Ba SONTA NAKE BA CHAPTER 11

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 11

AL-HUSSAIN MANSION+ Ana gobe za’a fara biki daddare Mamy ta kira Zara dakin ta. A lokacin kuwa gidan ya cika da baqi harda dangin Mamy na Egypt. Dangin mahaifiyar Zara ma duk sun zo. Granny kuwa tun ana sati daya ta iso. Zara tana kwance akan cinyar Mamy a bisa gadon Mamy yayinda take shafa kanta ne tace “Princess Ina so ki saurare ni da kyau ki ji abinda zan fada miki” Zara tace “I am all ears Mamyna” Mamy tace “kin dai san aure ba wasa bane, dukda dai dan uwanki zaki aura wanda kun san halin juna sossai you need to take it seriously” Zara ta dan turo baki a ranta tace “wai su basu san ma duka wata daya zamuyi tare ba?”2 Ji tayi Mamy tace “ina so idan kin je gidan Farouq ki tabbatar duk wani abinda zai ci ke kika yi shi, wannan zai sa ya so ki fiye da yadda ba kya zato” Zara tayi murmushi a ranta tace “laaaa, Mamy ta dauka sona yake wai?” Mamy tace “sannan ki dinga qoqari kina gyara mishi sashen shi, kar ki ba masu aiki access, na san akwai wahala but just try kin ji?” Zara tace “toh Mamy” Mamy ta cigaba da fadin “duk abinda yake so kiyi mishi, na tabbatar Farouq will take care of you very well, you will be more happy with him than with us here” Zara ta rungume Mamy tace “I doubt Mamy” Mamy tayi dariya tace “zaki bani labari ai” Haka dai Mamy ta cigaba da ba Zara shawarwari akan yadda zata zauna gidan Farouq wanda a qarshe kuma Zaran ta fashe mata da kuka ta koma lallashi. *************** A yau ranar Qunshin Zara wanda idan an gama ne za’a yi Fulani day a nan harabar gidan. Mutane ne cike da gidan yayinda team din Henna temple suke ta zirara lalle. Tuni anyi ma su Saima da ‘Yan biyu nasu. Hafsat tana zaune ana yi mata nata ne Zara ta zauna gaban Henna temple. Za’a fara yi mata kenan Granny ta zauna tace “ni zaki fara yi ma” Gaba daya aka fashe da dariya yayinda Zara ta turo baki tace “wallahi Granny baki isa ba” Granny tace “wacece matar mijin naki ta farko?” Hafsat tana dariya tace “ke ce Granny” Zara ta turo baki tana ta fushi. Granny tace “toh meye ma kike ta wani kumbure kumbure bayan nasan ma ba son lalle kike yi ba?” Hafsat ta zaro idanuwa tace “tab, ai Granny yanzu bala’in so take yi. Kin san tun lokacin da Ya Farouq yace mata yana so..” Zara ta harari Hafsat ta miqe tace “ni na ma fasa yin lallen” Muryar Granny ta ji tana fadin “aikin banza, ashe ma qwatar mijin daga hannun ki bazai yi wahala ba” STORY CONTINUES BELOW Zara zata tafi ne Anty ta riqo hannun ta tace “zo nan Princess, qyale granny, kishi take yi saboda zaki aure mata miji” Haka dai Anty ta lallashi Zara ta dawo yayinda ake ta yi mata dariya. Bayan an gama kuwa aka dinga yaba kyan da lallen Zara yayi, ita kanta ta san yayi kyau. Henna temple dai ta qware a aikin ta sossai. Hafsat ce ta ziga ta akan ta tura ma Farouq hoton lallen amma ta qi. Suna cikin hakan ne kuwa ta ga message din Farouq din ya shigo wayarta kamar haka: “Hey beautiful, na dai san an gama by now. A turo mun hoto mana in gani” Murmushi tayi ta tura mishi da reply kamar haka: “Sorry handsome, babu picture” Ko ajiye wayar bata yi ba ya turo mata da wani saqon kamar haka: “please mana, am I not entitled to see?” Hafsat wadda take zaune daf da ita tace “haba babes, ki tura mishi mana” Zara ta ajiye wayar tare da fadin “babu fa abinda zaiyi da shi, kin kuwa san Ya Farouq ya dauki komai na bikin nan kamar joke? Its like he is enjoying everything that’s happening” Hafsat tace “toh ke aren’t you?” Kafin tayi Magana ne kiran Farouq din ya shigo. Ko da ta amsa ji tayi yace “please beautiful” tana murmushi tace “Sorry Ya Farouq yau babu hoto, i am serious” Farouq wanda ya ji haushi yace “ina nan ina jira, idan baki turo ba I am not gonna attend any of the events” Bai jira tayi magana ba ya kashe wayar. Zara ta dan ji wani iri amma kuma sai ta matse ta qi tura mishi still. Farouq kuwa bai yi tunanin cewa bazata aiko mishi ba, wasa wasa dai tun yana sa rai har ya haqura. **************** Da yamma ne aka fara Fulani day a nan gidan Mamy. Jide of Stola ne yayi ma Zara kwalliya wanda babu yadda Granny da Mamy basu yi akan ta kira mace tayi mata ba amma ta qi, dayake dai dama lallaba ta ake yi sai suka haqura suka qyale ta. Aikuwa dai kwalliyar ta yi kyau, Zara tayi kyau babu qarya. Granny ce tace “ikon Allah, namiji da suna Hajara. Shi yanzu sana’ar da yasa a gaba kenan?” Zara tana dariya tace “ko ya zo yayi miki ne kema?” Granny tace “Allah ya tsare ni” yayinda aka cigaba da dariya. Zara dai kayan da ta sanya shahararriyar designer dinnan Hudayya ita ta dinka mata. Dukda kuwa dinkin simple ne amma tayi kyau sossai. Qawayen ta ma ankon kayan fulani suka yi. Sunyi kyau gwanin ban sha’awa. 14 STORY CONTINUES BELOW Aikuwa anyi shagali sossai, Zara da qawayenta sunyi rawa sossai yayinda BigH yayi ta kashe hotuna, kowa ka gani cikon farin ciki yake. Sai gab da magrib ne aka watse. Bayan Sallan isha’i ne Farouq ya shigo gidan wanda tunda ya shiga ake ta tsokanar shi. A lokacin da ya shiga gidan kuwa Zara da qawayenta suna sashen ta. Sashen Granny dinshi ya nufa domin kuwa shi dama duk lokacin da ta zo idan dai kana neman shi toh fa sashen ta zaka gan shi. Farouq yana kwance a kan cinyar granny suna hira kamar kullum ne Mamy tare da Anty suka shigo. Bayan sun gaisa ne Mamy take tambayar shi “ya su Ruqayya?” Shiru ya dan yi sannan yace “Mamy tana gidansu fa tun last week” Cikin mamaki Mamy tace “what?” Anty ce tace “sakin ta kayi ko me?” murmushi yayi yace “ko kadan Anty” A nan dai ya basu labarin yadda aka yi wanda kuwa suka hau shi da fada akan qin dawo da ita da yayi. Akan dole kuwa yayi musu alqawarin zai dawo da ita kafin ranar daurin auren shi. Daga nan kuma duk suka sauko yayinda suka cigaba da hira. Farouq yace “wai ina kuka boye mun amarya ta ne? ni fa ita na zo gani” Granny ta riqe baki tace “lallai ma baka da kunya” Su Mamy suna ta dariya ne Zara ta shigo a guje, bata kula da Farouq ba har sai da ta qaraso daf da shi sannan na ga ta tsaya cak. Tashi yayi zaune yana kallon ta yayinda su Granny suke ta kallon ikon Allah. Gani nayi ta juya zata fita sai ya riqo hannun ta da sauri yace “ai baki isa ba sai na gani” Zara wadda take ta qoqarin qwacewa tace “Ya Farouq please” Granny ce ta Harare ta tace “ka ji gulma, kamar dama ba shi kika biyo ba” Farouq yana dariya yayinda yake ta qare ma lallen ta kallo. Ji suka yi yace “beautiful, I love this” yayinda ya fiddo wayar shi ya dinga snapping din lallen. Bayan ya gama ne ya saki hannun ta yace “toh princess din Farouq I am done” cikin mamaki ta kalle shi yayinda ya koma ya kwanta a kan cinyar Granny. Zara tana nan tsaye ta ji yace “Wai Mamy me kuke ba Zara ne na ga duk ta canza ta zama kamar baturiya?” Mamy ce ta jefe shi da pillow tace “yanzu zaka tashi ka bar mun gida don na kula rashin kunyar naka ya fi qarfi na” Granny ce ta shafa kanshi tare da fadin “haba Mamy kiyi mishi haquri, kin ga fa ko ya koma gida babu mata tunda tayi yaji” Ji suka yi Zara tace “what?? Dagaske??” Gaba dayan su suka mayar da kallon su kanta yayinda ta wayance tace “uhm sorry” ta ruga da gudu ta fita. Su Mamy kuwa me zasuyi banda dariya. Anty ce ta miqe ta bi bayan Zara tana fadin “baiwar Allah bari in je in ji abinda take so”. **************** BLUE VELVET MARQUEE A Blue Velvet Marquee aka yi bikin Kamun Zara. Mutane ne damfam a wurin, Kowa ka gani yayi shiga ta alfarma. Amarya Zara tare da qawayenta suka shigo cikin birgewa. MC kuwa sai ziga ta yake yi. Zara dai tayi kyau har ta gaji. Ba zancen wasa ba jide ya iya kwalliya sossai, simple make up yayi ma Zara kamar dai yadda take so amma kuma classy one. STORY CONTINUES BELOW Kayan da ta sanya Galiafahad ne ya dinka. Red gown ne wanda ya bi jikinta har qasa. Kayan kuwa sunyi fitting dinta sossai. A taqaice dai Zara is looking simple but elegant. 9 Qawayen ta sunyi anko gwanin ban sha’awa. Dangin Mamy na Egypt sune suka kama amaryar bayan anyi ciniki da qawayenta. Bayan nan ne aka bude fuskar ta wanda aka dinga yaba kyan da tayi. Ita kuwa Zara sarkin fara’a, fuskar ta fal kamar gonar auduga. MC ne yayi sanarwar isowar ango da abokanen shi wanda hakan yasa kallo ya koma kan entrance na hall din. Aikuwa Farouq da abokanen shi suka shigo cikin taku na qasaita. Farouq ya sha kirari a wurin MC, shi kam dariya ma ya dinga yi domin kuwa wasu abubuwan da MC din yake fadi duk exaggeration ne. Farouq dai tunda ya hango Zara ya sa mata idanuwa kamar yadda itama ta sa mishi. Sun bala’in yi ma junan su kyau. Bayan ya qarasa kujerar ta ne ya zauna sannan ya matsa daf da ita yace “hey, you look absolutely beautiful” Murmushi tayi tace “and you, more handsome than ever” Yayi mata gwalo tare da fadin “say something I don’t know” Turo baki tayi ta bugi kafadar shi yayinda yace “oouch, ke muguwa ce fa” Ta Harare shi yayinda ya ja mata kumatu. Ji sukayi MC yace “Ango da amarya ku dan yi haquri ku bamu hankulan ku, a dan dakata da soyayya haka nan” Farouq ya runtse idanuwa ya bude tare da fadin “Oh My God” Ya dan kalli Zara wadda take yi mishi dariya yayinda gaba daya hall din ake ta yi musu dariya. Lokacin da aka kira Farouq da Zara don suyi rawa ita kadai ta tashi domin kuwa Zara akwai son rawa. Farouq wanda yake zaune gani yayi Zara ta zage tana ta rawa wanda gashi dai ko gyale bata yafa ba. Asali ma tunda aa gama kamun ta jefar da gyalen. Gani yayi ana ta kallonta yayinda MC yake ta ziga ta. Tsaki yayi a ranshi yace “she is definitely crazy” Ni kuwa ban ankara ba sai na ga Farouq ya tashi ya nufi dancefloor din. Gani nayi ya janyo Zara ta fado jikin shi wanda yasa tayi mugun tsorata. Gaba daya hall din kuwa suna ta kallon ikon Allah yayinda ake ta daukar hotuna, wasa wasa ma kowa zamewa yayi daga dancefloor din aka barsu su kadai. Zara dai idanuwan ta a rufe ta ji yace “meye na wani dagewa kina ta buga rawa kamar kina dance competition? Idan baki natsu ba zan wasta taron yanzun nan kowa ya tafi gida, kin san dai zan iya” Bude idanuwan ta tayi tana murmushi tace “yi haquri big brother bazan qara ba” Haka kuwa suka tsaya suna ta hirar su a dancefloor din yayinda MC yake ta surutun shi wanda ma su kwata kwata basu sauraron shi. Farouq ne yace mata “yanzu after 1 month shikenan?” Cikin mamaki tace “toh Ya Farouq kai baka so mu rabu ne?” Shiru ya dan yi sannan yace “it doesn’t matter ai, I have a wifey” Ji yayi Zara tace “toh zata dawo ne?” dariya ma ta bashi sossai sannan yace “I am bringing her back home today” Gani nayi Zara ta ture Farouq baya yayinda yayi saurin riqo hannunta yace “don’t tell me you are jealous” Kamar ance ma Zara ta waiga sai gani tayi kowa na kallon su. Shi kuwa MC dama tunda yayi surutun shi ya gaji ya koma ya zauna yana kallon ikon Allah. Banda slow music din da ke tashi ba’a jin komai. Cikin kunya da rudewa Zara ta dawo tayi hugging din Farouq tare da fadin “na shiga uku, Ya Farouq kallon mu fa ake yi” Murmushi yayi yace “who cares? Ai dama mu suka zo kallo tunda mu muka gayyace su” Zara dai runtse idanuwa tayi a ranta tace “he is going to be the death of me” Suna nan a tsaye ne Farouq yace “ni fa I am tired of standing, mu koma mu zauna tunda dai mun yi entertaining dinsu enough” Zara wadda har yanzu idanuwan ta a rufe tace “toh mu je” Ganin bata bude idanuwa bane yace “open your eyes hajiya” sai kuma yayi murmushi yace “ko in dauke ki ne?” Da sauri ta bude idanuwan ta wanda hakan ya sa shi dariya. Farouq dai yana riqe da hannun ta suka koma kujerar su yayinda ake ta yi musu tafi. (Ni kuwa nace kamar sunyi wani abun arziki🤣) MC dai ko da ya tashi kusa da Farouq ya zo yace “ango gaskiya this is not part of the deal fa” Farouq ya kalle shi yace “ba laifi na bane, its beyond me” Gaba daya aka kwashe da dariya yayinda shi kuma ya bata rai kamar ba shi yayi maganar ba. Su Mamy da suke zaune suna kallon ikon Allah sun sha dariya. Granny kuwa sai salati take yi tana fadin “wai yaushe maigidan nawa ya koma haka ne? yanzu duk yawan mutanen da suke wurin nan harda sirikai baya jin kunya?” Anty tana dariya tace “ba laifin shi bane Granny, soyayya ce tayi mishi kamu, kin san Zarar mu ba ta wasa bace” Granny ta tabe fuska tace “aikuwa dai mun shiga uku” haka dai aka dinga kwasar dariya. ************** ALH ABUBAKAR BULAMA MANSION Zaune yake a falon Hajjaju tare da abokin shi Mukhtar. Wasa yake yi da Junior wanda da ganin yadda suke wasan kasan sunyi missing din juna. Hajjaju ce ta fito tare da Ruqayya wadda take a yamutse saboda tashin hankali da damuwa. Ruqayya dai gaba daya yinin yau cikin tashin hankali take a dalilin sanin cewa an fara bikin Farouq da Zara. Ko social media ta kasa shiga saboda bata son ganin hotunan bikin. Har qasa su Farouq suka duqa suka gaida Hajjaju wanda ta amsa cikin fara’a kamar babu abinda ya faru. Masu aiki ne suka shigo da kayan motsa baki suka ajiye a gaban su. Hajjaju ce cikin zolaya tace “Ango ka sha qamshi” murmushi Farouq yayi Yayinda Mukhtar ya dan yi gyaran murya yace “dama Hajjaju mun zo ne mu tafi da Ruqayya..” Kafin ya qarasa Hajjaju tace “nima dai ban ga amfanin zaman nata a gida ba tunda dai ba rabuwa suka yi ba” Ta kalli Ruqayya tace “toh gimbiya, the decision is yours to make” ta miqe tare da fadin “ka gaida mun su Mamy, insha Allah gobe zamu zo” Farouq yace “toh Hajjaju, mun gode” Bayan Hajjaju ta tafi ne Farouq ya kalli Ruqayya yace “hey” Gani suka yi ta fashe da kuka. Mukhtar ne ya miqe tare da daukar Junior yace “bari in dan bar ku kuyi Magana” Farouq ya koma kujerar da Ruqayya take ya janyo ta tare da hugging dinta yace “hey Wifey, stop crying I am here for you, please come back home” Ruqayya tana maqale a jikin shi tace “I missed you so much Honey” yace “me too” Gani nayi ta dago kai ta kalle shi tace “don Allah kada ka auri Zara, ni na amince ka auri wata amma banda..”2 Kafin ta qarasa yace “sssshhhh, kar muyi wannan maganar. Kamar yadda na fada miki I don’t have a say in this” Tana kuka tace “kaima fa na san kana son ta” Shiru ya dan yi sannan yace “she is my sister ai Wifey, ya za’a yi in ce bana sonta?” Fuskarta ya shafa sannan yace “always remember cewa ke ce Uwargidar Farouq and I care about you a lot. Nothing will change I promise you, yanzu dai tashi mu tafi gida kin ji?” AL-HUSSAIN MANSION Zara kwance a kan gadonta yayinda qawayenta suke ta hirar abubuwan da suka faru a kamu. Gaba daya hankalin Zara baya kan su domin kuwa tunanin maganar da Farouq yayi mata take akan zai dawo da Ruqayya yau. Hafsat wadda ta kula da hakan ne ta matsa kusa da ita cikin rada tace “babes how far na ga kamar kinyi nisa, ko kina missing dinshi ne?” Zara tayi ajiyar zuciya tace “kin kuwa san cewa yau zai dawo da Anty Ruqy? Qila ma har ya dawo da ita” Hafsat tana dariya tace “lallai ma Zara, kin ce baki son shi kuma kina zabga kishi akan shi, toh wai ba matar shi bace?” Zara ta turo baki ba tare da tace komai ba yayinda Hafsat ta dinga yi mata dariya. *************** A yau Juma’a, yau ne ranar daurin auren Farouq Al-Hussain da Zara Al-Hassan. Tun da safe Zara ta koma sashen Granny ta kwanta a dakinta domin kuwa hayaniyar mutane ya hana ta yin bacci mai kyau. STORY CONTINUES BELOW Wuraren qarfe sha biyu saura ne Granny ta tada ta daga baccin tana fadin “sannu ‘yar hutu, kina ta bacci kamar kasa. Maza tashi ki je ki fara shiri an kusa daura auren ki” Zara ta tashi zaune tana sosa idanuwan ta alamun bacci bai ishe ta ba tace “ke wannan tsohuwar kin cika neman Magana, don ma na zo dakin ki shine zakiyi mun wulaqanci?” Granny tace “eh, ai dole ki gaya mun Magana tunda kin qwace mun miji” Zara ta fashe da dariya tare da rungume Granny tace “Aikuwa Granny da son auren nan nake yi da kun shiga uku ke da Anty Ruqy don kuwa sai na raba ku da shi” Granny ta Harare ta tace “ai yanzun ma kin raba mu da shi tunda dai duk abinda kike so shi yake yi, mu ai mun zama ‘yan kallo” Zara kuwa babu abinda take yi banda kwasar dariya. Haka dai suka cigaba da tsokanar juna har sai da Hafsat ta shigo dakin ta sanar ma Zara cewa Layla Hayat tana jiran ta. ********* A yau garin Abuja ya cika da manyan baqi daga bangarori na qasar mu Nigeria da sauran qasashe. Gaba daya duk inda ka gifta a garin Abuja labarin bikin ake yi domin kuwa biki ne na gani na fada. Bayan Sallan Juma’a ne aka daura auren a Central Mosque na Abuja akan sadaki naira dubu dari. Manyan mutane sun halarci wannan daurin aure. Shugaban qasa Alhaji Muhammadu Buhari ya halarci daurin auren, haka manyan gwamnoni na arewacin Nigeria tare da Ministers harda Senators duk sun halarta. Abokanen Farouq kuwa na Ingila da Germany da colleaques dinshi wadanda suka yi karatu tare daga qasashe daban daban sun halarci daurin auren. Fatan mu shine Allah ya bada zaman lafiya ya kawo zuri’a dayyaba. AL-HUSSAIN MANSION Guda ke ta tashi a cikin gidan tun bayan da aka daura auren Zara da Farouq. Qawayen Zara ne suka saka ta a gaba suna ta tsokanar ta musamman Hafsat da Saima. Suna zaune suna ta shirin Yinin biki ne Jide da team dinshi suka iso. Hafsat dai qiri qiri ta hana shi shigowa yayinda take ta masifa cewa bai kamata namiji yayi mata kwalliya ba tare da izinin mijin ta ba. Zara wadda take ta roqon Hafsat din ta qi. A qarshe dai su Mamy aka kira wadanda suka goyi bayan Hafsat din. Anty ce ta kalli Zara tace “idan dai kin ga wannan dan daudun yayi miki kwalliya toh kuwa Farouq ne ya amince da hakan” Jin haka ne yasa Zara ta dauko wayarta zata kira Farouq ta tambaye shi wanda aka dinga yi mata dariyar shiriritar ta domin kuwa sun sani sarai Farouq bazai bari wani gardi yayi mata kwalliya ba. Ko da ta kira shi har ta gama ringing bai amsa ba, tana shirin sake kira ne ya kira ta wanda kafin ta amsa Hafsat tace “sa speaker phone don mu ji” Zara batayi tunanin komai ba ta sa speaker phone yayinda kowa a dakin suka yi shiru suna sauraro. Jin muryar shi suka yi yace “hello my beautiful amarya, are you missing me?” Mamy ta dafe kai yayinda kowa yake qoqarin danne dariya kar ta kufce. Gani suka yi Zara ta fashe da kuka. Nan da nan suka ji yace “subhanalillahi, me ya faru? Baki da lafiya ne?” Ta girgiza kai alamar a’a kamar yana ganinta. STORY CONTINUES BELOW Ji suka yi yace “please stop crying and tell me, wa ya taba mun ke?” Cikin shagwaba tace “Ya Farouq ka ga Jide ne zai yi mun make up kuma su Anty da kowa sun hana” Ji suka yi yayi shiru sannan yace “toh wai dama maza ne ke yin make up din?” Aikuwa wasu daga cikin qawayen ta sai da suka fashe da dariya yayinda Zara tace “ni fa Ya Farouq na fi son make up din shi, ka ga fa shi light make up yake yi mun. Please Ya Farouq ka amince yayi mun” Farouq yayi ajiyar zuciya yace “hey stop crying, I really don’t support this amma kuma bana so ran ki ya baci” Ya dan yi shiru sannan yace “there is no problem, he should go ahead” Su Mamy suka zaro idanuwa yayinda Zara tayi tsalle tace “Yeeey, thank you big brother, I love you” Mamy ce ta qwace wayar daga hannun Zara ta cire speaker phone din sannan ta kai kunnen ta tace “kana da hankali kuwa? Ya zaka bari wani namiji yayi mata kwalliya?” Farouq yayi murmushi yace “toh ya zanyi Mamy, I love her so much that I don’t wanna break her heart” Girgiza kai Mamy tayi tace “Allah ya shirye ka” yana dariya Mamy ta kashe wayar. Da haka kuwa Jide ya shigo yayi ma Zara kwalliya wanda kuwa aka yaba qwarai domin kuwa tabbas ya iya aikin shi. Anyi shagali sossai na yinin biki, Zara ta sa kaya na gani na fada masu kyan gaske. Ta yi kyau sossai, BigH ya dauki hotuna kala kala. Da yamma ne aka shirya Zara don kai ta gidan miji. Bayan su Daddy sun zaunar da ita sunyi mata nasihohi ne aka sa Zara mota. Wani ikon Allah fa Zara ko kuka bata yi ba har su Hafsat suna ta yi mata tsiya. Ita dai Zara gani tayi ba wani sabon wuri zata je ba, gidan Farouq ai kamar gida ne, meye na wani kuka balle kuma auren ma qarqarin shi wata daya.2 (Hahahaha🤣) FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Gidan Farouq wanda Mukhtar yake kira Villa nan ne aka kai Zara. Tunda aka iso gaban gate din gidan ne ‘yan kawo amarya suke mamaki. Gaba daya hankalin mutane yana kan tsarin gidan yayinda ake ta kallo. Gaba dayan su hatta Zara babu wanda ya taba zuwa gidan. Dukda fuskar Zara a boye take cikin gyale ta yaba ma abubuwan da ta hango ta cikin gyalen. Kowa ya rude da ganin tsarin gidan yayinda ake ta yabawa. Hafsat ce ta kai bakinta saitin kunnen Zara tace “what the.. babes kin ga gidan nan kuwa? Anya kuwa anyi adalci anan?” Zara dai murmushi take ta yi. 20 ‘Yan kawo amarya dai basu qarasa rudewa ba sai da aka shiga gidan. Tsarin gidan kamar a turai, duk wani kayan jin dadi da ka sani akwai shi a gidan. Wasu abubuwa ma kallon su kawai ake yi amma ba’a san amfanin su ba dukda kuwa ‘yan kawo amaryar wayayyu ne tunda dai duk dangi ne wanda kuwa a dangin Alhaji Umar Jimeta kaf babu talaka. Sashen da suka gani a bude shi ya tabbatar musu da cewa nan ne bangaren Zara. Ita kuwa Zara jin ana ta yaba gidan ne yasa ta yaye gyalen da aka rufe mata fuska da shi tace “haka kawai kun rufe mun fuska na kasa ganin gida na da kyau” aka dinga yi mata dariya. Bayan magrib ne aka fara shirin zuwa dinner. Tuni qawayen amarya sun shirya yayinda ake shirya Zara itama. Jide dai shi ya sake dawowa yayi ma Zara kwalliya. Dayake motoci sun riga sun iso sai aka dinga kwasar mutane zuwa event centre din. Hafsat kadai ta rage tare da Zara wadanda tare zasu tafi. Sadiq ne ya zo daukan su. Dayake yau da safe ya iso daga London bai ga Zara ba. Ai kuwa yana yin sallama ya shigo dakin Zara ne ta sa ihu ta rugo a guje zata rungume shi wanda yayi saurin kaucewa yace “ke Hajiya rufa mun asiri kin fi qarfi na yanzu, Haka kawai ki ja Ya Farouq ya sa a daure ni” Fashewa tayi da dariya tace “ka ma isa” Aikuwa bin shi tayi yayinda ya janyo ta ya bata side hug yace “kin ga yadda kika canza kuwa? Da na ga hotunan ku I thought BigH ne ya dan canza ki ashe ma you look more beautiful a reality” Dariya tayi tace “thanks My luv” Zama suka yi a kan kujerar dakinta suka cigaba da hira. Sadiq ne yace “hmmm, I cant believe wai you are married to Ya Farouq, ke kam shikenan babu ruwan ki da masifan nan da yake yi mana” Zara tayi dariya tace “ai daga baya ma na gane halin shi, ka san cewa Ya Farouq is very Simple and nice” Sadiq cikin mamaki yace “eh lallai kam princess, dole ya zama nice to you ai tunda matar shi ce ke, kuma ma ai sonki yake” Zara ta zaro idanuwa tace “wa ya fada maka so na yake? baya da choice ne fa Ya Sadiq” Sadiq ya girgiza kai yace “Ya Farouq loves you Princess, trust me” Zara dai bata qara cewa komai ba. Sadiq ne ya kalli tsarin dakinta yace “Gaskiya gidan nan yayi kyau, kin kuwa san turawa suka yi aikin gidan nan gaba daya?” Zara tace “haba?” Yayi murmushi yace “Sannan bayan an gama Anty Ruqy tace wai bata so dukda fa bata taba zuwa ta ga gidan ba. According to yadda na ji wai she has a dream house da take so” Zara ta fashe da dariya tace “shine wanda take ciki yanzu hala?” Sadiq yace “ke dai bari, ai tayi missing din gida” Hafsat ce ta dauko takalmin Zara tace “toh Hajiya kun fa san kowa ya tafi mu ake jira” Sadiq ne ya karbi takalmin yace “let me do the honours” Hafsat tana dariya ta miqa mishi takalmin yayinda Zara ta dago qafarta Sadiq ya fara sa mata takalmin. Tana murmushi tace “how I missed you Ya Sadiq” ************ CUNNINGHAM MARQUEE EVENT CENTRE Motar Amarya ce ta shigo harabar wurin inda gaba daya wadanda suke harabar wurin suka juyo suna kallon motar.+ Ko da Sadiq ya faka motar sai ya dauki wayar shi ya kira Farouq yace “Ya Farouq gata nan na dauko ta” Hafsat ce tace “toh babes, ni dai bari in qarasa wurin mutane, sai mun hadu” Kafin Zara tayi Magana ne Hafsat ta fita yayinda Farouq ya shigo motar. Qare ma juna kallo suke ta yi a dalilin kyau da suka yi ma junan su. Sadiq dai ta mirror yake ta kallon ikon Allah yayinda yake ta matse dariyar da take nema ta kufce mishi. Gani nayi Farouq ya buga kafadar Sadiq ba tare da ya kalle shi ba yace “guy, your job is done, I need some privacy please” Sadiq ya fashe da dariya yace “sorry bro, bari in tafi toh”. Ya bude qofar ya fita. Kallon da Farouq yake yi ma Zara ne ya sa ta ji kunya tare da duqar da kanta tana wasa da Zoben diamond din da ke hannunta. Murmushi yayi sannan ya kamo hannunta wanda ya sa tayi saurin dago kai ta kalle shi yayinda jikin ta yayi sanyi. Gani nayi yayi kissing hannunta wanda yasa ta lumshe idanuwanta. Ji tayi yace “na taba gaya miki cewa kin fi ko wacce mace kyau a duniyan nan?” Zaro idanuwa tayi tana murmushi yayinda ya saki hannun ta ya bude qofar motar ya fita ya zagaya ya bude mata tare da miqa mata hannu yace “come” Zara dai miqa mishi hannu tayi yayinda ya taimaka mata ta fito. Gani nayi Farouq ya tsaya cak yana kallon ta sama da qasa. Ganin yayi shiru kamar yana tunani ne ya sa ta dan matsa kusa da shi tace “Ya Farouq ana jiran mu” Bata rai yayi yace “wai haka zaki shiga?” Ta kalli jikinta tace “ban yi kyau bane?” nan da nan kuwa ta fara neman kuka yayinda yace “I mean, haka aka yi dinkin? Ehm, sorry aren’t you suppose to cover yourself up with a veil or something?” Zara tayi murmushi tare da bashi side hug tace “are you jealous?” yayinda ta kashe mishi ido daya wanda yasa ya girgiza kai yana murmushi. A cikin hall dai ana ta sanarwar shigowar ango da amarya amma shiru basu shigo ba don haka ne sai da aka aika a kira su. Ko da suka kama hanyar shiga hall din Zara dai riqe hannun Farouq tayi gam domin kuwa wani shegen takalmi ta sa mai tsawon gaske. Farouq ne yace “ke dai kin cika rigima wallahi, yanzu meye na sa wannan dogon takalmin gashi nan kina ta tafiya da qyar” Dariya tayi tace “toh Ya Farouq kai ne ai you are tall, idan ban sa takalmi mai tsawo ba za’a yi mun kallon dwarf” Farouq kuwa me zaiyi banda dariya. STORY CONTINUES BELOW Aikuwa Zara tana maqale da shi suka shigo hall din gwanin ban sha’awa. Hira suke yi sossai yayinda MC yake ta yi musu kirari amma kamar kullum hankalin su baya tare da shi. Daddy ya kalli Abba wadanda suke zaune tare da abokanen su yace “ka gan su ko? Kamar ba su bane suke ta bata rai don mun ce zamu hada su” Abba yace “ai wadannan yaran ka qyale su kawai” Zara dai yau all white ta sa na wani shegen dinki mai zafi da Galiafahad yayi mata, dinkin yayi masifar kyau. 8 Biki dai yayi biki, ana ta shagali. An ci an sha sannan anyi rawa. A lokacin da MC ya kira Zara ta fito tayi rawa da qawayen ta ne Farouq ya hana. Abu dai kamar wasa MC ya dage akan lallai sai Farouq ya bari ta fito amma ya qi. Haka kuwa aka dinga yi musu dariya. MC dai matsowa yayi kusa da shi yace “gaskiya idan ba qwaqwarar dalili zaka bamu ba bazamu yarda ba sai amarya ta fito” Farouq ya kalli Zara sannan ya bata rai yace “qafarta na ciwo” Gaba daya hall din aka dinga dariya yayinda MC ya kalli Zara yace “Amarya wai dagaske qafar ki na ciwo?” Zara wadda ta cika da mamaki ta matsa kusa da Farouq ta kai bakinta saitin kunnen shi tace “Ya Farouq ni fa ina so inyi rawa” Ya girgiza kai tare da fadin “ashe kuwa you will remain in my house forever” Zaro idanuwa suka ga tayi sannan ta kalli MC din tace “dagaske ne, qafana na ciwo” anan ma dariya aka dinga yi mata. Mamaki mutane suka dinga yi ace amarya guda bata taka ba ranar bikinta. Mamy ce tace “Allah sarki Zara sarkin son rawa, Allah kadai yasan me yace mata da har ta amince” Su Granny suka yi dariya yayinda Anty tace “ina kyautata zaton harda don kayan da ta sa ne” Granny tace “Allah dai ya qara mata” Su Mamy suna ta dariya. Haka dai ‘yan uwa da abokanen arziki suka dinga cashewa a fagen rawa yayinda Zara ta dinga turo baki tana fushi saboda Farouq ya hana ta. Farouq wanda ya kula ran ta a bace ne ya janyo ta jikinshi yace “hey I am sorry please, I have my reasons. Ba haka nan na qi amincewa kiyi rawa ba” Cikin shagwaba tace “but Ya Farouq…” Yace “ssshhhh, I am sorry please princess kinji?” STORY CONTINUES BELOW Yadda Farouq yake roqon ta ne ya bata mamaki domin kuwa ta sani sarai bai taba lallashinta haka ba. Gani nayi tayi murmushi tace “its okay, Na haqura” Bayan an tashi daga dinner din ne Zara ta tsaya tana ta gaisawa da mutane yayinda BigH yake ta kashe mata hotuna. Kowa yana ta son daukar hoto da ita. Ganin haka ne Farouq ya janye ta ya kai ta har mota sannan ya kira sadiq yace “take her home” Sadiq yana dariya yace “as you wish boss” Zara dai sai roqon Farouq take yi akan ya barta ta gama gaisawa da mutane amma sam ya qi ya kora ta gida. Hafsat ma bata samu bin qawarta ba sai wata motar ta bi. FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Bayan an dawo daga dinner ne ake ta hirar abubuwan da suka faru wanda yawanci Farouq aka dinga yi ma tsiya yadda duk ya bi ya hana Zara motsi. Ahankali kuwa aka dinga zamewa ana ta bacci. Zara kuwa Layla Hayat ta sa ta a gaba sai da tayi wanka cikin turaruka kamar kullum, ko da ta fito kuwa haka ta bata wasu mayyuka ta shafa. Zara dai ta gaji da wannan aiki na Layla, dukda tana qaunar qamshi a rayuwarta wannan karon dai ta gaji. Bayan ta kimtsa ne suka koma kan gado suna ta hira ita da Hafsat. Hafsat ce tace “babes wai Ya Farouq yayi confessing love dinshi zuwa gareki kuwa?” Zara ta zaro idanuwa tace “na shiga uku, wai ku wa yace muku sona yake?” Hafsat tayi tsaki tace “wai ke har ma sai ya fada ne?” Zara ta gyara kwanciyarta tana dariya tace “ke duk fa acting yake yi, sau nawa zan gaya muku baya da option ne shiyasa” Hafsat ta girgiza kai tace “okay ooo, ku cigaba da denying din juna, mu dai munyi mai wuyan tunda muka hada ku” Zara tana dariya tace “I really care about Ya Farouq but there is nothing between us, trust me babes” Hafsat ta Harare ta sannan tace “ke qyale ni da shirmen banza, good night” ************* Washegari da daddare ne aka shirya zara don tarbar angonta. Layla hayat ta kimtsa ta tayi kyau sossai. Zara dai ta sha qamshi har ta gaji. Farouq dai tare da abokanen su ya shigo gidan inda suka ba qawayen amaryan kudi har naira miliyan biyu su raba a dalilin suna da yawa. Tare da qawayen amaryan suka tafi bayan sunyi musu fatan zama lafiya. Sadiq ne ya tafi da su Saima gida yayinda aka bar Hafsat da Mukhtar. Mukhtar Zaune a falon Zara tare da Farouq inda Mukhtar din ya matsa kusa da abokin shi yace “abokina finally mun kawo maka love of your life, I don’t even need to tell you to take care of her, Please make her happy” Farouq yace “thank you my friend” Hafsat ce ta shigo falon ta kalli Mukhtar tace “ni na gama sweetlove mu tafi” STORY CONTINUES BELOW Mukhtar yace “har kunyi sallama? Hope dai baki sa ta kuka ba?” Hafsat tayi dariya tace “ai bata ma san zan tafi ba, I told her I was going to get some water ne” Mukhtar ya miqe yace “kin kyauta, lets go” Har wurin motar su Farouq ya raka su yayinda yayi musu godiya. Bayan sun tafi ne ya tsaya yin Magana da securities din gidan sannan ya wuce cikin gida. Kai tsaye sashen shi ya wuce don yin wanka. Zara tana kwance a kan gadon ta tana ta kallon posts din hotunan su a instagram wadanda ake ta reposting ana commenting. Tuni ta yaye gyalen da aka rufa mata. Wayarta ce tayi ringing inda ta ga sunan Mahmood, haka ta dinga kallon wayar har ta tsinke bata dauka ba. Text message dinshi ne ya shigo wanda ta bude ta ga saqo kamar haka: “please cutie just pick up even if its going to be for the last time” Bata ankara ba ta ga ya sake kiranta wanda ta amsa don jin abinda zai ce mata. Farouq ya fito daga sashen shi sanye cikin wandon sweatpant hade da polo T-shirt. Sashen Zara ya nufa. Ya iso bakin qofar dakinta ne ya ji kamar tana Magana. Dan tsayawa yayi yana sauraron abinda take fadi. Ji yayi tace “you know I love you very much, I ddn’t have a choice ne but to agree” Shiru ta dan yi sannan tace “please forgive me, kar ka damu ina ji a jikina bazan dade a gidan Ya Farouq ba, shima fa ba sona yake yi ba” Dariya tayi sannan tace “okay thank you, shiyasa nake qara sonka” Farouq wanda ya gama sauraron wadannan kalaman na Zara ne ya runtse idanuwan shi tare da girgiza kai ya juya ya koma cikin tsananin bacin rai. ************ Zaune yake a kan gadon dakin shi inda ya dafe kai yana tuno kalaman Zara, idanuwan shi sunyi ja a dalilin muguwar damuwa da ya shiga. Tuni kanshi yayi nauyi. Tambayar da yayi ma kanshi “wai dagaske dama Zara bata so na? Toh kenan dagaske rabuwar take so mu yi nan da wata daya? Shin ya zan yi da son da nake yi mata?” Ji nayi yace “inna lillahi wainna ilaihir raji’un, yanzu ya zanyi da wannan yarinyar?” Gani nayi ya qarasa hawa gadon ya kwanta ya rufe idanuwa yayinda zuciyar shi take ta zafi. Tuni kan shi ya fara sarawa. Zara dai bayan ta gama waya da Mahmood ne ta miqe ta shiga closet dinta ta dauko rigar bacci na wando da riga cotton ta sanya. Ko da ta fito mamaki tayi da ta ji gidan shiru, bata yi tunanin cewa qawarta ta tafi ba. Ji nayi tace “wato bestie guduwa tayi ta barni kenan” Tafe take yayinda take ta bin kowanne lungu na gidan. Har yanzu akwai wuraren da Zara bata shiga ba a gidan a dalilin mugun girma da gidan yake da shi. Tana tafe tana qara yaba ma tsarin gidan, ni dai ji nayi tana ta fadin “wow” Sashen Farouq ta shiga wanda yayi bala’in haduwa har a ranta tana fadin “this is definitely his side, how breathtakingly beautiful” Da qyar ta gano dakin shi wanda ta bude qofar kamar kullum ba tare da knocking ba ko sallama. Farouq wanda yake kwance a kan gadon shi yana jin shigowar Zara amma bai motsa ba, zuciyar shi ce take tafasa sossai. Zara dai ganin Farouq a kwance ne yasa tace “laaa, Ya Farouq yayi bacci ashe” Ta qarasa wurin shi ta hau kan gadon ta sa hannu a kan goshin shi don ji ko lafiyar shi lau. Ji yayi tayi ajiyar zuciya tare da fadin “thank God he is alright” Shi kam Farouq gaba daya qamshinta ya mamaye shi wanda ya qagara ta matsa daga kusa da shi domin kuwa ji yake yi kamar ba zai iya jurewa ba. Bargon shi ta ja ta rufa mishi sannan ta sauka daga kan gadon ta kashe mishi wuta ta fita. (Kamar ya sa ta🤣🤣) Tana fita daga dakin kuwa Farouq ya bude idanuwan shi tare da jan numfashi. Tashi yayi zaune, Yana dafe da kanshi yace “I am so in trouble, She is going to be the death of me soon, what should I do??” **************

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *