BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 5 by sumayyah Abdulkadir
Www.bankinhausanovels.com.ng
dake cinyarsa ya nufi bangaren nasa.
A barandar Safah ce cikin jini tana murkususu ita kadai. Da jinin jikinta da komai ya suro ta ya shimfide a gaban mahaifiyarsa.
Ita kanta Hajiya Nadeeya ta tsorata, ta ce, “Wannan ai (bari) ne. Abubakar’. Ta kwalawa Bukar dake uwar dakinta shi da Zahra’u kira.
Ya fito da gudu ganin abin da ke faruwa sai ya fita aguje dakin Malam ya kirawo shi. Malam ko hula babu a kansa.
Abubakar ya ce, “Ka gani ko Malam? Na gayawa Hajiyarmu Aunty Danejo ma kanta da motsi ta ki yarda dani, yanzu ga shi za ta kashe ‘yar mutane muna cikin gidan bamu sani ba”.
Malam bai yi magana ba, da kansa ya dauki Safah daga shimfidewar da Lamido ya yi mata a kasa ya koma gefe kwakwalwarshi na kara hautsinewa. Suka yi asibiti da ita.
An tabbatar ciki na watanni biyu ya fadi, kuma tana bukatar wankin ciki. Sun nemi_ ba’asi, Malam ya ce zamewa ta yi daga bene. Bayan an mata wankin cikin sun bata gado don ta huta, ta kuma sha magunguna.
Sanda suka koma gida jikin Lamido ya kara rikicewa, maganganu yakewa Hajiya Nadeeya na abinda Danejo ta yi masa.
Wanda in da cikin hankalinsa yake ba zai taba iya fada ba. Har cewa ya yi ba ta gamsar da shi a shimfida, hakuri kawai yake yi. Shekararsa goma da aurenta bai san me ake samu a jikin diya mace ba.
Safah ta kawo sabuwar rayuwa a gare shi, ta cike
gurbin mata goma!. Ta bashi farin cikin da bai taba samu ba. Ta girmama shi, girmamawar da babu macen da ta taba yi mishi.
Ta so shi ta kaunace shi, kamar shine sarkin mazan da babu kamar shi. Idan Danejo ta kashe ta wallahi ya sake ta saki uku, ko a lahira kada ta ce ta sanshi…..”
Sai ya buga kansa da bango ya yi wata irin mummunar faduwa da ta yi sanadin shanyewar barin jikinsa.
Kai abin babu dadi, idan har ka kasance mai birbishin imani a gidan nan, a yau sai ka zub da hawaye.
Wannan karon Malam Abdulkarim cire kawaici da fulatanci ya yi ya ce Danejo da uwarta su fice mishi daga gida cikin mintuna biyar da duk tsinken da suka san nasu ne cikin gidan. Idan sun ki karnuka zai sa su yagalgala mishi namansu. Danejo ta ce, “Babu inda za ta ko an sake ta, zaman ‘ya’ yanta take. Malam cike da mamakinta ya ce, “Ya’yanki randa suka girma don karan kansu sa neme ki. Lamido sauta, sauta Lamido, wannan ba matar zama bace, makamashin wutar jahannama ce, SA’IRAH! Ko a lahira kada Allah Ya tasheku tare”.
Malam kuka yake sosai, a lokacin da yake wannan maganar rungume da Lamidon.
Sun tafi amma cike da bakin mummunan kuduri, wato yadda Danejo ta rabu da Lamido, haka duk wata mace har da uwarsa za su rabu da shi, ba zai kara amfana musu komai ba.
Hajiya Nadeeya tuni ta taho daga rakiyarsu itama, tun daga lokacin da Lamido ya yi furucin Danejo ce ta sabauta masa kwakwalwa. Suka yi barambaram da ‘yar’uwarta Shatu, tana binsu da mugun alkaba’i.
A ranar a asibiti Lamido ya kwana, washegari Sulaiman Yakasai ya sake kwasarsu shi da Safah da Malam zuwa wani asibiti a Bienna, duk da Safah din ma bata gama jin karfin jikinta ba. Wannan bai hanata kula da Lamido ita da likitocinsa ba. Sai dai ita ma wani lokacin jiri kan kwasheta ta fadi sai an daga ta. Domin ta daku a hannun Danejo da uwarta ba kadan ba. Dukan da tunda uwarta ta kawota duniya wani mahaluki bai taba yi mata koda shigensa ba, hatta iyayen da suka haifeta.
Saukin Lamido sai wajen Allah, watanninsu hudu kenan a Bienna kafin hannun Lamido na dama ya soma amfanuwa. Gashin kashin da suke masa na musamman ne da ya sha bamban da na sauran asibitoci. Asibitin gabadayanshi ma na masu fama da larurar stroke ne.
A watanninsu shida a Bienna, wani dare da Safah ba za ta taba mantawa ba, karfe daya na sulusin dare tana zaune a gaban gadon Lamido a kan kujerar mutum daya ta roba, da karamin Alkur’ani a hannunta tana tilawa tana gyangyadi, har ta kai ga bingirewa a gaban gadon, Alkur’anin na neman subucewa, sai ta ji hannun Lamido cikin gashin kanta.
Ai sai ta kara rike Alkur’aninta ta ci gaba da
barcinta tana cewa cikin ranta, in mafarki take kada Allah yasa ta farka yanzu.
Wasa-wasa sai ji ta yi hannuwan Lamido biyu sun jawota sun kankame ta, sai ta bude idanu tangararau tana yiwa Allah tazbihi.
Zuwa asubah sai ga Lamido a kan kafafunsa ya shiga toilet don ya dauro alwala.
Tare suka yi sallah, sannan ta hada masa ruwan wanka mai dumi a jacuzzi ta taimaka mishi ya yi wanka sosai irin wankan da rabon da ya yi irinsa yau watanni takwas, sai dai na goge jiki da tawul da Safah din ke masa.
Sau biyar tana canza ruwa, tayi mishi gyaran fuska, ta hada mishi tea mai kauri ya sha, sannan ta ballo magungunansa na kwakwalwa da har zuwa lokacin bai daina sha ba.
Ya karba ya sha tare da wadanda yake sha na tofin addu’o’i (tawaida) da Malam ke masa kullum.
A lokacin Malam ya koma Nigeria, sai Ishak (mai bin Lamido) dake tare dasu. A lokacin shi yana Hotel bai ma shigo asibitin ba.
Karfe bakwai daidai na safe likita da Nurses suka shigo domin lokacin shan maganinsa da gashin kashinsa ya yi.
Nan suka ga abin mamaki, wato patient din ya yi matashi da cinyoyin sahibarsa suna ta hira cike da shaukin juna.
Doctor Tonnies kwararren physiothearapist ne da ake ji da shi a Bienna (Austria).
Warkewar Lamido wata irin warkewa ce ta bazata (ta karfin addu’ar al’umma), a lokacin da
basu taba zato ba.
Don haka har a Bienna weekly journal ta wannan satin da ake ciki ya saka labarin, domin Bature baya raina abin mamaki.
Gashin kashi basu fasa yi mishi ba har zuwa wani lokaci mai tsawo da sauran treatment dinsa da shan magani. A ranar da ya sallamesu ko kwana daya Lamido bai bari sun kara ba, suka taho gida Nigeria.
Gidansu Lamido babban gida ne me sassa daban-daban, don kowa a gidan yana da dakin kansa. Duk sun fito daga cikin mace daya wato Hajiya Nadeeya ‘yar asalin garin Jazeera ta kasar Sudan.
A ranar da su Lamido suka sauka a Taraba ana sunan jaririn da kanwarsa Talatu ta haifa wanda ya ci sunan Lamido wato (Naseer).
Don haka duk dangi sun hallara, su Zahra’u na ta karbar baki sai ganin Yaya Lamido su kai ya sanyo kai falon Hajiya, idanunshi rufe cikin glasses masu ruwan kasa yana rike da hannun santaleliyar matarsa Safah.
Don haka wadanda basu santa ba ma yau sun ganta sun yaba sun yi tofin albarka (classy wife) in ji Zahra’u. Perfect match (in ji Abubakar). Classikue (in ji Aliyu……. ). Duk cikin zuciyarsu suke fada, basu san cewa a fili suke yi ba.
Nan da nan gida ya kaure da ihun murna, addu’a da fatan alkairi. Cike da karramawa mara fasaltuwa Zahra’u ta yiwa Safah jagora har wajen Hajiyarsu da Malam, suka yi mata godiya suka sa
mata albarka, suka kara da yiwa Allah godiya da ya bawa Lamido lafiya a lokacin da kowa ya fidda rai da shi.
Hajiya Nadeeya da kanta ta kai Safah flat dinsu, tasa mukulli ta bude. A gyare yake tsaf kamar da mutane a ciki. Wannan kuma aikin Zahra’u ne da ba ta wasa da tsaftace flat din duk bayan sati biyu.
Safah na shiga wanka ta fara yi, kafin ta fito ma falon ya cika da ‘yan’uwan Lamido, farare sol-sol dasu har da maijegon da ta ce danta mai goshi ne, ya ci sunan Lamido ya kuma zo da kamannin Lamidon, sannan Lamido ya dawo da lafiyarsa ranar sunansa.
Kan ka ce meye wannan labari ya je kunnen Danejo, Lamido ya dawo kuma ya warke tare da matarsa.
A lokacin Lamido na zaune falon Hajiyarsa ‘yan’ uwa da abokan arziki zagaye da shi, ya mike kafafunshi Fahad da Fa’ik suna kai, yana ta kallonsu suna ba shi labarin makaranta.
Idan ya tuna Danejo ce ta haife su sai ya ji ya tsanesu, domin sun zamo shinge ga rabuwarshi da uwarsu dole watarana mu’amala ta sake hadasu saboda yaran.
Amma sai ya yi saurin kawar da wannan tunanin daga zuciyar shi da cewa laifin wani baya shafar wani.
Ya sake matso da yaran jikinsa ya ce da Hajiyarsa, sunyi hutu ne?
Ta ce, “Dawo dasu aka yi daga makaranta kudin shekara ya kare, ita kuma ba za ta iya biyan
miliyan ba, haka malam ko da a kasa suke hako kudin. Don haka Aliyu ya kai su_ wata makarankar kudi a nan unguwarsu”.
Bai samu kansa ba sai da aka kira sallar magariba. Ya fita dakalin Malam ya yi alwala ya sallaci magariba tare da jama’ar unguwa.
Bai shigo ba sai da ya sallaci isha’i. Kafin a tashi sai da Liman yasa aka yi addu’a ta musamman saukar Alkur’ani kan Allah ya karawa Lamido lafiya.
Sanda ya shigo flat dinsu Safah ta sake wanka har ta sanya rigar barci, tana busar da dogon gashinta da ta wanke da hand dryer.
Sai ya karbe ta, suka busar da gashin tare. Hajiya
wanda za su iya aka zo aka kwashe sauran.
Safah ce tsaye jikin madubin dogon yaro tana tufke doguwar jelar gashinta, Lamido ya yi tsaye daga bakin kofa yana kallon ta. Bai san adadin kaunar da yake yi mata ba.
A hankali yake takawa, kafarshi na nitsewa cikin lallausar kilishin da aka malale dakin barcin da ita, har ya cimmata. Ya zagayeta da hannuwanshi ya sanyata cikin kirjinsa. Wannan dare daidai yake da darare dari a garesu.
Domin dare ne da aka biya bashin soyayya mai yawa, aka baiwa so da kauna hakkinsu. Suke kuma fatan Allah ya basu zuri’a a cikinsa.
Wata guda suka kwashe a Taraba, Lamido ya warware sumul. Zuwa wannan lokacin dangin
Lamido sun san wace ce Safah?
Da zuciya daya take zaune dasu kuma da zuciya daya take son Lamido. Hankali, ilimi da nagarta sune suka sa Lamido ke son ta ba bushashar kudi da Danejo ke musu ba, ta koma bayan idonsu wajen kawayenta tana ce musu kwadayayyu, da kudi kawai nake saye su kamar sa hadiye ni.
A yau suka yi shirin tahowa Kaduna domin Safah ta ga iyayenta. Daga nan su wuce Abuja ta ga Shahidah wadda ta haihu satin da ya wuce. Sai su karasa wajen su Marwah, daga nan su kara dawowa gidansu na Asokoro Lamido ya koma bakin aikinsa.
Haka nan Safah ta tsinci kanta da rashin son tafiyar, ta saba da ‘yan’uwan Lamido da iyayensa wadanda ke kaunarta kamar me, musamman Abubakar da Zahra’u manyan aminanta a gidan. Kai ita da Lamido zai yarda, to ya barta a Taraba ya koma Abuja shi kadai ko ya dawo da Danejo su tafi ita ya dinga kawo mata ziyara.
Da ta gaya mishi hakan dariya ya yi, sannan ya girgiza kai kawai wai Danejo. Ya ce,
“Ban san Safah ba ta sona ba sai yau!”.
Furucinsa ya bala’in kada ta. Ta ce, “me ya kawo rashin so cikin maganata?”
Ya ce, “Da kika alakanta ni da wadda burinta ta hallaka ni. Me yasa har kika iya yin tunanin zan iya tafiya in barki? Da ba a gidanmu bane sai in ce gajiya kika yi dani…..”
Hannunta ta kai ta rufe mishi baki,
“Ba abin da nake nufi kenan ba. SABO ne mai sa mutum ya manta uwarshi. Lamido Allah Ya kai
mu lafiya!”. eK
A
kwai wani dan iskan saurayi a nan unguwarsu mai suna Zidane, kowa ya san Zidane dan daba ne. Amma yana son mu’amala da ‘ya’yan Malam Abdulkarim musamman Aliyu.
Ba yadda Malam bai yi ba ya raba Zidane da Aliyu, amma hakan ya faskara, domin Zidane ya likewa Aliyu, wani lokacin ma Aliyu na zaune Zidane ke zuwa ya ishe shi da hira.
To yau ma hakan, Aliyun na zaune a dakalin gidansu Zidane ya zo ya iske shi, ya bashi hannu suka tafa, ya zauna yana kallon dalleliyar ‘Ferrari’ din Lamido da Abubakar da Izuddeen dan Talatu ke wankewa.
Zidane ya kurawa motar ido ya ce da Aliyu, “Yallabai zai iya tuki yanzu kuwa?”
Aliyu ya harare shi ya ce, “Ko kafin wannan al’amarin ya same shi ka taba ganinsa yana tuki?” Zidane ya ce, “Ai zato nake yanzu ba shi da direba, tunda duk sojojin dake tare da shi suna tare da EFCC mai kujerarsa”.
Aliyu ya ce, “Eh, amma duk da haka ba zamu barshi ya yi tuki ba in ba jirgi zai hau ba, sai dai wani cikinmu ya tuka shi. Yanzu ma Ishak ne zai kai su Kaduna”.
Abin da Zidane ke son ji kenan ya katse hirar ya yiwa Aliyu sallama ya tafi.
Lamido da Safah kwance a bayan mota Ferrari, sanyin iyakwandishin na ratsa su, kamshin oud din motar na bin jikinsu da hancinansu wanda ya cakude da sassanyan kamshin turarukansu na Lamido chrome legend dana Safah Nina-Ricci. Ishak na sheka gudu dasu kamar ya tashi sama, Lamido carbi ne a hannunsa yana hailala, Safah na faman cin kasa (calaba) ko ta samu taste din bakinta ya dawo.
As a Doctor ba za ta iya hana kanta ba, sai dai ta hana wasu ci, amma in ba ta ci din ba, ba za ta iya zama lafiya ba.
Hannun Lamido cikin nata sai ya ji fatar hannunta gaba daya ta canza ta zama lukui-lukui kamar ta jarirai, gaba daya jikinta ya zama danye sharaf. Sai ya yi tsai da ido yana kallonta ya ce, “idan har bana tsallaka cikin fannin da ba nawa ba, Ina kyautata zaton YOUNG LAMIDO is on the way…..soon…. the soonest…..”
Dariya ta yi cikin jin kunya ta ce, “Nima na ga alama…..”.
Sauran furucin makalewa ya yi a makoshinta lokacin da duka tayoyin motar suka fashe a wani jeji dake gabashin garin Gombe. Motar ta hantsila ta wulwula ta yi gefe cikin jejin. Wasu irin ku
soshi ne aka zuba a kan titin cikin mintuna biyar kafin isowarsu gurin.
Lamido ta tagar motar ya fado kan titin domin babu belt a jikinsa, Safah da Ishak suna cikin motar basu fado ba, sai jini dake kwarara kamar an yanka rago, Allah kadai Ya san halin da suke ciki.
Allah ne Ya kawo wata motar haya irin (Gombe Edpress) din nan, suka ga mutum kwance tsakiyar titi cikin jini.
A gigice direban ya yi parking a gefe, wasu daga cikin pasinjojin masu imani suka fito suna salati. A take wani ya bugawa ‘yan sanda waya domin wajen ya yi nisa daga idon jami’an tsaro. Direban motar ne ya hango motar da akai hatsarin a can cikin kayoyi da surkukin bishiyoyi.
Kan ka ce meye wannan jami’an tsaro sun cika wajen sun zaro wadanda ke cikin motar sun hada da wanda ke kan titin sun zuba a (Ambulance), tare da rahotanni daga bakin mutanen hayis din, ba wanda ya san a mace suke ko a raye? Ko za su rayu, tabbas sai wani babban ikon Allah.
2K EK
BAKO DAGA LOS-ANGELES C ikin jerin gwanon masu fitowa daga cikin jirgin ‘Cathay Pacific’ har da Engineer Imam Zubair Dan-Kasa. Fari dan sirdidi mai kyakkyawan jikin dake lamushe shekaru ba tare da ya nuna ba. Sanye yake cikin jacket da wando bakake ‘yan gidan (Hilfiger). Idan har ka san Imam a da, to yau ma in ka ganshi ba za ka kasa gane shi ba, domin ba abinda ya canza daga sanin da ka yi masa. Shi bai kara girma ba, shi kuma bai ragu ba, tun can mai kyau ne kuma mai kyan jiki. Don haka cikin shekarun nan da suka gabata canjin da Imam ya samu ba mai yawa bane, sai uban kasumba kwantacciya da ta lamushe gefe da gefen fuskarshi kamar African-Laureate (Wole Soyinka). Abin nufi, babu wannan gayun na baya. Gashi nan dai bakin Bature zallah, wanda ke zaune a kololuwar Amurka (Los – Angeles) tsayin shekaru tara.
A yanzu ma ba wai ya dawo bane, dole ce tasa ya zo, da niyyar da ya tabbatar da abinda yake son tabbatarwa, ya komawa isolated-life dinsa, wadda tafi komi dadi agareshi, tunda baya neman komi a rayuwa.
Imam ya sauka ne a Airport din garin Abuja,
—=