Ayshat Ɗansabo lemuNAILAH CHAPTER 4 BY

Taƙare maganan tana buɗe plate ɗin da Amal ɗin ta zuba soyayyen irish ɗin da plantain a gefe,ganin da yawa xai ishesu suci su biyu yasa Nailah ɗaukan cup kawai don haɗa tea,anan kitchen ɗin sukai breakfast ɗinsu suka gama,Amal ce kawai batai wanka ba ta nufi ɗakinta don yin wanka ta shirya saisu amsa kiran Dady ɗin.

Nailah da Nafeesa kuma suka nufi falo,zamansu keda wuya ya Hussain ya shigo suka gaidashi ya amsa da fara’a yana duban Nailah yake faɗin.” Me sunan ƴan gayu Dadah na gaidaki tace kin rabu da zuwa yi mata tausa tayi kewarki.”

Dariya Nailah tayi kaɗan tana shagwaɓe face take faɗin.” Kai ya Hussain kaima me sunan ƴan gayun zaka ɗana yau,Allah sarki Dadah kaman tasan nima nayi missing ɗinta insha Allah anjima zamu leƙata.”

“Da dai yafi kuwa don tsohuwannan inta fara mitan tayi kewanka gara kawanke ƙafanka kaje kafin tace zata xoda kanta.”

Duk suka sanya dariya gaba ɗaya kafin dariyan Nailah ya riga nakowa ɗaukewa,sakamakon mayen qamshin turarensa daya iso hancinta,idanunta takai bakin ƙofa shi ɗinne ko ke tahowa face ɗinnan a haɗe babu alamun wargi,tayi saurin ɗauke kai ta maida hankalinta kan wayanta,tuni ya Hussain ya nufi dining don neman abinda xaici,koda ya iso tsakiyan falon tsaye yayi kiƙam,Nafeesa ce ta fara gaidashi ya amsa aciki ba tareda ya kalli inda suke ba.

Nailah ce itama ta gaidashi cikin sassanyar muryanta,shiru yayi bai amsaba saima wani uban tsaki daya ja yana takawa ya nufi hanyar da zai kaishi sashin Dady,ba Nailah kawai ba hatta Nafeesa yadda A.A Mainasara yayi ya bata mamaki,shiru sukayi suka kalli juna tuni idanun Nailah harya tara ƙwalla ta rasa me kuma tayi masa da xafi haka daya ɗauki karan tsana ya ɗaura mata.Sai dai bata dame amsa mata hakan yasa ta maida idanunta kan wayanta har zuwa lokacin da Amal ta fito ta shirya tsaf cikin riga da skat dayai fitting ɗinta na atamfar chiganvy red dayai asalin haska farar fatarta domin farace tas ita har tafi Momy haske.

“Ku muje ko ƴan matan Momy.”

Cewan Amal alokacin data ƙariso inda suke,babu musu suka bi bayanta don zuwa amsa kiran Dady,samunsa sukai zaune shida ya AA wannan karon babu Momy watakil tana side ɗinta ne.

Waje suka samu suka zauna suna jiran ya gama da ya Anwar ɗin,sunyi zaman kaman minti biyar ya AA ɗin ya fice hakan ya maido da hankalin Dady garesu ya fara da faɗin.

“Amal dake zan soma tunda kece babba,ki sanar dani wanene kika tsayar ya zama abokin rayuwanki?don nan da lokaci kaɗan zan haɗaku duka na aurar daku.”

Amal tai ƙasa da kanta alamun kunya kafin ta buɗe baki tana faɗin.” Dady Aliyu ne kawai muke tareda shi ɗan gidan Alhaji Ahmad Lawal.”

“OK to saiki sanar masa idan da gaske yake ya turomin magabatansa,ke kuma Nafeesa fa?”

ya jefi Nafeesa da tambayan yana tsareta da manyan idanunsa da Anwar yayi gado,Nafeesa tayi saurin sunkuyar dakai tana faɗin.

“Dady ayanzu gaskiya babu wanda muka dai dai ta dashi gaskiya.”

“To nabaki sati uku kacal cikin tarin samarin da akace kuna waya ki fitar da meson auranki ki turomin shi.Ke kuma Nailah Momy ta sanar min baki kula kowa ko?hakan yasamu yanke shawara akanki duk da cewa munyi laifi da muka zartar da hukunci ba tareda jin tabakinki ba,sai dai daga ni har Fateema mun tabbatar ba zaki watsa mana ƙasa a ido akan zaɓin da mukai miki ba.”

Dady yaƙare maganan idanunsa akan Nailah wacce tai ƙasa da kanta,zuciyanta na tsananin bugu sai dai azahiri bazaka taɓa gane halin data shigaba,har Dady yaƙare maganansa bata ɗago ta dubesa ba,daga Amal har Nafeesa suma idanunsu akanta yake.

“Nailah bakice komiba kodai kina da wanda kuka daidai tane aɓoye batareda mu munsani ba?”

Sai lokacin Nailah ta ɗago face taima Dady kallo ɗaya ta sake maida kanta ƙasa,ganin yadda shima idanunsa akanta yake,cikin dakiya da son ɓoye halin ruɗanin da zuciyanta ke ciki take faɗin.

“Babu Dady.”

“To masha Allah Nailah kiyi haƙury da zaɓin da mukai miki ba tareda jin tabakinki ba,Momy zata sanar dake ko waye shi,ku kuma Amal da Nafeesa ku tabbatas kun turomin waɗanda kuka tsaida,don inaso idan an daidaita komi a haɗa bikin gaba ɗaya ayi tareda na yayanku Anwar,ku tashi kuje Allah yai muku albarka.”

Kaman jira Nailah take Dady ya sallamesu dama tayi saurin miƙewa don barin falon,ta rasa meyasa nan da nan hankalinta yai masifan tashi,xuciyanta ke tsananin bugu tamkar xai faso kirjinta maganganun Dady ke mata amsa kuwwa,sun zaɓa mata miji,to waye wanda za’a haɗata dashi kuwa? tambayan daketa hautsina kwanyanta kenan har suka iso main parlor,
memakon Nailah ta tsaya saita wuce ɗakinsu direct ganin hakan dasu Amal sukayi yasa suma suka rufa mata baya,samunta sukai zaune bakin bed ta dafe kumatunta da hannuwanta biyu hawaye nabin face ɗinta.

“Nailah it’s owk please,kibar wannan kukan idan har don maganan da Dady yayi na cewa sun zaɓa miki mijine,to kisa ranki a inuwa kada ki cuci kanki idan kinada wanda kike so sanar dani maza yanzu inje in sanar da Momy nasan zasu janye maganan haɗaki da koma waye.”

Cewan Amal kenan cikeda tausayin Nailah ,Nafeesa ko ta kasa magana illah tausayin Nailah daya lulluɓe zuciyanta,tasan kome zai faru Nailah bazata taɓa iya sanar da iyayen goyansu zancen Sultan ba,ita kuma bazata so tayi mata katsalandan ba domin koda itace Dady ya sanar mata yayi mata miji to tabbas zata iya aje soyayyan kowa ta amshi zaɓinsu da hannu bibbiyu don tasan bazasu taɓa zaɓa musu abinda xai cutar da rayuwansu ba.
Nailah ce tayi saurin share hawayenta tana ƙirƙiro murmushi kafin ta dubi Amal wacce ta tsura mata ido tana faɗin.

“Ko kaɗan ya Amal ba ina kuka bane don Dady yace sunyi min miji,don nasan sun isa danine shiyasa kuma bazasu taɓa zaɓamin abinda zai cutar daniba,ina kukane na tausayin kaina da kuma wanda za’a haɗani dashi na rashin sanin cikakken asalina…..”

Kuka me sauti daya taho matane yasata kasa ƙarisa magananta,hakan yasa Amal zama tareda rungumota jikinta tana rarrashi da gaya mata kalamai masu daɗi da kwantar da hankali,har saida tayi nasaran tsaida kukan da Nailah takeyi,kafin ta fice tabar Nailan da Nafeesa aɗakin.
Kaman jira Nafeesa take Amal ta fita tayi saurin zama kusada Nailah ta buɗe baki zatayi magana Nailah tayi saurin ɗaga mata hannu tana faɗin.

“Kada kice komi Nafeesa nasan abinda zaki faɗi bai wuce kice meyasa bazan gabatar da Sultan amatsayin wanda zuciyata keso ba,sai dai ke kanki kinsan bazan taɓa iyayin hakan ba koda inama Sultan soyayyan dazan iya rasa raina akansa,sai dai na rasa ran nawa da in bijerawa zaɓin nagartattun mutanen da suka zamemin garkuwa kuma iyaye nagari,bazan taɓa iya watsa ƙasa a idanun mutanan da suka haska rayuwata da fitila mafi haske wajen bani nagartacciyar tarbiya da ilimi ba,zan amshi ko wani irin zaɓi sukaimin da hannu bibbiyu,sai dai abu ɗaya ke sani shiga ruɗu shine Allah yasa ba cikinsu ya Hussain bane domin,banaso a tauyesu a shiga hakkinsu wajen amsan mace irina da bata dace dasuba amatsayinsu na masu cikakken asali….”

A yanzu ma kukane ya hana Nailah ƙarisa magananta,ita kanta Nafeesa hawaye take na tausayin kansu itada Nailah,kuka sukeyi babu me lallashin wani acikinsu,har saida sukayi me isansu kafin suyi shiru kowannansu na sauke ajiyan azuciya,buɗe ƙofa da shigowan Momy ne yasa gaban Nailah yankewa ya faɗi,sai taji sam bataji daɗin yadda Momy tazo ta samesu ba,sam bataso su ɗauka cewa ta shiga damuwane don sunce sun mata zaɓin abokin rayuwa,zama Momy tayi kusada Nailah tana duban Nafeesa tareda bata umurnin ta fita ta basu waje zatayi magana da Nailah.

“Nailah maganan da Dady yai mukune ya saki shiga wannan halin?sanar dani damuwanki nayi miki alqawarin share hawayenki”

Cewan Momy tana me janyo Nailah ta rungume ajikinta,hakan yasa Nailah sakin ajiyan zuciya tana ji tamkar tana tungumene jikin uwa mahaifiya,cikin murya can ƙasa tayi saurin faɗin.
“Momy Allah banida wani damuwa,kuma ni badon maganan da Dady yayi yasani kuka ba,ina kukane wanda bana ji zan iya daina yinsa a tsayin rayuwata matuƙar bansan cikakken asalina ba.Momy duk wanda kuka zaɓa min wallahi na amsheshi koda ko Bilya driver ne.”

Yadda taƙare maganan cikin wani irin sauti me taɓa zuciyane,yasa Momy sake rungumeta da ƙarfi tausayin Nailan na sake ratsata,hannu takai tana shafa kanta kafin ta fara faɗin.

“Nailah matsayinki azuciyata da yadda nake jin ƙaunarki,shine yasa har wani tunani ya ɗarsu araina na yanke shawaran babu wanda ya dace ki aura face jinina da nake da iko akansa,nina yanke shawaran mu haɗa auranki da Anwar ya zama abokin rayuwanki,ina fatan hakan bazai zama laifi agareki ba,ba zaki gane hikiman da yasani yin hakanba Nailah sai nan gaba,ina so ki amshi zaɓin mu da hannu bibbiyu ki kuma yi haƙury da duk abinda zai biyo baya,nasani Anwar na nuna muku ƙyama musamman ke hakan dayake yasani zaɓansa ya zama abokin rayuwanki duk da ina da wasu yaran da zan iya nuna ikona akansu,Nailah kisa aranki ko bayan ba raina sai Anwar ya soki,kada zaɓinsa ya taɓa damunki kiyi addu’a kawai,maganan sanin cikakken asalinki kuwa ina so kisani komi yanada iyaka Nailah,duk abinda yayi farko zaiyi ƙarshe idan har da rabon zaki sadu da asalinki to Allah ya fimu sanin hanyan da hakan zai faru,sai dai inaso kisani akwai mutane da yawa da suka rayu kuma har suka koma ga mahaliccinsu basu san cikakken asalin suba,kuma hakan baisa sun fasa yin nagatacciyar rayuwan da Allah ya tsara musu ba,ayanzu kisa azuciyanki nida Dady mune asalinki kuma mune iyayenku keda Nafeesa,bana so ki sake kukan rashin asali Nailah,idan kinayi kina sani adamuwa har indinga zargin kaina da cewa nagaza daku ta wani fannin…”

Tunda Momy ta fara magana Nailah ke kuka me sauti,wani irin tashin hankali da ruɗani take ji tunda Momy ta furta kalman ya Anwar shine wanda suka zaɓa mata,ta daina gane komi,sai uban hawayen dake sake kwaranya mata,jijjigata da Momy tayi tana faɗin.

“Nailah! Nailah! kiyi magana please ki sanar dani ko kinada wanda kike so ne?”

Sai lokacin Nailah tayi saurin dawowa hayyacinta tana kai hannu don share hawayen da suka kasa tsayawa take faɗin .” Momy banida wani xaɓi sai abinda kuka zaɓamin,na kuma amshi ya Anwar amatsayin zaɓinku ina fata inkasance abin alfahari agareku dashi baki ɗaya,ki yafemin Momy bazan iya daina kukan rashin asaliba Momy, zuciyata kullum damuna da tunanin su waye iyayena da har suka zaɓi rayuwa ba tareda niba takeyi,sai dai nayi miki alqawarin zan cigaba dayi aɓoye….”

Taƙare maganan tana sake shigar da kanta kirjin momy har lokacin hawayen sun kasa tsayawa,tausayin Nailah na sake ratsa ilahirin jini da tsokan Momy,soyayyan da takeji akan Nailah tayi imanin daga Allah ne domin bazata iya misalta yadda take jin ƙaunar yarinyar aranta ba,hakan yasa take tsananin burin haɗa jini da ita koda ace har abada ba za’a taɓa gane asalin Nailan ba,bare tana ji ajikinta Nailah ba shegiya bace kaman yadda takaddan da aka sameta dashi ya nuna.kai koma shegiyan ce da aka haifa babu aure tana sonta ahaka kuma zata haɗa zuri’a da ita domin duk wanda ya tsinci kansa amatsayin shege mara galihu bayin kansu bane yin Allah ne,sosai ta dinga kwantarwa da Nailah hankali kafin tabar ɗakin tana ji aranta indai tana raye bazata taɓa zuba ido Nailah ta wulaƙanta a hannun Anwar ba…✍

NAILAH is for sale for just 300, ga masu sha’awan siya saiku tura 300 ta wannan account ɗin 0504192664 Aisha Ibrahim Ɗansabo GTbank,shaidan biyan ku tanan line ɗin 08167768704.

Esha Ɗansabo ce✍

DOMIN KARANTA CI GABA DANNA 

https://arewabooks.com/book?id=62a4973c772e179ad6e577b4

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *