BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 3 by sumayyah Abdulkadir
Kunya kamar ta kashe Inna da Marwah, basu yi aune ba sai gani su kai ya zare belt din jikinshi ya zuba mata a baya.
Ta bankare ta zabura ta yi kan Marwah, wata tsawar ya kara zubo mata, “Kika karya min Baby karyaki zan yi barambas, kuma wallahi sai kin gaya mini ko in kara zuba miki.
Ki yi ta yiwa mutane hauka, idan anyi magana kice ke marainiya ce, kowa ma marayan ne, kuma baya amfani da marayantakar wajen hauka da yiwa bayin Allah tijara. Za ki gaya min ko sai na kara zuba miki?”
Tana kuka sosai ta ce, “Wallahi ni ban taba yi ba”.
Yace, “To a ina kika sani?”
Ta ce, “Ai Rabi’a ta gaya mini mata da miji soyayya suke yi in aka yi musu aure”’.
Juyawa ya yi dariya kamar ta kashe shi. Inna ban da salati da sallallami babu abinda take yi. Marwah kuma ajiye Baby ta yi a cinyar Inna ta shiga bandakin Inna ta sunkuya ta yi dariyarta mai isarta.
Tana jiyo Inna na cewa, “Kai kuwa Dini baka da mutunci wallahi’.
Anisa ta ce, “Rabu da shi Inna, ko shine autan maza daga yau na hakura da shi. Ka sake ni in samu miji inyi aurena”’.
Inna ta bige mata baki, ta ce, “Kul! Kika kara furucin mijinki ya sake ki. Ba karamin batawa Ubangiji bane”.
Ya ce, “Rabu da ita Inna, sunan aurenmu auren zobe, ba saki ba yaji. Amma fa babu miji a
hannu. Ita ma Rabi’a za ta ci ubanta”’.
Kai yau Marwah ta ci dariya, duk sanda ta dago ido ta dubi Anisa wadda ke ta hidima da Baby sai dariya ta kama ta.
Ita kuwa Anisa sai tsuke baki take tana sakin tsaki, can kuma ta ce,
“Inna Yaya Dini dan rainin hankali ne. Ban da ya rainani shekarata shida a primary, shida a sakandire. Amma wai ban san me suke yi suke haifar “ya’ya ba.
Yo ko yaro dan shekara goma zai ba da wannan amsar balle ni mai sha shida”’.
Inna ta dunkule hannu ta sakar mata,
“Kin ci ubanki, na ce kin ci uwarki. Kika kara yi min zancen nan sai na fasa miki baki wallahi’’.
Da haka Inna ta samu ta kashe zancen, ita dai Marwah bata uffan, amma har garin Allah ya waye ba ta daina dariya ba. Yarinyar na kara shiga ranta.
Washegari karfe bakwai na safe, Inna na kicin Marwah na gasa jikinta a toilet, Anisa ce ke damawa Baby madara wadda ke ta tsala ihun neman uwarta. cikin feeder ya sanyo kai dakin Inna cikin shirin suit da sallama.
Tun kan ya karaso kamshin Dior Addict ya gayawa mutanen dakin shigowarsa. Ga mamakinsa ba ta amsa sallamar shi ba, kuma ba ta juyo ba balle ta kalle shi sai girgiza fidarta take.
Mamaki ya kama shi, ranshi ya dan tabu. Ya ce,
“Ke kina jin mutane suna sallama kika yi kunnen uwar shegu dasu?”
Ta juyo a slow ta yi masa kallon sama da kasa, sannan ta kyabe baki ta juya masa keya har da turo dankwali gaba.
Zahraddeen sai ya sandare a tsaye, daidai sanda Inna ta shigo tana cewa, “Bani hanya in wuce ka tokare min a bakin kofa”.
Ya ba ta hanya ta wuce, amma hankalinshi na kan Anisa wadda ta sauko Baby tasa mata feeder a baki, nan da nan ta kama ta yi shiru tana ajiyar zuciya.
An ce mai Da wawa……sai ya ce, “Inna ina Maman Daddy ne? Lagos zan wuce yanzun nan sai sun kwana biyu zan dawo”’.
Ya fadi yana kallon Anisa wadda ke ta baiwa Baby madara ba ta ko kara bi ta kanshi ba. Shi kuma so yake su hada ido ya kara gasgata wannan kallon ko in kula din da ya gani cikin kwayar idanunta, amma ta ki dagowa.
Sai dai fa da za ka tona zuciyar Anisa a wannan lokacin, ta fi duhun dare duhu, da jin cewa mijinta Dini zai tafi, wanda take gani ta ji dadi, ya yi mata tsawa ta yi kukan dadi, ba kukan bakin ciki ba.
Kawai sai ga hawaye suna biyo fararen kuncinta suna sauka a fuskar Baby. Inna ba ta gani ba, amma shi ya gani.
Sai ya ta’allaka zubar hawayen da tozarcin da yai mata jiya a gaban kishiyarta. Sai ya ji ransa babu dadi, tunda ga shi ita hakan bai sa ta yi fushi da jininsa ba (Baby), ga shi nan tana ta rainonta.
Marwah ta fito daure da tawul mai fadi, ta kuma rufo wani a kanta, gashin kanta na digar da ruwa tana tsaneshi da wani karamin tawul din dake hannunta.
Suka yi magana cikin harshen Turanci ba tare da sun karbi ‘yar daga hannun Anisa ba, suka shiga uwar dakin Inna inda ta kwana.
Doguwar riga ta fara sakawa sannan ta janyo manyan jakunkunansu ta zuge ta soma ware mishi kayan da zai tafi dasu tana shiryawa a jakar da babu komai.
Zahraddeen ya matso jikinta sosai cikin murya mai rauni ya ce,
“Yaushe zan zo in ta fi daku?”
Ta ce, “Ka yi hakuri Abban Daddy mu yi ko da wata guda ne Baby ta yi kwari”.
Ya ce, “Tab! Kema wasa kike, sai kun ganni kawai”’.
Ya kwantar da kai a bayanta, “Marwah kiss me plzzz….”
Ai kuwa ta soma manna mishi deep-kisses a goshi, idanu da karan hancin sa. Ta dire a bakinsa. Anan ne Zahraddeen din ya kankameta. Daidai lokacin da Anisa ta sawo kai rungume da Baby da ta yi barci don ta kwantar da ita cikin net dinta.
Zahraddeen ya tafi da yawa fiye da Maman Daddyn, wadda ita ce ke aikin ladan. Don haka bai san da shigowar Anisa ba, don a lokacin ma kalaman da yake furtawa matarsa cikin turanci bai san su ba.
Saura kadan ta saki jaririyar a kasa, ta juya da
sauri cikin gigicewa ta dangwarawa Inna jaririyar a bayanta.
Inna dake durkushe tana hadawa Daddy tapioca ta yi maza ta rike jaririyar saura kadan ta fado daga bayanta.
Ta ce, “ subhanallahi. Ke kam ban san yaushe za ki yi hankali ba”.
Ta so ta baiwa Inna amsa ko don Zahraddeen ya jiyo, sai kuma ta fasa, a sabili da sabon kudurinta na yakice Zahraddeen daga zuciyarta ko tana so ko ba ta so.
Don haka ba ta ga me ya yi mata zafi da rayuwarshi ba. Sai ta shige kicin don ta yi kalaci, ta debi soyayyar Agada (plantain) mai yawa, da soyayyen dankalin Turawa, da kunun alkama, ta ja kujera ta zauna ta sa musu ido.
Ga mamakinta duk da yunwar da take masifar ji ta kasa cin ko loma daya. Sai ta sa kanta cikin cinyoyinta ta fashe da kuka
Karfe takwas da rabi Zahraddeen ya yi musu sallama zai wuce, bayan ya barwa Inna komai da za a nema.
Tuni ya yiwa jaririyarshi huduba da sunan Inna. Inna har kukan dadi ta yi tana shi masa albarka. Daddy na ta kuka sai ya bishi. Yau ma kamar kullum kalaman nan ya gaya masa, wadanda inda sabo to yaron ya saba jinsu daga bakin mahaifin nasa.
“I’m bery sorry my darling Daddy, I’ll be back to you soon…… Da kyar Inna ta rike shi yana kuka yana birgima kamar ransa zai fita.
Zahraddeen abin so ne, ba ga ‘yammata kadai ba, har ma ga matan aure marasa kamun kai. Ga iyalinsa abin so ne abin kwatance.
A wurin matarsa abin tinkaho ne da za ta iya lika shi a goshi da ana likawa, ta shiga ko’ina tayi alfahari da zamantowarshi miji a gare ta. Ba wai don kyawun sura kadai ba, ‘a’a, sadauki ne a nuna so da kauna ga iyalinsa. Jarumi a fannin SOYAY YAH da idan yana son mace, hatta farcen jikinta sai ya shaida. Ta fannin kulawa a garesu da bukatun rayuwa kuwa, Marwah mantawa take ita ‘yar Aliko ce, domin a daidai wannan lokacin da Zahraddeen ya zamo wani kusa a cibiyar kasuwancin kamfanonin saka sittiru na Geneba, baya ga albashin da yake shiga account dinsa na kamfanonin DanKasa da yake jagoranta. Idan bai fita kudi ba, to bazata fishi ba. Runtse ido da yakeyi a kan mata kala-kala ma kadai wani babban jarumtaka ne da ba kowanne namiji dake mataki irin nasa ne zai iya yi ba. Wannan tunanin da Marwah ta yi sai ya fara kawo sauyi cikin ranta a kan muguwar akidar da zuciyarta ta dora ta a kai, a yau ta tabbatar ya zama mugunta ga ANISA, wadda ba ta ci mata ba, ba ta sha mata ba. Da shikansa Zahraddeenin. Sannan ba ta yi amfani da kalmar nan da ake fadi ba, wato ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne. Da hadisin da ya ce ‘imanin dayanku baya cika……….. Ta zama azzaluma, ta zamo muguwa ga ‘yar’ uwarta Musulma. Ta so kanta da yawa, KISHI ba hauka bane. Don
—_
ko Zahraddeen bai furta yana son Anisa ba, a yau ta karanto cikin ido da gangar jikinsa ta yi masa kadan (ba ta isarsa), balle kuma cikin wannan halin na biki da ta ke ciki.
Ta sani Zahraddeen zai iya hakuri da komai, amma ban da wannan. Gabanta ya ci gaba da faduwa da ta jiyo shesshekar kukan Anisa.
A lokacin yana kokarin saka takalmanshi rufaffu bakake da ya tube a kofar dakin Inna, zai wuce ta kicin sai ya tsaya a kofar kicin din jikinsa a bala’in sanyaye.
“Kuka Anisa? Me aka yi miki?”
Dagowa ta yi ta zuba mai harara, ta murguda baki ta ce, “Ina ruwanka da kukana? Allah ka dauki raina in bi Badijo in huta”.
Ta rarumo faranti ta maka masa a goshi ya kare, ta dauko katon kwanon samira ta daidaici kafadarsa ta maka masa. Ta ci gaba da rarumar duk abin da ya zo hannunta, muciya, bulugari, ludayi tana kwala masa yana tarewa yana fadin “Ke Anisa? Baki da hankali ne?”
Ta ce, “Bani da shi, sanda ake rabon shi ubana bai kaini ba”.
Kafin ya yi aune hannunta ya kai kan zaftareriyar wukar Inna, ta yo kansa da wukar ta ce, “Ko ka tafi ka barni ko in caka maka, in yaso nima a kashe ni”.
Sai ya shigo kicin din gaba daya, cikin zafin nama ya rike ta yana kokarin kwace wukar ta ki saki, idan kuma ya takura, to la-shakka shi ko ita, wani ya zaftare hannunsa.
Sai ya rungumeta da karfin gaske ya cika hannun
ya ce,
“To gani kashe nin”.
Sai ta saki wukar tana kuka, a lokaci guda tana kokarin kwatar kanta daga tsattsauran rikon da ya yi mata.
Dukkansu haki suke kamar wadanda suka yi gudun mita goma. Juyowar nan da za suyi suka yi ido shida da Inna, Marwah, da Nura.
Marwah ta mika mata wata karamar troller da Abaya da mayafinta kirar Oman ta ce, “Ungo sanya ku tafi’”.
A razane duka suka dube ta. Sai ta yi murmushi wanda da gani ka san na karfin hali ne.
Ta ce, “Ku tafi don Allah kada ku yi missing ebening flight it is past eleben fah”.
Inna ta ce, “Sannu ‘yar albarka, ku fito min daga kicin kada ku yi min kisan kai a gida”.
Marwah juyawa ta yi ta koma daki. Ya yi tsaki zai wuce ya ce da Inna, “Da wannan mahaukaciyar? Allah Ya tsareni”.
Inna ta ce, “Allah yasa daga turu ta fito wallahi bar min gida za ku yi, ba za ku yi min kisa a gida ba”.
Sai ya sa kai kawai ya yi waje jin Inna na rantsuwa. Nura na cikin motar yana jiransa, don shi zai kai shi filin jirgi.
Gaban motar ya bude ya zauna dafe da kansa dake sarawa tamkar ya tsage gida biyu. Inna ta sako Anisa a gaba da jakar da Marwah ta hada mata ta bude mata kofar baya ta shiga.
Ta ce, “Allah ya kiyaye hanya”.
Nura ya ja mota suka fita.
Inna ta koma cikin gida tana ce da Marwah, “Allah Ya tallafi zuri’arku, ya kyautata gabanki da bayanki, ya kara kaunarki a zuciyar mijinki.
Kin yi min abin da na kasa saboda kunyar kwayar idanunki, sai ki yi jegon ki cikin salama suje can su karata. Muma mu zauna bakinmu alaikum”’. Marwah dai murmushin karfin hali take, don haka Inna na ba da baya ta soma share hawaye.
Amma sai ta kawar da komai da ta yi wani tunani guda daya, wato dauki (taimako) ne Allah Ya kawo mata.
Da Zahraddeen ya dinga mu’amala da matan banza gara su hada kai ita da Anisa su tallafeshi, su taimaki juna. Ta sani tanada matsala a fannin auratayya wadda ta san ko Zahraddeeen bai fada ba tanada raki kuma tanada karancin sha’awa, ita dai barta a romancing a yi ta romancing ko za’a kwana a hakan bazata gaji ba, yayinda Zahraddeen din a lokuta da yawa sai ya hada da magiya, lallashi, wani sa’in har da hawaye, sannan take kai zuciya nesa tayi don samun rahmar Allah amma physical need dinta is bery low.
To dama haka ne, duk dan adam ai tara ne bai cika goma ba. Sai kuma in akan-karan kanta ne abin ya zo mata, (wanda ana dadewa hakan bai faru ba), to fa duk inda yake cikin duniyar nan zata bishi ko ta nemo shi koda Geneba ne.
Ko babu komai tana da guarantee a kan cewa yarinyar ba za ta cuce ta ba, ba za ta cuci Zahraddeen ba. Tsakaninta da Allah take son shi, gata ‘yar uwarsa da jininsu ke cakude da na juna.
Cikin kwayar idon Anisa kadai ta hango kaunar jaririyarta. Kauna ta jinin ‘yan uwantaka irin wadda Allah ke sanyawa a zukatan bayinSa da suke jini daya, Me za ta yiwa Inna a duniya ta biyata abinda take mata? Banda ta kaunaci nata da zuciya daya? Ta tayata su sauke alkawari da rikon amanar da Allah Ya dora musu.
Mene ne duniya? Guda nawa take? Balle jin dadin dake cikinta? Sama da wannan ma ta san ba wani abu Anisa za ta gutsira a jikin Zahraddeen ba. Duk wata kuruciyarsa ta kwashe ta, duk wata soyayyar da zai nunawa wata diya mace, wallahi ba za ta kama farcen wadda yake yi mata ko ya yi mata ba.
Sai ta fara neman abin da zai kau da hankalinta daga kansu. Ta soma neman ‘yar’uwarta a waya don ta sanar da ita ta sauka lafiya, amma har yau ta kasa kama layinta balle na Lamido.
Sai ta kira Mami da Shahidah, Mami ta ce, “Inna ta gaya mata haihuwar ai, yanzu haka suna kan hanyar tahowa Zaria, har sun iso Jaji’.
Ta gayawa Inna, tuni Inna abin nema ya samu wato hidima da jama’a. Kafin su iso sai ga Rabi’a ta iso da yaranta da mijinta da ya kawo su.
Sai dai shi bai dade ba bayan ya ga jaririya ya yiwa Inna barka sai ya tafi, da alkawarin dawowa daukar su bayan suna.
Rabi’a ita ta kamawa Inna, nan da nan suka kammala abinci na alfarma da Inna ta shirya musamman don bakin nasu.
Sanda su Mami suka iso azahar ta wuce, anan ne Mami ke gaya mata su Safah suna Miami Lamido
—_=
babu lafiya.
Kusan Marwah har ta fi Safah damuwa da ciwon Lamidon. Wuni ta yi abun na damun ta a zuci. Tana son ta ji lafiyar tasa, Safah ba ta hawa (any social network) kuma ba ta da lambarsu ta can Miami.
Don haka ta ci gaba da tsimayen kiran Safah, ba ta san ba ta da kwanciyar hankalin da za ta tuna da wani abu a duniya wai shi waya ba.
Kwanan su Mami biyu suka koma Kaduna, yarinya ta ci sunan Inna Fatima Binta. Hajiya Maama kullum cikin ciwon kafa take, shekaru sun tura. Kullum karfinta kara karewa yake. Don haka ta daina fita. Shekaru da girma na aiki a jikinta matuka, domin shekarunta tamanin da uku a duniya.
Don tana cikin kyakkyawar rayuwa ne ya sanya jikinta bai nuna hakan. Ga karfin imani da kula da addini wadanda duk suna kara lafiya.
Haka suka ci gaba da jegonsu cikin kwanciyar hankali, kullum sai Zahraddeen ya kirasu ya ji lafiyarsu. Har kukan Fati sai an sa masa ya ji,
sannan ne hankalinsa zai kwanta. ek kK
Zan so hasko muku rayuwar Zahraddeen da kanwarsa kuma amaryarsa a hanyar tafiya Lagos . Da suka bar Zaria ba Abuja ya nufa ba, dama Lagos zai je akan harkokin DAN-KASA HOLDINGS na man fetur da suke son kara bunkasawa a birnin Ikko ya zamana zai dan jima acan. Don haka jirgi suka hau daga Kaduna.
Karon Anisa nafarko kenan da hawa jirgin sama a rayuwarta, don haka da jirgin ya soma ruguginsa, ba ta san sanda ta kankame Zahraddeen ba. Zahraddeen bai yi magana ba, sai da jirgin ya daidaita a cikin gajimare, serbice suka soma turo troller din abinci sai ya ce,
“Dagani haka zan ci abinci, Bakauyar banza!”
A ranta ta ce, “Eh, na ji dai”.
A fili kuma ta zumbura baki ta juya mai keya.
Bai kara kallonta ba sai ya ji tana yiwa daya daga cikin masu rabon abincin masifa wai don me za ta ba ta naman Alade (Pig). Ita Musulma ce rainon Musulmi. Matar ko Hausa ba ta ji amma ta lura ta bata mata rai ne. Sai ta hau sorry-sorry, sannan ta bata menu don ta zabi wanda take son ci ta kawo mata. Don ta fahimci korafinta kenan. Kamar gaske sai ta karba tana dubawa, sai ta nuna mata (pork-tendertoin), da rawar jiki matar ta juya da naman kaza nikakke (grilled chicken nugget) da ta ki ci, ta kawo mata farfesun Alade. Domin a first class suke komai suke so za a basu. Zahraddeen dai yana gefe bai yi magana ba, amma dariya da haushi suna nema su kashe shi. Ya ga da gaske cin aladen nan za ta yi kuma alhaki zai hau kansa. Sai ya karbi takardar ya sunkuyar da kai (studying the menu). Ya ce ta koma da wannan ta kawo mata (roasted chicken) gasassar kaza.
Har suka sauka a filin jirgin saman Murtala Mohammed bai kara kula ta ba.
Direba daga office dinsu na Lagos na jiransa, ya kwashe su zuwa inda aka tanadar masu masauki