BABBAN GORO BOOK 1 END CHAPTER 13 by sumayyah Abdulkadir KARSHEN LITTAFI NA DAYA
Ya ce, “Me yasa tun a lokacin baki gaya min ba?”
Ta ce, “Ta yaya zan gaya maka alhalin lokacin idon ka ya rufe da soyayya? Baka ji ba ka gani balle ka gane inda ake maraba da soyayyar taka? Ta yaya zan shiga tsakanin ‘yan’uwa biyu? Karewa ma wadanda suka fito duniya tare a lokaci daya?”
Ya yi murmushi kadan ya ce,
“Ni ban sani ba, kuma ko da na sanin ba abin da zan iya. Safah kawai nasan rai da zuciyata ke so a fadin duniyar nan, kuma ita za su ci gaba da so har duniya ta nade.
Zan yi maneji haka Shahidah, kuma ina ji a jikina watarana na zuwa da zata so nin, musamman idan muka haihu tare, wuyarta mu_ kasance karkashin inuwa daya, shine mai wuyar kuma ya tabbata. Nidai na san bazan tsaya ina lallashin ta ba ta so ni, ai Sai ta raina ni,” Shahida dariya ce ta kama ta tace a ranta “Ya Imam ho! Son girma kamar gyambo. Wane raini
ne kuma ya saura tsakanin miji da mata? Ai da daban, yanzu daban babu zancen discipline sai unity and cooperation. A fili kuma ta ce,
“Yayana!”’.
Ya dago ya dube ta.
“Safah fa ba kai ne ba ta so kwatakwata ba, I’m sorry to say……. kai ma kana da laifi, mutum ne _ kai, tough…… ”
Ya saki rigar da yake ninkewa ya dan fiddo ido ya ce, “Ni din?”
Ta ce, (cikin dariya) “Kwarai, baka lallashi, tarairaya da nuna zahirin soyayyar ka.
Ba haka Zahraddeen yake ba, mutum ne dan soyayya wallahi, wanda ya iya nunawa mace so har ta ji tamkar babu wani da namiji da ya saura a duniya bayan nata.
Da wadannan makamai Zahraddeen ya yaki zuciyar Safah, kuma ya samu. Dalili shine, mu mata muna da indibidual differences a fannin soyayya. Wata tana so a nuna mata kauna a za
hiri da badini, wata tana so amma a boye, wato daga ita sai mijinta.
To Safah tana daga cikin rukunin matan da ke so a nuna musu so da zuciya da gangar jiki a zahiri da badini, idan suna tare, soyayyar da yake yi mata bata boyuwa, amma kai akidarka daban ce. Ban jin ko kalaman soyayyar ka iya.
Ka daina treating dinta kamar sauran matan da ka sani. Ka yi la’akari da bambancin kabila da al’ada, matan Turawa da kuke tare dasu basu san darajar kansu ba balle su san martabar da Allah ya yi musu, shi yasa suke hauka a kan ku, suke binku kamar jakai, su suke nuna muku soyayyar ba ku kuke nuna musu ba.
Unlike namu matan da aka halitta da kunya, kawaici, da _ bin _al’ada. Musamman Safah in kayi duba ga yanayin rayuwarta, za’a iya cewa kanta a duhu yake, banda karatunta batasan komai ba sai wanda aka koyar da ita. Abin nufi, she’s not edposed to
modern society…. not interested to social networkings….. She is just acting according to her edperiences wato yadda aka tafiyar da ita a baya.
Bata wani san cewa yanzu mata ke bin maza ba. Batasan wai mata tarairayar
namiji suke ba…… Safah fa ko talbijin bata kallo…… Ba kawa ba abokiya balle aminiya. ….Bata karance
karance sai wanda ya shafi karatunta. Wannan ce kake cewa bazaka rarrrasa ba sai dai ita ta kwantar da kai ta so ka? To a wane dalili? Rannan fa ina ji kana cewa wai Mami ta rarrasheta haba Ya Imam! Wannan dutse ce mai babban daraja_ like a diamond…..bazaka siye ta da sauki ba!!! Sannan an halicce mu mu mata da juriya fiye da ku, ta yadda ko muna son mutum zamu iya jurewa mu danne. Har sai ya sauke kai ya nemi soyayyar tamu don kashin kansa.
Ta wace hanya ka taba neman soyayyar Safah asanda ta soma mallakar hankalin kanta? Kwanciya fa kayi
kana harkokin cigabanka, sabida tabbacin da kake dashi kawai na cewa taka ce! Babu wanda ya isa ya kwace, anya?
Don haka Ya Imam _ nake baka shawarar ka cire rawanin girman nan ka lallashi matar ka, ka nemi soyayyarta….. (a hankalce), ka mantar da ita Zahraddeeeeni….duk da nasan ta zuciyarta ta Marwah ce bazata kuma darsa mata wani abu akan mijin Marwah ba. Ka ji tausayin ta mana, an rabata da wanda ta mikawa zuciyarta sabida kai, kuma ta yi biyayya, ai ko bata cancanci jin tausayi ba, ta cancanci rarrashi. Babu abinda zai ragu daga jikin ka don ka yi hakan. Ni na gaya maka idan har za ka jure da hakan wallahi za ta sauko”.
Murmushi ya yi yana mamakin a ina Shahida ta san duk wannan? Wannan ba abin mamaki bane domin Shahidah ‘yar Siyasa ce. Sai dai bai tambaye ta ba, bai kuma ce ya karbi shawarar tata ko bai karba ba? Saidai can a
karkashin zuciyarsa ya yarda cewa kowanne irin ilmi da irinnasa amfanin.
A kokarinsa na son kawar da tasirin da zantukan Shahida suka suka soma yi a yanayin sad a zuciyarsa kada ta fahimci hakan sai ya ballo sabon zance. Ya ce, “Ke kuma aure sai yaushe Shahidah? Duk wadannan AIhazan da ke yi mana sintiri a gida kullum ta Allah ina lura dasu fah, me zai hana ki fidda daya ki aura idan hankalinki ya kwanta da shi?”.
Ta ce, “Wallahi Ya Imam duk suna da iyali, ni kuma ba zan auri mai mata ba”.
Ya ce, “Allah ya yi zabin alheri, amma ya kamata ki san cewa kin girma fa (at 26) ya kamata a ce ne a yanzu kina da yara biyu”.
Dariya ta yi ta fita tana cewa, “Tunda kai ga shi ka riga ni yi sai in jira naka ‘ya’ yan mu raba, idan ban samu mara mata ba”.
Shi sam ya mance da wani sako da ya shigo mishi, Shahidah ta tafi da hankalinsa sosai. Sai da ya gama hada kayanshi tsaf, sannan ya dauki wayar, a take kiran shugabansu Mr. Ben ya shigo. Ya tambaye shi har yau bai taso bane?
Ya ce, “Zan taso anjima kadan”’.
Ya zauna bakin gadon shi ya bude sakon, bai san lambar ba. Ya karanta kamar haka:
“Za ka tafi, baka ce da Daddy komai ba”.
Nan take ya gane mai lambar, ya yi murmushi ya koma ya kishingida da pillow a karkashin hakarkarin sa, ya tura mata gajeren sako.
“Ban san mai lambar ba’”’.
“And you want to know waye ne koh?”
Da alama a kufule tayi reply din.
Ya yi murmushi ya kai hannu cikin sumar kanshi yana cakudawa, a yayin da numfashinsa ke racing yake fita da sauri da sauri.
Ya yi kokari ya yi replying amma ya kasa danna alphabet s din, saboda yadda wata irin kasala ta saukar mishi. Wani zazzabi-zazzabi ya soma kokarin rufeshi nan take sabida azabar soyayyar da yake dandana.
Gashi dai fada take yi ba kalaman soyayya ba, amma ji yayi kamar rungumeshi tayi tana blowing kisses on him. Gaskiyar Shahidah ne wannan dutse ce mai babban daraja like a diamond…… bazaka iya sayensa da sauki ba!!! Kowanne ‘acting’? dinta akansa burgeshi yake mai dadi ne ko mara dadi.
Da kyar ya samu ya rubuta kalmar “Eh”,
Ta ga nema yake ya yi yawo da hankalinta, sai ta kashe wayar gaba daya, ta koma gadonta ta kwanta abin tausayi. Ta rasa abin da ke mata dadi.
Sai da ya yi wanka ya zuba orange shirt DKNY product, riga mai dogon hannu da bakin wandon jeans, ya taje sumarshi ta kara kwanciya akansa, ya yi shiri tsaf kai ka ce half-caste ne, wato (ruwa biyu). Duk da duhun kalar fatar jikin sa.
Ko da yake ta wani fannin Imam din ruwa biyun ne, Mamanshi Shuwa Arab, Baban shi Bahaushe.
Yana rataye da wata kyakkyawar bakar jaka wadda su komatsen passport, ID card, wayoyinshi da mukullai ke ciki, ya nufi dakin Hajiya Maama suka yi sallama, sannan ya taho dakin Mami.
Sun jima suna sallama ya kasa tafiya, kuma ya kasa tambayarta abinda idanun shi ke son gani. Gane hakan da Mami ta yi, ya sanya ta ce, “Ka je mana ku yi sallama da kanwar taka”. Ya ce, “Kyale ta Mami, ita ya kamata ta fito ta yi min rakiya amma ban isa ba. Don haka kawai ki gaishe ta, ki gaya mata cewa, na tafi’”.
Mami ta rike hannunshi ta ce, “Idan ita yarinya ce kaima yaron ne da za ka dinga biye mata kuna kunci da juna? Wannan ba ya cikin tsarin musulunci, sam baya ciki, ko da ace ba ma’aurata kuke ba, what is the cause of all these nonesense?”’.
Ya ce, “ita za ki tambaya Mami, ba zan dinga shiga al’amarinta tana harara ta ba, ko ba mijinta bane ni ai gaba nake da ita, amma yarinyar nan ba ta jin kunyar ko a gaban waye ta harare nt”.
Mami ta yi murmushi ta ce, “To ka yi hakuri, babba juji ne”’.
Ya ce, “A’a, wallahi ban da ni Mami, yanzu sai in targada ta kuma in kwana lafiya wallahi’”.
Ta ce, “Je ka ku yi sallamar ka yi hakuri ta ci albarkacina”’.
Tana rike da hannun sa har saman bene, ta murda kofar anyi sa’a ba ta rufe da mukullin ba, suka shiga Imam na bayan ta.
Kudundune take cikin bargo, sai rawar
dari take. Mami ta ce, “Lafiya Safah? Duk uban zafin nan da ake kika shige cikin bargo?”
Ta bude idanunta a hankali, sun kankance sunyi ja. Da sauri Imam ya karasa ya janye bargon, ta yi hanzarin dunkule jikinta saboda kananun minis dake jikinta.
Daidai kanta ya zauna ya kai hannu bisa goshinta, zafi rau kamar wuta, sai rawar dari take, hakoranta na karo da
juna kaf-kaf-kaf! Ya ce, “Subhanallahi, Mami ba ta da lafiya…”
Duk ya gigice ya rude, rudewa da gigicewa irin wanda Mami bata taba ganin yayi ba. Tuni ya hullar da jakar hannunsa. Itama Mamin ta karaso ta dauki kanta ta aza a cinyarta, ta ce, “Kashe kanki kike so ki yi Safah, ki dinga kulle kanki kina cuta ke kadai cikin daki?”
Ba ta amsa ba kwayar idanunta ta mayar ta rufe. Zara-zaran gassun idonta suka bi idon suka yi linkif.
Mami ta nuna mishi doguwar riga a sakale jikin ‘hanger’ ta ce dauko ta sa mu tafi asibiti, kai kuma ka tafi kada jirgi ya tashi ya barka”’.
Wani irin kallo ya yiwa Mamin ya ce, ‘In je ina Mami? Alhalin bata da lafiya?” cikin fushi da haushin Safah Mami ta ce,
“To zaman ka ne zai sa ta warke? Ko me ya same ta ai ita ta jawa kanta. Ayi mutum sai taurin kai da_rashin tawakkali? Za ki hada kanki da hawan jini haka kawai? Me aka yi miki? In dai Imam ne tafiya zai yi ya bar miki kasar ma baki dayanta ba garin ba….. Aure kuwa saidai ki mutu, ko kin mutun zamu sa shi ne kawai ya wankeki ya kaiki kabari ya dawo mu shafa fatiharsa da wata, wadda ta fiki da duk abinda kike takama dashi, ni banda kai ma wa zai kwashi wannan mai bakin halin da bakar zuciyar?”
Yayi dariya aransa yace “mami kenan’, a fili ya ce, “Mami ni fa ba inda za ni sai Allah Ya bata lafiya”
Ta ce da shi, “To gwale ni (gwasalewa), ai dama kai ba’a yi ma gwanin ta in dai akan ta ne”.
Ya motsa baki, yana so yayi dariya. Ta taimaka mata ta sa rigar ta rufa mata mayafi, Mamin na rike da ita suka fito.
Mami ta ce, “Ni ba zan je bama, kuje sai kun dawo Allah ya sauwake. In kuma jirgi ya tashi ya barka kai ka jiyo”.
Har jikin mota ta rako su, ta bude mata kofar gaban motar ta shiga ya tada motar masu gadi suka bude get ya ja motar suka fita.
Mami ba ta koma ba sai da ta ga fitarsu daga get din gidan, ta koma cikin gida tana addu’ar Allah Ya nuna mata ranar da za ta ga Safah da Almustapha matsayin mata da mijin dake matukar son junansu, ko yaushe ce wannan ranar? Ko tanada rabon ganinta?? Ko yaushe zata zo??? Ko zata zo din kuwa???? Ko dai mafarkanta na gaya mata gaskiya ne????
Zuciyarta cike take da wani irin
tsoro da firgici mai yawa a dalilin mafarke-mafarkenta a dan tsukin akan Safah da Almustapha, masu nuna mata ko zasu yi zaman aure, to ba yanzu ba. Sai can wani karni mai zuwa a nan gaba. Lokacin da al’amuran rayuwa zasu juye su rikide su chanza da al’amura marassa dadi. Ya kuma sa tana da _ rabon_ ganin ‘ya’yansu da jikokinsu. Har ma da tattaba-kunne in Allah Ya nufa. A lokaci guda kuma tana tunanin halin da Marwah ke ciki da nata angon, ko su kuma wace irin wainar suke soyawa? Tunda wadannan har yanzu sun ki daidaita kansu, su san cewa Annabi ya faku. Ba duk abinda kake so a rayuwa kake samu ba kuma ka zauna lafiya. Amma su sun ki gane hakan da gangan.
MU HADU A LITTAFI NA BIYU. -Takori