BABBAN GORO BOOK 2 CHAPTER 7 by sumayyah Abdulkadir
(tedt message). A kasalance ta dauka ta bude.
“Ki dauki waya ki ji mai zan ce miki, rashin daukar wayar ba zai sa ba, kuma ba zai hana ni yin kiran ba”.
Ta shiga mamakin wannan karfin hali, ba ni na neme ka ba, kai ka neme ni sannan ka ce za ka yi min gadara?
Kawai sai ta kashe wayar gaba daya ta yi kwanciyarta.
Wunin ranar zungur a daki ta yi shi, ga shi tana fashin sallah, ba abin da ke tayar da ita daga gado sai shiga bandaki.
Washegari haka ta tashi sukuku, Mami ta rasa gane kan diyar tata. Gaba daya ta birkice mata tana ta kuka.
Tambayar duniya Mami ta yi Safah ta ki cewa komai. Addu’a kawai take ita ma Allah ya dau ranta ta bi Daddy ta huta da azabar zuciya da nadama.
A wannan lokacin babu wanda Mami ta tuno sai DADDY, magana daya mai sanyi zai gayawa Safah ta warware daga bacin ranta.
Ita ma sai ta saka kuka ta ce, “Safah mutuwa kike so nima na yi? Kukan ki na daga min hankali, idan ba ki ji tausayina ba bai kamata ki kara min damuwa a kan wacce nake ciki ta rashin IMAM ba”.
Cikin kuka ta ce, “Ki yi hakuri Mami, nima shi nake son gani. Mami na kasa son kowa, Mami shi
kadai nake so, ki taimake ni ki nemo min shi’.
A yau har na fara yin tunanin yin aure, sai kuma nake ganin idan nayi hakan ban kyauta masa ba, zai kara tabbatarwa da cewa shine bana so din muddin na auri wani. Ya dawo ya tadda ni a gidan aure”.
Ta ci gaba da kuka sosai.
Zuciyar Mami ta karaya sosai, ta yarda al’amarin Safah ba da wasa bane. Watakila hakki ne yake tambayarta.
Ta jawo ta a hankali ta rungumeta, ta ce, “Da da akwai abin da zan iya a kan ganin Imam da na yi tun kafin ki furta.
Kina gani ba irin neman da Daddy bai sa anyi ba, zancen dai daya ne ya bar Glasgow, babu wanda ya san inda ya koma.
Ina so ki tuna cewa Imam ba yaro bane, duk abin da zai yi yana sane, ba zai kai kanshi ga halaka ba duk rintsi. Sannan babu sauran maganar aure a tsakanin ku koda ace ya dawo. Ki dawo cikin hankalinki kisan abinda kike ciki.
Don haka ni kullum cikin mafarkina lafiya nake ganinsa. So ki cire Imam a ranki haka, ki zabi mutum guda cikin maneman ki ki yi auren ki ki huta, ko don muma mu huta da surutun mutane a kan rashin auren ku ke da Shahidah.
Don Allah Safah ki rufa min asiri ki yi aure ko na samu sukunin zuciyata”,
Ta share fuska da mayafinta ta ci gaba da cewa. “Kin ga Shahida ta fidda miji, da ke wata mai kirki ce sai a hada bikin ku a huta. Ku ku huta, muma mu huta’”.
Ta rungume mahaifiyarta. Ta ce, “Mami insha Allahu ina ji a jikina lokacin aurena nima ya zo”.
ae KK
A washegari ba ta je office ba, don haka ba ta je ba sai ranar Laraba. Inda ta cimma aiki jingim, don ma wai a hakan Dr. Garba ya taya ta.
Abu na farko da ta fara yi shine, kunna wayarta. A take kuma sakonni bila-adadin suka soma tittidowa.
Duk rabi daga wannan lambar ta Glo ne. Ba ta tsaya karantawa ba duk ta goge su. Don ta dauki mai wannan layin a dan rainin hankali kawai, sannan tasa wayarta a boicemail.
To amma kwakkwafi irin na zuciya, sai ta dame ta da son sanin waye wannan? Meye dalilin shi na wannan kira haka da wadannan ssakonni haka??
Ta bude file na farko dake gabanta kenan aka turo kofar ofishinta babu sallama, aka maida kofar a hankali aka rufe.
Ba ta dago ba don a zatonta patient din ce, tana ci gaba da rubutunta ba tare da ta dago din ba, ta ce, ‘Habe a seat plz”. Ta ci gaba da rubutunta. Tsayin minti biyu sannan ta dago don ta ji alamar patient din bai zauna ba ko bata zauna ba. A lokacin ne idonta yai arba da patient dinta da ya yi mata karan-tsaye a zuciya kwanaki biyu da suka wuce.
Sanye yake da caftan na wani lallausan yadi fari sol. Dogon Bafillacen, a idanunshi siririn farin
tabarau ne wanda ya kara kwarzanta kyawun halittar sa, ya fiddo ilhamarsa, bai kuma boye kwayar idanunshi ba, wadanda suka canja kala daga farare kal zuwa brown, suke kuma cike taf da wani babban al’amari da ba ta hango iyakarsa ko karshensa ba.
Ta dan bude baki tana murmushi mai nuna sanayya, ta kasa magana amma har cikin zuciyarta murmushi take. Sai kuma duk ya cika mata ido, ya yi mata kwarjinin da ya sanyata mikewa tsaye (alamar girmamawa irin ta Bature).
Sannan ta ce a hankali, “Habe a seat plz”.
Bai zauna din ba dai, kallon ta yake da idanuwa narai-narai kamar za su zubo da hawaye saboda maikon su (oily eyes) masu dauke da ‘tensions’ da rigingimu masu yawa.
“To shi kenan”’.
Ta fada a sanyaye, domin ya fara bata haushi. Wannan gadara da yawa take.
“Ko za ka dan matsa daga jikin kofa in duba patient na gaba?”
Nan ma shiru. Ai kuwa ta fusata, ta mike ta dauki jakarta ta ture files din ta ce a ranta, “Gara in bar maka ofishin tun baka shake ni ba”.
Abin haushin a jikin kofar yake, bai da alamar ko niyyar matsawa, sai dai ko in karfi za ta sa ta janye shi.
To amma da wane karfin zata ture ingarman mutum haka? Mai suffar larabawan Maghrib? Sai suka tsaya gab da juna suna kallon-kallo, zuciyoyinsu na motsi, suna maganganu masu girma da kwayar idanunsu.
A yayin da gangar jikinsu ke nata aikin na tura sakonni cikin zuciya da kwakwalensu, kowanne zuciya da gangar jikinsa abu daya take gaya masa irin na dan uwansa cewa.
‘“Wannan ce/ne daidai da ni a rayuwa, ta mizani da yawa; body structure, behabiuor, ilmi da duk wani daidaito na rayuwa da kowanne dan adam ke nema ga intimate — partner (wato abokin rayuwa).
Amma a zahiri, Lamido ya bude baki ya soma magana a hankali. Saidai yadda yake maganar a kasaice kai ka ce bashi yake yin furucin ba. Sabida lebbansa kawai ke motsi ahankall. “Sunana Naseer Abdulkarim (Lamido), na kasance mutum mai naci da shanye wulakanci a kan duk abin da zuciyata ke so. Don haka ba zan gaza komai a juriya cikin al’amarin ki ba, naci da kafiya ta a kanki ba zasu taba gazawa ba.
Na kira, kin ki dagawa, nayi msg kin ki replying. Dr. Safah gibe me a chance to edpose myself from this emotional torture. Ina tsammanin cewa zan samu sauki idan na fada din, ko da ba zan samu karbuwa ba. Kalmar ba mai wuyar fadi bace a baki, amma mai girma ce a zuci, ina SON ki ne Safah…..!!!”
Sai ta sunkuyar da kanta kasa tana murmushi ta gaza dagowa ta hada ido da wanda ya kirayi kansa da Naseer Lamidon. Wani irin mutum ne mai kidima zuciya da gigita ta? Ba ta da ja, ita ma ta afka tun daga first sight, me za ta yi? Me za ta ce? Ban da ta ba da kai bori ya hau?
Musamman a wannan lokacin da take a bukace da son yin auren. Ba wai bukatar gangar jiki kadai ba, har ma da son farantawa Mami.
Sai ga wani BABBAN GORON Allah Ya kinkimo Ya bata wanda bai taba zuwa cikin mafarkin ta ko tunaninta ba. A dai-dai lokacin da take tsananin bukatar zuwan nasa.
Idan bata amsa ba ai ya zama butulci ga Ubangijin da Ya dubeta Ya turo mata shi, don ta sharewa mahaifiyarta hawaye, again, ta taimaki kanta, ta rufawa rayuwarta da kuruciyarta asiri. Ta zamo cikakkiyar mutum mai daraja kamar ‘yar uwarta. Imam watakila sai a Darussalam, idan sunada rabon komawa auren sa yi shi a Aljan
Nasir ba boyayye bane, duk wani dan boko kuma dan Najeriya ya san da zamansa, ya san da hobbasarsa wajen yaki da mahandaman Najeriya a matsayin shi na shugaban (EFCC ) mai kuma kujera a yanzu. Bafillatanin Taraba ne, mazaunin Abuja a halin yanzu.
Dan kimanin shekaru arba’in, Naseer, yana da wasu halaye dake burge al’ummarsa da shi, fadin gaskiya komin dacin ta, rashin tsoro da magana daya. Baya taba cewa eh, ya dawo ya ce a’ah.
Ga faram-faram da haba-haba da jama’a, fara’a da son addini. Wadannan sune halayen shi dake bayyane, na boyen kam masu kyau ne ko ba masu kyan bane, sai ka zauna da shi za ka san su. Allah kadai Ya san halin bayinSa. Na zahiri da badini, duk da haka ance shaidar mutum nada alaka da
shaidar makusantansa, to duk wani wanda ke tareda Lamido, ya tabbatar da kyawawan halayensa. Duk wani wanda ya san Lamido Naseer, alherin sa ne a bakinsa.
Ya yi dukkan karatun shi a jami’ar Legas, a kan tattalin arzikin kasa ‘Economics’, shi da matar shi Danejo (Dijah) auren gida ne, kuma aure na soyayya, domin tun suna yara ake cewa a dangi Danejo matar Lamido.
Shi kuma sai ya girma da wannan furuci, tun tana karama yake hidima da ita. Yana son Danejo soSai, sai dai tana da nakasun da har yau ba ya yi mata kallon cikakkiyar mata a gare shi. Wadda zai dauka a matsayin uwar iyalinsa har karshen rayuwarsa.
Ba wai ba ta da kyau bane, Danejo kyakkyawar Bafulatanar Taraba ce, kuma wayayyar Legas kyankyasassar Abuja, kuma kawa ga manyan mata.
To amma fa ko kwalin sakandire Danejo bata da shi, yayi-yayi ta koma makaranta ta ki, kwatakwata ita Danejo Allah bai sanya mata son karatun boko ba.
A ganinta babu abin da ya kai shi wahala, don me ake yin shi? Ba don ayi aiki a samu kudi ba? To kudi Allah ya baiwa mijinta ya ishe su, tunda ta iya karatu da rubutu.
Don haka ne fa har yau a idon Nasir Danejo ba ta cika mace ba, ko taro baya shiga da ita balle wakilci a wani occassion.
Babu Turancin kirki a bakinta sai tsintaccen broken din Lagos inda suka fara zama tun farkon au
rensu a lokacin yana koyar da tsimi da tanadi a jami’ar Lagos inda yayi karatu kenan, balle ya shiga da ita wani taro matsayin uwargidansa, duk da haka yana son ta, don mahaifiyarshi na son ta, sannan tana hidimtawa ‘yan’uwansa, ba ta da rowa, ba ta da kyashi.
Ke dai barta a kishi, ko kallon ki Lamido ya yi sai ta fassara shi da wata manufa. To a hakan suke har yau, yaransu biyu Fahad da Fa’ ik. Mahaifiyarshi Yaya ce ga mahaifiyarta, Lamido ya yi aiki da dama a Taraba bayan ya bar lecturing a LASU, wadanda sakamakonsa na first-class ne yasa suka rikeshi, as opportunities flows….ya bar LASU ya dawo jaharsa Taraba. Da kwalayenshi uku, digiri, masta, da digiri na kololuwa. Lamido yayi aiki kala-kala a Taraba a bankuna da kamfanonin coca-cola, Daga baya ya koma aiki da Federal Inland Rebenue Serbice (FIRS), daga nan ne aka zabesu su goma a gwamnatin Marigayi Umaru ‘Yar Adua aka basu mukamai dabandaban, inda ya tashi da kujerar shugaban (Economic and Financial Crime Commission) da aka fi sani da (EFCC).
Lamido (Nasir) dan dangi ne gaba da baya, gidansu babban gida ne a jihar Taraba. Gidan da ya samu shaidar tarbiyya da riko da addini ga yaransu da manyansu.
Mahaifinsu Malam Abdulkarim Bafulatanin Numan ne, wanda kasuwancin fata ya kawo Taraba har ta zame masa mazauni shi da mai dakinsa Hajiya Nadeeya da ta kasance Ba-sudaniya ta usul, amma mazauna Najeriya, irin wadanda kakan
ninsu suka zo da su tun suna kanana domin kasuwanci ko gudun hijira, lokacin yakin Dafur, suka zama zaunannun Najeriya.
Sai dai za ka yi mamaki idan ka ji cewa cikin iyalin Malam Abdulkarim su bakwai, Nasir ne kadai ya yi zuzzurfan ilimin boko, shine babba, sai mai bi masa Talatu, tun tana shekaru (15) Malam Abdulkarim ya aurar da ita a Yola, tana can da ‘ya’ yanta rututu.
Sai mai bi mata Idris, iyakarsa sakandire ya tubure ya kama harkar dinki, ya ki karatun. Abubakar, Ishak da Aliyu su suka dan tabuka, Abubakar ya yi NCE, ya fara koyarwa a wata makarantar sakandire. Ishak da Aliyu kuma suna da Diploma, suna aiki a Local Gobt. Autar su Nasir mace ce Zahra’u, ko aurar da ita ba a yi ba. A halin da ake ciki yanzu, Mal. Abdulkarim girma ya cimmasa, zaune yake a gidan yana koyar da ‘ya’ya da jikokinsa Alkur’ani, ba ya komai, ba ya zuwa ko’ ina.
Duk nauyin gidan da na ‘ya’yan gidan yana kan Da daya kwal tamkar da dubu, wato Nasir. Inda duk ka gilma a gidan (Yaya Lamido) kawai za ka ji a bakin kowa.
“Bari Yaya Lamido ya Zo…….. ” (idan ana magana ta kudi kenan). Shi din kuma bai taba nuna gajiyawa ba. Kullum basu yake haka kullum kara samu yake, wannan alkawarin Allah ne, mai kyautatawa iyaye da ‘yan uwansa bazai taba yin talauci a rayuwarsa ba.
Sai ya yi dace da mace mai son ‘yan’uwan da taya shi sabgar zumuncin wato Danejo. ‘yar
shekaru talatin, gajeriya siririya mai jikin Fulanin usli, fara sol!
To amma a yau ga Naseer ya gigice a kan diyar Mami baka doguwa mara rama, mai ingantaccen ilimi yadda yake so, kuma ga alamar yana neman yin nasara, idan aka yi la’akari da zaratan maza bila adadin da ya kasa a kan malamar kiwon lafiyar hakorin.
Zuciyoyinsu sun yi amanna da juna cikin dan lokaci, sun yarda za su zauna cikin inuwar aure, su tashi tare ranar Alkiyama karkashin inuwar al’ arshin Ubangiji a matsayin ma’ aurata.
To bari mu bisu a hankali mu gani.
22k 362K
A ranar dai ba ta iya ta bashi amsar komai ba, sai shima bai takura da sai an bashin ba, juyawa kawai ya yi ya fita.
Ya ce, “Na barki lafiya”. Tare da rufo mata kofar ofishinta a hankali.
Escourt din shi da ya baro a bakin kofar shigowar suka mara mishi baya cikin sassarfarsu. Da bakaken kwat-kwat dinsu, da _ bakaken takalmansu masu sheki da kara. Ya barta tsaye a daskare, ko kafa ta kasa cirawa. Bafulatanin, ya sukurkuta ta da yawa, ya tafi da imaninta gaba daya, har ta soma cewa cikin ranta.
“Anya ba surkullen su na Fulani ya yi min ba?” Safah ta manta cewa Mami ma Bafulatana ce, kasancewarta da bakar fata baya nufin itama ba ta da jinin Fulani a jikinta.
A daren ma da ya kira wayar kasa dauka ta yi, shi
kuma ya so ya sanar da ita ne cewa ya sauka lafiya.
Tunda ta ki dagawa sai ya yi mata sako. Wannan karon kam da rawar jikinta ta duba.
“Just to say gooooood night!” – LAMIDO
Ta yi murmushi ta tura.
“Habe a sound sleep”.
“With you in mind???” Ya tambaya.
“In both the soul and mind….”. Ta amsa.
Sai ya yi murmushi, irin wanda bai taba yi a rayuwarshi ba.
28 KKK
Da safe da kuzarinta ta yi shirin aiki, Mami na kallon sauyuka da dama a tare da ita, tana walwala tana kuzari. Amma tunda ba a sata cikin lamarin ba sai ta yi shiru..
Shahida ce ta ce, “Mami ko dai Hassana ta yi waya da Ya Imam ne?”
Mami ta ce, “kayya. Bana jin hakan, bai kira ni ba ya kirata bayan fushi yake da ita”.
Ita dai tuni ta tsufa a office, ayyukan da ta tara tsayin sati guda su ta afkawa har ta ci karfinsu. Don haka karfe hudu daidai ta koma gida
Tun kafin ta yi parking motar a inda ta saba ta fahimci su Marwah na gidan, don ta ga motar Zahraddeen.
Tun kan ta shiga falon take kwala_ kira, “DADDY?”,
Da gudu yaron ya taho ya tare ta ya rungume. Marwah na zaune turus cikin kujera da tirtsetsen cikinta, kallo daya Safah ta yi mata ba ta san
sanda ta kyalkyale da dariya ba. Marwah ta zama kamar alkubus.
Domin dai jikin Marwah baya daukar family planning, ta makala robar rufe bakin mahaifa tuntuni, ba ta tashi ankara da cikin jikinta ba sai da ya yi watanni hudu a jikinta.
Har yau ba ta iya hada ido da Zahraddeen yadda ya kamata. Don haka gaisawa kawai su kai ta wuce dakinta rike da Daddy, ta cire lab-coat ta bude firjinta na gefen gado ta fiddo choculate da take adanawa musamman saboda shi. Suka hau shan abinsu yana ta yi mata hirar sababbin abokansa a Abuja inda suka koma da zama.
Mami ta shigo ta soma fada, “Kuna nan ba, kuna shan zakin naku. Ni ban taba ganin shashashar likitar hakori irin wannan ba, kina hanawa amma ke kina yi.
Dubi yadda hakoran yaron nan suka ciccinye saboda zaki, amma maimakon ki hana ke kike bayarwa da kanki’.
Ta yi dariya ta ce, “Mami da ya yi famfara fa shi kenan, duk zubewa za su yi’.
Mami ta ce, “Tun kan a haifi uwar mai sabulu Balbela take da farinta (tun kan ki zama likitar hakori na san wannan)”.
Ta mika ma Daddy hannu, “Bani alawoyin nan tun ban zuba maka rankwashi a katon kanka ba”. Daddy ya ce, “Zan fa sake ki, zan sake ki Mami?”
Gaba dayansu basu san sanda suka yi ta dariya ba.
Mami ta ce, “Yo ka sakenin mana? Ci kake bani
ko sha ko suttura? Ko na cefane ba bani kake ba”. Ya ce, “Sai kin yi kwalliya zan baki’”’.
Mami sai ta kama baki, wayon da ake cewa Daddy ya yi ba ta zaci ya kai haka ba.
Gaba dayansu suka yi falo ana hira har da Hajiya Maama, inda Zahraddeen ke gaya musu sun dau hutun karshen shekara ne za su wuce Zaria gobe, jibi za su Rugar Ardo garin su Inna Binta, in sun dawo kuma za su wuce Paris su karasa hutun a can har sai Marwah ta haihu.
A nan suka kwana, Safah da Marwah a gado daya suna hirarrakin da suka shafe su, kan Daddy karami na cinyoyin Safah, tana shafawa a hankali, wanda tunda ya gama shan (Banilla Icecream) da ta ba shi barci ya dauke shi.
Marwah na ganin wayar Safah na ta ruri amma in ta daga ta ga mai kiran sai ta mayar ta aje. Don haka ta shammace ta wayar na sake fara kuka ta yi wuf! Ta dauke, sai ta ga suna LAMIDO.
Kafin Safah ta kwace ta amsa da ingantacciyar sallama.
Daga can bangaren Nasir murya tausashe ya ce, “Na roke ki kada ki kashe min waya Dr. Safah, ya kike so inyi da raina? Idan jan aji ne hakan wallahi na janyu, idan kunya ce, to wallahi ba na son ta”.
Dariya ta kama Marwah, ta toshe baki tana ta yi sannan ta ce, “Don baka san yadda na kasa barci bane saboda tunaninka, ko barcin na yi mafarkin ka nake yi. Zuciyata kai kadai ta amincewa, ina dai yin shawara ne ka yi hakuri ka kara min
Safah ta kai mata duka ta fizge wayar tana cewa, “Ke kam anyi muguwa, kin zubar min da mutunci ga mutumin da baki san ko waye ba” ta fada cikin halin dafe kai da hannuwa bibbiyu.
Marwah dai dariya take, ta ce, “Ko waye wannan is a lucky guy… tunda har aka yi sabing no dinsa. I’m hundred percently his supporter. What a sweeet boice!”
Safah dai don haushi ba ta tanka mata ba, tana harhada kalaman da za ta yi mishi rantsuwa dasu kan ba ita ta amsa mishi waya ba.
Don haka baram-baram suka kwanta, hirar ba ta kare yadda aka faro ta cikin dadin rai ba.
Don in za ta kwana tana rantsewa ba zai yarda cewa ba ita ce ta amsa wayar ba, kasancewar hatta muryarsu daya ce.
Ta yi mata Allah ya isa ya fi sau hamsin, Marwa ta ce, “Daman ya isa mana. Da isarsa da buyawarSa yake hada zukata su zama daya. Wannan bawan Allah ta ko’ina ya yi a rayuwa duk da ban ganshi ba, don ko Ya Imam ba zai fishi dadin murya ba, classy, gentle!”.
Ta dau filonta ta dinga mammaka mata, duk da tsinin cikinta. Ta yi dakin Mami tana ba ta labari. Mami ba ta yi mamaki ba, take gaya mata itama sauye-sauyen da ta gani ita da Shahida daga Safah din kwana biyu. Zuciyarsu tayi haske.
Ta ce, “In Allah ya yarda shi wannan za a je da shi na ga alama, don ya samu karbuwar da babu wanda ya taba samun ta.
Ki ci gaba da taya ni addu’a a kanta, Allah ya tabbatar da alheri a kan lamarin. Don ni yanzu
sauran burina a duniya in ga Safah a dakin mijinta kamar ki, tana haifar ‘ya’ya kamar kowace mace”,
Ta soma share ido, “Allah ka ji kan Daddy….” Sai suka koma sharbe ita da Hussainarta.
Karfe tara na safiyar washegari Idi maigadi ya danna kararrawar shigowa falo. A lokacin duk suna bisa tebur suna kalaci, har Zahraddeen wanda ke ta kai lomar Alkubus da Taushe.
Daddy na cinyar Safah tana ba shi Kuaker Oat, wanda aka dama da madara sosai, tana jiran su gama su wuce Zaria ne sannan ta wuce Office. Zahraddeen ke tambayar Mami, “Amma Mami kamfanin biredi su suke gasa Alkubus ko?”
Ta yi murmushi a nutsenta ta ce, ““A’a, kamfanin SHELL ne”.
Sai a lokacin ya gane katobarar da ya yi, ya kama kai, “Mami ba fa santi nake yi ba, tambaya ce kawai”’.
Sai Safah ta dauko kwalin toilet paper ta kara masa a baya, “Bari mu sa ma Abban Daddy waigi”’.
Gaba daya aka sa dariya. Shima sai da ya murmusa yana girgiza kai. Ya ce, “Girki sai Arewa”’. Marwah ta soma taka yatsun kafarshi dake kusa da tata, tace, “Wash! Abban Daddy kafafuna sun fara kumbura yau ka manta baka yi messaging dinsu ba”.
Ai kuwa ya rude ya yi kasan tebur ya kama kafar, “Mu gani?”.
Kunya ta ishi Mami da Safah, sai kowa ya soma kokarin neman hanyar guduwa, sai kuma suka
jiyo kararrawar Idi. Sai Mami ta yi kofa, Safah kuma ta dauke Daddy suka yi sama.
Mami ta bude kofar tana cewa, “Ya aka yi ne Idi da sassafen nan?”
Ya ce, “Ki y. i hakuri Mami, wallahi bako ne na alfarma EFCC Lamido Taraba, wai ya zo wajen Dacta ne (yana nufin Safah)
Marwa ta yi tsalam ta mike, ta manta da nauyin jikinta, “Mami nake jin mutumin jiya ne, maza Idi ka bude masa guest room ina zuwa, bari in turo ta”.
Rawar jikinta bisa lamarin ya baiwa su Mami tausayi, hakan ne zai nuna maka matukar damuwarta kan ‘yar’ uwarta ta yi aure. Zahraddeen ya aje fork ya mike, “Bari in je in shigo da shi Mami”.
Ta ce, “Da ka kyauta”’.
Shahida kuwa kumburi ta hau yi don ba ta son kowa da Safah a duniya sai dan’ uwanta, to amma ba ta ga laifin kowa ba cikin lamarin da murnarsu da rawar jikin da suke a kan Lamidon.
Tunda ita ma ba za ta yarda Safah ta yi ta JIRAN TSAMMANIN WARABBUKA ba (in ji Mairon A Bari Ya Huce…….. )
Sanda Marwah ta shiga dakin tana bayan gida tana wanka, ta gane hakan ne ta karar ruwan da ta ji.
Kawai ta bude wardrobe din jikin bango da ke dakin, ta dauko wata tsaleliyar doguwar riga ruwan makuba da mayafinta kirar Oman, ta feshe ta da turaren Dabidoff (cool water) ta aje a bakin gado.