BA SONTA BAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 30

Sanye yake da ɗanyar dark blue ɗin shadda wadda tai masa masifar kyau bana wasa ba hannunsa ɗauke da manyan ledoji masu tambari,ajikinsu tafiya yake cike da jarumta bakinsa yaƙi rufuwa sabida tsabar farin cikin samun muradin zuciyar shi (tsohon littafina kenan muradin zuciya ) haka ya nufi cikin ƙayataccen falon gidan sa bakinsa ɗauke da sallama wadda Basmah ta amsa masa ita idanunta kafe akansa tana wani lumshe su zuciyarta na bugawa da tsananin shauƙin soyayyarshi.

A hankali ya zube ledojin hannunsa ya ƙarasa wajanta ya tsugunna tare da sanya hannu ya kamo tattausan hannunta yana matsewa ahankali ya zauna agefen ta.
“Amarya bakya laifi kokin kashe ɗan masu gida Allah ya zaunar damu lafiya ya bamu zuri’a ɗayyiba ni kin san ina matiƙar son yara sabida familyn mu muna da yawa ƴaƴan ammi mune kaɗai ƴan kaɗan shiyasa nake son naga jikokinsu sunfi na kowa yawa”
Murmushi ta sauke a kunya ce batare data ce komai ba.
Jan ta yayi jikinshi ƙamshin sihirtaccen turaren ta na manta uwa ya ƙara dukan hancin sa.
Jikinsa har rawa yake wajan tarairayota sosai ya miƙar da ita suka nufi bedroom ɗinsa.
Zaunar da ita yayi a gefen katafaren gadon shi na alfarma, Ya cire mata gyalenta sannan ya juya zuwa falo ya tattare ledojin yakai kicin ya fito da yoghurt ɗin da gashashshiyar kazar ya juye a plate tare da ɗaukar cup ya fita seda ya sauya kaya zuwa na shan iska sannan ya taimaka mata ta cire nata da kansa ya dinga bata kazar da yoghurt ɗin tana ci harta ƙoshi sannan shima yaci nasa.

Bayan sun kammala ya saɓeta a kafaɗa kasancewar ta ƴar firit ya nufi bethroom da ita wanka ya haɗesu sukai ya naɗosu a tawul suka fito sukai sallar nafila.
Wasannin soyayyah irin na ma’aurata shiya biyo baya kafin Aliyu ya fara more sadakin sa, Sosai suka baje kolin soyayya a wannan dare kuma ba laifi basmah tai kokarin kawo budurcinta zuwa ɗakin mijinta wanda hakan shiya ƙara mata ƙima a wajan Aliyu washe gari haka taita masa langwai wanda shikuma ya lalace a wajanta bai fargaba har ɗayan rana tayi.
Seda wasu ƙawayenta suka zo sannan ya samu ya zare jikinsa ya shirya ya nufi gidan su.

Abin mamaki ba kowa a falon se yayarsa mai shirin tafiya anjima tare da sarat matar baba karami zubewa yayi yana gaisar da ammi kannensa kuma na gaishe shi
Shafa kanshi yayi tare da cewa.
“Ammi ina matan su kawu kar dai sun wuce?”
Murmushi ammi ta sauke tare da cewa.
“Tun safe nake kiran ka baka ɗauka ba kowa ya wuce hajjah ma ɗazu aka kaita tasha yanzu wannan ƴar zata wuce ita da saratu”
Tafaɗa cikin ƙunar rai.
Kunya ce ta kamashi yama rasa me ze faɗa musu seya hau borin kunyar cewa.
“Anty jidda kuzo muje ku ƙara ganin gidan please kafin ku wuce”
Yafaɗa yana wa mufid ɗan sarat ƙanwar sa wasa.
Hakan ce ta kasance domin gaba ɗayan su suka shirya domin zuwa gidansa anty jidda harda ƴar humurarta wadda tace zata bawa amarya ammi kuma miyar kaji tacewa hassana ta ɗauko su tafar mata da ita haka ya zuba su a motarsa suka tafi dayake gidan nashi akwai ta zarar tsiran layuka biyar dasu ammi.

Waya ake masa dan haka seya ce musu su shiga gashi nan zuwa.

Tunda suka buɗe ƙofar falon sukejin shewa na tashi ga abinci nan a falo kaca kaca alamar anci an bari ne ga lemuka da ruwa kota ina, ga ƙashin kaji birjik.
T’v na faman yi ita kaɗai.
Har suka zauna bata fito ba seda hussaina taɗan doki ƙofar bedroom ɗin sannan sukaga wata taɗan leƙo A wani irin yamutse tace.
“Ku suwa ye?”
Cewar wadda ta leƙo ɗin wadda alama take nuna ƙawar tace.
“Kice mata yayin mijinta ne”
Cewar Anty jidda wadda taji jikinta yayi sanyi.
Taɓe baki tayi kana ta koma.
Cigaba sukai da shewarsu kusan minti goma bata da niyyar fitowa.
Se can ta fito.
Sanye da wasu ɗamammun riga da wando, Siririyace babu ko sharp ƙafafun nan duk sunyi kurumbin alamun shafa mai gefe baƙi gefe fari fuskarta kwa jajir duk tai glass na shafa mai bakinta baƙine ƙirin kamar mai shan taba wanda tsabar shafa mai ne ya mayar dashi haka.
Danne dariya hassana take amman seda ta fito dan haka aguje tai waje har Tana faɗuwa tana furta ina yaya ya samo ƴar daba mai baƙin baki.

Ko kaɗan bata da alamar gaishe su atsaye ta tsaya cak tana wani taɓe bakinta rannan nata ahaɗe murtuk.
“Ina yini amarya yaya baƙunta?”
Cewar Anty jidda tana murmushi.
“Lafiya baƙunta kuma nida gidana ai babu ita”
Ran sarat ne ya ɓaci wadda take bin Aliyu daman ita bata da wasa kamar shi take cikin zafi ta yunƙuro zatai magana shafa’atu ta riƙe mata hannu tana girgiza mata kanta.
Cikin haka suka jiyo muryarsa yana tambayar hassana mai take a waje.
Sum sum hassana ta shigo tana sunkuyar da kanta.
Bayyanar sa a falon basmah ta wani tafi da sauri ta rungumeshi tana shafa gemunsa tana wata narkewa ajikinsa.
“My love wai ashe su hassana ne suka zo amman baka gayan ba”
Tafaɗa da tsansar kirsa.
A hankali ya zareta a jikinsa tare da riƙo hannunta suka ƙaraso wajan su anty jidda suka zauna a kujerar dake kallonsu.
“Bara na kawo muku ruwa ƴan uwana tsananin murnar ganin ku ta hanani kataɓus”
Tafaɗa da kirsa tana murmushin shu’umanci.
Da har shafa zatai magana Anty jidda tai mata sigina da ido.
Dariya anty jidda ta saki tare da cewa.
“Ai sosai muka yaba ɗan uwa ka iya zaɓen mata, akwai tarbiya da kirki”
Cak basmah ta tsaya dan ta ɗauka wata acikin su zata gaya mata magana ne tai mata sharri seta ga akasin hakan ba laka ta ɗauko musu lemon ta riƙo tana kokarin ajewa ta ɗauko ruwa hassana tace.
“Ai anty basmah da baki gaggawar wahalar mana da kanki ba muda gidan yayanmu madadin abbanmu ai base an ɗauko mana lemo ba muma masu bawa wasu ne”
Tafaɗa tana dariya sarai magana ta gasa mata.
Haka suka zauna suna ta hirarsu a junansu suna dariya har lokacin tafiyarsu yayi suka bata sakon ammi tare dana anty jidda ya kuma kwasosu a mota suka yo gida.

Dare yayi dole su anty jidda suka ƙara kwana agidan.
Adaren kusan kwanan zaune sukai suna bawa ammi labarin basmah ƴar daba cewar su hassana.
Washe gari su anty jidda suka wuce.

A hankali rayuwa ke tafiya kullum basmah na ƙara fito da sabbin halinta na ƙin dangin Aliyu wanda shi sam bai gane ba sabida yadda yaga tana rawar jiki akansu idan sunzo tun suna zuwan ma suka dawo suka dena zuwa rayuwa na tafiya shekarun auren su naja basmah ko ɓatan wata bata taɓayi ba bare asaka ran samun ciki kullum sune wannan asibiti sune wancan ga basmah da ɗan banzan kishin tsiya.
Tana bala’in son Aliyu bata haɗa son shi dana kowa ba akansa zata iya yin komai.
Aikin bankinta take yi kullum zata fita office bata damu data masa abinci ba sedai su saya a wajan saidawa, shima kuma bai takura mata akan setayi ba sabida yana zuwa gidan ammi yaci wanda tun tana bashi harta dawo ta dena sedai yaje a sace ya ɗiba ya ci ya gudu gidansa.
A hankali ma yaso ma fashin zuwa gidan ammi ɗin sedai inya tashi a office ya biya wani wajan yaɗan tsakuri abincin yayo gida kamar wanda aka ɗaukewa hankali cak ya dena zuwa gidan ammi.
A taiƙaice seyayi wata biyu bai leƙa ba sedai in abba ko ammi nason ganinsa su mai waya idan yazo ma kamar baƙo haka ze tsaya yana raɓe raɓe wannan hali daya faɗa ya damu kowa agidan abba har kwanciya yayi asibiti amman Aliyu baije duba shi ba sesu baba karamine sukai masa jinya wannan al’amari ya dami kowa addu’a ake babu ji babu gani sabida kowa a dangi yasan Aliyu mai zumunci ne sedai hatsabibiyar mace da Allah ya bashi.
Dama ita basmah ba zuwa shagalin danginsa take ba ko gidan ammi zuwan ta biyu a tsayin shekarun nan haka nan haihuwar su sarat babu ko barka yayi faɗan yayi faɗan taƙi zuwa seda taga ya ɗauke mata wuta sannan ta kira sarat a waya sabida duk abinta tana shakkar sa dan in ƴan miskilancin suka motsa seyay kwana biyu bai kula taba.
Shiya rasa mai yasa duk wani abun ahalinsa seya na mantawa inyay nufin ya tuna seya dinga jin ciwon kai.
Ta ɓangaran maman basma kuwa tuni Aliyu ya rushe mata gidan data ke ciki an gyara shi an ɗaukar mata mai gadi da draver da masu aiki sosai take fanta mawa shiyasa duk sabon malamin daya fito seta je domin ƙara rikita Aliyu.
Addu’a bata faɗuwa ƙasa banza A hankali addu’ar ƴan uwa mahaifa jama’a ke tasiri akan Aliyu a wannan shekarar wadda suke da shekaru biyar da aure cif ya soma jin canji a jikinsa ya soma jin kewar mahaifan sa sannan ya fara tilawar alkur’ani mai girma azkar baya wuceshi.
Hakan yasa ya soma jinsa kamar wanda ake saukewa wasu manyan duwatsu a kansa.
Adai dai wannan lokaci tafiya ta kamashi kano domin gudanar da wata shari’a abin mamaki koda ze tafi seda yaje yayiwa maman basmah sallama harya bata kuɗi amman seya ji ya kasa zuwa wajan mahaifansa haka ya tarkato ya taho kano.
Yawan addu’a daya ke seyaji yana kewar su ammi sosai har yaji some times yana jin haushin basmah sannan kuma wayar da ammi tai masa akan yaje gidan hajja da rashin jin dadinta na yadda ze yi tafiya bai gaya musu ba nan ma seyaji ciwon abin da yayi musun.
Haɗuwa da wannan yarinyar a hotel da gidan hajja seya ke saka shi cikin nishaɗi da farin ciki yana jin kamar yana farkawa ne daga wani dogon mafarkin daya faɗa.
To koyaya wannan lamari ze tafi muje zuwa.
Kundai ji halin da Aliyu yake ciki……

Sannan kun san wacece Ummul wanene Aliyu?

DAWOWA LABARI

Babu abin da yake tashi se sautin bugun zuciyoyin su sannu a hankali kukan da ummul keyi ya soma raguwa.
Wata irin nutsuwa taji ta shigeta.
A hankali ya zareta daga jikinsa yaɗan matsa baya kaɗan ya harɗe hannunsa a saman kirjinsa yana aika mata da wani irin kallo mai tarin ma’anoni.
Da sauri tayi ƙasa da kanta tana wasa da yatsun hannunta wata irin mahaukaciyar soyayyar sa na ƙara jefata cikin wani irin yanayi.

Da wani irin salo kwantacciyar muryarsa mai cike da tarin nutsuwa ta doki cikin kunnuwan ta.
“Ummi ni kike gaggayawa waɗannan maganganun? a haka zamuyi auren?”
Yafaɗa tare da tsira mata kaifafan idanunsa.
Jikinta ne ya ɗauki rawa ahankali take ja da baya tana share hawayen ta kafin daga bisani ta juya aguje tayi cikin fallon hajja.

Murmushi yayi tare da fita wajen motar shi ya shiga tare da nufar hotel ɗin daya sauka ya soma tattare kayan shi wajan ƙarfe ukun rana yabar kano ya nufi abuja.

Tunda ta shiga ɗakin hajja take kuka tun hajja na tambayarta har tayi mata banza sabida ta gaji da yadda take mata magana tana shareta.
Bata yunƙura ta tashi ba se wajan ƙarfe biyun rana alwala ta ɗauro ta tayar da sallar azahar bayan ta idar ta miƙe zuwa kicin ta zubo abinci ta soma ci har akai la’asar tana zaune a falo duk abin duniya ya taru yayi mata zafi.

Ƙarfe biyar na yamma Ameerah ta shigo gidan hajja lokacin ummul ta idar da azkar tana zaune tana kallon arewa24 sallamar ameerah tasa taɗan saki ranta.
Wajan zama ta bawa ameerah tare da tashi ta nufi kicin ta kawo mata ruwa, Bayan ameerah taɗan kurɓi ruwan kaɗan ta aje tare da kallon ummul a nitse tace.
“Ƙanwata yaya jikin naki?”
Da murmushi a saman fuskarta tace mata.
“Naji sauƙi Alhamdulillahi yaya gidan namu yaya ake ciki?”
Duk ta jera mata tambayoyin.
“Lafiya lau amman de zaki zo mu koma ko kinsan da ƙyar nake iya bacci sabida sabon da mukai ga BB ya uzzira min kullum zancen ki yake ga wayarki har yau swich off”
Lumshe idanu ummul tayi har yau wayar tana wajan Aliyu bata sani ba koma yabarta a wannan hotel ɗin.
Kafin tace wa Ameerah.
“Nima ina son komowa jira nake har na ƙara warware wa, Amman naji hajja tana wai bazan sake tafiya nabar gida ba”
Tafaɗa muryarta tana ɗan rawa kaɗan.
“I to hakane nima dai banga amfanin komowar kiba ummul, maganar gaskiya idan har kina ganin zaman ki anan babu takura kiyi zaman ki sabida rayuwar zaman gidan karuwai bata kamaci yarinya mai hankali kamar kiba, abu nagaba babu namiji mai hankali daze ganki anan yaso auren ki sedai tsananin rabo”!
Ameerah ta faɗawa ummul haka tare da iyakacin gaskiyar ta.

Zazzafan hawaye ne ya zubowa ummul tunawa da cin zarafin da babanta yayi mata wanda ko ƙaunar ganinsa batayi kuma tasan muddin ta cigaba da zama anan tabbas zasu haɗu dashi wanda ita sam a tsarin ta babu wannan se abu, Nagaba Aliyu tana son ta tafi tai nesa dashi ko Allah ze taimake ta soyayyar shi ta bar ruhinta.
“Sedai idan na komo bazaki karɓe niba amman dai ina da tabbacin dawowa wajan ki da zarar na ƙara jin sauƙi”
Tafaɗa tana mai kallon ameera wadda take danna wayar ta.
“Ummul kenan kina bani mamaki wallahi wani bin akwai ki da taurin kai tsakani da Allah, meye aibun wannan gidan koni inda ina da irin gatanki da babu ni babu komawa wancan gidan”
Tabbas maganar ameerah gaskiya ce a wajan sedai bata ɗauketa ba sabida ƙudirin dake ranta, Har akai magariba ameerah na gidan hajja se wajan ƙarfe bakwai sukai sallama har bakin mota ummul ta raka ameerah kana ta juyo domin tana sauri ta koma wajan hajja dan taga ko lafiya tun yamma tana ɗaki bata fito ba.

“Wana ke gani kamar uwata ke ummi”
Taji saukar muryar babanta gabanta ne yayi mummunan faɗuwa..
Amman seta dake batare data nuna komai ba ta nufi buɗe gate wanda tun kafin ta buɗe gate ɗin ya ƙaraso gabanta.
“Uwata ina miki magana kina jina meya kawo ki unguwar nan?”
Saukar maganar babanta cikin kunnenta.
“Baba ba gidan ka nazo ba unguwar nazo iya gidanka kake da hurumin samin doka”!
Tafaɗi a dake.
Kallonta yayi daga sama har ƙasa tsananin ƙaunarta yana sukar ranshi tsabar dana sani sun cika masa zuciya na korar dayayi mata domin dai abin da yake gudu ya faru sabida gori kala kala babu wanda bai shaba haɗi da dariyar mutan gari hatta basira data sami miji seda aka kore shi da baki akace masa ai ubanta cima zaune ne akan haka yarsa tai ciki tabar gida kujifa sharri ire iren hakan yasa yaji yana nadamar korar ummul daga gabansa daya sani yayi imani da ƙaddarar ƴar tashi.
“uwata ni babanki kike gayawa wannan maganganun?”
Yafaɗa mata muryar shi a sanyaye.
Wani haushin sane ya kamata tana jin inta cigaba da tsaiwa zata gaya masa wadda tafi wannan sabida haka setai saurin buɗe gate ɗin ta shige jikinta har rawa yake sabida ɓacin rai tana jin inta cigaba da zama kusa dashi komai na ɓacin rai na iya faruwa mahaifinta ne amman sam ta tsane shi sabida halaiyar sa marasa kyau!

Ido rufe take neman ƴar jakarta dan bata jin zata kuma kwana gidan hajja.
Bata ganta a falo ba dan haka ta shige bedroom ɗin hajja tana nemanta.

Zaune ta tarar da hajja a saman sallaya alamun sun nuna sallah ta idar hannunta riƙe da waya tana murmushi tana cewa.
“Kai baffa yanzu ka sauka fa amman baka da saurin tuƙi”
Muryar ummul ce ta katse mata sauran maganar wadda take cewa.
“Hajja ina jakata ni zan koma inda na fito se an kwana biyu na warke”
Haɗe rai hajja tai tamkar bata taɓa dariya ba ta dube ta.
“Ummi idan har na isa dake karki yarda kibar gidan nan waike wace irin yarinya ce kamar ibilishiya bakya jin magana”
Hajja ta faɗa tana zabga mata harara!
Dira ƙafafu take a ƙasa tana zubo da hawaye tare da cewa.
“Ina fita naga baba hajja bana son in dinga ganin sa”
Salati hajja ta soma tana tafa hannu sam ta mance da wayar data keyi seda taji muryar shi ta cikin wayar yana cewa.
“Hajja bani ita”
Da sauri ta miƙa mata wayar tana cewa.
“Karɓi baffa na maki magana zakarar banza”
Tana miƙa mata wayar ta miƙe tare da ficewa daga falon.
Bata da niyyar masa magana se saukar shashsheƙar kukan ta dake tashi ta cikin wayar zuwa kunnen sa.
“Ke kurma ce?”
Taji saukar muryar shi wadda take nuni da yana cikin tsananin gajiya.
Turo baki tai gaba ta danna shi……………