BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 9 by sumayyah Abdulkadir

BABBAN GORO BOOK 3 CHAPTER 9 by sumayyah Abdulkadir

                  Www.bankinhausanovels.com.ng 

abinda ya tsana irin ya ji yarinyar na kuka ba a rarrashe ta ba. 

Gane hakan da Safah ta yi sai ta samu hanyar da zai kulata ko ya ki Allah, idan tana so ta tunzuro shi sai ta sawa ‘yar nono a baki da ta fara sha sai ta cire ta. 

Ai kuwa za ta soma ihu kamar za ta tsaga gidan. A take za ta ganshi ya zo ya fara yi mata yayyafin bala’i kamar ya kwada mata mari. 

Ita kuwa sai ta yi sukuti tana yi masa wani irin kallo beyond comment (sunan wani ganyen shayi) har ta kassara shi. 

Da ya gane da gangan take yi don Mami da Hajiya sun ce in baya nan bata yi, lafiya take zaunenta. Sai ya rabu da ita, amma ya yi mata nasa shirin shima. 

“Yammatan nan na office dinsa kawayen Hajiya Maama, Barbara, Samry da Geneibeib ya koma kwasowa in sun taso aiki. 

“Yammata ne zuka-zuka babu ta yarwa, in sun gama hirarsu da Hajiya Maama wai kowacce ta dage sai Hajiya Maama ta koyi yarenta. 

Barbara Irish ce, Samry Jamaican ce, ya yin da Geinebieb take Nagerian. In za su tafi sai ya faki idon Mami ya ce da Hajiya Mama zai taka musu, nan za a yi ta runguma da sumba wai sallama ake yi. 

Ya san tsayawa take kullum a tagar dakinta dake saman bene tana kallon su. Ko daga kai baya yi balle ya nuna ya san tana yi. 

Ai kuwa ta shaka, sai ita ma ta fiddo nata salon. Cikin Engilsh wears take cakarewa ta yi ta 

harkokinta cikin gidan ta daina zaman daki. 

Ba kuma ta tsananta shiga da ficen sai ta tabbatar yana main parlor. Gashin nan haka ake masa ado kala-kala, yau kalba da beads, gobe parking da ribbon, jibi manya-manyan kitso hudu. 

Ai kuwa ta yi nasara, domin Imam ya susuce ya kasa controlling kansa, muddin zai ganta a gidan. To rikirkicewa yakeyi ya daburce. 

Tun Mami na zuba ido har ta tsawatarwa Safah, domin abin nata na nema ya kaucewa addini ga daukar alhakin bawan Allah da babu aure babu sabon Allah. 

Mami ta lura ko hira suke idan Safah ta fito cikin wadannan designers din nata, kalma daga bakin Imam ta kare kenan sai ido. 

Don haka Mami ta kwashe kayan manya-manyan jakunkuna ta bar mata dogayen riguna sai atamfofi. Ta ce kuma duk randa ta kara barin kanta a bude ita da Allah. Ba ta nuna mata ta gane don Imam take yi ba. 

Ita dai Hajiya Mama ba ta san bidirin da ake yi ba. Ta soma matsa lamba, ita fa tunda ta ji sauki Safah ta warke, kuma Imam bashi da niyyar aure, to a tattarata haka a maida ita makyankyasarta. Bazata cigaba da zama a gidan da babu matar aure ba. Ta ishe shi ta uzzire shi. Ya ce, “Ba na kawo matar kin wulakanta su ba? Ni wawan ina ne zan je in kara kwaso wasu kasa da kasa ki muka musu muciya? To amma tunda kin damu ina son Barbara”. 

Hajiya Maama ta yi salati ta ce, “An gudu baa tsira ba, tukunna ma ka san me kalmar sunanta ke 

nufi a harshen Hausa? Barbara fa saduwar dabbobi, kana neman wa rayuwarka jidali”. 

Mami ta yi dariya har ta gode Allah. Imam ko a jikinsa. Ya daga murya sosai yadda Safah dake kicin za ta jiyo. 

“To tunda ita ma Barbara bakya sonta, to ki zabo min da kanki amma banda ZAWARAWA”. 

A nan ne Hajiya Maama ta gane inda ya dosa. Ta ce, 

“Ka yi magana Malam, a inda ya kamata a baka amsa. 

Wace ce Bazawara? By defination, Bazawara ita ce wadda ta taba yin aure ta fito. A dalilin saki, ko a dalilin mutuwa. Mene ne auren? Shine ta sadu da namiji. Ita wannan wadda ta yi auren, ko ta sadu da namiji, ko bata sadu da shi ba, a society sunanta Bazawara. Kuma society na kallonta as less-pribileged than the unmarried one. In haka ne kenan duk wadda ta sadu da namiji a waje komai kankantar shekarunta, sai dai a lika mata suna budurwa amma Bazawara ce. Don haka duk taron wadannan galla-gallan ‘yammata dake rudarku da kwalliya da kyawun sura da kananan shekaru duk zawarawa ne. Domin da ka kalli idanunsu kuru-kuru kamar kwado a miya ka san babu wadda ba ta san namiji ba a cikinsu. Namijin ma baka san wane kare da wane doki ba. Don haka ni a wajena a wannan zamanin wadda ta yi aure ta san namiji mai asali da tushe ta fiye 

min in aureta da in auri zawarawan kan titi. 

Abu daya kake wa bakin ciki Imam, budurcin Safah da Allah bai yi ka samu ba!” 

A firgice ya dago ya dube ta. Kunyar Mami, nauyin Hajiya, kunyar SAFAH suka taru suka lullube shi. 

Hajiya Mama ba ta yi shiru ba, ci gaba ta yi da cewa. 

“Don haka in ma za ka cire wannan a ranka ka baiwa zuciyarka abin da take so to ka cire. In ka ki, wallahi ba za ka zauna lafiya ba’. 

Ta mike ta dau ‘yar dake koyon zama cikin abin koyon zama ta dora masa a cinya. “Inda baka rabu da Safah tana budurwa ba ina za ka kai rabon wannan yarinya?” 

Ya rike ‘yar sosai ya rungumeta, kwallah ta ciko idanunsa. 

Ya ce, “Mami don Allah ki yi hakuri da furucin da na yi bacin rai ne”. 

Murmushi ta yi ta dora hannunta a kafadunsa ta ce, 

“Imam har yau ban cika Mamin Imam ba ko? Mamin Safah da Marwah ce?” 

Da sauri yake girgiza kai. 

*“….Ba nufina kenan ba. I know it will hurt, but you don no how much it deeply touches the 

Mami ki yafe mini furucina, Hajiya ki yi hakur’. Ya zube a gabansu gwiwoyinsa a kasa, kansa a kasa idanunshi a kasa. 

Ya ce, 

“Ina neman alfarmar ku bani auren Safah, ita 

kadai rai da zuciyata ke so har yanzu, soyayyarta ce ta hana ni yin aure, na zabi yin rayuwa….. drunkerd,….. isolated…., incomplete and meaningless…… Na yarda Mami Safah tana sona, kuruciya ke damunta a baya…..” 

Basu samu bakin bada amsa ba sakamakon fitowar Safah jaye da trolley har guda biyu. Daya tata daya ta ‘yar ta. 

Tana sanye da doguwar Abaya da dankwalinta ruwan toka. Idon nan ya ci kuka ya koshi. Tana rike da passport dinta da na ‘yarta. 

Kai tsaye ta nufo shi, ta dauki ‘yarta dake gefensa ta jefa a baya tasa zani ta goya ta. Ta shuri akwatinta tai gaba tana ta kuka mai cin rai. 

Dukkansu an rasa mai bakin kiranta har ta fice. Amma da ya ji ta tada mota sai ya mike cikin zafin nama ya bita. 

Daya motar ya dauka suka rika zuba tsere kamar sa tashi sama. Ga lafiyayyun titunan da ke da sama da kasa babu cinkoso a cikinsu, wannan ne ya basu damar tsula tserensu zuciyarsa cike da fargabar ‘yar jaririyar dake cikin motar. 

Don haka ya kara speed ya yi mata obertaking ya bugi motar tata ta soma yawo a kan titin tana tangal-tangal, sai kuma ta tsaya a tsakiyar titin cikin kudurar Ubangiji. 

Cikin zafin nama ya fito ya bude motar ya fizgo ‘yar daga bayanta ya zuba mata wani mahaukacin mari wanda ya yi sanadiyyar zubowar habo daga hancinta. 

Sai da ya fara kai babyn cikin motarsa ya sanyata 

a katifar jarirai ta musamman da aka kera motar da ita, sannan ita ma ya zo ya fincikota ya jefa a bayan mota ya kulle. 

Ya saukar da lotsattsiyar motar gefen titi ya kwaso jakunkunan ya jefa a boot din motarsa ya ja motar a hankali. Shukrah nata canyara kuka. Abinda bai so kenan (kukan Shukrah), dole ya yi parking a wani bus stop ya juyo ya dube ta. Kuka take ga jini da majina da hawaye sun cakude ba tare da ta yi wani yunkuri na sharesu ko goge su ba. 

Fushin bai sauka daga fuskarsa ba amma ya sassauta murya, 

“Ki yi hakuri ki manta komai ki dauke ta ki ba ta abinci, ba ta da hakkin mu”. 

Cikin bala’i ta ce, “Idan kai ka haifar min ita sai ka gaya min hakkinta dake kanka, yanzu-yanzu in cire in baka abinka”. 

Ya yi murmushi, 

“Na ji bani na haife ta ba, nima kuma ban fidda rai ba ina ji a jikina Allah zai bani daga jikin mahaifiyarta’. 

Tsaki ta yi dogo ta ki daukar yarinyar. Ta ce, 

“Wa zai aurekan, har ya haihu da kai? Allah ya tsare ni, ko maza sun kare ban ga me zai kal BAZAWARA auren SAURAYI ba!” 

Ya lumshe ido a hankali sannan ya budesu a kanta yana murmushi, murmushin da ya manta yadda ake yinsa, shekaru goma a baya. 

Bai ce komi ba, domin zuciyarsa ta galabaice. Idanunshi sun juye, sun rine gabadaya zuwa lub colour. Wani situation ne da bazata iya mantawa 

da shi ba. 

Irin halin da Lamido ke shiga kenan idan yana bidarta, ba sai ya yi magana ba take ganewa. 

Don haka ta ji tsoro ta yi shiru, har da daukar ‘yar ta rungume. Tana tsoron shayar da itan a gabanshi. Ga shi yarinyar ta ki yin shiru. Sai ta dauko empty feeder tasa mata a bakinta, ta kama tsotsa ta yi shiru. Sai ya ja motar a hankali, tafiyar da yake yi sannu-sannu kamar wanda ya dauko danyen kwai tana bala’in bata haushi. 

Amma cike take da tsoron yin magana. Basu san sunyi nisa da cikin gari ba sai a hanyar dawowar tasu. 

Da suka shigo cikin gida da sassarfa ta haye sama. Ya shigo sabe da Shukrah a kafadunshi wadda ta yi barci da (empty feeder) a bakinta. Ya dora ta cinyar Mami bai ce komai ba ya juya ya fice. 

Mami da Hajiya Maama na kallon wannan dramar soyayyah. 

A satin Safah ta bude wuta ita ta gama zaman gidan Imam tunda ya ce mata Bazawara. Ta ishesu ta uzziresu, ta ce in su ba za su tafi ba, to itaa bata passport dinta (don Imam ya kwace) taje can ta nemi Bazawari dan’uwanta ta aura. Rashin Lamido ne yasa aka ce mata Bazawara, amma ba rashin mijin aure ba. 

Hajiya Maama ta bi bayanta ta ce, 

“Kwarai Safah ta yi gaskiya. Ita ma kasar ta isheta a sallamesu ya zauna da uwarsa da bata ganin laifinsa, ita ta daure masa gindi yake yi 

musu rashin mutunci, ko kula su ya ki yi, sai ma security da yasa ya kukkulle kofofin gidan kada ta fita bai sani ba. 

A wannan lokacin abubuwa sunyi masa yawa, budi da nasara, arziki da albarka sai kwararowa suke yi ko ta ina. 

Kamfanin (DK Motors) wato Dan-Kasa Motors ya yi habakar da mutum bai taba zato ba, yana gogawa da manyan kamfaninnikan kera motoci na kasar Amurka. 

Kokarin da yake yi yanzu shine, shigo da motocin direct zuwa Africa cikin farashi mai rahusa, musamman gida Nigeria. 

Sai ya hada kai da DAMBATTA SHIPPING da zarar an kera motocin sai su taho dasu su raba a jahohin Nigeria talatin da shida. Sakamakon hakan Aminci mai karfi ya shiga tsakaninsa da Edcutibe Director na Dambatta wato Saifuddeen Aliyu Dambatta. 

Saifuddeen na mamakin abokin nasa idan ya ce wai har yanzu bai yi aure ba. A wani zuwa da ya yi Los Angeles suka zo gida tare don yin lunch, don Imam ya yiwa Mami waya cewa asa abinci da bakonsa. 

Shigowar Saifuddeen falon ya ga Safah na shayar da baby, ai kuwa ya ce karya Imam ke masa, shi baya son irin wannan wasan. 

Sai da Mami ta shiga zancen ta tabbatar mishi Safah kanwarshi ce ba matarshi ba, maigidanta ya rasu, sannan suka daidaita. 

Amma dai cikinsa fal da tambayoyin me zai hana Imam auren wannan zukekiyar kanwar tasa ko da 

aure goma ta yi ba aure daya ba? 

Da suka fita gidan a hanya yake tambayarsa hakan. Shi kuma ya koro masa labarinsa da Safah tun tana cikin mahaifiyarta har gabar da suke kai yanzu. 

Saifuddeen ya girgiza kai, 

“Bery interesting lobe story….. plz ka kwantar da kai haka, abokina yaki dan zamba ne. Girman kai ba inda zai kaimu wajen matar da muke so. 

Ita mace komin girmanta ‘yar lallashi ce da tarairaya (care and concern) abinda take so kenan daga namijin da take so. 

Idan ka ji labarina da mai dakina kuma kanwata Rukayya za ka samu dabarun samun soyayyar mace masu yawa ko mara lafiya ce balle mai lafiya. (ALHERI). Ya ci gaba da gaya mishi hanyoyin da zai bi ya wanke bakin fentin da ya yabawa kansa a idanunta. 

Sai dai wani abun ba zai aikatu ba sai da aure. Shi kuma ya yi rantsuwa ba zai auri Safah ba da son ranta ba balle ya sa iyaye su tirsasata tamkar wancan karon. Saifuddeen ya yarda da shi. “To abin sai mu koma addu’a”. 

Ita ma Mami addu’ar take yi, Allah ya daidaita mata hankalin Safah da Almustapha, domin kowannensu ji yake da JI DA KAI (wato ya ki sauke kai ya bi dan’ uwansa). 

Kyakkyawar mu’amalarshi da Shukrah sai abinda ya yi gaba. Har ta kai ga cewa yarinyar ta gane shi. Idan muryarshi ta jiyo a falo haka za ta rarrafo da gudu har tana faduwa tana fasa baki. Shi kuma surarta yake ya yi ta juyi da ita a tsakar 

falon tana kyalkyala dariya. 

Ga uwarta ta iya shirya baby, kullum tana tsuke cikin gayu da kamshi da tsadaddun sittirun da har yau bai daina sayo su ba, sai in bai ga wadda ta yi mishi ba da sauran kayan wasa iri-iri, walker, teddies, ribbons, shoes kamar a bude shago dasu. 

Shi take kalla a matsayin mahaifinta. Ba ta kuma aje shi nan kusa a zuciyarta ba, don ko kuka takewa uwar idan bai sa baki ba, ba za ta yi shiru ba. Haka in ta ki cin cereal sai ya zo da kansa ya bata, in ba haka ba sai dai a zubar da shi. 

A farkon wannan watan ne jirgi ya sauke Zahraddeen da iyalinsa har da Inna Binta da Anisa a filin jirgin saman Los – Angeles. 

Wai! Ina ka gano min Anisa a Turai? Ga albarkar aure like a jikinta, duk da ta yi hankali ba ta iya boye abinda ya birgeta sai ta yi magana. 

Yau sai ga Mami da ‘yan biyunta a gabanta da jikokinta, ta rasa inda za ta sa su don murna. Ga yara duk sun girma, babyn da ta kara haifa Zainab (Mami karama) itama ta yi wayo sosai. An ce jika wahal da kaka. Haka ta wuni hidimarsu, Zahraddeen na tare da Imam. Inna da Anisa daki guda Mami ta ware musu. 

A wannan daren Mami da ‘ya’yanta basu runtsa ba, kwana suka yi hirar abubuwan da suka shafe su, rayuwarsu da iyalinsu, ci gaban dukiyoyinsu and many more. 

Abinda Mami ta lura da shi a zamantakewar Marwah da kishiyarta Anisa daraja juna da mutunta juna ne ziryan. Aikin Anisa shine kula da ‘ya’ yan Marwah da take kulawa dasu fiye da ‘ya’yan da 

za ace nata ne. 

Sannan bata nuna zakewa a al’amarin Zahraddeen kamar da, ta yadda idan ka fuskance su sosai itada Dinin za ka fahimci ‘yan’ uwantaka ta fi karfi a tsakaninsu fiye da soyayya. 

Yana treating dinta as Rabi’a, sai dai hakan baya sawa ya tauyeta a kan hakkokin ta dake rataye kansa. 

Daddy da Fatee koyaushe suna jikinta, baka jin komai sai Aunty Anisa share min hancina, Aunty Anisa zan ci kazazan -sha kaza. Aunty Anisa kinga Yaya Daddy yana cin zalina koh? 

Haka dai, ita kuma ba ta gajiya hidima take dasu da zuciyarta daya, har barci tare suke yi sai in tana da girki. 

Kunkurunta ya mutu har zaman makoki ta tara a Zaria, anyi masa addu’a da sadaka, wannan rashi da ta yi ko Zahraddeen ya tausaya mata, domin kuka ta yi bilhakki, kamar dan’ uwanta ne ya rasu. A lokacin cikinta watanni shida amma saboda tsayinta ba a gani, sannan ba mai laulayi ba, bai hanata komai cikin sabgoginta. 

A lokacin suna Ibadan, to harka irin ta man fetur bata barin Zahraddeen zama waje daya. Daga nan Los-Angeles kasar Holland (Malta) za su wuce inda Zahraddeen, zai yi aikin assasa reshensu a Malta na tsayin watanni hudu, 

Don haka Inna daga nan Los gida suka maida ita, suka tattara suka nufi Malta. Sai muce Allah ya kara tsahon kwana da albarkar zuri’a ta gari. Ya kara arziki da lafiya, ya kuma kara dankon kauna da soyayya. 

oR OK OK 

au ne Shukrah ta cika shekara daya da wata takwas, kuma Mami ta cire ta a nono wato yaye. Ba ta barta ta kwana da mahaifiyarta ba. 

Don haka cikin dare take ta ihu tana kiran Mummy, duk abin da Mami ta bata ta ki yarda ta ci. A can ita ma Mummyn fama take da kanta, nonowa sunyi suntum kamar duwatsu, kuma kamar ana caccaka mata allura, ta kasa barci domin azabar ta yi azaba. 

Ta cire riga daga ita sai bra da under wear, sai Safah da Marwah take a daki tana hailala. Ta jawo first aid bod dinta ta fiddo panadol da ampiciline ta kora da ruwa, sannan ya sassauta mata, ta zauna a gefen gado ta dafe kai da hannuwa bibbiyu kamar za ta yi kuka. 

Daga can daki Imam ihun Shukrah-Nadeeya (Sunan da yake kiranta da shi kenan duka biyun a hade) ya hana masa runtsawa, don shi bai san ana wani yaye a gidan ba. 

Ya dai ji kwanaki Mami na fade za a yaye ta bai san yaushe ne ba. Kuma wunin yau baki daya bai shigo gidan ba sai da suka kwanta, don haka ya mike a fusace ya kasa tantance daga ina sautin kukan ke fita, ya fi kyautata zaton daga dakin uwarta ne take wannan barcin nata wanda baya ji 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *