BA SONTA NAKE BA TAUSAYINE CHAPTER 16

Bayan taci abinci ta ɗan kwanta abin ka da jikin talaka tuni bacci yayi awon gaba da ita sama-sama cikin baccin ta taji tashin maganganu masu kama da faɗa acikin tsakar gidan nasu muryar hadiza ce ke tashi tana cewa.
“Kaga malam baka isa kazo ka sakani agaba nida yarana ba ita matar so ka barta da auren ka aka tana fita tun safe bata dawowa se dare ai baka taɓa bita kanta ba duk abin duniyar data ke shigowa dashi bata baka takai yaranta makaranta suna ɗaga mana kai, seni daka raina zaka saka agaba ɗan cinikin danai ka rance idan na hana ka hauni da cin zarafi wallahi wannan mutuwar zuciya ta wasu mazan hausawan tana cutar su”
Tashi hassana tayi tsam daga kwanciyar ta zauna sosai ta fara jin maganar malam shi kuma.
“Ke hadiza dakata ke har kina da bakin cemin mai matacciyar zuciya kin manta da taimaka miki nayi na aureki sabida kurmantar ki babu mai zuwa wajanki seni dana ɗauki lalura, Kuma hassana da kike maganarta ai nagaya mata cewa itace uban yanzu nina zare hannuna akan ta ita da yaranta ayi dai mugani in ruwan ido ze dafa shinkafa”
Yafaɗa cikin ɗaga murya.
“Ahayye! shagali to ai bari kaji da namiji irin ka malam gwara zawarci kai to meye marabarka da gawa agidan nan mai kake mana maika tsinana mana ka kashe zuciyarka a banza kaiba musaki ba,ko ita hassanar da kake tutuya kabar mata yaranta ai ba wata uwar kake tsinana musu ba yara da ran ubansu amman suna yawo kamar marayu sabida mutuwar zuciyar mahaifin su……..
Tas!!!
Ya wanke hadiza da mari hannunsa yana rawa yake ce mata.
“Ki fita a idanuna hadiza in kika ƙara magana sena sake ki! kuma bazan baki ƴaƴanki ba suyi bara tunda ubansu mai mutuwar zuciya ne”
Yafaɗi haka kuma ya tsugunna ya kwashe ƴan canjinta tas yayi ficewar sa tukubar mai tsire.
Zaman ƴan bori hadiza tayi a tsakar gidan tana rusa kuka!
Ƴaƴanta da suke laɓe a ɗaki suka fito suka cicciɓeta sukai ɗaki da ita.
Abin duniya duk yayiwa hadiza yawa gaba ɗaya komai ya fice mata akanta ga jarabar babansu basira ga takaicin sauyin da hassana ta samu a kwana biyu.
Duk abin da sukai hassana tana jinsu bata ko tanka ba, bare ta fito har wajan tara yaranta suka dawo daga makaranta abinci ta zuba musu suka ci tana tambayarsu wuninsu har sukai bacci.

Wajan sha ɗayan dare malam habu ya shigo gidan aɗakin sa ya yada zango, Tunda dama gidan ɗakuna uku ne to matan ke zuwa ɗakinsa ranar girkinsu subar ƴaƴan su a ɗakunan su.
Ita dama hassana ta jima rabon ta da miji tun bayan cin mutuncin dayayi mata itama seta fita daga harkan shi sam ta nuna baya gabanta.

Malam habu zamansa keda wuya a ɗakin ya haska fitilar sa ya bude ledar naman yaci ya yarda ledar yasha ruwa tashi yayi zuwa ɗakin hassana daga bakin ƙofa ya tsaya tare da cewa

“Duk matar data ke ƙaura cewa mijinta kwana take mala’ikun rahma na tsine mata”
Gyara zama hassana tayi tare da cewa

“Idan ya kirata taƙi zuwa ba! in bai kirata bafa? sannan shi namijin daze gasa iyalinshi fa? wanda baya da nakasa ajikinshi se a zuciyar shi mai ƙarfi da lafiyar nema amman dan tsananin cutar kai ya kashe zuciyarsa a gindin matan sa yake ci yake sha ya mayar da ƴaƴan sa marayu?.shi wannan mutumin yaya ze dubi Allah da mala’ikun sa?”
Tafaɗa babu ko shakka.
“Hassana karki nunan halin ba ƙauye idan yaci miyar birni wallahi idan baki taso ba sena shigo nai miki tsirara gaban ƴaƴanki na karɓi haƙƙina”
Sanin halin tijarar sa yasa jikin hassana yayi sanyi.
Ta miƙe tana hawaye tabi bayanshi zuwa ɗakinsa wanda duk ya haɗa dauɗa dama ita ke mai gyara yanzu kwa ta dena.
A wannan dare seda malam habu ya fidda maitar sa akan hassana bai sarara mata ba se asubahi

Koda ta fita daga ɗakin kuka take sosai na rashin adalcin mijinta banɗaki taje tayi wanka.
Koda ta fito buɗa taji na tashi hadiza na yada magana.
“Wallahi anji kunya dan tsabar rashin zuciya mutum yace yabar miki ƴaƴanki amman sabida jaraba da baƙin naci seda kika bishi ganin munyi faɗa dashi”
Alokacin hassana ta ɗibi ruwan awala tare da cewa.
“Daɗin tama ba zina nayi ba” zina itace abin kunya to raya sunna nai mijina yana ta shimin albarka kinga kwa na sami lada”
Tana faɗar haka ta fara alwalar bayan ta gama ta wuce ɗakinta ta tada ummul da sadiya da kausar sannan ta soma gabatar da sallah

Bayan sun idar ruwan wanka suka ɗora yana tafasa suka shiga wanka da kanta ta ɗumama musu sauran abincin jiya suka ci ragowar malam dake tsaye bakin ƙofa yace abashi yaci.
Cikin mamaki hassana take kallon shi babu ko kunya ya karɓe sauran abincin buɗar bakin ummul tace.
“Allah bamu dana san shize ci dase na zubar shibai bamu ba kin samo ze wani ce ze ci”
Tafaɗa cikin haushi.
Duka bamu takai mata tare da cewa

“Nikam ban san yadda akai kika tsani mahaifin kiba ina rabaki da wannan uba ubane fa”
Hawaye ta zubo tare da cewa.
“Tun ranar daya fara zagin mahaifan ki naji bana son shi wallahi bamu ina ga bashine mahaifin muba”
Duka ta rufe ummul dashi sosai ta nuna mata ɓacin ranta na furucin data ma mahaifinta.
Ranar da kuka ummul ta fita makaranta ko a hanya da malam ya ganta ya tawo da sauri dama shi duk cikin yaran shi yafi son ta sedai ita sam ko sakar mai fuska batai haka zalika su kausar ma tsoron sa suke ji sabida tsabar yadda sukaga yana masifa……..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *