BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 2 by sumayyah Abdulkadir
Www.bankinhausanovels.com.ng
Don haka Lamido kan Mr. Deputy da Dr. Mohammed ya hada ya gwara da bango, sannan ya nuna musu kofa ya ce, “Habe your way here”. (Ku bi nan).
Deputy bai tsorata ba, haka Dr. Mohammed, sai ya rungume Lamido yana kuka sosai, goshinsa yah aye yayi suntum, ba tare kuma da ya damu da naushin da Lamido ke kai mishi ta ko ina ba.
Shi kuma likita yayi gefe bisa tebir yana ta rubuce-rubuce cikin file din shugaban EFCC Nasir Lamido Taraba.
Da lallashi da ban baki Deputy ya ciyo kansa ya yarda ya shiga mota suka maida shi gida, suka samu Amarya abin tausayi, ta ci kuka har ta gode Allah. Ko kayan barcin jikinta ba ta cire ba, tana zaune cikin kujerun falonta ta yi tagumi, fuskar nan data sha mari ta kumbura duk da ta mulketa da manthaleta.
Da saurinta ta mike ganin sun shigo da shi a rirrike. Yau ce rana ta farko da ta taba yin ido da ido da Deputy Sulaiman Yakasai, sai dai ta ji shi a bakin Lamido ko hirarsu in suna waya.
Ba wannan ne a gabanta ba, ta ce da Dr. Mohammed “Am sure Lamido is not well”. Ta gaya mishi abubuwan da ya yi a yau.
Allurar barci Dr. Mohammed yai mishi, bai kai minti biyar ba ya yi barci. Cikin dan lokaci manyan Psychiatrists sun cika gidan, har da jar fata.
A can bangaren Deputy da Mr. President tuni sun kammalawa Lamido da Safah shirin tafiya MIAMI. An dora wani a kan kujerarsa an kuma tafi
dauko Malam Abdulkarim daga Taraba.
Wanda ke can yana mamakin alert din da ya samu cikin wayarsa mai nuna cewa Lamido ya yi masa kyautar kudin da bai taba jin adadinsu a rayuwarsa ba.
Sai ga sako ya cimmasa Isaac ya zo, aka bude mishi dakin ganawa da bakin Malam. Can Malam ya je suka gaisa, ya gaya mishi an turo shi ne ya dauke shi. Bayan wannan bai ce da shi komai ba. A daren suka tashi zuwa Abuja.
Hankalin Malam Abdulkarim ya kai kololuwar tashi da ganin wai Lamidon shi ne riga daban wando daban, yana kallonshi cikin ido amma bai gaishe shi ba. Safah na gefe dukunkune cikin lafayya tana ta kuka mai ratsa zuciya.
Addu’a malam ya soma karantowa yana tofa mishi, sai ya soma kunkuni yana cewa, “Gaskiya ni ka daina tofa min miyau”.
A wannan dare da ya zowa Safah da sauyika da dama a rayuwarta, har garin Allah ya waye ba ta daina kuka ba, ba ta san tana son Lamido har haka ba sai yau da rayuwa ta juya masa baya.
An sauke Lamido daga kujerarsa an mayar da wani a gurbinsa. A cewarsu, dakatarwa ce ta rashin lafiya a bisa shaidar motsuwar kwakwalwa da likitocinsa suka bayar.
A washegari suka tashi zuwa MIAMI su hudu, Malam Abdulkarim, Safah da Lamido, sai Dr. Mohammed (personal Doctor ) dinsa da iyalinsa.
2k ok 3k
Ss MUTANEN PARIS un sauka a Paris karfe goma sha biyun dare, motar Hotel din da Zahraddeen ya yi booking tun kamin su taso tana tsimayen saukarsu, suna sauka chauffer din ya kwashesu. Babu komi cikin wannan zama na Zahraddeen da mai dakinsa sai so da kauna zallah. Hutu suke mai suna hutu da tsimayen isowar jaririnsu ko jaririyarsu. Sun manta da wata Anisa da al’amarinta wadda suke kallo a matsayin wata wadda ta yi musu karan tsaye a cikin rayuwarsu. Sai dai Marwah zuciyarta babu mugunta. Da ta samu nutsuwa ne ma ta soma tunanin hanyoyin da za tabi ta janyo hankalin Zahraddeen da su ya kaunaci amaryarsa, in dai ba zai kusance ta ba ita bata damu ba, ko duniyar ne ya tattara ya bata. A ranar da suka yi kwana uku ta kira Inna ta sanar da ita sun sauka lafiya, kuma tana samun kyakkyawar kulawa daga likitocin ta. Inna ta baiwa Daddy, ta sha surutu. Sai ta ce, “Inna Anisa ba ta kusa ne?” Inna ta yi shiru, domin dai ita tun jiya ba ta ga Anisa ba. Ta dauki makullan sassan Zahraddeen da suka ba ta ajiya ta ajiye a kan talabijin ta je ta zabi daki ta yi zaman ta. In ta ji yunwa can take dafa abin da take so ta ci don babu abinda babu a store da freezer. Jin Inna ta yi shiru sai ta ji gabanta ya fadi, ta cika da taraddadin kada dai wani abu ne ya samu Anisan
saboda son Zahraddeen.
Ta ce, “Inna wani abu ya faru da ita ne?”
Inna ta ce, “A’a, babu komai. Ta dai tattara ne ta koma sassanku. Kin santa ba kan gado ne da ita ba”.
Maimakon Marwah ta ji haushi sai abin ya yi bala’in bata dariya. Wannan tusa kai ga miji har ina?
Tana dariya ta cewa Inna, “A kyale ta Inna ta yi zamanta a tayamu addu’ar sauka lafiya, da na sauka zamu dawo”.
Inna ta ce, “Allah ya yi miki albarka Marwah, ya baki ‘ya’ ya masu kyakkyawar zuciya irin taki. Ya tallafi maraicin ki kamar yadda kika tayani tallafar nata maraicin. Shi kuma Allah ya ba shi ikon yin adalci a tsakaninku”.
Cike da jin dadin addu’ar Inna Binta ta ce, “Ameen Inna, Inna Allah Ya kara girma”’.
Ko kusa ba ta gayawa Zahraddeen ba, ta ci gaba da hidimomin gabanta.
A cikin tsarin da likitarta ta yi mata har da na yawan motsa jiki da yawan tafiyar kafa. Karfe hudu na yamma agogon su n a can ta idar da sallar la’asar kenan Zahradden ya fito cikin shiri na red trouser din jeens da farar shirt samfurin BBulgari.
Ta daga kai tana kallon shi yana tazar sumarshi kamar ta hadiye shi, “You are looking takeaway….”.
Ta fada cikin ranta, ba ta san cewa furucin ya subuto ya shiga kunnensa ba.
Dariya ya yi ya girgiza kai amma bai juyo ba,
kada ta fahimci ya ji ta. Ta ci gaba da cewa.
“To yanzu haka zai je yana romancing yarinyar nan, na shiga uku na lalace……. ” sai kuka. Zahraddeen ya ce, “Uh Allah!”
Sai ya hau cire kayan ya janyo dakakkiyar shadda har da babbar riga ya zurma. Ya kawo hula kube ya dora kamar angon da za’a daurawa aure. Ya kama hannunta ya mikar da ita tsaye. Ya rada mata cikin kunnuwanta
“Idan ta ganni a haka itama ta san ko kusa dani bata isa ta zo ba”.
Ba ta san sanda ta yi dariya ba, dariya sosai, ta dunkule hannu ta buga mai a kirji, shi kuma sai ya yi azamar rungumeta.
Wata irin soyayya suke gudanarwa a tsaye, ba tare da zungureren cikin ya hana komai ba. Ta yarda ta amince Zahraddeen nata ne ita kadai.
A cikin wannan halin dai da yake ciki ko cewa ta yi ya saki Anisa wallahi zai saki ko saki hamsin ne in akwai.
Kawai dai abin ya zo mishi a kaddara ne, wadda ba shi da ikon kauce mata.
Fitar da aka shirya yinta karfe hudu ba a yi ta ba sai bayan magariba. Yana rike da hannunta suke zagayawa wani dankareren shagon jarirai a tsakiyar birnin Suisra.
Dauki wannan jefa cikin kwando, dauki wancan haka suka yi ta yi. Kayan jarirai ne suka hada masu ban sha’awa, sannan ta dibarwa Daddy, da Anas da Malik ‘ya’yan Rabi’a kanwar Zahraddeen.
Basu koma masaukinsu ba sai karfe daya na dare.
Zahraddeen na bisa Ipad dinsa yana tura sakonni. Ni’imar birnin Suisra na ratsa kowacce gaba a jikinsu. Sai Marwah ta mike ta shige toilet da kyar don rage mara da wani mugun fitsari da ya kulle ta a marar.
Amma me? Da ta tsuguna ta yi fitsarin sai ga jini ya biyo baya hade da wani azababben ciwo mai gigitarwa.
Sai kuma ga kan kyakkyawar jaririya ya danno, ji kake suluf! “Yar baby a cikin masai.
Da karfinta ta ce, “Abban Daddy…….. ”
Ya sheko da gudu ya tsamo ‘yar dake ta wutsilwutsil…..cikin masai, sai kuma ta canyara kuka mai karfi.
Da jinin dake jikinta da cibi ya hada a kirjinsa ya rungume. Marwah da kanta ta yanke cibin ta goge mata jiki da olibe oil.
Cikin kayan da suka sayo ta ce ya je ya sa mata masu kauri ya lullube ta.
Fadi yake, “Kin san nakuda kike kika yi shiru? Saboda Allah da wani abu ya faru fa? Baki taba bani haushi irin yau ba. Wannan wane irin gangancine?”.
Ita dai ba ta kula shi ba ta ci gaba da kokarin gyara kanta. Ba ta fito ba sai da ta gasa kanta cikin ruwan zafi da tawul, ta tabbatar ba ta samu kari ba.
Ta sha magungunan da suka dace sannan suka wuce asibiti. Lokacin asubah ta yi. Rungume yake da babyn mai mugun kama da Rabi’a.
A asibitin ya yi sallah sannan suka wuce ofishin likita. Su ma fada suka yi ta yi. Ta ce su yi hakuri
ita ba ta ji wani ciwo ba sai a toilet.
Nan suka rike su suka ci gaba da basu kulawa. Basu sallamesu ba sai bayan sati daya.
A ranar ne kuma suka biyo jirgi zuwa Nigeria. A airport din Abuja suka sauka. Duk kokarinsu na samun layin Safah ko maigidanta hakan ya faskara.
Don haka kai tsaye Saifullahi abokin Zahraddeen da ya taho dasu daga filin jirgi ya wuce da su Asokoro, wajen Gumsu da Isaac dake bakin get, suka samu labarin cewa suna Amurka, Oga babu lafiya.
Har suka zo Kaduna tambayar junansu suke ko me ya faru da Lamido?
Inna na yankan ganyen shuwaka da za ta yi musu miya da ita sai jin shigowar mota ta yi gidansu.
Kamin ta gama sakar zucin waye ya zo ta jiyo jaririya tana ta tsala kuka, ga kamshin iyayenta ya fara simnana cikin hancinta.
Ai sakin wukar hannunta ta yi ta tsallake ganyen dake jibge a gabanta ta taresu ta karbi ‘yar tana hamdala ga Allah har da hawayenta.
Sai ga Daddy ya shigo da gare-garensa ya yi fututu da ka ganshi ka ga dan unguwar TukurTukur.
Ya watsar da gare-garen ya sheko da gudu, “Momi! Daddy!!””
Ya rungume uwar, sannan ya juya ya rungume uban. Shi kuma ya sure shi ba tare da ya damu da fututun kafarsa da laimar hancinsa ba ya soma
juyi da shi a tsakar gidan….. hugging him, kissing him…….. “TI cannot edpress how much I missed my darling Daddy……. 7,
Hayaniya ta hana Anisa barci, wacce ke narke cikin lallausar bargon bed room din Zahraddeen.. Ta leko ta taga, nan ta ga abin da ta gani, ta dafe kirji tana numfarfashi ta ce, “Wayyo madarar raina….. ya dawo”.
Da gudu ta dirgo daga gadon ta soma kokarin canza kaya, ta zare siket da riga cikin wadanda Nura ya dinka mata ne na atamfar super shudiya za ta saka leshi, sai ga Zahraddeen ya shigo. Salati ya yi sannan ya ja da baya, don shi bai san tana sassan ba, ya dai sha mamakin ganin kofofin a bude. Marwa ba ta gaya mishi hirarsu da Inna ba.
Yarinya kamar aljana, ya fusata matuka don ya ga karambanin nata ya yi yawa. Ya daka mata tsawar da ta gigita ta ya ce, “Wa ya baki makullina? Da izinin wa kika shigo mini daki?”
Jikinta ya hau mazari don ba ta taba ganinshi cikin matsanancin fushi irin wannan ba. Amma bakinta bai mutu ba, amsar da ta ba shi ta sanya jikinsa yin sanyi.
Idonta cike da kwalla ta ce, “ALLAH!” (wato Allah shi Ya ba ta izinin shigo masa daki a matsayinta na matarsa).
Ta juya ta soma hada tarkacenta tana kuka tana shessheka tana sharce majina da hawaye. Ta mayar da kayan jikinta da ta cire don ta yi masa kwalliya, ta hada sauran tana kullewa cikin zanin atamfarta. Ta bi ta gefensa bayan ta daura kullin
kayanta a kanta ta fita.
Ya zauna a gefen gado, ya kai hannuwansa biyu ya dafe kai, ya rasa abin da ke mishi dadi.
Daga nan inda yake ya jiyo ihunta a dakin Inna tana birgima a kasa wai Yaya Dini ya korota. Inna wadda ke kici-kicin daura garwar wankan jego ko juyowa ba ta yi ba balle ta rarrasheta, don ta san dama za ai haka tunda ita ba hankali ne da ita ba.
Nura da Marwah da dan yaro Daddy sune ‘yan lallshi.
Daddy ya ce, “Aunty Anisa ki daina kuka”.
Ta zazzaro masa ido ta ce, “Kai tafi can, ba saboda uwarka ake wulakanta ni ba?”
Nura ya yi baya yana ta dariya, ya janye Daddy suka yi waje yana cewa, “Zo muje my son rabu da ita, ba mu muka kar zomon ba balle a bamu ratayarsa. alhakin soyayyata ne yake dawainiya da ita’.
Wannan karon ne Inna ta yi magana, ta ce, “Nura!”
Ya dakata ba tare da ya juyo ba. Ta ce, “Kada in kara jin maganar nan a bakinka. Anisa matar aure ce karewa ma matar Yayanka, ka ji na gaya maka”’.
Ya sa kai ya fice yana ta dariya cikin ransa, shi dai ba zai daina son Anisa ba sai ranar da ya daina numfashi.
Don haka yake jin dadin dizgin da Zahraddeen ke mata.
Ita ma Marwan Inna tsawa ta yi mata, ta ce ta rabu da ita ta taho ta yi wanka. Inna ta salle
jikarta tsaf da sabulun salo da dama ta tanada don haihuwar.
Ta shafe ta da zaitun, ta sa mata farin kwalli har da fashin goshi (dan dirimi). Ta shiryata tsaf ta goye ta shiga harkokinta.
Nan da nan ta hada tuwon shinkafarta da miyar shuwaka, ta dauki kaji a frezer ta gasa daya, ta yi farfesu da daya, duk ta dire a gaban surukarta. Marwah cike da tausayin hidimar da dattijuwar take da iyalanta ta ce, “Sannu Inna, Inna Allah Ya bar mana ke”.
Har ranta ta ji dadin furucin Marwah, ta yi murmushi kawai.
Ta kara da cewa, “Inna nan dakinki ai zan zauna sai na yi arba’in”.
Inna ta ce, “Sai ka ce wata haihuwar fari? A’a, ki gama hutawa ki ci abinci ki tafi dakin ki zan ke shigowa ina ma baby wanka tunda kuna da ruwan zafi na lantarki. Dini ma zai fi son haka”.
Ta dan ji kunya, ta ce, “Haba Inna? Shi mai amarya? Ai zai fi son a barshi da amaryarshi”’. Inna ta yi dariya, domin dai ko gashin idonta ka kalla ba ma kwayar idanunta ba, sai ka ga yadda suke russunawa suna rankwafa kansu saboda KISHI.
Ta koma tana lallashin Anisa ta yi hakuri ta ci abinci, amma fur! Ta ki sai jiniya take yi wai ita ba Inna take aure ba, idan Zahraddeen ba zai barta a dakin aure ba, to za ta shiga duniya kowa ya huta tunda baya sonta.
Marwah na baiwa baby nono tana jiyo danger girl (sunan da ta sa mata). Ta yarda yarinyar da zuci
yarta daya son Zahraddeen take, kuma frank ce bata da munafunci, shi din ne dai bata sani ba ko yana sonta ko baya sonta???
Kasancewarsa jajirtaccen namiji da mace ba ta juya shi, ko ya zauna yana yin zancen wani. Bai taba yi mata zancen Anisa ba tunda suka tafi har suka dawo.
Sai ta ji wani bangare na zuciyarta ya soma tausayin Anisa. Kawai ba za ta iya juriyar Zahradden ya yi gamayyar jiki da ta zuciya da wata diya mace ba. Saboda tsoron halin maza, masu canzawa kamar wahainiya. Sabida dai kowacce mace komi muninta da baiwar da Allah Yayi mata, balle danyar kyakkyawar bafulatanar yarinya irin wannan.
Ba ta sani ba shi Zahraddeen ko da sadaka bai jin zai iya auratayya da Anisa, ko don tattalin martaba da manyantakarsa a idanun kanwar tasa. Shi kansa bai sani ba, yana sonta ko baya sonta? Da kyar Inna ta samu ta shawo kanta ta dawo daki, nan ta ga Maman Daddy na shayar da Baby. Ta yi turus! Don dai ita ba ta san anyi haihuwa ba. Sai kuma jikinta ya yi sanyi don ko Allah Ya raya bata ce ba.
Ta koma gefe ta zauna tana satar kallonsu, an ce “Naka sai naka”. Sai ta mika hannu wai a bata “yar.
Marwah ta yi murmushi ta cireta a nono ta bata. Ta kurawa jaririyar ido ta ce, “Inna kamar Rabi’a’”’.
Inna ta yi murmushi ta ce, “A’a, Anisa dai, musamman wannan bakin rigimar”’.
Ta yi dariya ta ce, “Kai Inna, wannan ai ta fini kyau, ‘yar ‘yan gayu, wadda haihuwarta ma ba za a yi ta a Nigeria ba sai cikin Turawa ‘yan’ uwansu”.
Marwah na ta dariya Inna ta ce, “Kema in kin yi hankali kin kwantar da hankalinki Allah kadai ya san iya adadin da zaku yi ta haifa kuna kawo mini ina goyawa kafin ta Allah ta kasance a gare ni. Koda duk shekara ne, domin na sadaukar da sauran rayuwa ta ga jikokina da zaman lafiyar ku. Amma idan kina ta yin wannan haukan da kike, yaushe mijin zai yi miki duban arziki?”
Ta ce, “Bari ke dai Inna, ai ni ko mayya ce daga yau na hakura da Yaya Dini. Mugun dan wulakanci ake gaya miki, baki ga tsawar da ya yi min ba kamar wata dabba, nima makaranta zan Kalmar da ta shiga kunnen Zahraddeen kenan a sanda ya sanyo kai cikin dakin. Ya ce daga bakin kofa.
“Da auren wa za ki koma makarantar? Ba dai da aurena ba, in je ki je ki lalace alhaki ya dawo kaina, tunda har za ki iya bude baki ki ce za ki yi zina idan miji bai tafi dake ba.
Kin dauka na manta ne? Babu inda za ki, kuma mijin ba zai dauke kin ba sai kin gaya min inda kika san meye amfanin miji ga mata, tunda ba karance-karance kike yi ba amma wai har ‘yan madigo kin sani, a gidan uban wa kika sani?”
Ya zazzaro mata manyan idanunsa masu maiko (oily eyes), fiye da tsawar baya, ta gigice ta kidime ta soma inda-inda.