BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 1
by sumayyah Abdulkadir
BUDEWA Shekara ta 1980 G ida ne na gani a bada labari cikin unguwar Gwamna Road dake cikin garin Kaduna, kafatanin harabar gidan an_ kakkafa ‘canopies’ (rumfuna) da kujeru na alfarma.
Gidan cike yake da gawurtattu kuma tsofaffin ‘yan siyasar Najeriya wadanda suka dade ana damawa dasu a siyasar kasar, na jiya dana yau, har ma da na shekaranjiya duk ba’a barsu a baya ba, musamman yankin Arewa.
Daga cikin gida Najeriya da wajenta ma abokan huldar sa na siyasa duka sun halarta, manyan jifa-jifai (Jeep) kadai ke ta neman wajen adana motocin su, to haka kekuna da Baburan ‘yan achaba, kekenapeps, hade da kananan motoci na talakawa ma duk ba’a bar su a baya ba. Sun taru ne musamman domin taya Alh. Aliko Dan Kasa murmar hayewa kujerar Gwamnatin garin Kaduna, a sanarwar da aka yi yanzun nan a kafafen yada labarai, ciki har da gidan rediyon BBC da gidan talabyjin na CNN da dukkan jaridu da mujallun da suka fita a safiyar yau, karkashin jamiiyyar NPC _ (Northern People Congress) jam’iyya mai farin jini a wajen talakawa.
Kowa ka gani cikin farin ciki da nishadi
yake, ana ta shige da fice domin fitar da Hausawa, Igbo, Yoruba, Arabian har na Turai babu irin wadanda ba a fito dasu ba. Sai da kowa ya cika tumbinsa aka soma gabatar da makasudin taron cikin tsari na ‘yan siyasar da suka wadatu da ilmin zamani suka kuma san ciwon kansu; (ba mahandama ba), suke kuma aiki da iliminsu wajen gudanar da siyasarsu.
Cikin wannan halin ne mai girma Gwamna ya fito cikin rakiyar jama’a masu dimbin yawa, ya fara da gabatar da jawabin godiya ga mahalarta taron, sannan aka ci gaba da gudanar da taron kamar yadda aka tsara.
Mai girma Gwamna Alh. Aliko Dan Kasa, ya yi maganganu masu zafi a kan yadda gwamnatinsa za ta bambanta da sauran gwamnatocin da suka shude. Ya yi alkawarurruka masu ma’ana da yake fatan Allah Ya bashi ikon saukewa.
Ba shi ya samu kansa ba sai karfe goma na
dare, ya shigo gida a gajiye matuka, mai dakinsa Hajiya Zainab ta tare shi cikin murmushi mai nuna tsantsar farin cikin da itama take ciki a yau.
Suka tari juna da runguma cikin nuna godiyarsu ga Allah, kamin ta taimaka mishi ya cire babbar rigarsa, safa da takalmi, sannan ta gabatar masa da abin sha mai sanyi, kafin su zauna a tebir tayi ‘serbing’ din shi wainar masa, sinasir da miyar agushi data ji tsokar naman tolotolo, wannan shine nau’in abincin da Alh. Aliko ya fi so a rayuwarsa.
Saidai bai kai ga yin loma hudu ba, wayarshi dake gefe ta soma kurarin neman agaji. Yayi wa Haj. Zainab alamar ta amsa, Sal ta amsa a ‘hands-free’ cikin yin sallama.
“Kwamishinan ‘yan sanda ne, Ibrahim Rigasa. Muna son yin magana da mai wannan wayar, saboda shine ‘last call’ (kira na karshe) da muka gani a wayar Alh. Zubair Dan Kasa, wadanda suka taso daga Abuja shi da iyalinsa a safiyar yau’’.
Kasancewar a handsfree (murya waje) suke maganar, don haka yayi azamar amsawa da cewa, “Da mai wayar kuke magana”. Kwamishina ya ce, “To ku gaggauta kuzo nan asibitin ABU sun samu hadarin mota da shi da matarsa da ‘ya’ yansu biyu mace da namiji’”. Alh. Aliko ya tsame hannu daga abinci ya soma Salati yana fadin “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’ un!” Itama Haj. Zainab salatin take yi. Suka mike a tare suka fito harabar gidan. Direba da masu tsaron lafiyarsa suka fito da mota suka shiga, a daren suka dauki hanyar Zaria. Da suka iso basu sha wahalar samun kwamishinan ‘yan sanda ba. Nan da nan ya yi musu jagora zuwa dakin da suke. Ya dubi tilon dan uwansa Ministan FCT Zubairu Dan Kasa, ko’ ina a jikinsa jini ne, bandeji ne plasta ce, yana numfashi da taimakon abin janyo numfashi. Daga shi har matarsa Haj. Kaltume cikin
yanayi daya suke. A gefe yaransu Almustapha da ake kira (Imam) da kanwarshi Shahidah ne suke ta kuka.
Al-mustapha da plasta a kansa da karaya a hannun dama, ita kuwa Shahidah abin mamaki ko kwarzane ba ta yi ba, amma hakan bai hana ta kuka ba, musamman ganin iyayenta duk a kwance cikin wani hali duk da kankantar shekarun ta.
Suna shiga Alh. Aliko ya karasa ga dan’uwansa hawaye na zuba a idonsa, yayin da Hajiya Zainab ta nufi su Almustapha tana rarrashin su. Ta kama Shahidah ta rungume tare da shafa kan Imam tana rarrashinsa.
Ko minti goma basu yi da shigowa ba Haj. Kaltume ta cika. Washegari da asuba shima Alh. Zubair ya ce ga garinku nan.
Tashin hankalin da mai girma Gwamna Aliko Dan Kasa ya samu kansa a ciki, ya mantar da shi farin cikin da yake ciki bakidaya.
Dan’uwansa tilo da ya rage masa duk fadin
duniya, yau ya tafi ya barshi. Abokin shawararsa kwaya daya rak, a duniya, su fadi tare, su tashi tare, yau babu shi. Kai shi da za’a kwace mulkin a dawo masa da Yayan sa Zubairu, da yafi farin ciki. Kuka yake wiwi da shi da mai dakinsa.
Gari na wayewa aka shiga watsa mutuwar FCT Minister Zubairu Dan-Kasa a kafafen yada labarai. Da motar asibiti aka dauko gawarwakin zuwa_ ainahin _ gidan mahaifinsu, inda mahaifiyarsu take zaune a Unguwar Rimi.
Jama’a suka _ shiga_ tittudowa domin halartar jana’izar mazan jiya, wadanda tarihin Najeriya bazai taba mantawa dasu ba, tun bayan rushewar mulkin soja (return to cibil rule), wadanda suka taimakawa Najeriya ta kawo matsayin da take kai a yau: (from agrarian to industrial) irin su Minista Zubair Dan Kasa. Nan mai girma Gwamna ya zauna karbar gaisuwa, yayin da Haj. Zainab ke tare da su Imam a asibiti.
Haj. Maama, tsohuwa ba tukuf ba, wadda ta kasance mahaifiya ga Alh. Aliko da Alh. Zubairu, wadda samun kulawar ‘ya’ya nagari ya boye zahirin shekarun ta, ta sha kuka har ta gode Allah. Sai dai da yake mace ce ma’abociyar imani da rikon addini, cikin kwanaki uku da _ rasuwar babban dan nata da mai dakinsa ta dawo cikin nutsuwarta. Tana amsa gaisuwar kowa. Saidai bata umh bata umh-umh, sai jan carbin dake hannun ta, sai kuma in an yl mata ta’aziyyah ta amsa.
Da ganin mai girma Gwamna Alh. Aliko Dan-Kasa, ka san mutuwar ta buge shi yadda ba a zato. Ya rame ya yi duhu, ya manta da wata baiwa da Allah yai mishi na ba shi shugabancin al’ummar jihar su ko rantsar dasu ba a yi ba.
A ranar da aka yi sadakar bakwai ya hattama komai na marigayan ya adana a babban bankin Iloyds TSB na kasar Ingila. Sannan suka taho Kaduna, inda aka rantsar da shi a washegari.
Suka tattara shi da mai dakinsa da
‘ya’yansu Al-mustapha da Shahida, suka koma Gobt. House Kaduna State. Mulki ya soma kankama.
A
washegarin komawarsu gidan gwamnati, ya shiryawa gyatumar shi tafiya da Imam wani asibitin kashi a kasar India, garin Punjabi. Bayan ya yi magana da hukumar asibitin ta yanar gizo (Internet). Suka tashi ranar asabar, inda Imam (Al-mustapha), ya soma karbar treatment daga kwararrun likitocin kashi.
Cikin sati biyu ya warke ragas suka dawo gida Najeriya, kowa na murna da samun lafiyar Imam, kasancewarsa yaro mai shiga rai, babu wanda zai kalli Al-mustapha bai ce yana son Sa ba.
Bayan kyau tsurar sa, da Allah Ya halicce shi dashi. Wani irin hazikin yaro ne mai kwarjini da kuzari hade da nutsuwa ta banmamaki. Haj. Zainab ta dauki kaunar duniya ta dora a kan marayun nan da maigidanta ya damka mata amanarsu. Bata taba haihuwa ba, a tsayin shekarunsu ashirin da aure. In har suna da matsala a rayuwarsu, to wannan ce.
Anyi jelen asibitin, anyi na gargajiyar shiru har yau. Don haka suka dauki komai suka mikawa Allah. Wanda ba’a sa Shi, kuma ba’a hanaShi. Shine mai bayarwa da hanawa ga wanda Ya so. Don likitoci sun tabbatar musu kowannensu lafiyarshi lau, lokaci ne Allah bai kawo ba.
Akwai aminci na hakika tsakanin Haj. Zainab da marigayiya Haj. Kaltume. Basu san wata kalma wai ita ‘faccalanci’ ba da
matan hausawa ke yi, musamman idan mijin wannan ya fi na waccan, duk da ratar arziki mai yawa dake tsakanin Zubairu da Aliko a lokacin da suka aure su. Don haka su Imam tuni sun saba da Haj. Zainab da Kawunsu Alh. Aliko, don a kan kawo su hutu wajensu lokacin da iyayensu na raye. Don haka ne da Imam da Shahida suka bude ido suka gansu a gaban Uncle dinsu da Haj. Zainab, sai basu damu sosai ba. Sai dai jefi-jefi Imam da yafi wayo kan tambayi Haj. Zainab Mummy da Daddy. Ta kan ce sun je Kano sai hutu ya kare za su zo su dauke su. Ita Shahida da yake karama ce ko ambaton iyayen ba ta yi, wasanta kawai take da ‘toys’ da ‘teddies’ (‘yar tsana) da aka cika mata gadonta dasu ba abinda ya dame ta. Alh. Aliko ya dauko gyatumarshi Haj. Mama daga Unguwar Rimi (gidanta da Alh. Zubair ya gina mata) ya dawo da ita Govt. House, sassa guda aka ware mata, babu abinda babu na jin dadin rayuwar
duniya, babun ce kurum babu. Kun san dai tsari irin na gidan Gwamnati.
Mulkinshi mulki ne mai cike da takawa (wato tsoron Allah), tsantseni (da dukiyar al’ummah) da tausayin talakawa.
A shekara daya kacal da ya yi yana mulkin jihar Kaduna da local governments dinta (kananan hukumomi) guda ashirin da uku (23), ya kawo sauye-sauye na ci gaba da dama, musamman ta fuskar tsaro da kariyar lafiyar al’umma.
Ya tsayawa malaman makaranta ta hanyar kara inganta albashin su, da basu rancen motoci a dinga diba da kadan da kadan daga albashinsu.
Haka ya tsayawa iyayenmu ‘yan fansho (pension) tare da taimako ta hanyar bada kayan aiki ga makarantun firamare da sakandire na jihar Kaduna.
Bai tsaya a nan ba, gwamnatinsa ta tsayatsayin daka kan wutar lantarki da ruwan sha, wadanda sune manyan matsalolin da jihar ke fuskanta. Haka ya_ taka