BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 5 by sumayyah Abdulkadir
wuce cikin gidansu ainahin sassan Inna ba flat din su ba. Bata taba shiga ba, bata san hanyar ba, sakai kawai tayi.
Ya kashe motar ya fito rike da hularshi a hannu da briefcase ya doshi dakin Innarshi, ya sha mamaki ganin Marwah a dakin Inna suna yiwa juna ta’ aziyya.
Da kuzarin shi ya shigo, amma ganin Marwah yau a dakin mahaifiyarshi sai ya ja ya yi turus a bakin kofa yana kallon ta, don bai san da wacce ta zo ba.
Inna ta ce, “Ka zo ka tsaya mana kerere a ka, in shigowa za ka yi ka shigo, in fita za ka yi ka fita”. Ya saki fuska sannan ya juya ya fice ya nufi sassansu zuciyarshi ta yi mishi sanyi a karo na farko tun zuwan ta gidan. Ba mamaki mutuwar mahaifinta ta fara ladabtar da ita.
A yau sai ya samu kansa da zama a falon, don kawai yana son ya ga gilmawar ta, daga shi sai singileti da wandon shan iska (short niker) samfurin Adidas, ya jona kettle ya hado ruwan gahwa (coffee) a kofin tangaran ya zauna cikin kujera yana kurba kadan-kadan yana duba wayar hannunsa, amma a zahiri hankalinsa baya kai, yana kan kofar falon.
Da an dan jima sai ya dubi kofar shigowa ko za ta shigo, amma shiru. Shi kanshi ya kasa gane kanshi a kwanakain nan, matarshi yake ji sosai cikin zuciyarshi tun bayan rasuwar Alh. Aliko.
Can sai gata ta shigo rike da mayafinta da jakar hannunta. Ya daga shanyayyun idanunshi a hankali yana kallon ta yana kurbar coffee.
Kallo daya ta yi mishi ta kau da kai, don ji ta yi kunya ta kama ta, don bata taba ganin namiji haka ba. Amma shi din bai gane hakan ba. Ko kuma ya gane din ba damuwarshi bace.
Ta zube shirgin hannunta ta yi kicin don ta samarwa cikinta abin da zai ci, don Inna danwake ta yi mata tayi ta ce a koshe take, don ba za ta iya jefa wadannan lunkuma-lunkuman abubuwan a bakinta su wuce makogwaronta ba.
Yana nan zaune duk kamshi ya cika masa hanci, Marwah rainon Mami ce ta fuskar girki na zamani kala-kala, ba wanda ba ta iya ba.
Inda ta sha bamban da Safah kenan, ita sai karatu da son tsarge jarrabawa.
Ta debo danyen nama a firiza ta zuba a na’urar nika nama ta markade shi sannan ta juye a frying fan ta sanya albasa, maggi da tafarnuwa da curry ba tare da ta zuba ruwa ba, ta sa wuta kadan sannan ta kawo green beens kofi daya ta zuba ta rufe. A gefe ta kwaba fulawa ta yi falle-falle da ita ta hau gashin pita-bread wanda za ta ci da sauce din. Cikin Zahraddeen in banda kugi ba abinda yake, ga wani irin kamshi ya cika shi. Shiru-shiru ba ta fito ba ta barshi sai hadiyar miyau yake, dama muguwar yunwa ta sa shi shan gahwar, tun karin kumallon da yayi a Kaduna bai kara sanyama cikinsa komi ba.
Can sai gata ta fito da plate a hannunta da robar lemon Mountain Dew za ta wuce dakinta, sai ya sha gabanta.
Ta dago ido ta dube shi sai ya rausayar da kai gefe ya lumshe lumsassun idanunsa, sannan ya
budesu ahankali a kanta a lokacinda ita kuma ke ta kokawar kawas da ido daga gareshi.
“Ni baki bani ladan ganin ido ba!”’.
Harara ta zabga mishi ba tareda ta yarda ta dubeshi ba. Sannan ta ce, “Ban girka da kai ba, ko da ni nake baka abincin?”
Ya yi murmushi ya karbe ‘plate’ din hannunta, ya bata hanya ya koma kujerar tsakiyar falon hankalinsa kwance ya soma cin abinsa.
Karshen kulewa ta kulu, ta juyo ta koma kicin ta juyo sauran a wani ‘plate’ din ta zauna nan cikin kichin din tana ci, kada ya sake kwacewa wahalarta ta zama haramiyarta, sai gashi ya shigo. Daga bakin kofa ya tsaya hannun shi daya ya sanya jikin kofar kicin din, ya rike fankon filet dinshi da hannu daya……. ya mika mata plate din, fuskarsa dauke da wani kayataccen murmushi wanda ya fitar da annuri mai yawa akan fuskarsa, da sabuwar soyayyah dankare cikin kwayan idanunsa. Kamar almajiri yana bara;
“I’m asking for more….Maa!!!”
Yadda ya yi maganar cikin kwantaccen sauti, duk sai ya bata dariya, yana iya hango siririn murmushi, a siririyar fatar bakinta, amma ba ta ce da shi komi ba, har ya saki kofar ya karaso ya tsugunna a gabanta, kamin ya zauna sosai ya sanya hannu cikin ‘plate’ dinta suka ci gaba da ci tare.
Wannan girki dai, bata koshi ba ko kadan. Itama yunwar take ji dole dai ta hakura ta kyaleshi. Don bata son magana ta tsawaita a tsakaninsu don ta
lura yau dai neman shiri yake. Ta kowacce fuska alamu sun nuna. Da suka kammala hannunta ya kama ya wanke mata a cikin ‘sink’, bai cika hannun nata ba, janyo ta ya yi da hanzari suka nufi bed room dinta.
Ta ce, “To cika ni guduwa zan yi ne?’
Ya sassauta rikon da yayi mata amma bai cika ta ba. Zama ta yi a gefen gadonta ta kwace hannunta, ya jawo stool din madubi ya zauna a kai daf da ita yana fuskantar ta.
Ya ce, “Bayan rashin SO, girl,… sai mene ne matsalarki a zama dani?”
Yadda yake magana kadai ya saukar mata da kasala, balle yadda hucin sassanyan numfashinsa ke dukan fuskarta. Ta samu kanta da rikicewa ta kasa amsa mishi tambayarshi.
Ya ce, “Ke nake sauraro?”. Tareda daga girar shi sama kadan, alamar sauraron.
A hankali ta dago ta dube shi, abinda ta gani cikin kwayar idonshi ya sanyata kokonton anya Zahraddeen ne? Kwayar idanunshi ta nuna wani mutum da ke fama da azabtacciyar soyayya da kauna mai yawa, (yet he’s not weak), amma dai kamar ba Zahraddeen din da ta sani ba, mai ji da kai da rashin son wargi.
Sai ita ma ta yi cooling, gwiwoyinta sun sage, ta ce, “Ni na ce bana sonka?”
“Kwarai kin ce ba kya sona, saboda ni yaron Babanki ne. BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE koh? Ko ba haka kika ce ba? Kunnuwana suka jiye min, ba wani ya taso ya gaya min ba”.
Za ta yi magana ya katse ta.
eee Ba na kalubalantar ki, not eben a little, na yarda na amince in cigaba da zama YARON KI (serbant), kuma MIJINKI, (husband) mahadin rayuwar ki (life-mate) kamar fiyayyaen halitta da Uwargidansa Nana Khadijah Bint Khuwalid, idan har za ki bani wannan gurbin, zan samu Marwanatuh?”
Kunya ta kama ta. Kamar tace da kasar ta tsage ta shige. Magana zarar bunu….ta riga ta fita. Wannan ba itace tarbiyyar da mahaifin su ya dora su akai ba. Ta tuno dukan mutuwan da Daddy yayi mata a lokacin da tayi wannan furuci. Ashe Zahraddeeen din ma ya ji. Sai ta soma kokarin yin repenting. Ta yi murmushin yake ta ce,
“Idan ni na ce bani son ka, kaima ai bani kake so ba, Safah kake so, aka lika maka ni, don haka bai kamata ka ga laifi na ba.
Soyayya ba lallai ta faru a sanda aka so faruwarta ba. Ita wata irin aba ce da ba ruwan ta da lokaci, matsayi da dangoginsu. Abu ce wadda ke faruwa a duk sanda ta so, ta gudanar da tunani ta sarrafa gangar jiki (duba littafin ALHERI). In hakane kenan banida laifi don nace bana son wanda na san ba so na yake yi ba”.
Ya ce cikin murmushi, wanda ya kara kawata kyakkyawar fuskarsa.
“in haka ne, we habe the same problem, sai mu kirkiro SON mu taru mu rufawa juna asiri, ta hakan ne kadai zamu sanya marigayi farin ciki a kushewar sa.
Auren mu babu rabuwa, (mutu-ka-raba ne). In
haka ne kenan dole mu mance baya (past), mu fuskanci gaba (future), mu yi gini a kan sabuwar rayuwar da muka tsinci kanmu (present), ba tare da waiwaye ba!”.
Ba ta amsa ba, amma zuciyarta sanyi take, haka fuskarta ta nuna sassauci. Soyayyar mijinta na kutsawa har cikin bargo da kasusuwanta. Ashe wannan shine ZAHRADDEEN din da_ take kalubalantar Safah a kan ta so shi? Ashe ita soyayyar baka saninta sai ta zo kanka? Ashe Zahraddeen din ba’a sonsa ba’a saninsa sai an dan yi kyakkyawar mu’amala dashi, koda ta dan lokaci ce? Ashe wannan itace SOYAYYAHr da Safah ta dandana, amma take ganin bekenta akan rashin alkawari???
Zata iya fassara tata soyayyar a yau da ‘definations’ da yawa, wadanda neither Safah nor Zahraddeen edperienced it. Sai ta sunkuyar da kanta, ta kasa hada ido da Zahraddeeenin……. wanda ke kallon yanayinta, yana binta da ido, da zuciya, yana karantar weakness dinta; tana da karfin hali, tanada tsiwa, tanada son aji (class) amma bata da power a fannin soyayya (abin nufi, bata iya fin karfinta bata da juriya a fannin ta, mijin aurenta zai iya gane hakan, zai iya yin amfani da hakan ya cutar da ita batareda ta kare kanta ko ta ankara da hakan ba), irin su ne ake cewa da wuya su fada a soyayyar, amma in ta samesun, ko ta zo kansu, to basu iyata ba, suna yin ta ne (wholeheartedly).
Murmushi yayi, murmushi mai mika bukatar miji zuwa ga matar sa….kowanne sassa na zuciyar ta
da gangar jikinta na kaduwa, kaduwa mai ban mamaki irin wadda bata taba ji a rayuwar ta ba. Kamar yasan abinda take ciki, (kodayake ya sani din), zai iya cewa nashi ya fi nata, tunda ita mace an halicceta da kawaici da alkunya, wanda shi baya dashi. Sai ya mika hannu ya kama hannunta biyu hagu da dama, ya mikar da ita tsaye. Dukkansu dogaye ne tsayinsu daya, fadin kirji kawai ya fita.
Lokaci na farko da ya jata cikin jikinsa, a hankali ya rungume ta. Ya sanya hannu cikin sumar kanta cikin wani salo na kwarewa da sanin weakness din duk wata lafiyayyar mace. Banda karkarwa da bari ba abinda take yi cike da tsoro, fargaba da razana na rashin sabo. Sai dai duk wata gaba ta jikinta ta amshi sakon da Zahraddeen din ke aikawa ta cikin gashin kanta zuwa sassan jikinta. To such an edtent that, lamarin ya zo wani ‘limit beyond her capability to ignore….’ (ya zo wani mataki da bazata iya hanawa ba).
Karo na farko a rayuwarta da ta tsinci kanta a wata duniya ta daban, da bata taba tsintar kanta a ciki ba.
2K KK
“Kalli ‘ya’yan hutun, da hutun bai sa su sun kaucewa tarbiyyah ba! MADALLAH da wannan Uba nagari. Allah Ya nuna maka aikin ka har makwancinka.”.
Haka Zahraddeen ya fada cikin zuciyarsa, yana rungume da amaryar tasa, wadda yake kallo tana
barci sadidan cooly, ta hasken farin wata wanda ya ratso ta cikin shara-sharan farin labulan dakin barcin ta.
Ya rungume matarshi sosai, cike da so da kauna, hadi da godiya ga Allah tare da yiwa Alh. Aliko addu’a. Wannan ta mallaki duk abinda yake so matarshi ta kasance tana dashi. Koma fiye. Ya yarda soyayyah is not the most important thing in marriage (ba itace abu mafi muhimmanci a cikin aure ba). Akwai wasu abubuwan da yawa bayan ta; neman zabin Allah a duk sanda maganar aure ta taso, albarkar iyaye, bin shawarar na gaba (musamman Uwa), da rashin nuna gaggawa akan abinda mutum yake so.
Ta yi juyi a hankali ta bude idanunta wadanda ke cike da barci da gajiya, suka hada ido kunya ta kama ta, Zahraddeen din sai ya kara lumshe mata idanun, ta sunne kanta cikin yalwatacciyar sumar da ta cika kirjinsa.
Zuciyarta fal da so da kaunar mijinta, wanda ya siye duk wata soyayya da Allah Ya halittawa dan-adam cikin zuciyarsa a dare daya kacal. Ta ta lumshe ido, hawaye suka zubo, zuciyarta cike fal da so da kaunar mijinta da ya mamaye 90% na zuciyarta, cikin dan lokaci kalilan.
Bayan ta gama wanka ta yi sallah ba tare da ta cire hijabin sallar ba ta cimmasa a kicin yana ta kiciniyar sama musu abin karin kumallo, yana sanye da wasu “pj’s” ruwan makuba. Kanta a kasa ta shigo kicin din ta ce,
“Da ka bari zan yi’.
Ya aje dankalin da ke hannunsa, ya iso gareta ya
zagaye ta da hannayensa ya kwantar da kai a kafadunta.
“Ya zan dora miki gajiya the whole night (a tsayin daren bakidayansa) kuma in dora miki aiki? Hakan zai zama injustice (rashin adalci)” cikin matsananciyar kunya tace
“Na hutasshe ka. Ka je zan karasa. Wannan ba aikin ka bane. Ban taba ganin Daddy yana taya Mami aiki a kicin ba, ni nake tayata, nida su Dije” dariya ta bashi amma bai bata ba, kallonta kawai yake yi, sai tasa hannunta cikin nashi ta karbi wuka da dankalin dake hannun shi. Ya harde a gefe yana kallon yadda take girkin ta cikin kwarewa, mamaki fal ransa, don bai zaci ko kicin tana shiga ba. A yadda yake kallon takunta, ya kuma fassarata.
Don ko sanda suke off campus ya lura Biola take sawa tayi mata komai. Ya cigaba da kallonta cikin yin obserbations masu yawa akanta, kamar wani ‘psycho-analytist’ koko ‘behabioural analyst…….. i.
Ta juyo suka hada ido, har zuwa lokacin ya kasa dauke ido a kanta.
Cikin shagwaba ta ce, “Ni dai don Allah ka tafi, idan kana kallona haka sai kasa na kone ko na yanke”.
Ya yi dariya ya juya zai fita yana cewa, “Na fita,your edcellency!” (Wato ranki shi dade). Shower ya je ya sakar ma kanshi, sannan ya fito ya shirya cikin kananan kaya na Hilfiger, yana tazar sumar kanshi ta shigo dauke da katon tray, ta ja tebir ta dora tana satar kallon shi ta gefen
idonta. Ba karamin burge ta Zahradden dinnan yake yi ba, wajen dressing, ba tun yau ba, tun sanda yake zuwa zuwa gidansu na makaranta, domin mutum ne da ya san sirrin dressing na western ne ko namu na Hausawa.
Duk irin dresing din da ya yi kuma, karbar jikin shi yake ya dace da zubin halittar shi, kara juyawar nan da za ta yi suka yi ido hudu tayi saurin dauke idonta. Da sassarfa ta juya zata fice, ya riko gefen mayafinta, batareda ya juyo ba.
“Ba inda za ki sai kin gaya min me kike kallo?”. Cikin sauri da sarkewar murya ta ce, “Ni ba abinda nake kallo…”.
Sai ya rungume ta, yana kwaikwayon ‘yar muryar ta yace
““….da abinda kike kallo. Zahraddeen kike kallo. Kuma shi din mijinki ne, mahadin rayuwar ki na har abada!
Babu laifi a cikin hakan. Kalleni ki more, nima tube wannan zurmemen hijabin in kalleki cikin hasken safiya in more…… , wata rana irin yau na zuwa da zaki bude ido ki ga kin cika gidannan da ‘ya’yan Zahraddeen har ki aurar dasu ki goya jikokinsu. To wace kunya ce ma ta rage afterall abinda ake ma kunyar Zahraddeen ya kawar dashi gabadaya jiya.??? ”
Ya fadi, tareda juyowa gabadaya, domin da ya juya mata bayane rike da gefen mayafin nata. Kamar ta rafsa ihu don kunya. Alkunyar ta na burge shi. Ya janyota ya rungume gabadaya. Ya soma kissing karan hancinta da bakinta yana gaya mata kalamai masu nauyi da suka fi karfin biro ya
rubuta. Sai bayan wani lokaci ne ya bari suka yi kalacin tare.
Ta koma kicin ta dauko fulas din da ta zubawa Inna don Rabi’a ta koma makaranta, ta je ta kai mata har dakinta ta gaishe ta.
Ba karamin jin dadin hakan Inna Binta ta yi ba, don dama ita bata dauka da zafi ba, bata sa mata ido ba, tunda tasan yadda auren ya kasance. Ramar da Zahradeen ke ta yi a lokacin ita tafi damunta, ita da kanta ta lura yarinyar ta sauko don kanta.
Ta janyo kula cike da kosai da soyayyen dankalin hausa tace ko zata diba, tace “na koshi Inna, amma bari na kaiwa Yayan Rabi’a ko zai kara” ta debi kadan a filet ta rufe. Ta sanar da ita yau za ta koma makaranta.
Inna ta yi musu addu’a mai yawa, ta koma sassanta, ta tarar da Zahraddeen ya gama shiryawa ita kadai yake jira.
Ta dauko jakarta da mayafi da wasu takardu cikin file ya janyo kofar, suka yiwa Inna sallama bakinta ya ki rufo da ganin sauyukan da ba ta zata cikin dan lokaci ba.
Tabbas mutuwar mahaifinta kadai yasa ta shiga taitayin ta, ita kanta Marwah yanzu duniyar tsoro take bata, saboda rashin tabbas na rayuwa da ta gani.
Shi ya taya ta ta gama registration dinta na sabuwar shekara, duk da a makare ta zo, ya maida ita gida. A ranar ya juya Kaduna, don yana da aiyukan dake jiran shi a ofis masu dimbin yawa, ya bar mata motarsa daya don zuwa
makaranta.
2B KKK
To haka rayuwarsu ke garawa, cikin nasarori da falalar Ubangiji iri-iri. Shekara kwana ga mai yawan rai, a yau ne ake yaye daliban Jami’ ar Ahmadu Bello na wannan shekarar, ciki har da Safah Aliko Dan kasa, wadda ta karbi kwalin MBBS mai daraja ta farko, tuni ita Marwah ta karbi kwalinta tun shekaru biyu da suka wuce, don nata karatun bai kai tsayin na Safah ba. Ita ta fito da kwali mai matsayi na biyu.
Cikin farin ciki Hajiya Zainab ta rungume ‘yar ta, Zahraddeen na daukar su a hoto da digital. Har suka zo gida farin cikin da suke ciki a yau ba zai fasaltu ba.
A daren ranar suka juyo Zaria wato shi da tashi matar, duk yadda Marwah ke so ya barta ta kwana dasu Mami ya ki amincewa, tana ta kumburi kamar ta fashe da kuka, ya bude mata kofar gidan gaban motar ta shiga ta zauna.
Ya yi murmushi ya ce, “Kwanan ne ba zan iya ba Marwah, ni sai ki barni in ragaita?”
Ta zumbura baki ta harare shi yana dariya ya ja motar aguje suka harba kan titi.
Karfe goma na dare suna cikin gida, sun dade a dakin Inna ana hirar yadda taron ya kasance, sai
da Inna Binta ta kore su ta ce suje su kwanta. 2K kK
Likitar hakorin Dr. Safah Dan Kasa da mai harhada magungunan (Pharmacist) Marwah Aliko Dan Kasa sun zauna sunyi shawara a
tsakaninsu cewa, za su sayar da wani kaso na gadonsu su bude babban asibitin hakori (pribate). Kuma Zahraddeen ya goya musu baya.
Bayan kammala karatunsu a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake Zaria (ABUTH). Da taimakon malamansu da sauran manyan likitoci ‘yan’uwansu. Dan Kasa Dental Hospital ya samu kafuwa cikin dan lokaci kalilan, a garin Kaduna. A lokacin sun bar Zaria, sun bar Inna da Rabi’a wadda ta fitar da miji a wannan watan, an sanya kwanakin bikin watanni biyu cif!
Nura yana tare dasu a Kaduna, domin ya gama sakandire ya fara karatu a Kaduna State Unibersity.
Zahraddeen na cigaba da sauke wannan nauyi da Alh. Aliko ya aza masa, dukiyoyinsu suna hannun sa har kawo wannan lokacin cikin AMANA sai bunkasa suke, abin kamar a jinin sa yake, komai kara hauhawa yake. Kuma baya wasa da hakkin Allah cikin dukiyarsu. Su kansu bazasu iya tyakance abinda suka mallaka a duniya ba. Saidai fa daya alkawarin da yayiwa Daddy har yau yana nan yana yawo a kwanyarsa, yana masa kuda a kunnuwansa, wa zai aura, don ya cika wannan alkawari? Matarshi ta ishe shi ta kowanne bangare, tun bayan da suka shirya baya ko iya daga ido yayiwa wata diya mace koda kallon kirki. Matsalarsu daya ce wadda Zahraddeen din shikadai ya santa, matsalace wadda ta shafi auratayya, ba kuma wata gagarumar matsala bace da ta gagari a yi solbing dinta, tunda babu yadda za’ayi ace dan adam ya rayu ba tareda
wani nakasu ba. Kowanne dan-adan tara ne bai cika goma ba . Ga Matar tashi da bala’in kishi, duk sakatarorin shi mata da abokan aiki saida ta san yadda tayi ta raba masu wajen aiki. Ta maye gurbinsu da karti.
A lokacin ne suka kara bude DAN-KASA INDUSTRIES na sakar tufafin auduga wanda ke da reshe a Geneba, wanda suka bude da sunan Zahraddeen halak-malak ba tareda shi din ya sani ba. Har sai lokacinda ribar da kamfanin ke samu gabadaya ta soma tittida cikin account dinsa, ya yi kokarin yin musu, amma ‘yan biyun suka fashe mai da kuka, wai in Daddy ne yayi masa kyauta domin nuna godiyarsa abisa wani kokari ko taimako da yayi masa ya ji dadi, ya amfana har fiyeda yadda yayi zato, yayi masa dan ihsani domin domin ya nuna jin dadinsa ko godiyarsa, zai maida masa ne yace ba za ya karba ba? Sai albashi kawai? Da haka suka rufe bakin sa domin ya kasa cewa komai.
Shi kuma ya yi amfani da wannan damar ya koma karo karatun PhD dinsa a babbar Jami’ar garin Geneba. Wanda ke _ karkashin kasar Switzerland. A lokaci guda kuma tareda bunkasa ayyukan kamfanin DAN-KASA INDUSTRIES. Zuwa rassa guda biyu daya a Munich (Germany) daya a Zurich (the greatest city of Switzerland).
Likitar, (Safah) ta dauki kwararrun likitocin hakori, musamman abokan karatunsu na jami’ar Ahmadu Bello. A gefe guda na ‘Dan-Kasa Dental Hospital’ tankareren dakin shan magani ne (phar
macy) wanda ke dauke da duk wani nau’in magani na gida da waje, wanda ake shigo dasu kai tsaye daga kasar India, mallakin Marwah Aliko Dan-kasa.
Zuwa wannan lokacin Marwah ta gama mallake zuciyar mijinta da kyawawan halaye, biyayya, soyayya da kyautatawa. Ta yadda har ya zamo cikin nadamar alkawarin da ya yiwa Alh. Aliko na cewa zai kara aure, wai aure na soyayya a cewar Alhajin, domin matarshi ta ishe shi, ba shi da gurbin da zai iya jogana soyayyar wata diya mace. To shi yanzu wajen wa zai je yace yana son ta? Kallon mata yake a dage, a kaikaice (basu da abinda za su ja hankalinsa kansu). Har ya ke tambayar kansa ashe dama ‘your first lub might not necessarily be your true lub???’
Marwah bata bi Zahraddeen Geneba ba, sakamakon tsohon cikin da take da shi na haihuwa yau ko gobe. Suna gidansu na Malali a Kaduna. A lokacin Zahraddeen yana can sai Inna Binta ce ta dawo gidan dan kula da ita. Duk wata kulawa da ya kamata uwa ta gari ta yiwa diyarta Inna Binta na yiwa surukarta.
Ranar wata litinin a lokacin watanni Zahraddeen biyar a Geneba, nakuda ta tashi gadan-gadan, Inna ta kira Nura a waya ta ce maza ya zo ya fiddo mota su tafi asibiti.
Ko kamin Nura ya zo faya ta fashe, kan kyakkyawan yaro mai kama da ubansa a komai ya sako kai. Haihuwa mai matukar sauki Allah Ya bata, sai Inna ta shiga hamdalah, ta yanke cibi ta zaro mahaifa ta kunshe.
Duk wani taimako da ya dace ita tayi mata, sanda Nura ya fiddo mota suka je asibiti an tabbatar da koshin lafiyarsu ne kawai itada jaririn. Tareda basu magunguna na karin lafiyarsu. Inna ta yi mata wanka da tawul ta wanke jariri, ta shirya shi cikin kayan sanyi.
Nan da nan ta hau damun kunun kanwa, gasa nama da farfesu don maijegon ta samu ruwan nono da karfin jikinta. Ta aika aka samo runhu daga Zaria don fara wankan jego.
Mami da iyalanta tare da Hajiya Mama sai zuwa suka yi suka tarar da maijego da jaririnta fes dasu, su kansu sun gamsu da kulawar da Inna ke mata babu wanda ya ce zata koma gida wanka. Mami don kunya ba ta dauki jaririn ba, sai Aunty Shahidah da Safah ke rige-rigen dauka. Suka sunkuto shi suka kawo shi cinyar Mami. Hajiya Mama ta ce, “A’a, ku yi a hankali kada ku karya shi ko ubansa bai ganshi ba, sun san zafin abinsu, kun san kuna son dan kuka zauna a gabanmu har yanzu gotai-gotai da ku kuna gantalin aiki da karatunda bashi da karshe?”
Suka sa dariya, Safah ta ce, “Here comes Daddy!”. Wato ga Daddy ya zo.
Mami ta ce, “Da yake ke kika haifar musu dan da za ki sa masa suna? Ni matsa nan kada ki taka ni”.
Marwah ta yi murmushi ta ce, “Allah Mami sunan Daddy za a sa, Deen ba zai ki ba. Kullum addu’arshi kenan Allah Ya sa namiji ne mu samu mai sunan Daddy”.