BA SONTA NAKE BA CHAPTER 12

BA SONTA NAKE BA CHAPTER 12 

FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Kwance yake a kan gadonshi yana ta bacci.+ Wayar shi ce take ta ringing. Janyo wayar yayi sannan ya amsa ya kai kunnen shi ba tare da ya duba ko waye ba domin kuwa har a wannan lokacin idanuwan shi a rufe suke. Daga asibiti ne inda Dr Ibrahim yake tambayar shi akan wani report na wani patient. Bayan ya gama yi mishi bayani ne ya kashe tare da jefar da wayar. Bai ankara ba sai ya ji muryar ta saitin kunnen shi inda tace “Good morning Handsome” Da sauri ya bude idanuwan shi yayinda ya ganta zaune daf da shi tana murmushi. Farouq dai ya dade yana jin qamshin Zara a kusa da shi wanda yayi mishi kamar a mafarki, ashe kuwa ita din ce a zahiri. Cikin mamaki yace “yaushe kika shigo?” Murmushi tayi tare da gyara zama tace “na kusa thirty minutes da na shigo, da na ga kana bacci shine na zauna kawai ina kallon ka” Tashi yayi zaune yayinda ya sa mata idanuwa. Sanye take da rigar baccin ta na riga da wando. Gashin kanta buzu buzu kamar kullum. Hannuwan ta ya kalla yace “let me see your hand” Matsawa tayi kusa da shi ta miqa mishi cikin mamaki tace “me zaka yi da hannu na?” Ba tare da yace mata komai ba ya dinga bin lallen hannun ta da kallo yayinda yake ta juya hannun. Shafa lallen ya dinga yi sannan ya kai bakin shi bisa hannun yayi mata kiss yace “I love this” Murmushi tayi sannan tace “yauwa Ya Farouq jiya fa kayi mun laifi kuma ni gaskiya ban yarda ba” A ranshi ne yace “I cant believe this, tayi mun laifi sannan yanzu tace ni ne nayi mata laifi” Ji yayi tace “ka ga fa na sani cewa idan aka yi aure ana kawo ma amarya kaza kuma fa ni baka kawo mun ba” Farouq dai bai san lokacin da ya fashe da dariya ba yace “you are crazy, I thought kin ce you are my sister and not my wife, wane kaza kuma zan kawo miki?” Ta turo baki tace “ni gaskiya kawai kayi mun wayo” Yana dariya ya sauka daga kan gadon yace “yanzu dai thanks for waking me up, let me go and take my bath” Gani yayi ta shige bargon shi ta kwanta tace “toh bari in jira ka, idan ka gama sai mu je muyi breakfast, Mamy ta aiko tun dazu” Girgiza kai yayi yace “as you wish”. Ko da ya wuce dressing room dinshi wayarta ta dauka ta shiga instagram inda take ta kallon hotunan bikin su wanda aka yi posting. STORY CONTINUES BELOW Zara tana nan kwance Farouq ya fito daga wanka. Ganin ya fito daure da towel ne yasa tayi saurin tura kanta cikin bargon shi wanda ya sa shi yin murmushi tare da girgiza kai. Bayan ya gama ne ya nufi dressing room dinshi don sa kaya. Ya fito Sanye cikin Grey Sweatpant da black T-shirt yayinda ya nufi gaban madubi yana fesa turare. Zara ta dan leqo shi ta cikin bargo don tabbatar da ya sa kaya sannan ta sauko daga kan gadon ta dawo kusa da shi tace “Ya Farouq dakinka ya fi nawa kyau” Yace “toh ko zaki dawo nan ki dinga kwana?” Ta zaro idanuwa tace “what?” Bata rai yayi yace “toh meye?” shiru ta yi sannan ta duqar da kanta tana murmushi. Bayan ya gama brushing kanshi ne ya janyo hannun ta yace “I am done, mu je” Yana riqe da hannun ta suka nufi dinning room. Bayan ta zuba mishi ne ta janyo wani plate zata sa ma kanta. Gani nayi ya riqe hannunta yace “sit, let’s eat together” Murmushi tayi ta matsar da kujerar ta kusa da shi ta zauna cikin shagwaba tace “ni kai zaka bani da kanka” murmushi yayi sannan ya fara bata. Zara dai murna fal a cikin ta yau Farouq yana bata abinci a baki alhalin lafiyarta qalau. Kallon shi take ta yi yayinda take murmushi tace “Ya Farouq zaka dinga bani da kan ka kullum?” Murmushi yayi yace “duk abinda kike so zanyi miki” Cikin mamaki tace “dagaske Ya Farouq?” ya girgiza mata kai alamar eh. Gani nayi tayi dariya tace “thanks big brother, you are the best” Bayan sun kammala breakfast ne Farouq ya miqe tare da fadin “i am going out for a while” Gani nayi ta riqo hannun shi tace “ina zaka je?” yace “hospital” Turo baki tayi tace “ba ance ba’a zuwa ko’ina ba idan anyi aure?” Murmushi yayi ya janyo ta kusa da shi yace “so kike in zauna?” Da sauri tace “Eh ya Farouq, please don’t go anywhere, bari nima in je inyi wanka sai in zo muyi kallo” Har ta juya zata tafi ne ya riqo hannunta tare da fadin “mu je in raka ki” Murmushi tayi sannan tace “mu je toh” Farouq yana nan zaune a kan gadonta ta shiga wanka, aikuwa ta dade domin kuwa har ya ma manta abinda yake yi a dakin. Yana latsa wayar shi ne ya ganta ta fito daure da dan qaramin tawul fari. Tana zaune a gaban dressing mirror dinta ne ta hango shi ta madubi inda ya sa mata ido. Murmushi tayi tace “Ya Farouq stop staring at me” Murmushi yayi tare da miqewa ya zo ta bayanta ya tsaya. Duqowa yayi saitin kunnenta yace “you are my property so I have the right” STORY CONTINUES BELOW Zaro idanuwa tayi tana kallon shi ta cikin madubin. Ji tayi ya dafa kafadarta yayinda ya kai fuskar shi kan wuyanta yana shaqar qamshin ta. Zara dai tuni jikinta ya fara rawa. Muryar ta qasa qasa tace “Ya Farouq” Farouq wanda hankalin shi yayi nisa bai ma ji ta ba. Jin yayi shiru ne yasa ta dan daga murya tace “Ya Farouq please stop” A kunnen ta ya rada mata “why? Are you scared?” Kafin tayi Magana ne ya sake ta tare da kallonta ta madubi yace “ko in shafa miki man ne?” Zaro idanuwa tayi ta miqe ta ruga dressing room dinta a guje yayinda ta bar Farouq yana murmushi. Wayar shi ce tayi ringing ya amsa. Dr Ibrahim ne daga asibiti wanda yace “Sir please I am sorry to disturb you” Farouq ya girgiza kanshi yace “what is it again? Yanzu yau din ma ba za’a bar ni in huta ba?” Dr Ibrahim yayi murmushi yace “kayi haquri Sir, its about that patient..” Farouq ya shafa kanshi sannan yace “gani nan zuwa yanzu” Bayan ya kashe wayar ne ya matso kusa da dressing room din Zara yace “hey I have to go” Zara tana tsaye a gaban wadrobe dinta yayinda take ta sauke numfashi. Abinda ya faru yanzun nan take tunani. Gaba daya jikinta yayi sanyi yayinda ta kasa yin komai. Farouq wanda yake ta yi mata Magana ma kwata kwata bata ji shi ba. Shi kuwa da ya ji shiru ne ya leqa. Ganin ta yayi a tsaye wanda ga dukkan alamu tayi nisa a tunani. A hankali ya qarasa wurinta tare da rungumeta ta baya ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “are you thinking about me?” Zara dai a firgice tace “uhmm.. I was… ina so in ciro kayan da zan sa ne” Murmushi yayi tare da bude mata wadrobe din sannan yace “I just received a call, I have to go” Gani nayi Zara ta dan bata rai sai kuma tace “toh yaushe zaka dawo?” Hancin ta ya ja sannan yace “are you going to miss me?” Shiru tayi yayinda ta duqar da kanta qasa. Murmushi yayi sannan yace “ina gamawa zan dawo, I will call you” ya matsa kusa da ita yayi mata kiss a kumatu yace “take care” Bayan Farouq ya fita ne Zara ta saki numfashi wanda da alama ta dade riqe da shi. zuciyarta ta dafa yayinda take bugu da sauri. Tambaya take yi ma kanta, anya zata iya zama a haka tare da shi har tsawon wata daya??? (Hahahaha… habawa Zara🤣🤣) FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN RUQAYYA) Ruqayya zaune a falonta tare da qawarta Aliya wadda tun da aka fara bikin Farouq take gidan tana taya Ruqayyar zama. STORY CONTINUES BELOW Ruqayya dai tunda aka fara bikin Farouq ta rabu da kwanciyar hankali, Qawarta Aliya ita take ta sanyaya mata rai. Matsalar ta a yanzu shine yadda zata yi da Zara. Ruqayya ta qagara gobe tayi don su tafi Cotonou wurin Malamin da qawar Hajjaju zata kaisu wurin shi. Aliya wadda take ta faman kallon hotunan bikin Farouq da Zara ne tace “amma dai gaskiya Zara tayi kyau, kin kuwa san ban taba yi mata kallo sossai ba sai a hotunan bikinta?” Ruqayya wadda ta ji kamar ta mutu tace “meye abin kyau qawata? Don Allah ki bari” Aliya tace “kin kuwa san kayan da ta sa masu tsada ne? Talking about millions of naira fa. Galiafahad yayi posting a page dinshi ai” Ruqayya tayi tsaki tace “ta kusa gane batada wayau ai” Wayarta ta janyo ta kira layin Farouq wanda kamar kullum bai amsa ba. Tsaki tayi tace “yanzu haka yana can maqale da ita, wallahi yarinyar nan matsala ce a rayuwata, na so ace ta mutu tun lokacin da ta fado daga steps dinnan” Aliya tace “hmmm, don ma dai Allah ya sa ta manta abinda ya faru ai da yanzu kina gida qawata” Kafin Ruqayya tayi Magana ne wayar ta tayi ringing. Ganin sunan Farouq ne yasa tayi tsaki sannan ta amsa cikin sallama. Bayan ya amsa ne yace “how are you and Junior?” tace “we are fine, Junior yana ta missing dinka. Ka tafi wurin amarya ka qyale mu” Murmushi kawai yayi sannan yace “na ga missed call dinki, hope all is well?” Tace “uhm dama ina so in fada maka cewa Hajjaju zata je Cotonou gobe shine nace bari in tambaye ka if I can go with her” Shiru ya dan yi sannan yace “kwana nawa zaku yi?” tace “just 3 days. Please Honey” Yace “its okay, Allah ya kiyaye hanya” tace “ameen, thanks” Yace “zan zo anjima insha Allah” tace “okay” ************* Bayan sallan Isha’I ne Farouq ya shigo gidan Ruqayya. A lokacin da ya shiga gidan ya tarar da ita a qaramin falonta kwance a bisa kujera. Hankalinta yayi nisa a tunani da bata ji shigowar shi ba. Zama yayi gefenta yace “hey” Da sauri ta tashi zaune ta rungume shi tace “Honey I am so happy to see you” Farouq ya dan yi murmushi yace “me too, meyasa kike zaune ke kadai? Where is your friend??” Ya kalli TV yace “na ga ko TV baki kunna ba” Ajiyar zuciya tayi tace “Aliya ta koma gida dazu da yamma” Yace “okay, Junior fa?” Tace “yana wurin Nanny dinshi” Farouq ya miqe yace “mu je in gan shi kafin in tafi” STORY CONTINUES BELOW Jin yace haka ne yasa Ruqayya ta bata rai tace “Yanzu Honey shikenan haka zamu koma yi, idan ka zo nan sai ka je wurinta ko?” Janyo ta yayi jikinshi yace “kiyi haquri wifey, always remember that both of you are my wives kuma I will treat you equally Insha Allah” Ruqayya dai a ranta fadi take yi “bari dai in je in dawo, zata gane cewa ni da ita ba daya muke ba” Farouq dai ya dade yana wasa da Junior har sai da Junior din yayi bacci sannan yayi ma Ruqayya sallama wadda take ji kamar ta hana shi tafiya don baqin ciki. (Naki wasa ne Madam Ruqs🤣) FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Wuraren qarfe goma Farouq ya shiga gidan. Ganin dare yayi ne ya sa yayi tunanin lallai Zara tayi bacci don haka ne ya wuce sashen shi kai tsaye. Ganin TV din babban falon shi a kunne ne yasa ya qarasa shiga don kashewa. Qamshin Zara ya ji wanda yasa shi waigawa da sauri ya hango ta kwance a kan kujera tana bacci. Sanye take da three quarter jeans da wata ‘yar qaramar T-shirt. Tayi masifar kyau dukda kuwa bacci take yi. Farouq dai zuwa yayi ya zauna daf da ita ya sa mata ido. A ranshi ne yake fadin “how i so much adore her” Gani yayi ta dan motsa tare da fadin “Ya Farouq ka dawo?” Murmushi yayi sannan ya kai bakinshi saitin kunnen ta yace “hey sleeping beauty, me kike yi anan? Tashi ki je dakinki ki kwanta” Ba tare da ta bude idanuwan ta ba tace “you said you were going to call me and you didn’t” Murmushi yayi yace “I am sorry, kinyi mssing dina ne” tace “sossai Ya Farouq” A ranshi ne yace “that’s the idea Zara, good job Farouq”. Farouq dai da gangan ya qi kiranta dama saboda tayi missing dinshi wanda kuwa da kanta ta fada tayi. Girgiza kai yayi sannan ya miqe yace “let’s get you to your room” duqowa yayi ya dauke ta cak yayinda ta maqale a jikin shi kamar mage. Ji nayi yace “ko a dakina zaki kwana?” Da sauri ta bude idanuwan ta tace “No please No ya Far…” Ji tayi yace “ssshhhh, dakinki zan kai ki My Baby angel, relax” Gani nayi tayi murmushi tare da sagala hannunta a wuyan shi tace “ina son sunan Ya Farouq, zaka dinga kira na haka?” Murmushi yayi yace “My Baby angel you shall be henceforth” Tayi dariya sannan tace “thank you Ya Farouq” Har dakinta ya kai ta inda ya kwantar da ita bisa gadonta sannan ya rufa mata bargon ta. Gani nayi yana stretching hannuwan shi tare da squeezing din fuskar shi yace “gaskiya kin yi nauyi dayawa, bazan qara daukar ki ba” Tashi tayi zaune tare da turo baki tace “haba ya Farouq wane nauyi gare ni?” Ya zauna kan gadon yace “ni dai yanzu sai ki biya ni don gaskiya kin bani wahala” Cikin mamakin halin shi tace “toh me zan baka Ya Farouq?” yace “A kiss will do” Zaro idanuwa tayi tana mamakin abinda ta ji wanda yasa tace “Ya Farouq??” Ya bata rai tare da fadin “what?? A banza ma fa an sha yi mun kuma yanzu da na tambaya sai a qi?” Jin haka ne yasa tayi murmushi ta matsa kusa da shi tayi mishi kiss a kumatu tace “thank you big brother” ya girgiza kai yace “anything for you my Baby angel” Ya miqe kenan ta riqo hannun shi tace “ka ci abinci?” yace “na sha fruits and I am okay” Murmushi tayi tare da sakin hannun shi sannan tace “good night ya Farouq” Shima murmushi yayi mata yace “Good night my Baby angel” Haka Farouq ya fita ya bar Zara tana ta murmushi tare da jin dadin abinda ya wakana a tsakanin su. A yanzu ta fara yarda da maganar Mamy akan lallai Farouq zai kula da ita fiye da yadda take tunani. Gani nayi tayi ajiyar zuciya tare da lumshe idanuwa tace “Oh Ya Farouq, kwana daya kawai and it already feels like a thousand days..” ************** FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA) Kwance take a bisa gadonta amma fa ba bacci take yi ba dukda dai bata dade ta farkawa ba.+ Farouq ne ya qwanqwaso qofar dakin sannan ya shigo. Zara wadda ta sa mishi ido ne a ranta tace “Oh Ya Farouq, always looking cute” Yana murmushi ya qaraso wurinta ya zauna bisa gadon yace “and how is my Baby angel doing today?” Gani nayi ta matsa ta kwanta bisa cinyar shi tace “i am doing just fine Ya Farouq, good morning” Ya dan ja mata hanci sannan yace “ke fa lazy girl ce dama, haka kawai su Mamy sun hada ni da wahala” Cikin shagwaba tace “Ya Farouq me nayi maka kuma?” Yace “toh gashi nan yanzu qarfe goma na safe amma har yanzu kina kan gado, kin dai san babu masu aiki a gidan nan ko?” Tashi tayi zaune tare da zaro idanuwa tace “what? Toh yanzu ya zamuyi Ya Farouq?” Farouq dai ta bashi dariya amma sai ya matse yace “ke zaki dinga yin komai hajiya, har tsawon wata daya” Fuskarta kamar zata yi kuka tace “Ya Farouq wallahi bazan iya ba, ka fa san gidan nan yana da girma” Girgiza kai yayi ya janyo ta jikin shi yace ”hey relax, wasa nake yi akwai masu aiki dayawa, tashi mu je inyi introducing dinku, I was supposed to do so jiya amma na fita” Cikin murna tace “yauwa Ya Farouq, thank you very much” Dogon hijabi ta sanya sannan suka fita. Ainihin main palor din gidan wanda yake qasa suka nufa. Zara dai mamaki tayi ganin masu aiki tsatsaye a falon sanye cikin uniforms dinsu. Aikuwa suna shigowa falon masu aikin suka duqa har qasa suna gaida Zara. Ita kuwa kamar kullum cikin fara’a take ta amsa su tare da fadin “ku tashi tsaye don Allah, ni bana so kuna duqawa” Farouq wanda yake riqe da hannunta ya janyo ta jikin shi ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “you command respect Hajiya, better get use to this here. Wadannan ba su Larai bane” Dariya tayi yayinda suka zauna a kan kujera. Farouq ya kalle ta yace “Oya ga masu aikin ki, sai ki tsara yadda kike so” Zara ta kalle su tace “aikin ku zai zama daga kicin sai nan ground floor din” Farouq yace “sauran fa?” tayi murmushi tace “I will do it myself Ya Farouq” Zaro idanuwa yayi cike da mamaki yace “what?” Zara ta juya tace ma masu aikin “zaku iya tafiya” suka ce “okay Ma” Bayan sun fita ne Zara ta langwabe a jikin shi tace “kasan fa Mamy tace in dinga gyara part dinka, kuma zan dinga gyara nawa ma sai kuma abincinka ma ni zan dinga dafa maka, ka ga su sai su dinga dafa nasu ko??” Murmushi yayi a ranshi yace “kin kyauta mun Mamy na, Allah ya bar mun ke” Ganin yayi shiru ne yasa tace “ko baka son haka ne Ya Farouq?” ya girgiza kai sannan yace “wai ke dama haka kike da son jiki? Gaskiya Mamy ta sha wahala. Duk kin bi kin danne ni. Kwanan nan zaki karya ni na ga alama” STORY CONTINUES BELOW Dariya tayi tace “I love you big brother” yace “arrggghhhh” Tare suka yi breakfast a dinning wanda kamar yadda yayi mata alqawari shine ya bata da kanshi. Daga nan ne ta wuce dakinta don yin wanka. Farouq dai Game room dinshi ya wuce don buga game. Dama kwana biyu jin shi yake yi wani iri don bai buga ba. ************** Yayi nisa a buga Game ne Zara ta shigo. Bayan shi ta tsaya tare da sa hannuwanta ta rufe mishi idanuwa. Hakan kuwa ya sa aka ci shi. Cikin masifa yace “what the hell” Da sauri ta zare hannuwanta tare da kai bakinta saitin kunnen shi tace “sorry” Janyota yayi ta fado jikinshi yace “ai baki isa ba, sai kin rama mun cin da kika ja aka yi mun” Tana dariya tace “Ya Farouq ai ban iya ba” Cakulkuli ya fara yi mata wanda yasa tayi ta ihu tana dariya tare da fadin “Ya Farouq don Allah kayi haquri bazan qara ba” suna cikin haka ne wayarta tayi ringing. Da qyar ta kufce daga hannun shi sannan ta dauki wayar. Sunan Saima ta gani. Bayan ta amsa ne tace “wai ku bazaku zo bane? Na ji Mamy tace jibi zaku tafi” A dayan bangaren Saima ce tace “gamu a cikin falon ki amma kuma bamu gan ki ba, kina ina?” Zara cikin murna tace “yeeeeey, gani nan” Ta kashe wayar sannan ta kalli Farouq wanda ya cigaba da buga game dinshi tace “su Safa ne, let me go and get them” sannan ta wuce ta fita yayinda yayi murmushi. Tare da su ta shigo Game room din yayinda suke ta qara yaba ma tsarin gidan. Marwa ce tace “kai, amma dai gidan nan fa ya hadu” Saima tace “ni Game room dinnan ma kawai za’a bani” Zara tana dariya suka qaraso wurin Farouq wanda ya sa pause. Bayan sun gaida Shi ne kuma suka shiga hira. Saima ce ta dauki control pad tace “oya Ya Farouq, tunda Allah ya kawo ni lets play” Zara wadda take zaune a gefen Farouq tace “play what? Abeg jor ki qyale shi” Su Safa suna dariya yayinda Saima ta kalle ta cikin mamaki tace “toh wai ke Zara meye ne matsalarki? Bakya so in buga ne ko kuma duk zafin kishi ne?” Farouq wanda yake ta matse dariyar shi ne ya zuba ma Zara idanuwa yayinda ta miqe tare da turo baki zata tafi. Da sauri ya sa hannu ya janyota ta fado kan cinyar shi ya rungume ta kamar qaramar yarinya ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “what is it my Baby angel? Game kawai zamu buga, Ko ba kya so ne?” Cikin shagwaba tace “toh nima ka koya mun sai mu dinga bugawa yadda ba sai ka buga da wani ba” Murmushi yayi yace “an gama Baby angel” yayi mata kiss a goshi sannan yace “kin amince ta buga yanzu?” ta dan juya ta harari Saima sannan tace “shikenan Ya Farouq” Su Saima dai dariya suke ta yi yayinda Zara ta tashi tana hararar ta. Saima tace “tab, wallahi Anty Ruqy ta shiga uku, Allah ya so ba gida daya kuke ba” Farouq yana ta dariya yayinda Zara ta kalli su Safa tace “ku zo mu je ku taya ni yin Lunch” suka miqe suka fita tare yayinda suka bar Farouq da Saima suna buga game. Wasa wasa dai Saima ta qara cin Farouq wanda yayi mamaki matuqa. A yanzu dai ya amince ta fi shi iyawa. ************* STORY CONTINUES BELOW Ko da suka zauna yin Lunch Farouq ne ya fara ba Zara abinci a baki yayinda su Saima suka kalli juna suna murmushi. Saima ce tace “gaskiya Ya Farouq duk kai kake shagwabar da Zara wallahi, yanzu abincin ma bazata iya ci da kanta ba sai ka bata?” Murmushi yayi yayinda Zara ta harare ta tace “toh me ya ruwanki, sarkin sa ido” Marwa ce tace “dama fa Anty Zara is very lazy, idan an biye mata ma komai sai dai ayi mata” Safa tace “ni ina mamakin yadda ma fa take yin wasu abubuwa” ta nuna table din tace “wai duk kalolin abincin nan ita ta dafa, I never thought..” Zara ta turo baki tace “dagaske idan baku yi mun shiru ba zan kore ku daga gida na” Gaba daya suka fashe da dariya yayinda Farouq yace “ayi musu afuwa Baby angel” Saima tana dariya tace “anya Baby angel ce wannan kuwa?” Zara ta harare ta tace “toh Baby devil ce ni ko me?” haka dai suka dinga kwasar dariya. Su Saima dai basu bar gidan ba sai bayan Sallan isha’i wanda direban Farouq ne ya mayar da su gida dayake Sadiq ya koma London inda zai rubuta final exams dinshi wanda daga nan ya kammala karatun shi na Phd kenan. ************ Wuraren qarfe tara da rabi na dare Farouq yana zaune a falon shi yana kallon CNN ne ya dauki wayar shi ya kira Ruqayya. A lokacin kuwa tana tare da Hajjaju wadda suke tsara tafiyar su zuwa gidan Malamin Hajiya Baraka a gobe. Yana waya da Ruqayya ne Zara ta shigo falon sanye cikin kayan baccinta na riga da wando. Direct kujerar da yake zaune ta nufa. Remote ta dauka sannan ta kwanta a kan cinyar shi ta canza channel zuwa Zee TV. Ji tayi yace “I am really missing my Junior, please ki gaida mun Hajjaju” can kuma sai yace “I love you too, bye” sannan ya kashe wayar. Ji yayi Zara ta saki wata ajiyar zuciya wanda ya sa shi saurin kallon fuskar ta yace “ya akayi ne na ji kina ajiyar zuciya?” turo baki tayi tace “nothing” Murmushi yayi yace “hey that was My wifey on the line” ji yayi tace “Allah ya bar ku tare” Fashewa yayi da dariya yace “wai dama haka kike da kishi? toh meye ma na damuwa tunda dai nan da wata daya zaki bar ni” Zuciyar Zara ce ta buga da ta tuno da cewa in less than a month zata bar gidan Farouq. Ganin tayi nisa a tunani ne yasa ya kai bakin shi saitin kunnen ta yace “ko kin fasa ne?”2 Da sauri ta tashi daga kwanciyar ta miqe zata tafi daki wanda yayi saurin riqo hannun ta tare da janyota ta fado jikin shi yace “I am sorry my Baby angel” Gani nayi ta kwanta a jikin shi cikin shagwaba tace “toh Ya Farouq ni ka daina kiran sunan Anty Ruqy a gaba na” girgiza kai yayi yana murmushi yace “an gama my Baby angel” Daga nan suka cigaba da kallon tashar Zee TV yayinda take ta bashi labarin series din da ake yi. (Zara Drama queen🤣) GIDAN MALAM COTONOU Zaune suke a gaban Malam inda yake ta bubbuga qasa. Gani nayi ya murtuke fuskar shi sannan ya dauki wata casbaha ya miqa ma Ruqayya yace “kama wannan mu gani” Ruqayya ta kama sannan ya riqe daidai inda ta kama. Yanzu ma gani nayi ya murtuke fuska sannan ya kalle su yayi gyaran murya yace “a gaskiya na dade ban samu irin wannan murdadden aikin ba, gaba daya kai na a kulle yake domin kuwa na kasa samo hanyar da zan warware miki wannan matsalar taki” A firgice Ruqayya take kallon Malam yayinda hawaye suka fara bin fuskarta. Hajjaju ce tace “yanzu babu abinda zaka iya yi Malam?” ji suka yi Ruqayya tace “ni ko kashe ta za’a yi ayi, kawai a batar mun da ita” Malam ya girgiza kai sannan yace “ai bazai yiwu bane, a yadda al’amarin yake babu yadda za’ayi in kashe ta sai lokacin ta yayi, yarinyar tana da tsaro sossai” ya cigaba da fadin “idan har nayi yunqurin salwantar da rayuwarta lallai daga ni har ku sai mun halaka” A yanzu kuwa hankalin Ruqayya ya kai qololuwa wurin tashi. Banda kuka babu abinda take yi. Hajiya Baraka tace “Malam ka qara dubawa dai idan akwai wani abinda za’a iya yi mana” Malam ya sake bubbuga qasa sannan ya dago kai ya kalli Ruqayya yace “akwai wani abu daya dai da zan iya yi miki sai dai kuma zaki biya kudi masu yawa” Cikin qaguwa da son jin zancen ne Ruqayya tace “idan dai kudi ne kar ka samu damuwa, menene zaka yi mun??” (Nima dai natsuwa nayi ina sauraron abinda malam zai ce🙄) Malam yayi gyaran murya yace “zan iya riqe miki mahaifar ta yadda bazata taba iya haihuwa a gidan ba” Dukda dai ba abinda Ruqayya ta so kenan ba ta dan ji sauqi. Ji nayi tace “ai hakan ya fi da ace ba’a yi komai ba, na amince da hakan” Malam yace “amma akwai sharadi” Tace “ina jin ka Malam” Yace “zan riqe mahaifar ta matuqar kina gidan, da zarar kin bar gidan toh komai zai warware. Ma’ana duk lokacin da kika rabu da mijinki aiki zai warware” Ruqayya tace “idan dai wannan ne babu matsala, ai babu abinda zai fitar da ni daga gidan Farouq. Ni da shi mutu ka raba” (Ni kuwa nace anya madam Ruqs????🤔)3 ****************** FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN ZARA)+ Tsaye take a bathroom din shi tana ta wankewa kamar dai yadda Mamy ta umurce ta akan lallai ta dinga kula da sashen shi. Zara dai tayi ya fi awa daya tana abu daya. Ni da nake kallonta har addu’a nake yi kada ta zame ta fadi domin kuwa yadda take yin aikin da gani kasan ba ta saba yin shi ba. Farouq ne ya shigo dakin rataye da towel a wuyan shi, da alama daga Gym ya fito. Wandon three quarter ne kadai a jikin shi. Kai tsaye bathroom din ya nufa don yin wanka. Tun yana bakin qofar shiga ne ya ji motsi wanda har yake mamaki domin kuwa a lokacin da ya fito zai tafi Gym ya leqa Zara wadda take kwance a dakinta tana bacci, bai yi tunanin ta tashi ba. Yana bude qofar kuwa ta juyo a tsorace. Sanye take da wani wandon three quarter hade da wata ‘yar qaramar T-shirt. Ta kama gashin ta a tsakiyar kanta. Ganin Farouq tsaye babu riga a jikinshi ne ya sa ta rude. Idanuwan ta ne suka sauka akan six pack abs dinshi yayinda ta qarasa rudewa. Gani nayi kawai ta saki bowl din da yake hannun ta tare da rufe idanuwan ta tana fadin “na shiga Uku, Ya Farouq..” Tana qoqarin guduwa ne ruwan da ta zubar ya zamar da ita. Ni dai gani nayi Zara tana ihu yayinda ta fadi a qasa. Farouq wanda yake tsaye yana kallon ikon Allah sai gani nayi ya fashe da dariya. Zara zaune dirshan a qasa tana kuka tace “Ya Farouq don Allah kazo ka taimake ni, ina ganin na karye”4 Yana dariya ya qaraso wurinta ya duqa yana kallonta yace “toh wai meye haka?” Cikin kuka tace “ba kai bane ka tsorata ni?” girgiza kai yayi yace “yi haquri Baby Angel” Gani nayi ta daga hannun ta tace “please help me up” Farouq ya dauke ta ya fito da ita zuwa dakin shi. Kan gadon shi ya dora ta sannan ya koma ya dauko balm a cikin First aid kit ya dawo ya zauna a gefen ta yace “please stop crying, ina ke miki ciwo?” Cikin kuka ta nuna mishi Butt dinta. Ji nayi yace “juya toh in shafa miki” Zaro idanuwa tayi tace “what?” cikin rashin fahimta yace “did I say something wrong?” Tana share hawayen ta ne tace “you are not supposed to see, ni ka bar shi ma ya daina ciwo” Dariya yayi yace “toh shikenan” ya miqe tare da fadin “bari in je inyi wanka” STORY CONTINUES BELOW Zara tana kallon shi har ya shige bathroom din. Ajiyar zuciya tayi tace “Ya Salaam, I am in trouble” Zara dai tana nan kwance a kan gadon Farouq ne ya fito daga wanka. Tana kallon shi ya nufi gaban dressing room dinshi yayinda ya leqo ta madubi ya hango ta tana kallon shi. Ganin ya kama ta tana kallon shi ne yasa ta juya fuskar ta tare da shigewa cikin bargon shi. Girgiza kai kawai yayi yana murmushi. Bayan ya gama ne ya nufi dressing room dinshi ya sa kaya, da alama ma fita zaiyi. Bayan ya feshe kanshi da turarruka ne ya dawo wurin Zara wadda har yanzu tana cikin bargo. Matsawa yayi daf da ita ya janye bargon daga fuskar ta sannan ya rungumeta ta baya tare da kwantar da kanshi kan kafadarta yace “hey baby angel, ya daina ciwo?” Zara wadda idanuwan ta suke a rufe girgiza mishi kai tayi alamar eh. Murmushi yayi yace “I am sorry” Fuskar shi a kan wuyan ta yayinda yake shaqar qamshinta ne yace “I love your smell” Zara dai idan Farouq yana mata irin haka gaba daya wani yanayi take shiga. Shi kanshi ya kula da hakan. Gani nayi yayi mata kiss a kumatu sannan yace “zan je asibiti ne, are you going to be okay?” tace “yes, amma dai ina so in je daki na” Farouq ya dauko ta ya kai ta dakinta ya kwantar da ita sannan ya zauna a gefen ta yace “forget about cleaning my side, I will do it myself henceforth kinji?” Zara tace “but Ya Farouq kasan fa Mamy ta…” kumatun ta ya ja sannan yace “kar ki damu ni nace I will do it myself” Murmushi tayi tace “thank you big brother” Miqewa yayi yace “zan turo miki one of your maids to watch over you before I return, is it okay??” Tace “don’t worry Ya Farouq, Hafsat tace mun zata zo anjima” yace “okay, as soon as I am done zan dawo, call me if you need anything” ta girgiza kai. Bayan Farouq ya fita ne Zara tayi ajiyar zuciya. A yanzu dai ta shiga rudani akan Farouq, A zahiri tana bala’in son yadda yake nuna damuwar shi akanta.1 Tana bala’in jin dadin zama da shi domin kuwa komai take so yana yi mata. Bata taba tunanin haka yake da sauqin kai ba. ji nayi tace “ya Salaam” A haka kuwa har bacci ya kwashe ta. ************ Jin muryar qawarta tayi tana fadin “toh gimbiya, tashi baccin ya isa haka” Zara wadda ta bude idanuwan ta ne ta ga Hafsat zaune a gefenta tana kallon ta. Murmushi tayi tace “babes how far, ke da kika ce sai da rana zaki zo?” Hafsat ta harare ta tace “bayan kin hada baki da Ya Farouq akan lallai sweetlove ya amince in taho inyi jinyar ki?” Zara ta tashi zaune tace “laaa, yanzu Ya Farouq sai da..” Hafsat tace “shut up jor, me ke damun ki? Yace wai kin samu minor accident, ya akayi? ina ciwon?” STORY CONTINUES BELOW Murmushi Zara tayi tace “dama na zame ne a bathroom dinshi kuma ma duk laifin shi ne but i think i am okay” Hafsat ta girgiza kai tace “Allah ya shirye ki bestie” Zara tana dariya yayinda ta miqe tace “bari inyi wanka in zo” Hafsat tace “je ki zo in baki wani albishir” Zara tace “haba bestie? Dan fada mun please” Hafsat tace “ni dai nace ki je kiyi wanka ki fito” da sauri Zara ta wuce dressing room don shirin wanka yayinda Hafsat ta kunna TV tana kallo. Kamar kullum sai da ta dade a bathroom din sannan ta fito. Hafsat ta kalle ta tace “mutum ka shiga wanka kayi awowi kamar zaka canza fata” Zara tana dariya tace “bazaki gane bane bestie” Bayan Zara ta gama shirinta ne ta dawo kan gadon tace “ina jin ki qawata, tell me” Hafsat tana murmushi tace “kin kusa zama Aunty, I am pregnant” Ihu Zara tayi tare da rungume qawarta tace “wow, I am so happy for you, wallahi I cant wait to see my baby. Allah ya sani ina bala’in son yara” Hafsat tana dariya tace “toh ai sai ki dage ki haifo kema” turo baki tayi tace “ba dai anan gidan ba”2 Cikin mamaki Hafsat tace “ban gane ba” Zara tace “uhm, manta da zancen bestie” Hafsat tana murmushi tace “in tayi tsami zamu ji” Zara tayi dariya. ************ Farouq bai dawo gidan ba sai wuraren qarfe tara na dare. Ko da ya shiga ya tarar da Zara kwance a kan kujerar falon qasa tana kallon tashar Zee TV. Hankalinta yayi nisa a kallon da bata ji shigowar shi ba. Muryar shi ta ji yana fadin “hello My Baby Angel” murmushi tayi ta miqe tare da rungume shi tace “Ya Farouq welcome, ka bar ni ina ta missing dinka” Murmushi yayi yace “sorry dear, wani emergency ne, besides ki daina missing dina dayawa” cikin rashin fahimta tace “ban gane ba Ya Farouq” Janyo ta yayi suka zauna a kan kujera yayinda ta maqale a jikin shi yace “kin san gobe zan koma gidan Ruqayya, na raba muku kwana bibbiyu..” Gani nayi ta tashi da sauri cikin bacin rai ta nufi dakinta ba tare da tace komai ba. (whoa🙄) Dafe kai yayi yace “I didn’t see this coming” Tashi yayi ya nufi dakin shi don yin wanka domin kuwa a gajiye yake. ************ Zara tana kwance a kan gadonta ne ya shigo dakin. Tsayawa yayi bakin qofa yana ta kallonta yayinda take ta ajiyar zuciya. Qarasowa yayi kan gadon ya kwanta daf da ita yace “hey, what is it?” cikin shagwaba tace “I don’t want you to go” murmushi yayi yace “are you falling in love with me already?” STORY CONTINUES BELOW Juya mishi baya tayi tace “that’s not it, ni dai kawai bana so ka tafi” ya girgiza kai yace “I have to my baby angel, that’s how it’s gonna be” Bai tsaya sauraron abinda zata ce ba ya tashi tare da fadin “what’s for dinner?” Gani nayi ta turo baki ba tare da tace mishi komai ba. Farouq dai dukda ya so ya lallashe ta haka nan ya qyale ta ya fita domin kuwa ya sani sarai idan ya biye mata rigima kawai zata yi mishi. Shi kuwa a tsarin shi yana da niyyar yin adalci a tsakanin su domin kuwa ya san illar rashin yin hakan. Yau kam shi kadai ya zauna kan dinning din ya ci abincin shi. bayan ya kammala ne ya wuce dakin shi. *********** Washegari da sassafe Zara ta hada breakfast ta koma dakinta ta kwanta. Ko da yayi shirin fita dakin ta ya nufa inda ya tarar da ita kwance bisa gado. Ji nayi yace “Good morning my Baby Angel” Zara dai turo baki tayi sannan ta juya mishi baya. Murmushi yayi ya qarasa wurinta ya duqo tare da daukar ta cak yayinda take qoqarin sauka. Ji nayi yace “idan baki natsu ba I will slap you” daga nan kuwa sai gani nayi ta natsu.3 (har na tuno Farouq a kwanakin baya🤣) Dinning ya kai ta inda ya zaunar da ita bisa kujera. Ko da ya bubbude zaro idanuwa yayi yace “when did you make all these” Zara dai shiru tayi bata ce komai ba. Gani nayi ya zuba blueberry pancake a plate sannan kamar kullum ya fara bata. Da farko qin karba tayi amma ganin ya canza mata fuska ne yasa ta bude baki. Sai da ta qoshi kamar kullum sannan ya fara ci. ji nayi yace “Allah ya sani cewa I am going to miss your delicious delicacies” da sauri tace “toh kayi zaman ka kawai anan mana” Murmushi yayi yayinda ya cigaba da cin abincin shi. Zara dai haka ta gama kumbure kumburen ta, tana ji tana gani Farouq ya tafi ya barta wanda ba zai dawo ba sai bayan kwana biyu. (An fara shifting kenan🤣… an koma home and away🤣) FAROUQ AL-HUSSAIN MANSION (GIDAN RUQAYYA) Wuraren qarfe goma na dare ne Farouq ya shiga gidan, dawowar shi kenan daga asibiti. Dakin shi ya wuce direct ya watsa ruwa sannan ya fito ya nufi dakin ta. Kwance take tana waya da Musty. Hankalin ta yayi nisa a wayar ne Farouq ya shigo dakin. Ji yayi tana fadin “wallahi mun je Cotonou ne tare da Hajjaju, kasan fa nayi missing dinka sossai” can kuma tayi shiru sai tace “okay, I will try” murmushi tayi tace “Junior is fine, I love you too. Bye” Farouq wanda yake tsaye ya gama sauraronta ne yace “hey who was that?” (Ghen ghen ghen🤔) A firgice Ruqayya ta tashi tsaye tana kallon shi. Qarasowa yayi cikin dakin ya tsaya a gaban ta tare da miqa mata hannu yace “give me the phone” (Kai🙄) A razane tace “Honey cousin dina ne fa” cikin rashin yarda yace “call him, ina so mu gaisa” Hannuwan Ruqayya na rawa tayi dialling number din Musty. Ko da ya amsa cewa yayi “hey love kin manta ki fada mun wani abu ne?” A sanyaye Ruqayya tace “ehm, dama Honey ne zaku gaisa, kasan fa har yanzu baku taba haduwa ba” Musty ya fashe da dariya tare da fadin “ya kama ki kenan” Ruqayya dai cewa tayi “toh ga shi nan” (Hehehehe🤣🤣) Farouq ya karbi wayar, bayan sun gaisa ne Musty yace “Allah sarki my In-law har yanzu dai bamu hadu ba, the last time da na zo baka nan” Farouq ya girgiza kai yace “haka ne, and I really want to meet you don na ga alama wifey tana ji da kai” Dariya Musty yayi yace “ai she is my favorite, I love her sooo very much” Farouq ne ya dan bata rai yace “easy bro, its my wifey you are talking about” Musty yayi dariya yace “My sincere apology” Farouq ne yayi murmushi yace “we need to set up a time, what do you say?” Musty yace “ba damuwa, zanyi tafiya gobe idan na dawo, we will insha Allah. Please take care of my sister” Farouq yayi murmushi yace “she is in good hands trust me” Ruqayya dai tana nan tsaye tana kallon Farouq yana waya da Musty. Gaba daya hankalinta a tashe yake yayinda ta kasa motsi. Ta sani sarai Musty dan iska ne kuma zai iya fadin wata Magana da zata iya zame mata matsala. Ganin Farouq yana sallama da Musty fuskar shi a sake ne yasa ta saki ajiyar zuciya. Farouq ya miqa mata wayar sannan yace “your cousin seems nice, I really want to meet him, please idan ya dawo do let me know” A sanyaye tace “toh Honey” (Ni dai ina daga gefe nace habawa madam Ruqs🤣) *********** A yanzu dai abubuwa sun birkice ma Zara, sati uku kenan da yin auren su wanda yayi daidai da saura sati daya Farouq ya sake ta a yadda suka yi plan dinsu. A kullum Farouq qara shiga ranta yake yi, gaba daya yanzu tunaninta duk na Farouq ne. A duk lokacin da zai koma gidan Ruqayya ji take yi kamar ta mutu. Gaba daya bata jin dadin rayuwarta sai ya dawo gidanta. A ‘yan kwanakin nan duk ta bi ta rage Magana. Kullum tana cikin tunani da calculations. (Ni kuwa nace Zara ta zama calculus🤣🤣) ************

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *