BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 2 by sumayyah Abdulkadir

  BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 2

by sumayyah Abdulkadir

muhimmiyar rawa a kan harkar ilmin manya (adult education) a jihar bakidayanta, da karo karatun malamai na jami’a dana sakandire a kasashen ketare ta hanyar daukar nauyin’ karatun§ da ‘accommodation’, da baiwa mata sana’o’l da tirenin akan sana’ar, haka matasan da basu samu damar yin ilmin zamani ba. 


Kan ka ce meye wannan? Ya zamo zakaran gwajin dafi cikin gwamnonin Najeriya tsararrakinsa, sannan abin koyi, kuma abin so a zukatan al’ummar jihar. Sunanshi ya yi tambari a jihar baki dayanta, babu abinda ke fita daga bakunan al’ummar jihar, sai fatan alheri ga gwamnatinsa. 


Wadanda suka san matsalarshi ta cikin gida kuwa (wato rashin haihuwa) sai addu’a suke masa Allah Ya ba shi magajin kyawawan halayensa. 


A wurin shi kuwa, bai tsanantawa kansa kan rashin haihuwa ba. ‘Ya’yan dan uwansa sun isheshi, har gaba da abada in akwai, ‘ya’ya ne a gareshi da yake so fiye 

da ‘ya’yan da zasu kasance shi ya haifesu. Wato Imam da Shahidah. Fatansa Allah Ya raya masa su cikin tarbiyyar Islam ameen. 

2K KK 

H aj. Zainab ce zaune a katafaren falonta tana kallon tashar MBC da ‘remote’ a hannunta, Al’mustapha na ‘game’ cikin wata na’ura ta yara. Shahida ta lallaba ta zagaya ta kashe, ya dago a fusace ya yi kanta da duka, da kyar Hajiya ta kwace ta. Ta ce, “Haba Imam, irin wannan duka kamar ka samu sa’an ka? Baka ganin Shahida yarinya ce ne?” Ya zumbura baki, “To wa ya ce ta kashe min ‘game’ dina?” 

Ta ce, “Ka yi hakuri ba za ta sake ba. A bar ‘game’ din haka, aje ayi alwala ayi sallah, sannan ayi shirin fita lesson (darasi) kafin teacher (malam) ya zo”. 

Duk suka amsa, suka fita. Ta bisu da kallo, tana jin kauna da tausayin yaran har cikin zuciyarta. 

Ta tashi ta nufi sassan surukarta Hajiya Maama, ta tarar da ita tana sallar la’asar. Ta samu kujera ta zauna har Hajiyar ta idar ta yi addu’a ta shafa. 

Ta juyo da murmushi ta ce, “Ya ya Maman Imam? Ina ‘yan rigimar naki sun dawo ne?’ 

Ta ce, “Sun dawo tun dazu, har anyi wanka an ci abinci an tafi daukar lesson, yanzu aka gama rigimar na sha rabon fada, kin san Imam din nawa ba dai karfi ba. Ai Shahida tana cin duka, wannan bai hanata gobe ma ta sake tsokanarsa kamar ba jikinta ake tika ba”. 

Hajiya Mama ta yi dariya ta ce, “A kullum na dubi yaran nan suna tuna min da Kaltume. Da wata hira da muka taba yi da 

ita. Ta ce Allah Ka bawa Haj. Zainab ‘ya in aurawa Imam”. 

Hajiya Zainab ta yi murmushi cikin jin kunya kuma mai ciwo a zuci. Suka ci gaba da hira da _ surukuwarta, duk da shimfidaddiyar damuwar da Hajiyan ta gani a fuskarta a dalilin zancen haihuwa data yi. 

Wayar mai girma Gwamna ce ta tada ita daga hirar da suke yi mai ban tausayi a kan marigayi Minista Zubair da mai dakinsa Hajiya Kaltume. Cikin su babu wadda bata zubar da hawaye ba. 

Imam na aji uku na sakandire, Shahida na aji shida na firamare. Tenure din Alh. Aliko ta cika, ya sauka daga gwamnatin jihar Kaduna. 

Ba yadda jama’a basu yi da shi ba a kan ya sake tsayawa takara amma ya_ ki amincewa, ya ce tunda ya tsira da mutuncinshi da kaunar shi a zukatan al’umma, to Alhamdulillahi. Suka baro Gobt. House suka dawo katafaren gidan da 

ya gina a Jabi Road, dake cikin birnin Kaduna. 

ASALINSU A salin mahaifin su Alh. Aliko mutumin Kaduna ne, a wani gari, CHIKUN. Cirani ne ya shigo da shi cikin garin Kaduna tare da mai dakinsa Salamatu (Hajiya Maama). Itama ‘yar Chikun ce kamar miinta 

Malam Salihu. 

Haihuwar Salamatu bakwai duk suna mutuwa (wabi), sai a kan Zubair na takwas Allah Ya bar mata. Ba dadewa ta sake samun wani cikin, ta haifi Alh. Aliko, wanda sunan shi na ainahi, Aliyu. Baban shi ke kiran shi Aliko, kuma sunan ya bishi har girma. 

Zubairu da Aliko sun rayu tare da iyayensu har girmansu, kafin Allah Ya dau ran mahaifinsu Malam Salihu. A_ lokacin Zubairu yana da shekaru ashirin, yayin da Aliko ke da sha bakwai. 

Duk da iyayensu basu yi karatun boko ba, Mal. Salihu bai bar ‘ya’ yanshi haka ba, sai da ya ga kowannensu a jami’a sannan ya samu kwanciyar hankalinsa. Ya _ tsaya tsayin daka a kan karatun su, wanda shine tsani na duk wani mataki da suka taka yau a rayuwa. 

Karatu mai suna karatu, sun yi shi har sun kure biro, idan har ana kurewa, dukkansu akan siyasa. Amincin dake tsakaninsu na shakikan juna, ba kasafai ake samun irin 

shi a wannan zamanin ba. Daya baya zartar da komai kan abinda ya shafeshi ko iyalinsa ba tareda yayi shawara da daya ba. daga kan Kakaki (speaker house of representatibe), dan majalisa, kwamishina, sanata, shugaban karamar hukumar Chikun da wasu da dama, har kawo na yau, wato matsayin daya taka na Gwamnan jihar Kaduna. 

To haka Zubair ya rike mukamai da dama kafin Allah Ya dau ransa. Har kawo na karshen, wato Ministan FCT. Inda ya gamu da ajalinsa a kan hanyarshi ta zuwa taya dan’uwanshi murnar hayewa kujerar Gwamna. 

Mutuwar Zubair ta taba Aliko ba kadan ba, yadda har ta shafi lafiyarshi. Sai dai kullum ya dubi Imam da Shahida dake gabanshi, yana godewa Allah da bai barshi da kewa ba. 

Kullum ya daga ido ya dubi Imam (Almustapha) fuskar dan’uwanshi Zubair yake gani a fuskarsa. 

Don haka son da yake yiwa yaron ba kadan bane, ta yadda har yake mantawa da 

cewa ba shi ya haife shi ba. 2K ok ok ok 

mam Zubair Dan Kasa, yaro ne mai hazaka tun yana kankaninsa, yana da wasu baiwarwaki da dama da ba duk ‘ya’ya Allah Ya mallakawa ba. 

Yaro ne da ya lakanci wani darasi daga cikin darusan da ake koya mishi a makaranta wai shi introductory technology. Ga kyau ga kyan hali, ga nutsuwa da rashin son wasa, ta ko’ina Imam Almustapha, abin alfahari ne ga iyayenshi da ‘yan’uwan shi bakidaya. Rashin iyayenshi da ya yi a_ lokacin kuruciya bai sa shi ya yi maraici ba ko kankani. Baffanshi da matarshi a tsaye suke a kansu, farin cikinsu da walwalarsu. Sannan Hajiya Maama ba ta da abin so irin mijinta Imam, wanda take sawa a gaba tana koyar da shi dabarun zaman duniya, da yadda za a yi a ci ribarta. 

A irin wadannan lokutan, Imam kan dauki dukkan hankalinsa ne kacokan ya likawa Hajiya Maama, yana kwankwadar ilmin manya na yadda za’a gina rayuwa a duk halin da aka samu kai, yana aunawa a ma’auni na hankali da tunaninsa, yana hadawa yana tarawa yana_ rarrabewa, sannan idan ta gama ya jefo mata tambaya wadda ta fi karfin shekarunsa. 

Akwai ranar da ya tambaye ta “Me yasa Daddy ya ki ci gaba da takara duk da kaunar da jama’ar Kaduna ke mishi?” 

