tare da mi’kewa tsaye cikin 6acin rai take magana “haba Hafiz wannan wace irin rayuwace, kabar ganin nakawo kaina gareka hakan ba yana nufin zan mallaka maka duk abinda kake bu’kataba daga gareni, akwai dalilin dayasa na amince da zuwa gidanka harna baro gidan aurena, duk wannan maganganun Hussaina tanayinsune cikin tsananin fushi da matsananancin 6acin rai.
Ran hafiz ya 6aci da jin maganganun Hussaina yayi niyyar gayamata magana kamar yanda gayamar amma sai wata zuciyar tace “fushi ba naka bane kabita a hankali har kasamu ha’karka ta cimma ruwa.
Cikin sanyin jiki hafiz ya dur’kusa gabanta shikenan babyna na ha’kura amma kitaso muje mu kwanta yafad’a tare da kama hannunta.
Fizge hannunta tayi daga rikon dayayimata tare da komawa kan kujera ta zauna tace “kaje kawai ni anan zan kwanta, tashi hafiz yayi yanufi bedroom jikinsa a sanyaye a zuciyarsa ba haka yasoba yaso ace ya kwashi gara ta hanyar kusantar Hussaina dan dama ya dad’e rabon dayayi mu’amula da wata mace tunda suka samu sa6ani da zuby kusan sati batazo gidanshiba wanda ada yasaba baya kwana biyu basu had’u suka she’ke ayarsuba.
Da haka ya haye gadonsa zuciyarsa fall da tunani “to miye amfanin zuwan wannan yarinyar guna tunda bazanji dad’i da itaba, amma bari inbarta inga iya gudun ruwanta zuwa gobe kuwa idan ta’ki amincewa zan danneta kota ‘karfi, dan nariga na kwad’aitu da ni’imar jikinta da wannan tunanin bacci 6arawo yayi awon gaba dashi, yayinda Hussaina batayi wani baccin kirkiba sakamakon wani mummunan mafarki datayi da Hassana Hakan yasa ta yanke hukuncin komawa gida gobe dan ganin halin da ‘yar’uwarta take ciki.
** ** **
Kiraye-kirayen sallarY asubah yatashi jabeer daga bacci yakai hannunsa inda yake tunanin jin matarsa amma sai yaji wayam tunaninsa yakai ga tana toilet yadad’e yana jiran firowarta amma har ana niyyar kabbara sallah masallaci batafitoba ahankali ya tura ‘kauren toilet d’in ganin bata ciki yabashi mamaki shiga yayi ya d’auro Alwala yafito falo ga mamakinsa ganinta yayi kwance kan kujera ta tada kanta da pilon kujerar tanata sharar bacci.
Cike da mamaki jabeer ya’karema Hassana kallo wacce shi atunaninsa Hussainace a zuciyarsa yace “me hakan ke nufi Hussaina ta canja hali ta ko’ina tana kyautatamin amma kuma yanzu tana ‘kauracema shimfid’ata sa6anin da da bata kyautata min amma kuma tana bani Ha’kkina na aure dan koban kirataba zata kawo kanta to kodai tana cikin lalurane, amma kotana lalurar fashin sallah tasan duk hanyar sazatabi ta biyamin bu’kata kuma bata ta6a ‘kin kwana tare daniba, amma koma miye zan tambayeta inji dalili.
Da wannan tunanin yatasheta sannan ya umarceta dataje tayi sallah, ba musu tatashi cikinagagin bacci tanufi toilet ta d’auro Alwala ta kabbara sallah, shikuma ya wuce massallaci dan gabatar da tashi sallar.
Bayan an idar da sallah jabeer yadawo gida tundaga falo yake jiyo sautin karatun al’qur’anin da Hassana ke rerawa abin ya matu’kar bashi mamaki dan yasan tunda yake da Hussaina bata ta6a yin karatun Qur’anic irin wannan lokacinba, cike da mamaki ya wuce bedroom yahaye gado ya kwanta yana sauraren yanda karatun ke ratsa kwalwarsa cikin zazza’kar muryarta.
Saida tayi da yawa sannan ta tsaya tayi addu’a tashafa inda jabeer yake kwance taje ta zauna nesa dashi cikin ladabi tace “barka da kwana
“Barka dai jabeer yafad’a batare daya d’ago daga kwancen dayakeba.
“Antashi lafiya? Takuma tambayarsa “lafiya lao, ya amsa tare da gyara kwanciyarsa.
Daga nan bata ‘kara maganaba tafito tanufi kitchen domin sama masu abin karyawa.
Love u all my fan’s 💃🏻 shoki 👄🍬
[1/28, 8:12 AM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace* 👩🏻
Page…………………. 32
®TALENTED WRITER’S GROUP (TWG) 📝
Gidansu Hassana kuwa Hankalinsu yayi matu’kar tashi ganin ankwana d’aya ba Hassana ba labarinta, Momy tayi kuka harta godema Allah yayinda dady yarasa sukuni ankai report police station sannan daddy da kanasa yaje duk wani babban asibiti dake garin ko Allah zesa yaga Hassana koda kuwa gawartane hankalinsu ya kwanta anma kome kama da ita be ganiba.
Dole ya hakura ya dawo gida ya zauna hankali a tashe yasaka cigiya gidajen redio da television,
Maganar 6atan Hassana ta bud’e ko’ina ‘yan’uwa da abokan arzi’ki sai zuwa suke jaje, Momy Kuwa kuka kawai take idanunta sun kumbura abinci kuwa sai dai tad’an tuttura abinda ya sauwa’ka dan abincinma d’acinsa takeji ga matsanancin ciwon kai dake addabarta.
** ** **
Da misalin ‘karfe takwas ta kammala had’a masu breakfast ta jera kome a dining Sannan ta hau gyaran d’akin duk da bawani datti yayiba ta ‘kara gyarashi ta share sannan ta kunna turaren wuta, a hankali ta tura ‘kofar bedroom d’in wani dad’i taji ganin jabeer baya d’akin saboda haka da sauri tashige tare da maida ‘kofar ra rufe hada sa key. A gaggauce ta gyara d’akin ta goge ko’ina sannan ta feshe da freshener, kayan jikinta ta cire ta d’aura wani ‘karamin towel tafad’a toilet ta she’ka wanka bayan tafito gaban dressing mirror ta tsaya simple makeup’ tayi sannan tanufi wadrope wasu riga da siket na less tasaka, kayan sun masifar fito da ainafin kyawunta dukda ba wata kwalliya tayiba.
Lokacin kuma jabeer yafito cikin shirinsa sanye yake cikin ‘kananun kaya milk d’in riga da ba’kin wando ‘kafarsa sanye da ba’kin takalmi yan kamfanin masaraci, hannunsa ri’ke da jakarsa ta Zuwa office, ajiye jakar yayi kan kujera sannan yanufi d’akin da Hassana take tura ‘kyauren d’akin yayi da mamakinsa sai yajishi gar’kame da key, saboda haka nocking yayi sannan yanufi dining ya zauna yana jiran fitowarta dan bayaso ya makara office dan yanzu ayyuka duk sun dawo hannunsa saboda daddy baya fita office saboda 6atan Hassana
Saida gabanta yayi ‘yar’karamar fad’uwa lokacin da jabeer yata6a kyauren d’akin.
Jiki a sanyaye ta bud’e tafito kan dining ta hangeshi saboda haka can tanufa tana takunta cikin nutsuwa, idanuwa jabeer ya ‘kuramata ko ‘kiftawa beyi wata matsananciyar sha’awarta ke fizgarshi dan jabeer irin mutanannane masu ‘karfin sha’awa dan baze iya kwana biyu batare daya kusanci matarshiba kuma itama ta sabamai da hakan dan kobe nemetaba take kai kanta gareshi shikuma bewuce tayi. _lol_
Jitayi dukta tsargu da kallon dayake mata, ba ‘karamar dauriya tayiba lokacin data iso taja kujera d’aya ta zauna sannan ta fara zubamar kalacin duk illahirin jikinta kyarma yake.
Haka suka fara breakfast d’in bayan sun kammala ne jabeer ya kalli Hassana yace “waini Hussaina kwana biyu naga kin canjamin kinayimin duk wani Abu dakikasan ze faranta raina sa6anin da davaki damu da damuwataba.
Murmushi tayi “kada ka damu mijina kasan Allah ba yanda baya sauya Al’amarinsa jiya ina zaune ina kallon TV aka sanyo wani malami yana wa’azi, to wa’azin dana tsaya na saurara sainaji kamar hallayatace kaf yake zayyanawa sannan kuma tafad’i irin azabar da Allah yatanada ga mata masu irin halayyarmu shine nikuma abin yad’agamin hankali.
Cike dajin dad’i jabeer yace “kai amma Allah yayima wannan malamin Al’barka
Hassana ta amsa da “Ameen.
Shiru yad’an ratsa nayan mintittika kafin jabeer ya’kara magana karo na biyu “to amma malamin beyi magana kan matar dake “kauracewa shimfid’ar mijintaba dakuma irin azabobin da Allah ya tanadar mata.
Love u all my fan’s 💃🏻 shoki 👄🍦
[1/30, 9:01 AM] Zee Elkaseem: 👭 *AUREN TAGWAYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
🕸🕸
🕸
*Written & Story by*
*Zee Elkaseem*
*{Mmn khady}*
*Dedicated to All member’s group of Ciwon “ya mace* 👩🏻
Page………………….33
® _TALENTED WRITER’S GROUP_ _(TWG)_ 📝
Shiru Hussaina tayi dan batada cikakkiyar Amsar dazatabashi akan wannan tambayar da yayimata, ganin batada niyyar magana yasashi mi’kewa tare da d’aukar jakarsa “ni zan wuce wurin aiki “Allah kiyaye hanya kawai tacemasa batare data motsa daga inda takeba.
Yana fita ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya da sauri tanufi bedroom waya ta d’auko ta shiga laluben sunan Hussaina sannan ta danna kira cikin sa’a kuwa tasamu wayar na ringing amma harta tsinke ba’a d’agaba, batayi ‘kasa a gwiwaba ta’kara kira karo na biyu nanma tanata ringing sai gab da zata tsinke sannan aka d’aga
“Hussainace tafara magana Hellow sister ai ganinan ina shiri inshaAllah yau zandawo yanzuma bada dad’ewaba.
Wata ajiyar zuciya Hassana tayi “nidai dan Allah ki dawo kinga muna shiga hakkin mijinki saboda na kula irin mutanennane mabu’kata nikuma kinga ba yanda za’ayi inbiyamasa dan Allah ki dawo saboda gudunmatsala.
Kada ki damu sister inshaAllah yau zandawo “To shikenan tafad’a tare da ajiye wayar kan mirror datake kwalliya gabanshi,
gefe kuma ga jakar kayanta da sauri tagama kwalliya sannan ta jawo jakar taciro wani riga da zani na atamfa ta sanya sannan ta d’aura d’ankwalin kayan wata madaidaiciyar hijab tasaka sannan takoma bakin gado tazauna tana jiran dawowar Hafiz, tund’azu yafita be dawoba shi kawai take jira gashi har ‘karfe sha d’aya da mintittika, ‘kara duba agogon wayarta tayi lokaci naja wani d’an guntun tsaki tayi tare da ajiye wayar gefenta ta sadda kanta ‘kasa tunanin yanda zasuyi Hassana takoma gida batare da wata matsalaba takeyi dan tafi kowa sanin halin daddy.
Wata zuciyar tace ki kira zuby tunda itace tabaki wannan shawara itakad’ai kuma zata baki shawarar yanda za’ayi Hassana takoma gida batare da ansamu wata matsalaba.
Murmushi tayi tare da mi’kewa dan d’auko wayarta, gabantane yayi wani mummunan fad’uwa lokacin dasukayi ido hud’u da ita, sanye take cikin wani matsatstsen wando da wata figigiyar riga wacce da kad’an tawuce ‘kugunta sai wani yabud’ad’d’en gyale datayi rolling dashi fuskarta ba Alamar fara’a ko kad’an.
Cike da mamaki Huasaina ta kalleta tare da fad’uwar gaba, dakewa tayi ta tanufo inda take tsaye ta maida hannuwanta baya tanayima Hussaina wani shu’umin kallo.
“Naji dad’in zuwanki ‘kawata kamar kinsan dama yanzu nake ‘ko’karin kiranki, Hussaina tafad’a tana fad’ad’a murmushin dake fuskarta.
‘Kara d’addaurewa Zuby tayi ba Alamar wasa tattare da ita, duk da haka Hussaina daurewa tayi tacigaba da kusanto inda zuby take, batayi auneba sai jitayi zuby ta hankad’ata iya ‘karfinta tayi taga-taga zata fad’i da kyar tasamu ta daddafe ta kalli zuby wacce ke ‘kara tinkarota har yanzu dai hannunta d’aya na bayanata, ‘kara Hankad’a Hussaina tayi iya ‘karfinta wannan karon saida tayi nasarar kayar da ita.
Wata irin fad’uwa Husaainar tayi kanta ya bugu da gefen gado take gurin yafashe yafara zubar jini, Hannu Hussaina tasa ta dafe gurin tana kallon zuby dake tunkarota Hannunta ri’ke da wani ‘katon icce.
Cike da tsoro da fargba Hussaina ke ‘ko’karin mi’kewa dan samun matsera dan taga Alamar ba wasa ko kad’an a idon zuby kuma ba Alamar d’igon imani tare da ita.
Ganin Hussaina na ‘ko’karin mi’kewa yasa Zuby d’aga iccen dake hannunta ta kwantarama Hussaina akai, nan take ta zube jini yagama wankemata fuska, ta kalli Zuby cikin ‘karfin hali da kyar ta iya d’aga bakinta tayimata magana.
“Zuby me nayimaki kike neman kasheni, mena tsaremaki a rayuwa?
Wata mahaukaciyar dariya zuby ta gagga6e da ita sannan ta d’addaure kamar bata ta6a dariyaba, sannan ta du’ko dai-dai inda Hussaina take kwance male-male cikin jini tana maida numfashi da kyar tace “Kin taremin kome a duniya Hussaina na dad’e ina ba’kincikin kasancewarki d’iyar masu kud’i nikuma d’iyar talakawa wad’anda talauci yayima kanta.
Sannan na dad’e ina mutuwar son Hafiz beta6a nunamin soyayyaba dai-dai da rana d’aya sai dai yana biyan bu’katarshi dani aduk lokacin daya bu’kaci hakan.
Amma lokaci guda ya nuna ba wacce yakeso sai ke, tafad’a tana nunata da yatsa.
Sannan tami’ke tsaye tayi taku biyu zuwa ukku “ban ‘kara shiga tashin hankaliba sai ranar danaje gidanki mijinki yayimin kyautar kudad’e masu yawa tundaga lokacin naji ba wanda nakeso samada mijinki jabeer kuma naci Al’washin sai yazama mallakina.
Na zauna nayi tunani nayi nazari naga ba yanda za’ayi insamu biyan bu’kata saita hanyar kawar dake daga doron duniya.
Hussaina najin haka wani irin kuka da nadama sukazomata lokaci guda.
Zuby kuwa ba tausayi ba imani tacigaba da bugun Hussaina aka da wannan ‘katon iccen saida ta tabbatar da babu sauran numfashi tattare da ita sannan tayi saurin barin gidan.
Love u all my Fan’s 👄
[1/31, 9:AYE* 👭
🕸🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸🕸
🕸🕸🕸
Da musalin ‘karfe biyar na yamma Hassanace Zaune itada jabeer sai janta yake da fira amma ita kwata-kwata hankalinta baya gurinsa itadai fatanta d’aya Hussaina tadawo itakuma ta koma gida dan yau ya kasance weekend jabeer be fita ko’inaba tun safe yake gida sai wani shu’umin kallo dayakebinta dashi.
Wayarta ta jawo tacigaba da try number Hussaina wacce tun misalin sha d’aya na safe daaukayi waya ta gayamata tana hanya, tundaga lokacin kota kira sai tayi ringing tagama ba’a d’agaba, yanzu kuwa data kira cemata akayi (switch off) kashe take baki d’aya hankalinta ya’kara tashi ga jabeer yatasata gaba da Alama yanada bu’kata.
“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un ta furta tana ‘ko’karin ‘kara try number Hussaina lokacin jabeer ya’karaso inda take zaune shima zama yayi kusa da ita har jikinsu na gugar na juna, Hannu yasa ya kar6e wayar tare da jawota yahad’ata da jikinsa “wai tund’azu wa kike faman kira haka kinbarni ni kad’ai sai fira nakemaki amma Sam hankalinki baya gurina yafad’a tare da ajiye wayar kan centre table, itakuwa Hassana yana Had’a jikinta da nashi jikinta yahau 6ari, kyarma take kamar mazari, shikuwa jabeer shiga yayi cikin wani irin yanayi me wuyar fassarawa, wata matsananciyar sha’awa ta’kara saukarmai lokacin yakai ‘kololuwa gurin bu’katar mace.
Tureshi tafarayi tana ‘ko’karin raba jikinta danashi,
Lokacin ya fahimci halin datake ciki sakinta yayi tare da ‘kuramata ido sannan ya kira sunanta cikin wata mabu’kaciyar murya “Hussaina
“Na’am ta amsa batare data d’ago ta kalleshiba.
‘Kara kiran sunanta yayi karo na biyu “Hussaina, d’agowa tayi ta kalleshi batare datakuma yin maganaba, gabanta yayi wani mummunan fad’uwa ganin irin cikin halinda jabeer yake ciki idanunsa sun kad’a sunyi ja, magana yafara muryarshi na sar’kewa kamar zeyi kuka “dan Allah ki taimakeni kibani ha’kkina sanin kankine ban iya neman matan banzaba kece halalina bekamata ki gujeniba, banida wanda ze d’aukemin wannan sai ke, kuma tun acan baya kinsabin da bani ha’kkina duk lokacin dana bu’kaci hakan amma cikin kwanaki biyu kingujeni, meyasa ? miye dalili? namaki wani laifine? ya’karashe maganar yana kallonta.
Wani irin tausayinshi yakamata, batasan lokacin da wasu zafafan hawaye suka zubo daga idanuntaba a zuciyarta tace “Hussaina kin cuci mijinki kinbarshi cikin wani hali wanda ni ban isa in fiddashiba,
Nikuma kinsani tsaka me yuwa, ya Allah ka kawomin d’auki.
Ganin hawaye a fuskarta yasa hankalin jabeer tashi yafara tambayarta “maganar danayimakice ta 6atamaki rai, indan wannanne kiyi ha’kuri nima na ha’kura, yana gama fad’in haka yatashi yanufi bedroom,
Minti sha biyar da shigarsa saigashi yafito sanye da wasu kayan ba Wanda yashiga dasuba ko kallon inda take beyiba yafice daga gidan, tanajin lokacin dame gadi yabud’emasa get yafice da motarsa, fad’awa tayi kan kujera tafashe da wani sabon kuka
Wayarta tajawo tasake kiran number Hussaina amsar dai d’ayace wayar na rufe baki d’aya.
Haka tacigaba da kukanta ita d’aya cikin gida bame rarrashinta,
Da misalin ‘karfe takwas na dare jabeer yadawo gidan hannunsa d’auke da leda da sallama yashigo falon, zaune take jikinta sanye da wata ‘karamar hijab, sannu da zuwa tayimai tare da kar6ar ledar dake hannunsa fresh milk ce sai gasashshin kaji, zama sukayi tsakiyar kafet d’inda ke malale falon suka fara ci, jabeer ciyake sosai yayinda Hassana take d’an tutturawa dan batada wani sukunin cin abinci.
Duk abinda take yana kula da ita amma be tankamataba, saida yaci ya ‘koshi sannan yabi da fresh milk itama madarar ta zuba ta kwankwad’a saitaji tamata dad’i saboda haka duka ta shanye tata, shikuwa jabeer daya gama dama d’aukar sauran nashi milk d’in yayi yanufi bedroom dinshi.
.
Tana gama shan milk d’in taji kanta yamata nauyi duk illahirin jikinta yayi sanyi wani irin bacci ya rin’ka fizgarta duk abinda ke falon takoma ganinsa bibbiyu, da kyar tasamu ta isa bedroom tare dayin nasarar sa key ta kulle ‘kofar sannan tafad’a gado ko sauya kayan jikinta batayiba zuwa na bacci.
Kusan minti goma da shigarta d’aki jabeer yafito daga gudan d’akin tura d’akin nata yayi amma sai yajishi gar’kame da key wani irin haushi ya ‘kuleshi da sauri yakoma d’akinshi sai gashi yadawo da wani key d’in a hannunsa, sakashi yayi gurin key d’in ‘kofar sannan ya murd’a ‘Kofa kuwa ta bud’e shiga yayi d’akin haske fayau dan Hassana ko damar kashe fitilar d’akin bata samuba bacci me nauyi yayi awon gaba da ita.
Tsayawa yayi yakaremata kallo wata irin kwanciya datayi, wani Shu’min murmushi yayi sannan ya rage hasken d’akin ya maida ‘kofar yarufe hayewa yayi kan gadon yajawota zuwa jikinsa yafara wasa da jikinta cikin ‘kan-‘kanin lokaci yabiya bu’katarsa da ita batare datasan inda kanta yakeba.
Saida ya gama abinda yake yafad’a tunani a Zuciyarsa yake cewa “yanaji Hussaina kamar budurwa wacce bata ta6a sanin namijiba abin da mamaki.
Wata zuciyar tacemai ba wani abu yasa kajita hakaba sai dan bada amimcewarta ka kusancetaba.
Nan take yayi na’am da abinda zuciyarsa ta raya masa sannan kuma ya tsinci kansa cikin tsananin farin ciki.
Ahaka bacci yayi awon gaba dashi yana rungume da hassana jiyake wani sabuwar ‘kaunarta na’kara shigarsa
Kiran sallar asubar farko Hassana ta farka daga nannauyan baccin datayi, jinta jikin mutum yasata saurin ida bud’e idanunta dan tabbatarma kanta shin abinda taji da gaskene ko mafarki takeyi ganin jabeer kwance yana sharar bacci ga ya had’e jikinshi da nata ya wani rungumeta, ga jikinta ba kaya ko d’aya tana ganin haka tasan aikin gama ya gama, jabeer yagama biyan bu’katarsa da ita, wani ‘kululun ba’kin ciki yazo ya tokareta batasan lokacin data fashe da wani irin kukaba.
Kukanta yatashi jabeer daga nannauyan baccin dayakeyi me cike da Farin ciki, tambayarta yashigayi “lafiya Hussaina meyasaki kuka, a zuciyarta tace jabeer tsakanin kaida sister bansan wanda ya cuceniba sanadiyyar haka gashi narasa abinda kowace d’iya mace take ta’kama da tin’kaho dashi.
“Wayyo Allah nashiga ukku tafad’a hawaye nabin kumatunta wasu bayan wasu.
Jabeer kuwa ‘kara jawota yayi jikinsa ya ‘kara ‘kan’kameta yana rarrashinta “please and please tell me, shiru tayimai dan batada amsar dazata bashi.
“Haba Hussaina ki gayamin abinda ke damunki duniya idan baki gayamin damuwarkiba amatsayina na mijinki waye zaki fad’amawa.
Hassana kuwa jitayi kamar tadad’amai tace “bafa matarka bace Hussaina ni ‘yar’uwartace, saurin sa Hannu tayi ta toshe bakinta tana cigaba da kuka gani take kamar tunanunta zefito fili har jabeer yaji.
Ahankali ta zame daga jikinshi tana tafiya da kyar tanufi toilet tahad’a ruwan gumi tagasa jikinta sannan tayi wankan tsarki ta d’auro alwala tazo ta tada sallah lokacin shima jabeer yana d’akinsa wankan yayi tare da kabbara sallar a zuciyarshi yana tunanin dalilin kukan matar tashi danya kusanceta Wanda ba yau suka faraba.
Bayan ta idar da sallah tana zaune kan abin sallar hawaye nacigaba da zuba daga idanunta jabeer yashigo d’akin zama yayi bakin gado yana fuskantarta ya kula da har yanzu kuka take ajiyar zuciya yayi sannan yace “Hussaina yau inaso ki gayamin dalilin ‘kauracemin dakikayi kuma dan na kusanceki kike kuka kamar na kasheki.
A zuciyarta tace “kara kisa da abin kunyar dana aikata, nayi matu’kar danasani da amincewa da “kudirin ‘yar’uwata.
Maganar jabeer ce tadawo da ita daga tunanin datake “zaki fad’amin kokuwa saina kira daddy ‘kila shi ki fad’amasa.
Saurin d’agowa tayi da jajjayen idanunta ta kalli jabeer ba Alamar wasa tattare dashi, gabanta yayi mummunan fad’uwa kawai saita tsinci kanta da gayamashi “dama Hussaina ce………..