BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 8 by sumayyah Abdulkadir

 BABBAN GORO BOOK 1 CHAPTER 8 by sumayyah Abdulkadir


bar mishi falon.Ya yi dariya ganin yadda ta cika, ta yi tam, kiris take jira ta fashe. 


Shahidah kuwa dake gefe tana kallon su ciwo ta ji sosai na halin ko in kula da Safah ta nunawa _ dan’uwanta, wanda ya taho tun daga_ tsakiyar duniya don ya gansu, abin mamaki akan idonta ko kunyar kwayar idanun ta yarinyar nan bata ji ba, a take ta ji ta fara tsanar Safah, duk da cewa ita dinma ‘yar uwarta ce, amma ai wata kusan….. hausawa suka ce “ta fi wata”, amma ta ga shi bai damu ba, dariya ma yakeyi sabida rashin zuciya. Mami ta fito fuskarta yalwace da murmushi, ya isa gareta ya amshi tray din da ke hannunta. Hannun shi ta kama suka isa dining tare, ita ta yi serbing din shi da kanta. 


A lokacin da Daddy ke saukowa daga matattakalar bene, ya yi arba da Imam ba zato ba tsammani. 


Ya ce, “What a surprize? Cikin satin nan nake shirin cewa ka zo, to kuma 

sai ga ka. Amma me yasa baka sanar dani zuwan ka ba?” 

Yana dariya ya ce, “Nima tafiyar ban shirya mata ba Daddy, kamar wanda aka tunkudo haka nan na ji duk hankalina yayo gida….(nostalgia)” Marwah ta shigo da ledoji biyu a hannunta ta yi arba da Yayannasu, ta watsar da ledojin ta rugo da gudu kamar za ta rungume shi, amma sai ta tsaya a gabansa ta maida hannuwanta baya ta sarke su tana dariya. 

Ya mika mata hannu ya ce, “Come on…. my dear Sissy, na yi kewar ku da yawa”. 

Ba ta mika mishi hannun ba ta yi dariya ta ce, “Har dani Ya Imam a wadanda ka yi missing? Ban yarda ba”. 

Ya dan fiddo ido “Na yi karya kenan, gemai-gemai da ni ko?” 

“A’a, ni ban ce ba’. Ta fada cikin dariya. 

“To ki yarda dani, I missed all of you a lot”. 

Marwah ta ji dadi, yau ne rana ta farko da ya taba yi mata kalami na kulawa tun tasowar su. 

Mami ta ce, “Kyale Marwa ka ci abincin nan Imam’. 

Ya ce, “Bari Mami in fara shan furar uwargida na” 

Sai da ya shanye furar Haj. Maama, sannan ya aje jug din ya soma cin abincin Mamiunsa, cike da nishadi da kewa mai yawa. W ata tara ba kwana tara ba. 

Ya ce, “Gaskiya ne da Bature ya ce, “No place like home”. Mami na yi missing girkin ki yadda bakya zato, kullum na zo cin abincin gongoni sai na tuna ki Mami, na tuna girkin ki mai sawa mutum ya manta sunan sa. 

Ba don kowa da inda Allah Ya tsaga mishi hanyar abincinshi ba, da babu inda zan je in barku Mami’. 

Ta yi murmushi ta ce, “Imam kenan, nima kullum sai na tunaka, sai in ce da Imam yana nan da kaza ta faru, da kaza bata faru ba’. 

Marwah ta shiga dakinsu da ledojinta, sai ta tarar da Safah tana sanya kayan barci, ga dukkan alamu kwanciya za ta yl. 

Ta girgiza kai ta shiga toilet ta yo alwala, a ranta tana cewa da wannan banzan yaron ne ya zo da yanzu tana nan tana shafe-shafe da murje-murje. Ta yi alwalarta ta yi sallar isha’i, ta fice falo inda ake ta hira ta barta a nan. Kwanan Safah uku a daki ba ta fitowa don kar su hadu da Yaya Imam din, ko yunwa take ji sai dai ta yi waya kichin a kai mata abinda take so. Shi ma Imam din ya share ta baya shiga sabgarta, ga shi ga dukkan alamu a yanzu kam ya fara amincewa da gaske Safah ta ke ba ta son shi. 

Idan a da yana yi mata uzuri da kuruciya a yanzu fa? Shekarunta goma sha tara, ta isa ta bambance abinda take so da wanda ba ta so. Wato dai ta isa ta yiwa rayuwarta ZABI ba tare da an tursasa ta ba. 

Shi kuma ya amince ba zai aure ta 

bisa tursasawar iyaye ba. Zai yi mata yadda take so muddin ta furta da bakinta cewa ba ta son shi. 

A dakin Hajiya Mama yake a safiyar yau suna hira, ta ce, “Ban da abin kuruciya irin na Safah ga dan’uwanki jinin jikinki, wanda ya san ciwo da darajarki, amma ki nace sai wani can da bai san zafin ki ba?” 

Sai kuma ta tuna da wa take magana, ta yi hanzarin gyara subutar bakinta, ta ce, “Au, wanda yake son Safah shi Alhaji zai baiwa Marwah’’. 

Imam ya yi tsai da ranshi yana duban ta a tsanake. Ji yayi tamkar aradu ta rikito kansas Amma _ ya _ nuna maganarta ba ta taba zuciyarshi ba. 

Ta hanyar cewa 

“Shi wanda take so din a ina yake?’ Hajiya Mama ta ga babu amfanin yiwa Jikan nata rufa-rufa, kallo daya ta yi mishi ta karanci matsanancin KISHI a kwayar idanunshi. 

Duk sai ta ji babu dadi, ta kuma yi Allah wadai da surutun ta. Koda yake 

dole kuma ta gaya mishi yadda abun yake, tunda kuma Daddy ya kashe maganar. 

Ta ce, “Ma’aikacin Alhaji ne, wa yake da suna? Ni sunan wuyar fada yake mini’. 

Ya ce a nitse, “Kutama ko Peter ko Maitama?”’ 

Ta ce, “Kai, ba haka na ji sunan ba”. Ya mike ya zura takalmin shi yana cewa, “Idan kin tuna ki kira ni, kin san baki san sunanshi ba kika fara gaya mini?” 

Ta ce, “Dawo ka zauna zan tuna a hankalv’. 

Ya ce, “Kada ma ki tuna, bana son j1’. 

Karfe sha biyu na rana Zahraddeen ya shigo gidan, cikin shadda edcelcior maroon colour, kanshi babu hula wanda hakan ya _ bayyanar da kwantacciyar sumar_ kanshi ta Mallawan usli, sai sheki shaddarshi take tana maiko tana nuna tsadarta. Kiris ya rage suyi karo da Imam dake 

fitowa daga kofar cikin — gida. Dukkansu basu san juna ba sai a suna. Imam ya kan ji sunan ZAHRADDEEN MAITAMA a bakin Daddy ba tun yanzu ba, ta yadda yawan ambaton Zahraddeen din da Daddy ke yi Imam ya fahimci shi din wani hadimi ne mai muhimmanci ga Daddyn, domin adadin kaunarka da mutum adadin yawan ambaton sa a bakin ka, Zahraddeen kan ji dana ALMUSTAPHA a_ bakin Daddy, amma basu taba ganin juna ba. 

A take Zahraddeen ya yankewa zuciyarshi wannan ne Almustapha, tunda ga kamannin Safah nan a kyakkyawar fuskarsa, ta wani fannin kuma da Daddy yake kama. 

A take ya ce, “Imam…..” 

Shi kuma ya ce, “Maitama….” 

Suka yi hannu suna murmushi. Amma fa zuciyar kowanne na zabalbala da kishin dan uwan ansa, amma fa tsabtataccen kishi na masu aiki da hankali da tunani, ba kallon juna suke 

don son hango aibu ko nakasun junan su ba ko makamancin hakan a’ah, kallo ne na son hango how much lucky are you??? Kowannensu ganin dan uwansa yake a matsayin wanda yafi kowa sa’a a duniya. Imam ya fasa fita ya yiwa Zahraddeen jagora har main parlour. 

Yau kadaran-kadahan Mami ta yiwa Zahraddeen karba ta mutuntawa. Tunda ya zama dolenta. 

Ta ce, “Zahraddeen ga Almustapha fa’. 

Ya ce, “ai na canka Mami, from the first glance…” (daga kallo na farko) 

Ta ce, “Imam. Ga Zahraddeen din Daddy”. 

Ya ce, “Nima na canka Mami, ko daga tsagin Mallawan’’. 

Duka suka yi dariya. Suka zauna tare cikin kujera, daga nan kuma sai hira rai-rai-rai kamar sun dade da sanin juna. 

Cikin dan lokacin Mami ta soma fahimtar Zahraddeen mutum ne mai 

dadin mu’amala, kuma dole mutumin da ke alaka da shi ya so shi, saboda saukin kansa. Nutsuwarsa da yadda yake fidda kalamansa a ilmance, duk wata kalma data fito daga bakinsa mai ma’ana ce, daga yadda yake Magana zaka fahimci zurfin ilminsa, ga kyau da kwarjini, gashi mai wayayyen kai. Safah bata yi laifi ba don tayiwa kanta sha’awar auren Zahraddeeen domin ta ko’ina yayi a rayuwa. 

Ta tabbatar Daddy na da hujjar shi na son Zahraddeen, kuma bai yiwa diyarta zaben tumun dare ba. Auren gata yake so yayi mata. 

Sai ta russunar da kwayar idonta kasa ahankali cikin saduda. Sai azahar Daddy ya_ shigo yana_ baiwa Zahraddeen hakurin bata mishi lokaci da ya yi. 

Zahraddeen ya ce babu komi. Saima halayen Alhajin dake kara masa ganin kimarsa. Bai dauki kanshi a bakin komi ba. Suka nufi masallacin Daddy dake wajen gidan suka gabatar da 

sallar azuhur. 

Kamin su dawo Mami da Marwah sun shirya dining, ita ‘yar mulkin tana daki ko fitowa ba ta yi ba. Tana jiyo muryar Zahraddeeeeeeeen dinta…… ; cikin tausasan lafuzzansa. Ya na yiwa Imam bayanin nasarorin da “‘Dan-Kasa Holdings’ ta cimma a _ wannan shekarar. Bata san cewa hawaye ke zuba tarara daga idanunta ba. Saida ta ji su cikin kunnuwanta, da yake a kwance take. 

Bayan sun kammala cin abincin Imam ya yi musu sallama zai je Rabah Road. Zahraddeen ke jan Daddyn _ cikin motarshi ‘buick’ da Imam ya kawo mishi, a kan hanyarsu ta zuwa ofishin Daddy. 

Suna tattauna al’amura = masu muhimmanci a garesu. Kamar Uba da dan sa, da yake matukar so. Kamin su gangaro kan muhimmiyar maganar dake cin zuciyar kowannensu. 

Daddy ya ce, “Kai nake saurare Zahraddeen, ya ya ka yi shawara da 

Inna?’ 

Yana tukin, amma hakan bai hana shi sunkuyar da kai ba, ya ce, “Na karbi Marwah Daddy, na karbi musayan ka da hannu bibbiyu, ka yi min addu’a Allah Ya sa ta so ni……….27?” Dariya ta kama Daddy saboda yadda Zahraddeen ya yi maganar cikin sanyi? Kamar mai tambaya, kamar kuma mai hasashe. Ya mika hannu ya dafa kafadar Zahraddeen yana bubbugawa ya ce, 

“Ta ina Allah ya rage ka da diya mace ba za ta so ka ba?” 

Ya cira kyawawan idanunsa ya dubi Daddy. Ya daga mishi kai yana murmushi cikin bada karfin gwiwa, ya ce, 

“Kada ka yi haufi kuma kada ka karaya Zahraddeen, you are a genius…… 

Allah Ya yi maka duk wata falala ta rayuwa, da dan adam ke burin samu. Ba Marwah ba, duk ‘yar wanda kake so za ka aura Zahraddeeni, idan fa har 

za ka cire inferiority compled din daka Sanyawa zuciyarka na kasncewar ka karkashi na. Tunda har Safah ta so ka, duk da akidunta da _ baudaddun dabi’unta, a gabana take kuka saboda son da take yi maka. Wanda na tabbata har yau bata daina ba, don tanada_= karfin’ zuciya ne _ da sadaukarwa. 

Don haka count yourself among the luckiest, wanda ake so fiye da Imam dina. (yayi murmushi) Ni na gaya maka Marwah zata so ka fiye da son da Safah take yi maka. Ba duk abinda muke so a rayuwa lallai shi zamu samu ba. 

Muna barin wani abu duk son da muke mishi don wani abu muhimmi, wanda ya fi son zuciyar mu muhimmanci. Ba duka mafarkanmu ne suke zama_ gaskiya ba. Su, (mafarkan) kamar ‘ya’ya suke; abin nufi, muna daukar cikinsu, amma ba kowadanne muke yin sa’ar haifewa 

ba. 

Wasu tun suna ciki suke zubewa. Wasu kuma kuma a haife su a mace. (Zaynab Alkali). Irin wannan auren albarkatacce ne Zahraddeeni, kuma ba’a ganin fa’idarsa sai an zauna da juna, an fahimci juna ciki da waje. Soyayyah ta gaskiya ba lokaci daya take faruwa ba, sai a hankali, idan an zauna tare. 

Ni dai fatana da kai shine ka zamo tsayayyen namiji wanda zai fi karfin gidansa, kada ka yi la’akari da kasancewar Marwa diya a gare ni ka kasa lankwasa ta. 

Ka lankwasata da duk irin tarbiyyar da kake so ta mike da ita. Sannan auren ka da Marwah, baya nufin shi kenan ba za ka kara aure ba, ka auro duk wadanda kake so ka kara, in har za ka 1ya yin adalci a tsakanin su, nine kuma mai biyan sadakin kowaccensu”. Zahraddeen sai ya yi murmushi yana mamakin halayyar GIRMA irin ta Alhaji Aliko. Ko da_baya_ son Marwah, ya yiwa zuciyarshi alkawarin 

rike ta da amana saboda mahaifinta. Sai dai yana shakkar Marwah dinnan, a yadda ya ga takunta da tsarin rayuwarta da kyar in za su daidaita, kwata-kwata halayenta da dabi’unta opposite na ‘yar’uwarta ne, ko ma ya take, ko yaya ne, ya yi alkawarin zai rike ta amana tare da dora ta kan turba sahihiya. Anya??? 

2K ok 6 

anar alhamis 9/9 na shekarar alif dari tara da casa’in da tara (1999) Baffannin Zahraddeen da_ kannen mahaifiyarshi suka gabatar da komai na auren dansu da Daddy ya ce sadaki kawai yake so. 

Domin shine mai alhakin § yiwa Zahraddeen aure, ko da ba diyarshi zai aura ba. Amma Baffan Zahraddeen ya ce tunda yaro yana da halin yi a barshi ya yi daidai_ karfinsae TUWON GIRMA…….miyar sa nama. 

Duk wata dukiya da ake bukata kafin aure da al’ada ta gadar sun gabatar 

tare da sadakinsu, sama da yadda Alhajin ya nema. Da lefe saitin jakunkunan lefen zamani_shidda, dankare da sittiru na masu rufin asiri, don dai shi Zahraddeen baisan wasu kayan adon mata ba, Rabi’a bata sani ba, balle kuma Inna. Umma kuwa ai ba’a zancenta, bakauya ce ta a bada labari ko Rabi’a tafita sanin kwalliya, don haka matar Peter ce abokin aikinsa Kafilat ta hado lefen ya biya komai bayan ta ci riba yadda taga dama, don bayerabe baya aikin banza. Itama da taimakon makociyar ta Maryam da yake ita bahaushiya ce kuma mata ga ma’aikacin Zenith ta san yadda ake hada lefe a al’adar hausa. Sun tsaida ranar daurin aure asabar mai zuwa, saboda su Marwah za su koma makaranta litinin, wato kwana biyu bayan daurin aure. 

Marwah ba ta san bikin da ake yi ba, ta dai ga Zahraddeen ya daina zuwa wajen Safah, sai ta dauka cewa 

Daddy ya ja masa birki ne tunda ga Imam ya dawo. 

A satin duk kafafen yada labarai na radio, talabijin da jarida na_jihar Kaduna, basu da muhimmin kanu sai na yada labaran gayyatar daurin auren ‘ya’yan tsohon Gwamnan, Alh. Aliko Dan Kasa, wanda al’ummar Jihar basu taba mantawa dashi ba. Har gobe cewa suke “baza’a taba yin Gwamnati irin ta Dan-Kasa a Kaduna ba!!!’”’. Yana tuna musu da gwamnatin Janar Murtala Ramat Mohammed ta dan lokaci a kasarmu Najeriya, amma kuma ‘rebolutionary’ a zuciyar al’ummah duk da ta dan takaitaccen lokaci ce; considering his zero 

tolerance for corruption…… , for ladity…..,maladministration and nepotism….. 

A kuma ranar ne Alh. Aliko ya tara iyalinshi baki daya, ga mahaifiyarshi da kanin mahaifinshi Malam Safiyanu a gefe, ya umarci Hajiya Mama da ta 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *