BA SONTA NAKE BA TAUSAYI NE CHAPTER 19

A kasalance yake amsa gaisuwar hajiya binta wadda tsabar kirsa taƙi bari shiya gaisheta a matsayin ta na babba harda russunawa tana sunkuyar da kai ƙasa.
Murya can ƙasa yake mata bayani kamar haka.
“Mama kuyi haƙuri da wannan dattijon ni na ɗauki nauyin baku adadin kuɗin da gidan zeyi”
Yafaɗa idanu lumshe.
Saukar kukan ta ƙasa ƙasa ke tashi tana furta.
“Shike nan kaima ya gama, Gaya maka aibuna wallahi makiri ne komi ya gaya maka ƙarya yake”
Girgiza kai yake yafara jin sarawar kai baya son kukan mace bare babba wadda zata kai ammin shi, shiya ma kasa gane mai gaskiya a tsakanin su dan haka ya ɗaga mata hannu alamar tayi shuru.
“Mama kuyi haƙuri Don Allah nidai zan baki kuɗin gida ki duba zumuncin Allah kuyi sasanci anan base ankai taiyara ba”
A wannan karon idanu ya zubawa basma wadda ta sunkuyar da kai kasa tana wasa da yatsun hannunta fuskar nan kamar tumatur amman hannayen ta baƙaƙe ƙirin alamun anci bilitin an more kenan.

Kuka hajiya binta take kamar zata shiɗe wanda tsabar makirci ne wanda sam kukan shiya danne murnar samun kudinta sabida idan tai saurin waskewa ze nuna cewar kamar tana murna da kuɗin dayace zaya bata ne kaga maganar kawun basmah zatai wa barrister tasiri amman daya ke makira ce setai kamar bata bukatar kuɗin ta cigaba da kukan ta.

Numfashi take ja da ƙarfi wanda basmah tai saurin riƙota tana cewa.
“Na shiga uku mama karfa ki bari ciwon ki ya tashi kar kema ki mutu kibi abba nifa kin fi min komai aduniya tafaɗa tana kuka!
Tausayi suka bashi dan haka seya ce suzo ya sauke su a gida shima gidansu ze wuce ƙiftawa basmah ido hajiya binta tayi wadda nan da nan ta soma zuwa mai godiyar daya ji ya shiga wani yanayi.

A hankali suka shiga motar shi lafiyayya wadda kallonta kaɗai ya kuma jefa hajiya binta da basmah halin ɗaukin ganin cimma muradin ransu.
Tafiya suke a hankali basmah na bashi kwatancen gidan su ai seya ga ma basu da wani nisa ashe tsiransu layi ka biyar da gidan su da gidan daya ke ginawa kuma layi huɗu bin kofar gidan yayi da kallo yana mamakin yadda baiga wata alama ta lalacewa a tare da gidan ba amman dayake baida magana yasa bayan ya sauke su ya zaro kuɗi rafar ƴan dubu ya bawa maman basma yana ɗan murmushi yace.
“Ai mama bama mu da nisa daku anan layin gaba nake gidan Alhaji Ali Dikko ɗan gwangila”
Zaro idanu tai a firgice sabida kowa yasan Alhaji Ali dikko shararren ɗan gwankila mai kuɗi tare da kirki da son taimakon al’ummah tabbas in ƴarta tai dacen auren ɗansa ai sun gama kuɗi.
waskewa tai tare da cewa.
“Kai yaro kasa na xaro idanu sabida ganin ɗan mafita lallai baka gado a sama ba gada kai tun usuli”
Bai ce komai ba yaja motar shi yayi gida sedai me gaba ɗaya ya kasa walwala da sukuni kasancewar sa bamai yawan magana ba, yasa tsayin kwanaki biyu babu mai gane a halin daya ke ciki sedai ammi ita kaɗai ta gane yanayin ɗan nata takwa tirke shi akan son jin matsalar sa amman yace mata babu komai.

Bayan sati ɗaya Aliyu ya kaiwa su hajiya binta kuɗin gida wanda akai masa kuɗi mai ɗan karen tsada anan ta turkeshi akan seya ci abinci amman yace a ƙoshe yake basmah kamar zatai kuka sabida yadda suka kashe kuɗinsu akan haɗin abincin wanda naman suna da tabbacin zuwan Aliyu a ranar domin yace ze kawo musu kudin.

Lemon kwakwa kaɗai yasha batare daya ci komai ba yayi musu sallama ya tafi sedai me tunanin wannan budurwa ya addabi Aliyu ko bacci ya kwanta ita yake kallo tana zuwar masa mafarkinsa babu shiri ya nemawa kansa mafitar zuwa wajan hajiya binta akan shifa yaga matar aure ranar hajiya kwana tai tanawa kanta kirarin taci dubu se ceto duk abin da sa gaba setaga bayan sa.

A hankali soyayya ta ƙulu a tsakanin Aliyu da basmah wadda zuwanta ɗaya gidan ammi ta gaisheta tana fita hassana kanwarshi ta dubi ammi tace.
“Nifa ammi wannan matar yayan batai min ba wallahi na tsani mutum mai shuru shuru asalin munafukai ne mutum sak yafi”
Ashe Aliyu na falo yana jin hassana bayan ya dawo daga raka basma ranar hassana seda tai zazzaɓin azabar duka yana huci yana cewa seya aureta yaga ɗan iskan daze takata ya barshi.
Da ido ammi ta bisa tana mamakin yadda ya doki hassana duk yadda yake son ƙannensa ko zazzaɓi suke yayta kaiwa yana komowa kenan akansu amman yau akan wadda ze aura ya xage ƙwanji yayi wa hassana dukan kawo wuƙa.

Addu’a tai masa akan Allah yasa basmah ta gari ce.
Cikin watan akaje tambayar auren basma wajan kawunta sosai su kawu usman suka yaba da dattakon mutumin wanda yayita jimantawa Aliyu auren basma amman dan kar ace bakin ciki yake yaja bakin sa yayi gum amman yasan wannan lauyan ne ke neman auren ta.

Sosai ɓangarori biyun ke shirin biki Aliyu kamar ze taka rawa dan murna komai Anty jidda ta siyo na lefe seyace bai yiba daga ƙarshe ma sarat ya tura dubai da maƙudan kuɗi taje ta haɗo akwatunan waɗanda ammi tai ta faɗan yayi almubazzaranci amman abba yayi mata faɗan cewar ita dai tasa albarka.
Ranar da yakai su ammi gidan sa daya gama sakin baki sukai sabida dukiyar daya narka ta kayan ɗaki daya ce baya buƙatar ko cokalin basmah komai yayi mata sosai ƴan uwansa suka dawo da santin gidan wanda ya lamushe miliyoyin kuɗi wajan ginawa da kuma zuba kayan alatun rayuwa ita kanta hajjiya binta tai santin gidan nan da nan ta fara kiran kawaye da danginta akan suzo suga gidan basmanta wadda za’a ɗaurawa aure nan da sati guda mai kamawa.
Kowa yaje gidan seyayi santi haka suka baro gidan suna farin ciki hajiya binta na buɗa kai ciki danginta.

Satin biki ya kama sosai ake shagali fati kala kala aka gudanar ranar juma’a aka daura aure amarya ta tare agidan mijinta cike da huɗu bar ƙawaye data uwarta.