Ta yi murmushi ta ce da shi, 

‘Don ya tsira da mutuncinsa ne, ka san an ce tsira da mutunci ya fi tsira da kudi’”. (Wannan Magana ta zauna cikin ran Imam har girman sa) 

Akwai kuma ranar da ya tambaye ta, “Ita Mami (Hajiya Zainab) mai yasa ba ta haihuwa?” 

Ta ce, “Allah ne bai bata ba Imam, amma ka dinga yi mata addu’a”. 

Tun daga wannan ranar Imam bai kara tashi daga inda ya yi sallar farilla ba, ba 

tare da ya rokawa Mami dinsa haihuwa ba. 2K ok 

ayan barin Alh. Aliko Gwamnati, kasuwanci ya fada ka’in da na’in. Ya hada gwiwa da wani kamfanin kera injinan wutar lantarki dake kasar Birtaniya, suke shigo masa da injina nau’i-nau’i manya da kanana. 

Sannan ya bude manya-manyan gidajen man fetur guda uku a ciki da wajen garin Kaduna. Ya kuma zuba hannayen jari a wasu manyan kamfanonin Inshorar Nigeria irinsu. NAICOM_ (National Insurance Commission), African Alliance Insurance, da Consolidated Hallmark Insurance Plc. . Wata ranar asabar Hajiya Zainab ta tashi ba ta jin dadi, kamar da wasa taje ganin 

likita, ya dudduba ta ya yi mata tambayoyi, ya kuma umarceta da ta ba shi fitsarinta. Wanda nan take ya mika ‘lab’ aka auna, sakamako ya fito, inda ya tabbatar mata tana da shigar karamin ciki dan watanni biyu. 

A nan ofishinsa ta zube ta yi sujjada ga Allah, buwaya gagara misali mai yiwa bawa baiwa da abin da bai isa ya bawa kansa ba. 

Sannan ta ja bakinta ta tsuke ba ta gayawa kowa ba. Don ita kunya ma take ji tsofaitsofai da ita da ciki. Ita kadai ta yi ta fama da laulaye-laulayen ta, amma da yake babba-babba ne, Hajiya Maama ta gane. 

A lokacin cikin na da watanni hudu Alh. Aliko baya nan yana Bristol, wato ainahin kamfanin dake shigo masa da_ injina samfurin (Binatone). Hajiya Mama ta yi kiranta ta ce, “Zainab kin je asibiti a kan wannan haraswar?” 

Ta ce, “Na je”. 

Ta ce, “Basu gaya miki kina da juna biyu 

ba?” 

Kanta a kasa ta ce, “Sun gaya mini’. Hajiya ta kama baki cikin al’ajabin fulatancinta, ta ce “To don me baki gaya min ba? Wannan ai abin mu taru mu yi farin ciki ne mu godewa Allah”. Ta tsura mata ido tana ta zuba addu’a na Allah Ya sauke ta lafiya. 

Ko da Alh. Aliko ya dawo, dakin mahaifiyarshi ya fara isa kamar yadda ya saba kullum yayi tafiya. Far’ar Hajiya yau ta fi ta kullum. Shi kanshi ya fahimci tsantsar farin cikin da mahaifiyarshi ke ciki. 

Ya zauna_~ cikin luntsuma-luntsuman kujerunta ya ce, “Hajiya me muka samu ne? Da alama kina cikin farin ciki”. 

Ta ce, “Kwarai, mun samu abin da kudi da mulki basa bayarwa!”’. 

Ya ce, “Ni kuwa mene ne shi wannan abun?” 

Ta ce, “Da, Zainabu na da ciki har tsayin watanni hudu”. 

Suman zaune ya yi, kafin ya tattara hankalinsa da nutsuwarsa ya mika su ga 

mahaifiyarshi, ya kuma murza idanunshi ya sosa kunnensa, ya tabbatar ba mafarki yake yi ba. 

Ya ce, “Don Allah Hajiya ki kara yi min bayani”’. 

Ta ce, “Abin da na fada haka yake Ali, Zainabu za ta haifa maka Da, naka na kanka, hakurinku da tawakkalin ku basu tashi a banza ba!!!””. 

Alh. Aliko sai hawaye ya soma sharewa, ya yiwa mahaifiyarshi sallama ya nufo bangarensa. Alwala ya yi ya kawo raka’o’i hudu kwarara domin mika godiyarshi ga Allah bisa wannan falala da ya yi mishi a lokacin da bai zata ba, a kuma lokacin da ya riga ya fidda rai. To ina ruwan Allah. Hajiya Zainab ta shigo ta sha kwalliya, cikin sassalkar shadda_ dinkin ‘yan Senegal, jikinta na fidda wani_irin sihirtaccen kamshi. Tunda ta shigo yake kallon ta har ta karaso gabanshi. Ta mika mishi kofin fadi-ka-mutu cike da tataccen rowan inibi mai sanyi. Cewa yake cikin ransa…. 

“Wannan kyakkyawar bafulatanar mace, kamar Beni take bata tsufa. Ga kyakkyawar zuciya da fawwala al’amura ga Allah, ba irin matan manyan dake matsayi irin nata ba. Ko kawaye bata dasu a Kaduna, sai ‘yan uwanta na gida Yola. Ba shige-shigen gidan malami babu na dan tsubbu. Komai na duniya bai fiya damunta ba. Sai ya bude mata dukkan hannuwanshi ta wuce ciki, cike da kunya. Ya mayar ya rungumeta. 

Ya tambaye ta ko me take so nan duniya ta fada mishi ya yi mata. Domin ya nuna mata farin-cikinsa da godiyarsa. Sai ta yi murmushi ta ce, 

““Addu’a za ka yi min. Allah Ya sauke ni lafiya”’. 

A lokacin Imam na ayji hudu na sakandire. Yayin da Shahida ke J.S 1. shi da kansa ya lura cikin Mami na kumbura, ya kuma san wannan kumburin ba komai bane Da ne a ciki. 

Don haka ya soma tara kudi in ya samu, in 

sun taru sai ya sayi kayan jarirai ya adana. Cikin na da watanni takwas Alh. Aliko ya shirya musu tafiya kasar Ingila, inda yake so ta haihu a can don ta fi samun kulawa. Sai dai girman cikinta yana baiwa kowa mamaki, ga shi dukkansu basu yarda da yin scan ba. Watanni hudu kamar watanni takwas, da ya shiga watanni takwas din kuma, kamar watanni goma sha biyu. Gidan Alh. Aliko na Birtaniya na nan garin Bournmouth, ‘flat? ne hawa daya, wanda aka gina da (Red-bricks), wato jan bulo, irin tsarin gidajen Ingila. Furanni sun yiwa gidan rumfa daga sama har kasa. Sannan ga ‘spring’ na bubbugowa daga cikin dutse. 

Daga Hajiya Zainab sai Hajiya Maama a gidan, a lokacin Almustapha da Shahida duk suna makarantar kwana. Sai da suka yi hutu ne Alh. Aliko ya taho dasu Bournmouth, a lokacin watan haihuwar Hajiya Zainab ya tsaya. 

Tun ana lissafin EDD har an gaji an daina babu alamar haihuwa. Sai da cikin ya shiga 

watanni goma cif, sannan ne likitocin ta suka yanke shawarar yi mata fida, wato (Cesarean). 

A ranar da za a yi aikin duk gidan kuka suke, kada Imam ya ji labari. Alh. Aliko ke tausarsu tare da basu karfin gwiwa. Karfe goma na safe aka shiga da Hajiya Zainab dakin tiyata. 

Suna zaune a kan wasu kujerun ‘waiter’ na asibitin, Nurses biyu suka nufo su rungume da jarirai cikin ‘showell’ farare sol! 

Dukkansu mikewa suka yi cikin al’ajabi, suka taryi Nurses din. Imam ya karbi daya, Hajiya Salamatu ta karbi daya suna kabbara, cike da girmama buwayar Ubangiji. 

Alh. Aliko ne kadai ya tambayi yaya Uwar? Tunda su murna tasa sun manta da ita. Suka ce itama lafiyarta kalau, yanzu za a tura ta dakin hutu. 

Imam ya rasa inda zai sa kanshi don muma. Kememe ya hana Shahida daukar jariran, idan ya dauki wannan ya kalla, sai 

ya ba Hajiya ya karbi dayar, wai yana so ya gane wacce ce Hassana wacce ce Hussaina?. 

Daga baya ya gane kwata-kwata basa kama. They are no more identical. Hassanar baka ce sosai, Husainar fara sol, sannan Hassana da Daddy take kama, yayin da Hussainar da Hajiya Zainab take kama, kasancewar ta Bafulatanar Yola ce. Ya ce, 

‘“Hajiya Maama na sake ki, ga matata ta zo!!!”. Ya nuna bakar wato Hassanar”’. Hajiya Maama da Alh. Aliko suka yi dariya, Hajiya ta ce, “Aure yanzu muka fara Imam, na linka shi igiya goma, wannan ‘yar bakar ba za ta razana ni ba. Mu buga ni da ita in yaso wadda ta fi son mijin ta kwace”. 

Alh. Aliko yana dariya ya ce, “Yo ban da shirme irin na Imam ga farar mace sol kamar Balarabiya ka ce bakar kake so, mai kama da ‘yan kauyen Chikun?” 

Ya ce, “Wallahi Daddy bakar nake so, don baka ga kayan da na saya mata ba”. 

Daddy ya ce, “Wacce kake so ita za’a baka Almustapha, insha-Allahu! Muddin ina raye!!!””, 

Dai-dai lokacin da Nurses suka turo Hajiya Zainab dakin hutu, gaba dayansu suka nufi dakin. Barci take sosai lokacin da suka shiga, don haka Nurses din asibitin suka hana su shiga don kar su tashe ta. Kwanansu uku aka sallame ta tare da Nurse guda daya wadda za ta dinga kula da yaran a gida har sai sunyi wata shidda, a ka’idar asibitin. 

Alh. Aliko ya narkar da kudi ba na wasa ba, amma wannan ba shine damuwarshi ba, face’ ‘yan jariranshi su kasance cikin koshin lafiya. 

Duk wani masoyin Alh. Aliko ya taya shi murnar samun wannan karuwa. Talakawan Kaduna, ‘yan siyasa da masu kudinsu kowa kawo barka da fatan alheri yake ta duk hanyar da ya san za ta riski Alh. Aliko. 

Ranar suna ya yiwa jariranshi wadanda duk mata ne huduba da suna SAFAH da 

MARWAH. Da fatan Allah Ya_ basu albarkacin (dutsen Safah da Marwah). 

Da zuwansu gida Imam ya fiddo jaka cikin kayansa ya soma fiddo kayan baby da suka basu mamaki. Sai dai na mutum daya ne, don bai taba zaton ‘yan biyu Mamin za ta haifa ba. Kaya ne masu kyau da tsada (unised). 

Mamaki ya ishi Hajiya Zainab, ta ce, “Imam ina ka samo kayan nan? Wa ya baka kudi?” 

Ya ce, “Siya nake yi Mami, ina tarawa ne tun sanda na ga cikinki yana kumbura, wasu abokan daddy ke bani, wasu cikin wadanda Daddy ke bani na kashewa a makaranta, amma na Safah ne kawai, ita Marwah in ta samu nata mijin, sai ya siya mata”. 

Da zuciya daya yake fadin maganarshi. Don tuni har ya daura musu auren. Har ga Allah shi iyakar gaskiyar abinda ke zuciyar shi yake fadi. Ta kama baki can kuma ta ce, 

“Ai ‘yan biyu ba’a yi musu haka, dole 

itama ka saya mata, ko ba za ka aure ta ba”. 

Ya yi dariya ya ce, 

“To zan sayo mata Mami” can kuma yayi dan tunani sai ya ce “amma ba da yawa ba”. 

Ta ce, “A’a Imam, yadda ka sayowa Safah saiti goma haka za ka sayawa Marwa saiti goma”’. 

Ya ce, “Nifa ba zan aure ta ba”. 

Ta ce, “Duk da haka, ai kanwarka ce. Kai babba ne dole ka zama mai adalci a tsakanin kannenka, in kana so su dinga girmama ka”. 

Tunda aka haifi yaran nan Hajiya Zainab ba ta san kukan su ba, Imam da Hajiya Mama ke rainon su. Shi yana rainon Safah, da yabi ya kankane, ko baki baya bari su dauketa sai Haj. Mama ta kwantar da murya ta rokeshi ya basu, ita kuma tana rainon Marwah. Kiri-kiri Almustapha yake nuna bambanci tsakanin Safah da Marwah, don ma Mamin na kwabar shi. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *