BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 12 by sumayyah Abdulkadir

 BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 12 by sumayyah Abdulkadir

Mami ta shigo, ya yi amfani da hannun daman shi wajen amsa wayar yayin da yake tuki da na hagun cikin kwarewa da gwaninta. 

Mami ta ce, “Ka taso ne?” 

“Har na kusa isowa Minna Mami, nan da ‘two hours’ insha Allah zan iso”. Ya kashe wayar tare da kara taka totur din motar sosai, gudu yake kamar zai tashi sama. (Tukin Mota), na daya daga cikin abubuwan da ke sanya shi nishadi. Har dai ace motar mai budadden sama ce. 

Sanye yake da shadda coffee kala kanshi babu hula, wanda hakan ya bayyanar da tulin kwantacciyar sumar kanshi baka sidik mai santsi da sheki. Yana jin kansa cikin wasu mutane kalilan masu sa’ar samun duk abinda suke so a rayuwa, tunda Allah Ya mallaka mishi abin da rai da zuciyarshi ke so, tsayin shekaru goma sha tara. At last, ya samu. Don haka ba shi da abin da zai ce da mahaliccin shi sai godiya, da neman dadin 

falalarsa da ni’imarsa. 

Karfe shida da rabi ya shigo garin Gwamna, don haka kai tsaye alwala ya yi a harabar gidan ya wuce masallaci don samun = jam’in maghariba. 

Mami ta kwankwasa kofar dakin da ta ji an kulle da makulli, Safah ta zo ta bude, sanye take da ‘shirt’ da wando samfurin polo kalar ruwan zuma, ta matse gashin kanta daga tsakiya. Mami sai ta ga ‘yarta ta kara kyau na ban mamaki. Ko da yake hasken amarci daban ne, ta yi murmushi ta ce, “Mene ne na sanya mukulli a kofar?” Ta ce, “Haka nan’’. 

Mami ta sake yin murmushi, ta san don wanda ake kulle kofar. Tunda aka tafi kai Marwah Zaria tun shekaranjiya ko falo ba ta kara lekowa ba. 

A dakinsu take hidimominta ta kulle kanta ba ta son yin mu’amala da kowa. Daga Mami har angon babu wanda ke shiga sabgarta, shi ba ya garin ma tun wayewar garin litinin ya 

wuce Abuja, inda yake fafutukar bisar ta da passport dinta da ya amsa wurin Mami. 

Ta ce, “Fito maza ki tayani aiki, ai tunda Marwah ta tafi na san na yi rashin mai taimaka min a kichin”’. 

Ta yi rau-rau da ido kamar za ta yi kuka ta ce, “Kai Mami ni bana tayaki?” 

Ta ce, “Da yaushe da yaushe kike taya nin? Kin ga bana son dogon turanci wuce muje”’. 

Haka tasa ta a gaba har kicin tana cewa, “In ban da Imam din wa zai iya zama dake? Ga kiwa ga son jiki, ga yawan kwanciya kamar mage, bakya um bakya um-um kamar_ wata jikakkiyar tsumma. 

Ayi mace sai ka ce namiji, daga takarda sai biro? Ko huda-huda yana samun lokaci ya_ shiga _cikin ‘yan’uwansa ya yi mu’amala mai dadi dasu. 

In bakya hutar da idanuwanki in kin tsufa za ki samu matsala dasu kin ji na 

gaya miki’. 

Ta rausayar da kai ta ce, “Nice zan tsufa Mami?” 

Ta ce, “A’a, ba za ki tsufa ba tunda hurul-eeni ce?” 

Ta yi smiling har wushiryarta da jerarrun hakoran’ suka fito. Ta taimakawa Mami suka hada abincin dare mai rai da motsi suka jera a dining, sauri take a gama ta gudu kada Imam ya zo ya same ta wanda take Allah-Allah ranar tafiyar shi ta zo ya bar gidan ta huta, don bata da masaniyar yaushe zai tafin. 

Dan halak din kuma dan gatan Mamin sai ga shi ya shigo cikin takunshi na sassarfa ya shigo kicin din. 

Daga bakin kofa ya tsaya yana kare mata kallo kamar bai san ta ba. Daga Mami har ita babu wanda ya san da shigowar sa, hirar su suke suna dariya. Sai da ya kalle ta son ransa sannan ya yl gyaran murya ya ce, “Mami wane delicious ake shirya mana ne? Irin wannan ‘aroma’ haka tun daga bakin 

get?” 

Tana murmushi ta ce, “Duk naka ne, na san ka tunda ka bar gida ba za ka tsaya ka ci wani kwakkwaran abinci ba sai shirme wanda baya rike hanji’’. Ya yi dariya kadan ya ce, “Mami kina sangarta ni, sai na tafi inda bani da gata in yi ta ragaita…..” 

Ta ce, “Ga shi kuma Allah ya baka makiwaciyar mata, ya ya za a yi kenan?” 

Ya kai duban shi ga sashen da take, idanunshi a sanyaye, ta hade fuska ta yi murtuk kamar hadari, kai ka ce tunda aka halicceta ba ta taba dariya ba sai hura hanci take. 

Ya girgiza kai ya ce, “A haka zan yi maneji Mami, an ce “da babu…..” 

Ta karasa mishi “…..Gara babu dadi!”. Ita dai ba ta tanka musu ba, karewa ma ko inda yake ba ta kalla ba ta tsallake su za ta wuce. Muryarshi ta yi kasa so cool ya ce, “Kin gani ko Mami za ta tafi ta kulle kofa saboda ga dodonta ya zo….” 

Ita ma Mamin ranta babu dadi, tausayin Imam take ji sosai. Ciwon kana so ba a sonka matukar ciwo ne da shi. 

Ta ce, “To ya zan yi muku ne Almustapha? Ita taurin kai, kai kuma baka ya lallashi ba”. 

Ya ce, “Wallahi Mami ba zan zauna ina lallasarta ba, ai sai ta raina ni’. 

Ta yi dariya ta ce, “Ka daina cika baki 

IMAMU-ALMUSTAPHA, ranar rarrashin ba ta zo bane, amma tana nan tafe”. 

Ya ce, “To Mami ke ki lallasar min ita man ko ‘yar hira ce ta bari mu yi kafin in tafi? Kin san halin rai……” 

Mami ta katse shi da cewa, “Ni nake maka auren da zan je ina maka bambadanci? Tunda ka ce ba za ka yi ba, to ku yi ta zama a yadda kuke, ruwan ku. 

Lafiya za ka je ka dawo insha Allahu, ka zo ka same mu cikin alheri da koshin lafiya kamar yadda ka barmu”. Ya tayata da daukar warmers suka 

fito. Masallaci ya koma don yin sallar isha’i, inda ya tarar da Daddy suka yi sallar tare sannan suka shigo cikin gidan suka nufi tebir din cin abinci. Daddy ya dago yana kallon su ya ce, “Wai ina Safah ne?” 

Shahida ta ce, “Tana dakinsu’’. 

Yace, “Kirawo ta”. 

Har ta yi shirin barci cikin wasu tausasan nighties bakake wuluk, tana tufke gashin kanta yadda zata ji dadin kwanciya. Shahida ta kwankwasa kofar, daga ciki ta ce, “Waye?” 

“Idon matambayi ne”. Shahida tace a kufule. 

Ta bude kofar tana dariya ta ce, “Ki zo Daddy ke kiran ki”. 

Ta yafa mayafi ta bi bayanta tana kunkuni, ita an dame ta. 

Shahida ta ce, “Ki ce ba za ki je ba mana short and simple….” 

Ta tura baki ta ce, ““To ban ce ba’”’. 

Daddy ya bita da kallo har ta zauna a jikin Mami, gaba daya ta rame ta yi 

sanyi, tausayin ta ya kama shi. 

Sai dai ta wani fannin ya fi jin tausayin Imam din da ya kallafa burin rayuwarshi da soyayyar shi a kanta tun haihuwarta. Ya rasa mene ne aibun dan shi da ta kasa son shi. Shi kuma ya rantse har bayan ransa ba zai ta da wannan aure ba. 

Cikin kulawa ya ce, “Baki da lafiya ne?’ 

Ta girgiza kai, “Lafiya ta kalau”. Daddy ya ce, “Gobe ne za ki koma makarantar?” 

Ta daga mishi kai. 

Ya ce, “Ki yi min magana mana, sai daga min kai kike kamar kadangaruwa…” 

Ta ce, “Eh, amma ‘hostel’ zan koma, ba zan iya zama ni kadai a gidan ba”. Ya dube ta yana kiyasi ya ce, “To mene ne fa’idar komawar taki tunda barin makarantar za ki yi gaba daya?” Hawayen da take tattali suka kwace, tsoronta Allah, tsoronta kada ace ta bi Imam, ta ce, “Don Allah Daddy a 

barni in yi karatuna, na yi nisa kuma ina jin dadin sa….” 

Ya ce, “To, mene ne abin kuka a nan? Kin san dai yanzu ba mu da iko dake sai yadda mijin ki ke so”. 

Ya juya ga Imam wanda kanshi ke kan wayarshi yana danne-danne kamar bai jin su, ya ce, “Yaushe za ka tashi?” 

Ba tareda ya dago daga abinda yake yi cikin wayar ba Ya ce, 

““Gobe da asubah insha Allahu”. 

Ya ce, “To in zai yiwu ka kara kwana daya don ku samu_ lokaci ku yi shawara a junanku”. 

Ya ce, “Ni Daddy duk yadda ka yi daidai ne”. 

Ya yi murmushi ya ce, “Saboda kana tsoron ta? To in gaya maka ba a sakarwa mace ragamar kanta, ka zama namijin duniya ma’ abocin gwagwarmaya da rayuwa kala-kala. Kada ka bari soyayyar da ke zuciyarka tasa ka kasa tankwara iyalin ka. 

Ku tashi ku je ku yi shawara a tsakanin ku abin da kuka yanke gobe 

ku sanar dani”. 

Da haka taron ya tashi kowa ya nufi dakin sa. Sai dai har zuwa washegari babu wanda ya nemi dan’uwansa tsakanin Safah da Imam. 

Ita taurin kai da rashin son duk wata alaka da za ta hada ta da Imam din. Sai ta hadu da wanda ya dame ta ya shanye wajen rashin son wargi da miskilanci. 

Imam irin mazan nan ne da duk soyayyar da suke yiwa mace, ba za su lamunci ta raina su ba. Sannan bai taba barin ka gane ‘weakness’ dinsa akan soyayyah. Shi Imam ko yana matukar son abu, da wuya ka gane sabida rashin son raini ya ratsa. Sai a inda yasan za’a yi maraba dashi, da abinda zuciyarsa ta zo dashi ko ta ke kunshe dashi. Mami kadai yake iya gayawa cikinsa. Kamar ba ita ta haifi Safan ba. 

Abun duniya ya taru ya yiwa Safah yawa, ga kewar ‘yar’uwarta, ga 

hukuncin da Daddy ya yanke mai nuni da cewa, in har tana son karatun ta sai da amincewar mijinta. 

To ina ta ganshi balle ta tambaye shi? Shi wani irin mutum ya zame mata yanzun mai wuyar sha’ani ba kamar sanda yake yaro ba. Ta manta shekaru kan canza mutum. Kana girma ne kana kara sanin ciwon kan ka. Ba ya shiga sabgarta, ba ya zuwa inda take tun daga ranar da aka daura musu aure. Harkokin gabansa kawai yake, hankalin sa a kwance 

Ga shi ita ko lambar wayar shi bata sani ba. Dole ta tsaga billenta ta tambayi Aunty Shahida, don ta san agogon dake like a bangon dakin ta, dana swatch din dake daure a hannun ta na hagu, ba karya suke gaya mata ba; saura ‘yan awanni kalilan Imam ya bar Nigeria da igiyoyin aurenta, da igiyoyin karatun da ta sha matukar wahala akai. Ba da bata lokaci ba ko tambayar dalili Shahida ta bata. 

Ta zuba su cikin wayoyin ta da 

Zahraddeen ya bata, wadanda dasu take amfani har yanzu, don ranar daurin aure ta bawa Badar ta ce ta neme shi ko cikin mutane ne ta bashi, amma ya dawowa Badar dasu ya ce ta ce mata ta rike ya bar mata duniya da Jahira. 

Karfe hudu na yammacin ranar ta yi zugum rike da wayoyin a hannunta ta rasa ta inda za ta fara mishi magana, kira za ta yi ko tedt za ta yi? 

Duk wani tunaninta ya kare ne a kan cewa idan ta yi mishi tedt ko kira, ya tabbata ta dauke shi a matsayin miji kenan. 

Bayan ta gama cewa bata son shi a matsayin miji, kuma haka abin yake har gobe a ranta, sannan ba ta san irin karbar da zai yi mata ba, don ta lura green snake ne, ta ruwan sanyi suke ladabtar da zuciyar diya mace, ba ta lallashi da tarairaya kamar Zahraddeen ba. 

Da ta ga duk wannan ba zai mata ba, ga lokaci yana ja, kuma ta ji yana 

gayawa Mami jirgin “Cathay-Pacific’ zai bi karfe takwas na dare, ga shi yanzu karfe biyar na yamma. Sai ta saduda ta soma yin tedt din fuskarta kamar ta fashe da kuka. 

Yana hada kayan shi cikin troller a lokacin da ya ji alamar shigowar sako cikin wayarshi. Mami ta aiko Shahida da kilishi da dambun nama mai yawa ta ce ya hada a kayan. 

Hajiya Maama kuma gireba ce bokiti guda ta kawo mishi, don yana son gireba sosai. 

Yana murmushi ya karbi sakon Mami ya yi masa mazauni kusa da na Hajiya Mama, ya ce da Shahida, “A ce da Mami, na gode!”’. 

Har ta kai bakin kofa ya kira ta, ta dawo ta zauna. Ya ce, “Safah me take yi yanzu?” 

Ta ce, ‘“Wallahi ban sani ba, rufe kofar take yi”. 

Kamar ba shi ba, saboda yadda muryarsa ta yi kasa sosai, ta nuna wani mutum mai azabtuwa a cikin 

soyayyah matuka. Yanayi ne da Shahidah bata taba ganin dan uwanta a ciki ba (rauni) Ya ce, 

“Shahidah don Allah, a matsayin ki na mace mai shekaru fiye da kannenki, kuma shakikiya agareni wadda nake da tabbacin bazata gaya min karya don inji dadi ba ta boye gaskiya don na cutu ba, ina da wani aibu ko wani hali mara kyau ne da Safah ta kasa so na?” 

Tausayin dan’uwanta ya kama ta, ta ce, “Wallahi-wallahi ka ji rantsuwar musulmi kenan, baka da shi’. 

Ya ce, “To a ganin ki mene ne matsalar?” 

Ta runtse ido ta ce, “Ya Imam shi SO ba a nan yake ba. Dubi Zahraddeen ai bai kai ka ba, ka fi shi komai, amma ta so shi. 

Shi ya sa tun farko na yi fatan a ce ina ma MARWAH ka nema, don ita ce mai yi maka soyayyar aure ta gaskiya……..” 

Ya bude baki yana kallon ta ya ce, 

“who told you?” (Wa ya gaya miki) Dariya ta yi “Na san komai, kada ka manta kannena ne, tare muke rayuwa, kuma na fi su hankali, sannan duk wani takunsu a kan idona suka yi shi tun haihuwar su har girmansu. Abobe all, (sama da komai) I’m far more sociologistic than a political scientist. Marwah ce take yi maka e-mail ba Safah ba. Marwah ce take baka greeting cards da sunan_ Safah, Marwah ce take yi maka asirtacciyar soyayya wadda babu son zuciya a cikinta, domin ta yi juriyar da har yau, ‘yar’ uwarta ba ta taba ganewa ba”. 

Ya ce, “Me yasa tun a lokacin baki gaya min ba?” 

Ta ce, “Ta yaya zan gaya maka alhalin lokacin idon ka ya rufe da soyayya? Baka ji ba ka gani balle ka gane inda ake maraba da soyayyar taka? Ta yaya zan shiga tsakanin ‘yan’uwa_ biyu? Karewa ma wadanda suka fito duniya tare a lokaci daya?” 

Ya yi murmushi kadan ya ce, 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *