BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 6 by sumayyah Abdulkadir
Don haka a washegari shine mutum na farko da ya danna musu kararrawa, Biola ta zo ta bude, ya umarceta da ta kwaso kaya a boot, sannan ya sanya kai cikin falon cikin sallama.
Tashinsu. kenan daga barci suna kalaci. Safah ta daga fararen idanunta tana kallonsa, wadanda a take ya gano sun kankance sun dan tasa sunyi ja kadan, alamun rashin wadataccen barci kamar nasa.
Kada ya yi haufi (in ji zuciyarshi), itama ta kwana cikin kwantankwacin irin situation din da ya kwana jiya. Marwah ta tura mishi kujera ta ce, “Bismillah Yaya Deen, join us…..”’
Ya dafa kujerar yana kallon Safah cikin mayatattun sedy idanun shi, ya ce, “Anya anyi haka? A kan hanyar airport nake”’.
Ta ce, “Na sani, wannan sammakon da ka yi bai isa a ce ka yi kalaci a gida ba”.
Ya ce, “Ba yadda Innata ba ta yi ba don in yi hakan amma ban yi ba. Amma idan Yaya Babba ta yi min iZini sai in ci”.
Safah ta aje cokali ta ce, “In dai nice sai in ce kada ka ci”.
Shi da Marwa suka yi saurin kallon ta. Ta ce, “Bai ji maganar Inna ba don me zai ji tawa?”
Ya yi ajiyar zuciya ya nuna ta da dan mukullin shi ya ce, “Hidimarki ce ta hanani, na yi sammako_ saboda sabgogin ki”.
Ta murmusa gently ta ce,
“Zauna Deen, in yi serbing din ka!”. Da kanta ta zuba mishi chips da ‘yar sauce ta hanta da koda da aka yayyanka siri-sirt aka kuma yi ta da koren tattasai a wani plate mai girma, ta mika mishi daga tsayen da yaken, don bai zaunan ba.
Amma sai ya ce, “Ku yi hakuri bana jin yunwa, ga sakon an kawo, sauran kuma ki saurare ni. Sai kin ji wayata”’. Suka yi sallama ya juya ya fita.
Bayan sun kammala Biola ta kwashe kayan, suka shiga wanka suka yi shirin shiga cikin makaranta.
Mamaki ya kama Marwah ganin Safah da kan waya har biyu tana sanya su a
chargi. Cikin mamaki ta ce.
“Yaushe kika sayi waya?”
Ta yarfar da hannu,
“Ba nawa bane na Zahraddeen ne” Cikin mamaki ta ce, “Zahraddeen kuma? Yaushe ya zo? Ko manta su yay dazun?’
Cikin gundura da tambayoyin kanwar tata ta ce, “Jiya, lokacin kin fita saloon”.
Ta jinjina kai tana mamaki. Don dai kowa ya yi kokarin ganin ta rike wayar amma ta ki. A yau ga Zahraddeen ya sanya ta farat daya ta rike su. Ba ma daya ba har biyu. Babu musu, ba daga murya, ba busa ba daga hannu.
Da daddare har sun kwanta wayar Safah ta yi kara, ta mika hannu ta dauka don ta san babu wanda zai kirata sai shi.
A kasalance take magana, ta ce, “Baka kwanta ba?”
Ya ce, “Na kasa ne, na sauka lafiya
amma tunani na neman mayar dani mara lafiyar karfi da yaji”.
Ta rage amon muryarta don kada ta tashi Marwah ta ce,
“Kai kuwa_ tunanin me_ kake Zahraddeen?”
Kai tsaye ya ce, “Tunaninki?’
Ta yi ajiyar zuciya mai sanyi, cikin ranta ta ce, “Nima haka!”. Bata san cewa a fili ta fada ba. Kunnuwanshi sun zuko mishi. Yayi murmushi mai fidda sauti, cikin ranshi kuma godiya yakewa Allah. Da ya takaita mishi wahala da rashin tabbas din da yake hangowa al’amarin.
Daga nan sai me? Sai hira ta barke kamar ba Safah ba. Ita kanta har mamakin kanta ta shiga yi, ta yadda cikin kankanin lokaci Zahraddeen ya tankwasa zuciyarta ya sauya mata akida da tunani.
A wannan daren aka kulla soyayya mai ban mamaki da Safah Dan Kasa, ba ta taba tsintar kanta a ciki ba.
Tun daga ranar kullum sai sun raba dare suna waya. Har ya bar Lagos ya nufi Kwatano. Ya sanar da ita ya samu littafan a Lagos.
Yanzu ne Safah ta san tana cikin soyayya ba soyayyar kuruciya da ake son tursasata a kai ba. Wasu emotions ke laga-laga da zuciyarta a kan Zahraddeenin, dake aiki har cikin zuciya da kwakwalwarta.
Cikin sati daya Marwa ta fahimci komai, Safah da Zahraddeen soyayya suke. Soyayya tsurarta. Wadda ta kasa boyuwa a al’amuransu da appearance dinsu. Da yadda suke raba dare suna hira mai cin rai a waya, a zaton Safah barci take. Ta sha mamaki ba kadan ba, domin ko Zahraddeen bai ko kama kafar Ya Imam a komai ba.
Tausayin dan’uwanta da soyayyarsa suka kara ninkuwa a ranta. Sai dai ta amince ko za ta mutu da soyayyar Imam ba za ta taba bayyanata ba, saboda son da yake yiwa ‘yar’ uwarta.
Saidai son ya kasheta idan yana kisa, amma bazata taba barinsa yayi tasiri akanta ba, koda kuwa ace Safah din ta mutu kafin ya aureta. (wannan itace kauna ta hakika, wadda tayi karanci a wannan zamanin har ga ‘yan uwa na jinni kuwa, kowa kansa ya sani da nasa farin-cikin. Allah Ka sa mu fi karfin zuciyoyinmu ameen.) Kwananshi hudu a Kwatano ya yi ma Safah waya ya sanar da ita yana bisa hanya. Ashe Marwa ba ta gama shan mamaki ba, don yau Safah da kanta ta shiga kicin ta hada ‘dinner’ mai rai da motsi da taimakon Biola.
Sannan ta shiga wanka ta fito ta shirya cikin riga da siket na swiss lace ruawan zuma. Tana fesa turare kararrawar shigowa ta yi kara, sannan wayarta ta hau ruri tabbacin Zahraddeen ya iso.
A karo na farko gigicewa_tayi. Kasancewar a yau ne zata taba fuskantar wani da namiji a rayuwar ta, da idanun soyayyah. Da kanta ta bude
mishi kofa suka bi juna da kallo, wani irin sassanyan kallo mai kwantar da zuciya. Kafin kowannensu ya _ saki sassanyan murmushi mai dauke da boyayyar ajiyar zuciya.
Ta kauce ta ba shi hanya ya shigo cikin caftan na wagambari mai hasken sararin samaniya, gilashin idonshi na yau fari ne kal dan sirit, wanda ya fiddo da zahirin cikar kamalarshi na cikakken namiji, wanda rayuwa ke garawa tare da shi, ga bokon, ga opportunity, sannan ga mahadin su wato kyau.
Safah ta yi nisa sosai a kallon sa, ya yi murmushi ya soma karkada mata makullan mota a idanunta.
Ta ji kunya sosai, ta wuce ciki suka zauna cikin kananan leathers da suka yiwa karamin falon nasu kawanya.
Ta ce, “Ya hanya? Ya zirga-zirga?” Ya ce, “Komai lafiya, ga motarku ta iso”. Ya mika mata mukullin karamar ‘Optima’, daidai lokacin Marwah ta
II O <
fito daga daki tana rike da takardu zata shiga cikin makaranta.
Ta yi dan jim, tana kallon su, sannan ta saki fuska suka gaisa da Zahraddeen. Ta ce,
“Motar ta iso ne?”
Ya ce, “Tana waje, muje ku gani, in ba ta yi ba sai a sake’”’.
Dukkansu suka fito. Marwah na cewa “ballema nasan zata yi, Yaya Deen, bazaka zabo abu mara kyau ba”. Kwarai motar ta birge su, ta yi musu daidai. Kalarta fara sol!
Marwa ta bude ta zauna, ta tattaba gaban motar, ta kunna, ta bata wuta, ta ce, “Kai! Yaya na ka iya zabe”’.
Ya ce, “Koh?”
Ta ce, “Wallahi’’.
Ya ce, “To alhamdulillahi’’.
Suka koma cikin gidan suna hira dukkansu. Marwah ba ta dade ba ta kwashi takardunta tayi daki ta bar musu falon, ko daukar laccar ta kasa
zuwa, saboda yadda suka kasa boye soyayyar dake zuciyoyinsu a gabanta. Ranta a jagule da mamaki, tausayin Imam da al’ajabi. Me Safah za ta yi da Zahraddeen yaron Babanta? Duk yadda Ya Imam ya kallafa rai a kanta tana nufin ba za ta aure shi ba ko me? Ta kira Mami tana haki, Mami ta ce, “Ke lafiya kike numfarfashi?”
Ta ce, “Mami…”
Sai kuka ya kwace mata…….. tausayin Imam take har ba ta san me za ta ce da Mamin ba.
Ta ce, “Ki yi min magana mana, ya za ki fasa min kuka alhalin ban san abin da ya faru daku ba. Wani abu ne ya faru? Ina Safah?”
Ta ja shessheka amma ta _ kasa magana, ba ta son ta hada Safah da iyayensu, don ta san muddin suka ji Sai sunyi wani abu a kai. Ko dai su dakatar da karatun ko su tada maganar aure yanzu. Kuma ita Safah za ta blaming kan tana yi mata sa-ido,
wanda a kullum Mami ke nuna musu rashin amfanin sa.
Bugu da kari tayiwa kanta alkawarin daina shiga zancen Safah da Ya Imam, tunda hakan rashin jituwa yake haifarwa a tsakaninsu. Don haka ta yi saurin alkawartawa ranta cewa babu ruwanta. Ta ce da Mami, “Bani da lafiya ne”
Ta ce, “Me ya same ki?”
Ta yi diri-diri na rashin gaskiya ta ce, “Ciwon marata ne har yau bai daina ba’.
Ta ce, “To ki nemi Zahraddeen ku je asibiti, Allah Ya sauwake, kuma ki samu Zam-Zam ki tofa ayatulkursiyyu kafa bakwai ki sha, insha Allahu za ki samu sauki”’.
Ta ce, “To Mami”.
Ta ce, “Daina kukan haka nan, wannan ciwon duk mata suna yinsa, sai dai na wata ya fi na wata. Nima da girmana har yau ban daina shi ba. Kira min Safah mu gaisa”’.
Ta ce, “Tana falo ta yi barci ne”,
Ta ce, “To ki gaida ta, Hajiya Maama na gaishe ku, ga Shahidah ma tazo tana kewarku”. Ta yi dariya ta ce “Allah Mami aunty Shahida bata kewarmu da ta zo mana weekend ai” Ta daga labule domin iska ta shigo, nan ta hango su bisa dining suna cin abinci. Ba abinda ya dame su sai junansu, sun dace, sun yiwa juna daidai, kamar don junansu aka halicce su. Kalar fatarsu iri daya. Ga kuma alamun kowannensu ba mai yawan magana bane. Fatar bakinsu kadai ke motsi ahankali.
Ta saki labulen ta koma ta kwanta tana cewa, “Ya Allah ka janyo hankalin ‘yar’uwata zuwa ga mai sonta tun ranar da ta zo duniya, tun tana tsumman goyon ta, koko tace tun tana ciki. Idan kuma babu alkhairi a ciki, Allah Ka zaba mata wanda ya fi alkhairi, ba tare da ran iyayenmu ya baci da ita ba”.
Soyayya tsakanin Zahraddeen da Safah ta ci gaba da mikawa cikin salo mai ban mamaki. Basu iya sati basu sanya junansu a ido ba. Ba shi Kaduna ba shi Zaria, kullum a tafe yake.
In kuwa bai zo ba, to suna makale a waya ana ta yiwa MTN da ‘Glo’ ciniki na fitar hankali. Sai da jarrabawar karshen zango ta matso sannan suka saurara, inda ya tattara ya koma Kaduna don ba zai so abinda zai shafi karatun ta ba.
Duk da haka su kan gaisa na ‘yan mintuna su kuma ji lafiyar juna.
Da suka kare jarrabawar suka sami hutu na watanni uku, suka tattaro suka dawo gida.
Sai dai kuma Safah cike take da taraddadin wannan hutu, don ta san babu wanda zai yi na’am da zabinta daga iyaye har ‘yan uwa da Kakarta. Wannan bai sa ta ji ko dar a zuciyarta ba game da soyayyar da take yiwa Zahraddeen Maitama. Shi din, ya san
mene ne SO? Ya san darajar abinda yake son, ya kuma tya tafiyar da shi ta hanyoyi daban-daban. Ta yadda duk wadda zata so shi, zata so shi ne da dukkan zuciya, ruhi da bargon jikinta ko da ta ki Allah, shi ba dan bariki ba. Amma ga matar da yake so, mugun dan soyayya ne kamar ba’indiyennan haifaffen Iran John Abraham. Irin kalaman da yake furta mata cikin waya, idan ka ganshi a zahiri rantsewa zakayi ba shi yake fadar su ba, sabida tsare gida, da rashin son raini.
Don haka ne bai sha wahalar yiwa zuciyar Safah kamun kazar kuku ba. Ba ta da wani tunani sai na Zahraddeen, ba ta da wani ra’ayi sai nasa bata da wani buri sai na mallakarsa, matsayin intimate —lifetime partner (abokin rayuwa na har karshen rayuwa).
Gaba daya ta mance da Almustapha dake dake can wata uwa duniya yana fama da dakon soyayyar ta, wanda
HI O <
shima ke sonta da dukkan zuciya, ruhi da gangar jikinsa. Ta mance da wanda ya rayu cikin kaunarta, tun bata san kanta ba.
Ya yi hidima da soyayyarta, shekaru goma sha tara. Rana daya tasa kafa ta yi fatali da wannan, auren SO ko auren KAUNA bari muga wanda ke da tasiri.
Karfe takwas na dare Zahraddeen ya iso gidan uban gidansa, kasancewar ya zama dan gida tsakanin Mami da Daddy duk basu bawa zuwan nashi wata ma’ana ta daban ba.
Marwah da yake ta san dawar-garin ta zuba ido don ganin yadda za a karke. Duk da halin sa-idon, ba halinta bane, wannan dai confrontation ne like a chase-game da take son ganin yadda zai kare. Don haka take ganin bai kamata ta kira sa-idon nata da sunan sa-ido ba, saidai ta kira shi curiosity. Wanda hali ne na kowanne dan adam akan abinda ya bashi mamaki.
Bayan sun gaisa da Mami shi da Daddy suka shiga kasafce-kasafcen su cikin takardu da computer. Daga bisani Daddy ya hau sama ya barshi da Mami.
Itama bata jima ba suna ‘yar hirar Innarshi ta yi dakinta. Safah ta fito daga dakinsu, ta yi kyau kamar kullum cikin cotton-lace mai taushi fari sol da yarfin silver, riga, zani da kallabinsu, dinkin da bai kama jikinta ba. Domin Mami ta yiwa ‘ya’yanta_ tarbiyyar sanya sutura, don haka da wuya ka gansu cikin matsattsun kaya irin na ‘ya’ya ire-irensu.
Tun daga nesa suke sakarma juna murmushi mai _ sanyi. Kwanaki biyunnan da suka yi basu ga juna ba, jinsu suke kamar shekaru biyu. Ta zauna a kujerar dake fuskantarsa, da karamin teburin gilashi a tsakaninsu, wanda aka dora faranti cike da kayan marmari uku; tuffaha, inab (grape) da pear. Shi kuma ya zame daga kujerar
II O <
ya zauna a kilishi, ya rausayar da kai ya ce,
“Yan makaranta, barka da hutu!’’,
Dariya ya bata sosai sabida yadda yayi maganar. Ta ce “Wane irin hutu an dankara mana uban assignment a cikin hutun?”’.
Ya ce, “Babu damuwa, don na san you can make it, keep the flag flying….”. Sai ta sa dariya.
Ya yi shiru zuwa wani lokaci ya ce, “Safah, na zauna na yi tunani mai yawa a kan al’amarinmu, ni talaka ne Safah, kuma sannan dan talakawa. Wadanda basu aje ba, basu kuma baiwa wani ajiya ba, sai abinda karfin jikinsu da lafiyarsu ya samo musu, wanda ke samun abinci a karkashin mahaifinki. Kina ganin za ki iya aurena a hakan in nemi Daddy alfamar neman auren ki?”
Maganganun shi sun mata ciwo. Ta
UII O <
ce, “Da ban san da hakan ba Zahraddeen na amsa ina sonka?”
Ya langabar da kai ya ce, “Za ki iya zama dani Safah cikin dan akurkin gidanmu a Zaria? Ba zan iya rabuwa da Innata inyi nisa da ita ba Safah a dalilin aure. Tayi min komai a rayuwa. Bayan kasancewarta Uwa, ta taka matsayin Uba ma. Za ki tya taimaka min in tallafi rayuwar ta, da marayun kannena?”’
Ta lumshe ido cikin wata sabuwar kauna dake kara mamayarta, ta kuma lullube zuciyarta, ta ce,
“Kada ka yi haufi a kaina Zahraddeen, soyayyarmu hadin Allah ce, ba don wasu. kyale-kyale na rayuwa_ ba. Continue be your natural-self Yaya Deen I like it, and I respect your balues too much……. Zahraddeen din nake so ta yadda har bana iya waiwayawa in hango hierarchy din da shi ya ke gani. Wanda so baya la’ akari
99
da su……. sai bayan ta furta hakan
kuma kunya ta lullubeta don ganin irin yadda ya saki jiki sharaf ya zubawa fatar bakinta dake motsi ido kawai sai ta ke ganin kamar har ta zarme tayi subutar baki. Sai tayi sauran gyara zancenta da cewa
‘Ni dai fatana da burina shine ka rike soyayyata cikin amana. Ka yarda dani, nima in yarda da kai, Allah Ya yarda damu bakidaya. Idan ka yi min wannan ni kuma na yi alkawarin zama da kai cikin kowanne hali, akwai ko babu, dadi ko akasin sa……” Unconditionally ya mika mata hannu “Shake my hands, Safah….. na gode da soyayyarki……..na rokon Allah Ya fidda ni kunyar soyayyar…. Ya bani ikon fita hakkokinta,…. Ya bani ikon muhimmantata fiye da duk wani al’’amari da dan adam ke _ burin samu!!!.”
Suka hade hannunsu wuri guda kamar
masu kulla alkawari. 2K K
Mami ta soma tsarguwa da yawan zuwan Zahraddeen cikin gidansu, da yawan kebewar da suke yi shi da Safah, ba dai wani waje suke tafiya ba anan ‘main’ falon su ne, don da sai ya yi wata guda bai zo gidan ba, amma tun dawowarsu hutu kullum ya taso ofis yana gidan, tare suke dinner da jama’ar gidan.
Ga wata sabuwar al’ada da Safah ta bullo da ita na yawan kwalliya wadda ta lura saboda Zahraddeen take yinta. Ta shiga damuwa ainun tana neman bayani, ta san babu kuma inda za ta same shi sai a bakin Marwah. Sai dai kuma Marwah ba a jin ta bakinta in dai a kan ‘yar’uwarta ne, suna rufe sirrin junansu ta yadda ko su iyayensu basu san tsakaninsu ba.
Sannan Marwan ba ta taba fadin aibun ‘yar’ uwarta sai dai alherinta. To haka ita ma Safah, duk da halayensu ba daya bane tana matukar kaunar ‘yar’ uwarta, kashewa suke su rufe ba
wanda ya ji ba wanda ya gani.
Ko fada su kai a junansu baya wuce kwana daya sun shirya sun manta komai. Don haka ta ga gara ta tunkari Safan kai tsaye ta yi mata bayanin abinda take zargi.
Karfe tara na daren ranar ta yiwa Zahraddeen rakiya ya tafi. Tana dawowa ta cimma Mami a gefen gadonta ta yi tagumi.
Ta zauna a gefenta ta sauke mata tagumin ta ce, “Maminmu, lafiya kika zuba wannan uban tagumi? Har na shigo baki san na shigo ba”.
Ta dube ta sosai da idanunta da ba sauki a cikinsu, ta ce,
“Safah”’.
Ba ta amsa ba illa ta dube ta, sabida yadda ta kirayi sunan nata_ cikin kakkausan harshe.
Ta ce, “Me ke _ tsakaninki da Zahraddeen?”
Ta sunkuyar da kanta kasa. Ba ta yi magana ba, sai da Mami ta yi mata