BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 6 by sumayyah Abdulkadir

 BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 6 by sumayyah Abdulkadir 

                 Www.bankinhausanovels.com.ng 

daga nan ya hau karamin jirgin Mangal mai zuwa Kaduna. 

Mami (Hajiya Zainab) na dakin uwar marigayin wato Hajiya Maama dake kwance bisa katifa tana diga mata ruwan zam-zam a baki, domin zuwa wannan lokacin Hajiya Mama sai dai a kwantar a tayar. 

Ciwuwwukan girma iri-iri sunyi mata rubdugu, hatta abinci mai ruwa-ruwa Mamin ke bata shi ma Sai ta tallafo kanta ta ba ta a baki da kankanin cokali. 

Damuwa da tunani, sun karawa tsufan nata armashi. Amma duk da haka bakin wannan tsohuwa bai fasa ambaton Allah Ya kawo mata Almustapha kafin Ya dauki ranta ba. 

To yau ma hakan, da ta bata zam-zam din ta sha ya isheta, sai ta soma bata fura da ta yi lukuiJukui cikin kindirmo da karamin ludayi. 

Suna hakan ya daga labulen dakin ya sanyo kansa ciki, sallamar da ya yi ma basu ji ta ba, domin sautin muryarshi ba shi da amo. Kamar ta mai fama da mura. 

Da farko ita Mami tsorata ta yi har robar da furar ke ciki ta kife a kan Hajiya Mama, ita kuma Hajiyar salati ta yi don gani ta yi kamar marigayin danta Zubairu ne a gabanta, don shima haka yake barin kasumba mai laushi a fuskarsa. 

Sai ta dauka mala’ ikan daukar rai ne ya zo mata a suffar Zubairu. Ta ce, “Ashhadu an la’ilaha illallahu, wahdahu lasharikalahu, wa asshahadu anna Muhammadun -rasulillah……. cika umarnin Ubangijinmu, na shirya”. 

Rabon da Imam ya yi dariya yau shekaru tara kenan, sai yau da wata irin dariya ta sarke shi, har sai da ya dauki ruwan hajiyar na swan dake gefe ya shanye robar bai rage ko dis ba. Ya dauki wani ya soma zazzagawa a cikin sumar kanshi da fuskarshi rowan na sauka a kafadunsa. Ba tareda ya damu daya goge ba. 

Mami ta kura masa ido, sai hawaye suka mirgino mata. Ganin Mami na kuka ya tabbatar ya yi mata laifin da ba za ta iya yafe mishi ba. 

Ko yaushe ya yi tunanin zuwa gida, tunanin hakan kan kashe masa gwiwa. Bai san da bakin da zai yi mata bayanin dalilin tafiya ya barta ba idan ya rabu da Safah ba. 

Ba Safah ce ta hada su ba, tasowa ta yi ta gansu tare. Mamin UWA ce da ba zai iya mantawa da ita ba. Da hobbasarta cikin rayuwarshi, da rawar data taka wurin ginuwarshi, da kaunar data ke mishi, wadda ko ‘ya’yan data haifo daga cikin ta, sai dai su ce ta haifesu (bata basu rabin-rabin ta ba). 

Ya dade da sanin rasuwar Daddy ta hanyar wani sakon ta’aziyya da Ahmad Kutama ya taba aika mishi ta email. Ya bi diddigin maganar ya tabbatar da ita. Halin da ya shiga a lokacin yana (Detroit) ba zai taba kwatantuwa ba. 

Watanni uku ya kwashe a Saudiyya yana kwana a Harami ba a Hotel ba, in ka ganshi a dakinsa na otel, to lalurar dan Adam ta kai shi, irin su wanka, cin abinci, canza kaya da sauransu. 

Ba abinda yake yi sai nemawa Daddy da iyayensa 

gafara, ko da ya dawo Detroit ajiye aikin ya yi da ‘General Motors’ ya hada gadonsu shi da Shahida da abinda ya mallaka a tsayin shekarun daya kwashe yana yiwa G.M aiki, ya bude kamfanin kera motoci nasu na kansu, don ba zai ce nashi shi kadai ba, domin kasonta yana ciki, duk da nashi yafi yawa nata bai wuce 20% ba a birnin Los – Angeles. 

Ya debi ma’aikata bila’adadin musamman bakar fata masu irin karatunsa daga kasashe daban-daban, musamman kasashen Africa, Asia da LatinAmerica. 

A yanzu haka Dan-Kasa Motors sune ke manufacturing motoci irin su Rio, Honda City, Acura, Cruiser, Legend, Sienna, Renult, Duster Adbenture da sauransu. Kuma babu inda motocin su basa yawo a duniya, musamman kasashen Africa da ‘Middle East’, kasancewar motoci ne masu rangwamen farashi ba kamar na GM (General Motors) ba. 

Rayuwar Almustapha a Los-Angeles wata irin mummunar rayuwa ce kazantacciya da baya so ya tuna. Rayuwa ce da babu hope, ko tunanin gina future a cikin ta. 

Tun daga giya har cocain ba abin da bai sha ya shaka ba, a shekararsa ta farko a birnin kenan. Ba don komai ba sai don su mantar da shi SAFAH da al’amarinta. 

Da suka gaza, sai ya budewa mata kofa (black Americans) masu irin structure dinta, don su taimaki zuciya, gangar jiki da kwakwalwarsa 

daga tunaninta. 

Da suma suka gaza hakan tsayin shekaru uku, sai ya tattarasu duka ya yi gefe dasu, ya maida cinemas da club-life suka zama wajen kwanansa, inda za’a sheke aya a sha barasa, ayiwa shaidanun mata da shaidanun abokai bushasha. 

Giya ce ta fara kwantar da shi a asibiti, ya yi jinyar watanni biyu domin ta taba hantarsa.° 

Ganin wannan hali na rai kwakwai mutu kwakwai da ya samu kansa a ciki, ba don Allah ya yi yana da sauran shan ruwa a gaba ba, da ya mutu cikin wannan halin saboda soyayyah, me zai ce da Sarki Allah? 

Tun daga lokacin Imam ya saduda ya dawo hanya ba tare da wani ya karkato da shi ba, ya koma Isolated -life wato rayuwar kadaici da babu komi a cikinta sai ibada da juya kobo ya koma dari, ta hanyar amfani da fasahar da Allah Ya ba shi wadda ba kowa Ya baiwa ba. Wato sarrafa karfe da karfe su bada abin hawa mai ban mamaki. 

A wannan shekarar ne ya yi bikin cikar (Dan Kasa Motors) shekaru biyar da kafuwa. A kuma shekarar ne barci ya kauracewa idanunsa. Mafarkai yake masu ban tsoro a gare shi da Daddy da Minister Zubairu, mafarkansa suna nuna suna cikin fushi da shi da barin mahaifiyarsu cikin halin ka-ka-ni-kayi alhalin yana da rai saboda mace. 

Mene ne amfanin dukiyar da yake tarawa idan ba su zasu ci ta ba? Ya bar Mami da nauyin ‘ya’ya 

mata uku da tsohuwa ba tare da ya tallafa mata ba. 

Wadannan mafarkai da maganganu da yake ji cikin barcinsa, su suka tunkudo hankalinsa gida. Ya yanke duk abubuwan da yake yi ya taho. Ganin Hajiya Maama cikin wannan hali, gida duk ya bushe saboda rashin namiji ba rashin kudi ba, hatta shukoki sun mutu, grass carpet sun bushe saboda babu mai basu ruwa da taki. 

Ma’aikata duk sun kama gabansu, maigadi ne kurum ya yi saura, saboda tun Marwah na biyansu har ta gaji ta watsar, mai wanke-wanke kadai ta ragewa Mami, hatta girki ita take yin abinta. 

A ganina “not all what man can do a woman could. Wannan karya ce ta Bature. Cewa da yayi wai what man can do a woman can do better . Shi namiji ko an ki, ko an so shine shugaba, domin Allah Ya bashi juriya da karfin zuciyar da bai baiwa diya mace ba. Bata ne babba, mace tace zata hada kanta da namiji ko zata iya yin abinda yafi na namiji. 

Ubangiji (S.W.T) da kansa ya ce, “Ar-rijal kawwamuna alan nisa’i). Kenan maintaining the belief that, duk abinda namiji zai yi mace za ta iya, har ma fiye da shi,ta zamo izgili ga ayar Ubangiji. 

2K OK KK 

WwW annan tunanin da Imam ya yi, shi ya sanya shi fi

tar da hawaye masu yawa a yau. Ya gurfana yana baiwa Mami da Hajiya Maama hakuri, yana rokon afuwa da rangwamensu, ko su Daddy sa yafe masa. 

Ita fa Mami ba ta taba yin fushi da danta Almustapha ba, hawayen da take fitaswa na farin cikin ganinsa ne…… amma shi ya kasa gane hakan. 

Rungume shi ta yi duk girmansa suna kuka dukkansu. Hajiya Maama kuwa cewa ta yi, “Imam tunda ka zo kuma fushin me zan yi? Alhalin na samu makwafin Zubairu da Aliko, wanda zai kama gawata ya sanya cikin kabari da sunan JINI NA?”. 

Ya ce, “Ba inda zaki ki barni, ai rashin gatan sai ya yi min yawa. Daure ki mike ki kwarara jikinki mu koma aurenmu, ai ni da ke mun fi tattabaru soyayya”’. 

Gaba dayansu sai da suka yi dariya. Daidai lokacin da wayar Mami ta yi kara. A yau Mami jin zuciyarta take kamar takarda ba abinda zai kara bakanta zuciyar ta. 

Anya??? A wannan rayuwar mai cike da SIRADI iri-iri, daga wannan sai wancan??? 

“Kwamishinan ‘yan sanda ne Abdullahi Fika, muna tare da wadanda suka taso daga Taraba zuwa Kaduna a safiyar yau, mace daya maza uku. Sun samu hatsari mummuna a wani jeji kamin a shigo garin Gombe. 

Mun samu wannan lamba ne a cikin jakar macen cikin motar da suka yi hatsarin da suna Ma mere, 

kuma ita kadai ce lamba a cikin wayar. Ku gaggauta zuwa daukar gawarwakin a asibitin Jiha na garin Gombe……” 

Sai wayar ta subuce daga hannun Mami ta tarwatse a kasa…… 

Mami tana salati tana juya kai tana tafa hannuwa. Ni Zaynabu-Abu wace irin rayuwa ce wannan, daga wannan sai wancan?” 

Sambatu sosai ta shiga yi tana zagaye katon dakin ko dankwalin ta da ya zame ta kasa daurawa. Imam kokarin hada wayar da ta tarwatse yake har ya samu isa reciebed calls, ya kira last call. Abinda aka gayawa Mami shi aka gaya masa. Jin cewa daga Taraba ne sai ya dauka “yan’uwan Mami ne da take dasu a Taraba. Wadanda tun yana yaro ya sansu. 

Ya kamo Mami ta zauna ba tare da ta yi shiru da sambatun ba……. 

“Safah ce da Uncle Lamido wallahi, jiya-jiyan nan ta gaya min za su taso yau”. Ta fada, cikin wani irin yanayi na saduda, da rashin tabbas na rayuwa da fita hayyaci. 

Hantar cikin Imam ta cure wuri guda. Hanjin cikinsa ya hautsina, sai ya dafe cikin ya sunkuya yana kiran sunan Allah. 

Imam bai taba zuwa Taraba ba, amma a yau sai gashi ya dauki hanyar Taraba cikin motar Mami, sai in Mamin ta ga zai kauce hanya sai ta nuna masa har Allah ya kawo su garin Diban-Fari, (Gombe)suka tambayi asibitin Jiha aka nuna musu. 

Imam ya kara kiran kwamishina ya yi directing 

dinsu a lokacin masu hadarin suna Mutuary. Allah mai girman da babu kamar sa, kunfa yakun ne wanda ya yi alkawarin “Kullu nafsin za’ikatul maut!” 

Lamido Mami ta fara shaidawa cikin gawarwakin biyu, don ba ta san Ishak ba. Sun ce macen akwai hope na samuwarta, sai dai tana ICU (Intensibe care Unit). 

Mami ta fita harabar asibitin tana kuka wiwi, ta kira Malam Abdulkarim wanda ke can yana fama da faduwar gaba da takurar zuci. 

Ko da ya daga wayar Mami ya ji tana kuka sai ya ce, 

‘““Zaynaba ta kashe su ko???” 

Daidai da shigowar Hajiya Nadeeya, ta ji furucin bakinsa. Tire din abincin Malam dake hannunta na tuwon laushi miyar kubewa ya kwankwatse a kasa. 

Mami ta ce, “Hatsari dai suka yi, Allah kuma ya karbi abinsa. Ita Safan ana sa rai da samuwarta, domin lokacin da suka yi hatsarin akwai belt a jikinta”’. 

Malam ya ce, “Babu lokacin tone-tone kawai amma ba zan taba yarda ba. Danejo ita ta kashe min Lamido, domin ga wancan watsatstsen yaron can abokin Aliyu a hannun ‘yan sanda, an kama shi a jeji da wasu irin kusoshi da ‘yan fashi da makami ke amfani dasu wajen huda tayoyin kowace irin mota. 

Shari’a zamu yi ta a DUNIYA nida Danejo da 

uwarta kuma zamu yi taa LAHIRA…!”. 

Malam kuka yake yi sosai tsigogin jikinsa na tashi, ya ajiye wayar ya mike tsaye yana cewa. “Kai SHAHIDI ne Lamido, wadannan wahalhalu da wannan shaidaniya ta sanyaka a ciki don kawai ka raya sunna ka yi koyi da ma’aiki, insha Allahu ko kabari ba zai karbe ta ba. 

Sai dai gawarta ta tozarta ta zama abincin ungulu da tsutsotsi. 

Na yafe maka Lamido duniya da lahira, ko da yake dama ni baka taba bata min ba. Lamido idan akwai abin da ya fi yafiyar iyaye, na roki Allah Ya yi maka. 

Ina yi maka addu’ar samun aljanna mafificiya, madaukakiya wato firdausi. Allah Yasa ka zamo mai ceto garemu (da duk makaranta littafin Takori)”. 

Ai jin haka sai Hajiya Nadeeya ta fadi kasa a kan gilasan da suka kwankwatse. 

Zahra’u ta ji karar faduwar tangarayen tare da faduwar gaba ita ma. Da gudu ta aje tsintsiyar ta yi dakin Malam inda ta tabbatar daga can karar ta fito. 

Ganin halin da Malam da Hajiyarsu ke ciki sai ta dora hannuwa aka ta kwarara uban ihu da iyakacin muryar da Allah Ya hore mata. Wannan ihu na Zahra’u har makota sun jiyo shi ba jama’ar gidan kadai ba. 

Aka kwashi Malam da Hajiya aka yi asibiti dasu. Cikin dan lokaci kankani mutuwar Lamido Nasir, ta zagaye kafafen yada labarai da lungu da kowanne sako na gida Najeriya. 

Deputy Sulayman Yakasai ya samu labarin ne ta 

yanar gizo, a take ya taho Taraba da jama’a masu dimbin yawa. 

A lokacin Mr. President yana London ya je (check up). Aka debo gawar Lamido da Ishak a jirgi zuwa Taraba. 

Yawan dimbin al’ummar da_ suka_halarci jana’izar Lamido ba za su lissafu ba. Garin Taraba zamowa ya yi ba shiga ba fita har sai da aka yi addu’ar uku. 

Malam tare da shi aka binne Lamido, shi ya sanya shi cikin kabarinsa ba tare da hawayen shi ko kadan ya zuba ba. 

Su Mami suna nan Taraba, Imam na cikin ‘yan zaman makokin da bai taba ganin irinsu ba, kusoshin Najeriya ciki da bai dinta, gwamnoni talatin da shida na jahohin da muke dasu sun halarta. Musulmin su da kafiran su. Ya soma tambayar kansa wannan wane irin miji ne Safah ta aura ne? Ashe hangen BABBAN GORO ne ba ZAHRADDEEN ba, yasa Safah ta ki shi??? Deputy na nan har kwana uku duk abin da al’umma za su ci a wajen zaman makokin daga aljihunsa yake fitowa. 

“Lamido na kowa ne!”,, 

Abinda suke fada kenan. 

Halinsa da gaskiyarsa su bishi. Domin ba shi da abokin hamayya sai wanda ya tabbatar shi barawo ne, mai cin dukiyar Najeriya ne da yunkurin karya tattalin arzikinta. 

Har zuwa wannan lokaci Safah na ICU. Ranar da aka yi sadakar bakwai ranar ne aka sallamo Hajiya Nadeeya. 

Ta roki Mami da su tafi da ita ta ga halin da Safah take ciki. A lokacin an mika ta asibitin koyarwa na Zaria. 

Zahra’u sai ido, ba ta um ba ta um-um. Don haka Hajiya tare da Abubakar suka bi su Mami Zaria. Sanda suka je numfashinta ya daidaita an cire odygen an ba ta daki a aminity. Hajiya Nadeeya ta tsaya a gaban gadon Safah tana kallon ta hawayenta na zuba a kirjinta. In ba wanda ya yi mata kyakkyawan sani ba, ba zai gane ta ba. 

Gaba daya halittarta ta jirkita, kanta ya kumbura, na’urori rututu a kanta da fuskarta. Ga karin ruwa da na jini. Ga karairayayyun kafafu da suka sha daurin Bature. 

Hajiya Nadeeya ba ta taba ganin tashin hankali irin wannan ba, sai ta fito daga dakin da gudu tana kuka wiwi. 

bubuwa masu yawa sun faru cikin watanni uku da suka biyo baya. Kama daga shigar da kara da Malam ya yi a kotun gwamnatin tarayya ta Abuja (Federal High Court). 

Domin Zidane da ya ji wuya a hannun jami’an tsaro ya ba da tabbacin tabbas sasu aka yi suke ta bin diddigin fitar Lamido da mai dakinsa, amma 

babu shi sanda aka je aka zuba kusoshin a kan titin. Ya dai rike musu ne. 

Da aka ci gaba da azabtar da shi sai ya fadi cewa hayo kwararru aka yi suka yi measuring time and space ta hanyar amfani da na’ura mai kwakwalwa suka zuba kusoshin a kan titin gab da isowar motar Lamidon. 

Amma fa baya cikinsu, ya dai dauko musu rahoto ne ya raka su. Bai kuma san wa sanya su ba. 

Babu wanda bai kadu ba da jin wannan rashin imani. Ai basu kyale Zidane ba kotun koli suka gurfanar da shi. Aliyu da Malam su su kai kararsa. 

Bala’i ya yi bala’i ga Zidane, da ya tabbatar zai mutu ne a banza shi kadai a kan dan kudi kalilan, masu kasurgumin laifin ko a jikinsu. 

Sai ya fito fili ya bayyana cewa matar marigayin da gyatumarta su suka sa su, a kan kudi naira miliyan uku. 

An nemi Danejo a Yola da Taraba an rasa, ta sace Fahad da Fa’ik ta bar kasar dasu. Tun ranar sadakar uku wata kanwarta ta je gidan ta faki idon kowa ta kwashe su. 

Wannan al’amari ya kada zuciyar masoya Lamido, musamman amini na kwarai Deputy President Sulaiman Yakasai. 

Nan da nan ya baza hotunan Danejo a Embassy na dukkan kasashen duniya tare da yaran. 

Tuni an cafke Inna Shatu, Hajiya Nadeeya ta zuba mata ido a lokacin da aka dannata a shiga ba biya, wai kanwarta uwa daya uba kowa da nasa. Duniya ina za ki damu? Ina zumunci da 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *