BAKIN DARE CHAPTER 10

BAƘIN DARE 
CHAPTER 10
Alhaji Bala wani irin murmushi ya ringa yi shi kadai a lokacin da yake bin ko ina da kallo yana hararo irin dukiyoyin da zai tafi dasu 
Lion da Killer a tare suka dawo palon a gigice suna “oga babu kowa fa a gidanan babu inda bamu duba ba” 
Adai dai lokacin da Akram da black suma suka fito daga d’aya d’akin dake cikin palon suma suna “Oga wlh mun duba ko ina babu alamar mutane a gidan ballantana kaya” 
“What”!!!! Alhaji Bala yace yana mikewa hankalinsa a tashe a tsawace yace ” spread yourself and check every where ina zasu je sai Dana samu information sosai akan Alhaji Buba mai gwala gwalai kafin mu taho” Da Sauri suka kara raba Kansu suna duba ko ina Akram kuwa kamar gaske har da cilli da duk abinda ya gani 
Alhaji Bala bin bayansu yayi hankali a tashe yana kuma following description d’in da 
Sharon ya tura masa na gidan sai gashi har a bedroom d’in Alhaji Buba mai gwala gwalai 
babu inda basu duba ba babu kowa kuma babu abun d’auka sune harda duba su drawer 
da karkashin gado 
Jikin Alhaji Bala ne ya dau rawa yana tunanin ko dai Sharon ne ya sanar dasu zasu zo shiyasa suka gudu suka bar gidan idan ba haka ba ya akayi suka San zasu zo 
Rai a mutukar bace yace cikin kakausar murya “Ku wuce mu tafi inaga ya Riga da yasan da 
zuwan mu” 
Akram wani irinjuyowa yayi in serious mode yana “waye zai gaya musu zamu zo yanzu haka zamu zo mu tafi bamu samu komai ba” 
Alhaji Bala da zuciyarsa ke tafasa bai samu sararin bashi amsa ba sabida bacin rai ya sa kai ya bar palon da sauri suka Mara mishi baya 
Akram kuwa yayi ta godewa Allah aransa yana “soon zaka zo hannu dan iska kawai” 
Indai zasuje operation black ne ke Jan motar amma Alhaji Bala da kansa yaja motar sai gudu yake falfalawa Su Killer dai kallonsa kawai suke Dan sun San ransa a bace yake wani daji ya yanka da basu San dashi ba yana ta kutsawa ciki suna taso su tambayeshi suna tsoro 
Parking yayi awani kofar gida ya fito a fusace su killer suka Mara mishi baya da sauri,, Alhaji Bala buga kofar yake kamar zai balla kofar 
Sharon dake kwance shi da buduruwarsa suna bacci a Firgice suka tashi jikinsu na rawa suka kankame juna suna Neman wajen buya 
Alhaji Bala ganin babu alamar za’a bud’e gidan ne yasa ya kalli Lion atake Lion ya gane mai yake nufi ya dalle katangar gidan tare da dira ciki ya bude musu k’ofar Akram kuwa hankalinsa ne ya tashi yafara tunanin mai suka zo yi a gidan Allah yasa ba wani muguntar Alhaji Bala zai yi ba adai dai lokacin da suka shige suna bin Alhaji Bala a baya 
Akram sai addu’oi yake aransa 
Bugu daya Alhaji Bala yayi wa kofar dakin Sharon ya Bude 
Sharon da buduruwarsa harfitsari suka saki awando sabida tsorata da sukayi 
Sharon kuwa ganin Alhaji Bala ne da yaransa yasa ya sauke ajiyar zuciya yana dafe kirjinsa yana “Oga Ashe kai ne ai da ka kirani awaya wlh ka tsorata mu” Wani mugun tsawa Alhaji Bala ya daka mishi yana “Ni zaka Yaudara Sani ni zaka ciwa amana nasaka ka aiki na biyaka kudinka a karshe ka zagaye kaje ka fad’awa Alhaji Buba akan ya gudu yabar gidan za’a zo ayi mishi sata ko” 
Sharon jikinsa ne ya hau rawa cikin in ina ya fara girgiza kai yana “wlh tallahi ban gaya mishi komai ba karka manta Oga ba yau na fara maka irin wanan aikin ba” 
Alhaji Bala ransa a bace ya nufi wajen Sharon a tunzure ya shako vest dinjikinsa ya hada
shi da bango yana “u would pay for all I loss babu Wanda ya isa yaci amanata na kyalle shi” Akram Sallati kawai yake a cikin ransa dan yasan sai Alhaji Bala ya kashe Sharon 
Alhaji Bala a tsawace ya kira sunan Akram yana “Shoot him” Sharon kuwa ya zube a kasa ya rike kafar Alhaji Bala yana rokon shi Akram kuwa jikinsa ne ya dauki mugun rawa Dan bazai iya kissan kai ba shima yasan rashin Harbin zai sa asirinsa ya tonu Dan Alhaji Bala yace indai suka kara fita operation sai yayi kisan kai idan yaki kuma Alhaji Bala zai dago shi 
Wani tsawan Alhaji Bala ya kara buga mishi yana “ka Harbeshi nace kana bata min lokacin Akram daga bindigar yayi duk da yasan ba iya Harbin zai yi ba Hannunsa sai masifar rawa yake adai-dai lokacin da buduruwar Sharon ta tafi da gudu ta fada jikin Sharon tana “please don’t kill him he is the only one i have pls I beg of you sir” 
Da yake buduruwarsa Yoruba ce kuka take sosai tana rungume da Sharon da jikinsa ke rawa gumi na keto mishi ko ta ina 
Wani irin bakin ciki ne ya rufe Alhaji Bala yace a tsawace “Akram shoot the both of them before counting of two” 
Akram jikinsa ne ya cigaba da Rawa shima take ya jike da Gumi Alhaji Bala kuwa ya nufi wajen Akram yana “zan harbeka wlh ka Harbesu Nace” 
Alhaji Bala yace yana buga kafarsa da kasa 
Buduruwar Sharon kuwa sai ihu take Tsabar rawar dajikin Akram keyi bindigar subalewa yayi daga hannunsa Alhaji Bala ya dauki bindigar hannunsa ya bugawa Akram akai sau biyu 
Akram ya saki wani gigitacen kara a lokacin da jini ya wanke mishi fuska tare da faduwa kasa Alhaji Bala ya juya a fusace ya sakarwa Sharon bullet akai sau biyu ya sakarwa buduruwarsa a kirji 
Kana nufin Kana cikinmu bazaka iya kashe mutum ba sau nawa zan gaya maka aikinmu babu imani babu imani sau nawa kake so na gaya maka this would be the first and last da zan saka ka kayi Abu kaki yi wlh if u try it again I would kill you”. Yace yana wurgar dashi tare da yin waje 
Lion yayi sauri ya taro shi Akram ya rikeshi sukayi waje kansa kamarya fado 
A ranar Sam Alhaji Bala bai yi bacci ba bakin cikin kudin da bai samu ba da abincin da bai 
ci ba kawai yake acan k’asan ransa kuma yana mugunjin haushin Akram 
A daren ya fara tunanin gidan Wanda zai kuma zuwa acikin garin kano a gobe da zai samu 
makudan kudi 
Bangaren su Saiam kuwa tunda aka daura Auren Saiam da Fawazz Safna da Faisal suke iya kokarinsu wajen kwantar musu da hankali da faranta musu rai ta hanyar zuwa gidan su hadu gabadaya a Palon gidan suyi tajansu da hira hardasu Samha 
Hakan kuwa ba laifi ya taimaka wajen kwantar musu da hankali Dan su Samha gani suke tamkar ‘ya’yyensu ne su Fawazz Hakan kuwa ba karamin dadi yayi wa Alhaji Nazifi ba dan yaran nashi sun dan fara farfadowa ba kamar da ba duk da kullum cikin dare in suka zo kwanciya a cikinsu sai wata ta zubar da hawaye sabida Hajiya Nafeesa lokacin da take raye kafin su yi bacci sai tazo ta tayasu hira idan sunyi bacci ta tofesu da addu’oi takan lekosu sau daya biyu kafin gari ya waye basu tunaninta ma su zubar da hawaye sai sunzo kwanciya kullum cikin tsinewa Alhaji Bala suke suna tashin dare akan Allah ya tona mishi asiri Duk da Nazifa wata cousin d’in Alhaji Nazifi da mijinta ya rasu shekara uku da suka wuce itama tana bakin kokarinta wajen ganin tana debe musu wanan kewa daddare hakan bai sa sun kasa tuna mahaifiyarsu ba 
A ranar da akayi sadakar Arbain tamkar aranar akayi rasuwar sabida yanda aka cika gidan Alhaji Nazifi inda mutuwarta ya kara dawo musu sabo fil addu’oi kawai ake bin hajiya Nafeesa dashi ana fad’ar kyawawan halayenta Alhaji Nazifi kuwa aranar har da dan 
zazzabinsa 
Bayan kwana uku da akayi Arbain din Hajiya Nafeesa aka fara shirye shiryen tariyar Saiam Safna inda hankalinsu ya tashi gabadaya in banda kuka babu abinda suke yi Dan basa so su rabu da juna ko kad’an ganin junan da suke yi yana dan rage musu kadaice 
Da kuka da kyar aka banbare su Samha daga Jikinsu Saiam a lokacin da aka zo tafiya dasu gidan mazajensu Alhaji Nazifl ma sai da ya koka sosai aka rasa wanda zai rarrashi wani a cikinsu 
Aranar babu Wanda ya runtsa a cikinsu dan gidan wani irin girma da fadi ya kara yi musu 
lnda bangaren amaren amadadin amarci angwayen kwana sukayi suna aikin rarrashi dan Saiam har da zazzabi 
Wasa wasa sau Hud’u Alhaji Bala ya na fita operation inda suka je babu abinda suke samu gidan empty suke samun shi nan kuwa aikin Akram ne dan yana fada musu inda zasu je 
operation zai yiwa Ogansa Abdullahi text message duk da Alhaji Bala yasa mishi ido sosai dan haka kawai yafara dorawa Akram karan tsana a 
Aranar da Alhaji Bala yaje gidan wani Alhaji Tahir Hamshakin mai kudi daya tada kai Alhaji Bala baije gidan ba sai daya tabbatar da akwai kudi a gidan kuma iyalansa na nan da confidence dinsa ya hada Kansu Killer sukaje suna zuwa suka tarar da gidan wayam babu kowa ballantana a samu abun dauka 
Jikin Alhaji Bala ne ya hau rawa hankalinsa a matukar tashe yana mamakin abinda ke faruwa dashi ji yake kamar ya zauce 
Su Killer kuwa tuni hankalinsu ya tashi suka fara zargin duk yanda akayi an fara ganosu idan ba haka ba ya akayi duk inda suka je basa samun kowa 
Zaman dirshan Alhaji Bala yayi a kasa ya dora hannu aka yana tunanin abinda ke faruwa dashi take mai gida ya fado mishi arai da a lokacin da yake raye ne da yanzu ya fada mishi abinda ke faruwa dashi yanzu wa zaije ya samu baya San zuwa wajen Na maliya dan bai San mai zai ce ya bashi ba a ladan aikin da ya mishi Hajiya Nafeesa ta daina zuwar mishi to ya zai yi dolensa dai yaje wajen nasa dan shi kadai zai iya gaya mishi abinda ke faruwa dashi da duk inda yaje baya samun abinda yake so  wanan tunanin ya shirya da sassafe bayan ya sallami su Killer yace zai musu waya ya dauki hanyar sokoto 
Yana isa wajen Na Maliya yafara arba da ruwa mai yawa yana ambaliya kamar zai yo kansa a tsorace yaja ya tsaya yana ganin yanda ruwan ke yowa kansa baya ya fara yi da sauri adai dai lokacin da ruwan ya b’ace bat sai ga Namaliya agabansa sai yawo yake a saman ruwa fuskar nan tashi a murtuke Gaban Alhaji Bala na faduwa ya zube a kasa kamar zai mishi sujadda bai d’ago ba Na maliya ya fara magana cikin wannan irin murya yana “Kura kana wasa dani ya mukayi dakai” 
Jikin Alhaji Bala na rawa yace “Kayi hakuri nayi maka laifi Allah ya huci zuciyarka yanzu ka fadamin ladan aikina ko menene k0 nawane zan bayar akwai kuma wani gagarumin matsala dake tafe dani” 
Wani Mahaukacin Dariya Na Maliya ya fashe dashi sai da yayi dariyar na wajen minti goma kafin ya tsagaita yace “ya zama dolenka ne ka bayar da ladan aikin da nayi maka idan ba haka ba sai ka gwammaci ace mutuwa kayi da ace kana rayye bazan kuma saurararka ba har sai ka biya ladan aikin Dana maka da farko kafin na Saurareka” 
Alhaji Bala jiki na rawa a tsorace yace “menene Ladan aikinka”? Na Maliya dariya ya kara fashewa dashi yace ” ladan aikina shine ka kawo min Naila in ba Aljanina dan Saurayi ya huta da ita na wata uku bayan wata uku kazo ka dauketa” 
Alhaji Bala bai San lokacin da ya mike tsaye ba yaji kamar guduma ake kwada masa akai kirjinsa kuwa kamarya fado cikin inina yace “Na Maliya bazan taba iya baka Naila ba Dana baka ita gwara ni ka kasheni banida sama da ita arayuwana zan iya sadaukar da komai nawa sabida ita Haba Na Maliya ya za kayi min haka dan Allah ka fadi wani abun na baka ni ko Mahaifiyata ce ma dan Allah banda Naila” 
Murya a kaushashe Na Maliya yace “baka isa ba dan Dana maka aikin sai Dana baka sharadi ka kuma yarda dan haka dole ka kawo min ita nan da sati daya ko kuma duk abinda ya biyo baya kai ka siya da kud’inka dan sai ka nemi mutuwa ma ya daukeka sabida tashin hankalin da zan jefaka a ciki 
Alhaji Bala zubewa yayi a kasa take hawaye ya hau wanke mishi fuska yace ” Na Maliya ka rufa min asiri karka min haka dan Allah zan kawo maka Mahaifiyarta zan kawo maka Mahaifiyata amma dan Allah banda Naila dan Allah ka taimaka min wlh Naila yarinya ce shekararta goma sha biyar” 
Na Maliya Wani Mahaukacin dariya ya kara kwashe wa dashi yace “ko matan duniyan nan zaka bani bana so Naila nakeso ka kawo min idan ba haka ba duk abinda ya biyo baya kai ka siya da kud’inka na baka nan da Sati daya ka kawo min ita” 
Bat Na Maliya ya bace Alhaji Bala ya saki wani gigitaccen kara yana “wlh bazan iya ba Na Maliya bazan iya baka tilon ‘yata ba gwara ka kasheni Dana baka ita” 
A haka Alhaji Bala ya kwanta a k’asa yana ihu da kururuwa akan bazai iya bawa Na Maliya ‘yarsa ba sai da yaga wajen ya fara duhu sosai ya mike ya bar wajen sai kuka yake kamar 
wani karamin yaro ….. Hmm Alhaji Bala yaga ta kansa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *