BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 4 by sumayyah Abdulkadir
Daddy WATARANA na zuwa da zuciyoyinmu zasu hadu, cikin yardar wanda ya nufe mu da zama karkashin inuwar aure, bada jimawa ba. Insha Allahu!!!.”
“Ban janye ba, ba kuma zan janye ba”. Ya fadi a hankali. Hawayen da suka cika idon Zahradddeen suka gangaro, ya ce, “Na yi wannan alkawarin Daddy…”
Ya sake yin tari ya ce, “Sai alfarma ta biyu, kuma ta karshe.”
Gaban Zahraddeen in banda faduwa ba abinda yake, cike da tsoron wadannan alkawarirrika masu nauyi da Alh. Aliko ke sa shi yana yi. Ya ce, “Wace irin alfarma ce kuma Daddy?’
Ya ce, “Abin da baka so ne, nake son ka yi min. Ka yi min alfarmar kulawa iyalina da dukiyata bayan raina, ina nufin ‘Dan Kasa Holdings, Dan Kasa Inbestment, Dan Kasa Electronics, Dan Kasa…….. duk suna cikin AMANAR KA”
Ya kasa karasawa saboda yadda tari da shakuwa suka taru suka sarke shi. Gaba daya falon kuka suke, in ka cire Hajia, kada Zahraddeen ya ji labari. Babu shakka kukan da Zahraddeen ke yi a yau bai taba yin irinsa a rayuwarsa ba.
Cikin karkarwar murya Hajiya Maama ta ce, “Aliko ka daina fidda rai da rayuwa saboda ciYa dubi mahaifiyarshi yana murmushi, sannan ya ci gaba da tari, da ya lafa ya ce,
“Ban fidda rai da rayuwa ba Hajiya, (mutanen kirki Allah kan nuna musu karshen rayuwarsu. Takori ) na yarda rayuwa da mutuwa duk na Al
lah ne.
Wai hasashe nake, ko da ta Allah za ta kasance a gare ni. Na yafewa Safah da Marwah, ku gaya musu na yafe musu duniya da lahira.
Duk ranar da Allah ya juyo da Almustapha gida, ku roka min shi alfarmar ya yafewa Safah ko ma me tayi mishi, koda Allah bai kaddari aure a tsakaninsu ba, domin hakika ta yi nadama, ku gaya mishi na so in yi tattaki har can Glasgow in isar mishi da wannan sakon Allah Bai bani iko ba.
Hajiya ki yafe ni idan na taba yi miki ba dai-dai ba…”
Ta taso ta kama hannunshi, a lokacinne hawaye suka zubo a idonta.
Ta ce, “Na yafe ka Aliyu, na yafe maka. Na yafe maka…..Kai dan albarka ne, daidai da rana daya baka taba bata min ba, ban taba aje kara ka tsallake ba.
Allah Ya yi maka albarka, kuma Allah Ya baka lafiya….”
Mami ta kunshe fuska cikin mayafi sai kuka take. Don dai ita bata ga dalilin wadannan maganganun masu kama da wasiyya ba, ciwo ai ba mutuwa bane. Daddy ya juya gare ta zai yi magana shakuwar ta kara sarke shi.
Da kyar ya samu ya ce, “To mene ne abun kukan? Ke ma ki yafe ni Zainabu, tunda na yiwa ‘yarki aure ba tare da son ranki ba. Ki yarda dani gata na yi mata. Ba kowadanne mutane ne irin Zahraddeen ba!
Ba kowadanne mutane ne ke da irin nagartarshi
ba, ba kowadanne mutane ne a wannan zamanin ke da irin kyakkyawar zuciyarshi da Amanar shi ba…”
Shakuwar ta kara sarke shi. Da sauri Mami ke kiran wayar Dr. Mathew, Hajiya Mama ta mike ta fita don ta samu ruwa ta yi mishi tawaida.
Ko kafin ta dawo shakuwar ta ci karfinsa, har gudu ake tsakanin Mami, Zahraddeen da Shahida don a kawowa Daddy ruwa, ko kamin su dawo
rai bakon duniya ya yi halinsa. KK
Babu wanda bai zo da ruwan ba a cikin su, kuma daidai da isowar Dr. Mathew. Mami ta isa gare shi ta tallafo shi don ta ba shi ruwan ba tare da ta fahimci abin da ya faru ba.
Dr. Mathew ya karbi ruwan daga hannunta ya sa hannu ya rufe mishi kwayar idanunsa. Ya kwantar dashi a kasa. A lokacin ne duk suka gane abinda ya faru.
Ganin Dr. Mathew ya ja zanin gado ya rufe shi, “TInnalillahi wa’inna ilaihi raji’un!…” Abinda Zabraddeen ke fada kenan yana kuka riris a kasa kamar karamin yaro.
Yayin da Dr. Mathew ke basu hakuri amma dukkansu kuka suke ba ji ba gani.
“Allah Ka ji kan MAZAN JIYA…..” Abinda Shahida ke fadi kenan a zuciyarta. Tana sharbe
nata hawayen da habar zaninta. 2K OK ok
Daruruwan jama’a ne suka halarci jana’izar
tsohon Gwamnan, wadanda suka hada da ‘yan siyasa, ‘yan boko, talakawa da al’ummar garin Kaduna baki dayan ta.
Sai dai wanda bai samu jin sanarwa a kafafen yada labarai ba, kamar Safah da Marwah, wadanda basa sauraron rediyo ko talabijin.
Ita Marwah wayar ta babu caji, domin kwanansu biyu kenan basu da wutar NEPA, ga shi masu gidan (su Inna kenan) babu wanda ya damu da wata wutar NEPA, duk sun kunna fitilar kwai duk da cewa akwai inji cike taf da petir a gidan.
Ita kadai cikin duhu don bakar zuciya ta fi karfin ta ce da Nura ya tayar mata injin ko Rabi’a ta sayo mata kyandir.
Haka nan take kwance cikin bargo a lallausar gadonta da yake tana hutun sallah, haka nan take fama da faduwar gaba akai-akai, da rashin jin dadin zuciyarta. Tana tuna irin abubuwanda take yi a cikin gidannan wanda ba halinta bane ba, bana iyayenta ba, ba wani ya koya mata ba, shaidan ke ta koya mata launi-launi da nau’inau’I na rashin mutunci don a koreta. Amma bayin Allahnnan kamar basu san tana yi ba. Shin idan Mami ake yiwa abinda take yiwa uwar Zahraddeeen da kannensa yaya zata ji a zuciyarta?
Ko Rabi’a tayi fushi ta daina dosar flat din, idan taji ta kunna kira’a sai ta shigo ta zauna koda bazata kulata ba, sabida itadai bata da waya bata da radiyo kuma tanason kira’ar Khusairi da Marwahn ke sawa. Kasancewar da kira’ar warshu yake yi ba hafsu ba.
Malamansu na islamiyyah sun sha gaya musu kira’ar warshu itace kira’ar ‘yan aljannah. Rabi’ah hafiza ce tanada haddar hizfi arba’in akanta. Don haka duk inda ma’abocin sauraron Alkur’ani yake, Rabi’a abin so da girmamawa ne agareta.
Sai tace a ranta ita wannan dai rashin arzikin (rashin mutuncin) a fatar bakinta yake, ba’a zuciyar ta ba. Gata da sallah, goshinta ya nuna, kafafunta sun nuna, kuma kusan kullum ta shigo sallah take ko girki mai shegen kamshi irinna turawa. Wani abin dariya ma in Rabi’an na zaune ko bata kulata ba in tagama dafe-dafenta da gashe-gashenta sai ta zubo ta ajiye mata ta shige daki.
Wani lokacin ta ci kadan, in bakinta ya ki karba ta bar mata abinta. Idan nama ne sai ta nikashi, har bakin Rabi’a ya kasa tantance ko menene. Don haka ita wannan_ cakude-cakuden da ganyayyakin kayan lambu dana gongoni da Marwan ke ci ta aje mata agabanta bata iya cinsu, sai ta dauka ta mayar mata cikin firjinta.
Idan kuma taga dama sai tasa wakar India, nan ma Rabi’a na so. To haka a can dakin daliban Medicine na asibitin koyarwa na jami’ar Ahmadu Bello, Safah Dan Kasa ke kwance da tulin takardu da litattafai a gabanta, amma ta kasa kammala thesis din da aka bata.
Wata irin kasala ce ta sauka a zuciyarta, sannan gabanta ya yanke ya fadi, ta kai hannu ta dafe kirjinta, hankalinta ta ji ya yo gida. A lokacin karfe hudu na yamma.
Ta aje biro ta mike a sanyaye, ta juya ta dubi Jamila wadda ke ta sharar barci a gadonta. Ta bar mata dan ‘note’ a saitin kanta inda take sanar da ita ta tafi Kaduna.
Gudu kawai take shararawa a kan titin da zai sada ta da garin Kaduna daga Zaria. Allah ne kawai ya kawo ta lafiya amma ba nutsuwar tuki ba. Cincirindon mutane ta gani fal a layin su, wanda ya tabbatar mata lallai wani abu ya faru. Ga canopies (rumfuna) an saka, tun daga farkon layin har zuwa karshen sa.
Ko gurin da za ta yi parking babu, haka ta aje motar a farkon layin ta karaso da kafafunta. Domin daga baya da Daddy ya huce ya maida mata motar.
Cikar al’ummar dake cikin gidansu ya sanya ba za ta iya gane ko su wane ne ba, haka ta rika cira kafa idanunta a rufe ba tare da ta damu da kallon da jama’a ke binta da shi ba, ko inda take cilla kafartata.
A babban falonsu ta cimma Shahida ta ci kuka har ta gode Allah, Mami da Hajiya Maama na daga cikin daki cikin jama’a.
Ta kukkutsa ta shiga, ta fada jikin kakarta ta fara kukan itama, tana tambayar abinda ya faru. Hajiya Maama ta ce,
“Ki yi hakuri Safah, Allah da Ya bamu Alhaji ya Karbe shi…..”
Iyakar abin da ta ji kenan sai farfadowa ta yi ta ganta kwance a cinyar Mami tana kuka itama.
Gudu sosai Zahraddeen ke yi a kan hanyar
Zaria, domin ya dauko Marwah, ta_halarci makokin mahaifinta.
Zai iya kwatanta mutuwar Alh. Aliko da mutuwar mahaifinsa a zuciyarsa. Har zuwa wannan lokacin hawayensa basu bar ambaliya ba.
Karfe hudu na yamma a Zaria ta yi mishi, yadda ya shigowa Inna ta tabbatar ba lafiya ba, ba ta taba ganin Zahraddeen yana kuka ba tun tasowar shi.
Ta ambaci “Innalillahi…!” A zuciyarta.
Shi kuma ya zauna a gefenta yana zubar da hawaye. Inna ta soma nasiha tum ma bata ji makasudi ba, tana cewa,
“Duk abinda ya faru ga bawa mukaddari ne daga Allah, kuma Allah yana sane da shi, sai ake so bawa ya karbi wannan kaddara da hannu bibbiyu. Ya godewa ni’imomin Ubangiji a gare shi, amma ba ya yi ta kuka ba”.
Zahraddeen ya daga jajayen idanunshi yana kallon Inna, nitsatstsiyar dattijiya mai kyautatawa ‘ya’yanta, tare da yin duk wani kokari don ta faranta musu, a cikin halin bakin ciki ko tashin hankali.
Ya ce,
“Dole in yi kuka Inna, domin ya cike min wani gurbi a rayuwata na Uba-mahaifi. Yayi min kaunar da bayan iayayena babu wanda yayi mini. A yau Allah Ya karbi ransa, a kan idona. Dole in kokawa gushewarsa a doron kasa.
Sannan ya hadani da wani al’amari mai nauyi; kula da dukiyar marayunsa. Ga shi ina auren ‘yarsa, ba don haka ba da ba zan damu ba.
A daidai lokacin da nake kokarin janye jikina daga cikin dukiyarsa, sai ya daura mini nauyin ta gaba daya (dungurungum). Inna yaya zan yi? Nauyin mai girma ne! Tunanina da karfin Zuciyata sun kasa dauka”’.
Inna tasa bakin zaninta ta share hawayenta, domin ta fahimci abinda Zahraddeen ke koka mawa.
Ta ce, “Bari in shirya mu tafi, jeka taho da ita ta samu makokin mahaifinta. Tunda har ka yi alkawari, to ka daure ka cika, ka yi komai da zuciya daya, ka daina la’akari da abin da mutane za su ce a kanka, domin shi dan Adam ba a iya mishi. Amma idan sun ce a raba gado shi kenan, sai ka kula da na ‘ya’ yanshi kadai. Idan kuma su ma sun fi son dukiyarsu a hannunsu, babu alkawarin da zai ce dole sai ka rike, tunda hakkinsu ne ba naka ba”.
Ranshi ya dan samu nutsuwa daga kalaman Inna. Ya mike ya nufi sashensa yasa mukulli ya bude kofar glass wadda za ta sada shi da falon, yasa kai dauke da sallama a bakinsa.
A nan falon ya ganta a kwance a doguwar kujerar hutawa (sofa) tana barci sadidan, lokaci na farko kenan da ya samu damar kare mata kallo, sanye take da riga da wando na Pakistan ruwan ganye, kanta babu kallabi, ta daure gashinta da koren ribbon mai girma.
Fara ce sol doguwa, don ta fi Safah tsayi kadan, ga dogon hanci da karamin baki. Ba ta da yawan sumar kai kamar Safah, sai dai ba ta a layin marasa gashi.
Hasken fatarta ‘natural’ babu alamun shafe-shafe. Ya ji wani tausayin ta ya tsirga masa, sannan wani sabon al’amari ya soma samun muhalli daga can karkashin zuciyarshi.
Maimakon ya tashe ta sai ya samu kanshi da zama a gaban kujerar da ta ke kwance, ya dade yana kallon ta yana jin wani irin sanyi a zuciyarsa, domin akalla ko babu Alh. Aliko, a yau ya yi farin ciki da karbar auren diyarshi. Ji yayi kamar ya sunkuya ya sumbaci siririyar fatar bakin ta. Yana kuma tattara kalaman da zai gaya mata ta shirya su tafi Kaduna yanzunnan batareda hankalinta ya tashi ba. Tunda jiya ya tafi, kuma aka’ ida in ya tafi sai karshen sati yake dawowa. Domin ko ba komai yana tare da jininshi da za ta dinga tuna masa da shi yana yi masa addu’a.
wadda kila watarana …. zata haifa masa jikan Aliko, …… yasa masa suna Aliko. Ya dora shi a kujerar ofishin Aliko…….. ya gaya masa ko
wanene Aliko.
Ko yaushe ce wannan ranar? Ya tambayi kansa. “Allah Shi Yafi kowa sani”. Ya baiwa kansa amsa.
Ya yi ta maza inji mata ya kama tafin hannunta. Ta yi saurin bude idanunta ta ga Zahraddeen ne yau zaune a gabanta, har da kama hannun ta, mutumin da ko kyakkyawan kallo bai taba yi mata ba.
Ta riga ta fassara shi da mutum ‘mai girman kai’, (dama an ce gwano baya jin warin jikinsa. Takori
)
Rana ta farko tun zuwan ta gidan da ya yi mata
murmushi. Ya ce, “Sorry, kina barci na tashe ki. Ki tashi mu wuce Kaduna yanzu”.
Kallon rashin fahimta ta yi mishi. Bai bari sun sake hada ido ba ya wuce dakinsa, tana so ta tambaye shi ba’asi ko da cikin tsiwa ne babu fuska. Ta mike ta yi dakinta don ta canza kaya tana cewa a ranta, “Allah Yasa gajiya yai da auren ta zai mayarwa da iyayenta ita”.
Tana gidan gaba na motar Inna na baya, tunda suka dauko hanyar Kaduna bayan gaida Inna da ta yi, ba ta ce uffan ba.
Ta lura daga shi har Inna basu da walwala, don basa cewa komai. Ita Inna carbin hannunta take ta ja, shi kuma gaba daya ya tattara hankalinsa a kan tukin da yake yi.
Faduwar gabanta ya kara tsananta, ta samu kanta da satar kallon sa lokaci-lokaci, ko zata iya karanto dalilin tafiyar ta babu-gaira babu dalili, kallon da a da ba ta taba yi masa ba.
Gayen ya hadu karshe, ga iya shiga ta ‘suit’, da shaddah, kai har ‘white cotton laces’ ma da ‘white materials’ na maza masu taushi da santsi yana yin amfani dasu dinki Mohammed, idaniya basa gajiyawa da kallonshi har ga maza ‘yan uwansa ba mata kadai ba, ga yawan sumar jiki data kai, ga wani kwantaccen saje da ya aje a gefen fuskarshi wanda ya hade ya zagaye da gashin bakin kuater million din sa. Baida hasken fata sai hasken boko, dangayen gaske, mai kwarjini na ban mamaki.
Sai dai ba ta taba ganin shi cikin rashin walwala da rashin kuzari irin wannan ba. Idanunshi a
rikide sun koma brown daga farare sol. Ta ji wani sabon al’amari yana fizgar zuciyar ta, tsigar jikinta na tashi.
Ta cigaba da satar kallonsa yana sauya kaset daga wakar larabawa zuwa addu’ar tahajjud din Sudaith. Ji take kamar ta dora kanta a kafadun miyin ta, ta ji dalilin damuwar da yake ciki, ta kuma rokeshi gafarar babban gorancinta na shirme da rashin hankali irinna yaran goye, inda hali ta rungumeshi, ta shaki wannan ‘dior’ din mai kokarin janye numfashin ta a kullum mai shi ya doso ta.
“Ya ilahi!” ta furta a hankali, tareda kai hannu ta dafe kirjin ta, sabida karfin bugunsa daya karu. Me ke damu na ne akan Zahraddeen a yau? Juyowar nan da za ta yi sai idanunsu cikin na juna, ya yi maza ya daure fuska, ita kuma duk kunya ta kama ta, tunda ya kamata tana mishi kallon kurillah kamar bata taba ganin shi ba, kallon da baya jin ko Safah da yace yana so itama tana so ta taba yi mishi sabida batada ketare kallon muslunci, amma Sai ta yi saurin dauke kanta ta mayar tagar damanta, kirjinta ya cigaba da bugawa fat-fat-fat, cunkushe da al’amura masu dimbin yawa.
Ko da suka isa bakin layinsu ta hango cincirindon mutane a kofar gidansu ba karamin kaduwa hantar cikinta ta yi ba.
Ta dubi Zahraddeen da sauri nan ta ga idanunshi sun cicciko da kwallah, yana dubanta kamar ya riketa ya hanata fitar, kamar ya riketa ya lallasheta, in zai ya ya gaya mata da bakinsa, zata fi fahimta fiye da ta ji al’amarin daga tsakar ka, a
sukwane ta bude murfin motar ta fita da gudu ta doshi gate din gidansu ba tareda ta bi ta kansa ba. Ba abin da ta kawo cikin ranta sai Hajiya Mama ce Allah Ya yiwa rasuwa.
Sai dai kuma da Hajiya Maaman ta fara cin karo, a lokacin da ta sanyo kai babban falon Mami, saura kadan su kara.
Ai Safah na ganinta ta taho da gudu ta rungume ta, ta saki wani irin kuka mai gigitarwa. Cikin kukan da karkarwar jiki ta ce,
“Mun zama marayu Marwahh, yau babu Daddy….ya tafi….ya tafi….ba zai kara dawowa ba!!!” Sai ita ma ta rushe da kukan da bata taba yi a rayuwarta ba.
Nan komai ya dawowa kowa na gidan sabo, sun tabbatar maraici ya same su, mai daci da wuyar mantawa.
Daddy Uba ne da babu kamar sa, an edemplary Dad!. Ya tsaya tsayin-daka wajen inganta rayuwarsu ta kowacce hanya.
Don haka mance ciwon rashinsa a zuciyoyinsu ko
barin kewarsa wani abu ne da ba zasu taba iyawa ba.
FRR KK
D uk wani wanda yake da alaka dasu ya zo musu ta’aziyya, kama daga ‘yan’uwansu na Yola, malamai da abokan karatun su. Ranar sadakar bakwai anyi addu’o’i na musamman, anyi sadaka kowa ya kama gabansa, sai
wadanda abin ya shafa.
Idan ka ga Safah da Marwah a wannan lokacin gaba daya sunyi sanyi, kamar idan ka sanya musu dan yatsa a baka ba za su ciza ba.
A ranar da daddare Baffan Alh. Aliko wato Baffa Sufyan da Hajiya Mama wuni suka yi neman layin Imam, amma basu samu ba.
Mami ta yi kuka har ta gode Allah saboda rashin samun Imam a yau, Baffa Sufyan ya kira su family meeting wanda ya bukaci Zahraddeen ma ya halarta tunda shima yanzu ya zama ahalin gidan kuma babban Yaya a gare su tunda ba imam. Maganar gado ce ake yi, kowa ya fadi ra’ayinsa na yadda yake son rabon gadon ya kasance.
Baffa ya yi shiru yana sauraron kowa. Safah da Marwah sun ce basa bukatar komai na gadon mahaifinsu sun barwa Mami.
Hajiya Maama kuma ta ce ta barwa Imam da Shahida kason ta. Mami ta ce “Ayi haka Hajiya? Su ma suna da gado, wanda har yau ba a taba komi a cikinsa ba, wanda ya bunkasa ya hayayyyafa a bankunan Turai sabida dadewar da aka yi ba’a taba shi ba.”.
Ta ce, “To ni me zan yi da kudi? Gida ko mota Zainabu? Shekaru nawa suka rage min IN BI BAYAN Zubairu da Aliko a duniyar bayan shekaru tamanin?”
Sai da suka gama Baffa Sufyan ya yi murmushi ya ce, “ duk na ji ra’ayoyin ku. Shi gado wani muhimmin abu ne wanda Ubangiji Subhanah da kanSa Ya raba shi a cikin Alkur’ani saboda muhimmancinsa.
Don haka dole za a raba a baiwa kowa kason shi, in yaso sai kowa ya yi yadda yake so da shi, imma za ku bari Zahraddeen ya ci gaba da juya muku kamar yadda marigayi ya ce ko za ku siyar ku sayi hannun jari, ko kuyi gararin gabanku. Don haka za mu raba gado kowa ya yi yadda yake so da nasa”.
Dukkansu sun gamsu da bayanin Baffan, don haka a washegari aka raba gadon kamar yadda musulunci ya tsara.
Hajiya Maama ta zabi yin sadakatul jariya da nata, wato gina masallaci, kai tallafi ga gidan marayu da nakasassu, tare da gina makarantar Islamiyyah.
To haka Mami ta zabi yin sadaka da sayen hannun jari, yayin da a take Safah da Marwah, suka bi umarnin mahaifinsu suka damkawa Zahraddeen nasu takardun a kan sun amince ya ci gaba da juya musu, sun amince ya cigaba da daukar albashinsa da Daddy ke bashi a ciki, sun amince ya zama Yayansu na jinni har zuwa ranar da Allah zai juyo da hankalin Imam gida.
Karfe hudu na yamma Zahraddeen ya shigo cikin gidan, lokacin Safah da Marwa na daki suna kara kokawa junansu.
Safah na bata labarin yadda Imam ya sake ta, wanda ta san har da bakin cikin wannan al’amari ya yi sanadiyyar ajalin Daddy da halin da take ciki a yanzun na nadama da dana sani, uwa-uba soyayya mara algus da ta kanannade zuciyarta a lokacin da Imam din ya tafi ya bar ta, koko tace, damar ta riga ta kubuce mata bakin alkalami ya
riga ya bushe. Tunda ko yana nan din me zai kuma shiga tsakanin su? Sai ido. Sai gaisuwa ta muslunci in ya kai zuciya nesa.
Ta yiwa ‘yar’ uwarta nasiha sosai ta ce ta godewa Allah ta kuma godewa Daddy ta kama mijin da Allah Ya bata tun ba ta zo tana irin nadamar da take yi a yanzu ba.
Ta taushe ta da cewa, duniya ba komai ba ce tamkar matafiyi ne a kan tafarki. Daddy kadai ya isheki misali. Ko ince Ubangiji Ya dauke abinSa ne, don mu hankaltu. Mu gane gatan da yake cewa yayi mana mun ki yarda da gangan sabida kuruciya da son zuciya. Ta ce ki duba ki ga mene ne Allah Bai baiwa Daddy a duniya ba? Wace irin shahara ce Daddy bai yi a Nigeria ba? A yau yana ina? Ya tafi ya barsu a inda ya same su, ya tafi inda abinda ka shuka shine kadai jarinka.
Bai tafi da gidajen ba bai tafi da motocin ba. Bai tafi Birtaniya ba bai tafi Bournmouth ba; karkashin kasa ya tafi cikin yadin likkafani daidai dana kowa, babu AC babu katifa. Sauran al’amarin tsakanin sa da UbangijinSa ne, to haka kowa fah…..!!!
Kina kin Zahraddeen ne kawai based on hierarchy of social class, nakasunsa a wurin ki shi ba dan wani bane ba kowa bane face wani matashi mai tarin ilmi, mai neman na kansa a karkashin mahaifinki ta hanyar gajiyar ilmin sa don dai banace kwadayi kike ba, na wani wanda ya fishi abin duniyar. Amma ba don yayi lacking anything a rayuwa ba. Marwah me kike so a namiji, sabida Allah me kike so da Zahraddeen baya da
shi?
To bari in gaya miki gaskiya in baki gode rahmar Allah da zabin Sa ba, zaki godewa azabarsa a ranar da baki da sauran wata dama da za ki gyara kuskurenki kamar yadda nayi. Kukan kurciya jawabi ne, mai hankali kadai ke ganewa….” Marwah ta share hawayen idonta jikinta ya yi sanyi sosai. Wani irin sanyi da bai taba yi a rayuwarta ba
Mami da Shahida ya tadda a falon, ya zauna bisa kilishi suka kara yiwa juna ta’aziyya, sannan ya ce da Mami, “Ko za mu iya tafiya yanzu? Gobe litinin ina son ta koma makaranta gobe”’. Mami ta ce, “Hakan ya yi, Shahida kirawo ta su tafi”.
A yadda Shahida ta gansu face-face da hawaye ya taba zuciyarta, ‘yan kannen nata sun sanya ma ransu damuwa mai yawa. Basu taba bata tausayi ba sai yau.
To ai gara su suna da Mami da za su rika gani su ji dadi, su kuwa fa? Ta juya musu baya tana dauke nata hawayen da ‘yan yatsunta ta ce. “Marwah fito ku tafi mijinki na jiran ki”.
Da kyar ta shiga toilet ta wanke fuskarta da sabulu ta fito ta tadda su a falo cikin shirinta rataye da jakarta.
Zahraddeen ya riga ta fita, bayan ya yiwa Mami sallama ba tare da ya iya hada ido da Marwahn ba, saboda shi yanzu matsanancin tausayin su yake ji, duk wasu makaman yakin day a tanada don dai-daita sahun matar tasa, ya nemesu ya
rasa, yadda suka shaku da mahaifinsu har ya fi shakuwar su da Mami.
Mami ta daga ido ta kalle ta, idanun sun yi jawur sunyi luhu-luhu, duk da wanke sun da ta yi da sabulu.
Ta yi mata kallo na zuciya da zuciya, wato kallon kauna na da da mahaifi. Suka yi sallama ta bi bayan Zahraddeen. Mami ta kasa ce mata komai. Banda “agaida Hajiya Binta”’.
Yana cikin motar kafarshi daya a waje yana danna wayarshi ya hangota ta fito, ya mika hannu ya bude mata gaban motar ta shiga ya rufe suka dau hanya.
Tunda suka hau titi babu mai uhm, babu mai umh-umh a tsakaninsu. Da shirun ya ishe shi sai ya danna sautin Sudais cikin suratul An’am. Tafiya suke sannu-sannu, domin Zahraddeen baya gudu sosai. Ya kara karfin A.C din motar ya rufe tagogin motar wadanda suke bakake wulik (tintic), ba mai iya hango mutanen da ke ciki. Duk wasu kudurarrika na batanci da yake dasu a kanta, sai ya neme su ya rasa, sai tausayin ta da yake ji kamar-kamar me, zuciyarshi tayi laushi da yawa, yana tuna lokacin da shima ya rasa nasa mahaifin (the same feeling…).
Karo karatun ma ya fasa, zai tabbata a serbant din Alh. Aliko Dankasa muddin rayuwarshi. Zai kula da diyarshi duk da cewa ba ta son shi, ya ji ya yarda ya amince (shi yaron Babanta ne) kamar yadda take ikirari. Sai me?
Yana yin ‘parking’ cikin garejin shi ta dauki Jakarta ta fice ba tare da ta ce da shi komai ba, ta