BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 2 by sumayyah Abdulkadir

 BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 2 by sumayyah Abdulkadir

race. Ya ja motar aguje, kamar za ya tashi sama. Ya ce, (kamar mai tambayar zuciyarsa ba Safah din ba) “……. Yanzu na tabbata dan halak, ba shege bane ko???” Wani irin kuka ya kwace mata ta shiga girgiza kai tana fadin “Ya Imam da gaske?? Ka sake ni??? Daya, biyu, har uku……???7” Idonsa na kan titi bai dubeta ba bai tanka mata ba. A lokacin da yai parking a harabar gidansu. Ta dauki takardar ta dunkule a hannunta ta yi cikin gida da gudu, saura kadan ta fadi, gaba daya ta firgice ta rude, rudewa irin wadda bata taba yi ba, hankalinta ya kai kololuwar tashi a lokacin da ta rabe a gefe ta warware takardar tana karantawa; 

“Ni Almustapha Zubair Dan Kasa, na saki matata Safah Dan Kasa saki uku. A bisa bukatar kanta, ina yi mata fata da addu’ar alherin duniya da Jahira”’. 

Sulalewa ta yi ta zauna a kan dandaryar kasa a corridor din da zai sadata da hanyar cikin gida…. Wani irin gumi (zufa) ya soma bubbugowa daga kowanne sashe a jikinta. 

Me za ta ce da iyayenta, daga tafiya asibiti? Sai saki uku ringididis? Da wane ido za ta dubi Mami? Me zata ce da Daddy bayan ta yi masa alkawarin yin biyayya ga umarninsa? Babu irin yabon da baya yi mata, ya yarda da ita da halayenta na kwarai fiye da Marwah. Itace abar misalinsa da alfaharinsa indai wajen halayen kwarai ne, Marwah ce mara kirki kullum, mara kyan hali, mara jin Magana. Ta toshe baki tana kuka, jikinta yana rawa. 

Ta dade a wurin bata san inda kanta yake ba, batasan abinda ya kamata tayi ba, zuciyarta ta riga ta kekashe da tabbacin cewa, iyayenta tsine mata zasuyi ko su sanyata a turmi su kirba suyi miyar kubewa da ita muddin ta basu wannan takarda ta kuma_ budi 

baki ta gaya musu da bakinta. Don haka ta soma tunanin matsera,…… tun kamin la’anar Daddy da Mami su tabbata a gareta…. tana jin sanda ya tada motar aguje ya bar harabar gidan su, tafiyar da ya tabbatar shi da dawowa……. sai wani babban ikon AI

llah ne ya kawo Daddy zai wuce cikin gida 

ya ganta a nan durkushe tana kuka, cikin mamaki da tashin hankali ya cira ta, ta mike yana tambaya “Lafiya? Me ya faru? Ina Imam din?” 

Ya jero tambayoyin a jere don duk hankalinsa ya gama bashi cewa wani abu ne ya faru d a Imam din, don Mami ta gaya masa sun fita tare asi

biti. 

Safah ba baki sai kuka take tana jujjuya kai, kawai tayi kundumbalar mika mishi takardar dake hannunta. Bai bude ba tukunna ya sata a gaba suka shiga cikin gidan juwa na hajijiya da ita tana dafa bango yayi azamar riko hannunta barin jikin shi. 

Mami na zaune a falo tana waya, shigowarsu haka yasa ta katse wayar, itama tambayar da ta yi shine “Lafiya? Ina Imam din?” 

Dukkansu babu wanda ya bata amsa. Daddy ya zauna kusa da Mamin, ya ciro medicated dinsa cikin brief case dinshi ya sanya, ko kadan zuciyarshi bata kawo mishi wani abu makamancin wannan ba, sannan ya soma warware dukunkunanniyar takardar ya soma karantawa. 

Mami sai gani ta yi Daddy ya sulale kasa, kamin ta yunkura ta mike ya sume. Da gudu ita da Safah suka isa gareshi. 

Safah hannuwa ta daga ta dora aka tana ihun a zo a taimake su. Da gudu Hajiya Maama da ma’aikatan gidan dake kusa suka shigo, kowa kokarin shafa masa ruwa yake har aka samu ya farfado. 

Ya shiga bin kowa da kallo a hankali, kamin ya dire idanunshi a kanta, tana gefe sai kuka da makyarkyata take yi, kamar wadda aka sanya cikin sanyin kankara. 

Ya maido idon shi ga Mami wadda kansa ke bisa cinyarta, sannan ya maida idon shi ga mahaifiyarshi wadda ke ta faman yi mishi firfita da mayafinta. 

Tana cewa, “Ni Salamatu me ya faru ne Aliko?” 

Duk sauran ma’aikatan suka fita, ya rage sai su hudu. 

Ya mike da kyar ya zauna, ya dauki takarda ya bawa Mami ya ce ta karanta kowa ya ji. 

Mami ta bude takarda ta karanto. 

Itama sai ta fashe da kuka. 

Ta ce, “Haka kika zaba ko Safah? Haka kike so kuma ya yi miki. Ai shi kenan ki je ga duniyar nan ta ishi kowa riga da wando…..” 

Hajiya Maama ta katseta, “A’a, Zainabu yi hakuri kada ki yi mata baki, ku yi hakuri gaba daya ayi tunanin hanyar gyara, dukkan su kuruciya ke diban su. 

Shima Imam mene ne na saurin saki, ko me za ta yi masa ai yarinya ce….” Mami cikin kuka ta ce, “wane gyara za’ayi cikin saki ukku? ‘Yar shekaru 19-20 ce yarinya? Allah kadai ya san irin rashin mutuncin da ta _ yi masa…amma ni na san Imam Saral…..haka kawai ko giyar wake ya sha ba zai yi wannan aika-aikar ba. 

Ga gidan nan ki zo ki zauna, mu jera kafada ni da ke….idan na yiwa mijina kwalliya ki bini da ido….wannan ce dai rayuwar da kika zaba ko? To zauna mu yi ta. Allah Ya baki sa’a’”’. 

Shi kuwa Daddy tunda ya farfado neman Imam yake yi a waya, amma 

gaba daya layukan shi a rufe suke. Alamar yana cikin jirgi. 

Tana rabe a bayan kujera sai kuka take, Daddy ya mike ya wuce ta gabanta ba tare da ya dubi inda take ba, bai ce mata komai ba, ya bi matattakala zuwa dakin sa. Mami ta mike ta bi bayansa tana ta sharbe hawaye da majina da gefen mayafinta. 

Hajiya Maama ta zuba mata dundu da iya karfinta ganin yadda take kikkifta ido na rashin madafa, tace, “Yar banza, mai munafukan idanu, kukan me kuma za ki yiwa mutane tunda burinki ya cika? To Zahraddeen din mijin ‘yar’uwarki za ki aura ko Ubanki? Bace min da gani tun ban yi miki Allah Ya isa ba….” Ta fada tana nuna mata hanya. 

Sum-sum-sum Safah ta wuce ta nufi dakinta, ta kwanta a lallausar gadonta, amma yau sai ta ji kamar ta kwanta a kan kaya. 

Wata irin nadama ta sauka a zuciyarta a sannu, filla-filla take tariyo majigin 

rayuwarta tun haihuwarta, da kaunar da Almustapha ya wwanzar da rayuwarshi a nuna mata. 

Shin mene ne ya shiga kanta ne da ya makantar da idanunta ga soyayyar dan’uwanta? Me Almustapha ya yi mata? Mene ne aibunsa? Me take nema a da namiji da babu a Imam? Zuciya ta gama zaluntar ta, ta kaita ta baro, da ta yi mata hudubar banza ta yi mata silar kubucewar mai kaunar ta da gaskiya, kaunar da ta tabbatar har duniya ta nade, ba za ta samu makwafinta ba, indai daga da namiji ne ba daga iyayenta ba. 

Me yasa ta fi baiwa soyayyah muhimmanci fiye da kauna? LOBE is not the only thing we are to go for in marriage…… There are other important aspects; sacrifice and debotion. (Abin nufi anan, bamu zo duniya don muyi auren soyayya kadai ba. Akwai wasu abubuwa da yawa da suka fita muhimmanci cikin aure, kauna_ da sadaukarwa)…… 

Ta yi tumus cikin nadamar da ALAMEEN BELLO MAKARFI ya kira NADAMA MARA AMFANI. (Duba SIRADIN RAYUWA, littafin Takori na farko, tare suka fito, an sake buga shi a karo na biyu ga wadanda basu karanta ba) 

Ga shi ta bata goma daya bata gyaru ba. Ta yi asarar mijin kwarai irin ALMUSTAPHA ZUBAIR DAN-KASA. Bata ga tsuntsu bata ga tarko. 

Ta bata da iyayenta da Kakarta da ke tattalin ta da so da kauna, amma ‘yar kankanuwar biyayya ta kasa yi musu a rayuwa sabida soyayya. Wace rana haihuwarta tayi wa iyayenta, tunda basu isa su zaba mata abinda suke ganin shine alkhairi a gareta ba. Ta sanya su cikin baki-ciki da takaicin da watakila har su mutu, bazasu yafe mata ba. Idan ba Imam ne ya dawo garesu ba. 

Mene ne makomar rayuwarta a halin yanzu? Wa za ta aura? Ko zama za ta yi ta yi a gida gaban iyayenta tana sa 

musu ido kamar yadda Mami ke cewa? 

Rashin sanin hakikanin wadannan amsoshin ya sanya ta rushewa da kuka mai cin rai, kuma mai cakude da NADAMA MARA AMFANI…. 

ok 2K KK 

Cc 

ikin kwanakin da suka biyo baya, rayuwa ta yi zafi ga Safah, wata irin rayuwa take agidan Ubanta tamkar ta wadda aka saki uwarta aka bawa kishiyar uwa mara mutunci rikonta. Mami ta daina kula ta, ta daina shiga sabgarta. 

Ba’ a maganar Daddy, wanda ko inda take ba ya kallo, da ya kalleta gara ya ga bakin kumurci, da yana da karfin zuciyarma da korarta zaiyi daga gidansa taje ma duk inda zata, amma zuciyar iyaye data muslunci ta rinjayi komi. 

Har zuwa yau din kuma bai taba ce mata komai akan al’amarin ba, hankalinsa ya tafi ga binciken inda Imam 

ya shiga a fadin duniyar nan, domin an tabbatar masa bai bi jirgin da yayi booking ba zuwa Glassgow, wani daban ya hau, wanda ba’a tantance na ko’ina ne ba a nahiyar Birtaniya, har assistant dinsa Mr. Kalakari mutumin India na waya yana tambayar Daddyn dalilin rashin isowarsa a washegarin ranar daya je daukoshi a filin jirgi.. Duk wannan tarairayar da Daddy yake yi mata ada ya daina, ido kawai yake binta da shi idan ta zube agabanshi wai tana gaisheshi. 

Wajen Hajiya Maama kadai take samun sanyi wani lokacin, duk da kullum itama ta tuno Imam sai ta zage ta. Ta kukkunduma mata ashariya, ta kai mata hauri ta kai mata duka da mangara, sai kuma ta koma kuka tace “annamimiya, wallahi kin yi asara, kuma sai kin nemo min Almustapha”. Tayi ta kuka. 

Duk kokarin Daddy na neman layukan Imam ya kasa samun shi, don 

haka ya soma shirin tafiya Glasgow ya gani da idonsa da gaske Imam bai koma bakin aikinsa ba, don watakila sun hada baki ne da Mr. Kalakari ya bugo ya nemeshin don Daddyn ya debe tsammanin kasancewarsa a can, in ba haka ba ina Kalakarin ya samu Jambar wayarsa? Shirinsa yake ba tare da ya gayawa kowa ba. Saidai kuma ya samu tsaikon tafiyar sakamakon tsohon pasport dinsa da ya nema ya rasa cikin takardunsa. 

Mami na zaune a gefen gadonta tana sauraron muryar Ahmad Sulayman cikin Suratul-Tagabun daga cikin wayarta, ta idar da sallar la’asar kenan, a lokacin ma tunanin Imam take, da halin da yake ciki. Jikinta na bata amatsayinta na UWA, Imam baya cikin kwanciyar hankali, yana cikin wani hali da yake bukatar mai kaunarsa akusa dashi ya rage masa maraicin da baiyi a kuruciyarsa ba sai a girmansa, tasa gefen hijabinta tana 

tsane kwallar idonta, ta yi sallama dakinta ta amsa ciki-ciki. Tunda amsa sallama ya zama wajibi ga musulmi, da bazata amsa ba. 

Ta samu gefen kafafunta ta zauna, ta dora kanta a cinyoyin Mamin tana rero kuka a hankali. Mamin bata katseta ba bata rarrasheta ba saida tayi iyakacin wanda take ganin zata 1ya ta samu Sassaucin zuciyarta sannan cikin rishin kuka ta ce, 

“Don Allah Mami ku yi hakuri ku yafe min, na yi nadama na gane na yi kuskure wanda bazan iya repenting ba, wallahi sharrin zuciya da sharrin shaidan ne. 

Ban taba zaton ‘yar maganar da na gaya mishi zai sa shi furta saki ba. Ko kadan ban kawo haka ba, sakin ma har guda uku? Mami idan kowa ya juya min baya na jure, ba zan iya jure naki fushin ba, domin dafi ne mai barazana ga rayuwata”. Ta ci gaba da kuka. Mami ba ta katse ta ba sai da ta yi mai isar ta. Abinki da da da mahaifi, a han

kali ta ji zuciyarta na yin sanyi. Abinda take so ta ji, bazai yiwu ba idan bata saurareta ba. 

Daga can karkashin zuciyarta ta ce, “Ni me kika yi min Safah? Amma saboda Allah ki gaya min abin da kika yiwa Imam har ta kai ga saki? Saki ukku?? Wanda bazai gyaru ba, wanda Allah baya so???” 

Ba ta iya karya ba, ta gaya mata dalladalla. Mami ta yi shiru tana nazari, ta ce, “Ai shi kenan, tunda hakan kike sO…….” Sai hawaye sharrr! Data yi tunanin watakila sakamakon hakan Imam zuciyarshi ta buga ya mutu ne, ko ya haukace. 

Hankalin Safah ya kara tashi, yau ga mahaifiyarta na kuka saboda bakin cikin ta. Ta ci gaba da rokon Mami ta yi hakuri, amma Mami kuka take haikan tun daga karkashin zuciyarta. Sai da ta share hawayenta da tafukanta ta ce. 

“Haka Allah Ya so, na kuma yarda da kaddara, idan Allah Ya rubuta ke ba 

matar Imam ba ce a duniya yaya zan yi? Halin da yake ciki, a ina yake? Shine abinda ke damuna. 

Ki tattara ki koma makaranta, don in ina ganin ki cikin gidan nan ba zan rabu da bakin ciki ba. Wanda zai iya zamowa barazana ga lafiya ta’. 

Cikin kuka ta ce, 

“Mami baki yafe min ba kenan?” “A’a, na yafe miki, Allah Ya yafe mana baki daya. Ki je ki nemi afuwar Daddy shi kika batawa ba ni ba. Cikin sha’aninki yanzu kam ni ‘yar kallo ce”. 

Jikinta babu kwari ta taso ta fito daga dakin Mamin ta nufi sama sassan Daddy. 

Kishingide yake da jaridar New Nigeria da medicated glass dinshi yana dubawa, ta yi sallama ya amsa ba tare da ya dubi hanyar da ta bullo ba. 

Ta isa gabanshi ta kwantar da kai a kan kafafun shi tana kuka tana rokon shi da kalaman da ta roko Mami. 

Shiru ya yi mata kamar ba da shi take 

ba. Da ya gaji da kukan ta ya ce, “Me kike so in ce miki Safah? Kin nuna min ban isa dake ba, na yi hukunci kin tozarta ni, na ce ga abinda nake so sabida kyautatuwar rayuwarku gabadaya ko bayan raina kin ce bakya so. To ya bi umarnin ki ya rabu dake ba sai ki yi abin da kika ga dama ba?” 

Ta ce, “Don Allah Daddy ka yi hakuri, na yarda na yi kuskure na yi nadama”. Ya yi murmushi ya ce, “Nadama ko? Tukunna ma. Yanzu me kika yankewa rayuwar ki?” 

Ta ce, “Makaranta zan koma gobe in Allah Ya kaimu”’. 

Ya sa ido yana kallon ta ya ce, “Aure kuma fa?” 

Ta sunkuyar da kai ta ce, “Zan yi Daddy in Allah Ya kawo myin”. Ya 

kyabe baki. Ya ce, “Tashi ki je ki yi shirin tafiyar’. 

Ya janyo brief case ya rubuta mata chekue din kudi masu yawa, ta karba ta yi godiya ta fito. 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *