BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 10 by sumayyah Abdulkadir

 BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 10 by sumayyah Abdulkadir


ajin auren ka? Ai BABBAN GORO…… sai magogin karfe”’. 


Ya yi kamar bai ji ta ba, yana ta faman lallatsa wayarshi, amma a_ zahiri obserbing maganganunta yake ji, cikin amfani da hankali da tunani. 


Ta kara shaka da kunnen uwar shegun da ya yi da ita, ta yi kwafa ta ce, “Yo ma in ban da wuce gona da iri da kaikai, inda Allah bai kai mutum ba, ina mutum ina Uwargijiyarsa? 


Dan aikena ne za a ce mijina saboda a wulakantani, to wallahi sai ka sake ni….” Ta fashe da kuka. 


Imam yana ta mamaki, dama yarinyar nan tana da baki haka? Lallai rashin kunyarta ta isa. 


Ya ce, “Kai ka bar bakin ‘yar banza yake motsi har yake gasa maka bakar magana. In nine tabdijan, da tuni leben yarinya ya haye ya yi suntum!” Ya ci gaba da tukin shi yana cewa, “To zauna nan ka zama_ gallafiri, 


wawa, ‘yar cikinka tana gaya maka magana”’. 

Zahraddeen sai ya yi murmushi, “Ina ruwan ka? Mun fi kusa, wai harshe da hakori’”’. 

Daidai inda za su zauna Imam ya yi parking, abokai da ‘yan’uwa suka nufo su domin tarar su. A tare suka bude motar, Imam da Zahraddeen suka fito ta kowanne gefe. Sai walkiya suke cikin hasken fitilun da ya haskake wajen. 

Suka russuna daidai yadda babu mai ji Sai amaren nasu, “To ya ya? Za ku fito ne ko mu nade hannun riga?”’ 

Ba shiri suka yunkura suka fito suna ta kumburi. Dariya sosai Imam da Zahraddeen suka yi. Wadda ta jawo hankalin masu daukar hoton bidiyo da talbijin. Sannan suka jera kowanne yana gyarawa amaryarshi gwaggaro, amaren na ta zabga musu _harara, kamar kwayar idanun su ta fado. 

Masu daukar hoto da masu bedio na yi, haka kawaye da abokanansu ke ta daukar su da wayoyinsu da ipad saboda kyau da matching din da suka 

yl. 

Aka fara bude taron da addu’a sannan Engr. Umar Nahaja , babban abokin ango (one) ya soma karanto tarihin Imam. 

Ya karanto makarantun da ya yi tun daga kuruciyarsa ta primary da sakandire, da kwalayen da yake dasu a ‘auto-mobile (automotibe) engineering’. 

Ya gangaro ga cewa, “Ango one (Imam) da amaryarshi rainon gida daya ne, shine mutum na farko da ya fara sanyawa Safah ‘pampers’, kuma shine mutum na farko da ta fara yiwa tumbudi….” 

Aka kyalkyale da dariya. Bai damu da dariyar jama’a ba ya ci gaba da cewa, “Ya gaya min cewa akwai ranar da ya ci kwalliyar sallar shi da farar shadda zai tafi sallar idi, ya dauke ta yana cewa matata me za ki bani goron Sallah? 

Ta kuwa feso mishi kashi mai yawa a farar shaddar shi. Ya ce Idin da bai je 

ba kenan’’. 

Aka sake kwashewa da_ dariya. Takaici kamar ya kashe Safah. Ya ci gaba da cewa, “Ya gaya min cewa, ‘yan biyun, don sun raina mini hankali, idan na yo mata sako (email) sai dayar ce za ta karanta ta bani amsa da sunan daya. 

Tun bana ganewa har na gane, don abin da ake rubuta min ba shi nake gani a zahiri ba…… Safah da Marwa suka dubi juna. Kowacce idonnan jawur. 

Umar ya cigaba da cewa, “amma da yake Allah na son Imam, a yau ga shi ya mallaka mishi abin son shi, ba da tsimi da dabarar shi ba’. 

Mutane suka girgiza kai, suna so su tambaya “to ba ta son shi ne? Ita mai bada amsar da sunanta son shi take yi?” Ba’a basu wannan damar ba. 

Kutama ya amshe abin maganar ya ce, “Sai ango (two), dan gidan Mallawa_ ne, haifaffun unguwar 

Tukur-Tukur. Ya soma karanto tarihin Zahraddeen da makarantun da ya yi har zuwa matakinshi na Engineer a petrochemical. Yana bayyana kwalayenshi da matsayinsa na Manajan gidajen man fetur na ‘DAN KASA HOLDINGS’. 

Ya ce, “Zahraddeen uwar dakinshi ce ya aura, saboda kankanba da giggiwa irin tasa, ga shi nan sai yanga take Dariya aka yi (in applause). Ya ci gaba da cewa, 

“To amma mu mun san mace ba ta fin karfin NAMIJI in har ya amsa sunan shi NAMIJI. Don haka zan iya cewa abokinaaaa….., ta wani fannin bai yi kankanba ba, tunda shi ma BABBAN GORO ne…….” 

Aka sake kwashewa da dariya. Ya ce, “A’a, ku bar dariyar nan, kada ‘yan biyu su ji haushi suyi mana (kofi)”. Umar ya amshe lasifikar ya ce, 

“Yo suyi mana kofin man? Sai mu sunkuce su mu goya, mu basu hakuri, 

mu lallashi kayanmu, tunda mun ji mun gani muna son _ abinmu ahakan…… kowane iri ne kofine muna maraba da_ shi…..!”’ Kai wadannan Injiniyoyin, idan aka biye musu da nishadin su na yau sai su sa cikin mutum ya yi ciwo. Haka jama’a suke cewa”. 

Daga nan aka soma ciye-ciye da shaye-shaye. Taron bai tashi ba sai karfe goma sha biyun dare. 

Amare suka nemi angwaye suka 

rasa sun bace bat cikin jama’a, ana ta kwashe mutane don duk kawayensu sun tafi. Haushi kamar suyi yaya? Marwah na mamakin yawan ilimin Zahraddeen dinnan, da Engr. Nahaja ya fada, a ‘yan kananan shekarunsa da ajin sa da ta ke rainawa. Ba suyi aune ba sai gani su kai filin yana yashewa sai su kadai cikin tent din, suka tsaya kawai standstill, cike da tsoro da faduwar gaba suna kallon ikon Allah. 

Can kuma sai gasu, dukkansu suna gaban motar, wannan karon Zahraddeen ke tuki Imam na gefen sa. Imam ya ce, “Don Allah ku yi hakuri, mun kai ‘yammatan mu gida ne”. Basu ce komi ba don takaici suka bude kofar motar suka shiga, suka ja motar aguje suka harba kan titi. 

Sun hau titi sosai Imam ya ce, “Wani zubin shiru ya fi yiwa mutum amfani, amma idan ba tsoro ba yarinya ta bude baki ta sake yin magana mana, ko ta maimaita abinda ta fada dazun’. 

Basu tanka ba. Ya ce, “Ango (two) ko za ka dan rage zafi ne? Na ga sai zufa kake, ko mu dan zaga in nema maka ‘Guest Inn?’’ 

Zahraddeen ya yi murmushi idanun shi na kallon hanya ya ce, “A’a, ni babban Yaya ne ban san wannan ba, in dai kai za ka zaga ne to ku fara sauke min kanwata”’. 

Daidai sanda suka shigo layin gidan Alh. Aliko, masu gadi suka bude musu tangamemen gate din suka 

shigo. 

Tun kafin su daidaita parking Safah da Marwah sun bude sun fice, saura kadan su kifa, suka shige cikin gida da gudu. Dariya suka yi sosai. Kuruciyarsu zallah a fili take Washegari lahadi Mami ta shirya (mothers’ day) a harabar gidanta, ita ta shirya amaren da kanta. Sun yi kyau har sun gaji, cikin wani lallausan leshi (swiss), na Safah blue ne, na Marwah orange, sannan aka kawo goggoro deep colour na leshin kowaccensu. Har daga NTA Abuja an zo daukar labarin shagalin bikin ‘ya’yan Aliko Dan Kasa, ban da gidajen talabijin dake nunawa a ciki da wajen gidajen garin Kaduna. To haka masu daukar 

hoton mujallun delight da obasion. 2K OK 

Daddy ya yi kiran Zahraddeen da Imam don ya ji ra’ayinsu game da tarewar amaren nasu. Bayan duk wannan ruguntsumi ya lafa. Ga shi za 

su koma makaranta gobe. 

Imam ya ce, “Safah ta koma makaranta zan koma Glasgow jibi, zan yi mata shirin inda za ta zauna, da sabon gurbin karatu ta dora akan nata, maimakon ta sako daga farko, duk da dai bata yi nisa da wannan din ba”. Daddy ya juya ga Zahraddeen ya ce, “Na ji ra’ayin Imam kai fa?’ Zahraddeen ya sunkuyar da kai ya ce, “Nan Zaria za ta zauna a gidanmu, na yi ginin sassa na daban (flat) ina ganin zai ishe ta”. 

Daddy ya ce, “Shikenan”’. 

Ya jawo mukullai cikin bounch of keys din sa, ya ware wasu ya mikawa Zahraddeen ya mikawa Imam sauran. Suka dube shi cikin yanayin tambaya, ya ce, “Gidaje ne guda biyu da na yi cinikinsu a Malali na mallaka muku halak-malak a matsayina na Baban ku. Ko da ba za ku zauna a ciki ba, idan kun zo sai ku ke sauka a can. Bana son musu, bana son godiya. Ku tashi ku je, Allah Ya ba da zaman lafiya, ya 

bada zurri’a dayyiba. 

Ku yi hakuri, kuyi hakuri, kuyi hakuri da iyalanku, namiji abinda ya gada kenan hakuri da iyali, koda a auren inaso kana so ne kuwa. Balle aure irin wannan yadda ya zo muku. Hakurin shine kawai zai sa a cimmawa manufar da aka gina auren akai. Watarana sai labara!!!’. 

Fuskar Zahraddeen ta yi jajir, ga dukkan alamu bai ji dadin kyautar ubangidan nashi ba. Bai yi kauron baki ba ya ce. 

“Daddy ka yi hakuri ba zan karba ba!”’. 

“Alh. Aliko ya ce, “Saboda ba ni na haife ka ba ko?” 

Ya girgiza kai da sauri ya ce, “A’a, ba don haka bane. Ina gini a unguwar Rimi kadan ya rage a kammala’. Daddy ya dan zuba mishi ido ya ce, “Na riga na baka, idan baka so ya rage naka ka baiwa wani, amma wannan kyautar babu mai tada ita, ko bayan raina!”’. 

Haka taron ya tashi zuciyar Zahraddeen babu dadi, ba don ya san halin Daddy ba, da sai ya ce raina masa ya yl. 

Amma shi kansa shaida ne a kan halayen Alh. Aliko, babu raini ga na kasa da shi, sai mutuntawa da darrajawa. Kuma da zuciya daya yake yin kowacce kyauta. 

Karfe takwas na dare motocin daukar amarya zuwa Zaria suka iso. Duka rabi abokan Zahraddeen ne da abokan aikinsa. 

Marwah ba ta tashi kuka ba, sai da ta ga da gaske raba ta za ai da Mami da ‘yar’ uwarta. Zuwa inda bata sani ba, bata taba rayuwa a ciki ba. Zuwa cikin rukunin rayuwar wasu mutane da bata san irin tasu rayuwar ba. Suka rungume juna suna ta kuka. Mai tsuma zuciyar duk mai imani. 

Shahidah ke lallashin su, ita kanta Mamin dauriya takeyi saboda ta shaku da Marwah fiye da Safah, sannan Marwan ta fi taimaka mata a kan 

harkokin cikin gida da sabgoginta. Rakiyar unguwa, biki, kasuwa, ziyarar dangi da sauransu. 

Da kyar wata daga dangin mahaifin Zahraddeen ta goyata zuwa wajen mota ana ta yi mata guda, suka dauki hanyar Zaria. 

Basu isa Zaria ba sai karfe goma na dare, ‘yan’uwan Zahraddeen da mahaifiyarshi suka yi musu tarba ta mutunci da karramawa. 

Kai tsaye dakin Innar Zahraddeen aka nufa da amarya. Ta rungume Marwah tana ta yi mata addu’a, aka bata amanar amarya ta ce ta karba, Allah Ya taya ta riko. 

Daga nan ta yi musu jagora zuwa sassan Zahraddeen dake cikin gidan. Su Shahida, Badar, Rahima da sauransu duk a nan za su kwana. Tsarin flat din ya yi musu, ya basu sha’awa sosai; bai cika girma ba, ‘self-content’ ne. 

Karfe sha biyu na dare kowa ya 

kwanta, sai Marwah dake ta kuka cikin mayafinta, don a ganinta Daddy ya gama kashe mata rayuwa, har kukan ta ya tashi Shahida. 

Ta mike ta zaunaa a gefen gadon ta ce, “Kukan nan ya isa haka Marwah, ina so in san damuwarki? Tunda abin nan dai anyi ya riga ya tabbata, ya kamata ki hakura haka nan ki karbi mijin da Allah Ya baki. Shin ma mene ne aibun Zahraddeen don Allah?” 

Ta ce, “Ni ina ruwana da wani rashin aibunsa, ni dai kawai ba zan iya zama da yaron Babana bane, dama wani ne daban sai in hakura. 

Dubi dan akurkin dakin da aka ajiye ni, sannan an kawo ni gida cike da mutane duk ‘yan kauye dasu, ana nufin a cikin su zan yi rayuwa? 

Ke yanzu idan aka ce ki auri yaron Daddy za ki yarda ne? Sai ni da aka raina ma wayo? Ko nima bagidajiya ce irin Safah?” 

Shahida ta yi murmushi ta ce, “Ki iya bakin ki Marwah, arziki na Allah ne, 

kuma dare daya Allah kan yi Bature. Kuma ni miji in dai kamar Zahraddeen ne Daddy ya zabo min babu abinda zai hana ni in yi mishi biyayya, ba ma’aikacin Daddy ba ko masinjansa ne, in dai zai iya ci dani ya sha dani ya biya min bukatar aure, shi kenan. 

Ki rage daukan duniya da fadi, kuma ki daina daukar rayuwa da zafi. Ki daina alfahari domin halin la’anannu ne. 

Daddy gata ya yi miki domin ya kawo ki inda za a rike mishi ke cikin mutunci da amana, inda ba zai kasance cikin zullumin a hannun da kike ba, inda ya tabbatar ko bayan ransa, ba za a tozarta ki ba”. 

Da maganganun Aunty Shahida ta kwana suna juyi a kwakwalwarta. Mai jama’a ke gani a tareda Zahraddeen ne? Wanda ita bata gani? Me yasa Zahradden keda kima da farin jini haka duk da ba dan kowa bane? Haka 

su. Rahima ma_ suke ta _ fade. Zahraddeen bai iso Zaria ba sai washegari da safe. 

Yana isowa motocin abokanshi suka juya da su Badar, Shahida da sauran jama’a Kaduna. Ya rage daga ita sai halinta. 

Ta zuba ido don ganin ta inda Zahraddeen zai bullo ta zazzage masa rashin mutuncin da ko shi kare ne dole ya maida ita inda ya dauko ta. Tuni nasihar Shahidah ta bi ta _ bayan kunnen ta. 

Motsin bude kofa ta ji tare da sallama, Inna Binta ta shigo Rabi’a kanwar Zahraddeen biye da ita, suna dauke da ma’adanan abinci da jug mai rike zafi. Suka ajiye daga gefen ta, ta dube ta tana murmushi ta ce, 

“Tashi ki ci abinci, tun jiya an gaya min baki ci komai ba”. 

Ta bisu da kallo cike da haushi, ta ce, “Na koshi ne”. 

Inna ta ce, “Ko kadan ne ki daure ki taba, zama da yunwa ba shi da dadi. In 

kuma baki son wannan ki gaya min wanda kike so ayi miki’. 

Ta juyar da kai ta tabe baki a ranta tana cewa, “Dube ku don Allah, local daku, kune za ku yi min wani girki in ci?” 

Da ta ga Inna ba za ta tafi ba dole sai ta ci abincin, sai ta ce, “Zan ci anjima kadan idan na yi brush”. 

Inna ta ce, “To ko ke fa? Ko akwai wani aiki da Rabi’a za ta yi miki?’ 

Ta ce a takaice, “Babu”. 

Inna ta juya ta fita, ta ce, “Rabi’a zauna mana ki taya ta hira kamin Dini ya shigo”. 

Wai an ce shimfidar fuska…….. ta fi ta tabarma, don haka Rabi’a ta lura da fizge-fizgen amaryar tasu, wanda ita Inna ba ta kula ba, kasancewarta ba mai sa ido ba, don haka ta ce, 

“Zan yi walha ne Inna, anjima in ya fita sai in dawo”. Suka juya suka fita. Ta jawo kulolin guda biyu ta bude, funkason fulawa ne, sinasir, masa, kisra da miyar ganye, ya ji nama 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *