BAFULATANA COMPLETE
*_GYAMBU ((TARABA STATE))_*
______Tafiya suke cikin daji tare da shanunsu wata matashiyar yarinya Ce wadda bazata wuce shekaru goma sha hudu ba se kuma dattijon dake kusa da ita da alama dai mahaifin ta ne, cike da damuwa yarinyar ta daga Kanta ta kalli mahaifin Nata cikeda damuwa tace "wllh Baba nagaji kawai ka tafi Gida idan na huta zan tawo da shanun ta Ƙare maganar Da damuwa akan fuskarta.
Tunda ta fara magana mahaifin nata Ke kallonta sannan Yayi murmushi yace "to Rabe Babu damuwa amma fa ki kula sosai Da kanki. a nitse ta amsa da to "Baba.
Shafa kanta yayi sannan ya juya ya Kama hanyar gida Ya barta a Dajin tareda Dabbobin, yana tafiya Rabe ta nufi wata Ƙatuwar bishiya dake gefanta ta zauna dan ta huta a nitse ta Ta fara cire Takalmin Robar dake Ƙafarta, tana Gama cirewa ta Jingina da jikin bishiyar bata jima da kwanciyar ba Wani gajiyayyen bacci ya Samu nasarar ɗauke ta sabda Tsabar gajiyar dake tareda ita, kallo daya Zakayi mata ka fahimci tana jin dadin baccin da takeyi.
A hankali iska me daɗi ta fara kadawa Tareda ƙamshin ƙasa wanda hakan ya gauraye a guri guda ƙamshin ya canza zuwa wani yanayi me daɗin gaske, can kuma se aka fara iska me qarfi wadda itace ta zama sillar farkawar Rabe daga baccin datakeyi, a hankali ta daga Dara-Daran idanunta Sama Tana kallon hadarin daya gauraye sararin Samaniya ya koma launin baki aiko da sauri ta mike tafara kada shanun tana fadin su kama hanyar gida cikin harshen fulatanci tayi maganar, nan da nan shanun suka fara tafiya kamar yanda tace musu, suna cikin tafiya Yayyafi ya fara sauka a hankali can kuma se ruwan ya balle kamar da bakin Ƙwarya, A maddin ta nemi maɓoya se kawai ta dinga tsalle tana murna Ruwan na sauka a jikinta tana dariya, Haka nan Ruwan yayiwa Rabe dukan tsiya amma itako ko a jikinta wai an tsikari kakkausa inji 'yana magana lol
Cike da annashuwa take tafiya tana tsalle tana kuma shiga cikin ruwan da ya taru a kan hanya Har Ruwan ya ɗauke Kasancewar kayan jikinta na farin Saƙi ne yasa Duk yayu jajir Sabida jar Ƙasar dake hanya, haka tai ta shiga cikin ruwan dake kwance bisa hanyar tana bin shanun Suka kama hanyar gida, basu jima ba suka iso gida seda ta fara kai shanun cikin garken su sannan ta Ƙarasa inda bukkokin su suke, da gudun ta ta Ƙarasa bakin Ƙofar da zata sada ta da Bukkar matar babanta da sallama ta shiga Ɗakin cikin harshen Fulatanci tace " inna na dawo.
cike da bacin rai tare da tarin tsana take kallonta, cike da masifa tace " Uwar me zan miki da kike gayamin kin dawo shegiya me mugun hali, Zaki fita ko sena fito naci ubanki shegiyar yarinya me baƙin jinin tsiya har yanzu kinƙi auruwa sabida baƙin jininki, uwarki ma a tsiyace ta Ƙare kuma kema a haka zaki Ƙare Tinda kikayo gadon tsiya. Inna ta ƙare maganar tana hucci kamar macijiya
DOWNLOAD HERE👈