Cikin so da ƙaunar ta yace.
“Uwata tafi ta kowa waye ya taɓaki?”
Ya kamo hannunta yana saka ɗayan hannun sa yana goge mata hawayen dake zubo mata.
Wata kalar harara ta zuba mai ta fincike hannunta tayi gaba.
Sadiya ce take binta abaya tana mata faɗa kamar haka.
“Haba ummi ubanmu ne fa duk abin da ze mana bazamu biyasa haihuwar dayayi mana ba”
Da tarin takaici ta juyo gaban sadiya tace.
“Seki gaya min tunda aka haife mu abin da yata ɓa tsinana mana in ban da ma neman kashe mana uwa daya keyi wallahi kinji na rantse duk ranar danai kuɗi sena ɗauke uwata daga wannan baƙin gidan”
Tafaɗa a tunzure tare da fisgar hannun ihsan sukai gaba.
Dama mai haƙuri idan ya tashi bai da daɗin kai.
Itama hassana shirin fita aiki tai amman can ƙasan zuciyarta tana addu’ar Allah ya sassauta zuciyar ƴar ta akan ubanta.
Abin mamaki koda ta fito zata tafi yau malam yana zaune akan bancin mai rake daya ganta bai mata wannan kallon tsanar ba sema tashi dayayi yana cewa.
“Ƴan biyu kyautar Allah tawa uwar sadiya da kausar”
Ya kuma riƙo mata ledar kayanta ya sakata agaba se surutai yake na rashin kan gado.
Aranta kuma mamaki take lallai mutuwar zuciya masifa ce seta mayar da mutum mahaukacin ƙarfi da yaji.
Seda ya kaita har bakin layin sannan ya koma.
Aikam zata shiga layin ta hango talatu suka gaisa sosai.
“Wa nake hangoki dashi ɗazu kamar babansu?”
Cewar talatu cikin barkwanci
“I wallahi shine ya rakoni”
Hassana ta bawa talatu amsa kai tsaye
Wata shegiyar dariya talatu ta sanya tare da cewa.
“Iko se lillahi wato shidai malam habu ya zama ƙadangare mai bin ledar manja oh”
Tafaɗa tare da kuma cewa hassana.
“Toni na wuce mu wuni lafiya”
Tsaf hassana ta gane magana ta gasawa malam habu amman seta danne sabida bahaushe yace tsuntsun daya ja ruwa shi ruwan kan doka!
Itama gidan aikin nata ta wuce yau ma wai yaran gidan zasuyi partyn gama makaranta.
Tunda taje take tilar aikin kaji waɗanda suyar su zatai bayan ta kammala.
Ba ita ta sami kanta ba se magariba tayi sallah ta haɗa karonta tayo gida da uban nama don kai da ƙafa ma seda ta ciko wata baƙar ƙatuwar leda.
A bin mamaki malam yana waje yana ta sintiri aiko daya hangota ya wani saki ƙayataccen murmushi tare da amso ledar hannunta suka shiga gida atare.
Ɓuɗa hadiza ta sanya tana cewa.
“Oh ni dije ALLAH wadaron naka ya lalace wai mazan zamani nakasassun maza”!
Babu wanda ya kulata haka malam ya raka hassana har ɗakinta wanda ummul ta biyoshi da harara!
Ƙaton kwano hassana ta ɗauka ta zuba mai jallof ɗin taliyar data yo tare da soyayyan naman ta bawa kausar tace akai masa.
Dan tura haushi agaban hadiza ya amsa ya zauna ya buɗe yana ci yana dariya yana yada magana ita namiji mai zaman banza.
Jimm kaɗan ihsan ta fito hannunta ɗauke da wani kwanon ta mikowa basira tace mata.
“Yaya wai gashi inji bamu”
Basira tasaka hannu zata karɓa hadiza ta tungure kwanon ya faɗi abincin ya zube ƙasa.
“Dan ubanki ku mayu ne? me zaki da abincin da baki san daga inda ya fito ba?”
Hadiza ta faɗa da ƙarfi yadda bamu zata ji.
Cikin sauri bamu tacewa ummul taje ta kirawo ihsan buɗar bakin ummul tace.
” Bamu kullum inna ga umma fa dariya take min kuma taita kallona shine na gayawa hajja se hajja tace na dena zuwa wajanta karta cinye ni da baki da idanun ta”
Tafaɗa kamar zatai kuka!
“Kul karki kuma faɗar haka ummi kinji kita lahau’la insha Allah bata isa tai miki komai ba”
Sadiya tasa taje ta kirawo ihsan.
Shiko malam habu wata dariya ya saka tare da tattare naman da hadiza ta zubar ya ƙara akan nashi tare da cewa.
“Hassada cinikin matsiyaci”
Yayi ɗakinsa da ƙarfi hadiza ta ɗaga murya tace.
“Mutuwar zuciya masifar jiki”
Ta faɗa cikin takaici tayi ɗakinta.
A wannan daran ma seda malam habu ya buƙaci hassana.
***********
Kwanci tashi asarar mai rai yanzu haka hassana takai kusan shekaru huɗu agidan aikinta tama shiga ta biyar kuma sosai take samun canji ackin rayuwarta data yaranta waɗanda suka murje sukai.kyau nan da nan masassaƙin budurci ya soma bayyana a jikin ummul dama abinka da kyakykyawa har maza sun fara biyota da kuka take ƙarasowa gida lokacin suna jss3 ita da sadiya kausar jss 1 ihsan aji shidda.
Ta ɓangaren islamiyya kuwa tuni sunyi wajan izif 30 suna bada hadda sosai rayuwarsu ta canja sanadin aikin hassana wanda hatta malam shima yana cin arzikin aikin sedai duk ranar da ƴan cin mutuncin suka motsa tofa seya taɓa
Sam hassana bata kula shi sabida bata ma yinin gidan kusan kullum tana gidan aikinta.
Kuma ko can gidan aikin nata ma aikin gabanta takeyi ta iya da kanta sabida ta fuskanci mutan gidan suna jin kai da kuɗinsu sun ɗauki talaka banxa wofi rayuwarsu data yaransu kaɗai suka sani jin daɗinta ma wannan mima da yayanta Samir sun tafi london karatu se anyi hutu suke dawowa wani bin ma basa dawowa hutun dama kuma duk ciki sunfi bata matsala.
Sauran yaran basu kaisu girma ba da alamu sune manya agidan kuma su iyayensu suka fiso sannan uwa uba sam basa ganin mutuncin kowa hatta mahaifansu basu isa dasu ba.
Dama ƙiri ƙiri hajiya timo tace mata su sunɗauki talakane kawai wahalalle mai aiki da gaɓarsa abiya shi dan haka karta yadda ta ɓatawa ƴaƴan su rai don akan ƴaƴansu zasu iya komai wannan tasa hassana take kama kanta sosai babu ruwanta da kowa.
Acikin gidan iyaka cinta aikin ta ta kammala tayo gida abinta tana saka rai da cewar komai na Allah ne kuma bawa baya yanke tsammanin rahma daga ubangijin sa.