BAKAR KADDARA CHAPTER 1

Umma kwata-kwata nawa nake da kaka zai zartar da wannan dan’yen hukuncin a kaina Umma Kaka yarasa dawa zai Hada aure na saida Hamma Faruq”
mutumim daya maida mutane kamar ka’shi mutumin dako Murmushin sa ban taba gani ba Umma tayaya ake tunanin zan iya zama da ba’kin Mugu kamar Hamma Faruq, “Umma wannan wane kalar Bak’ar Qaddara ce wayyo Umma wallahi Allah mutuwa zanyi idan har aka matsa saina Auri Hamma Faruq Umma dan girman Allah kuji tausayi na Umma kumun rai kuje ku fadawa Kaka bana son wannan Auren”
” Wallahi Hamma Faruq yace idan har nabari aka daura auren kashe ni zayyi Umma kina so a kashe maki buddun ki Umma nice fah wacce kikace zaki iya mun komai sabida Ganin nasamu Farin ciki toh meyasa wannan karan kika kasa samar mun Farin ciki Umma”
takare maganar da fashewa da matsanancin kuka hade da kankame Umman nata tana Sa’kin wani kukan me ban tausayi,
cike da tausayawa Umma tafara bubbuga bayan ta tace, “Ayya Buddu na Bawai nakasa samar maki da Farin ciki bane kawai banda yanda zanyi ne anriga da anfi karfi na kuma ke kanki kinsani idan har Alhaji babba yafadi magana babu me canza ta babu meja da maganar shi Kiyi hakuri Buddu kiyi biyayya InshaAllahu zakici riba a rayuwar ki zaki canzawa Faruqu tunani Zaki sauya sa kamar sauran mutane”
InshaAllahu Auren ki da Faruqu Alkhairi ne kiyi shuru ki daina wannan kukan kada ya saukar maki da Zazzabi kinji Buddu na”
Maimakon tayi shurun sai ta kuma fashewa da wani kukan a karo na biyu tana kara kankame Umman ta da Tausayin yar tata yacika mata zuciya tabbas da tanada halin sanyawa a janye maganar Auren da tayi saidai kash batada wannan halin,
Cikin muryan kuka me nuna Alamun mutum yana cikin tashin hankali da kuma tsananin son a taimaka masa ta kuma bude baki a karo na biyu tace,
“Umma duk bagasu Adda Lauratu ba dasu Adda Rukayya meyasa Kaka bai Zaba masu Hamma Faruq ba saini sannan meyasa baice zai aurar dasu ba saini Umma wallahi Allah Kaka baya kauna ta”
Umma Yanzu bazaki iya Taimako naba kinfi son na kasance da mutumin dabai maida dan’adam a bakin komai ba Umma kinfi son nayi Auren da Rayuwa ta zai koma abun tausayi,
Umma Aure nada Hamma Faruq Bak’ar Qaddara ce Umma Kunfi kowa sanin wanene Hamma Faruq mutumin da babu Tausayi a cikin Ransa mutumin da Mugun halin Sojojin yagama Aur…”
Bata kaiga karasa maganar dake bakin taba taji an da’ka mata wani rikitaccen tsawan daya kusa sumar da ita dan hatta Umman ta saida ta tsorata a matukar firgice Buddu ta da’ga manya manyan idanuwa ta,
ta sauke su akan na mahaifin ta wanda tun farin shugowan Shi cikin parlon yagama jin duk maganganun da takeyi,
Nandanan jikin ta yadauki wani matsanancin rawa a hankali ta janye jikin ta daga na Umman , hade da tashi tsaye tana zazzare idanuwa cikin muryan kuka mai ban tausayi ta furta,
“Abbu kamun ra..”
bata ida karasa maganar dake bakin taba ya kuma da’ka mata wani tsawan a karo na biyu hade da nunata da Dan yatsa dan daka kalla fuskar shi zakasan lallai ran maza yabaci yace,
” Fatima Fatima Fatima so nawa nakira ki” bakin ta na rawa tace
“So Uku Abbu”
Umma zubawa sarautar Allah ido kawai tayi tana jiran taji hukuncin da Abbun zai yanke,
jinjina kanshi yayi hade da cewa “na rantse maki da Allah kika kuma fadan mugayen kalamai akan Faruqu sai na mugun bata maki rai sannan yazama dole kiwa mahaifi na biyayya inko ba haka ba gab nake dana cire ki a cikin ya’ya na”
A matukar tsorace ta zaro idanuwa hade da sanya hannayen ta guda biyu ta rufe Bakin ta hade da fashewa da kuka sai tasoma girgiza kai tana ja da baya tace,
“A’a Abbu wallahi bazan taba bijire maka ba koda kuwa hakan yana nufin na rasa rayuwa tane Abbu kayi hakuri ka yafe mun na Amince da Auren Hamma Faruq”
Baiko saurari maganar da Buddu takeyi ba yajuya kan Umma da hankalin ta idan Yayi dubu tofa yagama tashi da furucin da Abbun yayi,
yace “ki sameni a daki”
daga haka yafice daga parlorn ranshi a matukar bace,
Wani kukan me Tsuma zuciya Buddu takara fashewa dashi hade da rugawa da gudu ta wuce dakin ta ta turo kofan da mugun karfi hade da sanya mata key kana ta Tsulale kasa ta fashe da wani kukan me ban Tausayi,
Umma tana shiga dakin ta tadda shi a zaune a bakin gado idanuwan shi sunyi jajawur dasu sai kace wanda yayi kuka,
A matukar tsorace Umma takarasa inda yake ta zauna a gefen shi hade dakai hannu ta dafa dukkan kafadun shi kana tace,
“Abbun Buddu kayi hakuri tabbas nasan Buddu tayi laifi amma ta nemi yafiyar ka kuma idan har mukace zamu dinga nuna mata bacin ranmu mu kanmu baza muji dadin hakan ba sabida Buddu ya’ce me matukar biyayya tun taso wanta bamu taba sata abu ta mana gardama ba”
Wa’insu hawaye ne masu matukar Zafi suka soma gangarowa a fuskan Abbu ai nandanan Umma takara tsorata dan bakaramin abu yake sanya Abbun kuka ba ko hawaye ba bakin ta har rawa yakeyi wajen furta,
“nashiga uku kadadai ace sabida Buddu na kake zubda hawayen ka Abbun Buddu Dan Allah kadaina zubda hawayen ka akan Yarinyan nan tun kafin bakin ka yakamata”
Girgiza kai Abbu yayi hade da kallon Umma kana yace,
“Ba saboda Buddu na tabata mun rai nake zubda hawaye ba saidan sanin da nayi Faruqu bai dace da yarinya salihar kamar Buddu naba yarinyan da hayaniya bai dabai taba yarinyan da bata san yanda ake fada ba, tabbas ina jin tausayin Buddu na kuma nasan Alhaji babba bai mata adalci ba saidai shi kadai yasan dalilin hada wannan Auren wanda har cikin zuciya na bana kaunar Hada wannan auren daza ayi sabida sanin danayi Faruqu sam baida isasshen tarbiya mutumin dani kaina ba gaisarwa yakeyi ba baya ganin daraja na a matsayi na, na kanin mahaifin shi, sannan babban damuwa na bai wuci zaman da Buddu zatayi a garin da batasan kowa ba”
“Bakomai yasa nama Buddu ihu hade da barazana ba saidan kada ta bijirawa umarnin mahaifi na sannan ina son ko bayan Auren ta tama mijin ta biyayya kada bakin ta yasaba da furta muggan kalamai wa mijin ta”
Murmushin karfin hali Umma tasaki hade dacewa,
“Haba Abbun buddu meyasa zaka dinga kalamai irin haka Addu’ar mu kadai Buddu take bukata kuma InshaAllahu ina saka ran Buddu tazama silar canzawan Faruqu”
Cikim dauriya da kuma yaba hankalin matar tashi yace, “Allah yasa yakuma miki albarka”
Murmushin jin dadi tasaki hade da kwanciya akan kafadun shi tana fada mai kalamai masu kwantar da hankali.
A bangaren Buddu nandanan wani Mugun Zazzabi yakamata tuni tafara rawan sanyi hade dafara kwara amai dan ita ba wuya idan har tayi kuka tofah da wuya Zazzabi bai kama taba.

Adda Buddu Adda Buddu ki bude kofan Adda Rukayyah na Kira cewan wani dan karamin yaro da bazai gaza shekaru goma ba,
Buddu dake yashe a kasa Dakyar ta iya kai hannun ta tabude kofan hade da kara zubewa a kasa a matukar galabaice,
Ganin halin da buddun take ciki ne ya sanya yaron fasa ihu hade da kwala kiran sunan Umma da sauran mutanan gidan,
Kuka kawai yakeyi har Su Adda rukayya suka karaso dakin suma ganin halin da Buddun take ciki ne yayi matukar da’ga hankalin su kuka suke wiwi kamar wa’inda akace masu ta mutu,
Umma da Abbu suma a matukar rikice suka shugo dakin saidai ganin halin da Buddun take ne ya sanya Umma fashewa da kuka hade da zubewa a kusa da Buddun da take yashe kamar wata matatta,
Sosai hankalin Abbu yatashi dan duk cikin ya’yan sa yafison Buddu dan ita yarinya ce me matukar shiga rai,
Dakyar yasamu karfin halin kiran family doctor dinsu,
Kafin Doctor din yakaraso tuni Adda lauratu da Adda Rukayya suka gyara mata jiki hade da sauya mata kaya sannan suka kwantar da ita akan gado,
Nanfa gabaki daya mutanan gidan suka taru a kanta suna mata kuka dan sun san ciwon Buddu baida kyau ko kadan dan duk sanda ciwon ta yatashi kaf’kaf dinsu basuda kwanciyar hankali har sai taji sauki,
Wayar Abbu dake hannun shine tafara ringing cikin hanzari yayi picking hade dacewa,
“DOCTOR kashugo kawai muna dakin Buddu”
Sannan yakatse wayan ya zubawa Buddu ido yaga lokaci guda ta rame tayi wani fayau da ita daman gata ba auki ba,
Doctor yana karasowa duk suka mimmike suka tsaya shi kuma yakarasa gadon da Buddun take kwance yahau duba ta,
Umma Zubawa Buddu ido kawai tayi danji takeyi kamar zasu rasa tane dan tashin ciwon Buddu shine babban tashin hankalin su Shiyasa basuyin abunda zai bata ranta,
Doctor yana gama yan dube duben shi yakai duban shi gunda Abbu yake tsaye yace,
“Alhaji wato bawani abun tada hankali bane danba ciwon nata bane yatashi kawai Zazzabi ne hade da damuwa saidai Dan Allah ayi kokarin ganin tacire wannan damuwar a cikin ranta inba haka ba zai iya shafan lafiyar ta Allah dai yabata Lafia”
Yakare maganar da curo wani dan takarda ya rubuta masu magungun nan da za’a siyo mata sannan ya mikawa Abbun,
tare da Doctor din Abbu suka fita har zuwa farfajiyan gidan sannan Abbu ya sallame shi hade da juyawa ya koma cikin gida,
Kai tsaye dakin buddun ya koma yace masu Adda rukayya su wuce dakin su, su barta tahuta har zuwa lokacin da zata farka,
Adda Lauratu da itace babban su gaba daya tace,
“Abbu Dan Allah a janye maganar auren nan tun kafin sanadin haka mu rasa Buddu”
Takare maganar da matso hawayen da suke makale a cikin idon ta”
Girgiza kai Abbu kawai yayi shi kanshi da yanada ikon hana Auren nan daya hana tau Amma ba shida wannan ikon dan shi kanshi karfin Hali kawai yakeyi amma shi kadai yasan kalar halin da yake ciki,
ganin Abbun nasu baice komai bane ya sanya su ficewa daga dakin,
Sai dakin ya rage daga Umma sai Abbu dake tsaye sai kuma Buddu dake kwance akan gado tana bacci da alama kuma tana jin jiki sosai,
karasawa inda Umma take Abbu yayi hade dakai hannun shi yahade ta da jikin shi yashiga rarrashin ta maimakon taji sauki a cikin ranta sai ta kuma fashewa da wani sabon kukan tace,
“Buddu na nawa take da zata fara fuskantar matsala a rayuwar ta yarinyan da bata wuci sha bakwai ba meyasa Alhaji babba zai za’bi Buddu yabar sauran yaran dangi tabbas nasan a zalunce Buddu na saidai kawai mu mata addu’ar samun rayuwa me albarka da kuma jin dadi a gaba”
rarrashin ta sosai Abbu yakeyi harya samu tayi shuru hade dace mata subar Buddun ta huta har zuwa lokacin da zata farka,
Dakyar Umma ta iya barin dakin dan gani take kamar tana barin dakin Buddun zata tafi tabar su,
“JIMETA da kaifa nakeyi kayi shuru bafa nason wulakanci wallahi sai na tashi na tafi bazai yuyu ka kira niba sannan nazo ina magana kana banza dani daman kasan yan miskilancin suna kanka ka kirani ”
sai yakare maganar da jan tsuka yamike tsaye yana shirin barin dakin,
Cikin wani yanayi dake nuna alamun mutum yana cikin matsanancin bacin rai da kuma damuwa yabude bakin shi dakyar yace,
“Alamin can you believe that Alhaji babba aure zaimu and the most painful yarasa dawa zai hadani saida yar ciki na can you imagine Buddu yar wajen Ba!ah Hassan zan aura yar ciki nafa”
Sai ya kuma maimaita maganar yana wani sanya hannayen shi a cikin sumar kanshi yana barbaza su,
Sosai Maganar ta daki Alamin shiyasa yakoma inda Jimetan yake yasamu wuri ya zauna,
Hade da cewa “Jimeta stop kidding me please ba zaima yuyu bane ace wannan yarinyan zaka aura tau me take dashi aiba mace bace har yanzu”
cikin kunan rai Jimeta yakuma bude bakin shi a karo na biyu yace,
“I’m marriyin that rat no no impossible kwata-kwata nawa take me take dashi menene abun dazan gani a jikin wannan rat din yarinyan da nayi imanin ko Two couples basu gama bayyana a kirjin taba balle kuma akai ga manyan, wallahi tallahi tsohon nan ya cuceni kuma sai Allah yabimun hakki na”
“Na rantse maka da Allah Alamin idan har suka bari aka kawo wannan rat din cikin gida na wallahi sai na mata wulakancin dasai sun gwammace basu daura auren ba saina dan’dana mata azabar dazai sanya tabar gidan da kafar ta saina azabtar da ita”
Yakare maganar da dukan cinyar shi hade da sakin wani huci me zafin gaske,
Hannu Alamin yakai yadafa shi kana yace,
“Jimeta relax kaifa jarumi ne kada mana dan wannan abun yatada maka da hankali”
Sannan yakai hannun shi cikin aljihun wandon shi yacuro Cigarettes guda daya hade da kunna ta yamika mashi,
Cikin kwarewa Jimetan yake Zukan Sigarin yana wani tada hayaki,
saidai harya gama zukan sigarin baiji hankalin shi ya kwanta Ba shiyasa kawai ya mike yakarasa yadauko babban Bottle din beer ko jiran Cup bayyi ba yabude yakafa ta yafara kwalkwala,
Tuni yafara wa’insu surutai marasa kan gado,
I promise i will make ur life miserable Buddu saina mai dake abun kwatance sai Aure yafice a cikin zuciyar ki saina illata Rayuwar

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *