BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 4 by sumayyah Abdulkadir

 BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 4 by sumayyah Abdulkadir 

Www.bankinhausanovels.com.ng 

tun kafin zuwan nasu. 

Wanka ya fara yi sannan sallah, ya yi shiri cikin kananan kaya ya fice. Bayan ya yi umarni ga yaronshi Stebe ya yi girki mai kyau ya bata. Yadda ya fita ya barta haka ya dawo ya same ta, ko kayan jikinta bata cire ba ba’a maganar wanka, tana zaune cikin 3 seater tana barci. Ga jakar kayan da Marwah ta bata a gefe ko zugeta ba ta yi ba, balle ta ga mene ne a ciki, ga abincin da Stebe ya jera a dining da ya duba sai ya ga ko budewa bata yi ba. 

Tausayi ya kama shi, don ya san bai bata daki ba kafin ya fita. Ya zube shirgin da ya shigo dasu daga Shoprite ya soma tashinta. 

“Anisa….ke Anisa, tashi mana. Ya kike barci a zaune sai wuyanki ya sankare?” 

Ta yi mika sosai bayan ta bankaro mai kirji ta yi hamma, sannan ta yi farr! Da lumsassun idanunta a kansa. Ya yi hanzarin kau da kai ya koma fada tamkar wani laifi ta yi masa. 

“Don me za ki hau barci a kujera ko abinci baki ci ba, balle sallah da wanka. To ba zan dauki kazanta ba. Tashi maza ki je ki wanka ki brush ki fesa turare sannan ki yi ta barcin, kin ji na gaya miki’. 

Ya cilla mata mukullin daya daga cikin three bed rooms din flat dinsa. Ta dauki jakar da makullin ta doshi daya daga cikin dakunan da ba ta san kowanne ne mai makullin ba. 

Ta yi ta gwadawa har daki daya ya bude, a ranta tana cewa, 

“Mafadacin banza wanda in bai likawa mutum 

laifin da ba nashi ba baya jin dadi. 

Ko yaushe ya bani mukullin dakin oho! Da zai hau ni da fada. Ai ko wannan galleliyar matar tasa ba za ta gaya min yadda ake wanka ba, mu da muka taso da yin wanka a kogi ma ba a famfo ba”. 

Zahraddeen na jin kunkuninta sai ya yi maza ya shige dakinsa kada ta ga dariyarsa. Yarinyar nan ko bai so ta don komai ba, personality dinta da gabuntarta na sa shi dariya da nishadi. 

Tunda ta shiga dakin ba ta fito ba tana can tana murna da abubuwan da Marwah ta hada mata cikin jaka da ba ta taba ganin irinsu a rayuwarta ba. 

Ta saka wannan ta kalli kanta a madubin dogon yaro ta cire ta saka wannan. Wasu tsala-tsalan rigunan barci ne (nighties) design daban-daban, kala daban-daban. 

Turarukan cool water (Dabidoff) set daya, brush, maclean din signal, mouth wash da fresh mint kala-kala. 

Ga kuma dinkakkun kaya marasa nauyi, atamfa, material da swiss lace uku. Nata ne ta dinka musamman don ta yi fitar suna dasu ba ta taba sawa ba, ga saitin kayan make up da mayukan pond’s flawless masu kara kyau da taushin fata. Ga Anisa da son kwalliya, don haka a tsayin daren baki dayansa kwalliya take tana sakewa. Abincin da Stebe yake hadawa yana ajewa haka yake kwasar kayansa yadda ya barsu. Iyakaci in ta ji kishi ta bude dan karamin bed side fridge din dake gefen gadon da ya zam nata ta kwankwadi 

jusi da fresh milk ba abinda ya dame ta. 

A haka suka kwashe sati guda, Anisa ba ta da aiki sai wanka akai-akai kamar agwagwa. Ta yi kwalliyarta da kayan kishiya (kamar yadda take kiransu), ta yi feshe-feshenta ba kuma don Zahraddeen ba, ita kawai nature dinta ne yin kwalliya, ba kuma don Zahraddeen ya yaba ba. 

Ta san ba shi da lokacinta, saboda in ya fita tun takwas na safe ba ta kara ganin kalarsa sai dai ta ji shigowar motar daga dakinta wajejen goman dare. 

Wani lokacin ma sai ta yi barci. Shi ko kalaci a ofis yake yin abinsa. Sai dai yana tabbatar da lafiyar ta, cikin dare yana lekata ya ga ta yi barci tana shan A.C, idan zai tafi ofis ma yana kula da tashin ta lafiya. 

Sannan ya umarci Stebe da ya dinga girka mata abinci mai kyau kullum duk ranar da ba ta ci ba ya gaya masa. 

Ta hakan ne Stebe ya gane Anisa ba ta da cin abinci, sai shaye-shayen jusis da madara da su Hollandia. Sai yasa Stebe yake yawan cika firji dasu, kuma ya ce ya rage yawan abincin da yake dafawa a daina zubar da abinci., tun lokacin da ya gaya masa abin da take tsakura baya fin loma biyar. 

Kan ka ce meye wannan, cikin watanni biyu kacal sai ga Anisa jiki ya canza completely, farinta da taushin fatarta sun fito. Jikinta ya zama smooth kamar ‘yan matan dake rayuwa a Switzerland. Budurcinta ya kai ya kawo har ta tumbatsa, dukiyar Fulani kamar sa tsaga rigarta. 

Ba ta yi kiba ba, sai gogewa da ta yi, ta zama looking takeaway (in ji Marwah), wato kamar a sace ta a gudu. 

Abu daya ne Anisa take da nakasu a kansa, wato gyaran dogon gashinta. Ba ta iya ba, ba ta san ya ake yi ba, kuma ya fi karfinta. 

Ba ta wanke shi balle (steaming ko relading). Sai dai kawai ta tattara ta kulle ko da danshi ba ruwanta, gashin ya yi ta rima. 

Rannan Stebe na kicin ta shiga fuska murtuke (kamar yadda take mai kullum), amma na yau ya fi na kullum. Stebe bai jin Hausa, ta tsaya a kofa ta ce, “Kai Stebe!” Ya juyo da sauri “Yah Madam!” Ya kame a tsaye. Ta ce, “Meye fassarar sunanka?”’ Ya ce, “I donno Madam”. Ta ce, “Kai dan wane Kabila ne? Yoruba, kanuri, Fulfulde, Igbo, Itsekiri, Ibra ko Ibibio?” A nan ne ya dan fahimce ta, ya ce, “Ibibio”. Ta ce, “Allahnka nawa?” Sai ya dauka cewa shekarunsa ta tambaya. Ya ce “Twenty fibe’’. Sai ta nuna masa hanyar kofa ta ce, “Jeka, da; yau kada in kara kanin kafarka cikin gidana, zan zauna da mai Allah ashirin da biyar ba’. Stebe bai ji ta ba, amma ya fahimci korarsa ta Nan ya kai gwiwoyinsa kasa yana afi yana hu yana magiya ta barshi da hanyar sa abincinsa. Yana yiwa Oga biyayya baya 

masa rai, ita ma baya bata mata. Idan laifi ya yi mata ta gaya masa zai gyara. 

Ta harde kafa a jikin cabinet tana taunar cingum kas-kas-kas bakinnan ya sha jambaki jawur radau dashi, tana cewa, 

“Wallahi sai ka tafi, in kuma ka ki in ce da Yaya Dini ka bugeni a duwawu”’. 

Daidai lokacin da Zahraddeen ya sawo kai ya jiyo muryar Stebe a kicin kamar yana kuka. Don haka da sauri yayo kicin din, kalamanta na karshe a kunnensa. 

Sai jin muryarsa ta yi cikin kunnuwanta, “Bari ni in fara bugun mazaunan naki kafin shi ya buga”’. Ya kwanto belt dinsa ya zuba mata, ta yi tsalle ta yi gefe ta soma kuka. Ya dubi Stebe da har lokacin yana durkushe abin tausayi, domin dai shi madam Babba ba ta taba yi mishi haka ba in ta zo Lagos, ya lura kuma ta fi hankali da imani. 

Ya ce, “Jeka sai na neme ka’. Da sauri ya mike yana ta godiya ya fita. 

Ya daga belt din ya kara zuba mata a baya, ta rike wajen tana kuka ta ce, “da sannu Allah Zai saka mini”. 

Duk sanda aka ambaci “ALLAH” to Zahraddeen ba shi da sauran kuzari. Sai ya juya ya fita yana dana sanin abinda ya yi, wato dukanta a gaban yaronsa, a matsayinta na matar aure a gare shi. 

Ta gabansa ta wuce zuwa dakinta tana ta kuka, sai ya mike ya bita, karo na farko tun zuwansu Lagos da ya shiga dakin. 

Wani irin sassanyan kamshi na sprays da turarukan da take amfani dasu ba control da rabar 

iya kwandishan mai karfi shi ya fara ratsa jikinsa da hancinsa. Turare yana tada sha’awa, kuma yana kara dankon kauna. 

Tana zaune a bakin gadonta fuskarta cikin tafukanta tana kuka, wata irin doguwar rigar barci ce a jikinta ruwan hoda, wadda ba ta boye komai na halittarta ba. 

Ya tuna shi da kansa ya zabowa Marwah rigar a wani boutikue a Paris, bata taba sawa ba. Sai ya ji idanunsa a yau na kunyar sake hada ido da MARWAH, a lokacin da ya janyo Anisa jikinsa yana lallashinta. 

Gaba daya ya susuce a lokacin da sanyin fatar jikinta ya shafi nasa. Hannunsa ya kai cikin yatsun hannunta mai laushi kamar auduga. Sai ga Yayan dake masifa da rashin mutunci ya koma sambatu. Wannan wace irin yarinya ce kamar ba’indiya? Ba ta da maraba da wata jarumar India da ya taba gani a Cardiff (Amisha Patel). Al’amuran da suka biyo baya ba za su fadu ba. Abinda ya sani shine, shi ya raba Anisa da budurcinta, ta yin amfani da karfin da Allah ya hore masa na namiji (by force) ba tareda tausayawa ko concern ba. 

Sai da ya nutsu ya dawo hayyacinsa ya fahimci aika-aikar da ya yi, kwana suka yi basu yi barci ba tana ta kuka banda Allah Ya isa ba abinda take masa duka ya karba yana ta lallashin ta da dukkan iyawarsa. . 

A kwanakin da suka biyo baya, Zahraddeen 

lallaba Anisa yake yi tana kara botsarewa, tunda ta fahimci ashe tana da amfani a bayan idon matarsa. 

Ita da Rabi’a ta kwadaitar da ita al’amarin ashe ba haka yake ba. Ta ki yarda sam ko kusa da ita ya zo. Ta tubure ita lallai ya maidata wajen Inna. Amma da ya sayo tsaleliyar Blackberry ya kira mata Innar ta ji muryarta ya kuma danka mata sai ta bada kai bori ya hau, ya ci gaba da kwasar ni’1mar da Allah Ya bashi, ba tare da ya yi zato ba. Ai fa tunda Anisa ta yi waya aka manta da zancen komawa gidan Inna, shi ya zauna ya hada mata ya nuna mata komai yadda za ta fahimta. 

Bata fahimci komai ba ban da yadda za a danna kira (green botton) bayan an saka lamba. 

Nura aka fara kira da ta roki Zahraddeen ya ba ta lambarsa. 

Sanda ya dauki wayar bai san waye ba, sai ji ya yi ta ce, “Kai da Allah bakauye how far?” 

Nura ya tintsire da dariya ya ce, “Fine my wife, ya masifaffen mijinki?” 

Anisa da baki babu linzami ta ce, 

“Kai da Allah ya daina masifa ya zama dan kirki, har Ice-cream yake sayo min”. 

Ya ce, “Banza, don yana sayo miki Ice-cream shi kenan sai ki yi zaton yana sonki?” 

Ta ce, “Kai da Allah yanzu fa ko magana zai min sai ya make murya kada na ji haushi nace ya maido ni wajen In…….. ” 

Fizge wayar ta ji anyi, sannan ya bita da hauri da kafa da bakin cober dinsa da bai cire ba, ta tuntsura cikin kujera babu shiri ta zuba ihu sa

boda azabar da ta ji a kwaurin ta. 

Ta ce, “Wayyo Allah…… , wayyo Bodijo”’. 

Ya ce, “Ke wace irin dabba ce a cikin dabbobi? Kike min terere a idon masu ganin kima ta da girma na, saboda na dubi Allah na kula ki ina sauke hakkin ki dake kaina? 

Uban wa ya ce miki son ki nake? Ni na gaya miki? Waya na kwace ta daga yau tunda baki da hankali. Tattara kayan ki gobe in san yadda zan yi dake ba zan iya zama da mahaukaciya ba”. Kuka take yi sosai tana rike da kwaurinta. Jin abin da ya yanke a kanta ya sanya ba ta san lokacin da ta ce cikin kuka. 

‘Don Allah don Annabi Yaya Dini ka yi hakuri ka bani wayar na daina ba zan kara ba”. 

Bai tanka mata ba da sassarfa ya bar wajen kamar zai hadiyi zuciya don takaici. Haka tai ta binshi da ban hakuri kwana da kwanaki duk ta rame ta yi muzu-muzu don babu kwalliyar da aka saba, ta manta yadda ake yin ta. Ba don komi ba sai don tashin hankalin fushin Zahraddeen, har cewa take ita in ba zai ba ta wayar ba ma to ya yi hakuri ya daina fushi da ita, kaurace mata din da ya yi na tsayin sati guda ya fi komai tashin hankali a gare ta. 

Ya ce, fushi ba zai daina ba sai ranar da ta zama me hankali. 

“Mene ne hankali?” Anisa ta tambayi kanta a wani maraice. Tana mai bubbuga kanta a jikin bango da karfi. Ta ci kuka har ta gode Allah akan son sanin me kalmar HANKALIN nan da kowa 

yake yi mata gorinsa ke nufi. Musamman mijin aurenta da tafi so kan komai da kowa a rayuwa. 

A take kwakwalwarta ta bata amsa daidai tunaninta. 

“Hankali shine nutsuwa, kame kai, da baki daga fadar abinda bai da muhimmanci, da yawan surutu marasa ma’ana. Rashin sirri rashin hankali ne, balle sirrin mij1’’. 

Ni Anisa na yi alkawari daga yau na yi hankali, na daina wauta na daina magana mara amfani. 

Sai ta rage baiwa Zahradden din hakuri yana yankwanata. Ta fita sabgarsa ta ci gaba da rayuwarta kamar yadda ta faro tun zuwan su, wato daga daki sai daki, kwalliya an daina, feleke da comedy duk an daina. 

Shi kansa Zahraddeen ya ga sauyi, sauyi kuwa mai ban mamaki. Shi da kansa ya koma yana ‘yar murya don ya yarda ta yi hankalin. Miji da mata sai Allah! A karshen watan suka tattara suka taho 

gida Zaria. ROKK 

A MIAMI B 

abu irin kokarin da Dr. Al’ameen bai yi ba ta hanyar addu’a da kwarewarsa a fannin nasa a kan Lamido, sai da ta kai ta kawo Al’ameen ko abinci baya ci sosai saboda kula da Lamido. 

Bai taba samun (complicated case) irin na Lamido ba. Idan an ga sauki kwana biyu, ba a kuma yin wasu biyun bai karkace ba. Magungunan da ya dora shi a kai ba a samun su ko a Miami sai a makotansu South Florida. 

“Yan rakiyar, ko in ce ‘yan jinyar suna a hotel din Mandarin Oriental Miami, don basu bukatar mai zaman jinya. Sai dai su je lokaci-lokaci su duba jikin nasa. 

Magunguna masu karfi da allurai suka soma aiki jikin Lamido, ya soma shiga cikin hayyacinsa. Kauna mai ban mamaki ta soma shiga tsakanin Dr. Al’ameen da patient dinsa Lamido. Haka matarsa Ihsan da kusan kullum tana biye da shi suka saba da Safah. Daga karshe ma gidansu ta koma da zama ta bar su Malam a Hotel din. 

Dr. Mohammed ya rigasu tahowa gida, Dr. Al’ameen ya dora alhakin shan maganin Nasir a kanta, da gargadi mai yawa na shan magani a kan lokaci. 

A karshen satin suka taho gida Nigeria, kai tsaye Malam ya ce su wuce Taraba. 

Lamido tsaf dinsa yake kamar ba shi ba, ya zuba ido don ganin da wane ido Danejo za ta dube shi? Bai san cewa ita ba ta san ma ta yi wani laifi ba, balle ta san da rashin lafiyarshi. Tun daga irin tarbar da aka yiwa Safah jikinta ya soma yin sanyi, gwiwoyinta suka salube. 

Wato Hajiyar Nasir ko amsa gaisuwarta ba ta yi ba. Kallo daya Danejo ta yi mata ta gane ta, wato likitar hakorin nan ce da suka taba shiga asibitinta. Lallai ba ta tsargu a banza ba. 

Zahra’u da Abkar kadai suka yi mata kyakkyawar tarba, suka kwashi kayansu zuwa sassan Lamido dake cikin gidan. Gini ne Australian flat mara girma can-can, mai fenti ruwan kwaiduwar kwai. 

Lamido zaune gaban mahaifiyarsa Haj. Nadeeya ya mike kafafunsa a kan kilishi yana bude wayoyinsa dake rufe tsayin lokacin yana duddubasu suna magana jefi-jefi da Innar. 

Ta layinsa na Glo sakonni suka soma karon shigowa daga ‘yan’uwa da abokan arziki, duk dai na fatan waraka ne da addu’ar samun sauki cikin halin da ya samu kansa, wanda duk wani mai kaunarsa idan har ya san wane ne Lamido? To ya zubar masa da hawaye. 

Hajiya ko zancen Safah ba ta yi masa ba, shi kuwa magana daya biyu sai ya ambato ta, yana gayawa mahaifiyarsa hidimarta gareshi a wannan al’amari da ya same shi. Ko sau daya bai ambato Danejo ba. 

Ta gaji da zancen Safah da yake mata ta ce, 

“Wai kai me Danejo ta yi maka ne ka ce ta taho gida?”’ 

Yana murmushin mamaki ya ce, 

“Ni ba ta yi min komai ba, cewa na yi ta taho ta huta. Amma in ta fadi wani abu sabanin wannan ban san shi ba”. 

Haushi ya kama Hayjiya Nadeeya, ta ce, 

“Lamido!” 

Ya dago ido cike da kwalla ya dube ta. Abinda zai sa Lamido kwalla, ita ta san ba karami bane. Don haka sai jikinta ya yi sanyi ta kasa yi masa sababin da ta yi niyya. Shi kuma ba wani abu ya sa shi yin kwalla ba, illa mamakin butulci irin na Danejo. 

Su Danejo Fulanin jeji ne ta bangaren mahaifinta, amma a dalilinsa sai da ya zamanto duk wani nata yana cikin gidan siminti. 

Babu wani da ya shafeta da bai kai shi dakin AIlah ba balle iyayenta. 

Ya dauke ta ya fifita ta, ya darajata cikin mata ‘yan’uwanta ba don matsayinta ya kai ta samu wannan alfarmar ba, sai don kawai yana sonta. Amma shine ta sabauta masa rayuwa saboda kawai ya raya sunna don tserar da kansa daga zina. 

Ji ya yi ko gawarta bai son gani, ya runtse idonsa ya bude a dai-dai lokacin da Danejo da Innarta suka shigo suna kumburi. 

Ashe dawowa suka yi daga flat din Lamido, bayan sun yi wurgi da kayan Safah waje, sun hadu sunyi mata dukan mutuwa sun jawota sun watsar a baranda sun sawa gidan kwado, wai gidan Danejo ne babu shegiyar da ta isa ta shige shi. 

Abin da Shatu ke gayawa Hajiya Nadeeya kenan a gaban Lamidon. 

Ya ce, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!” Ya mike da gudunsa bayan ya watsar da wayoyin 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *