Lumshe idanun nashi yayi tare da ɗaukesu daga kallonta tsananin tausayin yarinyar yana ratsa dukkan sassan jikinshi.
Tabbas inda yana da hali daya taimaki zuciyarta ya sadata da abin da take muradi.
A hankali ya sauko zuwa ƙasan karfet.
Da sauri ita kuma ummul ta matsa can nesa dashi janyo try ɗin abincin tayi tare da ɗaukar plate ta zuzzuba masa wainar ƙwai da soyayyan dankali se miyar hanta da albasa wadda take ta tashin ƙamshi se kunun gyaɗa daya sha madara.
Ta zuba mai wadatattu ta tura mai gabanshi.
Cikin nutsuwa ta miƙe tare da nufar ɗakin hajja dan ta basu waje.
Seda yaga ta ƙulewa ganinshi sannan ya ɗauke kanshi daga hanyar data wuce ya sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya da sauri ya janyo plate ɗin ya ɗora spoon ya soma kai lomar abincin bakinshi wani irin daɗi ya mamaye bakinshi.
Murmushi hajja tayi tare da cewa.
“Aliko tun da ummi ta tashi kake bin ta da kallo kodai ƴar gida zakuyi?”
Bai daina cin abincin nashi ba kuma bai bata amsa ba har seda yaci mai ɗan dama sannan ya ture abincin daga gabanshi ya ɗauki ruwa yasha kaɗan.
Sannan yayi hamdala ga sarki Allah.
A nutse ya dubi hajja yace.
“Hajja wani irin magana kike haka? kinsan a wani hali na fara ganinta? hajja ko kaɗan bana son ta, Ban taɓa jin sonta araina ba Hajja BA SON TA NAKE BA TAUSAYI NE! kaɗai narke acikin zuciyata tare da tarin ruɗu kala-kala tabbas ganin yarinyar nan agidan nan ya sakani a shakku na yadda a farko na ganta a hotel sannan na dawo na ganta agidan nan duk da na shaida ƴar can gidan ce to amman mai ya kaita hotel? dik da ni lamarin wani bai shafeni ba dan bana ɗora idanuna akan abin da bai shafeni ba amman wannan ya tsaya min araina”
Ya faɗa yana mayar da numfashi sama sama alamun baya jin daɗi ajikinshi.
Ga mamakin shi hajja batai wani acting daze nuna taji mamakin maganar daya faɗa ba na cewar yaga ummul a hotel sema murmushin data cigaba dayi wanda bai gushe gareta ba.
“Aliko banyi mamaki dan kace kaga ummi a hotel ba amman tabbas nina san iskanci baze kai ummi can ba sedai ɗaukar fansa wadda rayuwarta da hakan ta taso! makauniyar ƙaddara mai ɗauke da ƙalubalan rayuwa sune ummul aba’isin ɗin jefa yarinya ƙarama cikin garari dan Allah Aliko idan na baka labarin ummi ka taimaki rayuwarta ka amshi soyayyarta ka aure ta ko hakan zesa wannan tausayin ya juye ya zama so! ada nayi niyyar biyo maka ta bayan gida sena ga kuma cewar gwarama ayi mai yuwuwa”
Hajja ta ƙarashe maganar da ƙarfin gwiwar ta.
Jin kanshi yake kamar ze tarwatse tayaya da idanunsa yaga yarinya acikin hotel sannan har hajja tazo tana bada shaida akan cewa wai ba iskanci taje ba!
Shafa kanshi yayi tare da cewa.
“Hajja hotel matattara ce ta mutane kala kala kowanne kuma akwai abin da ya kaishi cikin sa sedai ita a yadda na ganta a shigar dana ganta a yanayin dana ganta hajja na shiga shakku”
Ya faɗa murya can ƙasa.
Murmushi hajja ta kuma yi kana ta fara magana.
“Aliko ummi ba iskanci taje yi hotel ba ka nutsu ka cire zargi cikin zuciyarka fatana kayi min alƙawari muddin na baka labarin ummi zaka taimake ta?.zaka aure ta?”
Hajja ta faɗa tana share hawayen fuskarta.
Jinjina kai ya shiga yi idanun shi ƙurr a fuskar hajja.
Murmushi ta sauke tare da fara bashi labarin kamar haka……………………………….
Tunda ta fara magana yake kallon ta tsigar jikinsa na wata irin tashi gaba ɗaya idanunshi ya kaɗa yayi wani irin jajir jikinsa na wata irin rawa.
Dafe kanshi yayi yana juyawa wani irin rauni ya mamaye ilahirin jikinsa.
Hajja ta ƙare tana sakin kuka!
Da sauri ya matso gaban tsohuwar ya rungumeta shima yana jin inda yana da hali dayayi kukan.
Amman daya ke namijin duniya ne seya dake seda ya tabbatar hajja ta dena kukan sannan ya koma da baya yana fesar da zazzafan numfashi.
“Hajja an kai shekara nawa kuma mai yasa baki shaida min ba?”
Cikin mayar da ajiyar zuciya hajja tace.
“Za’a kai shekaru biyu lokacin kayi aure kasan tun da kai aure shekara biyar baka taɓa zuwa nan ba tayaya zakaji?”
Jinjina kai yayi tare da matse yatsun hannunsa suka ce ƙas! sau uku sannan ya dubi hajja da nutswar sa da kamewarsa yace.
“Karki damu hajja zan taimake ta amman hajja inda kin gayawa su ammi maganar nan da kin ɓata lamarin ai sabida ba kowa ne ze fuskanci abin ba kamar yadda na gaya miki na ganta a hotel inna gayawa su ammi abba baze yadda ba ina son wannan maganar su tsaya a iya mu please har na kammala shirina”
Yayi maganar yana nuna mata iyakacin gaskiyar shi acikin idanunshi.
“To yaya alƙawarin mu?”
Ta tafaɗa tana kallon shi.
“Yana nan hajja zan aure ta kodan na kare martabar ta domin ni har yanzu ina hangen abin da baku hanga ba tayaya shekara har biyu sannan kuma kuce kuna kan ra’ayin ku?”
Yafaɗa yana tsareta da idanun shi.
“Karka ɗora zargi kan auren ku domin aure da zargi baya yuwuwa Aliko”
Hajja ta faɗa tana mai ƙarfafa masa gwiwar sa.
Bai iya ce mata komai ba face miƙewar dayayi.
“Hajja zan tafi idan naje gida zan shaidawa abba kudai kawai ku kasance cikin shiri koda yaushe su abba zasu iya zuwa nema min auren ta”
Murmushi hajja ta saki tana mai karantar yanayin shi yayi kama da wanda yake cikin tsananin kishi tausayi da rashin sanin makama.
“Ummi zo ze tafi”
Muryar hajja ita ta fito da ummul wadda take cikin ɗakin hajja da sauri ta ƙaraso falon lokacin har ya fice daga falon da sauri domin ya tsinci kanshi da rashin son ganinta yana maijin dana sanin alƙawarin dayayi ma hajja na aurenta.
Ganin ya fita ya sanya hajja tace mata tayi sauri ta bi bayan shi tayi masa sallama.
Yana gab da buɗe ƙofar gate tai saurin cimmai ta dakata agaban shi tana mai tsare shi da idanunta dasu ka ciko da ruwan hawaye.
“Tafiya zakai kuma zaka iya yin tuƙi a haka bayan baka da lafiya?”
Tafaɗa tana tsire shi da idanunta.
Kallon ƙurullah yake mata mai cike da tarin ma’a noni da dama batare daya ɗauke idanun shi akan ta ba yace.
“Kin tilassa ma hajja kina son ta nema miki aure na? to ina so ki buɗe kunnen ki da kyau kiji ni”
Yafaɗa yana kallonta.
Jikinta ne ya tsananta rawa sam batai zaton hajja zata gaya masa ba.
“BA SON KI NAKE BA TAUSAYI NE! yes tausayin ki nake ummi kairiy zan aureki abisa wasu dalilai dana barwa kaina sedai fa ki sani koda na aure ki jinginar dake zanyi agidan mahaifa na domin matata bata raba soyayyata da kowa ba tabbas taji labarin ki zata iya halakaki dan haka ki shirya yadda zaki zauna da mahaifana domin ni bakya cikin tsarin matan dana ke so ban taɓa sonki ba sedai kina tsananin bani tausayi musamman da hajja taga gaya min koke wacece nasan in bani na taimaka na aure ki ba haka zaki ƙara komawa jagaliyar karuwan………..
“Dakata Aliyu”!!
Tayi saurin katse shi gaba ɗaya jitai komai ya fitar mata aranta.
“Mai yasa zaka min haka mai yasa kake son shiga cikin jerin maza marasa adalci? shin ƙaddara ba zane bace nina kai kaina inda kake tunani ba ƙaddara bace ko kaima kana son shiga cikin jerin wasu daga cikin ahalina da suka ƙi amsar ƙaddara ta bani da wani gata a yanzu sena Allah seku ma kai dana ɗauki soyayyar ka na ɗarsawa raina Aliyu karka zama namiji mara adalci aso! duk macen da zata kalli idanun namiji tace tana sonsa wallahi ta gama masa komai domin mace bata furta yaudara! sabida Allah ya ɗora min son ka zan zama wulaƙantacciya a wajan ka to karka aureni ka gani idan bazan yi auren ba”
Tafaɗa tana fashewa da wani irin kuka!
Dafe kanshi yayi wanda har lokacin ciwo yake masa da wani irin zafin nama ya janyota ya manne ta da jikin gate ɗin ya rungumeta da zafi zafi yake shafa gadon bayan yana jin zuciyarsa na barazanar tarwatse wa………….
Wai waye Adon tafiya*
Bahaushe yace wai waye adon tafiya ina son duk wani makarancin wannan labari daya saurara ya bada lokacin sa domin karanta asalin labarin wanda nai masa laƙani da wai waye sabida karantawar ne kaɗai ze baka haske akan manufar labarin harma da saƙon dake tafe dashi.
Ummul kairi Abubakar shine asalin sunanta, malam Abubakar shine mahaifin ummul haifaffan garin kano kuma ɗan gargajiyar cikin unguwar tunga anan aka haifeshi har ya girma ya zama matashi.
Iya karatun arabiya kaɗai ya samu amman Allah bai sanya ya samu karatun zamani ba, Su uku ne ƴaƴa a wajan mahaifansu wanda tun dama suka taso mahaifinsu ya rasu mahaifiyarsu ce saura.
Malam Abubakar irin mutanan nan ne masu ɗan banzan surutu uwa uba kuma akwai shi da faɗa kamar ze ari baki tun yana ƙarami yake da wannan hali najan faɗa har zuwa girmanshi anan kusa da gidansu ya samu matar aure mai suna hadiza wadda takasance kurma amman tana ɗanji kaɗan kuma tana magana sama-sama.
Cikin hukuncin Allah Abubakar ya auri hadiza anan kusa da gidan mahaifansa yayi ginin ƙaramin gida na ƙasa dayake sauran ƴan uwan shi guda biyu duka mata ne kuma sunyi aure tuni,
Cikin hukuncin Allah zaman Abubakar da hadiza zamane na soyayyah yana fita kullum yayi aikin shi na leburanci wanda baya dawowa se yamma yaci abinci ya koma majalissa ahaka hadiza ta samu ciki wanda watan su tara cif da aure ta haifi ƴarta mace.
Zokuga murna wajan su abubakar na samun wannan ƙaruwa ranar suna yarinya taci suna Basira bayan basira hadiza ta haifi zainab bayan zainab hadiza ta haifi sakina to rayuwa na tafiya kullum nauyi ke ƙara ɗoruwa akan malam abubakar gefe ɗaya kuma baƙin cikin haihuwar ƴaƴa mata tana nausar shi.
Cikin wannan lokaci aiki yakai shi ƙiru na ginin wata makarantar kwana lokacin basira na shekara uku zainab nada shekar biyu sakina nada shekara ɗaya sabida hadiza kurma konika take yi.
Bayan tafiyar Abubakar ƙiru acan Allah ya haɗashi da wata yarinya bafulatana mai suna hassana wadda take kawo masu tallen nono inda suke aiki.abu kamar wasa Abubakar yace yana son hassana da aure.
Abokan tafiyar shi suka kada baki suka ce masa.
“Kaiko Abubakar hannun ka bai isa ya cuɗa bayan ka ba har kake jiran wani ruwan wankan?”
Buɗar bakin sa seya ce.
“Ai rayuwar duniya ƴar saka kaice komai kaga dama kayi”
Sanin halin masifar sa yasa suka ja baki sukai masa shuru.
Kafin su kammala aikin abubakar yaje har gidan su hassana waɗanda suke tagwaye wajan mahaifan su ita da ƴar uwarta hussaina.
Sosai malam jauro mahaifin hassana yayi na’am da abubakar har suka tsaida magana bayan ya koma gida ze aiko ai maganar biki.
Hakan ce ta faru domin bayan dawowar su gida yajewa da mahaifiyar shi mai suna innah maganar auren hassana sosai innah ta rufe ido take zazzaga mai masifa akan cewa.
Damme ze tarko aure bayan yasan cewar bai gama wadata iyalinshi ba sannan gidan shi duka ɗaki uku ne ɗaya na yara ɗaya nashi ɗaya na hadiza ina ze aje wata matar.
Buɗar bakinshi se yace shidai yana da ra’ayin ƙara aure ko babu komai ya sami arziƙin haihuwar ƴaƴa maza.
Murmushi innah ta sanya tare da cewa.
“Habu kenan ga talauci ga buri”
A zuciye ya tashi yabar gidan yaje gidan kawun sa yayi masa maganar shima dai kamar ta innah ɗin yayi domin faɗa yayi masa akan yadda sha’anin duniya yake tayaya hannun ka bai cuɗi bayan ka ba zaka ƙaƙalo wa kanka aure.
Haka ya tashi daga gidan kawun nashi ya nufi gidan maƙocinsa yayi masa bayanin komai wanda shiya je wajan innah ya bata baki badan taso ba ta amince aka tafi ƙiru kai kuɗin auren hassana.
Sosai suka dawo da murnar karamcin da mahaifan hassana sukai musu.
An saka aure wata uku wanda zuwa lokacin Abubakar ya gyara ɗakin sa ya mayar a mazaunin na amaryar shi wanda hadiza dan tsabar kishi jitai kamar ta sanyawa gidan wuta abinka da kurma nan da nan ta haukace ita ce harda yaji innah ta bata haƙuri ta dawo da ita.
Kowa a unguwar zagin malam habu yake sabida yadda ake ci da ƙyar agidan shi ake sha da ƙyar amman yaje ya kankamo aure.
Shikuma ya shafawa idanun shi toka yayi biris da kowa ya cigaba da hidimar shirin uren shi wanda yace hadiza in bazata zauna ba ta zube mai yaranshi tabar masa gida.
Haka hadiza tai haƙuri ta zauna ta cigaba da kula da yaranta domin tace koba komai zata zauna domin taga bayan hassana amaryar tata.
Haka kwanaki sukai ta tafiya kwanci tashi biki ya rage sauran kwana ki biyu shiri kota ina yana kan kama haka Allah ya nuna ranar ɗaurin aure wanda bayan an ɗaura aure baffan hassana ya damƙawa malam habu amanar ɗiyarsu da ƙyar aka raba hassana da hussaina wadda a rana ɗaya akai auren su ita hussaina tana nan cikin garin ƙiru ita kuma hassana tayo nan tunga gidan malam habu wajan inna aka soma kaita bayan tai mata nasiha aka wuce da ita ɗakinta.
Fafur malam habu yayi yayi da hadiza akan tazo su gaisa da hassana taƙi fitowa haka ya kaɗe babbar rigarsa yabar mata ɗakin yayi na amaryar shi bayan cin kaza da komai malam habu ya umarceta dasuyi sallar ma’aurata bayan komai na ibada ya kammala suka ja labule ihun hassana ya cika gida amman hadiza tai buris koda safe kasa fitowa tayi seda malam habun yaje ɗakinta sannan ta rufeshi da faɗa haka ya tashi yabar mata ɗakin ya koma na amarya wadda zazzaɓi ya rufeta da taimakon shi ta gyara kanta.
Sannan ya samo mata abin karin kumallo taci.
Haka rayuwar ta cigaba da tafiya a hankali hassana ta soma fuskantar zaman gidan malam habu da matar shi hadiza kurma wadda ƴaƴanta ke kiran da suna ummah!
Hadiza ba mutunci ƴaƴanta ba kunya.duk da ƙanƙantar su basu fasa zagin hassana ba kuma hadiza tai buris taki ɗaukar.mataki hakan yasa hassana ta tattarasu ta watsar kasancewar ta mace mai hakuri.
Haka hadiza zatai ta zagin ta a hankali ba damar ta rama sabida hadiza kurma ce koda ta zagenta ma baji zatai sosai ba.
Ta ɓangaren malam habu yana kokarin kawo garin tuwon dare wanda shi za,a ci da daddare aci da rana in yay ragowa a kwaɗa da daddare nan da nan hassana tai baƙi ta rame.
Watanta biyar ta sami ciki sedai bai kai ko ina ba ya zube, haka ta kuma samun ciki na biyu shima ya zube lamarin ya soma bawa iyayen hassana tsoro abinka da fulani nan suka dage mata da addu’a haka nan kuma ta kuma samun ciki na uku shikam seda ya ma fito amman ya zube lokacin ka dubi hassana bazaka shaidata ba sabida yadda ta rame tai baki ga talauci gashi bata gayawa mahaifanta komai kasancewar ta mace mai zurfin ciki gasu a nesa suke bare su dinga leƙo wa.
Rayuwa na tafiya shekaru naja yanzu haka hassana tana cikin shekara ta biyar da aure amman har lokacin cikinta bai samu tsayawa ba sannu a hankali sukaje asibiti akai mata daurin mahaifa wanda aka ce zata ɗan huta kafin aga mai Allah zeyi.
Dayake malam habu yana son ta yasa yake lallaɓata lokacin baya samun aikin ma sosai amman haka yake fita yayi dako domin ya samo musu abin da zasu ci.
Ita kuma hadiza tana dambu da rana na sayarwa da shinkafa da wake bayan an kwancewa hassana ɗaurin mahaifa ba jimawa ta samu ciki sosai ta dage da addu’a akan Allah ya bar mata wannan cikin don itama tana son ganin ƙwan ta aduniya, cikin hassana yana da wata bakwai Allah yayiwa innah rasuwa mahaifiyar malam habu sosai aka shiga rudun mutuwa bayan sadakar arba’in malam habu ya ɗaga gidan innah ya sayar aka raba gado inda ya samu jarin buɗe kantin saida kayan masarufi.
Lokacin da cikin hassana yakai wata tara wannan lokacin aka tada gyaran gidan innah wanda yake makotansu wanda malam habu ya sayar, ba jimawa aka tare agidan wata tsohuwa ce ta tare wadda ta shigo har gidan su hassana tai musu sallama a matsayinta na makociyar su………