BAKIN DARE
CHAPTER 19
Bangaren Akram kuwa yana ta tunanin yanda zai fuskanci Alhaji Nazifi yace mishi babu wacce tayi mishi a cikinsu so d’aya tak Samha yake yiwa Yazeed babu yanda bai yi dashi ba akan ya hakura da Samha yace Sam idan ba Aure ko mutuwa tayi ba babu abinda zai sa ya hakura da ita dan duk addu’oi da istahara da yake yi akan Allah ya mishi zabin da yafi Alheri Samha yake gani a matsayin matarsa kuma yana ji a jikinsa Samha matarsa ce ahaka dai ya daure akan zaije ya samu Alhaji Nazifi ya gaya mishi halin da yake ciki Dan kar yaji shi shiru
Bangaren su Samha kuwa washegari Alhaji Nazifi na fita Suhaima ta hau tambayar Samhar data tasa breakfast dinta agaba ta kasa ci sabida tunanin Akram akan me yake damunta haka take tunani kwana biyu bata gane mata
Samha d’aurewa tayi ta saisaita kanta Dan kar su dagota tace musu babu komai kawai Mummy ce ta fado mata abunka da Wanda yakejiran kiris take hawaye ya hau zubo mata
Saheeba ta guntsa dariyar data taho mata dan tasan karya Samha take yi San Akram ke dawainiya da ita
Suhaima kuwa tab’e baki tayi tace ta dai fadi gaskiya ba abinda ke damunta ba kenan akwai dai wani Abu da take boyewa yake nukurkusarta a zuciyarta
Samha kuka ta fashe dashi tana ita babu abinda take boyewa daga haka ta mike da gudu tabar palon ta nufi d’akinsu
Suhaima harara ta bita dashi tana ce mata munafika Saheeba kuwa sai Dariya take dan tasan zallar yarinta ke damun Samha
Aranar hawan jini ne kawai basu sawa Samha ba Dan har daki suka bita suna hirar Akram kowace na cewa Allah yasa ya zabeta har suna fadar irin San da suke mishi Samha kuwa
duk inda ta kai ga San ta daure sai da ta fashe da kuka Dan ji tayi gwara su rufeta da duka akan maganganun da Sukeyi su kuwa sai dariya suke aransu
Bayan kwana biyu Akram ya shirya shi da Yazeed suka nufi gidansu Samha Dan ya gayawa Alhaji Nazifi gaskiyar abinda ke ransa daga nan kuma ya shigar da maganar yazeed akan San da yake yiwa Saheeba
Har palon Saukan baki aka sauke su Akram dan Alhaji Nazifi yasan da zuwansu sai da ya leka d’akinsu Suhaima yace su shirya bakonsu yaZo duk wacce ya zaba a cikinsu ta
karbeshi da hannu bibiyu
Samha da bata da aikin Da ya wuce kwanciya da tunani tabi ta rame tayi zuru zuru sabida tunani wani irin mikewa tayi kirjinta kamar ya fado k’asa dataji abinda Alhaji Nazifi yace
Su Suhaima kuwa da gangan suka nuna farincikinsu a flli Dan so suke Samha tayi admiting
tana San Akram da kanta
Alhaji Nazifi halin da yaga Samha a ciki ne yasa ya zuba mata ido yana “Baby Laflya kuwa
mai ya sameki”?
Samha kuka ta fashe dashi Alhaji Nazifi yayi Sallati yana nufar inda take hannyenta ya ruko yana tambayarta abinda yake damunta kamar kara zugata yayi ta kara volume din kukanta Dan agaskiya bata jin zata iya shiru ta cutu gwara ta gayawa Alhaji Nazifi halin da take ciki
Su Suhaima kuwa ido suka zuba mata sunajiran suji mai zatace
Aikuwa Hakan data gani yasa ta sadda kanta k’asa tana tunanin yanda zata fito ta gaya musu halin da take ciki
Alhaji Nazifi kuwa ganin taki magana ne yasa ya mike ya kalli Suhaima yace tazo ta tambayeta abinda yake damunta zaije wajen su Akram kar ya bata musu lokaci
Samha tuni hankalinta ya tashi Dan tasan idan ba Fitowa tayi ta ajiye kunya da jin nauyinsu a gefe ba zata kwari kanta Akram yayi mata Nisa
Da Sauri ta tsayar da Alhaji Nazifi dake dab da ficewa daga dakin tace “ Daddy” Alhaji Nazifi juyowa yayi yana kallonta
Samha kuwa tayi sauri ta sunkuyar dakanta haka kawai kuma taji wani irin kunya da nauyinsa ya rufeta
“Ya akayi Baby”?
A hankali ta daga kanta ta kalli su Suhaima da suka kura mata ido tayi sauri ta maida kanta
ta sunkuyar gabanta na faduwa
Alhaji Nazifi kuwa ganin tana bata mishi lokaci yasa yayi tunanin shagwabar tane ya motsa tsaki yayi yajuya zai bardakin yaji siririn muryar Samha na cewa ” Daddy wlh ina Sansa ina kaunarsa”?
A mamakince ya juyo Dan ya gaskata abinda tace yana juyawa yaga ta mike dagudu ta shige bandaki ta kulle
Suhaima da Saheeba kuwa dariya suka kyalkyale dashi suna tsokanar Samha akan data
tsaya girman kai taga ikon Allah
Alhaji Nazifi kuwa maida kallonsa kansu Saheeba yayi Dan su mishi Karin bayani aikuwa suka hau bashi labarin irin San da Samha keyi wa Akram
Hamdala Alhaji Nazifi ya runga yi a zuciyarsa Dan Yasan Akram zaiji dadi idan yagaya mishi Samha ta amince girgiza kansa yayi cikin farinciki ya daga muryarsa yanda Samha zata jiyo
shi yace “ai da kin tsaya girman kai kiga yanda kwado zai miki kafa”
Samha kuwa dafe kirjinta tayi tana mamakin yanda akayi Kalmar ta fito daga bakinta wani irin kunya da nauyin Alhaji Nazifi da su Saheeba ne ya rufeta ita da ta gama cika baki bata San sa sai gashi babu kunya babu tsoron Allah ta bude baki tace tana San sa ahaka ta makale a band’aki ta kasa fitowa
Su Suhaima kuwa sai tsokanarta suke suna kwaikwayar muryarta lokacin da tace bata San shi
Alhaji Nazifi kuwa yana zuwa palon da su Akram suke suka zub’e a kasa suna gaishe shi wani irin kunya da Nauyin yanda zai ce mishi baya San su Suhaima ne ya rufe shi
Alhaji Nazifi kuwa yana lura da yanda Akram ya takura kansa yaki d’agowa murmushi yayi ya kira Sunan Akram
Akram ya dago yana kallonsa ce mishi yayi kar ya damu yasan yanajin nauyin ya fada masa baya San su Suhaima kar ya damu matar mutum kabarinsa Allah ya Riga da ya tsara
Samha rabonsa ce dan ta amince zata Aure shi
Akram sakin baki yayi yana kallon Alhaji Nazifi dan badan yasan babu ‘yar wasa a tsakaninsu ba da sai yace wasa yake masa
Yazeed cikin tsananin farinciki yace Alhamdulillah amma munji dadi
Akram kuwa fad’ar farincikin daya tsinci kansa a ciki b’ata bakine dan kasa rufe bakinsa yayi da ace Alhaji Nazifi baya nan babu abinda zai hana shi taka rawa
Alhaji Nazifi kuwa addu’a Ya musu na Allah ya tabbatar musu da Alheri ya mike zai tafi Akram yayi sauri ya dakatar dashi yana sunkuyar da kai dan so yake ya mishi maganar Yazeed dan tundazu yake mitsininsa
Farinciki Gaza boyuwa yayi a fuskar Alhaji Nazifi bayan Akram ya fada mishi Yazeed na San ‘yarsa da ta kawo musu ruwa ran nan
Alhaji Nazifi tambayoyi yayi wa Yazeed akan family dinsa da irin aikin da yake yi
Aikuwa ya samu gamshashiyar bayani akan family dinsu Yazeed dan kanin Mahaifin Yazeed abokinsa ne tare sukayi secondary school addu’a ya kara musu na fatan Alheri suka ringa
mishi godiya ya mike yace bari ya turo su Saheeba
Yana fita Akram da yazeed suka rungumajuna suna murna Akram kamar ya jawo Samha gabansa yayi ta kallonta haka yakeji sai kallon bakin kofa yake yaga ta inda Samha zata bullo
Alhaji Nazifi kuwa d’akinsu Samha ya nufa fuskarsa d’auke da murmushi har a lokacin su
Suhaima maganar Samha suke Samha kuwa na makale a bandaki Alhaji Nazifi tambayarsu yayi inda Samha take suka ce mishi tana bandaki taki futowa
Kwalla mata kira ya fara yi Samha kuwa kamar ta nutse dan kunya dakyar ta bude kofar
bandaki tafito kanta a sunkuye
Alhaji Nazifi murmushi yayi yace “jaira kawai ana so ana kaiwa kasuwa maza shirya kije gashi can a Palon baki yana jiranki Saheeba kema kije kina da bako idan kin dawo zan miki bayani akan shi”
Daga haka yasa kai ya fice daga d’akin
Yana fita Suhaima ta rangada gud’a tana sun kusa shan biki Saheeba kuwa tunda yace taje tayi bakojikinta ya hau rawa dan bata taba tsayawa da Saurayi ba da taimakon Suhaima suka shirya duk da Samha nonokewa take yi Suhaima kuwa sai tsiya take mata har bakin kofar palon ta rakasu tajuya
Dukansu sanye suke da dogwayen riguna iri daya sai dai bambamcin kala na Samha bakine na Saheeba kuma Pink
Samha kuwa sai data rufe fuskarta rufjikinta na dan rawa har suka isa palon dasu Akram suke
A tare suka amsa sallamar da sukayi musu Akram kuwa ya zubawa Samha ido da ta rakube
a bakin kofa kanta a sunkuye ‘ Wani wawan ajiyan zuciya ya sauke daya sa sai da Yazeed ya dago ya kalleshi
Saheeba ce tayi karfin halin gaishe su dan Samha sabida rawar da jikinta yake yi ta kasa buda bakinta
Yazeed ne ya amsa sabida hankalin Akram na kan Samha dake neman shigewa kasa
Sai a lokacin Saheeba ta d’aga kanta suka hada ido da Yazeed gabanta ne ya yanke ya fadi take itama jikinta ya hau rawa
A takaice aranar zancen kurame akayi su Akram ne kawai suka ringa kidansu suna rawarsu
dan su Samha basu taba tsayawa da namiji da sunan zance ba
Kasan zuciyar Samha kuwa duk fitar maganar Akram sai taji kamar kara rura mata wutan
San shi ake a zuciyarta ake
Saheeba itama tunda ta hada ido da Yazeed taji ya kwanta mata aranta
Akram babu yanda baiyi ba dan yaga fuskar Samha amma fir Samha taki buda mayafin
data rufe fuskarta dashi akan dole ya hakura dan ko magana taki tayi mishi Sai wayarsa ya mika mata da tasa mishi number ta ta mike da sauri tabar palon
Yazeed shima lambar Saheebar ya karba dan itama kunya ya hana ta sakijiki suyi hira
Tundaga lokacin soyayya mai zafi ya shiga tsakanin wannan masoya kowace kullum tana
makale da waya a kunne idan kuwa basa waya to suna musayar messages
Suhaima itama tuni ta fara kula wani Saurayinta Khaleed da bata bashi fuska ada itama ta shiga sahun su Samha
A cikin kankanin lokaci manya suka shiga maganar kafin kace me ankawo kudin Aure dasa rana lokaci guda aka sa ranarsu Suhaima nan da wata uku masu zuwa Wanda yayi dai dai da gama exams d’in Samha
Akram da Samha kamar su hadiyejuna sabida so duk da a filli idan yazo bata wani nuna mishi so sabida kunyar shi da takeji amma idan a waya ne ko a chart tayi ta nuna mishi irin San da take mishi
Watarana yazo zance shi da Yazeed yana tayiwa Samha hirar bikinsu da yanda zai kasance Samha kuwa murmushi kawai take mishi bata cewa komai aranar kasancewar bakin kaya ne ajikinsa haka kawai bakin Daren da suka zo gidansu da Alhaji Bala ya fado mata Wanda hakan ya dan sa gabanta fad’uwa tare da kura mishi ido
Akram tsayarda maganar da yake yi yayi dayaga yanda ta kura mishi ido ya kirata da Sunan da yake kiranta dashi yace “Soulmate lafiya kuwa kike kallona haka“?
Samha kuwa take hawaye suka hau tsare a kumatunta data tuna Hajiya Nafeesa da jajircewar da tayi dan kar a keta musu haddi
Kau da kanta tayi daga kallonsa ta cigaba da zubar hawaye Hankalin Akram kuwa idan yayi dubu ya tashi a gigice ya hau tambayarta abinda ya faru
Samha kuwa ta kasa magana sai hawaye dan kamar a faifai take hango duk abinda ya faru
D’aga idanuwanta da suka rine suka koma tamkar garwashi tayi ta zubawa Akram da
jikinsa ya fara rawa yana tunanin abinda ya sata kuka
Murya a dakushe tace “Akram Mummy na tuna Kissar gillar da Alhaji Bala yayi wa mahaifiyata a wannan Bakin Daren na tuna da ace Mahaifiyata na Raye babu Wanda zai kai ta farincikin Aurenmu bata da burin daya wuce taga ranarda AutarTa zatayi Aure sai gashi yanzu bata rayye zanyi Aure Akram na tsani Alhaji Bala da ace zan samu bindiga babu abinda zai hana ni harbeshi na kona shi a wuta na tsane shi Akram na tsane shi wlh”
Ta karasa maganar tana fashewa da kuka
Akram da shima hawaye suka fara kok’arin zubo mishi sabida tsanin tausayin Samha murya na rawa ya durkusa a gabanta ya Ciro handkerchief daga aljihunsa yace “Soulmatel know how you feel wlh har gobe idan na tuna ta ina zubar da hawaye Samun irin Mummynku a ayanzu sai an tona tunda Alhaji Bala ya kashe mummynku ya rasa kwanciyar hankali tun ba’aje ko’ina ba Allah ya saka muku zaluncin da ya muku Soul mate ko da baki harbeshi ba halin da yake ciki kawai yanzu ya ishe shi dan har roko yake a harbeshi dan yanzu shi ba mutum ba haka zalika shi ba Dabba ba shi ba rayayye ba shi ba matacce ba Soul mate addu’a kawai zamu ringa bin mommy dashi dan nasha mafarki da ita tana ce min na kula daku and I promise insha Allah zan zame muku tamkar yaya pls stop crying ki
daina zubar min da wannan hawayen naki mai tsada” Akram yace yana share mata hawaye da handkerchief d’in hannunsa mai kamshi
Samha janye fuskarta tayi tace “I want to see him Akram inaso naga Alhaji Bala da idanuna inaso naga halin da yake ciki ganinsa ne kawai zai kwantar min da hankali in dainajin radadin danakeji a zuciyata”
Murmushi Akram yayi yace “Anything for you my princess your wish is my command”
Samha murmushi itama ta sakar mishi Akram ya koma ya zauna yafara janta da hira sai
data fara kyalkyale dariya hankalinsa ya kwanta ‘
As promise Akram yazo bayan kwana2 dan ya kaisu Samha su gano Alhaji Bala dan su Suhaima ma sun dage sai sunje sun gano shi su Saiam da Safna ma ba a barsu a baya ba dan burinsu suma suga yanda Alhaji Bala ya koma su cigaba da la’antar shi
Har sukaje inda aka ajiye Alhaji Balan dake kwancejikinsa na fitar tsutsosi basu gane shi ba sai toshe hanci suke suna waige waige dan su gano inda Alhaji Bala yake
Akram murmushi yayi dan yasan bama su San mutum bane a kwance Samha juyowa tayi
tace “wai yana ina ne”? Murmushi Akram ya kara yace ” Gashi nan a kwance a gabanku”
Direction din hannunsa suka bi da kallo idonsu ya sauka akan Alhaji Bala da babu k0 fata a jikinsa sai kasusuwa da tsutsosi dake fita ajikinsa in badan yana numfashi ba tunani zakayi
wani dabbar ne Rabin fuskarsa a kwailiye
A razane sukaja da baya suna gwallo ido suka kurawa Alhaji Bala ido
Saiam ce tayi karfinn halin magana cikin inina tace “kana so kace mana wannan abun dake kwance Alhaji Bala ne”?
Akram girgiza mata kai yayi yace ” kwarai shine ya koma haka bamu San mai yake damunsa ba zakiga yana ta ihu yana cizge fatarjikinsa yana fad’ar abubuwan da ya aikata yana ya tuba ya daina kullum sai ya rok’i a harbeshi ya mutu akan azabar da yake ciki”
Girgiza Kansu kawai suke yi suna mamakin halin da suka ganshi a ciki dan ko iya manya manya tsutsosin dake crawling a jikinsa ya ishe shi azaba
Samha na kok’arin magana Na Maliya ya bayyana yana kyalkyale dariya babu Wanda yake ganinsa sai Alhaji Bala
Alhaji Bala da muryarsa bata flta yana daga kwance ya fara ihu yana Na Maliya ya kashe shi ya huta
Aikuwa na Maliya na watsa mishi ruwan kaikayi ya mike da skeleton d’in jikinsa ya fara cizge Sauran fatar dakejikinsa yana ihu har Dana fuskarsa
A tsorace su Suhaima sukaja da baya suna kallon ikon Allah Alhaji Bala kuwa sai cizge cizge yake yi Yafi k’arfin minti Ashirin ahaka kam ya zube a k’asa yana kuka yana rokon mutuwa tazo ta
daukeshi
Girgiza kai su Samha kawai suke suna Al ajabin halin da suka ga Alhaji Bala a ciki Saiam kuwa cewa take lallai Allah ba azzalumin bawa bane tun a gidan duniya yake Hisabi ko ahaka aka bar Alhaji Bala ya girbi abinda ya shuka
Ahaka Akram ya maidasu gida suna Al ajabin halin da suka ga Alhaji Bala
Dangin Alhaji Nazifi kuwa ganin suna tayi mai zancen Aure yaki basu hadin kai ne yasa suka sa ranar da za’a d’aurawa su Suhaima Aure shima zasu d’aura mishi da Nazifa Cousin d’insa.
Hmm za,asha bukukuwa kenan