Cikin nutsuwa ya ƙarasa cikin bedroom ɗin hajja murya can ƙasa yayi sallama wadda ta tsaya a iya fatar bakinshi.
Tsaye yayi a bakin gadon ya zuba mata ido yana kallon yadda jikinta yake rawa ta cikin bargon data rufa ajikin nata.
Yafi ƙarfin mintuna goma a tsaye yana auna yadda zeyi ya tayar da ita acikin yanayin daya same ta.
A hankali yaja ƙafafunshi kamar mai tsoron ƙasa ya ƙarasa gaf da gadon ya sanya ƙafa yaɗan bugi gadon kaɗan A hankali ummul taɗan zabura tare da furta.
“Wayyo Allah! dan Allah karka kuma kayi haƙuri na dena na dena”
Muryarta ke tashi cikin wani irin ƙaraji! rintse idanu yayi alama ta nuna mafarki take wanda sautin maganar mafarkin nata ta fito fili, ɗan tsaki yaja ya kuma dukan gadon da ƙafarshi
Wannan karon ƙara tasan ya kaɗan tana jan ajiyar zuciya ƙaƙƙarfa.
“Khairy! khairy”
Yake kiran sunanta ahankali.
Cikin nutsuwa takejin saukar muryar wanda batai zato ba acikin kunnuwanta ahankali take dai dai ta nutsuwarta wadda ta rasa acikin mafarkinta.
Yun ƙurawa tayi ahankali tana rintse idanunta sannan ta tashi daga kwanciyar data yi.
Ganin yana gab da ita ya sanya taɗan ja baya ta matse jikinta acan ƙarshen gadon ta cure kamar mai jin sanyi wani irin ƙaƙƙarfan kuka ne ya tawo mata batare data shirya masa ba.
Kukan take da iyakacin ƙarfin ta tana jan ajiyar zuciya mai ƙarfi.
Rasa yadda zeyi da ita yayi, se kawai ya tsaya tare da harɗe hannunsa a saman kirjinsa ya zuba mata dukkan idanunsa yana binta da kallo.
Cikin nutsuwa ya ƙarasa inda ta raɓe murya can ƙasan maƙoshi yake furta mata.
“Ke bani son sha shanci miye aka maki kike faman ɓare baki kina ma mutane kuka?”
Bata bashi amsa ba se cigaba da kukan nata data yi.
Rintse idanu yayi ko kaɗan baya son hayaniya arayuwar shi musamman kukan mace yana sanya wa jikinsa ya mutu.
Wannan karon a hankali ya bita.
Samun waje yayi can gefenta ya zauna tare da kallonta kaɗan yace.
“Ɗago fuskar ki malama ki dube ni”
Yafaɗa muryarshi adake!
A hankali ta sanya hannu ta goge hawayen dake Zubo mata.
Tare da ɗago fuskar ta data yi jajir ta dube shi batare data iya janye idanunta akan shi ba.
Wani irin sahihin kyau yayi mata wanda take jin dama zasu dauwa ma a haka tana kallon shi.
Yana da wani irin baiwa ta musamman wanda ba kowa ne ze lura da hakan ba seya zauna dashi Allah ya bashi abubuwa da dama musamman nagarta tare da kyawun zuciya da tausayi.
Baya cikin jerin maza masu mugun kyau! sedai yana daga cikin jerin nagartattun maza waɗanda kowace mace take burin taga ta mallaka! kyawunsa sassanyan kyaune mai kwanciya a zuciya.
“Sabida karki sha magani yasa kika dame ni da kuka?”
Muryar shi ta katse ta acikin tunanin data faɗa.
Janye idanunta tayi daga cikin nasa tare da ɗan turo bakinta gaba kaɗan.
“Nifa bana jin daɗi zazzaɓi ke damuna shiya hanani shan maganin”
Tafaɗa tana wani haɗe fuska kamar wadda zatai kuka!
“Hajjah zatai maki ƙarya ne?”
Yafaɗa yana ƙoƙarin saka idanun sa cikin nata.
wasa take da yatsun ta a wannan karon batai magana ba.
Ɗan sassauta fuska yayi tare da ɗan matsota kaɗan.
Duk girmanshi ya cika mata idanu da ɗakin.
Murya can ƙasan maƙoshi ya furta.
“Kiyi haƙuri kisha magani duk wani ciwo in ba’a shan magani wallahi baya tafiya ta sauƙi ki ɗaure kisha ki shafa wannan cream ɗin shima in Allah ya yarda zuwa gobe zakiji kin warke”
Yafaɗa yana wani mayar da numfashi kaɗan kamar wanda yayi gudu!
Girgiza kai tashiga yi tana zubo da hawaye tasan maganarshi gaskiya ne gareta sedai ita ko kaɗan bata ƙaunar magani.
Bata kai dayi mai magana ba taga ya miƙe tsaye ya fita daga ɗakin ba jimawa ya dawo hannunsa riƙe da cup ya dire a gabanta.
Tare da ɓallo mata maganin guda ya miƙo mata babu musu ta karɓa yana tsaye akanta ta haɗiyi maganin tana wani yamutsa fuska kamar mai shan maɗaci.
Amsar cup ɗin yayi ya fita waje mintuna kusan biyu suka dawo shida hajja abin mamaki da kanshi ya shiga toilet ya haɗo ruwan ɗumi cikin bawo ya sanya tawul aciki ya fito ya miƙawa hajja tare da furta.
“Ina falo zan ci abinci kafin ku kammala ke kuma ki mata gardama karki fasa”
Yafaɗa tare da fita falo.
Da ƙyar ummul ta yarda hajja ta taimaka mata wajan gasa wajan ta shafa mata cream ɗin wanda babu abin da ummul take se kukan shagwaɓa tana matso hawaye!
A haka suka gama hajja takai bawon bayi ta dawo tana mata dariya tana cewa.
“Ke kam ummi raguwa ce ahaka zamuyi wankan jegon lallai duk mai maki wankan jego ze kwashi takaici”
Tafaɗa tana dariya.
Turo baki ummul dake zaune rashe rashe a carfet ɗin hajja tayi wadda take ta faman zubo da hawaye kafin tace.
“Allah hajja bakiji zafi ba wallahi Shikam yaci ka mugunta shine ze haɗo ruwan da zafi”
Murmushi hajja tayi tana cewa.
“Ai ni mamaki ma abin ya bani lallai kinci sa’ar Aliko da har ya tsaya ya kula dake! wanda ƙannen shima in suna ciwo suna kuka zane su yake amman ke ai kinci sa’ar shi”
Hajja ta faɗa tana ficewa a ɗakin.
“Nikam ba wani sa’a se wahalar daya hassasa mini”
Tafaɗa tana mai shafo wajan wanda yade na mata zafin kuma zazzaɓin ma yaɗan soma sauka ba kamar ɗazu ba.
Ya gama cin abincin ya kunna TV yana kallon labarai hajja tayo sallama falon.
Fuskarshi ɗauke da murmushi yake amsawa hajja tare da cewa.
“Har kun gama?”
Murmushi hajja tayi.
“Da ƙyar muka gama wannan yarinya badai kafiya ba,duk wanda ze mata wankan jego seya shirya dambe”
Lumshe idanu yayi batare daya ce mata komai ba ya miƙe yana duba wayar shi tare da fiddo dukkan girman idanunshi waje.
“Hajja 11 ta kusa fa bara na ƙarasa gobe nake son tafiya insha Allahu amman kafin na tafi zan shigo na maki sallama”
Yafaɗa yana ƙoƙarin fita.
“Amman meya sa bazaka kwana anan ba tunda akwai ɗakuna naga an fara yayyafi”
Murmushi yayi wanda ya ƙara haska kyawun fuskarshi.
Yaɗan shafo kanshi kaɗan.
“Haba hajja ada dai na kwana amman yanzu ina magidan ci ina zan kwana gidan…….”
Filo ta kwaɗo mai tana cewa.
“Ni zaka cewa haka to babarka ma nina haifeta bare kai”
Dariya yake wadda tai masa mugun kyau yana mai kallon hajja data haƙiƙance tana ta surfa masifa.
“Allah ya huci zuciyarki hajja akwai ayyukan dazanyi da system shiyasa zan koma”
Yafaɗa yana mai dena dariyar daya keyi.
“ayyo to shikenan kaje ka ma ummi sallama seka wuce”
tafaɗa tana mai mayar da hankalinta wajan tv dan hajja tana tsananin son kallo.
Ɗan haɗe ran shi yayi kaɗan tare da cewa.
“Miye haɗina da ita hajja wannan ma bada maganin arziƙin ki taci ay”
Yafaɗa yana mai ƙoƙarin ya fice.
“Aliko karka fita kaje kawa ummi sallama ai babu daɗi yarinya babu lafiya ka kasa yi mata sallama”
Babu yadda zeyi haka ya koma da baya zuwa bedroom ɗin hajja daga Bakin ƙofar ya tsaya yana kallon ta yadda take ta faman saka hannu ta cikin rigarta tana shafo wajan ciwon.
A ranshi yake ayyana wannan yarinya ta cika raki.
Kafin ya ƙarasa ciki yayi sallama wadda ta bayyana gareta.
A hankali ta amsa mai batare data dubi inda yake ba.
“Ya jikin?”
Yafaɗa kamar an masa dole.
“Da sauƙi”
A hankali tai furucin.
“Zan tafi seda safe don gobe nake son komawa garin mu”
Yafaɗa kamar baya so.
Lumshe idanu tayi kirjinta na dokawa kaɗan kaɗan tace.
“Mai yasa baza ka kwana anan ba dare yayi fa sannan ruwa ake duba kaga window”
Tafaɗa tana mai nuna masa window ɗin da hannunta.
“Kawai sena kwana anan dan baki da hankali ke koda yaushe kin fi son mu keɓe da juna salon na kwana anan ki lallaɓa ki bini ɗakin dana kwanta ai ko rashin shan maganin ki ma gulma ce dan kinsan zan zo ne shiyasa kika ƙi sha dan mu keɓe ko?”
Yawani faɗi maganar cike da rainin hankali.
Ɗimauce wa ummul tayi da jin sharrin daya lafto mata.
Shura ƙafafunta take tana faman sakin kuka ƙasa-ƙasa.
“Allah ya saka mini ni wallahi ba haka bane”
Tafaɗa cikin kuka!
Dariya ya saki mai ƙayatarwa tare da saurin ficewa daga ɗakin ya tsincin kansa cikin nishaɗi da shagwaɓar datai mashi ayan zu.
Bai tsaya wajan hajja ba yayi saurin fita waje.
Wanda hakan yayi dai dai da sanda ruwan ya kuma gocewa da tsananin ƙarfin gaske…………