BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 5
by sumayyah Abdulkadir
tiryan-tiryan kuma rai-rai babu gargada, kai kace ‘Prince Charles’ ke magana.
Daga can dakinsu Marwa ta fito da sauri don ta sanar da su Daddy su kalli programme din, ta tarar su ma suna gani. Mami ta ce ta kirawo Hajiya da Safah don a lokacin Shahida tana Benin inda take bautar kasa. Hajiya Mama da Marwa suka shigo falon kowa yana tambayar ina Safah?
Can a study Marwa ta isketa, ta yi dai-dai da takardu tana ta aikin nata (karatu). Tace cikin ranta “ko huda-huda nan ya ganki ya barki, nagani idan karatun zaki aura”.
Ta ce, “Maza taso ki gani’”’.
Ta ce, “Me zan gani?”
Ta ce, “Ke dai ki taso, wani programme ne”.
Ta ajiye biron ta biyota tana mitar ba ta son tana karatu ana katseta.
Ta yi turus, ganin kyakkyawar fuskar Imam ma’abociyar zati da kamala, hadi da kwarjini bayyananne, ta cika fuskar dirkekiyar akwatin talabijin din jikin
bango (Plasma) dake falon. Ta ji gwiwoyinta sunyi sanyi. Amma don bakin rai sai ta daure fuska . Ai ba laifinta bane idan bata so Imam ba, mai sanya soyayyar ne bai sanya mata ba.
Ta kalli Marwa ta yi tsaki ta ce, “Yanzu a kan wannan ne kika taso ni daga karatuna? Mts!” Ta juya ta koma daki a fusace. Duk suka bita da kallo.
Itama Marwa sai jikinta ya yi sanyi. Da gaske ‘yar’uwarta BA TA SON Ya Imam, inama itace! Inama….Ina ma…..!!! Kiyayyar ta wuce ta zuci kadai har ta fito fili. Tunda har zai samu ci gaba irin wannan ta kasa taya shi farin ciki. Ranta ya baci sosai da abin da Safah ta yi, don haka ta bita dakin. Ta manta da gargadin data yi mata a baya kan zancen Ya Imam. Da alkawarin da ita Marwan ta dauka na bazata kuma yi mata Magana akan Imam ba.
Tuni ta maida hankali kan karatunta, ta tsaya a kanta ta ce, “Safah”.
Ta dago a fusace ta dube ta, “Saboda Allah
mene ne kuma???”
Ta ce, “Babu komai, abin da bakya so ne dole zan gaya miki, don bani da wacce ta fiki. Ya Imam bai cancanci kiyayya irin wannan daga gare ki ba don kawai yana son ki, yana kaunar ki.
Mutumin da ke sonka, to ya wuce komai, balle wanda ke son ka zama abokin rayuwarshi na har abada! amma ki yi tunani, ba nufina in tursasa ki bisa abin da bakya so ba”.
Ta juya ta fito ta rufo mata dakin. Safah ta yl tsaki ta ce cikin ranta, “Ai sai ki sani in so shi dole, sarkin kankanba, iyayi da rashin aikin yi kawai”’.
A can falo Daddy ya dubi Mami ya ce, “Wai me ake ciki ne maganar Safah da Almustapha?”
Mami ta yi shiru tana tunani. Hajiya Mama ta ce, “Ni dai ban taba ji ta yi zancen sa ba, Marwa ce dai na ga ta fi kula da al’amarinsa, amma wannan miskilar me ta sani ban da takarda da biro?”
Daddy ya ce, “Imam bai taba yin zancen
Marwah ba, tun ranar da aka haife su ya fada gaban kowa cewa Safah yake so, ni kuma na yi alkawari tun a wancan lokacin cewa ko bayan raina na ba shi Safah. Sai dai a halin yanzu ne ban san abin da suke ciki ba”.
Mami ta dago ta dube shi, “Tunda Imam bai taba tada maganar nan ba, ina ganin in da hali a barta. Domin Safah ba ta so na dade ina karantar ta. Ba abin da ta sa gaba sai karatunta da al’amarin dake gabanta”’. Daddy ya ce, “Zancen banza ne wannan, da sun fara jami’a aure zan yi masu. Sannan alkawarin da na dauka tun a wancan lokacin a kan Safah da Imam babu mai tada shi banda ikon Allah. Gara ma tun wuri ki sanar da diyarki bata da miji sai Imam in Allah Ya yarda”’.
Hajiya Mama ta ce, “Wannan magana haka take, ita ma Marwa Allah ya kawo mata nata a kan lokaci dan a hadasu a aurar gaba daya a lokaci daya”’. Gadan-gadan Safah da Marwa suka fara jarrabawar fita sakandire, duk da Safah ta
fi Marwah dagewa a kan karatu, wannan bai hana dukkaninsu samun gurbi a jami’ar Ahmadu Bello ba, a kuma fannin da kowaccensu take so.
Don haka da _ yardar iyayensu. da amincewarsu suka tattara suka koma Zaria (off campus), flat guda Daddy ya kama musu a kusa da makaranta, da karamar mota kirar ‘kia-Picanto’ don zirga-zirgarsu cikin makaranta da wajen ta.
Suka soma karatunsu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, don Imam din bai kara ta da zancen Safah ba, ya ba ta lokaci har Zuwa sanda yake ganin ta mallaki hankalin kanta.
Ko waya ya yiwa Mami, Daddy da Hajiya Maama, cewa kawai yake a gaishe ta. Sannan shi ma ayyukan gabanshi sunyi mishi yawa. Ko lokacin da zai ‘emailing’ dinta baya da shi, duk da ya sha gwadawa
yana jin sa a rufe. 2K 2k ok ok
D addy ya wakilta Zahraddeen Maitama
babban yaronshi dake kula da gidajen man-fetir na ‘Dan Kasa_ Holdings’, matsayin mai kula da al’amuran karatun Safah da Marwah a Zariya, kasancewar shi dan asalin garin Zaria. Duk abinda suke bukata kamar kudi da sauran matsalolin karatun su Zahraddeen za su nema.
Shi kansa wannan mukamin da Daddy ya baiwa Zahraddeen albashi yake bashi mai zaman kansa, sannan a boye kamar wani security ne dake ganowa Daddy halin da ‘ya’yan nasa ke ciki, da irin kawayen da suke mu’amala dasu.
A watanni uku kacal, Zahraddeen, ya fahimci Safah da Marwah ‘yan biyu ne kawai, amma mabanbanta a halayya da dabi’a.
Safah ta fi Marwah mai da hankali a karatu, ta fita nutsuwa da rashin son hayaniya, sannan Marwah ce ma’abociyar hulda da jama’a, duk da bata da samari tana hulda da mazan ajinsu da kawaye da yawa.
Don haka Zahradeen ya sanar da Daddy
obserbations dinsa a kansu. Ko jarrabawar zangon farko da suka yi, Safah ta fi Marwa scoring GPA..
Duk da haka Marwa ba ta fadi ba, ta lashe duka takardunta da maki kadan, wanda ake kira aberage. Ba kamar na Safah ba oberall din ajinsu. Don haka ran Daddy ya baci. Karfe Shidda daidai na yamma suka yi parking motar su a harabar gidansu suka shiga a gajiye. Biola ta karbi jakunkunansu tana yi musu sannu da zuwa.
Gidan ko’ina fes don Biola (yarinyar da Mami ta basu take musu aiki) bata wasa da tsaftarsa, sai kamshin air freshner ke tashi. Ko zama basu yi ba Zahradeen ya yi musu dirar mikiya, Daddy biye da shi. Suka taho da gudu za su rungume Daddy ya daga hannu ya dakatar dasu.Ya ce,
“Babu gaisuwa tsakaninmu Marwah, zuwa na yi in ji dalilin da yasa Safah ta fiki maki Marwah?”
Ta sunkuyar da kanta ba ta yi magana ba. Daddy ya shiga yi mata fada ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Har saida ta
soma kuka. Ya ce babu ita babu kawayen da take hulda dasu, in ba haka ba za ta koma gida ya ba da sadakarta tunda aure take so karatun bai dame ta ba.
Tana kuka sosai take ba shi hakuri, ta ce insha Allahu ba za ta kuma ba, kuma zango mai zuwa za ta dage.
Sai kuma ta bashi tausayi, ya sassauta ya shiga yi mata nasiha a kan ta dinga yin koyi da ‘yar’uwarta a kan komai. Ya yi musu addu’a a ranar ya koma Kaduna bai kwana ba.
A karshen satin Zahraddeen ya kawo musu ziyara kamar yadda ya saba. Marwah ba ta gida ta je saloon, sai Safah da Biola a gidan wacce ke kicin tana hada musu abincin rana.
Tana zaune a falo cikin atamfa mai karshen tsada, kanta babu kallabi, ta matse gashinta a tsakiyar ka, farin gilashin dake idanunta ya kara ma fuskarta ilhama da kwarjini, tana nazarin wani littafin ilmin halin dan adam wanda a fakaice ba komai ne ciki ba sai applied Christianity, amma
Malaman kimiyyar halin dan adam ke amfani dashi a jami’o’I matsayin hanyoyin gyara mu’amalar zamantakewar dan-adam, tana tsintar na tsinta, tana zubar da na zubarwa, sunan littafin “The Power of Positibe Thinking’.
Ya danna kararrawar kofar shigowa, Biola ta bude. Ya bayyana cikin kyakkyawar suit (Japanese) da bakin gilashin Prada a idanun shi.
Falon ya gauraye da kamsassan turaren shi na (Dior Addict), kafafunshi rufe cikin cober baki, da ganin shi ka ga gogaggen dan boko mai ji da bokon da aljihunshi da ya soma nauyi albarkacin aikin sa’a da ‘Dan – Kasa Holdings’.
Kallo daya ta yi mishi ta ji zuciyarta ta buga a yau, kamar yau ta fara ganinsa. Ba wai yau ta fara ganinsa ba. Saidai bata fiya yiwa mutum kyakkyawan kallo ba. Yau ta ganshi ne sosai a gabanta, ba daga nesanesa ba. Shi ma gabansa ne ya fadi, sakamakon ganin Safar yau a ainahinta ba cikin mayafi da rigunan sanyi kamar
kullum ba.
Ta lalubi dankwalinta ta daura, ta zare gilashin idanunta ta yi mishi barka da zuwa, tare da mikewa tsaye (alamar girmamawa irin ta bature ga bakonshi).
A tare suka zauna cikin kujeru masu fuskantar juna. Shiru ta ratsa na ‘yan dakikai, wani chemistry mai ban mamaki na aiki a zuciyoyinsu da kwayoyin idanun su, yana shiga cikin zukatansu. yana kurdawa har cikin kwakwalensu.
Sai da suka ci mintuna biyar suna kallon juna sannan suka kawar da kai a tare, tare da aje wata boyayyar ajiyar zuciya.
Ya ce, “Ina kanwata ne? Ban ji motsinta ba?’
A sanyaye ta ce, “Ta je saloon ne?”
Ya ce, “Na zo ne in ji ko akwai matsala?” Ta zuki iska ta fesar, cikin yangarta ta halitta. Ta ce,
“Dama dazu nake ce da Marwah ta yi maka waya, akwai wasu tedtbooks da suka shafeni da nake bukata matuka ban samu a school bookshop ba; ‘Modern Dental
Assisting’ (Bird Robinson), ‘Esthetics and Biomechanics in Orthodontics’ (Rabindra Nanda), ‘Endodontics’ (Mahmoud Torabinejad) ko za ka samo min a cikin gari?
Sannan motar mu tana bamu matsala kwanan nan, akwai bukatar a sake wata”’. Tunda ta soma magana yake kallon siraran labbanta dake motsi a hankali kamar basu ke furta maganarba, tareda_ sauraron sassanyar muryarta dake fita cikin nutsuwa da taushin kalami. Turancinta a sarke, kai kace a Turai take karatun.
Da kyar ya daure ya ce,
“Gobe zan je Lagos ki rubuta min sunan littafan sai a nemo. Ina zan iya rike wannan compled language naku? Maganar mota zan bar muku tawa ku yi amfani da ita kafin in je Cotono in na dawo Lagos, don Daddy yayo odar wasu motoci daga Cyprus sai a daukar muku daya”.
Ta ce, “Anya mun yi amfani da motar ka? Babba ce sosai, bana son abinda zai ja hankali a kanmu?”
Ya ce, “alright! To ku lallaba takun a hakan kafin a kawo zuwa nedt week, shi kenan?”
Ta ce, “Babu malta a fridge, sannan muna bukatar naman gongoni da juices”.
Ya ce, “Wannan ba matsala, gobe kafin in tafi zan biyo in kawo”’.
Ya mike yana amsa call, sai da ya gama ya juyo ya dube ta da wani irin lallausan murmushi, ya rankwafa ya ce,
“Ko zan iya samun lambar wayar uwargijiya ta?”
Ta dago cikin slow-motion ta zuba mishi kyawawan idanunta farare tas, tana girgiza kai ta ce,
“Bani da waya!”’.
Ya yi mamaki sosai. Sannan ba tare da ya tsawaita mamakin ba ko ya tambayi dalili ba ya zura hannuwanshi cikin aljihun wandonshi ya fiddo kan wayoyi guda hudu ya zube mata guda biyu a kan cinyarta. “Zama haka babu waya a wannan zamanin kanwata ba zai yiwu ba, ko kuma in ce bai dace dake ba. Kuma bashi da dadi.
Ba wai sabida nishadi da bata lokaci kawai da ake yi da wayar ba, ita wayar dai tanada nata amfanin akan-kanta. Ki yi hakuri ki yi amfani da nawa kafin in taho miki da wasu daga Cotono…..ki yi min alfarma kada ki ce min a’ah…….”
Ba ta san me yasa ta kasa yi mishi musu ba. Ya juya ya fita tare da cewa,
‘Na barki lafiya”’.
Ba ta dauke idonta a bayan shi ba har ya fice daga falon, zuciyarta na kai kawon da bata taba ji a rayuwarta ba.
Ta maido idanuwanta bisa cinyarta a hankali, ta zubawa wayoyin da ya zube mata ido.
Wayoyi ne masu tsadar gaske, HTC da BB. Ta debe su ta kaisu ga hancinta, tana shinshina su, ni’imtaccen kamshin ‘Dior — Addict’ ya kama su sosai.
Sai ta samu kanta da lumshe ido, tare da bude su duka a tare, cikin wani sabon
al’amari da ba za ta iya kwatantawa ba. 2K 2K ok
ASALIN SA Z ahraddeen Aminu Maitama, dan talakawa ne tulis! Bazazzagen usuli ne da ya fito daga cikin Mallawan Zazzau na asalin unguwar Tukur-Tukur. Ya yi karatu da tallafin Gwamnati da kulla-kullar mahaifiyarshi da taimakon Allah a jami’ar Ahmadu Bello. Inda ya karanci (Petrochemical Engineering). Ya sha matukar wahala wajen karatun nan, wanda aka yi cikin halin babu, da taimakon Scholarship, abokai da Inna Binta. Bayan kammala hidimar kasa ya sha wahala sosai kafin ya samu aiki. Shekaru hudu kwarara ya kwashe duk da kyan sakamakonsa da nagartar karatunsa bai samu aiki ba. Sai da Gwamnatin NPC ta hau mulki ya samu aiki a matatar man fetur ta NNPC, da taimakon Aliko, wanda ya kasance abokin mahaifin wani abokinsa Idris, aka dauke su su biyu.
A wani juyi da NNPC ta yi, ta zubar dasu a kwandon shara da ta samu wadanda suka fisu yawan kwali. Wannan ya zaburar da Zahraddeen ga komawa makaranta ya yi masters shi da Idris, sannan mahaifin Idris ya hadasu da tsohon Gwamna Aliko DanKasa ya basu aiki da ‘Dan-Kasa Holdings’. Shekarar baya ne Allah ya yiwa Idris rasuwa ya barshi da kewa mai yawa da gurbin da har gobe bai cike ba. Domin bai kara yin aboki ba tun rasuwar Idris. Haka yake cikin rashin karsashi a duk abinda yake yi.
Da lallashi da addu’a Daddy ya samo kanshi, domin malamai na musamman ya sanya suke mishi rubutun dangana ganin yadda gidan mansa ke neman durkushewa saboda rashin maida hankalin Zahraddeen, wanda ke hidimta mishi da dukkan zuciya da amana, ba don kudin da yake biyanshi ba.
Bai taba samun hazikin ma’aikaci irin Zahraddeen ba. Mai innobations cikin kwakwalwarsa (fasahar kawo_ sababbin
abubuwa na cigaba iri-iri). Don haka shi ma bai dauke shi da wasa ba, albashi yake biyanshi mai tsoka, kuma shine (Managing Director) na ‘Dan-Kasa Holdings’ baki dayan ta.
Daddy na yabawa da hazaka da amanarsa, wannan na daga cikin dalilan da ya sanya ya damka mishi amanar kula da walwala da karatun ‘ya’yan shi. Yana kuma gudanar da aikinsa sosai cikin gaskiya da tsayawa bisa matsayin sa. Saidai kuma gashi ga dukkan alamu, a yau Zahraddeen na neman wuce matsayinsa.
Zahraddeen matashi ne dan kimanin shekaru talatin da haihuwa, amma ayyukan da yake gudanarwa ‘Dan Kasa Holdings’ ko dan arba’in sai haka.
Duk inda ake neman kyau ga da namiji, to Zahraddeen ya mallake shi. Kin san dai kyau irin na Mallawan zazzau, farare ne tas masu dogon hanci da yawan suma. Saidai shi Zahraddeen wankan tarwada ne mai kyawawan idanu, farare kal kuma manya masu cike da ilhama.
Shi ne da na farko a gun iyayensa, sai kannin shi Umma, Rabi’a da Nura. Su kenan Inna ta Haifa. Mahaifinshi ya dade da rasuwa tun yana sakandire. Don haka nauyin mahaifiyarshi da kannensa duk a kanshi yake.
Ita Umma anyi mata aure a nan cikin Zaria, Rabi’a na _ karatu) a_ babbar sakandiren ‘yanmata mai tsohon tarihinnan ta Sarauniya Amina dake cikin Kaduna, sai autansu Nura wanda ke JS (karamar sakandire).
Wadannan iyali sun taso cikin kulawa da tarbiyyar nagartacciyar uwa Inna Binta, wadda bata taba gazawa a kan bukatunsu da karatun su ba don sun rasa mahaifinsu. Babu irin sana’ar hannun da ba ta yi don ta tallafi rayuwarsu, ta inganta farin cikinsu. A rugarsu ta ainahin iyaye da kakanni, dake can bayan garin Lere tana kiwon garken shanu da suka gada itada Yayarta daga wurin iyayensu, haka take saida su daya-bayan-daya don hidimar_ karatun Zahraddeen mai tsada, har Allah Ya sa ya
kammala. Shanu kuma babu ko daya. Don haka su ma ‘ya’yan basu da abin so da kauna tamkar ta, da burin faranta mata. Barin Zahraddeen wanda duk abin da ya samo na mahaifiyar shi ne.
Daga fara aikinshi da ‘Dan _ Kasa Holdings’, kodayake kafinnan ma ya tara sosai a aikin da yayi a NNPC, ya bige ginin gidansu ya tsantsarawa Inna Binta ‘bungalow’ gida na zamani mai rufin daukar hankali (modern European bungalow) kalar ruwan kasa mai duhu (deep brown), gidan kuma ciki dawajensa fentt ne ruwan madara, ya ajiye mata karamar motar shiga don bukatunta. Nura ke kaita ko’ina ta ke so. Sannan yayi wa kanshi nashi flat din duk anan cikin gidansu, daidai rayuwar kowanne dan boko mai aji daidai nasa, wato ma’aikaci mai sa’a. Cikin tsari na masu ilmi da sanin ciwon kai, ba na karyar rayuwa ba.
Komai dake cikin gidansu Zahraddeen mai amfani ne, baya bari inna tayi girki da icce saida cooker, bata markade sai a blander,
bata gashi a garwashi sai a oben, bata dumame sai a microwabe zaka rantse da Allah ba gidan tsohuwa bane, duk da dai ma bata tsufan cancan ba, bazata wuce shekaru hamsin da biyu ba, da kwarinta da kuzarinta da koshin lafiya duk albarkacin haihuwa da ilmin data tsayawa Zahraddeen yayi wanda yafi karfin aljihunsu, ga mai aiki ya ajiye mata tana yi musu gyaran gida amma duk rintsi Inna ke girki, don ita kadai Zahraddeen ya yarda da tsaftar ta a duniya kuma ita kadai din ce ke yi mishi abincin da yake gamsar dashi mai cike da hikima irin ta manya da sanin sirrin girki walau na gargajiya ko na zamani, don sau tari Rabi’a tana makarantar kwana.
Ya bawa Umma jari mai tsoka take dinki da kekunan dinki na zamani, har shagon dinki take dashi a kofar gidan ta, ya zuba mata kwararrun teloli tana biyansu kuma tana samu sosai, ya sauyawa Nura da Rabi’a makarantu masu nagarta.
Ba shi da abin da zai ce da Alh. Aliko sai fatan alheri, domin a jikinsa yake samun
duk wannan rufin asirin.
Ko da yake morar juna suke, amma dole ya gode mishi, don abin da yake ba shi ya fi karfin aikin da yake yi mishi.
Ga shi yau ya tsinci kansa cikin wani al’amari mai GIRMA a kan diyar shi, duk da cewa ya san bakin rijiya ba wajen wasan yara bane. Don haka ya soma yaki da zuciyarshi, ta hanyar yakar sabbin kibiyoyin dake huda kowanne sako na cikinta.
Sai dai duk iya kokarinsa a wannan daren ya gaza rintsawa, ko ya runtsan, surar Safah yake gani cikin murmushi. Abin kamar azal.
Don haka da ya yi sallar asubahi ya dade yana rokon Allah sauki cikin al’amarin, amma kamar turi, Safah Dan Kasa, ta kankane ko’ina na _ zuciya’ da kwakwalwarshi, ta kassara gangar jikinsa bata barshi da ko sako daya da zai sanya tunanin kansa ba.
Don haka a washegari shine mutum na farko da ya danna musu kararrawa, Biola