BAKUWAR FUSKA CHAPTER A
“Yallabai kana da bakuwa.” Matashin saurayin ya fada bayan ya sunkuya kasa a lokacin da yake magana da Ogan nashi.+
“Waye?” Ogan ya fada yana ci gaba da rubutunshi.
“Yallabai ba wata bakuwar fuska ba ce, wannan yarinyar ce dai ta kullum. Na ji ta ce wai sunanta Mahbooba. Yallabai ka taimaka dai yau ka saurare ta, watakila tana da muhimmiyar magana ne da…”
“Shut up Kamal! Just shut up! Who the hell are you? Kai ne za ka fada mun abin da ya dace? Get out from my Office. And ka fada mata kar ta sake zuwa inda nake, ta daina bibiya ta. Idan kuma ba haka ba sai na wulakanta ta…”4
“Wulakanci na nawa kuma?” Ya tsinci zazzakar maganarta a daidai lokacin da take shigowa Office din. “Dr. Ishraq Sulaiman.” Ta iso daidai gabanshi, ya bi ta da kallon tuhuma yana son jin me ta taka da har ta tako cikin Office dinshi ba tare da an ba ta izini ba. “Dr. Ishraq, ka yi hakuri na kutse da nake ma rayuwarka. Ka yi hakuri na shisshigi da nake maka. Na sani ni ba kowan kowa ba ce. Na sani ba ni da wani matsayin zuwa inda kake. Sai dai ka sani, zuciyata…” ta dafe saitin da zuciyarta take. “Zuciyata ce ba ta yi mun adalci ba. Zuciyata ta kasa samun sukunin rashin furta maka kalmar so. Ina tsananin kaunarka Dr. Ish…”2
Ba ta kai karshe ba sanadiyyar wani irin zazzafan mari da ya kai mata. Tana kokarin ci gaba ya sake wanka mata a dayan sashen. Ya murza yatsunshi cike da bacin rai ya ce “Mahbooba kike ko wa? Ki fita daga rayuwata. Tun da nake a rayuwata ban taba jin na tsani wani mai rai ba sama da ke. Na tsane ki ba na kaunarki. Kar ki sake zuwa inda nake, idan ba haka ba zan azabtar da ke fiye da tunaninki.”2
Ta gyada kanta cikin hawaye ta saki murmushi. “Azabtarwa? Har wace iri kuma? Azabtarwa duk ta wuce wacce zuciyata take min ta silar kaunarka? Abu daya ya yi saura Ishraq, kawai ka nemi mashi ko takobi ka daba mun, ka idasa gangar jikin da ke amsa sunan rayayya bayan rashin amfanin zuciyar jiki. Ka kashe ni Dr Ishraq, ita kanta mutuwar in dai daga gare ka ce zan ji dadi. Ko ba komai zan mutu da farin cikin samun matsayi a zuciyarka ko yaya ne tun da har ka yi kisan kai karon farko a rayuwarka kuma a kaina.” Ta gyada kanta hade da sake sakin wani murmushin. “Zan tafi Ishraq, sai dai ka sani ba zan sake dawowa Office dinka ba sai tare da bindiga ko wukar da za ka kar ni har lahira. Gwara mutuwata a kan halin da soyayyarka ta jefa ni ciki.” Tana kaiwa nan ta fice daga Office din jikinta sai karkarwa yake.1
Da karfi ta fada cikin motarta, ta hada kanta da sitiyari hade da fasa kuka da karfi, ta dafe gefen da zuciyarta yake. ‘Me ya sa? Why Mahbooba? Don me za ki kamu da soyayyar mutumin da ya tsani halittar halittarki? Mutumin da ya tsani ganin fuskarki?’
Tun da ta fita ya duke kanshi kasa, wani irin takaici yake ji, tsana da kiyayyar Mahbooba na ratsa duk wata halitta tashi. Ji ya yi komai ma ya fita daga ranshi. Ya buga tsaki hade da jifa da file din da ke gabanshi. Gida yake son tafiya, yana son ganin Maminsa da ita kadai ce ta rage mishi, ganin ta ke sassauta duk wani kunci da zai shiga ko kuma ya shiga. Wayarshi kirar Iphone 11pro max ya zaro daga jikin chaji. Ya cire lab coat dinshi ya rataye a hanger sannan ya fice daga Office din. Yana fita da sauri Kamal ya zo ya rufe yana mishi sallama.2
***
“Wai Mahbooba me yake damunki? Tsawon lokaci ke nan ina fama da ke ki fada mun abin da yake damun ki amma kin gagara fada mun. Shin kina da wacce ta fi ni? Me ya sa ba za ki nufe ni da damuwarki ba? Me ya sa?”2
Cikin kuka sosai ta kwantar da fuskarta a kan cinyar mahaifiyarta. “Momy, zuciyata ce ta kamu da soyayyar wanda ba ya ko son gani na. Na rasa yanda aka yi Momy. A baya ina daga sahun masu yin kaico ga yan matan da ke kasa ajiye soyayya a kasan ruhinsu. Ina daga sahun masu ganin laifin matan da ke furta kalmar so ga maza. Sai dai yanzu…” ta kokarta shanye kukanta. “Yanzu Momy wai ni ce da naciyar soyayya ga mutumin da ya tsane ni, ya tsani jin ko muryata. Yake wulakanta ni a duk lokacin da ya yi arba da halittata. Momy ya zan yi? Ya zan yi da soyayyar Dr. Ishraq?”1
“Hakuri.” Fareeda da ke daidai shigowa ta fada. “Hakuri za ki yi Yaya Boobah. Lallai na yarda zancen Hausawa da suka ce zuciya ba ta da kashi. In banda haka, Yaya Boobah ke din nan da na sani mai class, mai jan girma, mai kamun kai, mace mai daraja da kima wacce da daman maza ke rububin ganin sun zama masu matsayi a zuciyarta, wai ke ce ke yada girmanki a wurin namiji har yana wulakanta ki? Ban taba tunanin wannan ranar ba Yaya. Ban taba tunanin akwai ranar da za ki kasa kwabar zuciyarki ba.”2
Mahbooba ta dago kanta hade da jingina jikinta ga na yar uwarta. Cikin shesshekar kuka ta ce “Haka nake ta maimaitawa a kasan zuciyata Reeda. Daga farko na kasa gasgata ni ce. Na kasa amince Mahbooba Bukar ce da fadawa tarkon kaunar wani namiji. Sai dai daga baya na amince, a lokacin da zuciyata ke neman tsago tsakiyar kirjina ta bultso waje. A lokacin da soyayya ke neman zautar da ni, take neman gigita tunanina. Na tsani kaina Reeda. Wallahi na tsani kaina.” Ta sake fashewa da kuka tana kankame Fareeda.1
“Duka-duka yaushe zuciyarki ta warke? Yaushe kika tashi daga jinyar shekara da shekaru? Me ya sa za ki mana haka Mahbooba? Me ya sa kike neman dawo da hannun agogo baya? Uhm, me ya sa?” Ya iso gare ta ya durkusa a gabanta, hannuwanta ya kama ya saka a cikin nashi.3
“Yah Aliyu ban sani ba. Ban san amsar duk abin da kake tambayata ba. Na dai san kawai na wayi gari da soyayyar Dr. Ishraq. Na yi duk yanda zan yi ganin na yakice shi daga zuciyata amma abun ya ci tura. Ya Aliyu ya zan yi?”1
“Ba zan hana ki son shi ba Boobah. Ban isa in hana ki son shi ba. Sai dai tunatarwa da zan miki. Ki tuna kalar wahalhalun da kika sha a baya. Ki tuna jerangwamar da muka sha dukkanmu a kan larurinki. Sai yanzu da muke ganin sauki ya samu ne ke kuma kike neman ruguza farin cikinmu? Kar ki manta ba mu da uba. Kadan ya rage karfinmu ya kare duk a kanki. Idan kin manta ne ki tuna.”3
Daga haka ya saki hannunta hade da ficewa ya bar dakin.
Princess Amrah
RAZ 2″Mami! Mami!! Mamina!!!” Ya kira ta har sau uku. Daga kitchen ya tsinkayo muryarta ta ce,+
“Na’am Likita. Lafiya kake ta kwala min kira haka? Ko sallama fa ban ce ka yi ba.”
Ya isa har kitchen din ya same ta tana kokarin juye farar shinkafa a colander. Karbar tukunyar ya yi ya karisa juyewa sannan ya wanke shinkafar.
“Fuskarka ta nuna alamun damuwa Ishraq. Me ya faru?”1
Ya saki guntun tsaki a lokacin da ya tuno silar bacin ranshi. Shigowar shi gida, yin arba da fuskar Maminshi ya mantar da shi duk waccan damuwar, sai dai kuma tsananin karantar shi da ta yi ya sa kallo guda da ta mishi na farko ta karanto damuwar da yake cikinta.
“Mami, wannan yarinyar dai da na fada miki. Ko yau din nan ma sai da ta sake zuwa Office dina. Ni kam Mami na fara tsorata da ita ko dai mayya ce ko kuma aljana. Duk wani tozarci da wulakanci na mata amma ta ki ta yi zuciya Mami. Ni na ma rasa me zan mata in huce takaicin haushinta da nake ji. Tun da nake a duniya ban taba jin tsanar wani kamar ita ba. Ya zan yi da ita ne Mami?”2
Ajiyar zuciya Mami ta sauke, ta dafa kafadar Ishraq cike da soyayya ta ce,
“Na hane ka da wulakanta mutane Ishraq. Shi mutum da kake gani daraja gare shi, kuma ko kare yana da rana.”1
“Mami ba za ta taba yi mun rana ba wannan na tabbata. Tsanarta a jinina take. Kin fi kowa sanin na tsani naci da kwakwa, Mami.”2
Ta saki guntun murmushi. “Na sani Ishraq. Sai dai ka sani dukkan mai rai da kake gani akwai darajar da Allah ya yi mishi. Kar ka ga mutum a haka ka wulakanta shi, ta yiwu a gaba ka tsinci wani alfanunshi a gare ka. Ya kai dana, ina mai shawartarka da ka daina wulakanta yarinyar, a hankali za ka fahimtar da ita ba ka da ra’ayinta. Ni ma kaina duk da ban gan ta a ido ba amma ba ta shiga raina ba. Saboda duk yarinyar da za ta rinka bibiyar saurayi har Office dinshi da sunan tana son shi to lallai ba yarinyar arziki ba ce. Amma Ishraq hakan ba shi zai sa in goyi bayanka na ka wulakantata ba. A ruwan sanyi za ka nuna mata ba ka son ta, sai a zauna lafiya.”1
Ya gyada kanshi. “Mami yanzu wacce duk aka gama wulakantawa ta kasa hakura ita ce bi ta ruwan sanyi zai sa ta hakura? Ni fa na rasa ina zuciyarta take. Ban taba ganin mutum mai nacinta ba. Ba ta da aji ko kadan.”2
“Kai kuwa na san ka da son mace mai aji ba.”1
Ta saki murmushi tana kallon shi. Shi ma murmushin ya mata sannan ya sunkuyar da kanshi kasa.
“Maza ka je ka yi wanka ka canza kaya duk warin asibiti kake.”
Ya turo baki cikin shagwaba. “Lallai ma Mami, kamshi ne fa ba wari ba.” Ta mishi dukan wasa hade da harararshi.
“Ai sai kamshin. Ni dai je ka, kafin ka gama na kammala girki ka ci, don na san kana jin yunwa.”
Daga haka ya fice ya nufi dakinshi cike da shaukin kaunar mahaifiyarshi. Baki daya ya nemi wata damuwa ya rasa. Da ma shi ya sa duk damuwar da yake ciki yake tinkarar Mami da ita. Ita kadai ce maganin damuwar shi. Ita kadai ce warwaruwar dukkanin matsalolinshi.
Ya yi wanka hade da alwallar sallar azahar, bayan ya fito ya canza kaya ya feshe jikinshi da kamshi sannan ya kabbara sallah.
A lokacin da ya sallame ya ji wayarshi ta dauki kara. Yana dubawa ya ga Kamal ne masinjanshi, ya dauka, “Kamal ya?”
“Lafiya lau Oga. Da ma wai za ka samu dawowa da yamma? Yau Wednesday kana da duba patients daga 7pm.”
STORY CONTINUES BELOW

Guntun tsaki ya yi yana duba agogon hannunshi. “To har bakwai din ta yi ne?”
Cikin girmamawa Kamal ya ce “Yi hakuri yallabai, wai ina son tabbatarwa ne, saboda ni ma tafiya zan yi sai zuwa can an jima zan dawo.”
“Ka siyo mun fura da nono daga nan. Kar ka wuce karfe shida ba ka dawo ba.” Daga haka ya kashe wayarshi hade da mikewa ya nufi parlor.2
A dining ya tarar Mami ta shirya komai ta shiga sallah. Ya gyada kanshi cike da tausayi da soyayyar Mami, ya zauna a daya daga cikin kujerun dining din. Bai zuba ba, domin kuwa al’adarshi ba zai taba iya cin abincin ba in ba ta nan, ita take zuba mishi da kanta, idan kuwa ya yi tafiya haka zai ta fama da wahalar zaman yunwa, saboda wancan sabon da yai wa kansa. Idan ma ya ci to ba don dadi ba. Girkin Maminsa kadai yake ci ya ji dadi dari bisa dari.
Yana cikin haka sai ga ta ta fito. Ta zauna a kusa da shi ta yi serving dinshi sannan ita ma ta zuba ma kanta. Suna cikin ci ta ce, “Dazu kuwa Khalifa da Fahad sun zo.”
Ya dago kanshi cike da mamaki. “Me suka zo yi?”
“Hmm! Labarin gizo ai ba ya wuce na koki Ishraq. Duk da ba su fito kai tsaye sun fada mun dalilin zuwan nasu ba amma dai jikina ya ba ni zancen auren ka da Bilkisu ne.”
Bayyanannen tsaki ya yi yana hade abincin da ke cikin bakinshi. “Wai su miye ruwansu da ni ne? Me ya dame su da in yi aure da kar in yi?”
“Su kuwa ke da ruwa likita. Khalifa Yayanka ne uba daya. Fahad kanin mahaifinka ne uwa daya uba daya. Ta yaya ma za ka ce wai miye ruwansu da aurenka?”1
Yatsina fuska ya yi bai sake fadan komai ba har ya gama cin abincin ya hau kwashe kayan. Shi da kanshi ya yi wanke wanke, ya share kitchen din ya yi mopping sannan ya dawo parlor ya samu Mami ma ta gyara parlon ta kunna turaren wuta.
Daga karshe shida da rabi ya shirya tafiya asibiti. Ya ma Mami sallama hade da ficewa. Sai da ya yi sallar maghrib sannan ya fara ganin marassa lafiya. Daya bayan daya suke shigowa har lokacin isha ta yi, ya gabatar da sallar ya dawo ya ci gaba da ganin patients dinshi.
Wayarshi ce ta dauki kara ya duba, sunan Khalifa da ya gani ya sa shi gyada kanshi cike da takaici. Ya rasa dalilinsu na nace ma sai ya yi aure, auren ma kuma Bilkisu. Duk da yar uwarshi ce amma fa ba ya jin zai iya auren ta, kawai yadda yake ganin sun nace ma sai an yi auren yake ganin da walakin goro a miya. Bai san dalili ba, amma yana ji a ranshi akwai lauje cikin nadi. Shi fa duka auren ne ma ba ya gabanshi. Bai ki ya ci gaba da zama daga shi sai Maminshi ba a gida, ta yi mishi girki ta ba shi, ta mishi hira a duk sadda yake da muradin hirar. Ta kwantar mishi da hankali a duk sadda hankalinshi ya tashi.
A karo na uku wayarshi ta dauki kara, ya dauka ya kara a kunne hade da sallama a bakinshi.
“Na’am Yah Khalifa, ina wuni.”
A dayan bangaren Khalifa ya amsa da lafiya lau, ya dora da, “Dazu mun je kana asibiti sai Mami kadai. Daga gidan su Bilkisu muke.”
“E, haka Mami ta ce kun je. Ya kuke ya su Umma? Kwana biyu ina ta son zuwa gaishe ku Allah bai nufa ba. Amma zan kokarta zuwa cikin weekend in shaa Allah.” Ya yi kokarin chanja topic.
“Allah Ya kai mu. Ishraq Kawu Imran ya kara yi mana magana fa. Wai har yanzu ba ka gama tunanin ba ne?”
Da kyar ya hadiyi yawu ya sunne muryarshi, “Gaskiya Yaya ba zan boye maka komai ba ba ni da raayin auren Bilkisu. Kar in bata mata lokaci gwara tun wuri in fada muku ku sanar da su, a nemi wani kawai, ina mata fatan alkhairi.”
Bai so jin hakan daga gare shi ba. Bai so Ishraq ba zai auri Bilkisu ba, saboda tarin promises din da ita da Abbanta suka yi mishi matukar ya shawo musu kan Ishraq din.2
“Kar ka yi haka kanina. Bilkisu yarinya ce mai tsananin ladabi da bin na gaba da ita. Tana da tarbiyya sosai kai ma ka sani. Tana da kyau, kudi, gayu da kuma aji. Duk inda mace ta kai Bilkisu ta kai a so ta, ko in ce a aure ta. Ka dai sake dubawa likita.”
“Yah Khalifa kamar yadda na fada maka ba na son bata mata lokaci, gaskiya ba ni da raayinta. Kawai a yi hakuri da zancen, Allah Ya hada kowa da rabon shi.”
Daga haka ya kashe wayar, ba ya jin da na sani ko kadan na maganganunshi. Ya rasa me ya sa mata ke mishi haka. Ya rasa dalilinsu na nace ma auren shi. Idan kyau ne akwai dubunshi. Idan kudi ne akwai wanda suka yi linkin ba linkin din nashi. Haka gayu ma. ‘Farin jini ne.’ Wata zuciyarshi ta ba shi amsa. Ya gyada kanshi yana mai takaicin wannan lamari.
“Ameera nake so, ita ce zabina, kuma in shaa Allahu ita za ta zama uwar ya’yana.”
Ya sakar ma kanshi murmushi. A cikin dan taqin ne yake jin tsanar aure, yake jin da mahaifiyarshi kadai yake son ci gaba da rayuwa, sai dai yanzun nan kuma zuciyarshi ta tunatar da shi Ameera. Ta hasko mishi fuskar Ameera da ya jima yana so. Ko tana ina yanzu? Allah masani.
End of chapter
I know this is not a good start, but believe me, the story gets more interesting if you continue reading.
Vote, comment and share with loved ones.
Princess Amrah
RAZ 2″Yah Boobah ki fito mu ci abinci an gama ke kadai muke jira.”+
Ba ta ko dago kanta ta kalle ta ba ta zaro guntuwar magana daga qasan makoshinta, “Na koshi.”
“Kin koshi?” Fareeda ta tambaye ta cikin mamaki.
“Kin ji me na fada Reeda, me ya sa da tsiya kike so in maimaita?” Fuskarta da ta wadatu da ruwan hawaye ta dago tana sauke kallon ta a gefenta.
Ajiyar zuciya Fareeda ta sauke hade da isowa bakin gadon ta zauna. Ta kama hannun Mahbooba cike da tausayi ta ce, “Yah Boobah wai me ya yi zafi ne shi ba wuta ba? Wannan wace irin rayuwa ce kike neman jefa kanki a ciki? Yaya idan ke kin gaji da rayuwarki mu ba mu gaji da ke ba. Ba mu gaji da ganin ki ba. Don Allah kar ki kashe mana kanki. Ki cire son zuciya mu ma ki faranta mana. Ki yi kokarin rungumar kaddarar da mai kowa mai komai ya jefo a saitin duniyarki.”
Kukan da ya zame mata abinci ta kara fasawa, “Rayuwata ba ta da amfani Reeda. Ban so ba, ban so na kasance wata abar da za ta jawo muku abun kunya ba. Yes, abun kunya. Bibiyar Ishraq da nake kadai wani katoton abun kunya nake jawo ma ahalin gidan nan. Sai dai ina so ku sani, ba da son zuciyata ba ne. Ni ma kaina na so na daina, tun farko ma na so kar na zurfafa, sai dai kuma abun ya ci tura. Duk bayan daqiqa sai kaunar Ishraq ta qara girmama a kaf ilahirin zuciyata. Ko kadan daraja da soyayyarshi sun kasa raguwa, wulakanta nin da yake ya kasa yin tasiri. Kaunarshi nake da dukkan zuciyata Reeda. Da dukkan jinin da yake gudanya a halittar tsokar zuciyata.” Ta fada jikin Reeda tana kuka sosai.
“Wannan jarabta ce Yaya. Ban taba ganin soyayya irin wannan ba. Yaya don Allah ki saukaka ma kanki. Ki tuna duka ba ki fi sati uku ba da sallama daga asibiti. Ki tuna larurin da ya addabe ki tun kafin a haife ni that’s tun kina yar karama. Sai yanzu da muke ganin ciwon ya warke sai ke kuma kike neman kiran shi da kanki? Kike neman siyanshi da kudin da Allah ya mallaka miki? Na sani ba ke kika dora ma kanki ba. Amma kuma ki sani Allah madaukakin sarki da kanshi Ya ce ba a kallafa wa bawa sai abinda zai iya dauka. Ba don mu ba, ko don Momy, halin da take shiga a duk sadda jikinki ya taso, wannan kadai ya ishe ki. Ki kokarta tumbuke wancan malalacin likitan daga zuciyarki, ko ba kya so, tun kafin abun ya yi tsananin da tumbukewar za ta yi wahala.”
Da shesshekar kuka ta ce, “Ki je ki ci abinci Reeda, ba na jin yunwa.”

Ganin tana kokarin canza topic din da suke a kai ya sa Reeda daukan wayar Mahbooba. Ta ci sa’a datanta na bude, whatsapp ta shiga ta lalubo group chat dinsu ita da Haneefa da Saleema, group video call ta latsa kuma duk suna online. Bayan duk sun dauka ta juya back camera suna kallon yanda Mahbooba ke kuka sosai kamar ranta zai fita. Suna kallon yanda hawaye ya wanke fuskarta wanda mutum zai iya rantsewa da Allah ruwan alwalla ne bai bushe daga fuskar ba. Sai dai yanayin shesshekar da take fitarwa ne zai ankarar da mutum cewa kuka ne take yi da iya karfinta. Hankalinsu duk ya tashi sosai suna ta faman tambayan ya aka yi, ta mayar front camera ta ce,
STORY CONTINUES BELOW

“Wannan halin da kuka ga Yah Boobah a ciki haka take fin sati biyu. Ba ta ci ba ta sha an rasa dalili sai daga bayan nan da Momy ta tilasta ta fada mana. Yah Haneefa, Yah Saleema na bar wuka da nama a hannunku. Ku kokarta tsamo kawarku, ko in ce aminiyarku daga halin da take ciki.”
Haneefa ce ta yi saurin cewa “Ciwon nata ne ya dawo, Reeda?”
“Ko kadan ba shi ba ne Yah Haneefa. Ciwonta bai taso ba. Kawai dai ku yi kokari ku zo ku yi magana da ita. Ku yi mana wannan taimakon.”
Saleema ta share hawayenta ta ce “In shaa Allahu yanzun nan zan taho, Haneefa ki fada ma Umma ke ma ki fito yanzu mu hadu. Duk hankalina ya tashi.”
“To sai kun zo, Allah ya tsare hanya.” Daga haka ta kashe wayar, ba ta ko kara kallon Mahbooba ba ta fice daga dakin.
Ba a wani dauki dogon lokaci ba Haneefa da Saleema suka zo. Har kasa suka duka suka gaishe da Momy, Haneefa ta ce “Momy sam ba mu san halin da Mahboobah take ciki ba. Ba ta taba nuna mana ba, shi ya sa ba mu sani ba.”
Momy ta yi guntun murmushi. “Kun san ta da zurfin ciki ai. Ni ma na dauki tsawon kwanaki ina son sanin dalilin sauyuwarta, sai dai kullum ta ce mun babu komai. Da kyar na shawo kanta ta fada mun. Wai wani likita ne take so shi kuma yake wulakanta ta. Abun ma gwanin kunyar fadi.” Ta karisa zancen da gyada kai.
Cikin mamaki Saleema ta ce “Ikon Allah. Garin yaya to? Ko asiri ya mata?”
“Ba wani asiri Yah Saleema. Da asiri ne da bai rinka wulakanta ta har haka ba. Ni dai ina tsammanin dashen da aka yi mata na zuciya har da kwakwalwarta ya shafa, baki daya an juyar mata da tunaninta. Yah Booban da muka sani da ba ita ba ce yanzu.”
Ta share hawayen da ta ji sun sauko mata. Baki daya sai Haneefa da Saleema suka kamu da tausayin aminiyarsu. Sai suke tuno baya, suke tuna yadda take gara maza. Take da class sosai. Amma yanzu ita ce damuwar soyayyar namiji ta gama dabaibaye ta.
“Ku isa dakin nata. A yanda na tabbatar za ku same ta a haka take, ta daina ko fitowa inda muke. Daga kwanciya sai kishingida su ne aikinta.” Momy ta fada tana musu nuni da su isa dakin Boobah. Ba su jinkirta ba suka shiga dakin.
A bisa kafafuwanta Saleema ta mike. Ta kama Mahboobah ma ta mikar, ta sakar mata hannu, “Mike ki tsayu da kafafuwanki Boobah. Ki kalli cikin idanuwana ki fada min dukkan abin da ya faru. Kar ki boye mana komai Boobah, aminnankin nan ne guda biyun tun na yarinta, wadanda ba sa boye ma junansu damuwar zukatansu. Wadanda ke damuwa da damuwar junansu. Masu kula da dukkan motsin junansu. A tsaye nake son jin komai daga gare ki.”
Haneefa ma ta mike, dukkansu suka kura wa Mahboobah ido suna sauraren ta.
Cike take da rauni. Kafafuwanta ba su iya daukar gangar jikinta. Hakan ya sa ta nemi komawa ta zauna amma Haneefa ta kara mikar da ita. “Muna son zare miki wannan raunin Boobah. Kwananki nawa a wannan halin? Sallah ma an fada mana ta zaune kike yi. Yau ki tsaya a tsaye, tsayuwar da nake fatan daga ita za ki ci gaba da mikewa a saman kafafuwanki, a saman digadiganki. Ba tare da kowanne irin rauni ba.”
“Hany ya zan yi?” Ta fasa kuka mai kara, ta juya tana kauce ma haduwar idanuwansu, jikinta na karkarwa, zuciyarta na mata barazanar bultsowa waje saboda tsananin radadi, radadi ba irin wanda take mata a baya ba, wannan ya sha bamban, wannan na soyayya ne, soyayyar mutumin da ya tsane ta. Sosai rashin kwarin guiwa ya bayyana a saman fuskarta.
STORY CONTINUES BELOW

“Tun daga lokacin da aka sallame ni daga asibiti nake jin kaunarshi, tun ban gan shi da idanuwana ba sabuwar zuciyata ta fada tarkon kaunarshi. Ban gasgata ba sai a lokacin da muka sake komawa ganin Doctor Sadeeq a asibitinsu, ta gilashin mota na yi arba da fuskarshi, ta gilashin mota zuciyata ta tabbatar mun da shi ne.” Ta share hawayenta, wani zazzafa ya sake biyo baya. “Muna tare da Reeda lokacin, sai na dake, na kasa ce ma Yah Aliyu ya tsaya in yi magana da shi, sai dai kallo guda na haddace lambar motarshi, na haddace hanyar da na ga ya bi daga hanyar Office din su Doctor Sadeeq. Na sa a raina zan dawo, zan fitar mishi da sakon zuciyata.” Ta sake share hawayenta hade da gyada kai. “A wannan ranar ne na fara ganin Ishraq Sulaiman, sai dai bai zo mun a Bakuwar Fuska ba, saboda na san shi a zuciyata, na san zan gan shi ko ma a wanne lokaci, shi ya sa ina ganin shi kallo daya na gane shi ne wanda zuciyata ke so, shi ne wanda na kamu da soyayyarshi tun kafin in ga fuskarshi.”
Dukkansu kuka suke. Kallon ta suke yi, cike da tausayin rashin nutsuwar da suke ganin tana yawo a duk motsinta.
“Ta yaya kika je inda yake har kika bayyana masa sakon zuciyarki?” Haneefa ta tambaye ta. Saleema ta jinjina kai.
Da wata irin murya ta zaro magana daga can kasan makoshinta, damuwa na kara neman muhalli, ta zauna daram a saman fuskarta.
“Washe gari ban bari Reeda ta rako ni ba, da ma kuma Yah Aliyu yana da uzuri, duk da Momy ba ta so in je ni kadai ba amma na nace mata, na ce na ji sauki, ina son tabbatar ma duniya cewa na warke, don haka da kaina nake so na yi driving, da kaina nake son kai kaina wurin likita. Ta amince mun ganin yanda na nace. Tsabar azalzala da zuciyata ke yi in je wurinshi ban ko fara da ganin Doctor Sadeeq ba, hanyar da na ga ya bi na bi, sai dai na kasa gano inda zan gano shi. Ba ni ma da tabbacin a nan fa yake aiki, ba ni da tabbacin hanyar da na ga ya bi ta nan zan gan shi, abin da dai nake da tabbacinshi shi ma likita ne, saboda kayan jikinshi, ya saka lab coat kuma yana rataye da stethoscope, ya saka dan siririn gilashi irin na likitoci. Wannan shi ya tabbatar mun da shi ma likita ne. Ban san sunanshi ba, daga motarshi sai fuskarshi na sani. Na parker motar a wuri guda ina ta tafiya da kafafuwana, har na ci karo da bangaren kananan yara, motoci burjik a parking area. Ban wuce ba, haka na hau kalle-kallen motocin har idanuwana suka yi tozali da tashi. Na saki sassanyan murmushi hade da dafe zuciyata. Wani irin dadi na ji tamkar na furta masa kalmar so ne ya amince. Masu gadin wurin na tambaya hade da nuna musu motar, daya daga cikinsu ne ya ce min sunanshi Doctor Ishraq Sulaiman, likitan yara ne. Na tambaye shi Office dinshi ya kwatanta mun, na kama hanyar shiga Paediatric din ke nan sai ga shi ya fito, masinjanshi biye da shi. Da sauri na isa gare shi, na gaishe shi ya amsa ba yabo ba fallasa.
“Uhm…da ma, da ma na zo ne in gaishe ka.”
“Wace ke?” Ya fada yana ci gaba da tafiyar shi. Ko kadan tambayar tashi ba ta zo mun a mamaki ba, domin na san definitely zai yi. Na rasa me ma zan ce mishi.
“Are you deaf?”
Da kyar na hadiye yawu mai daci, “Na san ba ka san ni ba, kawai dai na zo gaishe ka ne.” Daga haka ban kara cewa komai ba na gaggauta tafiya.
Tun daga wannan ranar na mayar kullum na je wurin Doctor Sadeeq sai na je inda Ishraq yake. Haka yake wulakanta ni ni kuma ina nace ma zuwa, ban furta ina son shi ba sai jiya, ya min wulakancin da ko kare ba zai dauka ba. Ban san yanda zan yi ba. Da a ce zan iya ajje soyayyar Ishraq da ba a kawo haka ba. Da babu mai ji tuni zan yakitar da shi daga qasan zuciyata. Sai dai ba zan iya ba. Yakice Ishraq daga zuciyata daidai yake da yakice zuciyar ma baki daya…”
“Ba ki isa ba Boobah.” Haneefa ta fada cikin zafin rai. “Har yaushe za ki san muna kaunarki? Sai yaushe wai ma za ki yi wayo? Da ana miki kallon wata mai hankali wayayya ashe an saba lamba? Har fadi kike da bakinki wai yakice soyayyar wancan wawan daidai take da yakice zuciyarki? To ba ki isa ba wallahi. Na ba ki wunin yau kawai Boobah, ki san yanda za ki yi, idan kuma so kike mu yi asararki to.”2
Daga haka ta ja hannun Saleema suka fice daga dakin, zukatansu na musu zafi sosai, suna tsananin jin tausayinta.
Kafafuwanta ta manne wuri guda hade da sada su da kirjinta, tana jin girman da kaddararta ta zo da shi, tana ji rayuwa da duniyarta ba su yi mata adalci ba. Kuka sosai take yi da girman tashin hankalin da yake addabarta.
2
End of chapter
Hello dearies, how have you been? Fine, in shaa Allah. How was this chapter? Who hates Mahboobah?😂 who loves her?🧐oopps, gaskiya tana bada mata😣but sha, it’s love😓 what a pity😟
Thanks for reading
Princess Amrah
RAZ 2Flash back- 4th January 2010+
“Wai Ameera wace irin nawa ce kike da ita? Tun dazu kowa ya fito mu kadai ake jira, sai aike ake mun in fito kamar kaina farau diya mace. Na ba ki minti biyar idan ba ki fito ba sai da ki neme ni ki rasa.”
“Ga ni nan zuwa fa Mama. Allah kuwa na gama komai fitowa kawai zan yi.”
“Fitowa dai ai ba wani aiki ba ne idan kin gama. Ni dai na fada miki…”
Ba ta kai karshen zancen ba sai ga Ameera ta fito rike da karamar Ghana most go. Kyakkyawa ce ma shaa Allah. Duka a shekaru ba za ta wuce goma sha biyar ba. Fuskarta ta shafa hoda kadan sai kwalli da ya kawata idanuwanta. Ta yi dan digo karami a tsakanin girar fuskarta. Ta saki sassanyan dariyar da har sai da hakoranta suka bayyana.

“To Hajiya Mama ga ni na fito.”
Dukan wasa Mamanta ta kai mata. “Ban san me ya sa ba yarinyar nan baki daya kin mayar da ni Kakarki.”
“Toh Mama barewa a daji da wa take wasa in ba da ya’yanta ba?”
“Kanki dai ake ji.” Daga haka suka kama hanyar barin gidan.
A kofar gidan Kawu Badamasi suka hadu. Sun tarar duk yan tafiya kowa ya zo su kadai ake jira. Har motar da za ta dauke su din ma ta iso. Bayan an gaggaisa ana kokarin shiga mota Ameera ta noke. Mama ta kalle ta hade da bata fuska tana son sanin dalilin nokewar tata. Kafin ta ce komai ta hango Nura daga can nesa ya jingina jikin bango. Murmushi kawai Mama ta yi, ta ce “Ai sai ki je wurinshi. Kuma wallahi kina bata lokaci sai dai ki ga motar nan ta tashi, don babu wanda zai tsaya jiran ki kuma.”
Ba ta ko tsaya ta karisa jin zancen Mama ba ta gaggauta isa inda yake.
“Yah Nura ina kwana?” Ta furta tana kallon kwayar idanuwanshi.
“Yan matan Mama sai tafiya. Ina ta sauri kar in tarar kun tafi ai.”
“Yah Nura ai dan in samu mu gana din ne ya sa na yi ta shiririta, sai da na ga Mama na neman tafiya ta bar ni sannan na fito.” Ta kwashe da dariya.
“Lallai ma yarinyar nan. Kin kyauta dai duk da haka. Amma kar ki sake yin irin haka don ba zan ji dadi ba a tafi a bar ki.”
“Yah Nurah duk sun gama shiga motar bari in je.” Har ta juya za ta tafi ya kira sunanta.
“Ameera, ki kula mun da halittar halittarki. Ki kula mun da zuciya da gangar jikinki. Ki kula mun da dukkan dukkanki. Ina kaunarki Ameera.”
STORY CONTINUES BELOW

“Ina kaunarka sosai Yah Nura. Zan tafi, ni ma ka kula mun da Yah Nurana. Sai mun dawo.”
Daga haka ta nufi inda motarsu take tana jin kaunar Nura na ratsa dukkan tsokar zuciyarta. Ta sani, za ta yi kewar shi ta kwana biyar din nan da za su yi. Wannan shi ne karon farko da ta taba fita daga garinsu, in baccin bikin cousin dinta dole ne gare ta da sai ta hakura ta zauna ko don ta ci gaba da sada gannansu ita da Nura. Tana ji a ranta da so samu ne da ba za ta juri rashin ganin shi ba ko na daqiqa.
A kan idanuwanshi dreban ya tada motar. A kan idonshi suka dauki hanyar fita daga kauyen Hunkuyi, yana kallo suka bace ma ganin shi. Murmushi ya saki yana kara jin kusancin Ameera a cikin zuciyarshi.
***
Da yammaci suka shiga cikin garin Kaduna. Daf da faduwar rana motarsu ta dakata a daidai kofar gidan da suka je bikin. Daya bayan daya suke fitowa daga cikin motar har duk suka gama fita. Ameera ta dauki jakar kayansu da Mama, sannan ta rataya karamar jakarta.
Sun tarar har an gama wa’azin bikin. Abinci suka ci bayan an kai su masaukinsu, su kusan takwas ne, Ameera ce kadai budurwa a ciki.
“Ameera cikin yan mata ya kamata ki koma. Za ki fi sakewa da jin dadi fiye da nan cikin iyayenki.”
“Uhm uhm ni dai Mama. Kin san halin yan gayun nan, sun raina bakauye. Ina tsoron in shiga cikinsu su raina ni, zuciyata za ta zafafa sosai.”
Murmushi Mama ta yi, “Ba za su raina ki ba Ameera, ai yan uwanki ne. Yan uwa kuma na jini. Da Babanki da Babansu uwa daya uba daya. In banda ma zumunci da ya lalace yanzu ai da kun san juna kuma kun saba.”
Ameera ta tabe baki. “Ni dai duk da haka ina tsoro Mama.”
Dafa ta Mama ta yi cikin rarrashi ta ce, “Ta haka ne za ku saba ai. Ki daina jin tsoro. Na tabbata ba za su wulakanta ki ba. Za su kula ki in dai kin saki jikinki da su.”
Kafin Ameera ta kara cewa komai sai ga wasu yan mata guda biyu sun shigo. Har kasa suka gaishe da su Mama, su Mama suka zolayi daya daga cikinsu cewa amarya ta sha kamshi. Murmushi kawai take saki.
“Yanzu kuwa nake cewa Ameera ta tashi ta neme ku.” Mama ta fada tana musu murmushi.
“Lahh ai ban ma kula da ita ba. Ke wai sai ki yi zaune cikin manya? Maza tashi mu je can part din Abba, a can za mu kwana da kawayenmu.” Kanwar amaryar ta fada hade da jan hannun Ameera. Ta kalli Mama, Mama ta mata alama da ta tashi ta bi su.
Ta yi mamakin yanda suka ja ta a jiki. Ta yi mamakin kaunar da suka nuna mata su da kawayensu, hakan ya sa lokaci guda ta ji sun shiga ranta.
Ranar daurin aure aka daura aure amarya ta tare gidanta. Duk aka watse daga gidan amarya, aka bar kanne da kawaye kawai domin su yi mata yan gyare-gyare. Suna cikin gyaran ne aka duba babu detergent ko daya da za a yi mopping da wankin toilet, hakan ya sa aka yanke shawarar daya daga cikinsu ta fita ta siyo, kafin a ce ga wacce za ta Ameera ta karba, saboda a duk cikinsu ita ce karama, ita ce ya dace ta je ta siyo, kuma sun ga wani shop kusa da gidan, kasantuwar babu nisa da titi gidan amaryar.
“Ameera da dai kin bari Maryam ta je, ita ce yar gari. Kin ga ke bakuwa ce.” Amaryar ta fada tana kokarin hana Ameera fita.
STORY CONTINUES BELOW

“A’a Yaya Nafeesa. Babu komai in shaa Allahu yanzu zan dawo. Kar ki ji komai.” Ta sakar mata murmushi.
Tuki yake cike da nutsuwa, ya saita gannanshi a kan gaban motarshi, yana ankare da giccin komai da ka iya gittawa ta gaban gilashinshi. Sai dai bai sani ba, bai kula ba halittar mutum ta doso ta gaban motarshi gadan-gadan. Da saurin tsiya ya taka burki hade da ambatar sunan Allah. Lallai bawa ba ya tsallake wa kaddararsa. A dan karamin tunanin shi, sai yake ganin kamar irin wannan kaddarar ba za ta zo mishi a daidai wannan lokacin ba, lokacin da hankalinshi a wuri daya yake, ba ya tunanin komai sai tukin da yake yi.
Gani ya yi halittar mutum ta tashi daga gaban motar, hakan ya sa ya kashe motar tare da ficewa domin duba lafiyar halittar da ta yi barazanar bata mishi lokaci. Ya fita da niyyar balbala masifa, domin kuwa sakaci ne, ganganci ne halittar ta yi, saura kadan a ja mishi mugun abu.
“Ke!” Ya ambata ganin tana neman barin wurin ba tare da ko fuskarshi ta kalla ba.
Ko a kauyensu ta tsani a kira ta da ke. Duk mai son ganin bacin ranta to ya ce mata ke ya ga ikon Allah.
Ta juyo cikin bacin rai ta mishi kallon sama da kasa. “Mallam ba sunana Ke ba. Kar ka sake kira na da Ke. Idan Ke kake nema tana cikin ABCD. Sunana Ameera, Ameera Muhammad.” Daga haka ba ta kara cewa komai ba ta nufi shagon da za ta je.
Bin ta da kallo ya yi, mamakin kanshi yake, mamakin yanda karamar yarinya ke juya yan kananan labbanta tana mishi tsiwa yake. Da gatsine da harara, har ma da kyakkyafcin ido duka ta hada mishi. Sai ma abun ya ba shi dariya, ya saki murmushi yana bin bayan halittarta da kallo. In ban da karfin hali irin nata, ita fa tai mishi laifi. Ita ce ta tsallako titi ba tare da ta tsaya duba hanya ba. Gyada kanshi kawai ya yi tare da komawa cikin motarshi.
Ta yi sallama a bakin shop din, mutumin da ke tsaro ya tambaye ta abin da take so. “Omo nake so Mallam. Kuma mai kamshi sosai, sannan mai kumfa. Kar ka ba ni wanda ana aiki da shi gwara ruwan flour.”
Ya kalle ta ya kara kallon ta, duk abin da ya faru tsakaninta da Ishraq yana kallo. Ya rasa ita din ko wacce irin yarinya ce, ga kilbibi da sanabe, ga kuma tsiwa.
“Mallam ka min zuru kana kallo na, ni ka ba ni abin da na zo nema tun ba a ce na bace ko kuma an yi garkuwa da ni ba. Ka kuma daina kallon Ameera mallakin Yah Nura. Ahto!”
Gyada kanshi ya yi tare da dauko mata klin ya mika mata ita kuma ta fizga. “Yauwa ko kai fa, amma da ka tsaya kana abin da ba a ce ka yi ba. Yauwa ina da tambaya. Wai ku dan Allah da ma yan tsakiyar Birni haka kuke da kallo? Haka wancan zabayan…” ta juya hade da nuna wa mai shagon shi da yatsarta, a mamakinta sai ta gan shi a bakin kofar shagon ya nade hannuwanshi a bisa kirjinshi. “Mtsww ni karbi kudinka.” Ta jefa mishi kudin hade da daukar ledar klin ta tafi abunta.
Ya tako da sallama kunshe a bakinshi ya mika wa mai shagon hannu suka gaisa. “Don Allah ina da tambaya.”
“To Allah ya sa na sani.” Mai shagon ya fada hade da mayar da dukkan hankalinshi ga Ishraq.
“Wannan yarinyar ko ka san gidansu?”
“Wallahi ban taba ganin ta ba sai yau. Ai ina kallon dramanku fa, ina daga nan ina dariya. Ko ni daga zuwanta za ta mun tsiwa. Kai waccan da ganin ta za a sha fama.” Ya kwashe da dariya.
Ba abin da Ishraq ke son ji ba ke nan. Bai so a ce mutumin bai san Ameera ba. Haka kawai ya ji soyayyarta a cikin ranshi. Bai taba ba, wannan shi ne karon farko da soyayyar wata diya mace ta shige shi bayan mahaifiyarshi. Karon farko da soyayya ke neman yin tasiri a kasan ruhinshi. Ya dafe kanshi yana neman mafita. Kafin ya kara cewa komai mai shago ya ce,
“Da alama fa ba yar garin nan ba ce, don na ji tana zancen haka yan cikin birni suke. Hehe, alamu sun nuna wayayyar bakauya ce.” Ya sake kwashewa da dariya.
Bai ce komai ba Ishraq, ya taka ya bar shagon, ya so ya hangi ta inda ta bi, sai dai ko alamunta babu, ko inuwarta ba ya iya hange, ya hau duba sawun takalminta, sai dai a banza, da ya bi nan sai ya ga ya sake dawo da shi shagon nan.
“Ameera!” Ya kwala mata kira da karfi, a tunaninshi ko wani lungu ta bi za ta iya jin kiranshi, sai dai a banza. Ya hau motarshi yana bin dukkan layin da ya gani, bai gan ta ba. Ya koma tafiya da kafa, shiru bai gano ta ba. Da takaici ya koma motarshi. Ya hada kanshi da sitiyari yana tunanin kaunar karamar yarinyar da ta gama tsiwace shi. Bai da yanda zai yi, bai da zabin da ya wuce ya tada motarshi hade da barin wurin, zuciyarshi na mishi kuna.
Sukuku ya shiga wurin mahaifiyarshi. Ta kalle shi ta kara kallon shi. Ta karanci halin da yake ciki, ta hangi damuwar da ta dabaibaiye mata tilon danta Ishraq. Ta cikin idanuwanshi ta karisa tabbatar da yana cikin damuwa. Ta iso gare shi, ta soka tafukan hannayenta a cikin nashi. Soyayyar da da mahaifiya na gudanya ta cikin gumin hannuwansu.
“Ishraq habeebee, mene ne damuwarka?”
Ya kalli Mami sannan ya kawar da idanuwanshi. “Mami, I met her..I found her Mami. Sai dai ta bace ma gani na. Ban san a ina zan gano ta ba kuma.” Duk ya marairaice muryanshi.
End of chapter
Hello sweethearts🥰ya kuke ya gida ya kwana biyu? Fine in shaa Allah. And we are here, sannu a hankali za mu san wace Ameerah, za mu san alakanta da labarinmu, what if ita ce ma tauraruwan labarin?🤔🤥no oooo, Mahboobah? Ko su duka biyun?🤣oho. A bibiye ni don jin kome.
Okay Okay, I know the book is kinda boring😫😣huh, the game is about to start. I didn’t start Bakuwar Fuska to disgrace myself😄😅just tighten your belts.
Princess Amrah
RAZ 2Story continued…(Ci gaban labari)
A bisa screen din wayarta ta saita idanuwanta, tana kallon lambar wayar Ishraq da ta sa Kamal masinjanshi ya turo mata. Ta kira ko ta tura text message? Ta yi ko kar ta yi? Ta bi zabin zuciyarta ko ta bi na yan uwa da kawayenta? Ta fi karfin minti talatin a haka, ta rasa abin da za ta yi, ta rasa me za ta zaba me za ta ajje. Zuciyarta sai saka mata abubuwa take yi.
+
“Ya Allah!” Ta ambaci sunan Allah. “Ya Zuljalalu wal Ikraam! Ya Ahadussamadu lam yalid walam yuulade. Allah ka kawo mun mafita ya Allah!” Ta latsa kiranshi.
Bugu uku ya dauka da sallama. “Na tabbata da ka san wace ce da ba ka bata lokacinka wurin yi mini sallama ba. Da a ce ka san Mahboobah Bukar da kai ma tsanar duk duniya ce da ba ka dauki kiran ta ba Ishaq. Ni din ce dai na kira ka. Na nemi lambar wayarka domin na fada maka wani ab…” kafin ta kai karshe ta ji kit ya kashe wayarshi.
Ta gyada kanta da murmushi hade da kuka shimfide a saman fuskarta. Text message ta hau aika mishi,
‘Ishraq Sulaiman, duk da ba ka tsaya ka saurari me nake tafe da shi ba hakan ba shi zai hana ni bayyana maka ba. Ina so ka sani, daga yau, daga rana mai kamar ta yau, ni Mahboobah Bukar na fita daga rayuwarka, na fita daga sabgoginka, ni da kai har abada! Sai dai hakan ba shi yake nufin na janye kudurina a kanka ba. Rayuwata tana kaunarka, yau, gobe, jibi, har abada Ishraq. Na bar rayuwarka ba don wulakantani da kake ba. Na janye kudurina ba don ka nemi hakan ba sai don farin cikin family dina. Duk duniyar nan ba ni da masoya sama da yan uwana da mahaifiyata da kawayena na rai da rai guda biyu. To dukkansu ba su ba ni goyon baya ba. Duk sun ji haushina a kan naciyar soyayyar da nake a ganinsu ga mutumin da bai cancanta ba.
A karshe Ishraq, ina so ka sani Mahboobah mace ce mai aji, mace ce mai kamun kai, mace ce da ta san kanta fiye da kima. Kaddarar soyayya ce ta fada gare ta, wanda ba ta fi karfin ta fada kan kowa ba.
Idan ka ji labarin mutuwata ka yi mini addua. Na bar ka lafiya.
From,
Mahboobah Bukar’
Daga haka ta tura mishi sakon hade da jifa da wayanta kan gado, ta fasa wani irin kuka mai kara. Tana ganin komai na zo mata baibai a duniyarta.
Takun Fareeda ta ji a cikin dakinta. Ba ta daga kai ta kalli inda take ba, har a lokacin kanta a duke yake tana kuka, kukan hukuncin da ta yanke da kanta. Kukan zabinta da ta yakitar domin farin cikin ahalinta.
Fareeda ta zauna a gefenta. Ta gaji da rarrasar Mahboobah. Duk wasu kalamai nata na rarrashi sun kare, idea dinta ta kai karshe, sai dai ta zura ma yar uwarta ido tana ta kallon yanda take kuka da dukkan karfinta.
“Yah Boobah.” Ta kira sunanta. Kamar tana jiranta ta dago kanta, ta saita rinannun idanuwanta a cikin na Fareedah,
“Na cika muku burinku ba don zuciyata tana so ba. Na yakice Ishraq Sulaiman daga zuciyata ba don na daina son shi ba. Fareeda…” ta yi kokarin shanye kukanta, tana jin radadin kalaman da take bultsowa a tsakanin labbanta. Ambatar ta rabu da Ishraq daidai yake da ambatar mutuwar wani sashe na jikinta. Da kyar ta daure, ta ce “Ke da kika kira su Haneefa kika fada musu halin da ake ciki, sai ki kira yanzu ma ki shaida musu Mahboobah Bukar ta hakura da muradin zuciyarta, Ishraq Sulaiman. Sai dai ku shirya zama da holokon gangar jiki. Ku shirya zama da wata sabuwar Mahboobah ba asalin wacce kuka sani ba. Wannan wata ce daban da ke amsa sunan rayayya, sai dai a zahiri gwara butum butumi da ita.”
Daga haka ta mike a saman kafafuwanta, ta kalli Fareedah sama da kasa. “Ba a kaina farau aka fara zaman kunci saboda soyayya ba. Kar ku nemi tilasta ni a kan lallai sai kun ga na dawo daidai, abu ne mai matukar wahala wannan. Ku bar ni kawai, ina nan zaman jiran lokacin da kurwata za ta fice daga gangar jikina, a kai ni kabari a binne.” Kai tsaye ta wuce toilet.
STORY CONTINUES BELOW

Da sauri Fareedah ta sha gabanta, wani irin kuka ta ji ya zo mata. “Me kike nufi Yah Boobah? Kina nufin gwara halin da kika shiga na soyayyar Ishraq a kan halin da za ki shiga yanzu na rabuwa da shi? Kar ki mana haka, don Allah kar ki mana haka Yaya. Tilastakin da aka yi na ki cire soyayyar Ishraq ba shi yake nuna mun tsane ki ba. Hakan ba yana nufin ba mu kaunarki ba. Soyayya ce, soyayya ce dari bisa dari wallahi. Ki taimaka kar ki mana haka.”
Ba ta ce mata komai ba kawai ta janye jikinta ta shiga toilet.
Sunan Allah kawai Fareedah ke ambato. Ta kasa gasgata wannan al’amarin, har a wannan lokacin gani take akwai dai wani boyayyen lamarin da babu wanda ya sanshi. Ta janye jikinta ta fadi a kan gado dafe da goshinta, tana jin tsakiyar matsirar gashinta na sara mata.
***
Tsaki ya yi a karo na ba adadi, yana jin yanda kiyayyarta ke kara ratsa tsakiyar zuciyarshi.
“Na gaji da jin tsakinka fa Ishraq.”
Wani tsakin ya kara yi, “Khalid Zannah, ba za ka gane irin tsanar da na yi ma yarinyar nan ba ne. Ko sunanta na tsani ji balle maganarta. Na rasa wace irin ‘yar anace ce. Ko kadan Mahboobah ba ta jin wulakanci. Ba ta san wata kalma wai ita tozarci ba. Na tsane ta Khalid, na tsane ta da dukkan rayuwata.”
Kafadarshi Khalid ya dafa, ya yi murmushi hade da gyada kanshi. “Ishraq, we psychologists…”
“Just shut up Khalid Zannah. You psychologists what? In banda karya me kuka iya?”
Ya yi dariya sosai Khalid har yana tuntsirewa, “Doctor Ishraq Sulaiman, ban san gaibu ba amma na hango yanda soyayyar Mahboobah za ta narkar da zuciyarka. Na hango yanda kaunarta za ta nemi tsaga maka zuciya. Na hasasho yanda za ka rayu da Mahboobah, ku yi soyayya tare da samun albarkar aure…”
“Impossibile! This will never ever happen Khalid. Ka manta duk bakin da ya furta ki ko ya furta so karya ne? Ban yarda ba Khalid. Hakan ba za ta taba faruwa ba. Ni Ishraq Sulaiman ba zan taba son Mahboobah bah. Ba zan taba son wannan halittar da na tsana ba. Ameerah nake so ita kadai. Ameerah nake da burin aure komai daren dadewa.”
Khalid ya dan tauni lebonshi, “Tsananta mata wannan kiyayyar shi ne zai sa ka so ta din. Shi ya sa aka ce idan za ka so mutum ka so shi saisa-saisa. Idan za ka ki mutum ka ki shi saisa-saisa. Don wata rana zai iya rikidewa ko da ba a so ba.”
Ishraq ya yi shiru ba wai don kalaman Khalid na shigarshi ba.
“Wallahi Ishraq ina shawartanka tun wuri ka fita harkar yarinyar da kai kanka ba ka san asalinta ba. Ba ka san wace ita ba. Idan za a kashe ka a ce ka gano inda take yanzu ba ka sani ba. Kana nan zaman jiran ta ka gagara ka tsayar da matar aure har yanzu. Ishraq me ka rasa? Kana da kudi. Kana da kyau. Kana da asali. Sannan kuma kana da kyakkyawan tushe. Ba ka rasa matar aure ba, kusan kullum da kalar macen da take kawo maka hari. Ka janye wancan tunanin, ka janye kudurin nan, ka cire Ameerah daga zuciyarka domin Allah.”
Ajiyar zuciya ya sauke me nauyi, ya dafe kanshi yana jin radadin kalaman Khalid Zannah na cewa ya cire soyayyar Ameerah daga zuciyarshi. Daga zuciyarshi ma ko daga ruhinshi? Ba da zuciya kawai yake son Ameerah Muhammad ba, da ruhi da dukkan halittar halittarshi ne. Ta yaya zai iya? Kimanin shekara uku ke nan da haduwarshi da Ameerah, sau daya tak, amma har a wannan lokacin jin soyayyarta yake sabuwa a kasan ruhinshi. Jin ta yake har a jinin jikinshi. Ta ina zai fara? Ta yaya ma zai nufi farawar? Never! Never Khalid Zannah!
“Na sani akwai wahala Ishraq. Na san yanda cire abin da ake so yake daga rai. Na san ciwo da dacin rashin masoyi. Amma ina so ka gane wani abu, har yanzu ka kasa gano inda Ameerah take. Ba ka ma da tabbacin shin mutum ce ko aljanah ce? Yarinyar kirki ce ki ta banza ce? Tana da rai ko bata da shi? Duk ba ma wannan ba, kai da kanka ka amsa cewa bakauya ce. Shin kana da tabbacin tana nan har yanzu ba a mata aure ba? Ka san halin kauyawa da wuri suke ma yaransu aure, ba ka tunanin an aurar da Ameerah ga wani?”
Tamkar an daba mishi mashi haka ya ji. Tamkar ana zuba narkakken darma a cikin kunnuwanshi haka kalaman Khalid Zannah ke ratsa tsakanin kumnuwanshi. Zuciyarshi zafi take mishi. Ya san gaskiya ce duk abin da Khalid ke fadi, sai dai soyayya ta makantar da shi, ta sa ya kasa ganin duk gaskiyar da Khalid ke kokarin ganin ya tabbatar mishi da ita. Soyayya ta makantar da shi, ta sa ya kasa gasgata zancen da shi kanshi ya san gaskiya ne.
“Ni zan koma, Junior na fama da zazzabi zan kai shi asibiti. Ka fada ma Mami, ba zan samu shiga mu yi sallama ba.”
Bai ko jira jin ta bakin Ishraq ba daga haka ya kama hanya ya fice.
Tun da Khalid ya fita Ishraq ke saka da warwara. Zuciyarsa yake ji kamar za ta tsage ta fito waje saboda tsananin soyayyar Ameerah da ke cike da ita. Wai har a haka ne ake tunanin akwai wacce zai iya sakawa a ciki?
Hannuwanshi biyu ya saka a cikin sumar kanshi. Ya ji takun Mami da tun dazu take jiyo duk zantukan shi shi da Khalid, hakan ya saka shi kokarin daidaita nutsuwar shi, sai dai a banza. Shi kanshi ya san ba abu ba ne mai yiwuwa ya boye damuwar shi ga Mami, macen da ta fi kowa sanin shi. Macen da ta san damuwar shi a kan kowa. Ta nemi bagire a kusa da shi ta ma kanta masauki. Ta dafa kafadarshi tare da cewa,
“Ni ban san ranar da Ishraq dana daya tilo zai kawar da soyayyar halittar da ba lallai akwai ta a doron duniya ba. Ban san ranar da zai saka ma kanshi nutsuwa ba. Ban san ko sai yaushe Ishraq zai daina wulakanta mata ba ya kawo mun zabin shi.” Ta hadiyi yawu mai daci hade da kawar da kanta daga gare shi. Ta ci gaba da “Ko sai lokacin da numfashina ya rabu da gangar jikina aka kai ni kushewata aka binne? Ina ji kannena su ke da rabon ganin gudan jinin Ishraq dana. Hmmm…!”
Daga haka ta mike a bisa tafun kafafuwanta, ba tare da ta sake cewa komai ba ta fice daga dakin.
Kamar ya tashi ya bi ta ya ji, kamar ya sha gabanta ya ji, kamar ya ba ta hakuri tare da tabbatar mata da cewa zuciyarshi ba ta ba shi Ameerah ba ta raye. Sai dai bai da wata hujjar fadan haka. Dan dolenshi ya barta ta fita, har sai lokacin da ya samu nutsuwa sannan ya je gare ta tare da ba ta hakurin in shaa Allahu komai yana daf da warwarewa.
End of chapter
Hello cupcakes. Ya kuke ya iyali ya kwana biyu? Ya muka ki da wannan yanayi na rayuwa da muke ciki ga coronavirus😫? Allah ya saukaka mana ya kawo mana maganin abin da bamu iyawa.
Toh ya kuma labarin namu? Fatan yana tafiya yanda ya kamata. Well…Mahboobah son maso wani. Ishraq son wacce bai san wace ita ba bai san inda zai gano ta ba. Toh a cikinsu wa ya fi wani soyayyar iska?😂
Ok Okay, bari in barku haka. Meet y’ll later.
Princess Amrah
RAZ 2Flashback-10th January 2010 (Komawa Baya)
Hodar hannunta ta sake goga da soso ta shafa a fuskarta, wannan shi ne karo na uku da ta dangwala. Mama da ke kallon ta tun dazu ta gagara magana sai a lokacin dai ta daure ta ce, “Ameerah da dai kin hakura kin bar fuskarki haka, wannan hodar ai ta yi yawa. Ji beki dan Allah sai ka ce wata zabaya.”+
Ba ta dauke kallon ta daga kan karamin madubin da yake hannunta ba ta ce, “Oh ni Hajiya Mama, idan kuma ban shafa hodar nan ba sai ki ce zan fita fuskata sai maiko da naso take. Kuma na shafa an ce ta yi yawa. Yau ni Ameeratu jikar Habu da Sule ya zan yi?”
Mama ta gyada kai kawai, ta gagara cewa komai sai kuma kallon yanda take gwaguda kwalli take.
Da murmushi Ameerah ta ajje madubin ta kalli Mama. “To yau dai ba zan tambaye ki na yi kyau ko ban yi ba Mama, don na san ma cewa za ki na yi. Ko?” Ta fada tana dariya.
Mama ma dariya ta yi, “kin dai san cewa zan yi ba ki kyau ba. Ke wallahi ki sake duba madubi ki gani. Yanda fa kika san aljana haka kika koma Ameerah.”
“Yau ni na boni, daga zabaya kuma na koma aljanah.”
Kafin su sake cewa komai suka ji sallamar yaro. “Wai Nurah ya ce yana kiran Ameerah a waje.”
Ba ta amsa shi ba sai da ta kai dubanta ga Mama ta ga ita take kallo, ta sunne kanta tana dariya.
“Ja’ira! Wato kin san Nurah zai zo ashe shi ya sa kika dage murza jambaki da hoda a fuska. To ni dai aikenki zan yi kuma ke ma kin sani.”
“Uhm ai na sani Mama. Tsarabarshi ce fa kawai zan ba shi ya tafi. Kin san jiya da ya zo ai ba mu kwance jaka ba.”
Mama ta hau tafa hannuwanta, “Oh ni wai ba mu kwance jaka ba, sai ka ce wanda suka dawo daga Hajji. Allah ya shirye ki Ameerah. Ni dai ki maza ki je ki dawo ki tafi mun gidan Saratu.”
“Wai ma, Mama me ya sa kike masifar son zama dakina? Kina jin dadin hira da ni koh?” Ta dafe cikinta don dariya.
Ta rasa Ameerah wace irin takadarar yarinya ce. Haka take tun tashinta, duk inda take mutanen wurin basa taba bacin rai tsabar ban dariyar ta.
“Tun da bani da amsa bari in tafi in dawo.” Ta fada bayan ta jawo yar bakar leda daga cikin jakarta. Ta bar wurin tana kallon yanda Mama ke gyad kai da murmushi.
“Yah Nurah…Assalamu alaika.”
Ya kalle ta cike da murmushi da shaukin kauna. “Ameerana, Sallamar dai ya kamata ki fara yi kafin fitar Yah Nuran ko?”
Ta dan gatsine fuska. “Sai hakuri in dai Ameerah ce.”
“Na fi kowa sanin haka. Na fi kowa sanin Ameeratuna.” Ya sakar mata murmushi.
“To ya gajiyar tafiya? Ya Mamana take?”
“Ba gajiya wallahi. Mama tana lafiya.”
“To ma shaa Allahu. Ba ki ba ni labarin Kaduna ba. Kd baby.” Ya saki murmushi. Ta dan yatsine fuska hade da yi mishi hararar wasa.
STORY CONTINUES BELOW

“Lallai ma Yah Nura ni ce Kd baby din?”
“Ehh mana, ki ba ni labari samari nawa kika yi? Maza nawa suke kalle mun ke? Kawaye nawa kika yo? Sannan kuma mutum nawa kika tsokano fada?”
Ta kwashe da wata irin dariya. “Wato Yah Nurah har ma ka san na yi tsokana ko?”
Shi ma dariyar ya yi ya ce, “Ai na san wannan dole ne Ameerah. Ke din nan da tsokanan fada a ce kin je Kaduna kin dawo ba ki tsokani kowa ba, ai sai dai idan tare da Mama kike har kuka dawo. Ke ko kina tare da ita ma sai kin yi tsokana na tabbata. Mai hali ba ya barin halinsa.”
Ta tafa hannunta sosai tana dariya. “Ban tsokani kowa ba Yah Nurah ka yarda da ni.”
“Toh da mutum nawa kika yi fada?”
“Gaskiya ba zan maka karya ba…”
Kafin ta ci gaba ya ce, “Ehen, ai na san wannan dole ne.”
“Uhm. Ranan da aka kai amarya na fita in siyo omo, ni kam na taho ban saba da babban titi irin na can ba, na saba da dan karami irin namu na nan. Ban kula ba kawai na taho ashe wani mai mota ya taho, ai kam ya kusa yin sama da ni.”
“Na shiga ukuna! Bai dai taba mun lafiyarki ba ai ko? Motar ba ta taba ki ba?” Ya fada a rude.
“A’a ai ya take burki fa, amma na tsorata sosai. Wai amma mutumin nan don ya rainan hankali sai ma ya fito zai balbale ni. Wai fa Yah Nura ‘Ke’ ya ce mun.”
Bakinshi ya dafe Nurah, yana danne dariyar da ta zo mishi ba shiri. “Lallai kuwa ya taro match. Don da ya ce ma Ameerah ke gwara ya mari kanshi sau goma.”
Ita ma dariyar take sosai, “Ana ma magana Yah Nura. Ai ya sha masifa kuwa, ya tsorata da ni ya kasa cewa komai.”
“Bawan Allah. Kuma fa ke ce da laifi Ameerah. Me ya sa ba ki tsaya kin duba titi ba sosai?”
Bata fuska ta yi sosai kamar ba ita ba ce ta gama dariya. Yana ganin haka ya sha jinin jikinshi. Ya san halin Ameerah sosai, ya gano manufarta.
“Ni din banza na ce da Ameerana ta yi laifi? Shi dan birnin dai shi ne da laifi. Ai sai mutum ya ringa kula sosai…”
“Wai Yah Nurah ni za ka ma wayo ko? Amma tsakani da Allah mutum ya tashi kade ni da mota kuma sai ya zo zai nemi fi na masifa? Ashe ma sai in kyale shi ya ce mun Ke. Ka fi kowa sanin na tsani kalmar nan, komai girman mutum ya kira ni da Ke sai na ba shi amsa ko da ta ruwan sanyi ce. Yah Nurah ba dai ni za ka kware wa baya a kan wani zabaya ba ko.” Ta kara bata fuska hade da kawar da fuskarta daga kallon shi.
“Haba haba Ameerana, wasa fa nake miki dan Allah. Kin san ba na son ganin bacin ranki. Ki saki fuskarki kin ji muradin zuciyata. Amarya ga Nurah ikon Allah.”
Ba ta san sadda ta sakar mishi murmushi ba. Ya san sigar rarrashinta sosai. Ya san rigimar Ameerah kuma ya san hanyoyin magance ta.
Daga bakin zaure suka jiyo muryar Mama. “Wai Ameerah ba cewa na yi ku gaisa ba ki dawo ki je mun aiken nan? Na tabbata ba dai Nurah zai rike ki ya hana ki dawowa ba, sai in da ma ba ki fada mishi zan aike ki ba.”
STORY CONTINUES BELOW

Sosa keyarshi ya yi, wata irin kunya ya ji ta lullube shi. “Uhm ta fada mun Mama, wata yar magana ce muke yi kuma mun gama, yanzu za ta shigo in shaa Allahu.” Ya yi karya don ya rufa wa Ameerah asiri.
“To Nurah. Ya kuke ya su Innar taka?”
“Suna lafiya Mama. Ya kwanan gajiya?”
“An gode Allah. To sai ta shigo. A gaida gida.” Daga haka ta shige gida tana gyada kanta, ta sani, ta san cewa karya Nurah ya mata don ba ya son bacin ran Ameerah. Ta tabbata inda ta sanar da shi da tuni ta koma gida. “Kai Allah dai ya shirya mini yarinyar nan.”
Dariya sosai Ameerah ke yi tana kallon yanda Nurah ke rarraba ido ya shantalo karya. “Sannu don Allah Yah Nurah.” Da kyar maganar da fito daga bakinta tsabar dariya.
“Oh ni Nurah. Ke dai Ameerah babu wanda kika kyale wato. Bari in shiga in fada wa Mama gaskiya to.”
Ledar tsarabarshi ta ajje kasa hade da tafiya da gudu ta nufi gida sai faman dariya take.
***
Ya paka motarshi a gefen titi, a hankali ya taka ya isa gaban shagon, da sallama kunshe a bakinshi.
“Yauwa, barka dai Mallam Ishraq. Ya kwana biyu?”
Cikin sakin fuska Ishraq ya amsa da “Lafiya lau Mallam Mujaheed. Yau ma dai ga ni na dawo. Jiya da shekaranjiya duk ban zauna ba shi ya sa ban samu na zagayo ba.”
“Na ayyana haka a raina kuwa tun da ban gan ka ka zo ba. Wallahi Ishraq har yanzu dai shiru ban ji wani labari a kanta ba. Kusan duk yaran da ke unguwar nan idan sun zo nan sai na tambaye su ko sun san wata Ameerah Muhammad ko kuma wanda ya san ta, amma babu daya. Ko yanzu yarinyar can da ka hadu da ita ta fita, sai da na tambaye ta ta ce ai duk area din nan ma babu wata Ameerah.”
Cikin sanyin jiki Ishraq ya ce, “Da ma ai ba lallai a san ta ba na sani, na fi kawowa a raina ziyara ta zo. Gidan da ta kawo ma ziyarar dai ya kamata mu bincika, watakila a dace.”
Mujaheed ya ce, “Haka ne. Sai dai ta yaya?”
Shiru Ishraq ya yi yana nazari. Bai san ta inda za su fara ba. Wannan wani wahalallen aiki ne yake neman kinkimo musu.
“Abin da na rasa sani ke nan Mujaheed. Yanda za a yi, ka bar shi kawai. Ka yi iya kokarin ka na sani, Allah ne kadai zai iya biyanka. Na gode sosai da wanda ka yi. Ka hutar da kanka kawai, sannu a hankali in da rabo za ta sake dawowa, in ta dawo don Allah kar ka yi kasa a guiwa wurin kira na a waya, duk inda nake zan kokarta zuwa, ko ban zo ba ma akwai wata mafitar.”
“Babu komai Ishraq. Ina maka fatan alkhairi. Allah ya sa a dace.”
“Ameen ameen Mujaheed. Thank you once again.” Daga haka suka yi sallama, ya bar wurin.
Bakin titi ya isa, daidai wurin da ya hadu da Ameerah, ya kura ma wurin ido yana tuna ranar da idanuwanshi suka fara arba da ita, ranar da zuciya da gangar jikinshi suka karbi bakuncin bakuwar halittar da ta saye dukkan ruhinshi. Bai san sadda idanuwanshi suka cika taf da kwalla ba. Bai san lokacin da ruwan hawaye suka hau kwaranya bisa kumatunshi ba. Sai ganin halittar Ameerah ya yi a wurin, ya ga tana kallon shi tana sakin murmushi. Ta iso gare shi, ta saka hannuwanta a cikin nashi, ta saita idanuwanta a cikin idanuwanshi.
“Ina ta jin labarin nemana da kake yi, bawan Allah, sannu ka sha wahala. Yau dai ga ni na bayyana gare ka. Ga Ameerah a gaban Ishraq ya fada mata sakon zuciyarshi.”
Ya saki murmushi yana sake kallon ta, ya yi magana ma ya kasa, murna da farin ciki ba za su bar shi ba. Kallon fuskar Ameerah kadai ya hana shi ko da kwakkwaran motsi.
“Ishraq ga Ameerah Muhammad a gabanka, ka isar da sirrin zuciyarka gare ta.”
Ya bude bakinshi zai yi magana ke nan ya ji saukar mari a fuskarshi. Tuni ya dawo hayyacinshi, ya kalli dattijon da ke tsaye a gabanshi sai huci yake kaman bakin kumurci.
“Mallam how dare you? Waye kai? Me na maka da za ka mare ni?”
“Oh ashe cikakken mutum ne ba mahaukaci ba. Ashe ba kurma ba ne karar horn din da ake ta mishi ne ya gagara ya ji.”
Shiru Ishraq ya yi, bai san me yake damun shi ba. Bai san laifin da yai ma soyayya ba take wahalar da shi har haka.
“Ni ba mahaukaci ba ne, ba kuma kurma ba ne. Kuma marin da kai mun ka je kai da Allah.”
Daga haka ya bar wurin, ya nufi inda motarshi take.
Wannan shi ne zuwanshi na goma sha daya wannan unguwar, tun bayan haduwarshi da Ameerah. A rana har sau biyu yana zuwa neman ta. Ya je wurin mai shagon da ta siyi Omo ya ba shi cigiyarta. Sai dai shiru, babu ita babu alamunta, babu kuma wanda ya san ta.
Kanshi ya hada da sitiyari, zuciyarshi yake ji tana mishi tsananin zafi. Ya ji zafin marin da dattijon yai mishi, sai dai ko rabi-rabin zafin rashin Ameerah bai kai ba. Shi babban takaicin shi ma da tsohon ya dawo da shi duniya bai kai ga fada ma Ameerah sakon zuciyarshi ba. Ya so a imagination din da yake yi ya sanar da ita irin kaunar da yake mata, amma bai samu dama ba.
Ya jima a haka kafin ya tada motarshi ya bar wurin, yana jin ciwo sosai, yana jin yanda duniyarshi ke juye mishi. Wasu irin hawaye masu radadi na ketowa tsakanin idanuwanshi.
End of chapter
To fa! Ishraq fa abu ya girmama😨😹😹😹har da su dogon imagination kamar mai almatsutsai😹bawan Allah. Ni fa gare ni sai in ce gwara Mahboobah, yo ai ita ta san wanda take so. Shi kuwa sau daya tak daga kallon yarinya duk sai ya firgice kamar zautacce. So ke nan, inji Hameesu Breaker😹1
#amnoor
#bakuwarfuska
#nagartawriters
Princess Amrah
RAZ 2Da sallama kunshe a bakinshi ya shiga dakin Maminshi. Ya tarar da ita zaune a bakin gado tana kallon Sunnah TV. Har kasa ya duka ya gaishe ta ta amsa mishi ba yabo ba fallasa. Da tsananin kunar zuciya ya zauna a kusa da ita, ya dauki remote ya kashe kallon sannan ya fuskance ta bayan ya dora hannuwanshi a saman cinyarta.+
“Ki yafe mun Mami…” cikin rawar murya ya kwakulo kalaman neman yafiya a kasan makoshinshi.
“Me ka yi min Ishraq da kake neman yafiya a wurina?”
“Ki yi hakuri Mami, don Allah ba dan halina ba.” Ya dora kanshi a saman cinyarta ruwan hawayenshi na jika zanin jikinta.
Cikin rauni da tausayi ta kama shi ta tasar zaune. Hab’ar rigarta ta sa tana share mishi hawayenshi.
“Mami yau tsawon kwanaki uku ke nan bakya sakar mun fuska. Ko magana na yi miki ciki-ciki kike amsawa. Idan na gaishe ki ba na jin amsar gaisuwa a bayyane sai dai in kula da motsin bakinki. Mami…” ya koma a kasa ya yi kneel down. “Ni mai rauni ne a kanki kin sani Mami. Kin sani ba zan juri ganin bacin ranki ba, bacin ranki a kaina. Zan iya jurar bata wa kaina rai, amma zuciyata ba za ta iya daukar bacin ranki ba. Mami komai na yi miki ga ni durkushe a gabanki ina neman yafiyarki. Ga tilon danki na zubar da hawayen ganin kuncinki.”
Ta sake kama shi ta tayar tsaye. Ita kanta ba za ta iya jurar ganin Ishraq a wannan halin ba. Ba za ta iya jurar ganin hawayen rabin jikinta ba, rabin ruhinta, rabin duniyarta ma baki daya.
“Ya isa haka ka daina kuka Ishraq. Ka daina na yafe maka ka ji.”
Da hanzari ya saki murmushi, ya kura mata ido cike da soyayyar da da mahaifiya.
“Na gode Mami, thank you so much Mamin Ishraq.”
“Yauwa. Amma ba ka tambaye ni ba dalilin yin fushin da kai.”
Duk da bai gama tabbatarwa ba amma zuciyarshi ta ba shi kyankyashen labarin. Tun daga ranar da Khalid Zannah ya zo suka yi magana har Mamin ta shigo dakinshi ba ta sake sakar mishi fuska ba. Ba ta sake bari sun zauna shi da ita sun yi magana ba. Sai yake ganin kamar Khalid ne ya san duk ma yanda ya yi ya cusa wa Mami wani raayin a kanshi, tun da dama ba da dadin rai suka rabu ba ranar, yana tsaka da jin haushin naciyar soyayyar Ameerah da babu wanda ya tabbatar da wanzuwarta a doron duniya.
“Mami Khalid ne ko?”
Ta tabe baki hade da gyada mishi kai. “Me ya sa ka kawo sunan Khalid mutumin kirki? Me ma kake zargin ya yi? Ko na ce maka wani abu ne yanzu?”
Cikin marerecewa ya gyada mata kai.
Bari ka ji Ishraq. Duk maganganun da kuka yi kai da Khalid a cikin kunnuwana ne, babu abin da ban ji ba. Duk gaskiyar da Khalid ya fada maka kana botsarewa na ji.”
Duk da haka bai yarda ba Khalid din ba ne. Ya dai daga kai kawai don ba zai iya musa wa Maminsa ba, bare a daidai wannan lokacin da yake tsaka da lallabarta.
“Ishraq a yau zan yi magana ta karshe da kai game da aure. Zan ba ka dama ta karshe wacce daga ita zan zare hannuna daga duk wani batu da ya danganci samuwar iyalinka.” Ta mike a saman kafafuwanta.
“Na ba ka daga nan zuwa July ta wannan shekarar 2020, wata biyu ke nan, ka fitar da mata ka yi aure. Idan ba haka ba Ishraq, ba zan sake jin ban hakurinka ba. Ba zan sake saurarar ka ba, sannan zan yafe ka ga duniya, watakila hakan zai fi maka dadi, idan ka rasa mafadi.” Ta kama hanya za ta bar mishi dakin, har ta kai bakin kofa kuma ta sake juyowa ta ce, “Zancen Ameerah kuma ka ci gaba da yi. Ka ci gaba da ajiyar soyayyar halittar da ba lallai akwai wanzuwarta ba. Bai dame ni ba ko ita za ka kawo a matsayin matar aure, ko za ka kashe kanka wurin nemanta ne, mata na ce ka fitar kawai.” Daga haka ta fice daga dakin ba ta ko tsaya saurarar abin da labbanshi ke luguden furtawa ba.
STORY CONTINUES BELOW

“Ya Allah!” Ya fada da wasu irin zafafan hawaye. Tun da yake a duniyarshi bai taba ganin kalar wannan bacin ran shimfide a saman fuskar Maminshi ba. Mami mutum ce mai sakin rai, mutum mai son faranta ran kowa, bare kuma shi, gudan jininta, da ta tsani ganin bacin ranshi ko yaya.
Ya zaro wayarshi daga cikin aljihu ya latsa kiran Khalid,
“Likita barka da…” ya ci burki da maganar da yake yi sanadiyyar shesshekar kukan Ishraq da ya daki dodon kunnuwanshi. “Subhanallahi! Ishraq lafiya?”
“Ba lafiya ba Khalid. Kana ina? I want to see you urgently Khalid. Ina son ganin ka. Akwai damuwa, damuwa mai girma. Ka san kai ne asusun ajiyar dukkan sirrikana. Madogarar da nake dogara damuwata ta nisance ni a kowanne lokaci Khalid. Kai ne kadai hope dina, kai ne hope dina Khalid Zannah.” Ya l karisa zancen cikin kuka sosai.
“Kana ina yanzu?” Khalid ya tambaye shi cikin rikicewa.
“Ina gida.”
“Okay to ga ni nan zuwa yanzu in shaa Allah. Amma dai abin da nake so ka daina kuka ka ji. Ka kwantar da hankalinka in shaa Allahu komai zai zo da sauki, komai zai daidaita.”
“Sai ka zo.” Kawai ya iya furtawa, yana jin rashin yiwuwar kalaman Khalid Zannah na cewa ya kwantar da hankalinshi. Ta yaya? Ta ina zai fara kwantar da hankalinshi bayan duk damuwar da take mamaye a duniyarshi? Ya tashi jiki ba kwari ya doshi dakinshi. Damuwa da kunci mamaye da duniyarshi.
Yana zaune ya yi tagumi ya ji shigowar Khalid. Babu ko sallama Khalid ya zauna a gefenshi.
“Ga ni na zo to, ka daina kukan ka fada min dukkan abin da yake faruwa.”
Bai iya dakatar da kukan ba, sai dai ya nutsu sosai yana kokarin zakulo bayanai daga kasan makoshinshi.
“Khalid, Mami ce, ta ba ni wata biyu, nan da karshen July din wannan shekarar, wai in ban fitar da matar aure ba kafin nan babu ita babu ni. Khalid ya zan yi? Ya zan yi da rayuwata? Kai shaida ne, ba ni da wacce nake so. Ameerah kadai, ita kadai ce muradin zuciyata. Sai dai na rasa ta, na rasa inda zan gano ta Khalid. Ka taimaka ka ba ni mafita, ko ka roka mun Mami ta kara min lokaci, ina ta addua na san in shaa Allahu tana gaf da karbuwa. Ameerah za ta bayyana gare ni cikin lokaci kadan, ina ji a jikina.”
Gyada kai Khalid ya yi, sosai ya tausaya wa Ishraq, ya tausaya wa halin da yake ciki.
“Ishraq abokina, ka kwantar da hankalinka. Ka nutsu ka saurari bayanan da zan maka. Ishraq Maminka tana kaunarka, ya kamata ka gane na farko dai ba don bata sonka ba ne ta ba ka wannan umurnin, kawai gani ta yi idan ba ta maka haka ba ba za ka taba tsayar da hankalinka wuri daya ka tsayar da matar aure ba ne. Shekaru na tafiya, shekara 30 ke nan da wanzuwarka a duniya Ishraq. Inda ma a ce ba ka da halin yin auren ne duk da sauki, amma komai kana da shi, kawai dai ka ki ba kanka damar mallakar iyalin ne. Sannan abu na biyu, kai kadai Mami ta haifa, kai kadai gare ta duk duniyar nan sai kuwa dangi na nesa. Da a ce kana da siblings (‘yan uwa na jini) na tabbata ba za ta dame ka da zancen aure ba, saboda in ba ta samu jikoki a wurinka ba za ta samu a wurin ‘yan uwanka. To babu. Kai kadai din dai ne.
Ishaq, ina bayan Mami dari bisa dari. Na goyi bayan hukuncinta. Ka zauna ka nutsu ka san abun yi. Ka duba a duk cikin ‘yanmatan da suke kawo maka hari wace hankalinka ya fi kwanciya da ita? Wace ce diyar tarbiyya? Wace ce wacce za ka yi alfahari da ita na kasantuwarta uwar ya’yanka?”
Gyada kai Ishraq ya yi, “Ta yaya Khalid kake tunanin za a samu duk mai wadannan halayen a cikin macen da take kai tallar kanta ga namiji?”
“Ya kamata Ishraq ka gane bambancin tallar kai, da kuma tallar soyayya. Ko ba ka san suna da bambanci ba?”
Ya tabe baki, “Duk daya, wai makafi sun yi dare. Ni kam ban ga abinda ya bambanta su ba. Nakan raina duk yarinyar da ko salon wani abu ta canza a gaban namiji bare kuma ta iya furta mishi kalmar so. Ba na jin zan iya son ta. Ba na jin akwai wacce zan iya aure a duk wanda suke zuwa wurina da sunan soyayya.”
Shiru jim, Khalid ya yi, kafin ya ce “Bilkeesu fa?”
Sai ma yanzu ya tuno da ita, tun farko ko kadan ba ta fado mishi a rai ba. Ba ya son ta, bai taba jin ko kadan yana da raayin aurenta ba. Kamar yanda tun farko ya sa a ranshi akwai wata manufa a auren, haka yanzu ma bai cire wa ransa hakan bah. Sai dai yana ji a ranshi kamar ita ce rufin asirinshi a wannan lokacin. Ko ba komai ya san asalinta, ya san tarbiyyar yan gidansu, kuma ba ita ba ce ta kawo mishi tallar kanta ba, mahaifinta ne yake son hada su, wai yana son hada zuria da yan gidansu a yanda ya ce. Saboda k’arfafa zumuncinsu.
“Ka yi tunani dai, Bilkeesu ce kadai za ta hau wannan matsayin a yanzu Ishraq. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ba na so gaggawa ta haifar da nawa kuma. Kar a je garin sauri a yi zaben tumun dare. Ya kamata daga yau zuwa gobe, jibi har kwana biyar ma mu yi binciken halayenta, idan mun same ta da tsaftar hali sai ka tinkari Kawu Imran da zancen tun da dama abinda ya jima yana so ke nan.”
“Haka ne Khalid. Ta ina za mu fara?”
Khalid ya gyara zamanshi. “Ta makarantarsu ya kamata mu fara. Mu bincike su waye kawayenta? Su waye take muamala da su? A hankali muna dan bibiyarta har mu gane wace ce ita. Ko ya ka gani?”
Guntun murmushi Ishraq ya kirkiro, “Haka ne Khalid. Wannan ma wata mafitar ce. To amma idan ba mu same ta yanda muke so ba fa? Kana da wani alternative (mafitar)?”
“Ka daina kawo wannan zancen mana. A kodayaushe ka zama mai hope sai ka ga kana samun nasara a dukkan komai. In shaa Allahu za a dace. Kuma kar ka zauna, ka ci gaba da addua kana neman mafita da zabin Allah.”
Da murmushi shimfide a saman fuskarshi ya ce,
“Thank you so much Khalid Zannah. If you aren’t here, I wouldn’t be happy today. Thank you once again (Idan da ba ka zo ba da ba zan yi farin ciki ba yau. Na gode sosai).”
“Babu godiya a tsakaninmu Likita. Kai dai mu yi fatan Allah ya bamu nasarah. Sannan kuma, tun da dai bincike ne ake na gaggawa, ya kamata ka ba ni lambarta ma, yana da kyau a mana guntun tracing (bibiyarta) ta haka za mu qara sanin wace ce ita. Ko ya ka ce?”
“Haka ne Khalid. To amma matsalar ni ba ni ma da lambarta fa. Wai ma tsaya! Ina prouding (alfahari) din da kake you’re psychologist? Ba za ka hasasho mana halinta ba?”
Dariya sosai Khalid ya yi, “Kai din banza kuma kai da kake karyata mu? Kar ka wani damu, shi ma din zai yi aiki. Da yardar Allah cikin kwanaki biyar za mu gama duka.”
“Toh Allah ya yarje mana. Bari in samo lambarta yanzu.” Ya latsa kiran Khalifa.
Da sallama ya dauka suka gaisa sannan ya ce “Yah Khalifa phone number din Bilkeesu nake so idan akwai. Zan ba ta wani sako ne.”
Yana fadan haka Khalifa ya sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya. Dadi ya ji sosai, toh wane sako ne Ishraq zai ba Bilkeesu in ba na zuciyarshi bah? Ya sakar wa kansa murmushi.
“Hello Yah Khalifa are you with me? (Kana tare da ni?)”
“Uhmm…wai sorry. Eh ina jin ka. Ehh zan turo maka yanzu. Zan turo maka.”
Kashewa Ishraq ya yi hade da sakin guntun tsaki. “Duk ya dabarbarce na san har ya ayyana a ranshi son Bilkeesun nake. Mtswww! Allah ya kyauta mun in so wannan yarinyar. Bai san rashin wani zabin ba ne ya san ya ni neman ta.”
Cikin minti daya sakon lambar wayar Bilkeesu ya shigo mishi.
End of chapter
No long essay but I love you all. Don’t forget to vote, comment and share with family and friends.
Princess Amrah
RAZ 2A kan carpet din dakinta take zaune, ta hada kai da guiwa fuskart zuru-zuru. Gashin kanta duk ya barbazu a saman fuskarta babu gyara ko kadan. Rabon da ta gyara kanta tun bayan sallamarta daga asibiti, an fi wata daya ke nan. Lebonta a bushe duk ya farfashe ya tsage ta ko’ina. Idanuwanta sun zurma sosai, ga rashin kwalli sai abun ya kara lalace mata. Sannan k’ashi duk ya bayyana a wuyanta. Yatsun hannu da k’afarta duk akaifa ta yi zaqam-zaqam. Baki dayanta ta koma tamkar ba ita ba, gwara ma wata mahaukaciyar da ita, ko ba komai ita an san da ma can hauka take. Ita kuwa wannan da hankalinta, sai dai ta zauce, kallo guda za a ga bayyanuwar damuwa a saman fuskarta.+
A inda take jona chaji ta nufa, wayarta na jone jikin chajin ta zaro ta koma asalin inda take zaune, gallery ta shiga, hoton Ishraq da ya zame mata abincin cinta ta hau kallo, murmushi hade da hawaye suna bayyana a saman fuskarta. Sai dai idan hawayen ya diga a saman fuskar wayarta, saman hoton Ishraq da take kallo, ta sa harshenta ta lashe, ta sake ci gaba da kallon shi.
Haka take yi tun daga ranar da ta daukar wa kanta, Ishraq da kuma Fareedah alkawarin fita daga rayuwar Ishraq har abada.
Ba ta cin abinci sai dai kayan marmari da take fita kullum ta dauko a fridge dinsu. Sai ruwan shayi mai lipton wani lokaci. Momy ta yi bakin kokarinta har ta gaji ta zira mata ido. Fareedah kuwa da ma tun ranan da ta yi mata maganar karshe na cewa sai sun gwammaci gwara lokacin da take son Ishraq a kan yanzu, ba ta sake nufarta da zancen ba, ko tayin abinci ba ta mata, haka Yah Aliyu ma.
“Assalamu alaikum.” Haneefa ta yi sallama, hade da shigowa cikin parlorn.
“Wa alaikumussalam. Haneefa ne da Saleemah. Sannunku da zuwa. Ku iso.” Momy ta fada hade da gwada musu wurin zama.
“Yauwa Momy. Ina wuni?”
“Lafiya lau fa. Ya su Mamanku?”
“Lafiya wai a gaishe ku.”
“Ina amsawa sosai. Ina ta tunanin ganin ku ai shiru, na ce hala ko kawar taku ce tai muku wani abu.”
Saleemah ta yi karfin halin murmushi. “A’a Momy. Muna ta shirin fara jarabawa ne so ba zama sosai. A makaranta muke wuni karatu sai yamma muke dawowa gida.”
“Allah sarki! To Allah ya bada nasara ya sa a samu sakamako mai kyau. Ita dai waccan an bar ta a baya.” Ta furta hade da share guntuwar kwallar da ta fito mata.
“Abin da ma ya kawo mu ke nan Mommy, mu ji ko ba za ta iya zana jarabawar ba tun wuri a sanar da Level Coordinator dinmu, sai a san yanda za a yi ko deferring semester (jingine semester) din ne sai ta yi.”
Mommy ta gyada kai tana kallon Haneefa da ta yi maganar. “Ina fa Mahboobah za ta iya zana wata jarabawa a yanzu Haneefa? Ku shiga dakinta dai ku gan ta. Ni ba ni ma da tabbacin Mahboobah na da cikakken hankali fa. Kamar kwakwalwarta ta tabu.”
Cike da mamaki Haneefa da Saleemah suka zaro ido. “Tabuwa dai Mommy?”
“Toh, tabuwa mana Saleemah. Ko magana fa ba ta yi. Ba ta gyaran jikinta. Ba ta fitowa cikin mutane. Ba ta cin abinci sai kayan marmari. Sai haukar kuka da dariya. Ko dazu na leka dakinta har na gama tsayuwata na fito ba ta san da wanzuwata ba a dakin, idonta na kan waya tana kallon hoton Ishraq tana hawaye tana dariya. Toh ina hankali yake a nan?”
“Innalillahi! Ashe abun har ya kai haka Mommy. Ya salaam!”
Da kuka su duka biyun suka doshi dakinta. Sun same ta bacci ya dauke ta a kasan carpet din. Ga wayarta a gefe guda, gashi duk ya rufe mata fuska, hawaye ya bushe a saman fuskarta. Duk ma ba wannan ne ya fi rikita su ba, ramar da ta yi ce babban abun ji. Rama ta jiki da ta fuska, kamar ba ita ba.
STORY CONTINUES BELOW

Saleemah ta kalli Haneefa, Haneefa ta kalle ta, suka sakar ma junansu kuka mai karfi, kukan tausayin halin da kawarsu, ‘yar uwarsu kuma aminiyarsu take ciki.
Bubbuga ta Haneefa ta yi, caraf ta bude ido tana kallon su, yanayin kallon da take musu ma duk sai ya tsorata su, kamar wacce ta tashi daga cutar makanta. Kama ta suka yi suka tasar zaune, ta dukar da kanta kasa.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un! Mahboobah haka kika mayar da rayuwarki? Halin da kika jefa kanki ciki ke nan?” Saleemah ta fada cikin kuka sosai tana taba goshin Mahboobah.
Ba ta ce komai ba Mahboobah, ba ta kuma daga kanta ta kalli Saleemah ba. Sai dai jin karar kukansu ya saka ta fasa nata kukan ita ma, jikinta na karkarwa sosai, fatarta ta dauki zafi, idanuwanta sun kasa tsayar da zazzafan ruwan da yake bultsowa a tsakaninsu.
“Kukan me kike? Mahboobah da ke nake. Me ya sa kike kuka? Kuka ai ba naki ba ne. Bai cancanta ki yi ba. Ki bar mu mu yi, mu da kiri-kiri kike nuna rashin muhimmancinmu a rayuwarki. Kike nuna wani bare can ya fi mu amfani a duniyarki. Kike neman haukatar da kanki. Ki daina kuka kin ji? Namu ne wannan.”
Saleemah ta rike hannun Haneefa, “Ki bi komai a hankali kin ji Hanee? Kamar fa ba ta cikin hankalinta, zafin ran banza kike yi tun da ba ta san kina yi ba.”
“Ta sani sarai Saleemah. Ta san me nake cewa mana ki kalli fa yanda take kuka tana sissine kan rashin gaskiya.” Cikin kuka sosai Haneefa ke wannan maganar. Ta kara matsawa daf da Mahboobah, ta jawo ta a cikin jikinta, ta dora fuskarta a bisa kafadar Mahboobah, zukatansu jone da na juna, tana jin bugun zuciyar Mahboobah, “Boobah…dan Allah ki tausaya mana, ki tausaya wa kanki, ki tausaya wa larurarriyar zuciyarki. Ba don ni ba Boobah, ko don mahaifiyarki. Yanzu haka kuka take yi, tun da muka shigo gidan nan take zubar da hawaye, wanda na tabbata ba yanzu ta fara shi ba. Ashe duk soyayyar da kike fada mana kina wa Mommy ta karya ce? In har za ki fifita soyayyar wani a kan tata to tabbas da ma can ba soyayyar ba ce ba Mahboobah. Don Allah ki karyata mu, ki karyata abin da zuqatanmu suke mana hasashe.”
Wani kukan Mahboobah ta sake fashewa da shi bayan ta raba jikinsu, da sauri ta tashi daga kusa da su ta koma kan gado, ta dora fuskarta a saman filo, zafafan hawayenta na sauka bisa rigar filon. A take wasu abubuwa na daga cikin yarintarta suka fara dawo mata.
5th March, 2006
_Da gudu ta iso gaban wani mutum, ba wani mai shekaru masu yawa sosai ba, yaron da ya biyo bayanta yana ganin ta tsaya gaban mutumin shi ma ya ci burki yana haki._
_”To sarakan fada, me kuma ya faru?”_
_”Daddy, wannan yarinyar ka san halinta da tsokana, wai haka kawai ina tare da abokaina ta zo ta tsokane ni da wannan sunan wanda Inna ke ce mun, bayan kuma ta san ba na so. So take abokaina su ji su kama har su koma school suna ce mun haka ko Daddy.”_
_Ya mayar da kallon shi ga yarinyar, “Boobana wai haka?”_
_Shiru ta yi alamun rashin gaskiya._
_”Me ya sa kike son tsokana? Yanzu Fareedah kanwarki kina so idan ta tashi ita ma tana miki kalan abin da kike masa?”_
_Ta gyada kai yatsunta biyu a cikin bakinta._
_”Oya ba shi hakuri now!”_
STORY CONTINUES BELOW

_Ta yi rau-rau da idanuwa hade da juyawa ta kalle shi. “Ka yi hakuri Yah Aliyu.”_
_”Na yi.” Daga haka ya juya ya bar wurin yana dosar dakinshi._
_”Good girl. Allah ya miki albarka. Ki daina tsokana ko Mamana?”_
_”To Daddy.” Ta fada tana kallon Mamanta da take doso wurinsu._
_”Mommy Ina ta nemanki.” Ta fada hade da sauri ta shige jikinta._
_”Ina kan bene ina waya ne. Me za ki ba ni diyar albarka?” Mommy ta fada bayan ta kama yarinyar sun zauna kusa da Daddy._
_”Mommy wani labari ne zan ba ki. Dazu ina ta jin zafi a nan dina.” Ta saita hannu a kirjinta daidai inda zuciya take._
_”Subhanallahi! Kin buge ne?”_
_”Ban buge ba Mommy. Haka nan kawai yake ta min ciwo.”_
_Ganin Mommy kamar ta tashi hankalinta ya sa Daddy ya yi murmushi, “Ki fita zancen nan na Mamana. Sokanarta ce fa kawai. Yanzun nan ta gama tsokanan fada, ta je har dakin Aliyu ta jawo shi ya biyo ta da gudu.”_
_”Oh Mahboobah manyan gari. Kila duk a cikin ciwon nan din ne ko?” Ta fada tana dariya hade da nuna kirjin Mahboobah. Ita kam daga nan ta koma ta ci gaba da wasanta, sai dai lokaci zuwa lokaci tana dan dafe kirjinta, sai kuma a hankali ta koma daidai._
_Washe gari Mommy na mata shirin makaranta ta dafe kirjinta. “Mommy nan dina yana min ciwo, kuma a wurin numfashi babu dadi, daci gare shi.”_
_Dariya ce ta subuce wa Mommy, “Daci dai Booban Daddy? Ban taba jin numfashi ya yi daci ba.”_
_”To tsami Mommy.” Ta sake fadi tana kokarin d’aukar jakar makarantarta._
_”Hmm! Allah dai ya shirya min ke Boobah. Je ki ga ko Yah Aliyu ya gama shiryawa ki ce ya fito in kai ku, yau kun kusa makara.”_
_Da gudunta ta je dakinshi, a bakin kofa suka yi kicibus zai fito._
_”Da ma kai zan kira Yah Aliyu.”_
_Ya dafa kafadarta, “Ai na gama shiryawa ma. Mu je.”_
_Ta janye jikinta da sauri, “Toh Yah ai ban dauko launch box dina ba.”_
_Da gudu ta nufi kitchen ta dauko. Shi ma Aliyu ya dauko tashi sannan suka bi bayan Mommy bayan ta dauki Fareedah._
_Karfe takwas da minti goma ta sauke su makaranta, sai da ta ga shigarsu sannan ta tada motar ta tafi._
_Aliyu na dafe da ita sai da ya kai ta har gaban ajinsu, ya daga mata hannu hade da cewa “Ki yi karatu sosai Boobah. Ki daina tsokana, kin ga yara suna yawan complain da ke wai kina tsokanansu fada. Ki daina kin ji ko? Kina shiga kuma ki gaishe da Auntynku.”_
_”To Yah Aliyu Allah ba zan tsokani kowa ba.”_
_”Kin yi alkawari?”_
_”Ehh na yi.”_
_”Kawo hannu mu yi pinky promise. Idan kin tsokani wani me zan miki?”_
_”Ka…” ta yi shiru sanadiyyar tsirarta da gefen zuciyarta ya yi._
_”Lafiya? Me ya same ki?”_
_”Lafiya nake Yah Aliyu. Nan dina ne na ji allura a ciki. Kuma ta fita.” Ta saki murmushi. “Ka je class dinku Yaya. Sai anjima.” Ta daga mishi hannu sannan ta shige ajinsu._
***
Ta gyada kanta tana share ruwan hawayenta. Daga haka ne ciwonta ya fara ta’azzara. Daga haka ta fara tashi da ciwon da ita kanta ba ta san wane iri ba ne. Ciwon da iyayenta suka yi biris da shi, suka kasa fahimtar wani abu duk da yawan korafin da take musu na ciwon kirjinta.
Saleemah ta sake biyo ta a kan gadon. Ta rike mata hannuwa amma ta kwace hannunta da karfi tana guje ma haduwar idanuwansu.
“Shi ke nan Mahboobah, so kike mu fita daga rayuwarki? Well…za mu fita. Za mu bar gidanku, bari na har abada. Muna miki fatan alkhairi. Allah ya ba ki lafiya ya ganar da ke gaskiya.”
Daga haka Saleemah ta kama hannun Haneefa suka bar dakin. Sun samu Mommy zaune a falo, ganin yanayinsu kadai ya tabbatar mata da cewa zuwansu bai amfana komai ga Mahboobah komai ba.
“Mommy za mu tafi. In shaa Allahu gobe za mu samu level coordinator din, amma da Yah Aliyu ba ya komai da sai ya zo mu je tare, abun zai fi muhimmanci sosai.”
“Ehh ba matsala sai ya zo din mana. Bari zan ce ya kira wata daga cikinku, sai ku hadu ku je tare. Mun gode sosai, Allah Ya yi muku albarka ya saka muku da alkhairi kun ji.”
“Haba dai Mommy, godiya fa kike mana. An zama daya ai babu wannan a tsakaninmu. Fatanmu dai Allah ya ba ta lafiya ya yaye mata.”
“To ameen ya Allah. Ku gaida gida, Allah ya tsare.”
Da ameen suka fice, Mommy cike da kaunar ‘yanmatan biyu.
End of chapter
Assalamu alaikum my beautiful pipu. How have you been? Fine in shaa Allah😍toh ya labarin namu so far? Na san dai da dama sun kasa gane madosarshi😹😹😹sai dai hakan ba bakon abu ba ne ga ma’abota bibiyar labaraina, kome a hankali nake wayar da masu karatu in fitar musu kawuna daga duhu.
Kawai ku ci gaba da bibiyata, labarin zai kai ku inda ba ku yi zato bah.
I love y’ll
Princess Amrah
RAZ 2Flashback: 17th April, 2010
Ta rasa a yanayin da za ta misalta tsananin farin cikin da take cikinsa. Da a ce da hali da ta fitar da zuciyarta waje, na zagaye da ita su ga zahiri, su kara tabbatar da tsantsar dadin da take ji. A duk duniyarta, idan aka cire Mama, aka cire Abbah, to babu wanda take so sama da Yah Nuranta. Finally, yau ita ce aka yi baikonsu, ita da muradin zuciyarta. A cikin wannan halin ta jiyo kiran Mama, ta yi saurin share kwallar farin cikin da take yi, tana amsa kiran Mamanta.
“Ameerah, ke wato ko irin dan barin gidan nan ma da amare ke yi ranar baikonsu ke kin ki tafiya ko ina, kina nan sai ajje murmushin rashin kunya kike a saman fuskarki. Kai ni dai wannan yarinya ban san inda kika samo rashin kunya ba, ni dai da Abbanki ba haka muke ba, hasali ma ba mu san junanmu ba sai ranar da aka daura mana aure.”+
Baki Ameerah ta turo, “Toh amma kuma Hajiya Mama ai zamaninku daban namu daban. Ku lokacinku hadin aure ake, mu kuwa fa Mama ba hada mu aka yi ba, auren soyayya ne yana so na ina son…”
Da karfi Mama ta gwabe mata baki. “Ke Allah ya shirya mini yarinyar nan. Yanzu ba kya jin kunyata ki kalli tsakiyar idanuwana ki fada mun kuna son junanku? To ni ba da ni za a yi wannan fitsarar ba. Fito maza ki tafi gidan Saratu, wurin kawarki Hafsa. Na san ita ma Saratun tana hanya yanzu, su zo a raba biscuits din nan. Maza saka hijabi ki tafi yanzu. Kar ki dawo sai dare.”
Baki ta zumburo hade da saka hijabin tana dire-dire ta fice daga gidan.
A kan hanya ta ci karo da Saratu kawar Mamanta, ta gaishe ta, “Umma ai Hafsa na gida ko?”
Saratu ta amsa da “Eh tana gida, tuwo ma take mun. Maza ki je ku yi tare.”
Murmushi Ameerah tayi hade da takawa ta nufi hanyar gidan su Hafsa.
Ta same ta zaune kan tabarma tana gyaran alayyahu, ta zauna a kusa da ita. “Wash Allah!”
“Ya da wash Hajjaju se ka ce wacce ta wuni tana dambe?” Hafsa ta fada cikin murmushi.
“Ke wannan tafiya daga gidanmu zuwa gidanku ai abun a yi wash din ne. Na gaji.”
Hafsa ta gyada kai, “Duk fa na san takunki Amnoor, kar dai in ce ki taya ni aikin tuwo ne. Ko ba haka ba?”
Ameerah ta tintsire da dariya tana dafe ciki. “Ji wata banzar shaida Hafsa, wato in gaban wasu ne sai a ce ni kyuya gare ni ko?”
“Tambaya da amsa.”
“Zan miki Allah ya isa fa. Ke yarinya da ne kika san wannan, ni yanzu na tuba na bar halayen banza. Macen da za ta yi aure ina ita ina kyuya?”
Dariya sosai Hafsa ta yi, “Lallai fa, aure yakin yanmata. Ameerah yau ke ce da zancen kin shiryu? Ai ko kin shiryu dai na san ba za ki bar halin tsokana ba. Allah ma kadai ya sa adadin wadanda kika tsokana a yanzu tahowar ki kan hanya.”
“Ke wuyata da ke ba a abun arziki fa da ke. Daga farko kin kira ni da sunan da nake so kuma yanzu kin wani ce Ameerah. Miye wata Ameerah ga sunan kauna?”
Hafsa ta kai mata dukan wasa. “Allah ya shirye ki. Na ji an ce wai timetable din WAEC ta fito, da gaske ne?”
Ameerah ta zaro ido. “Ki ce dai abu ya gabato. Wohoho ni Ameerah na kusa zama mallakin Yah Nura. #AmNoor2010 ta kusa tabbata.”
STORY CONTINUES BELOW

“Wai ma 2010. Ke kin raina kanki fa. Kawai daga baiko sai aka ce miki aure tun yanzu?”
“Me kike nufi to? Wani baikon ma ai da wata biyu ko uku an daura aure.”
Hafsa ta kara tullewa da dariya. “Ba dai a garin nan ba kuwa, yan birni su suke wannan. Malama ki cire tunanin aure a ranki, ki ajje hankalinki ki yi karatun exams, ita ce gaba yanzu.”
Ameerah ta yi gatsine. “Ke in banda abunki har kin manta wace ce Ameerah? Lallai ma! Wato kin manta ni ba na karatun exams sai sadda za a shige ta nake dan duddubawa sama-sama.”
“Ya za a yi kuwa na manta. Kawai dai gani na yi wannan ta sha bamban, gwara ki yi karatun sosai.”
“Ke ban iya ba. Ni ban ma san yanda ake zama ai ta faman karatun jarabawa ba. Ni dai abin da na sani kawai sadda malami yake note ina rike abubuwa sosai. Ga exams sai idan kuna karatu daidai za a shiga in ara in duba.” Ta tuntsire da dariya.
“Na fi kowa sanin wannan. Toh Allah dai ya bada sa’a da rabo mai amfani.” Hafsa ta fada tana mikewa da kwandon alayyahu.
“Ameen dai. Allah kuma ya gwada mun aurena da Yah Nurana.”
“Ameerah!”
Ta dago kanta, “Yes, ko da magana ne?”
“Ahh wace ni na ce wani abu.”
Sai daidai maghrib Saratu ta dawo. Ta samu sun gama tuwo da miya suna haramar yin alwallah.
“Sannunku da aiki. Ameerah Mamanki ta ce maza in tura ki gida yanzu, dan ta san halinki kika hadu da Hafsa sai hali.”
“Oh ni Ameerah amaryar…” ta yi saurin dafe bakinta.
“Amaryar wa? Rasa kunya kajin birni.” Saratu ta fada tana kama habarta cikin mamaki.
“Amaryar Kakana fa nake nufi Umma.”
“Oh ni Saratu! Wai ka haifi da ya nemi yi maka wayo. Allah ya shirya mana ke Ameerah. Yarinya sai shegen iya-yi da kilbibi.”
Ameerah ta jawo hijabinta, “Toh Umma zan iya tsayawa in yi sallah ko kuwa dai ta ce lallai lallai in tafi gida ana tsaka da sallah a masallatai?”
Ummah Saratu ta gyada kanta, “Wa zai hana ki sallah Ameerah. Ai dole ma ki bari mangariba ta gota.”
“Toh ai ji na yi an ce a kora ni shi ya sa na tambaya. Allah ja da ran Ummah Saratu, gyatumar Ummaru da Hansatu.”
“Ke wace ce Hansatun?” Hafsa ta daure fuska ta tambaye ta.
“Yo oho, wadda ta tsargu.”
“Ai kuwa ba zan taka miki ba in za ki tafi. ‘Yar rainin hankali kawai.”
Ameerah ta kabbara sallah ba ta ko tsaya ba ta amsa ba.
Saratu me za ta yi ba dariya ba. A tarihin rayuwarta ba ta taba ganin yarinya irin Ameerah ba. Ga shi ba ta san wani abu ba wai fushi. Tana da dadin zama ga wasa da dariya. An ce wai haka Kakanta na wurin uba yake, baki daya halayenshi ne ta gado.
STORY CONTINUES BELOW

Bayan maghrib ta gota tai ma Ummah Saratu sallamah, Hafsa ko kallon ta ba ta yi ba, hakan ya sa ta koma kusa da ita tana dariya. “Wallahi in ba ki taka mun ba sai na yi wata uku ban kara zuwa gidan nan ba. Ko aiko ni Mama ta yi wurin Ummah Saratu sai in turo yaro a kofar gida. Ahaf! Ni za a gwada ma fushi.” Ta fashe da dariya. Ba shiri ita ma Hafsa ta fasa dariyar, “Allah ya shiryi dan iskan yaro.”
“Ameen dai.” Ameerah ta fada. “Sai ki tashi ki raka n ai tunda kin huce.”
“Ya na iya. Dole.” Ta mike suka fita.
Ba su wani yi nisa ba sosai a hanya suka yi kicibus da Nurah, Ameerah ta kalle shi da murmushi a saman fuskarta. “Yah Nura ango.” Ta rufe gefen idanuwanta.
“Oh innalillahi! Ke Ameerah yau ni na shiga ukuna ni Hafsa. Ji wata kunyar karya don Allah. Yarinya tun dazu kike uban tsageranci amma shi ne za ki wani kama rufe idanuwa.”
Dukan wasa Ameerah ta kai mata. “Ke dai wallahi ba ki da kirki Hafsa sam ba a sirri da ke.”
“Sirrin me kuwa za a yi da ni. Kai yau ina ganin abu.”
Da dariya Nurah ya ce “Ameerah da Hafsa kawayen juna, ko ma dai aminnan juna zan ce. In kuna drama dole mutum ya yi dariya.”
Hafsa ta murmusa, “Uhm ni dai Yah Nurah bari in koma gida to tun da de ta samu abokin tafiya.”
“Ahh kar ki mana haka Gimbiya Hafsa. Wai da sai mu tafi muna tattauna yanda hidimar biki za ta kasance.”
Baki Hafsa ta rike cikin mamaki ta ce “Kai wadannan mutane lamarinku sai ku. Wai yanzu daga baiko sai zancen hidimar biki? Hala dai tun da wuri aka ce za a yi?”
Nurah ya murmusa, “To ai da wuri wuri akan daki karfe. Ko ya kika ce Amnoor?”
Ameerah ta daga kai, “Ai Yah Nurah abin da nake so ta gane din ke nan, ta tsaya sai wani gani take da sauran lokaci.”
“Kanku dai ake ji. Ni na tafi gida sai da safenku.”
“Toh na gode dai ba dan halinki ba. Gobe ki biyo mun mu je mu fitar da timetable din nan.”
“Okay ba case.”
A hanya ma hirar yanda aurensu zai kasance kawai suke yi, suna yi Ameerah na taba barkwanci har suka isa kofar gida, ya kalle ta da murmushi a saman fuskarshi, “To Madam ni zan wuce, da ma duk yau ban gan ki ba ne ya sa na bi sawunki an ce min gidan su Hafsa kika je.”
“Ai ban so zuwa ba fa Hajjaju Mama ce ta ce sai na je wai saboda mutane.”
“To ai tana da gaskiya. Ba dadi bakin mutane. Yanzu ba wuya ki ga ana yamadidi da ke a gari wai ba ki da kunya, har sai a kara gishiri da maggi a kan zancen ma ki ji an ce ke da kanki kika tarbi masu kawo alewar baikonki.”
Ta kama dariya. “Lallai fa, yanda na san halin mutanen Hunkuyi, gulma da sa ido duk aikinsu ne. Amma fa idan na tsinci wannan zancen na yawo kuma na gano masu yawata shi ka san Yah Nurah zan iya samun mutum har gida in amayar da ta cikina.”
“Na san za ki iya kam. To amma ai matsalar gano mai yayatawar ne wahala. Mutum guda kawai zai kirkira sai mutum sama da hamsin sun daga zancen. Ke dai maganin kar a yi kar a fara. Gwara da Mama ta kore ki.”
“Uhm haka ne. To Yah Nurah ka je kawai ka ci tuwo. Na san ka yanzu cikinka yana nan yana kiran ciroma. Ba ka wasa da cikinka.”
“To meh ya fi raina yammatan Yah Nurah? Ai ki kara dagewa da girki yarinya, ni kam kowa ya san a nan na fi kwari.”
Ta tabe baki, “Kar ka wani damu ai yanzu na dage sosai. Amarya ai dole ta zage ko?”
“Haka ne. Bari in tafi to. Ki gaishe da Mama. Sai da safe.”
Bai tafi ba sai da ya ga ta shiga cikin gida sannan ya kama hanyar gidansu cike da kaunar Ameerah.
Tana shiga ta samu Abbanta zaune kan tabarma yana shan fura. Ta gaishe shi sannan ta zauna a gefenshi.
“Sannu Abba. Fura ake sha?”
Ya yi murmushi. “A’a miyar kuka nake sha.”
Ta tintsire da dariya. “Abba ke nan. Abbana ba dai bakar magana ba.”
“Ameerana ke nan. Ameerana ba dai tambayar rainin hankali ba.”
Mama da ke nan ta fashe da dariya. “Wannan drama taku akwai kayan dariya a cikinta.”
“Ai wannan takadarar yarinyar sai ana bin ta da yanda take so. Ki ga fa tana kallon abin da nake sha amma wai tambayata take.”
“Wayyo Allah Abbana to ai na fi son qarin bayani ne daga bakinka. Kuma ai Hausawa sun ce in ka ga kare na sinsina takalmi…”
“So yake ba.” Mama ta qarisa mata.
Sallama yaro ya yi ya gaishe da su, “wai wasu mutune suna sallama da Baban Ameerah.”
Abba ya ce “Ka ce wai yana zuwa.” Sannan ya dubi Mama. “Ko waye yake nema na da daren nan? Da mamaki fa.”
“To ai sai ka hanzarta zuwa ka duba ko waye, bari in rufe maka furarka kafin wannan kurar ta shanye ta.”
Murmushi Abba ya yi, “A’a ba ta ta sha, dan na tabbata duk yau ba abun kirki ta ci ba. Ameerah ba ta damu da cin abinci ba. Dauki ki sha kin ji autar Abbanta.” Da murnarta kuwa ta dauka ta fara sha.
Kusan minti ashirin Abbah ya dauka kafin ya shigo gidan, yanayin yanda jikinshi yake a sukuku kadai ya isa ya tabbatar ma duk wanda zai gan shi cewa ba lafiya ba. Ya zame ya zauna a bisa tabarmar hade da dage goshinshi.
Cikin kidima da tashin hankali Mama ke tambayarshi abin da ya faru.
“Magabatan Nurah ne suka zo, wai sun janye neman auren Ameerah…”
Tun bai kai aya ba Ameerah ta tofar da furar cikin bakinta wadda ta ji ta zame mata tamkar wani magani mai tsananin daci.
“Mene? Sun janye? To me ya sa? Me ya faru? Wani abu aka yi ne?” Duka a jere Mama ta sako mishi wannan tambayoyin.
End of chapter
Hello cupcakes. Duk ya kuke ya iyali?😍ya kwana biyu? Fatan na same ku lafiya. So ya labarin namu so far? Abu dai yana ta tafiya sai dai a hagunce😹kar ku damu soon zai koma a damance in shaa Allah🥰🙌🏻fatana koyaushe ina cracking brain din readers dina. Ba na son labarin da kai tsaye readers za suna hasko miye a gaba. Sannu sannu zanna haska muku kome da izinin Allah
Thank you all for supporting me. Keep voting, keep commenting and keep sharing. I do love you❤️😻
Princess Amrah
RAZ 2Story continued…(Ci gaban labari)
“Hello…please ina magana da Bilkeesu ne?”
“Yes, Bilkeesu my name (Sunana Bilkeesu) Waye kai?”
“Well…sunana Ahmad Deedah Muhammad.”
“Ok. Daga ina?”
Khalid ya yi gyaran murya. “Babana shi ne tsohon ministern tsaron kasar nan, Dr Muhammad Y Arkillah.”
“Ohh Okay Okay. Sannu Ahmad ya kake? Ya gida? How is your family (ya ‘yan gidanku)?”
Murmushin gefen baki ya yi Khalid, yana dad’a al’ajabin ‘yan matan yanzu.
“Alhamdulillah. Da ma dai an ba ni numberki ne, fatan zan samu shiga.”
“Ehh za ka samu sosai ma Ahmad. Sunana Bilkeesu Imran.”
“To ba tare da bata lokaci ba ni dai gaskiya son ki nake yi. Fatan zan samu karbuwa.”
“Me zai hana? Ai ka ma samu.”
“Haha ikon Allah! Tun ba ki gan ni ba ko a hoto? Wani hanzari ba gudu ba. Na ji labarin wani likita da kike so sosai, sunanshi Ishraq. Ban sani ba ko gaskiya ne ko karya ne?”
Bilkeesu ta yi sauri ta ce “Lahhh! Ka ga mutane da mugun abu da bakin sharri. Ni karya ake mun. Hasali ma ban taba jin mai irin wannan sunan ba. Share da zancen su yan karya ne.”
Khalid ya yi nurmushi. “Anya kuwa, na ji an ce fa dan uwanku ne ma. Wai shi kike son aure.”
Cikin kame-kame ta ce “Wai uhmm…uhm na tuno wai Doctor Ishraq ashe kake nufi. Haba ni me zan ci da wannan gunkin da ko dariya ba ya yi? Shi dai ne ya mutu a kaina kullum sai ya kira ni wai shi a dole sona yake. Daddyna ma kanshi baya son na so Ishraq saboda sam bai da girmama na gaba da shi. Yanzu hakan nan muna cikin waya da kai sai da ya kira ni.”
Cikin mamaki da zare ido Khalid ya ce “To fa! Yanzu yana miki irin wannan damuwar ne kuma har kika manta da sunanshi da farko kika ce ba ki san shi ba?”
Ta rasa abun cewa a nan, ta yi shiru tana muzurai.
“Anyway, zan bincike shi in ji in da gaske yake, saboda ni ba na soyayya a inda aka riga ni. In ya shaida mun da gaske aurenki yake son yi zan hakura in bar mishi ke.”
Da sauri ta ce “Uhm ka ga Ahmad, kar ka biye wannan ka ji. Na tabbata ko dan ya yi mun bakin ciki zai ce sona yake da gaske. Ka share shi kawai ka zo gidanmu mu yi magana.”
Gyada kai kawai Khalid Zannah ya yi hade da kashe wayar. Yana kallo tana ta kiran shi, a karshe ma ya yi blocking dinta. Ta wannan bangaren kam ya samu abin da yake so. Ya yi nasara!
Ya latsa kiran Ishraq, bugu biyu ya dauka. “Ya ake ciki? Ni dai kam na gama aikina.”
“Ni ma na gama Khalid. Ko kadan yarinyar nan ba ta da tarbiyya. Abu mafi muni da na tabbatar a kanta ‘yar maye ce. An ce wai duk gang dinsu na makaranta haka suke. Wani lokacin ma a wannan halin take komawa gida, idan abun ya tsananta ma kai ta gidan ake.”
“Subhanallahi! Ka ji kuma wani abun. A ina ka jiyo wannan?” Cike da mamaki Khalid ya yi mishi wannan tambayar.
“A wurin class rep dinsu na fara ji, shi ya kai ni har wurin level coordinator dinsu ya gwada min result dinta na last semester, har yana cewa yarinya mai kokari amma ta kashe kwalwarta. A karshe na samu mai gadin gidansu shi ya kara tabbatar mun da wani lokacin ma shi yake kama ta ya shigar gida. Ka ga kuwa ai babu sharri a wannan zancen.”
STORY CONTINUES BELOW

Ajiyar zuciya Khalid ya sauke, “Ya Salaam! Allah Ya shirya mana zuria. Ni ma din na kira ta…” ya ba shi labarin duk yanda suka yi da ita.
Bayyanannen tsaki Ishraq ya yi, “Ni wallahi kaina ya daure Khalid. Na ma rasa abin da zan yi. Gani nake komai yana juye mun, yana birkita tunanina.”
Cikin kwantar da hankali Khalid ya ce “Ka kwantar da hankalinka. In shaa Allahu komai zai zo da sauki. Kai dai kawai ka ci gaba da addua, kana rokon Allah mafita. Sannu a hankali za a samu mafita mai kyau.”
“Haka ne Khalid, in shaa Allahu. Yanzu dai a jingine batun Bilkeesu, wannan ta fi karfina.”
Khalid ya yi murmushi. “Dole kam. Me ake ci da makaryaciya yar maye? Kodayake, mashayi har abin da ya fi karya ma yi zai yi.”
“Wannan gaskiya ne. To yanzu what next (Menene a gaba)?”
“That’s what I don’t know Ishraq (Abin da ban sani ba kenan ni ma Ishraq), Wallahi kaina ya kulle, na ma rasa abin da zan ce. Amma ka san mene, zan zo gidanku anjima idan kana gida. Mu je wurin Mami, kawai ka ce ka mika mata wuka da nama, ta zaba maka matar aure da kanta, ka san ba za ta maka zaben tumun dare ba.”
Da sauri Ishraq ya ce “Wannan ba mafita ba ce Khalid. Na tabbata idan muka ce mata haka ga Bilkeesu za ta koma. Ko ba kai tunanin hakan ba kai?”
Khalid ya jinjina kai. “Kuma fa haka ne. Tabbas cewa za ta yi toh ka je ka nemi Bilkeesu, abin da ake ma gudun. Amma kuma idan ta ce haka ba sai mu fada mata binciken da muka yi a kanta ba? In ya so sai ta nema maka wata ko ma a ina ne?”
“Khalid wannan ba mafita ka kawo ba, sam hankalina bai kwanta da ita ba. Ka dai zo gidan, kodayake ma dai bari zan zo idan na tashi daga aiki, daga nan in duba Junior. Don Allah ka mana nazarin mafita kafin in zo.”
“Zan gitto ta Office din naku ma zuwa an jima. Daga nan sai mu yo gida ka duba shi.”
“To Allah Ya zama gatanmu.”
Daga haka suka yi sallama, kowa na tunanin mafita.
*
Ta zauna ta zabga tagumi, ba ta san sadda ruwan hawaye ya fara wanke mata kumatu ba. Jikewar da ta ji fuskarta ta yi ne ya sanya ta amfani da yatsarta biyu ta share hawayen.
“Adda Hanee har yanzu kina nan zaman tunani? Wallahi ki dai duba shawarata, ita ce kadai mafita a gani na. Allah zai iya duba zuciyar baiwar Allah Addah Boobah, ki ga hakan ya zama alkhairi.”
Haneefa ta dan yi Jim, kafin ta ce, “Rukayya ina gudun wulakanci, kin san ni, kin san ba na tolerating nonsense. Ba kya gudun abun da zai iya zuwa ya dawo? Ba ma wannan ba. Idan abun ya tabbata rayuwar Mahboobah ta shiga kunci fa daga baya? Komai na duniya yana da kyau ana yi ana hangen future. Gaba ta fi baya yawa Rukayya.”
Rukayya ta matso kusa da Yayarta Haneefa. “Amma Addah, ba na tunanin Adda Boobah za ta kasa jure wulakancin Ishraq. Tun da har ta shiga matsanancin hali a kanshi, ke nan za ta iya jure komai zai faru a gaba. Na tabbata abun ba zai zama na har abada ba. Dukkan tsanani yana tare da sauki. Amma ya kika ce?”
Haneefa ta sauke ajiyar zuciya, “Bari in kira Saleemah inji, idan ta goyi bayan shawararki sai a yi hakan.”
“Ba na jin Addah Saleema za ta ki goyon bayan wannan shawarar, da ma dai ke ce mai wahalar shaanin a duk cikin ku uku, kin fi su tsauri da zafin rai.”
STORY CONTINUES BELOW

Tana fadan haka ta ruga da gudu tana dariya.
“Ja’ira da ki tsaya mana. Yar rainin hankali.”
Daga haka ta latsa kiran Saleemah. Bayan sun gaisa ta shaida mata kaf shawarar da kanwarta Rukayya ta bayar. Sannan a karshe ta ce “To ni dai ina tsoro Saleemah. Kar a samu yanda ake so a yanzu, gaba kuma komai ya cabe a gwammaci gwara na farkon.”
“In shaa Allahu ma ba za a yi haka ba Hanee. Shawarar Ruky abun a duba ce. Bari in shirya in zo gidanku yanzu mu karisa tattauna yanda za a yi, in ya so daga nan sai mu wuce kawai.”
“Kamar kin san sai da Rukayya ta nunar wai kin fi ni saukin hali. Banzaye ku duka.”
“Huh! Su Haneefa manyan kasa, Yaya ga Ruky kanwar Aunty Ummi. Diyar Abba da Umma amaryar…”
“Amaryar uban wa?”
“Ahh ni dai ba ki ji ba a bakina.”
Ta kashe wayar tana dariya.
Few hours later (Bayan wasu Awanni)
Da tambaya suka gano Office dinshi. Sun samu Kamal masinja a bakin Office din zaune, suka gaishe shi cikin girmamawa. Haneefa ta ce “Don Allah ko Doctor Ishraq na ciki?”
Kamal ya kalle su ya kalli Yesmeen diyar Aunty Ummi da ke goye bayan Saleema. “Ehh yana ciki. Amma yana da bako. Ku yi hakuri lokacin duba marassa lafiya bai yi ba tukunna sai nan da awa biyu.”
Haneefa ta hadiyi yawu, “Da dai ka taimaka ka tambayo mun shi, muna da tsananin bukatar son ganin shi.”
“To zan iya taimakonku, amma idan ya tambaye ku waye ya ba ku izinin shiga ku ce ba ku tarar da kowa ba shigowa kuka yi kawai. Bari in yi saurin tafiya bandaki. Allah ya sa a dace.”
“Mun gode kwarai Mallam. Thank you so much.”
“Babu komai.” Ya bar wurin su kuma suka shiga ciki.
Ishraq ya dube su ya ce,
“Lafiya dai ko? Lokacin duba patients bai yi ba ai. Ku koma wurin kujerun can ku dan jira.”
“Uhm…da ma dai ba abin da yake tafe da mu ba ke nan.” Saleemah ta fada cikin in ina. Khaleed Zannah da ke zaune a ranshi ya ce ya san cikin masu kawo kansu ne ga Ishraq, musamman yanda ya ga Saleemah na yan kame-kame. Kodayake dai ga yarinya goye a bayanta ta yiwu gudar take tayawa. Ya ma kanshi murmushi.
“Don Allah ko za ka iya ba ni damar yin magana? And please, kar ka datse ni har sai na kai karshe. Alkhairi ne tafe da mu da kuma neman taimako, ko in ce ceton rai.”
Cike da mamaki Ishraq ke kallon su, ya gagara furta komai sai daga ma Haneefa kai da ya yi.
“Na san kai likita ne, kuma bayan kammala karatunka kafin ka fara aiki sai da aka yi muku induction kuka yi rantsuwa cewa za ku kare hakkin al’ummah, za ku ceci rayuka iya gwargwadon karfinku.” Ta sauke ajiyar zuciya idanuwanta na yawo a saman fuskarshi. “Sai dai Doctor Ishraq, alkawarin da ka daukar ma gwamnati yana neman tashi a iska. Kana neman salwantar da rai da karan- kanka.”
Cikin mamaki ya bude idanuwanshi, “Ni kuma?”
“Kai fa, Doctor Ishraq. You left her depressed. Ta ki kowa ta ki komai. Abinci ya gagare ta. Soyayyarka ta yi fatali da duk wata nutsuwa da walwalarta. Ta zama tamkar giri-giri, ko in ce mahaukaciyar da ta yi shekaru a halin hauka. Iyaye da yan uwanta sun guje ta saboda halin da suke ganin ganganci ne ya sanya ta fadawa a cikinsa. “
Ta mike tsaye hade da dawowa gaban teburinsa. “Shekararta goma sha takwas da haihuwa, sha biyar daga cikin sha takwas din can a halin ciwon zuciya ta yi su. Kwanakin baya aka samu aka yi mata dashen zuciya, bayan da aka cire tsammani daga ci gaba da rayuwarta baki daya. Tun bayan dashen sabuwar zuciyar da aka mata ne ta tsinci kanta tsamo-tsamo a cikin soyayyarka. Mu biyun nan mu ne manyan aminnanta, kawayenta na rai da rai tun yarinta har wannan lokacin da muke tsaye a gabanka. Mun fi kowa sanin wace ce Mahboobah. Mun fi kowa sanin kyawawan halayenta. A baya Mahboobah na sahun yammata masu matukar class da kame girmansu. Namiji zai ce yana son Boobah amma ba ta da lokacin tsayawa ta saurare shi balle har ta amsa soyayyarshi, karatunta kawai ta saka a gaba. Mun yi matukar mamaki a lokacin da muka ji halin da soyayyarka ta jefa ta.”
Ta koma ta zauna a mazauninta. “Ka taimaki Mahboobah in dai hakan ba zai zama matsala ba. Ka ceci rayuwar Boobah in dai za ka iya, kana da halin taimakon.”
Daga haka ta fice daga Office din, Saleemah ta bi bayanta.
Tun da suka fita idonshi ya bi bayan inuwarsu. Kalamansu yake ta tariyowa, yana son gasgata su, sai dai kuma wani sashen na zuciyarshi karyata su yake yi. Bai ga ta yanda soyayya za ta jefa wata halitta a wannan halin ba. Sai dai mafi rinjaye na zuciyarshi ya fara yarda, saboda tuno Ameerah Muhammad da ya yi. Shi da ya yi mata kallo daya amma ta bar shi da dafin son da ya gagara samun maganinshi har a wannan lokacin.
Ya kalli Khaleed Zannah, Khaleed ya sakar mishi murmushi hade da daga mishi kai.
End of chapter2
Oh Okay Okay. How are you and every every? Fatan na same ku lafiya. It’s Princess Amrah with chapter 10 of BKF. Suprise?
Tsakaninku da Allah how’s this novel?😫Issit nice or boring? Feel free and tell me what’s in your mind?
Thank you all da karatu.
Princess Amrah
RAZ 2Wishing myself a joyous birthday full of God’s amazing blessings. My being alive and healthy today is as a result of none other than the almighty God. I’ll forever be grateful to you, God. Happy birthday to myself.😻🥳🥳
Flashback…18th April, 2010 (Komawa Baya)
Da kuka ta farka, ta sa hannunta tana sharar ruwan hawayen da ya gama wanke mata fuska, tana cicije labbanta, da kyar ta samu ta bultso magana daga tsakanin labbanta,
“Mama…Mama don Allah ki fada mun mafarki ne nake yi. Ki fada mun ba gaskiya ba ne ba.”
Mama ta taso ta iso bakin gadon da Ameerah take kwance. Ta dafa ta cike da soyayyar uwa da diya. “Ba mafarki kike ba Ameerah, dukkan abin da kika san ya faru to da gaske ya faru din. Sai dai ina so ki kwantar da hankalinki. Ki kokarta yaki da zuciyarki ta hanyar fatali da soyayyar Nurah, duk da na san ba abu ne mai sauki ba. Ki daure Ameerata.”
“Ta yaya Mama? Ta ina zan fara zare soyayyar da jini da
zuciyata suka saba da ita? Ta yaya zan iya fatali da Yah Nurah bayan tarin shakuwar da zukatanmu suka yi? Wayyo Allahna, Mama ya zan yi?”
Kuka take sosai kamar ranta zai fita, tana wata irin shessheka mai ban tausayi. Mama ma sai ta ji hawaye na fito mata. Tun da ta haifi Ameerah idan aka cire kukan yarinta to ba ta taba ganin ta a irin wannan halin ba. Ba ta taba jin muryarta na irin wannan kukan ba. Yarinya ce mai kokarin boye damuwarta, mai kokarin danne kunci da bacin ranta. Duk yanda aka mata abu don ta hasala, ko alama ba za ta nunar ba. Za ta bi mutum da murmushi, a karshe har da barkwanci. Ta taba rasa Yayanta, ya rasu, amma ko a lokacin ba ta yi kuka irin wannan ba. Ta yi kuka sai dai iya ruwan hawaye ne, ita ta koma rarrasar Mama a wancan lokacin.+
“Ameerah kina
raunata mini zuciya da wannan kukan naki mai cike da zallar ban tausayi. Kina kashe mini dan sauran kwarin guiwar da nake ganin ina da shi zan iya rarrasarki in kwantar miki da hankali. Na sani da ciwo. Da ciwo sosai Ameerah. Dole za ki yi kuka, ko don shakuwar da take tsakaninki da Nurah, tun kafin soyayya, tun a iya Malamin islamiyya da dalibarsa kawai. Amma duk da haka ba zan fasa ba ki hakuri ba. Ba zan fasa rokonki ki yi shiru ba, kar ki jawo ma kanki wani ciwon kina zaman zamanki.”
Kokarin tashi zaune ta yi amma ta kasa. Mama ta kama ta ta tasar zaune, ta jingina da gadon asibitin da ya tsufa yake wata irin kara kamar zai karye.
“Ga fura nan Abbanki ya siyo miki kina bacci. Ya ce ki daure ki sha sai ki sha magunguna ga su nan tun dazu ya siyo da aka rubuta.”
“Na koshi Mama…”
“Wane irin kin koshi kuma? Kwananki daya da rabin wuni a haka, ba ki ci komai ba. Na tabbata dole kina jin yunwa, dole. Daurewa za ki yi ki cuccusa ta haka nan ko ba dadi, don dai ki samu ki sha magani.”
Ta gyada kanta wani hawaye na sake fitowa. “Mama Yah Nurah ya san ba ni da lafiya? Ya zo duba ni?”
Mama ta sauke ajiyar zuciya bayan ta share guntuwar kwallarta. “Ba na tunanin ya sani Ameerah. Kuma ma ko ya sani din ba lallai ba ne ya zo.”
“Me ya sa?” Ta tambayi Mama cikin kuka.
Mama ta dan yi jim, kafin ta ce “Saboda an masa iyaka da ke. Iyayenshi sun zaba mishi wata a birni.”
STORY CONTINUES BELOW

Ameerah ta runtse idanuwanta da karfi sauran kwalla suka gama fitowa. “Mama me ya sa iyayen Yah Nurah za su mana haka? Me ya sa tun farko ba su nuna ba su son aurenmu ba sai bayan an mana baiko, a ranar za su zo da wani batu?”
“Sun ce wai da ma can ba da yawun mahaifinsa ba, tun farko ya ce ba ya so Mamanshi ce ke so. To ba ya nan ya je birni, sai jiya da yamma ya iso. Yana zuwa ya ji labarin kaninshi da yan uwanshi sun zo nema wa Nurah aurenki, shi ne ya tada fitina fa ya ce bai yarda ba. A yanda kanin nashi ma yake fada wa Abbanki wai har neman goranta musu ya yi ai danshi ne ba dansu ba. Ba su da yanda za su yi don dole suka zo suka ce sun janye. Kuma suka ce sun yafe alewa da dabinon da suka kawo don da ma da kudinsu ne suka siya ba da kudinshi ba. Allah ya isa ma ya yi wa Nurah matukar bai rabu da ke ba. A yanda na tsinci zance dazu ina hanyar komawa gida, wai diyar Oganshi ke son Nurah, kin san a can Kaduna ya yi bautar kasarshi, to a gidan mutumin ya zauna. Tun daga nan ne yarinyar ke kaunarshi. Ameerah kin san lamarin yanzu, in dai ba ka da kudi to fa kai ba abun so ba ne.”
“Innalillahi wa inna ialihi raji’un! Mama me ya sa Baba zai mana haka? Me na yi mishi? Ina da wani hali na a qini ne?”
Mama ta gyada kai. “Ko alama. Ba wai dan kina tawa ba Ameerah, amma kina da halaye masu kyau da kowa zai so zama da ke. Kawai dai ina so ki sa a ranki da ma can ke ba matar Nurah ba ce. Sai mu yi addua Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi.”
Suna cikin haka suka ji sallamar Nurah. Cikin wuni guda duk ya bi ya rame, idanuwanshi sun zurma, ya fita a hayyacinsa. Ya durkusa ya gaishe da Mama, ya tambayi ya jikin Ameerah, sannan ya mika kallon shi gare ta. A maimakon ta zuba mishi nata idanuwan yanda ta saba, sai ya ga sabanin haka, ta yi saurin noke kanta, tana mai kauce wa haduwar idanuwansu.
“Ameerah ya karfin jiki?” Da kyar ya samu zakulo wannan maganar a kasan makoshinsa.
“Alhamdulillah!” Kawai ta furta har a lokacin ba ta hada ido da shi ba. Mama na ganin haka ta mike hade da tashi ta bar wurin.
Ya matso daf da ita, “Ameeraty…” yana son ci gaba da magana amma bakinshi ya kasa. Da kyar ya sake maimaita, “Ameerana ba za ki kula ni ba?”
Ta dago fuskarta ta kalle shi, abin da take ma gudun ya auku, hada ido da Nurah daidai yake da karin ruruwar wutar sonshi a kasan ruhinta.
“Ameerah kin ga yanda kaddara ke neman yi da mu ko?”
“Kaddara? Kaddara fa ka ce Yah Nura…hmmm! Ba haka ya kamata ka ce ba. Haka za ka ce kin ga yanda Abbanmu yake neman yi da mu ko? Babu ruwan kaddara, ba muhallin kaddara ba ne.” Ta yi shiru tana kokarin shanye kukanta. “Yah Nurah, kai ne mutum na farko wanda na so a duk duniyata. Kai ne mutum na karshe da nake jin ba zan taba son wani koma-bayanka ba. Na dauki dukkan soyayyata na mallaka maka. Na mika maka duk ragamar rayuwata. Na so ka, ko in ce ina son ka fiye da kima. Na zabure a soyayya ta silarka. Na zama wata mara kunya a idanuwan duniya duk don na tabbatar wa al’ummah da kai ne muradin zuciyata…”
Kara runtse idanuwanshi yake yi, yana jin yadda muryar da take amfani da ita ke ba shi wahala a kasan zuciyarshi. Tana daukar shi da komai da halittarshi ta nannade, tana kai su wata duniyar ta daban. Duniyar da kauna da soyayyarta ce kawai yake iya hangowa a ciki. Zuciyarshi yake ji tana harbawa, komai na cikinta kara budewa yake da soyayyarta. Tunanin yadda rayuwa za ta ci mishi gaba yake saboda wannan kaddarar da ta fada a tsakanin soyayyarsu. Yana son ta, sosai da sosai, irin son da bai san ya zai kamanta shi ba.
STORY CONTINUES BELOW

“Ameeraty…” ya fada cikin muryar kuka.
“Yah Nurah babu sauran wata alaka a tsakaninmu. Ba na so a sanadina wani abu ya faru tsakaninka da mahaifinka. Ka tafi kawai Yah Nurah.” Ta karisa maganar da fasa kuka sosai, tana jin yadda girman kaddararta ke dad’a hauhawa, damuwa ke mamaye dukkan halittarta.
Bai sake furta mata komai ba ya juya zai tafi, har ya kama hanya ta kira sunanshi.
“Yah Nurah!”
Kiran sunanshi da ta yi sai ya tuno mishi wani lokaci, sadda yake fita daga bakinta cike da shaukin soyayyarshi, akasin yanzu da ya fita cikin zallar tashin hankali da rashin nutsuwa. Ya hau tariyar wani dan lokaci da ya gabata…
_”Yah Nurah!” Ta fada tana murmushi._
_Ya juyo ya kalle ta, zuciyarshi cikin wani irin yanayi, mai wahalar fassarawa. Murmushi yake, yana jin komai na masa dadi. Murmushi yake, yana jin yadda kaunarta ke ci gaba da zagaya mishi ko’ina na cikin halittarshi, tana zarcewa zuciyarshi, tana kara samun wurin da ya tabbatar har gaban abada babu wadda za ta samu irinshi a ciki. Yana ji a ranshi ba zai taba gudun Ameerah ba. Ba zai taba nisantarta ba. Ba zai taba disappointing dinta ba, har abada da izinin wanda ya shimfida kaunarta a kasan ruhinshi._
*
“Yah Nurah.”
Ya yi saurin dawowa hayyacinshi, daga zurfin tunanin da ya lula. Ya waigo yana saita idanuwanshi a cikin nata.
“Yah Nurah kar ka manta da ni. Kar ka manta da innocent Ameerah da ta kaunaci rayuwarka fiye da kowa na duniyar nan. Ina son ka, kuma ba zan daina son ka ba har abada.” Ta duke tana kuka da iya karfinta.
“Zan iya jurar komai Ameerah, zan juri fushin Abbana a kaina, musamman da ba ni da hakki a kanshi. Amma ba zan juri ganin zubar hawayenki ba. Zuciyata na zafi sosai idan na ga ko digon hawayenki ya sauka a saman fuskarki. Wannan shi ne karon farko da na taba ganin ki a wannan halin, kuma ta sila ta Ameerah, ta silar soyayyata.” Kuka ya ci karfinshi, ya dafe karfen gadon da take kwance a kai.
“Da dai kun yi hakuri da yan koke-koken nan Nurah, ku rungumi kaddarar da mahaliccin soyayyarku ya jefo a saitin duniyarku. Ku sani da ma can Allah bai nufi kaddarar aure za ta gitta a tsakaninku bah. Sai duk mu taru mu yi fatan Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi.”
Da yana da yanda zai yi da ya ce wa Mama rashin auren Ameerah ba zai taba zama alkhairi a ruuwarshi ba. Da da hali da ya fada wa Mama Ameerah ita ce kyakkyawan future dinshi.
Ya so ya iya budar bakinshi ya mata sallamah. Ya so ya mata fatan alkhairi tare da fatan sassauci a kulluhin rayuwarsu. Sai dai ya kasa. Diga-digan kafarshi yake ji kamar za su dare, kamar za su farfashe saboda yanda yake tilasta taka su ba don suna so ba.
Da haka ya karisa ficewa daga dakin, bai ko sake waiwayowa ba. Kamar an ce ya fita ta sake rushewa da wani kukan. Mama ta yo kanta ta ma rasa ta inda za ta bullo ma lamarin. Duk wasu kalaman rarrashi da ta sani ta gama karar da su tun daga sadda Ameerah ta farfado.
Ta hau dan bubbuga bayanta a hankali tana share mata hawaye.
***
Kwanansu biyar a asibiti aka ba ta sallamah saboda ta ji sauki sosai. Sai dai rashin kuzari da ya zama bakon abu a gare ta. Tun asalinta ba ta san wani abu wai shi damuwa ba. Duk wanda ya san ta zai ba ta wannan shaidar. Cikin yan kwanakin nan biyar duk ta bi ta fige ta zube kamar ba ita ba. Surutu duk ya gama mamaye garin, wasu Yan gulmar har gida suke zuwa duba ta, zantuka kala kala na yawo kowa da abin da yake fadi.
Haka Nurah ma ya shiga tsananin tashin hankali. Abinci ya gagare shi ci. Ga fushi da mahaifinshi yake yi da shi na ba gaira ba dalili. Mamanshi ce take rararrasarshi, ita ma kuma Baban ya ce ta kyale shi tun da shi ba yaro ba ne, yana neman butulce wa zabinsa, ya ce ba zai auri Sameerah ba.
Rayuwa ta ma masoyan biyu kunci. Damuwa ta dabaibaye duniyarsu. Son zuciya da kwadayin abun duniya ya sa mahaifin Nurah ya farraka tsohuwar soyayyar da ta jima Nurah da Ameerah suna tanadi. Ya sa almakashi ya datse dadaddiyar alakar da take tsakaninsu.
Ganin halin da Ameerah take ciki, damuwa kullum kara rubanya take yi, ya sa Abbanta yanke shawarar ya tura ta Kaduna gidan Yayanshi, ta zauna da su Maryam watakila za ta rage wani radadi daga zuciyarta. Ya samu Mama da maganar, ta jinjina lamarin, ta ce “Wannan shawara ce mai kyau. Sai dai kuma matsalar ka ga sun kusa fara jarabawa. Bai kamata a datse ta ba ai.”
“Ba damuwa ba ne ba don wannan. In shaa Allahu zan kashe ko nawa ne a biya makarantar a nemi mai zana mata. Na san ana yin haka. Zai fiye mana sauki a kan mu zira ma Ameerah ido muna kallon ta a wannan halin. Rayuwata tana kuntata sosai da kuncin Ameerah.”
Mama ta sauke ajiyar zuciya. “To shi ke nan. Allah ya sa hakan ne mafi alkhairi.”
End of chapter
Okay here we are 😻fatan na same ku lafiya.
Allah sarki Ameerah😢kamar in taya ta kuka na ji wlh very heart touching 😫💔
Ameeraty from naughty to innocent. From funny to pity 😤
Allah ya raba mu da irin wannan kaddarar. Wannan shi ne kuskuren wasu iyayen, sai su hana ma yara freedom dinsu. Yes, iyaye suna da hakki a kan yaransu, amma kuma ya kamata iyaye su gane cewa yanzu ba da ba ne. Sosai aka samu sauyin dukkanin lamurra. Abin da yake jefa wasu yaran ga halaka fa ke nan. Toh idan ma an wa mace auren dole shi fa namiji? It’s very bad wallahi😢😣
Princess Amrah
RAZ 2Story continued…(Ci gaban labari).
Yunwa ta ji tana kwakwalarta, ba ta son komai, ta mike a saman tafin kafarta, sai dai rashin kuzari ya sa ta tafi luuuuuu! Kamar za ta kai kasa. Ta yi gaggawar dafe wardrobe, tana jin jiri na sake dibarta.
Kamar daga sama ta jiyo sautin wayarta, ta yi mamakin yanda aka yi ta mance ba ta mayar da ita a flight mode ba kaman yanda ta saba. Ta yi banza da wayar hade da ficewa ta nufi kitchen. Yankakkiyar kankana ta zuba a bowl, ta zuba condensed milk kamar yanda ta saba sannan ta dauko spoon and fork ta saka a ciki. Tana kokarin fita daga kitchen din Fareedah ta shigo. Ta mata kallon sama da kasa, tana neman wucewa Mahboobah ta jawo mata gefen riga. Duk yanda ta so ta yi magana bakinta ya gagara komai, sai ruwan hawaye da a dan lokaci kadan ya sauko ya wanke mata kumatu. Ganin Mahboobah ba ta da niyyar cewa komai ya sa Fareedah janye rigarta kawai ta shige don yin uzurin da ya kawo ta.
Cikin kuka da gudunta ta bar kitchen ta nufi dakinta. Ta duke a wurin tana kuka da iya karfinta. Jin wayarta ta yi ta sake kara, ta daga kanta ta duba, abun mamaki lambar wayar da tai ma hardar da har mutuwarta ba za ta taba wankuwa daga kwanyarta ba ta gani. Ta murje idanuwanta ta sake murjewa. Daidai suka ganan mata. Sai dai abin da ba ta gana tabbatarwa ba shi ne, shin mafarkin da ta saba yi ne yanzu ma take yi? Kafin ta gama dawowa daga duniyar tunanin da ta lula har ta tsinke. Ta sa hannunta ta dauko wayar, 2 missed calls ta gani duk da lambar. Ta gyada kanta tana tunanin ba gaskiya ba ne.+
Kankanar ta fara sha, ta yi nisa har ta kusa gamawa ta ji karar text message.
‘Ya jikin naki? Na ji labarin ba ki da lafiya. Akwai muhimmiyar maganar da nake so mu yi amma sai idan kin ba ni dama.
Ishraq Sulaiman.’
Gyada kanta take yi tana jin jerangwamar ruwa mai gumi na fitowa tsakanin idanuwanta. Sanyin AC ke akwai a dakin, amma gumi ne ke tsatsssfowa daga fatarta. Me take gani ne? Da gaske abin da idonta ke gane mata?
Ta dora hannunta a ka tana kokarin fasa kuka. Ta ina hakan za ta kasance? Ko dai wani ne ya karbi wayar Ishraq ya turo mata wannan sakon don ya faranta mata rai? Ko kuwa dai Ishraq kanshi ya fara tabuwa ne? Ba ta ga ranar da zai iya turo mata wannan sakon ba da kanshi. Hakan ya sa ta yi biris ba ta koma ta kai ba. Ta mayar da wayarta a flight mode kamar yanda ta saba.
*
“Ka gani ko Khaleed ? Ni fa abin da na tsana ke nan. Na ki jinin wulakanci. In ban da tsabar rainin hankali don ma ta samu an taimake ta shi ne za ta ki daga kira na?”
Khaleed ya yi murmushi. “Sai hakuri Ishraq. Ba komai ba ne ake saurin daukan zafi a kanshi. Duka ba sau daya ba ne ka kira ta? Sake kiran ta mu ji kila wani abu ne ya hana ta dauka.”
Ba don ya so ba ya sake latsa kiran ta. Ya samu lambarta ne a last text message din da ta yi mishi.
Shiru har a wannan lokacin ba ta dauka ba. Ya sake buga wani tsakin yana ajje wayar a kusa da shi.
“Ba ta fa da lafiya ka ji an ce Ishraq. Kai wallahi ban san irinka ba. In dai har ita ka yanke a matsayin wacce za ka aura fa dole ka jure ma wadansu abubuwan. Ka taushi zuciyarka.”
“Ta ina? Saboda an fada maka sonta nake? Ko kuwa zan iya son ta?”
Khaleed ya tabe baki. “Ban ce kana son ta ba. Ban kuma ce za ka so ta ba. Sai dai kuma za ka iya son ta din. Allah masani.
Ni dai ba wannan ba. Please Ishraq, ba don ni ba ka taimaka ka ajje mata sakon text message, na san za ta gani ko daga baya. Tana iya yiwuwa yanzu bacci take.”
STORY CONTINUES BELOW

“Gaskiya ba zan iya wannan aikin ba, hasali ma rubuta text message babban aiki na dauke shi. Rabon da in yi har na mance, ba kuma zan yi ma wata Mahboobah da zuciyata ke kinta ba.”
Khalid ya dauko wayar, “Ni zan rubuta mata. Ban dauke shi wani aiki mai girma ba.”
Ya yi kokarin kwace wayarsa. “Oh wato kana so ka kaskantar mun da girmana ko?”
“Ko kadan ba haka ba ne ba Ishraq. Ba zan rubuta wani abu mai aibu ba. Infact, idan ma na rubuta zan ba ka ka gani inda bai maka ba sai a gyara. Kai ka kasa ka gane duk abun na da nake for your own sake nake yinsa. If ba haka ba me yai ruwana da wata Mahboobah da har zan damu kaina a kanta?”
Ajiyar zuciya Ishraq ya sauke, bai kuma cewa komai ba har Khaleed ya gama rubuta sakon ya nuna mishi. “Ba sai na gani ba, ka tura mata kawai.”
Bai jira komai ba ya tura mata sakon sannan ya mayar da wayar kusa da Ishraq. “Ni zan tafi gida. Duk abin da zuciyarka ta yanke a abu na gaba kana iya kira na. Ina tsoron sake cewa ga abin da za a yi kana gwasale ni.”
Har ya mike Ishraq ya sha gabanshi. “Kar kai mun haka Khaleed Zannah. Kar ka yi zuciya da ni don Allah. Ka yi hakuri da halina, ka bi komai a sannu, ka san ni bako ne a abun.”
“Ni ban ce ina fushi da kai ba likita. Kawai gani na yi duk abin da zan kawo sai ka kawo suka a kai. Kiyayyar Mahboobah ko yaya ne ya kamata ka rage ta, tun da har kuke neman zama a inuwa daya. Na sani ba ka son ta. Za ka aure ta ne don ba ka da yanda za ka yi. Amma yana da kyau ka rage bin shawarar zuciyarka. Be a man, ka zama mai rinjayar mummunar shawarar da zuciyarka za ta ba ka. Daga haka sai ka ga komai yana tafiya yanda ake so.”
“Oh Okay Khaleed. Yanzu ta ya kake tunanin zan fara sanar da Mami wacce na zaba?”
Khaleed ya koma ya zauna. “Kar ka tsaya ba ta dogon essay. Kawai ka ce ka tsayar, ta sanar da dangin mahaifinka su je neman aure.”
“But Khaleed…kana ganin Mahboobah za ta amince bayan duk wulakancin da na mata a baya? Har yanzu ba ta yi reply ba kuma ba ta kira back ba.”
“Ishraq, ka ji abin da qawayenta suka fada ai. So dole ka yi mata uzuri. Ba na tunanin za ta ki amincewa kuma. Ko ba komai soyayya bata faduwa kasa banza.”
Ya sauke ajiyar zuciya Ishraq. “To ba komai, zan fada ma Mami yanzu idan na tafi.”
Tare suka fita, a parking lot suka rabu kowa ya hau motarshi.
*
Idonta kyam yake a kan screen din wayarta. Ta kalli text dinshi, ta karanta ya fi sau ba adadi. Ta sake komawa wurin 2 missed calls din da yai mata, sai kara kallo take tana al’ajabi. Wani bare na zuciyarta na karyatawa, yayin da mafi rinjaye ke gasgatawa, sai dai mamaki ya hana ta tabuka komai a daidai wannan lokacin.
Ta cire wayar daga flight mode, za ta latsa kiran shi kuma sai ta fasa. In ta kira me za ta fada masa? Rabon da ta bude baki ta yi magana an yi kwanaki. Sai ta fasa kira. Ta hada kanta da guiwa tana rasa a halin da take ciki. Na farin ciki ne ko akasin haka? Mamakin yanda Ishraq ya neme ta da kanshi take. Kamar daga sama ta ji sautin kira na shigowa a wayar, ta duba ta ga lambarshi ce, jikinta na rawa ta dauka tana mai karawa a kunnenta.
Yana jin sautin numfashinta. Yana jin shesshekar kukanta. Sai dai ba ta ce komai ba. Shi kanshi din da ya kira bai san me zai fada mata ba. Yana da abun cewa sai dai bai san ta inda zai fara ba ne.
STORY CONTINUES BELOW

“Ya kike ya karfin jiki?” Shi ne kadai abin da ya samu furtawa, yana fadi yana da na sani. Bai da wata mafitar ne.
Kamar mai koyon magana ta bude bakinta, ta fara ajje sautin maganar da ba kowa ba ne zai iya gane abin da ta ce. “Ji…jiki da…dada…da sssauki.”
Guntun tsaki ya saki a saman lebonshi. Wani irin haushinta ya kara ji.
“Zan aure ki ba don ina son ki ba. Na tabbata kina mamakin yanda na neme ki a karan kaina. Rashin mafita ne ya jawo haka. Ke ma kin san ba kaunarki nake ba. Kawai na yi bincike ne na gane tarbiyyarki da ta gidanku baki daya, bayan Mamina ta tilasta lallai sai na fitar da matar aure. Zan fada mata ke ce zabina dan rashin sanin madafa kawai. Ki sanar a gidanku za a zo neman aure. Idan an tsayar da ranar zuwa zan turo miki sako.”
Bai ko jira ya ji ta cewarta ba ya tsinke wayar cike da takaici da tsanarta.1
Murmushi ta saki mai hade da ruwan hawaye. Ta ji dadin hakan sosai, ta yarda za ta aure shi duk kuwa da tarin tsanarta da ya yi. A hankali za ta koyi zama da shi, za ta yi zaman ibada, zaman bautar aure, har zuwa lokacin da mutuwarta za ta riske ta.
Ta share hawaye, “In shaa Allahu wannan shi ne karshen zubar hawayena a kan soyayyar Ishraq. Alhamdulillahi Yaa Allah! Allah ka ba mu zaman lafiya ka ba ni ikon bin sa duk tsanani duk wuya.”
Mommy da ta zo gittawa ta dakin ta tsinci kalaman da Mahboobah ke furtawa. Cikin mamaki ta rike habarta tana zira ido ta saitin kofar dakin. Ta kasa daina mamaki, hakan ya sa ta bude kofar dakin da sallama a bakinta ta shiga.
“Ke da wa kike magana ke kadai?”
Ta zabura ta dawo hayyacinta. “Uhmmm…”
Zama ta yi a kusa da ita, ta dafa kafadarta. “Duk da na so na yi zuciya da ke amma na gaza yin hakan Mahboobah. Soyayyar uwa da ‘ya ta yi tasirin da na kasa iya share ki. Na kasa. Ki ga duk yanda kika bi kika mayar da kanki dan Allah. Kin koma tamkar mahaukaciya Boobah. Ji gashinki duk ya cukurkude babu gyara. Ji yanda akaifa tai miki, duk tsaftarki da na sani. Ki rufa wa kanki asiri, ki rufa mana asiri ki kokarta saita tunaninki, ki dawo hayyacinki tun ba ki kashe rayuwarki bayan kuruciya na tattare da ke ba.”
Mahboobah ta rintse idonta da karfi, babu ko dison hawayen da ya fito. Ta kalli Mommy hade da sakar mata murmushi.
“Hawaye ya kare Mommyna. Babu sauran kunci ko damuwa a tattare da ni. Na dawo hayyacina, Ishraq ya yarda zai aure ni.”
Har da guntun hawayen farin ciki Mommy ta yi hamdala. “Alhamdulillah! Na gode wa Allah, na gode wa Ishraq da ya tsamo mun ‘yata daga kogin da ya yi silar fadawarta. Duk da shi ne silar komai amma ba zan kasa gode masa ba. Ya jefa ki kuma ya tsamo ki. Ashe da gaske ne abin da kunnuwana suka jiye mini daga bakin kofar dakinki.”
Kai Mahboobah ta daga cikin farin ciki.
“Kai gaskiya wannan lamari ya yi mini dadi. Ashe akwai ranar da Mahboobana za ta dawo hayyacinta, ta dawo asalin Mahboobah Bukar dinta.”
Suka rungumi juna cike da jin dadi.
“Duk kokarina na ganin na gyara babban kuskurena na baya nake yi Boobah. Ban manta sakacinmu ba, sakacin da muka yi ni da Abbanki ba…” Ta hau tariyar wani dogon lokaci da ya gabata…
*12th June 2008*
_Tun daga bakin kofar daki take jiyo shesshekar da Mahboobah ke yi. Ta hanzarta shigowa cikin dakin, a tunaninta za ta gan ta tana kuka, amma sai ta ga akasin haka. Ta same ta zaune a kan lesson table dinsu tana homework, sai nishi take yi._
_Da murmushi a saman fuskarta ta ce “Mommyna kin ga na iya homework da kaina, Yah Aliyu ya zo zai taya ni na ce ya bar shi na iya, kin ga.” Ta gwada mata tana murmushi, sai dai duk karshen maganar da za ta kai da huttai take kai shi._
_”Ehh na gani diyar albarka. To shi kuma wannan nishin da kike na mene ne? Hala guje-guje kuka yi?”_
_”A’a ban yi komai ba Mommy, haka nan kawai na ji tauri a numfashina.”_
_”Lallai wai tauri, wannan yarinya da sokana kike.”_
_Daga haka ta fice daga dakin ba tare da ta yi kwakkwaran binciken dalilin da ya sa Mahboobah ke wannan huttan mai ban tsoro ba._
_Bayan ta koma daki ta zauna, Mahboobah ta shigo dakin da gudu ta zauna a gefen Fareedah._
_”Mommy…Mommy!”_
_”Ya aka yi kike gaggawar kiran sunana Mahboobah? Bi a hankali kin ji.”_
_”Uhm…Mommy nan dina ne, ya sake yi min tauri.” Tana yi tana jan nunfashi._
_”Ni dai wannan tauri na gaza fahimtarshi Mahboobah. Amma an jima idan Daddy ya dawo ki je ki fada mishi ko?”_
_”To Mommy.” Daga haka ta kama gabanta._
_Da Daddy din ya dawo ba ta sake jin taurin numfashin ba bare ta je ta fada masa, ita kuma Mommy ta ma manta da an yi, suka ci gaba da harkokon gabansu._
*
Ta sauke ajiyar zuciya hade da share hawayen da ta ji ya sauko mata.
“Momy kuka again? Na ce miki ki daina, ciwona ya warke, babu sauran depression tun da Ishraq ya yarda zai aure ni. Kar ki sake shiga damuwa in dai don ni, ni ma na miki alkawari duk rintsi ba zan sake shiga damuwar ba.”
Mahboobah ba ta san dalilin zubar hawayen Mommy ba, ba ta san cewa baya ta tuno ba, sakacinsu da har ya ta’azzara larurinta.
End of chapter
Hello sweethearts. Fatan na same ku lafiya. Ya kwana biyu? My birthday gifts?☹️lol
Okay Okay how’s our story so far?
Ko da gaske kukan Mahboobah ya kare? Za ta iya jurar wulakancin Ishraq kuwa? Shin😹😹😹ku bibiyi labarin😻
Thank you all❤️🥰
Princess Amrah
RAZ 2Flashback…20th April 2010 (Komawa Baya)
Hawaye share-share kwance a saman fuskarta, ta saka dogon hijabinta sannan ta dauko ‘yar jakar kayanta. Ta fito tsakar gida, ta samu Abbanta tsaye, Mama a kusa da shi. Ta dire jakarta a gaban Abbah, sannan ta rungumi Mama.
“Mama za mu tafi…” kuka ya ci karfinta, ba ta ko kai karshen zancen nata ba.
“Allah ya tabbatar da dukkan alkhairanSa a rayuwarki Ameerah. Allah ya sa wannan tafiyar ita ce silar farin cikinki. Allah ya yaye miki duk wani kunci ya musanya miki shi da alkhairi. In shaa Allahu zan kawo miki ziyara. Allah ya ba ki miji na gari. Allah ya yi miki albarka.” Ita ma ta ji hawayen yana sauko mata.
Ameerah ta kirkiro murmushi, “Ka ga Hajiya Mama ana hawaye za a rabu da ‘yar auta. Ashe dai za a yi kewar Ameerah sarkin kiriniya.”
Dukkansu sun san dariyar nan tata ba ta kai ciki ba, yake ne kawai. Ita kokari take na ganin ta saisaita damuwarta, ko dan hankalin iyayenta ya kwanta. Sai dai ba ta sani ba, damuwar wanda bai cika saurin damuwa ba sam ba ta boyuwa. Duk yanda ta so pretending ba ya taba yiwuwa dole sai an gane mata.
“Mu je ko?” Abba ya kalli Ameerah yana kokarin daukar jikkarta.
“To Mama, saduwar alkhairi. A yayyafe mu.” Ta yi saurin goge hawayen da ya sauko mata.
“Ba ki mun komai ba sai alkhairi Ameerah. Ku je, ki kula da kanki, ki kula da ibadarki, ki ji tsoron Allah a duk inda kike.”
Ta jinjina kai hade da bin bayan Abbanta.
Kamar an ce su fita Mama ta duke a wurin tana kuka sosai. Tun da ta haifi Ameerah ko kadan ba ta taba yin nisa da ita ba. Koyaushe suna tare, su yi fada su yi dadi. Tana tsananin kaunar Ameerah, da ma su biyu ne ta haifa ita da Yayanta, wanda ya rasu sanadiyyar cutar sickler.
Ta shaku sosai da Ameerah, tana mata kaunar da ita kanta ba ta san adadinta ba. Hakan kuwa bai rasa nasaba da yawan kyautata mata da take yi, duk damuwa da kuncin da za ta shiga sai Ameerah ta yi kokarin warware mata, ta saka ta nishadi. Ameerah mutum ce har da rabin mutum. Yarinya karama mai zuciyar manya. Yau ga shi dalili ya yi dalilin rabuwa da tilon diyarta, ta tafi inda za ta jima ba su sake haduwa ba. Ameerah da wannan garin kuwa sai dai ziyara, kawunta ya ce a mayar da ita can dindindin, ko za ta samu sassaucin zuciyarta.
“Ya zan yi da kewar Ameerah?” Ta sake fashewa da wani kukan.
Da azahar suka isa garin Kaduna. Sun sauka a Kawo, daga nan suka hau keke napep ta idasa isa da su cikin Sabon Kawo. A cikin napep din ma sai da Abba ya sake yi mata nasiha. “Ki kokarta ki rage wa kanki damuwa Ameerah. Ki sani cewa dukkan bawa ba ya tsallake wa kaddararsa. Kuma kowanne mutum da kike gani akwai jarrabtar da Allah zai iya aikowa a saitin duniyarshi. Ki dauka cewa rabuwa da Nurah wani yankin jarabawa ne daga cikin jarabawoyinki na rayuwa. Ki ci gaba da addua tare da rokon zabin alkhairi. In shaa Allahu za a zana miki jarabawa. Idan ta yi kyau Yaya Mukhtar zai nema miki karatu, ki ci gaba da yi har Allah ya kawo miki mijin aure. Ina alfahari da ke Ameerah.”
Ta saki murmushi. “Na ji dadi sosai Abba, ashe ni ma ina da rabon yin karatun nan da ban taba kawo ma raina yinsa ba.”
Ya mayar mata da murmushin shi ma. “In shaa Allahu kuwa Ameerah.”
Daga haka suka iso gidan. Abbah ya ba mai napep kudinshi sannan suka isa cikin gidan.
STORY CONTINUES BELOW

An musu tarba mai kyau. Iyalin gidan suna da kirki sosai. Maryam ta rungumi Ameerah cike da kauna, “Da ma mun so ki zauna ga bikin Yaya Nafeesah amma kika ki zama. Ga shi Allah ya rubuta a nan za ki ci gaba da rayuwa.”
Kanwar Maryam, Saudah ma ta rungume ta, “Mun ji dadin dawowarki sosai Ameerah. We love you.”
“Ni ma ina son ku.” Ameerah ta fada da murmushi shimfide a saman fuskarta.
Abbah ya ji dadi sosai a ranshi. Abinci ya ci ya yi sallah sannan ya ce shi zai koma. Maman su Maryam Hajiya Salma ta ce “Haba Baban Ameerah, yanzu kana nufin ba za ka tsaya Alhaji ya dawo ba ku gaisa?”
“Babu komai wallahi Hajiya. Ba na so in yi dare ne hanya babu kyau, ga shi har la’asar ta kusa. In ya dawo dai a gaishe shi. In shaa Allahu za mu yi waya idan na sauka.”
“To babu komai. Allah ya kiyaye hanya. A gaishe da Maman Ameerah.”
“In shaa Allahu za ta ji.”
Ta so ta taka wa mahaifinta, sai dai kuma idan har ta taka mishi za ta iya yin kuka, kuma kukanta zai tashi hankalinshi. Hakan ya sa ta dake kawai, daga inda take ta daga mishi hannu hade da yi mishi fatan sauka lafiya.
*
Bayan wata uku.
Tashi ta yi, tana jin nutsuwa sosai a kasan ruhinta. Ta shirya a cikin jar atampa riga da skirt, kafin ta tsaida kallon ta a madubin da ke girke daga gefen wardrobe din dakin Maryam. Ta kalli kanta tana mai nazartar fuskarta. Ko ba a fada mata ba ta ga yanda ta rame, ta kara fari tamkar wadda babu wadataccen jini a cikin halittarta. Murmushi ta saki wanda take jin shi yana saukar mata har a kasan zuciya. Ta tabbata da a ce Abbah da Mama za su ga sauyin da ta samu a yanzu, da zukatansu sun yi fari sol, sun haskaka, rayukansu sun farantu matuka. A tsawon watanni ukun da ta samu a gidan Kawu Mukhtar, ta samu nutsuwar da rabon da ta same ta tun da yammacin baikonta da Yah Nurah. Sosai ta kakkabe duk wani datti da ke zuciyarta. Ba wai don ta daina son shi ko kuma soyayyarsa ta ragu a kasan ruhinta ba, ko alama. Soyayya da kaunar Nurah na nan zuciyarta, har abada ba ta tunanin akwai ranan da za ta gushe, ko kuma za ta ragu.
Ta sa hannu ta shafi fuskarta, tana kara sakar ma kanta murmushi. Jikinta ta feshe da turaren dirham, sannan ta daura kallabinta da Maryam ta wayar da ita daurin ture ka ga tsiya na zamani.
A bisa duga-dugan kafafuwanta ta taka, ta nufi falo domin karin kumallo da tun dazu Maryam ta zo ta kira ta cewa an gama.
Karfe goma da rabi na safe ke nan, amma a mamakinta da wannan safiyar ta ci karo da Abbah da Mama zaune bisa tafkeken kafet din da ke baje a tsakiyar falo. Ta murje idonta ko ba daidai ta gani ba, su din dai ne.+
Da gudunta ta isa gare su, ta rungume Mama, tana jin wata irin nutsuwa na sauka a kasan ruhinta. Ta koma ta rike hannun Abbanta, tana sakar mishi murmushin da tsakanin d’a da iyaye ne kadai yake wanzuwa.
“Sai murmushi kike kin kasa ce musu sannu da zuwa.”
Ta juya da murmushi ta kalli Maryam, “Na rasa me zan ce ne Maryam. Murna da farin cikin ganinsu ya sa na rasa abin da zan ce.”
Ta sake juyowa ta kalli Mama. “Wannan irin zuwan ba zata haka.”
“Ya fi dadi ai. In kin san za mu zo na tabbata ba za mu tsince ki a wannan irin walwalar ba.”
STORY CONTINUES BELOW

“Haka ne Abbana. Ina kwana. Ya hanya? Sannunku da zuwa. Ya kuka baro ‘yan garin namu?”
Mama ta gyada kai da fara’a a fuskanta. “Wannan jerin tambayoyi naki Ameerah. To duk lafiya. Mutane suna ta kewarki sun ce a gaishe ki. Kowa ya yi kewar nishadinki.”
“Allah sarki! Ina amsawa sosai Mama. Wallahi na ji dadin ganin ku fa.”
“Ni ma na ji dadin ganin yanayinki a haka Ameerah. Duk da dai kin dan rame amma hakan bai sa fuskarki ta nuna damuwarki ba. Adduata ta karbu ke nan. Allah ya kara ninka farin ciki a cikin rayuwarki Ameerah. Allah ya ba ki miji na gari da zai faranta miki.”
Ta rufe fuskarta cike da kunya ba tare da ta amsa ba, sai Maryam da ke gefe ta amsa da ameen fuskanta kunshe da fara’a.
“Jarabawa dai an gama WAEC lafiya lau babu wata matsala, yanzu sai NECO ce ita ma muna sa rai in shaa Allahu za a dace.”
Ta yi murmushi. “To Allah ya tabbatar mana da alkhairi Abbah. Allah ya biya muku dukkan bukatunku na duniya da lahira.”
“Ameen ameen.”
*
Matukar haske rayuwar Ameerah ta haskaka. Ta manta da duk wani bacin rai da wani abu da ya faru a baya. Amma fa soyayyar Nurah na nan dal a cikin zuciyarta. Ba ta jin har abada za ta iya mantawa da shi, soyayyarshi ba za ta taba shafewa ba a cikin babin rayuwarta.
Ta bude jakarta, daga can kasa ta zakulo wani littafinta, ta bude, hotonsu ne ita da Nurah sun kalli juna, kowannensu dauke da dariya a fuskarshi. Ta gyada kai, idanuwanta na kawo ruwa, ta saka katin hoton a tsakanin kirjinta, tana jin bugun zuciyarta na sauyuwa, zuciyarta na hasko mata wani shudadden lokaci na daga rayuwarta…
Flashback
_Ya rufe littafinsa a daidai lokacin da ya kai karshe a cikin darasin tajweedi. “Akwai mai tambaya?”_
_Kowa ya yi shiru alamun babu. Ya sake maimaitawa nan ma shiru. “To ni bari in yi tun da babu mai tambaya…” kafin ya rufe baki Ameerah ta daga hannu. Dan da nan ‘yan aji suka fara kananan surutai, “Ke wannan Ameeran nan kullum babu mai bata mana lokaci idan an tashi sai ke. Kina ga har an fara watsewa daga makaranta shi ne za ki wani daga hannu.” Kowa da kalan surutan da yake yi._
_”Ehh an yi din ina ruwan wasu. A zo a daken in an ji haushi.” Ta murguda baki. Ba ta ko ji tsoron garadan cikin ajin ba, ita kadai ce ‘yar karama tun daga kan maza har mata, duka shekarunta goma sha biyu sauran kuwa har da masu ashirin da dori._
_”Ansituuuuu!” Malamin ya fada hade da buga teburinshi. Duk suka yi shiru rayukansu a bace. “Ina jin ki Ameerah.”_
_”Yauwa Ustaaz. To na ji a bayaninka babu wani bambanci tsakanin maddul asaliy da maddud’d’abi’iy. Amma me ya sa aka bambanta sunan bayan kuma duk ma’anarsu guda ne?”_
_”Barakallahu feeki. Idan kika auna ko a Hausance, aka ce miki dabi’a, aka ce miki asali, za ki ga kusan suna da alaka. Saboda dabi’ar mutum yana yin ta ne tun asali. Haka kuma asalin mutum dabi’arsa na bibiyarsa. Da wannan kadai za ki gano alakar sunayen. Gaskiya ne duk daya ne. Idan kika duba cikin Qur’ani mai girma irin wannan maddar da ake ma jaa guda biyu ta fi yawa. Ita ce ainahin maddar asali ta dabi’ar makarancin Al’Qur’ani. Don haka…”_
STORY CONTINUES BELOW

_”Na fahimta Yaa Ustaaz. Na gane.”_
_”To ma shaa Allahu. Sai ki yi mana addua.”_
_Daga haka Ameerah ta musu addu’a duk aka fita daga ajin. Kafin ta gama harhada littattafanta Hafsa ta ce “Ke ni ki yi sauri malama kina ganin rana ta yi sai jiran ki nake.”_
_”Yi hakuri Hafsa ga ni nan zuwa.” Ta fada ma Hafsa da ke tsaye bakin kofar ajin tana jiran ta, kasantuwar ba ajinsu daya ba, Hafsa na kasa da ita._
_Ta zo fita Mallamin ya tsayar da ita. “Ameerah kina da kokari sosai ma shaa Allah. Ina son dalibi mai kwazo da bada himma. Ki ci gaba da mayar da hankalinki kin ji.”_
_”In shaa Allahu Yaa Ustaaz.”_
_”Ina ne gidanku?”_
_Ta kwatanta mishi._
_”Ma shaa Allah. In shaa Allahu an jima zan zo wurin mahaifinki in gaishe shi, in fada mishi tarin kwazon da diyarshi take da shi.”_
_Ta yi murmushi kawai ba tare da ta ce komai ba._
_A hanyarsu ta komawa gida Hafsa ta ce “Wai miye hadinki da Ustaaz Nurah na ga sai wani murmushi kuke wa junanku?”_
_Ameerah ta zaro ido. “Me kuwa in ban da Malami da dalibarsa?”_
_”Uhmmm…lallai ma. Ni za ki boye wa ko?”_
_”Me zan boye miki Hafsa? Babu abin da na sani ni kam.”_
_Hafsa ta yi murmushi. “In ta yi tsami ma ji.”_
_Daga haka suka rabu kowacce ta kama hanyar gidansu._
_Da dare Nurah ya yi sallama gidan su Ameerah, Abbanta ya fito. Har kasa ya duka ya gaishe shi, ya gabatar masa da kansa shi ne malamin su Ameerah, sannan ya ce, “Yarinyarku tana da kwazo sosai, Alhamdulillah! Irin su ake so. Ina kara jinjinawa da kokarinku na ganin kun ba ta tarbiyya mai kyau.”_
_Abba ya saki murmushi, “Ku ma ina kara jinjinawa da naku kokarin. Ya sunan naka ne?”_
_”Sunana Nurah.”_
_”To ma shaa Allahu Mallam Nurah. Na ji dadin zuwan ka sosai. Ai tana dawowa dazu take sanar da ni za ka zo. Gaskiya na ji dadi.”_
_Nurah ya sosa keyarshi, “Babu komai Abbah. Sannan kuma magana ta biyu. Ina neman izini in dai ba a yi ma Ameerah miji ba, a ba ni damar kasancewa daya daga cikin manemanta. Ina son ta tsakanina da Allah, ina son ta ko don ilimi da tarbiyyarta.”_
_Murmushi Abbah ya fadada. “Ba a yi mata miji ba Nurah, sai dai yarinya ce duka yar shekara goma sha biyu. Karatu ma take yi, tsawon kafa ne ya kwashe ta haka da wuri.”_
_”Babu komai Abbah in dan wannan, zan jira ta, ni ma karatun nake yi a ABU Zaria, duka ma yanzu na fara ban yi nisa ba. Hutu ne idan mun samu nake dawowa, sai kuma nakan zo weekend duk bayan sati biyu. Izinin dai nake nema Abbah.”_
_Abbah ya dafa kafadarshi, “Babu komai Nurah, wannan ma wata cikon tabbatuwar tarbiyyarka ne, ka nemi izini kafin ka isar da soyayyarka gare ta. Na maka izini Nurah. Allah ya tabbatar da alkhairi a soyayyarku, Allah ya kawar da sharrin shaidan da na mutum.”_
Ci gaba…
Ta share hawaye mai gumi daga kumcinta, ta kokarta furzar da hawayen da ya shiga cikin bakinta, tsananin dacinsa take ji.
Wannan shi ne silar soyayyarta da Nurah. Sun gina soyayyarsu cike da tsafta da kaunar juna. Sai dai sabani na yau da gobe, wanda zai iya gittawa ga dukkan wanda suke tare da juna ko da ba da sunan soyayya ba ne.
End of chapter
Hello lovelies 😻❤️fatan na same ku lafiya. Yau kam na zo muku da tushen soyayyar Amnoor🥰masoyan da aka farraqa ta karfi da yaji😢💔 duk dakewar Ameerah ta kasa daina hawayen rabuwa da Nurah. She still loves him. Rabuwa da masoyi ba dadi😫so sorry Ameerah habibty 💕
Princess Amrah
RAZ 2Story continued…(Ci gaban labari)
Da yanayin annurinshi kadai Mami ta fahimci akwai kyakkyawan labari a bakinshi. Duk da cewa a iya bisa labba annurin yake, ya yi duk iya kokarinshi na ganin Mami ba ta fahimci damuwa da yake ciki ba, sai farin cikinshi kadai ta iya hangowa.
“Kamar akwai labari mai dadi a bakinka likita.” Ta fada a lokacin da take zuba masa farfesun kan rago da sinasir.
Ya dago kyawawan idanuwanshi ya kalle ta, ya sakar mata murmushinshi da yake kara yawaitar kyau a bisa halittar fuskarshi.
“Burinki ne ya cika Mami.” Ya furta yana mai sunne kanshi.
Ta sani, duk duniyar nan babban burinta guda ne, ta tabbatar kuwa da cewa shi Ishraq ke nufi. Hakan ya sa ta sakin murmushi a saman dattijuwar fuskarta. “Alhamdulillahi! Allah abun godiya. Gaskiya na ji dadin wannan labarin. Ya sunanta?”
Ya dukar da kanshi kasa. “Sunanta Mahboobah.”
“Ma shaa Allah! Kai anya kuwa yau zan iya bacci?” Ta zauna bayan ta gama zuba mishi abincin. “Ko kai fa Ishraq. Yanzu na ji batu. Gaskiya wannan lamari ya yi mini dadi kwarai da ainun. Allah Ya yi maka albarka ya sa yarinyar arziki ce gare mu baki daya.”+
“Ameen Mami. Sai ku yi magana da su Uncle Fahad. Kila yanzu za su sama mun lafiya da zancen Bilkeesu.”
“Ai yanzu ma in banda dare ya gabato da na kira su. Amma gobe da safe da izinin Allah zan kira Fahad, zan kuma kira kanina Salihi, su shirya zuwa neman auren tilon gudan jinina.”
Annuri ya kasa boyuwa daga saman fuskarta. Abinci take ci amma murmushi kawai take sakar wa kanta.
“Likita yaushe za a kawo mun ita ta gaishe ni? Na ji kaunarta ta shige ni sosai Ishraq. Ina son duk abin da kake so. Ina son Mahboobah tun kafin in gan ta.”
Tausayin Maminshi ya ji, ta yanda take tunanin auren soyayya ne zai yi. A wani bangaren kuma takaicin yanda ta tilasta mishi tsaida mata yake yi, ga shi dalilin haka ya sanya shi zabar wacce bai taba jin ko dison sonta a zuciyarshi ba.
“Mami ba sai na kawo ta ba, na tabbata ma a gidansu ba za a bar ta ba. Mami ita din da za ta zama taki. Ki daina azarbabi gare ki ma za ta dawo har sai ta gundire ki…”
Ta yi saurin katse shi, “Ba za ta taba gundira ta ba Ishraq. Zan so Mahboobah tamkar diyar da na haifa da cikina. Zan gwada mata soyayya tamkar yanda zan gwada maka. Zan ja ta a jikina fiye da yanda nake jan ka, saboda ita mace ce, na so diya mace sai Allah bai ba ni ba, Ya bar ni da kai daya tilo kuma ina godiya gare Shi. Ga Mahboobah nan za ta maye mun gurbin diya mace.”
Murmushin dole ya saki, kafin ya goge bakinshi da tissue ya fara kwashe kayan wurin.
*
Bakar cotton long sleeve ya saka, ya sanya ash din trouser, ya yi zanzaro, ya dora ash and black neck tie, ya dora ash suit a saman rigar shi, sannan ya sanya siririn medical glasses dinsa. Ya kalli kanshi a madubi, ya fito sak a Doctor Ishraq dinshi. Me ya rage? Ya dauko comb ya hau sharce kwantacciyar sumarshi. Zahirin kyanshi ya fito.
“Assalamu alaikum.” Ya tsinkayo muryan Mami daga bakin kofar dakinshi. Ya amsa sallamar yana mai waigowa tare da sakin kyakkyawan murmushin tarbarta.
“Mami ina kwana.”
“Lafiya kalau likita. Har yanzu ba ka fita ba?”
STORY CONTINUES BELOW

“Ehh Mami, dayake ma wata seminar za mu je National Hospital Abuja. Kuma sai karfe biyu na rana za a fara. So na fi so daidai sadda zan isa a fara, ba na son jira.”
Ta sakar mishi murmushi hade da neman wuri ta zauna. “Yanzu na kira kawunka Ibrahim, na shaida mishi komai, ya ce to ka sanar a gidan su yarinyar, gobe in shaa Allahu da laasar za a je neman aure.”
Cikin halin ko’inkula ya ci gaba da daura agogonshi. “Okay Mami. Allah ya kai mu.”
“Ameen ya Allah. Sai ka sanar da Mahboobah. Ni ya kamata ma ka ba ni lambarta mu fara zumunci tun yanzu. Don na san komai ba za a yi jinkiri ba, sai dai in daga gidan su yarinyar ne za a samu.”
Bai ce komai ba ya dauko wayarshi, ya karbi ta Mami ya rubuta mata lambar Mahboobah.
“Mami Allah ya sa dai kin yi kunu.”
“Na dai dora ruwan zafi na san yana gaf da tafasa. Bari in je in dama maka. Ai ni na zata ma har ka tafi shi ya sa ban damu sai na dama da wuri ba. Bari in dama maka da hanzari.”
“No Mami ki bi komai a hankali har yanzu ina da sauran time. Kin ga ko goma ba ta yi ba.”
Tare suka fita daga dakin, ya zauna a falo yana rubuta wa Mahboobah text message.
***
Rabon da ta jeru tare da yan uwanta wurin cin abinci har ta mance. Ta fito da murmushi kunshe a saman kyakkyawar fuskarta. “Yah Aliyu shi ne ko ku kira ni mu ci abinci tare ko?”
Cike da mamaki Fareedah ta dago ta kalle ta, sai kuma ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da cin dankali da plantain dinta.
“Wai ke Reedah me kika taka ne? Sam-sam babu ruwanki da ni. Me na yi miki?”
Ba ta dago kai ta kalle ta ba ta ce, “Yah Boobah tambaya kike me kika yi mun?”
Ba ta ba ta amsa ba sai ta iso dining area din, ta zauna a kujerar da ke fuskantar ta Reedah. Ta zuba ma kanta soyayyen dankali da scrambled egg. Ta zuba ruwan zafi a cikin cup din cappuccino, sugar cubes ta zuba, sannan ta hau karyawa ba tare da ta sake cewa uffan ba.
Sai bayan sun gama ne Mommy ta fito, Mahboobah ta gaishe ta, Aliyu da Fareedah ma suka gaishe ta.
“Alhamdulillah! Ashe ina da rabon sake ganin yarana a wannan yanayin? Ashe da rabon zuciya da gangar jikina za su sake tsunduma cikin farin ciki? Ina dad’a godiya ga Allah.”
Mahboobah ta sakar mata murmushi. “Mommy ina mai kara neman gafararki…”
“Shhhhhhh!” Mommy ta dora yatsa a saman labbanta. “Tun jiya na fada miki komai ya wuce Mahboobah.”
Karar text message ta ji a wayarta, ta yi gaggawar dubawa.
*’Gobe da yamma magabatana za su zo gidanku maganar neman aure. Ki sanar da iyayenki, bayan laasar za su zo.*
*Ishraq Sulaiman.’*
Murmushi ta saki wanda ita kanta ba ta san sadda ta sake shi ba. Ta gagara rufe bakinta, sai sake maimaita karantawa take yi, har sai da Mommy ta yi mata magana ta ci gaba da shan tea dinta kar ya huce. Da sauri ta ajje wayar, ta dauki cappuccino cup din tana ci gaba da sha amma duk da haka hankalinta ba ya kai. Ta yi nisa a tunanin sakon da masoyinta Ishraq ya turo mata, wanda har yanzu take ganin komai tamkar a mafarki.
STORY CONTINUES BELOW

Bayan ta gama duka ta koma falo kusa da Mommy. Ta shaida mata abin da Ishraq ya ce da ita. Mommy ta yi murmushi. “Mahboobah kin tabbata za ki iya rayuwar aure da Ishraq? Kin tabbata za ki yi hakuri da dukkan abin da zai iya faruwa a gaba? Ina jiye miki Mahboobah, ina jiye miki tsoron rayuwar kunci, ba fata nake ba.”
Mahboobah ta sunkuyar da kanta kasa tana wasa da zoben azurfan hannunta.
“Amma tun da ke kika ji za ki iya, fine. Ni dai fatana Allah ya tabbatar miki da dukkan alkhairanSa. Yanzu zan kira Yaya Adamu, zan sanar da shi zancen zuwan magabatan Ishraq gobe, in shaa Allahu.”
Ba ta kuma cewa komai ba daga nan, ta dauki wayarta ta koma daki, ta kira Haneefa da Saleemah video call.
“Hello buddies. I’ve missed you so badly (Na yi kewarku sosai).”
“Hi beautiful soul. We’ve missed you too (Mu ma mun yi kewarki).” Saleemah ta fada fuskarta kunshe da faraa.
“Bae kin ga yanda kika rame kuwa? Duk kankambar da kike kin fi ni kiba yanzu dai na fi ki.”
“Uhmmm…karyar banza kike Hanee. In kika fi ni kiba kuma ai da na shiga uku.”
“You no get sense at all MB. Wai kin ga yanda duk kika yi kashin wuya kuwa? Ke kin fa rame sosai da gaske.”
Mahboobah ta tabe baki. “Ni dai ba wannan ba buddies. Ku shirya shan biki very soon.”
Haneefa ta kwalalo ido. “MB are you serious? (Da gaske ko da wasa?)”
Mahboobah ta daga kai. “Am very serious buddies.”
Saleema ta rangada guda, “Ina ma a ce ina da dogon hanci yau da har neighbors sai sun gane halin farin cikin da nake ciki. Alhamdulillahi. Ishraq din?”
“Shi fa.” Ta ba su amsa.
“Wannan labari ya mun matukar dadi MB. Saleemah yaushe za mu je mu fitar da ashobe?”
Mahboobah ta kwalalo ido. “You fool! Ashobe tun yanzu daga fara magana. Sai ma fa gobe iyayenshi za su zo nan gidanmu wurin su Kawu.”
“This is serious ki ce dai abu kusa-kusa MB. Ni ai na ma kasa rufe bakina tsabar farin ciki. Hooo mu bride’s maids.” Haneefa ta fada ta mike tana taka rawa.
“To dai ba wannan ba. Za ku zo gobe ai ko? Kun san dai ni da Mommy da Reeder ba za mu iya aikin tarbansu ba. You have to come and help us Okay?”
“Really. Za mu zo in shaa Allah. Our very own best friend is getting married ai dole mu yi sammakon zuwa.”
“Yauwa Hanee, idan na shirya zan zo mu tafi. Ko kuma ki biyo ki dauke ni kin san my car is giving me headache.”
Suka kwashe da dariya su duka.
“Okay I will.”
Daga haka suka yi bankwana, kowaccensu cike da farin ciki, zuqatansu na musu dadi. A bangaren Haneefa da Saleemah, tsananin farin cikin halin da suka tsinci aminiyarsu a ciki kawai suke yi.
Washe gari.
Tun da garin Allah ya waye suke shirye-shirye, su ne ba su samu zama ba sai karfe uku na rana. Abinci da abun sha kala-kala suka hada. Tun daga kan fried rice, jollof rice, fried spaghetti, potato salad, pepper chicken, pepper soup, chapman, zobo, snacks iri daban-daban.
Bayan sun gama shirya komai suka koma dakin Mahboobah suna mai da numfashin gajiya.
“Buddies am tired.”
“Farawa ma kika yi yarinya. Kina amarya har kina da bakin ce mana kin gaji tun yanzu.”
“Uhmmm lallai ma Sally. Sai kar in gaji ashe.”
“Ehh mana, ko mu ai ba mu isa mu ce mun gaji ba tun yanzu. Hidima kuwa yanzu muka fara.”
“Saleema, Haneefa! Wai kuna ina ne? Kun dai san ai ba ku hada coleslaw din can ba ko?”
Haneefa ta dage gira tana murmushi. “Mommy fa shi ba da wuri ake hada shi ba dan kar ya lalace. Amma mun hada komai ana yin laasar za mu yi. An yanka cabbage an wanke da vinegar ba zai yi komai ba in shaa Allah.”
“To shi ke nan. Yanzu ku fito ku gyara falon bakin can. Rabon da a bude shi tun rasuwar Daddynsu. Da na yi tunanin a kawo su wannan falon ne shi ya sa ban sa an gyara wancan ba. To kuma na ga kamar wannan din zai iya yin kadan tun da ba wani girma ne da shi sosai ba. Ku tashi maza ga Fareedah can na tado ita ma.”
Su duka ukun suka mike. A kofar dakin suka samu Mommy tsaye. Mahboobah ta turo baki. “Ai dai ni Mommy ba sai na yi ba ko?”
Sekeke Mommy ke kallon ta. “Look at this girl (Ji wannan yarinyar). Ashe ma ba sai kin yi ba. Saboda ke kadai ce yar lele?”
Dariya suka sake su duka. Haneefa ta ce “Ahh wai saboda ita ce amarya nufinta ko?”
Duka Mahboobah ta kai mata, daga nan suka nufi babban falon bakin da ke haggu da bangaren su Mommy.
Karfe hudu da rabi magabatan biyu suka hadu. Sun yi gaisawar mutunci. Sun ci sun sha, inda a karshe aka yanke shawarar kawo kayan sa rana cikin sati biyu masu zuwa, a daura aure bayan wata biyu.
Bayan sun tafi, Haneefa da Saleemah suka dauki gud’a, hade da shewa da karfi. Cike suke da farin ciki, jin dadi da walwala sun kasa boye kansu.
Mahboobah na zaune kan gadonta, in ban da murmushi babu abin da take sakan ma kanta. A haka aminnan nata biyu suka zo suka same ta. Wannan ta dafa wannan kafadar, wannan ta dafa waccan.
“Finally, our buddy is going to be Ishraq’s property. Am really happy for you MB. Na ji dadin cikar burinki. Na ji dadi kwarai da gaske.” Cewar Haneefa, kamar ba ita ba ce mai zafin ran nan ba a farko.
Saleemah ta murmusa a karo na ba adadi. “We are going to be maids of honor (Mun kusa zama hadiman amarya). Muna zuwa a wani biki muna ganin yanda maid of honor ke burge mu. Yanzu ga shi mu ne, na babbar aminiyarmu.”
Rungumar juna suka yi, suna jin yanda duniyarsu ke musu dadi, kaunar junansu na dad’a ratsa duk wata kusurwa da take jikin gabbansu.
End of chapter
Assalamu alaikum watahmatullah! How have you been all? Fine in shaa Allah❤️ and we are here. Mahboobah Bukar is getting married to her lovely Ishraq. While he doesn’t love her. Ya wannan rayuwar aure za ta kasance?
Let’s go together 😻✨🙌🏻
I do love you
#bakuwarfuska
#amrahwrites
#nagartawriters
#bkf
Princess Amrah
RAZ 2Jin ta take baki daya a wata duniya, duniyar farin ciki, duniya mai cike da walwala. A rayuwarta, idan aka cire yarintarta, ba za ta taba tuna ranar da ta shiga farin ciki irin wanda take a kansa ba yanzu. Sai kuma ta runtse idonta, tana kokarin tuna silar komai, silar yi mata dashen zuciyar da tun da aka yi mata shi ta kamu da tsananin soyayyar Ishraq Sulaiman.
Flashback…
Da karfi take jawo numfashi, tana yi tana huttai, tana jin wani irin nauyi a tsakanin kirjinta. Ita kadai ce a dakinta, da tsakiyar dare kimanin karfe ukun dare. Sosai ciwon ya ci karfinta, ta yunkura domin ta dauko maganinta amma ina, ta kasa, ji take jikinta ya mata tsananin nauyi, nauyin da ta kasa ko da motsa gangar jikin nata.
A hankali ta kokarta daga hannunta, ta jawo side lamp (fitilar gefen gado) da ke girke bisa side drawer din ta, cikin cijewar labba, ta buga side lamp din da karfi, yanda ta tabbatar da dole sai an jiyo karar.
Cikin sa’a kuwa tamkar a mafarki Mommy ta jiyo, sai dai ta rasa takamaimai daga ina wannan kara ta fito, haka Aliyu ma ya yi saurin fitowa daga dakinshi, har suka yi kicibus da Mommy tana tambayan lafiya yana tambayan lafiya.
“Wata kara na jiyo mai karfi Aliyu. Ban san daga ina ta fito ba.
“Ni ma ita ta fito da ni…” kafin ya kai aya a zancenshi, suka jiyo huttan da Mahboobah ke yi, da karfin gaske.
A hanzarce duk suka isa dakinta, a halin da suka same ta sun gigita matuka, ganin ta unconscious ba karamin razana su ya yi ba.
“Innalillahi wa inna ilaihi raji’un!” Shi Mommy ke maimaitawa a bayyane, yayin da hawaye mai gumi ke sintiri a bisa fuskarta, ya wanke duk kumatunta.
“Aliyu, maza dauke ta mu tafi asibiti.”
Da hanzari Aliyu ya ciccibe ta, Mommy kuma ta yi gaggawar fita ta dauki makullin mota, sannan ta biya ta dakin Fareedah ta tashe ta suka fita tare. Tsabar gigicewa gidan ma a bude suka bar shi. Halin da Mahboobah take ciki, dukkanin wanda yake da dison imani a tsakanin kirjinshi sai ya tausaya mata. Ga wanda ya taba ganin fitar ran wani mutum, to zai iya rantsuwa da Allah cewa rayuwar Mahboobah ce ke kai da komowa, take neman rabuwa da gangar jikinta.
General hospital suka wuce kai tsaye, inda take ganin likitanta. Sai dai a rashin sa’a, ba su same shi ba a lokacin, ba ya ma garin, ya je Potiskum wani aiki.
Ganin halin da Mahboobah ke ciki ya sa likitan da suka samu ya tausaya mata, ya ce zai hada su da Doctor Sadeeq wanda yake cardiologist ne, wato likitan zuciya. Sai da ya fara ba ta first aid (taimakon gaggawa), kafin ya latsa kiran Doctor Sadeeq. Duk da yake tsakiyar dare ne, amma hakan bai hana bugu guda Doctor Sadeeq ya dauka ba.
Da sallama suka gaisa, sannan ya ce “Doctor Sadeeq taimakon nan dai da ka saba yanzu ma shi za ka yi. Patient gare ni unconscious, kuma likitan da ta saba gani Doctor Kabir ya yi tafiya. Ka taimaka ka zo ka duba ta, in da rabon ci gaba da rayuwarta, ka ceto ta, Allah ne kadai zai biya ka.”
Ajiyar zuciya Doctor Sadeeq ya sauke. “Yanzu haka ina asibiti tare da iyalina, labour take tun da yamma ga shi har yanzu ba ta haihu ba, hankalima ya gaza kwanciya Doctor Khamis.”
“Taimakawa za ka yi Doctor Sadeeq. Ni dai nan I did my very best (na yi bakin kokarina). Am not a cardiologist you know (ka sani ni ba likitan zuciya ba ne), ban san komai ba a kai sai abin da ba za a rasa ba. Na dai ba ta nitroglycerin. Idan a yanzu ta farka ba ni da sauran idea na abin da zan mata.”
STORY CONTINUES BELOW

“To shi ke nan Doctor. Ga ni nan zuwa yanzu in shaa Allah.”
“Ka kyauta sosai Doctor Sadeeq. Sai ka zo.”
Ba a wani dauki dogon lokaci ba sai ga Doctor Sadeeq ya zo. Sai da ya fara zuwa ya yi duk wani aune-aune da suka kamata, wanda hakan ya dauke shi kusan awa daya kafin ya gama. A sanyaye ya ce da su Mommy su biyo shi department dinsu, ya ba su lambar Ofishinsa sannan ya yi bankwana da Doctor Khamis, ya nufi parking lot. Motarshi ya hau, su Mommy kuma suka bar Mahboobah a nan, har sun yi tunanin ciccibarta su tafi tare, sai kuma suka yi gudun kar ta farka daga baccin.
Kai tsaye suka doshi wurin Doctor Sadeeq. Wurin zama ya gwada musu, sannan ya zare eye glasses dinshi.
“An kai minzalin da bai kamata a boye muku komai ba, ko don mu taru mu ceto rayuwar yarinyar nan. Magana ta gaskiya, Mahboobah na kan yanayin da dole sai dai mu dukufa da rokon Allah, Ya ba ta lafiya, idan kuma ciwon tafiya ne, Allah ya ba ta sa’ar tafiya…”
Tun bai gama rufe baki ba Mommy cikin kuka ta ce, “Haba Doctor! Me ya sa kana likita amma kake neman dakusar da dan kwarin guiwar da ya yi saura a duniyarmu? Me ya sa ba za ka fada mana zance mai dadi wanda kunnuwanmu za su so ji ba?”
“Saboda ba zan muku karya ba Hajiya. Wajibi ne a gare ni in fada muku gaskiyar abin da yake faruwa. A yanzu haka zuciyarta na kangin end-stage heart failure. That’s means the heart muscle is failing severely in its attempt to pump blood through the body (jijiyoyin zuciyar ba su da karfin tsotso jini daga jikinta). Wannan yake nunar da babu wani sauran magani da zai yi tasiri a yanzu. This is the final stage of heart failure (shi ne mataki na karshe a ciwon zuciya). Wannan heart failure ba wai yana nufin zuciyarta za ta daina bugawa ba ne, a’a, the term failure means the heart muscle is failing to pump blood normally (yana nufin jijiyar zuciyarta ba ta iya tsotso jini yanda ya kamata), saboda ko dai ya yi damage, ko kuma it’s very weak (ko dai ya yi dameji, ko yana da rauni sosai), ko kuma ya hada duka biyun, damage din ko weak din.” Ya yi shiru daga nan yana kallon yanda ruwan hawaye ke wanke fuskar Mommy babu kakkautawa.
Cikin karfin hali Aliyu ya ce, “To yanzu Doctor miye abun yi? Ko kana nufin shi ke nan?”
Ajiyar zuciya ya sauke, cikin kwantar da murya ya ce, “Akwai mafita guda daya.”
“Mece ce ita?” Fareedah ta watso mishi tambaya hade da share siririn hawayenta.
“Heart transplant (Dashen zuciya). Ya furta cikin wani irin yanayi. Sosai yake tausayin halin da Mahboobah take ciki. Shi bai ma taba ganin irin wannan ciwon ya kama mai karancin shekarunta ba. Ya fi kama dattawa wanda suka haura ma arba’in a duniya.
“Ban gane ba Doctor. Kana nufin dashen zuciya ke nan?”
Ya jinjina kai. “Haka nake nufi Hajiya. Shi ne kadai mafita. In ba haka ba kuwa rayuwar Mahboobah na daf da tsayawa. Kamar yanda duk wani mai rai ya sani zuciya ita ce ginshikin mutum. Ba a taba iya rayuwa babu ita a jiki. Haka kuma ba za ta taba amfanuwa babu pumping din jini ba. Dole sai da ita. Dole sai an yi heart transplant ko za mu iya ceto rayuwarta.”
“Innalillahi wa innaa ilaihi raji’un!” Mommy ta fada cikin kuka sosai, duk ta gama kidimewa. “Mun cuce ki Mahboobah. Mu ne silar komai. Duka sakacina ne. Ni ce na kasa ba ki kulawar da ta dace tun yarintarki har ciwon nan ya ta’azzara gare ki. A yau ne nake tir hadi da allawadai da halin sakaci irin nawa.”
STORY CONTINUES BELOW

“Ki daina kalar maganar nan Mommy. Kaddara ta rigayi fata. Yanzu mu san miye next, ba kuka ba.”
“Dole ne in tuna baya Aliyu, saboda mun cuci Mahboobah. Ba zan taba yafe wa kaina ba har in koma ga ubangijin al’arshi mai girma.” Kuka take sosai tana jin tsanani a duniyarta, tana jin tamkar ita ce ta fi kowacce uwa sakaci da ganganci. Nauyi take ji a kirjinta, wanda tun da take a rayuwarta ba ta taba jin irinsa ba. Kanta ciwo, yana sara mata ta ko’ina.
“Idan har kun amince da batun heart transplant din, yanzu za a saka ta a coma, za mu bada cigiyar zuciya, akwai abokin aikina da yake accident and emergency, sau daya ya taba samo mun zuciya, yanzu ma sai ya sake samo mana, amma fa akwai tsada sosai sai idan za ku iya biya.”
Cikin sauri Mommy ta ce “Ko nawa ne za mu biya Doctor, in dai Mahboobah za ta samu lafiya. Ko raina zan iya fansarwa domin tashin kafadun Mahboobah.”
Ya jinjina kai. “To ba damuwa. Bari in kira shi.”
Wayarshi ya dauka, ya latsa kiran abokinshi Doctor Ashraf. Babu jinkiri ya dauka suka gaisa.
“Ina da patient ne da ke kan end-stage heart failure Doctor Ashraf. Iyayenta za su iya biyan ko nawa ne su fanshi zuciya. Shi ne na ce bari in kira in ba ka cigiya, ko Allah zai sa a samu a cikin dan tak’in nan.”
Doctor Ashraf ya jinjina maganar. “Ka san it’s prohibited (ya sab’a ma doka) Doctor Sadeeq. Wancan din ma a boye aka yi komai, kodayake ka sani ai ba ka bukatar maimaici. Ina gudun zancen nan ya fita.”
Murmushi Doctor ya yi, “Ba zai taba fita ba sai idan kai ka fitar da shi Doctor Ashraf. Ko daga bangaren iyayen nata wannan zancen ba zai taba fita ba. Sirri ne a tsakaninmu. I promised.”
“To ba damuwa. In shaa Allahu za a samo musu. Amma ka fada musu za su tanadi naira miliyan talatin, ana samun zuciya su ba ni in ba su.”
A hands free da ma ya saka wayar suna ji. Cikin hanzari Mommy ta ce “Mun yarda za mu bayar, in dai hakan zai sa Mahboobahna ta warke.”
“In shaa Allahu kuwa.”
Daga nan suka yi sallama ya tsinke wayar yana kallon Aliyu. “To kun dai ji yanda muka yi da shi. Sai ku tanadi kudi, dan a kowanne lokaci zai iya kira na an samu, saboda sai idan an samu wanda suka yi accident ne da aka rasa danginsu, kuma sun mutu, to kafin tsayuwar bugun zuciyarsu ake gaggauta cirewa a yi dashen. Kun ga ke nan ko a yanzu zai iya kira na cewa an samu. Ku dai zama cikin shiri.”
Cikin kuka Mommy ta ce “in shaa Allahu za a kawo su nan da gobe likita. Wannan taimakon da kai mana ma mun gode sosai da shi.”
“Babu komai Hajiya. Sai kuma maganar rikon sirri. Sai da hadin kanku ne wannan sirrin zai rufu. Mu taru mu binne abun.”
“Babu matsala in dan wannan ne likita. Wannan halaccin da kuka yi mana kai da Doctor Ashraf, ko kadan ba za mu taba mantawa da shi ba. Kun taimake mu sosai Allah ne kadai zai iya biyanku.”
“Babu komai. Allah ya yi mana jagora, Ya sa a yi aikin nan cikin nasara.”
“Ameen Doctor. Thank you so much. To yanzu ya zancen sanya ta a coma din?”
“Kar ka damu, zuwa safe in Allah ya yarda duk za a yi wannan. Tun da an samu yanzu tana bacci, kafin ta farka za a saka ta. Kuna iya barin mutum daya a inda take, kafin safe zan dawo. Matata na labour ne ban san halin da suke ciki ba yanzu.”
“Haka ne. Babu damuwa to. Allah ya sauke ta lafiya.”Aliyu ya fada tare da mikewa.
Story continued…(Ci gaba)
Hawayen da ya tsatssafo mata ne ta share. Tana sakin hamdala a kasan ruhinta. Da yanzu no more Mahboobah. Sai dai wata ba ita ba.
Wayarta ta ji ta yi ringing, ta duba ta ga bakuwar lamba, hakan ya sa ta yi sallama hade da daukar kiran. Jin muryar dattijuwar mace ta amsa sallamar ya sanya ta cikin girmamawa ta gaishe ta. Mami ta amsa mata da sakin fuska.
“Na san ba ki gane ni ba. Mahaifiyar Ishraq ce.”
Da sauri Mahboobah ta sake gaishe ta tana yi tana sussunne kai.
“Ya Mamanku? Fatan tana lafiya. Dazu ne na ce da Ishraq ai ya ba ni lambarki mu gaisa.”
Kunya sosai Mahboobah ta ji ta lullube ta. “Ni ma na ce da shi ya ba ni taku, ya ce da ni zai turo amma bai turo ba. Duk sai na ji kunya fa Mama.”
“A’a babu komai ‘yata. Ai na san halinshi sosai, ni ma din don bai da yanda zai yi ne ya sa ya ba ni. Na kira ne mu gaisa. Za ki iya kira na Mami.”
“Okay Mami. Na gode sosai.”
“Babu komai. Allah Ya yi miki albarka. Ki gaida gida.” Daga nan ta tsinke wayar.
End of chapter
Hello sweethearts. Duk ya kuke ya kwanan gida? Ya lamurran yau da kullum? Fatan na same ku lafiya. To kun dai ji dalilin yi wa Mahboobah dashen zuciya, ko in ce kuna kan ji ba? Sannu sannu dai, kawunanku za su fita daga duhu😻
Masu daraja, taku gaisuwar ta daban ce. Hakika kuna darajta ni sosai ta hanyar dangwala ‘yar tauraruwar nan ta gefen haggu mai matukar kyau da dadin dangwalawa👌🏾😍ILY❤️
Princess Amrah
RAZ 2Flashback…June 2013 (Komawa Baya)
Cikin farin ciki take jera kaya a cikin jakar trolley dinta. Sassanyan murmushi take sakar wa kanta, tana ayyana tsantsar farin cikin da zai karu a zuciyarta yayin da ta yi arba da halittu biyun da idanuwanta ke matukar mararin gani. Sai kuma ta runtse idonta, hawaye mai gumi ya fito da karfin tsiya, ta sake bude idanuwan tana gyada kanta.
“Yah Nurah ko an yi aure yanzu?”
Ita ce tambayar da ta yi wa kanta a bayyane.
“Ban san sai yaushe Ameerah za ki zare soyayyar wannan Nuran daga zuciyarki ba. Ban san sai wane lokaci ba ne za ki gina sabuwar rayuwa ki gina wata soyayyar ba. Yau kimanin shekaru uku ke nan da rabuwarku da Nurah, amma har yanzu kin kasa zare shi daga duniyarki. Kin kasa tumbuke soyayyarshi daga zuciyarki. Ki daure Ameerah, don Allah ki daure ki ba samarin da ke dafifin kawo miki hari dama, watakila a cikinsu za ki samu wanda ya ninka Nurah duk wani abu da ya sa kike kaunarshi.”
Ta gyada kanta Ameerah, ruwan hawaye na zirara daga kwarmin idonta.
“Har abada Maryam. Har abada ba na tunanin zan iya samun wanda zai maye mini gurbin Yah Nurah. Soyayyarshi a jinin jikina take. Soyayyar Yah Nurah ta gama mamaye dukkan tsokar zuciyata. Da a ce zan iya zare soyayyarshi da tuni na zare ta, tun a lokacin da mahaifinshi qarara ya bayyana kiyayya gare ni, ya raba mana soyayyar da muka so ginawa, soyayyar da ta samo asali tun ina da kuruciyata.”
Maryam ta numfasa, ta dafa kafadar Ameerah, cikin rarrashi ta ce,
“Allah ba Ya kallafa wa bawa sai abin da zai iya dauka. Duk yanda kike son Nurah dolenki ki zare shi daga rayuwarki, ko don future dinki. So kike ki dauwama a haka babu aure?”
“Ban fada miki haka ba Maryam. Zare soyayyar Yah Nurah dai ce na fada miki ba zan taba iyawa ba. Infact, fadar in zare soyayyar tashi ma kara mini radadi yake a zuciyata. Ina jin dacin maganar, ina jin tamkar in tilasta miki tofar da yawu saboda rashin dadin zancen.”
Murmushi Maryam ta yi, ta saki kafadar Ameerah,
“To idan ba haka kike nufi ba, ta yaya za ki yi aure da dakon soyayyar wani gardi daban? Kina tunanin shi mijin naki zai juri wannan ne? Ko kuwa kina tunanin aurenki zai yi karko bayan kin yi shi ne kawai don ba ki da yanda za ki yi? Ki yi nazari sosai Ameerah. Ki tuna halin mazan yanzu. Babu mamaki ma shi din ya yi aurenshi yanzu haka yana cikin yanayi mai dadi da iyalinshi. Sai ke? Shekara uku amma babu wani ci gaba? Yanzu ko don su Abbah da Mama ba za ki saukaka ma kanki ba ki tumbuke Nurah daga zuciyarki?”
Ameerah ta gyada kai cikin hawaye ta ce,
“A duk inda Yah Nurah yake, na yi imani da Allah yana can cike da kewa ta, yana can yana tunanina, yana can ya kasa zare soyayyata daga zuciyarshi. Ni ba butulu ba ce Maryam. Ba zan iya daina tunanin mutumin da muka dauki tsawon lokaci muna gina soyayyar junanmu ba. Ba zan iya watsi da alkawarin da muka yi wa kanmu na kaunar junanmu ba duk runtsi duk wuya.”
“Shi ke nan Ameerah. Ki ci gaba da tufkar da ba ki da hanyar warwararta. Ki ci gaba da soyayyar da ba za ta yi leading dinki ga komai ba face tsantsar takaici.”
Daga haka Maryam ta fice daga dakin, ta bar Ameerah da bin inuwarta da kallo.
Cikin rashin kuzari ta gama hada kayanta. Ko powder ba ta shafa ba ta feshe jikinta da body spray sannan ta yana mayafin bakar abayarta. Ta fita a parlor ta samu Kawu Mukhtar a zaune da mug din coffee a hannunshi. Har kasa ta duka ta gaishe shi ya amsa mata da sakin fuska.
STORY CONTINUES BELOW

“Ba dai har an shirya tafiya ba.”
Ta saki murmushi.
“Ehh Kawu, ba na son yin yamma ne, muna ta jin labaran rashin kyan hanyar.”
“Haka ne.”
Kawu ya fada yana kurbar coffee dinsa.
“Toh Ameerah, na so dai a ce ba ranar aiki ba ne in kai ki da kaina, ko kuma in sa Ahmadu dreba ya kai ki, to amma babu dama yanzu haka Sokoto za mu tafi wurin wani aiki kuma tare da shi. Maryam kuma ba halin ta bi ki tana exams. Don Allah ki kula da kanki, kin ji ko?”
Ta jinjina kai hade da mikewa ta koma dakinsu. Akwatinta ta jawo ta fito, Kawu Mukhtar ya zaro dubu goma ya ba ta, hade da yi mata fatan alkhairi.
“Kar ki wuce wata guda din da kika ce, kin ga makarantarku ba za su juri fashin zuwa ba. Yanda suka ba ku hutun wata daya idan kika qara kin san sauran.”
“In shaa Allahu ba zan wuce haka ba Kawu.”
“Allah Ya yarda to. Ku tafi Allah ya tsare hanya.”
Da fadin ameen ta mike.
Har bakin hanya su Maryam suka raka ta, ta hau keke napep suna daga mata hannu har suka wuce, sannan su ma suka koma gida.
Tafiyar ba wata mai tsawo ba ce ba zuwa tashar Kawo, nan da nan suka isa, ta samu saura mutum biyu motar ta cika, tana zama sai ga cikon mutum daya an samu. Babu bata lokaci aka bukaci kowa ya biya kudin motarsa sannan suka kama hanyar barin garin.
Ear pierce ta jona a wayarta tana sauraron suratul yaaseen da qira’ar Shaikh Maheer, tana bi a hankali.
Ji ta yi an dan taba ta, ta juya ga ta kusa da ita hade da zare kunne guda na ear pierce din nata.
“Don Allah ki ba ni aron wayarki in kira mai gidana, Zaria zan sauka kuma ga shi har mun kusa isa, kar mu je bai kai ga isowa ba.”
Murmushi ta yi Ameerah, ta mika wa matar wayar.
“A’a ga lambar dai ki saka ki kira mun shi. Ni kam ina na iya wayar ma.” Ta sakar mata murmushi. Murmushin ta yi ita ma Ameerah ta karbi takardar ta saka lambar wayar sannan ta latsa kiranshi. Bugu biyu ya dauka sannan ta mika ma matar wayar. Ba ta wani jima ba ta mika ma Ameerah wayar cewa ta gama.
‘Tana ta farin ciki za ta ga mijinta. Allah sarki!’
Maganar da Ameerah ta yi ke nan a zuciyarta hade da gyada kanta tana jin hawaye na sauka a bisa kumcinta. A take kuma ta hau tariyar kalaman Maryam.
‘What if zancen Maryam ya tabbata cewa Yah Nurah ya yi aure?’ Ta share hawayenta. ‘Ko ka yi aure ba zan taba daina son ka ba, har abada Yah Nurana. Allah ne Ya jeho ka a rayuwata kuma Shi Ya san hanyar da zai fitar da kai daga zuciyata. Na bar komai gare Ka mahaliccin Ameerah da Nurah…’ Ba ta kai karshen zancen ba ta ga komai yana juye mata, tamkar a cikin bacci ta ga mota na tumbling da su. Tun daga nan ba ta kara sanin komai ba.
A warwatse fasinjojin motar suke, dreba kuwa ya manne a jikin sitiyari ya kone kurmus, tamkar gunki haka ya koma. Mutane zagaye da su, wasu na kuka, wasu cike suke da jimamin wannan mummunan hadarin da babu alamun akwai mai sauran nunfashin da za su fita daga cikinsa.
STORY CONTINUES BELOW

Daga can gefe suka hango Ameerah da fuskarta ta gama yin dameji, sai dai jin yanda take jan nunfashi da karfi ya sa wani mutumi fadin “Jama’a ku zo ga wata mai rai.” Ya sake jiyo nishin wata ‘yar yarinya ita ma.
A take suka taimaka aka ciccibi Ameerah da wannan yarinyar, domin ba su taimakon gaggawa.
“A Kai su Zaria ko kuma a koma da su Kaduna?”
“A’a Zaria dai ita ce kusa.” Wani daga cikinsu ya fada.
“Ina ga kamar dai gwara a tafi Kaduna da su, tun da daga Kadunar suke da ma, za a fi gano danginsu.”
Jakar Ameerah da ke kusa da ita suka duba, wayarta na ciki tun bayan da matar nan ta gama waya da mijinta ta mayar a ciki, suka duba last call, number suka gani aka latsa kira. Mijin waccan matar ne, bayan ya dauka suka masa bayanin abin da ya faru, sannan suka ce ga biyu daga cikin motar nan suna da sauran rayuwa sun koma Kaduna da su. A maimakon su yi scrolling su gano sunan wani, sai ba su yi ba. A tunaninsu tunda sun fada ma wani ai shi ke nan. Sai suka share kawai.
General hospital suka nufa da mutane biyun masu rai, tare da gawawwakin wadanda suka mutu. A accident and emergency aka karbe su, cikin azama likita da wasu daga cikin malaman jinya suka hau kansu, sai dai a rashin sa’a, ba a dauki wani dogon lokaci ba duk su biyun ma suka mutu.
*Rest In Peace Ameerah😭*
Hada su aka yi da sauran gawawwakin, inda aka hau bada cigiyarsu, ko akwai wanda ya san su, sai dai shiru har dare, ga shi fuskoki kusan duk sun dame, ba lallai a kalle su a gane ba.2
Kasantuwar a hannun Doctor Ashraf suke ya sa ya bada izinin a kai su mutuary dan kar su fara wari, shi kuma ya zagaye daga baya, tare da hadin bakin wasu nurses ya dauki gawar Ameerah, ya nufi wurin Doctor Sadeeq da ita.
Doctor Sadeeq!
“Alhamdulillah! Gaskiya na ji dadin samun zuciyar nan a kan lokaci Doctor Ashraf. Ka kyauta sosai ka yi jihadi, don yanzu haka Mahboobah na cikin coma, da ma kai kadai muke jira. Ga kudinka.”
Ya dauko wata bakar jaka daga can karkashin teburinshi, ya sada ta ga Doctor Ashraf.
“Ga kudinka Doctor, cash ne. Da na ce da su su kai maka banki, to kuma dai na jira har sai an samu zuciyar. Tun da an samu yanzu za a ba ka half, har sai an dasa zuciyar an ga yanayin lafiyarta sannan a ba ka sauran. Lafiya ai hakan ko?”
Kai ya jinjina Doctor Ashraf.
“Haka ya yi abokina. Ka yi gaggawar zuwa a cire tun kafin ta tsaya da bugawa.”
“Sai after 24 hours da mutuwar yarinyar sannan zuciyarta za ta daina bugawa. Yanzu ta yi hour nawa da mutuwa?”
“Tun da rana ne dai aka kawo ta, ana kawo ta din kuma ta cika. That’s pass 3pm.”
Doctor Ashraf ya ba shi amsa.
“Okay muna da sauran lokaci. Amma dai duk da haka we have to hurry. Bari in kira in shaida musu. Ka dauki kudin nan 15M ne. In shaa Allahu za a cika maka sauran, as soon as an tabbatar da lafiyar zuciyar after the transplantation.”
“No problem Doctor. Bari in tafi. Allah ya sa a yi aiki cikin nasara. Ga wannan kwafi ne na ID card din yarinyar da aka cire wa zuciyar, saboda watan-watarana, ba fata muke ba.”
“Ka yi tunani mai kyau Doctor Ashraf, thank you once again.”
“Ni ma na gode abokina.”
Daga haka ya fita daga Office din Doctor Sadeeq, shi kuma ya latsa kiran Aliyu.
“Ko me kuke ciki ku hanzarta zuwa, an samu zuciyar yanzu zan yi aikin cire ta, kafin ku iso in shaa Allahu na gama. Idan kun zo ku jira ni a Office, zan bar makullin a wurin masinjana, zan shiga theatre room yanzu.”
“Okay Doctor, ga mu nan zuwa yanzu in shaa Allah. Thank you so much. Mun gode sosai.”
Cikin minti talatin Doctor Sadeeq ya cire zuciyar Ameerah. Ko da ya dawo Office ya samu su Mommy zaune sun yi jigum-jigum suna zaman jiran shi.
“Ni dai likita am afraid, Allah ne shaida na. Ina jin faduwar gaba sosai. Ina jin sabuwar tashin hankali na kunno kai a duniyata. Doctor ba zan rasa ‘yata ba a wurin aikin nan?”
Ajiyar zuciya Doctor Sadeeq ya sauke. Ya ce,
“Ba zan boye miki komai ba Hajiya, amma akwai risks da za a iya haduwa da su. Kin san a komai na duniya akwai advantage akwai kuma disadvantage (Amfani da rashin amfani). To heart transplant ma yana da nashi disadvantages din, kamar, infection, zubar da jini during or after the surgery, Blood clots that can cause heart attack, stroke, or lung problems, matsalar numfashi, kidney failure, failure of the donor heart, and sadly…”
Ya dan yi shiru yana taunar lebenshi, kafin ya ce,
“…death (mutuwa).”
Mommy ta zabura ta mike tsaye tana jin sabon hawaye na zarya a bisa kumcinta.
“Yo Doctor cewa za ka yi dai dashen zuciyar bai da amfani.”
“Calm down Hajiya. Sosai dashen zuciya yake da amfani musamman ga Mahboobah da ke da sauran kuruciyarta. Disadvantages ko in ce risks din ne na fada miki. Ba na son boye muku gaskiya ne shi ya sa na fada. Saurara kuma ki ji amfaninshi.”
Ta koma ta zauna tana share hawayenta.
“Idan aka yi wa mutum dashen zuciya, zai iya reducing risk of heart diseases sannan kuma ya kare high blood pressure, high cholesterol, and diabetes by adopting a healthy lifestyle. Most people can return to work or normal activities and have good quality of life after a heart transplant (Da yawa suna komawa ayyukansu na yau da gobe bayan an yi musu dashen zuciya).”
Da jin haka sai Mommy ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, ko ba ta fada ba ya san ta gamsu da bayananshi, ta kuma samu nutsuwar ruhinta. Shi ya sa da ya tashi sai ya fara da fada mata risks din ciki kafin ya zayyane mata alfanunshi.
“Yanzu ga form nan za ku cike shi kafin a shiga aikin. Helpers dina suna can suna jira.”
Aliyu ne ya karba ya cike form din, kafin ya mika shi ga Doctor Sadeeq, yana jin rashin kwarin guiwa a tattare da shi, tausayin ‘yar uwarshi na dad’a bunkasa a birnin zuciyarshi.
End of chapter
Hello…good day my beautiful people. I know a lot aren’t happy but am sorry, ya zama dole Ameerah ta mutu kamar yanda na tsara labarina. Zuciyarta ce a tsakanin Kirjin Mahboobah. Ta mutu cike da kaunar Nuranta, tana kan tunaninshi. Tsananin kaunar da take wa Nurah ce ta fada kan Ishraq Sulaiman bayan zuciyarta ta koma ga Mahboobah. Bai zama lallai sai Nurah ne za ta so ba. Akwai dai soyayyar mutum daya a zuciyar Ameerah, wacce Mahboobah ta tsinta a lokaci guda bayan yi mata dashen zuciyar Ameerah. Ta fada a kan Ishraq Sulaiman duk da ba ta taba ganin shi ba, sai dai ta san akwai shi, fuskarshi ce dai ta zamo bakuwa a gare ta! Fatan masu karatu sun fahimce ni.
Tighten your belts, this is just the beggining.
Keep voting, keep commenting, and keep sharing with family and friends.
Princess Amrah
RAZ 2Story continued…(Ci gaban labari)
Cike da nutsuwa yake tukin motarsa, madaidaicin gudu yake yi, yana saita kallon shi ga tukin da yake yi. Jin wayarsa na ringing ya sa ya rage gudu, yana duba sunan mai kiran nashi.
“Hello Khaleed.”
Ya fada bayan ya dauki kiran.
“Ango ka sha kamshi.”
Khaleed ya fada cikin zolaya.
“Khaleed Zannah Abdullahi. Wato kai dai idan ba ka yi tsokana ba ba ka taba jin dadi.”
“Karya na yi kai ba angon ba ne?”
“Fadin kalmar ango ne kawai dalilin da ya sa ka kira ni?”
“Allah Ya ba ka hakuri. Ba shi ba ne. Gani na yi lokaci na tafiya duka bai fi sati uku ya yi saura ba a yi aurenku, amma har yanzu babu wata magana daga gare ka dangane da shirye-shiryen biki.”
Ishraq ya numfasa.
“Wane shiri zan yi Khaleed? Ko ka manta cewa ba auren soyayya ba ne zan yi? Ai shiri ana yin sa ne ga auren da ango yana so amarya ma tana so. To ni kam a nawa bangaren babu ko dison soyayyar amaryar a zuciyata. Ban ga amfanin shirin da zan yi ba. Ita dai da take so sai ta yi.”+
Daga inda Khaleed yake ya gyada kai.
“To tun da ka san cewa ita za ta iya yin shirin ai kuwa ya kamata ka mata adalci Ishraq. Ba fa ita ta tilasta maka aurenta ba, kai ka ji za ka iya. Don haka ka yi tunani da kyau, ka fidda mata hakkinta domin Allah.”
“Khaleed. Kana zancen wani hakki, wai mene ne ba a yi mata ba? Jiya-jiyan nan Mami ta kira dangin mahaifina da nata suka kai lefe tare da kudin dinki naira dubu dari. Kuma lefen nan duk daga account dina na bayar da kudin da aka hada shi over 2 million naira. To kuwa wane hakki ne ya rage gare ni wanda ban sauke mata ba da kake yi min waazi?”
Murmushi Khaleed ya yi,
“Ba wannan hakkin nake magana ba Ishraq. Biki ne na budurwa ba na bazawara ba. Kai ko zawarawan ma yanzu sun waye suna dan yin abubuwa ga bikinsu. Na tabbata Mahboobah na da bukatar ji daga gare ka, tun daga kan kudin su saloon, lalle da gyaran jiki. Sannan akwai bukatuwar a ji ko suna da raayin yin wani event. Ga wannan make up na zamani shi kanshi wasu kudade ne masu zaman kansu. Ko ni da na yi aure shekara biyu da suka wuce na ji a jikina ga wannan bangaren, bare ku yanzu da komai yake kara ta’azzara.”
Bayyanannen tsoki Ishraq ya yi,
“Wannan duk shirme kake fadi Khaleed. Ni har yanzu ban ga wani abu ba mai muhimmanci a maganarka. Duk bidi’a ce kuma ni babu wanda zai yi mun wata bidi’a a bikina. Kawai a daura aure shi ne wajibi, a kai amarya kowa ya watse. Khalas.”
Tsokin shi ma ya yi Khaleed.
“Tun da nake a rayuwata ban taba ganin mutum irinka ba Ishraq. A ce mutum kaifi daya wanda ba ya daukan shawara. Ni idan ba za ka musu ba zan yi musu bakin gwargwado iya karfina, in shaa Allahu.”
Daga haka ya kashe wayar cike da takaicin hali irin na abokinshi.
*
Ta yi bayyanannen tsaki hade da tabe bakinta tana kallon Saleemah.
“Kya gama tsakinki ma yarinya, don ba za mu lamunci biki gaya babu miya ba. Ba ta yiwuwa duk yanda muke alfahari da bikin nan muka ci buri da shi amma ki ce wai ba za mu yi kowanne irin event ba.”
Haneefa ta harari Saleemah.
“Lallai ma a gaishe ki da tsayawa dogon zance. Ai ni ba ni ma da lokacin batawa wurin mayar mata da amsa. Ko tana so ko ba ta so sai mun yi casu da izinin Allah.”
STORY CONTINUES BELOW

Cikin marairaicewa Mahboobah ta ce,
“Wai ku kuna manta waye angon nan ko? Shin wai ko na amince kuna tunanin Ishraq zai yarda a yi ne? Ba so na yake ba. Na tabbata ko don ya ba ni haushi zai iya yin mirsisi ya ce ba da yawunsa ba.”
“Ke kika san wannan MB. Mu dai ba za mu nemi ko sisinshi ba. Ba kuma za mu tilasta mishi dole sai ya je wani event namu ba. Ke din dai ce tamu kuma ke muka isa da ke ko bakya so mu tilasta miki.”
“Take it easy Hanee. Ni fa ban ma yi maganar da shi ba bare in san zai hana ko ba zai hana ba.”
“Oho dai, ai ke kika fada shi ne nake miki kandako. Ko da ma zai fara hanawar ki fada masa aminnanki sun ce dole sai sun yi.”
Saleemah ta kai mata dukan wasa.
“Ban taba ganin mutum irinki ba Hanee. Kina so ki fifita aminnanta a kan mijinta ne fa.”
Duk su duka suka kwashe da dariya. Wayar Mahboobah ce ta yi ringing, ta duba ta ga bakuwar lamba ce. Ta daga hade da sallama a bakinta. Amsa sallamar ya yi, suka gaisa cikin aminci.
“Sunana Khaleed Zannah Abdullahi. Dan uwa kuma babban aminin Ishraq Sulaiman.”
Da jin haka sai ta qarisa sakar masa fuska, suka kara gaisawa faran-faran tamkar da ma sun san junansu.
“Na kira ne in ji abubuwan da kuke da bukata. Sannan kuma idan kuna da shaawar wani event kar ki ji komai ki fada mun. Da ni da Ishraq din duk daya ne.”
Ta rasa abin da za ta fada mishi. Tana so, sai dai tana gudun ban-kunyar da Ishraq zai iya yi mata a bainan-naasi tunda ba son ta yake ba. Jin ta yi shiru ya sa Khaleed fadin,
“Don Allah kar ki ji komai Mahboobah, ki fada mun duk abin da kuke so, in shaa Allahu ba zai gagara ba.”
Dakewa ta yi, ta dan numfasa kafin ta ce,
“Ba za mu yi komai ba Khaleed…”
Ba ta kai aya ba Haneefa ta fizge wayar daga hannunta. Ba ta sani ba da ma sun kasa kunne suna sauraren duk maganar da Khaleed Zannah ke yi. Jin ba za ta iya daurewa ba Haneefa ya sa ta ga gwara kar ta bari Mahboobah ta cuce su, kawai ta fada mishi zahirin gaskiya.
“Barka da rana Mallam Khaleed.”
“Yauwa barka.”
Ya mayar mata da amsa.
“Ka san Mahboobah na da jin nauyi da alkunya. Yanzu haka kan zancen da muke ke nan sai ga kiran ka ya shigo mata. Tana da raayi, mu ma kuma muna da raayi Khaleed. In dai da hali muna son event ko da guda daya ne, ba lallai sai da ango ba. Akwai events da ake yi yanzu na mata zallah, kuma a yi nishadi sosai. So please in zai samu shi din muke so. Haneefa ce kawarta.”
Murmushi Khaleed ya yi bayyananne.
“Babu komai Haneefa, in shaa Allahu ba zai gagara ba. Kamar nawa za ta wadace ku?”
Shiru ta yi Haneefa tana nazari. Kafin ta samu cewa wani abu ta ji ya ce
“Kuna da bukatar nutsuwa sosai ku yi calculation. Bari in kashe, idan kun gama sai a tura mun total ko ta text message ne. Duk abin da kuke so ku ringa nema na a waya ku fita batun Ishraq, wannan miskilin ba za ku iya shaani da shi ba.”
Haneefa ta yi murmushi,
“To in shaa Allahu Khaleed. Mun gode sosai. Sai ka ji mu.”
Daga haka ta kashe wayar tana sakin dariya suna tafawa ita da Saleemah. Mahboobah dai shiru ta yi tana gyada musu kai alamun sun zautu. Sai da suka yi mai isar su sannan Haneefa ta ce
STORY CONTINUES BELOW

“Yo gani na yi kina neman cutarmu MB. Ta yaya muna son abu amma tsoro ya hana ni bayyana muna so? Allah kuwa ki canja hali ba a haka. Kina wannan sumu-sumun sai an raina ki da yawa. Shi namiji kin zabure mishi ma ya aka kare bare kuma kina nuna salihanci.
“Kanki dai ake ji kuma. Yanzu dai tunda kin gama aikin sai ki shafa mun lafiya.”
“Saleemah me ya kamata mu yi ne?”
“Kamu ko kunshi?”
Da sauri Haneefa ta ce
“Yauwa, kunshi dai. Kin ga ai kamu ma suna iya tunanin za mu bukace su. Amma idan muka ce kunshi an san event din mata zallah ne.”
Suka tafa hade da shewa suna kallon Mahboobah. Mahboobah ta tabe baki tana kai kankana a bakinta.
Bayan sati biyu
Shirye-shiryen aure sun kankama, yayin da duk bangaren biyu ake ta hada-hadar tarbar wannan kayataccen biki.
“Mommy don Allah ki bar ni yau in fita, wallahi ina da uzurirrika wanda dole sai da kaina ne zan yi su.”
Mommy ta gyada kanta tana ci gaba da shirin kayanta a wardrobe.
“Babu inda za ki je Boobah. Ki duba ki ga yanda fatarki ta yi kyau take sheki. Sannan kuma kike neman ki shiga rana duk ki bata gyaran da aka dauki mako guda ana miki?”
Cikin shagwaba Mahboobah ta ce
“Don Allah fa Mommy. Ai a mota ne kuma ni zan ja motar ma. Ba zan shiga rana ba.”
“Wai shi wannan uzurin wane iri ne wanda Haneefa da Saleemah ba za su iya yi miki shi ba?”
“Ni dai please Mommy…”
“To na ji.” Mommy ta dakatar da ita. “Ki shirya ki tafi amma kar ki jima ba ki dawo ba. Ki tabbata kafin laasar kin dawo saboda kar Layuza mai gyaran jiki ta zo ba ta same ki ba. Ga shi yau ne za a yi miki gyaran karshe.”
Cikin murna ta mike tsaye ta dafa Mommy
“Yauwa Mahaifiyata na gode.”
Daga haka ta fice daga dakin hade da nufar dakinta. Mayafinta ta yafa sannan ta rataya hand bag, ta je dakin Fareedah ta same ta tana FaceTime da kawarta Aishatu.
“Reedah barin FaceTime din nan za ki yi ki zo ki raka ni T&T.”
Reedah ta juyo ta kalle ta da murmushi a saman fuskarta.
“Me za mu yo a can?”
“Kina da son jin zance. Ni dai ki taso mu tafi Mommy ta ce kar in dade.”
“Aishatu bye. A yi karatu sosai best of luck.” Ta kashe wayar ta zira jilbaab dinta.
Mukullin mota Mahboobah ta dauka, ita ke driving Fareedah zaune a kujerar mai zaman banza. Bayan ta fitar da motar daga gate sun hau bisa titi ta ce
“Ina son na nemo abu mai muhimmanci ne wanda zan ba Hanee da Sally gift.”
Dariya Fareedah ta yi
“Haba dai Yah Boobah wa ya fada miki amarya ita ke ba friends dinta gift? Su ne ma fa za su ba ki.”
Idonta kyam a kan titi ta ce
“Ai ba dole sai yanda kowa yake yi ba ni zan yi. A matsayin fa souvenir ne tun da na san ba samun komai za su yi ba gwara in nema musu abu mafi cancanta in ba su.”
STORY CONTINUES BELOW

“Haka ne kuma.”
Daga haka suka yi shiru har suka isa T&T din. Nan fa suka hau dube-dube, sai ruwan ido suke sun ma rasa abin da za su zaba. Daga karshe dai Mahboobah ta dauko musu wani setin teddy mai hade da mug a cikin kwali mai madaidaicin girma. Ta dauki guda biyu Haneefah daya Saleemah daya.
“Wai ki rasa abin da za ki basu sai teddy. Tirr wallahi.”
Fareedah ta fada tana dariya.
“Ehh din ina ruwanki friends dinki ne ko nawa? Ai don na san sai sun fi son wannan gift din a kan komai shi ya sa din na zabar musu. Kuma ke aikin banza ce tun da ga shi nan tun dazu kin kasa zabar musu komai.”
“Uhm Allah Ya ba ki hakuri ni dai.”
Suka nufi wurin biya Mahboobah ta bada ATM dinta aka cira ta POS sannan suka tafi. Daidai za su shiga mota suka ga wata mota za ta gitta a kan titin, Mahboobah ta hada ido da Ishraq da ke zaune gefe, Khaleed na tukawa. Sun dauki kusan minti daya sai ga su sun yo reverse a lokacin har Fareedah ta shige motar ta bar Mahboobah tsaye tana jin wani yanayi a tattare da ita. Ta jima ba ta gan shi ba. Rabon da ta yi tozali da fuskarshi an dauki dogon lokaci. Hakan ya sa lokaci kadan ta ji kaunarshi ta dad’a tsuma a cikin zuciyarta.
Bai fito daga motar ba sai Khaleed ne ya iso wurinta da murmushi kunshe a fuskarshi. Ta gaishe shi ya amsa mata da sakin fuska.
“Khaleed. Right?”
Ya daga mata kai.
“Ya aka yi kika gane?”
“Haka kawai jikina ya ba ni kai ne.”
“Allah sarki. Sannu ko. Har mun wuce ai Ishraq yake fada mun ke ce, na ce lallai sai mun dawo an gaisa. Kin ga isasshen can bai ga daman fitowa ba.”
Ta saki murmushi bayan ta kai dubanta gare shi.
“Eyyah babu komai Khaleed. Ka ga ni ma gift ne na zo na siya wa friends dina muna shirin tafiya gida ke nan. Don Mommy ta ce kar mu jima.”
“Allah sarki. To ga wannan ku kara ku siyi wani abu.”
Ya zaro dubu ashirin ya mika mata. Fa-fur Mahboobah ta ce ba za ta karba ba. Da kyar dai da jibin goshi ya samu ta karba sannan ta mishi godiya ta shiga mota.
*
“Kai kam kana da matsala Ishraq. Wai yanzu ka leka din ku gaisa ne abun duniya ya faskara? Anya kuwa za ka iya zaman aure da innocent Mahboobah?”
“Mtswww! Wai innocent. Ai shi ya sa take wani shiru-shiru na mufanurci da ma don a ce mata ta kwarai. Haka Mami sai faman yabon ta take yi kawai daga yin waya. Ni fa ban ga mace ta kwarai ga duk yarinyar da ta iya tallar soyayyarta ga namiji ba. Har abada bata da kima a idona. Ba zan taba son Mahboobah ba kamar yanda ba za ta taba zama mai kima da daraja ba a idanuwana.”
Gyada kai Khaleed ya yi yana tsananin jin tausayin Mahboobah. Haka kawai daga haduwa da ita sai ya ga mutuncinta. In ma ban da kaddarar soyayya, me zai sa kyakkyawar yarinya mai ji da kuruciya kamar Mahboobah ta like ma Ishraq yana wulakanta ta.
“Ishraq har yanzu lokaci bai kure maka ba. Don girman Allah in dai ka san zaluntar yarinyar nan za ka yi kar ka aure ta. Ina guje maka fushin mahalicci. Kar ka karbi amanarta amma ka kasa rike ta tsakaninka da Allah. Wallahi matukar ka zalunce ta Allah ba zai taba kyale ka ba.”
“Khaleed Zannah, ba zan janye auren Mahboobah ba. A yanda Mami take cikin tsananin kaunar yarinyar matukar na tinkare ta da wannan zancen na tabbata tana iya tsine mun albarka. Kai ba ka san yanda Mami ta dauki abun nan da girma ba ne. Ni wallahi duk na tsani kaina ma, na tsani auren nan, har sunan Mahboobar ma ba na son jin an ambace shi.”
“Lallai kuwa akwai matsala mai girma. Ba ka son a ambaci sunan wacce za ka aura ku zauna a karkashin inuwa guda? Allah ya kyauta to.”
End of chapter
Assalamu alaikum warahmatullah. Barkanmu da wannan lokaci. Ya kuke ya gida ya iyali? Fine in shaa Allah.
Shirye-shiryen aure fa suna ta kankama. Ga ango ya tsani ko jin sunan amarya. Ga kuma amarya ta ci alwashin yin auren zaman bauta kawai. Ko ta yaya rayuwar aure za ta yi kyau babu ko dison soyayya a cikinsa?😤 I pity you Boobah.1
HML in addy Ma’ish2020😅❤️
Princess Amrah
RAZ 2Ya yi tsoki ya fi a kirga, Khaleed na jin shi amma ya mishi banza. Jin Khalid ya ki tanka mishi ya sa shi fadin
“Wai mallam ba za ka tambaye ni damuwa ta ba ka wani yi mun zuru kamar wanda ya warke daga makanta.”
Dariya Khaleed ya yi ya ce,
“Na ki in tambaya din. Kai karamin yaro ne da kullum sai ni ne nake tambayar ka matsalarka? Idan ka ga dama ka fadi ina sauraron ka.”
“Mtswww! Nonsense friend.”
“Whatever dai ba zan tambaye ka ba.”
Kamar ba zai fadi ba sai kuma ya daure ya ce
“Ina ta tunanin ta yanda zan yi rayuwar aure da wata ne bayan Ameerah. Khaleed, har ga Allah ni dai zuciyata Ameerah take so. Ina bukatar Ameerah ta mallaka mun zuciyarta, sai dai ta yaya? Ta yaya Khaleed? Mami ta mun katangar karfe da neman Ameerah. Ba zan gajiya ba in don ta ni ne. Duk wuya duk rintsi zan neme ta. Amma Mami ta hana. Ni kuma na kasa cire ta daga zuciyata. A kullu yaumin soyayyarta dad’a ninkuwa take a birnin zuciyata.”
Khaleed ya dafa kafadar Ishraq. Cikin rarrashi da kwantar da murya ya ce
“Soyayyar nan da kake ma Ameerah ita za ka yi kokarin mallaka ta ga Mahboobah. Na sani ba ka son ta amma ka jure, matukar ka sanya hakan a ranka sannu a hankali zuciyarka za ta kamu da kaunar Mahboobah.”
“Ba zan iya ba. Ba zan iya mallaka soyayyar Ameerah ga Mahboobah ba Khaleed Zannah. Anya kuwa ka san so? In har ka san miye so ko kadan ba za ka taba tunanin tsuntsun soyayyar Ameerah zai fada a kan wata mace can daban ba, musamman Mahboobah da na gama rainawa, nake dauka macen da duk duniya babu mara aji sama da ita.”
Gyada kai ya yi Khaleed Zannah, yana daidaita tsayuwar hannunshi da ke saman kafadar Ishraq.
“Ba zan fasa fada maka ba Ishraq, har yanzu lokaci bai kure maka ba. Don girman Allah ka janye batun auren Mahboobah in ba za ka iya ba. Kar ka wahalar da yarinyar mutane.”
“Haka ni ma din ba zan fasa fada maka ba zan janye auren Mahboobah ba.”
“Saboda ita ce rufin asirinka a yanzu ko?”
Ishraq ya daga mishi kai.
“You see! Ita ce rufin asirinka Ishraq, amma kai ba za ka zama rufin asirinta ba, ba za ka iya gwada mata soyayya daidai da kwayar zarra ba ko don farin cikinka da ta saita na tsakaninka da Maminka. Me ya sa? Uhm, me ya sa Ishraq?”
“Saboda ba na kaunarta.” Ya ba shi amsa cikin sanyin murya.
“Hmmm! To shi ke nan Ishraq. Ba dai zan gajiya ba. Ba zan fasa fada maka gaskiya ba ko da a ce hakan zai sa ka nemi mashi ko takobi ka daba mun.” Ya sauke hannunshi daga kafadar Ishraq. “An ce za su yi wani program ko kunshi ko sa lalle na mance dai. Suna da bukatar motoci.”+
Wani irin wawan kallo ya bi Khaleed da shi. Cikin bacin rai ya ce “To yanzu me kake nufi?”
“Ka san me nake nufi ai. Ni dai motata daya tal ka sani. Ka kira sauran friends dinka ni ma zan kira friends dinmu na bangarena. A taru a rufa wa juna asiri.”
“Rufin asiri? To da asirin waye a bude? Look, Khaleed Zannah. Ni babu wasu da zan kira in yi requesting mota a wurinsu. Kai da ka ji za ka iya sai ka yi. Bari in tafi. Ka fada wa Maman Junior na wuce.”
STORY CONTINUES BELOW

“Au haka ne? Babu komai je ka. Allah ya shirya ya ganar da kai gaskiya.” Ko rakiyar da ya saba yima Ishraq din bai yi ba a yanzu sai tufka da warwara yake yi.
Thursday 5:00pm
Kallon kanta ta yi a dressing mirror, from head to toe, ko ba a fada mata ba ta san ta yi kyau, kyau kuma na asali, wanda ya amsa sunanshi. Ta sakan ma kanta murmushi, tana jin babu ya ita a duk duniyar ma. A yau ita ce za ta auri Ishraq Sulaiman, muradin zuciyarta.
“To sarkin hanzarin mikewa, komawa za ki yi ki zauna a dauke ki hotuna, don na san da zarar kin fita nan ba samun yin hotunan kirki za a yi ba.”
“A’a bar ni Hanee. Gwara in kalli kaina sosai in kara.”
“To idan aka yi miki hotunan ko bayan biki ba sai ki ringa kallo ba kina jin dadi.”
“Kuma fa haka ne Sally.” Ta koma ta zauna, mai hoto da mai make up suka ci gaba da daukarta hoto. Ta yi matukar kyau cikin shigarta red colour. An daura mata head an dan ja shi da baya, kyakkyawar sumarta ta dan bayyana.
6
Karfe biyar da rabi motoci suka fara zuwa kofar gidan. Khaleed ya kira Haneefa ya shaida mata, a take kuwa ta fara fitar da mutane kai tsaye aka doshi Syde Ressort da su inda za a yi program din.
Budadden fili ne inda aka kawata shi sosai, ya ji decoration na gani na fada, kalar red shi ma. Hanyar shigowar ta sha ado sosai, kai ka ce ba hannu ba ne ya shirya shi.
2
Sai kuma wurin zaman amarya da kawayenta shi ma ya ji ado. A tsarin wurin na zaman amarya da ango ne, sai gefe abokin ango guda kawar amarya guda. To kasantuwar program din na mata ne kawai, sai suka bar shi a kan cewa amarya da kawayenta ne za su zauna. Ita a tsakiya sai Haneefa da Saleemah gefe gefe.

STORY CONTINUES BELOW

Wannan event ba karamin burge mutane ya yi ba. Babu maza sai masu DJ da masu hoto. An ci an sha an gwangwaje. Amarya ta cashe sosai ita da kawaye da danginta. Babu wanda zai je wurin ya dauka cewa angon ba ya son amaryar. Saboda duk wani abu da aka yi wurin na girma ne, ko kadan babu kankanta a ciki. Kuma dangin ango ma sun je an yi shagalin tare da su. Karfe bakwai da rabi aka gama kwasar kowa da ke wurin.
A gidan Aunty Shafa kanwar Mommy suka zarce kamar yadda suka tsara. Kasantuwar gidansu ya cika sosai da yan uwa da dangi, ba za su ji dadin zaman sosai ba. Fareedah ce ta koma gida ta kwaso musu komai nasu.
Washe gari mother’s eve ne za a yi wanda Mommy da kawayenta suka kirkira. Karfe biyar amarya ta iso gidansu. Nan ma wani adon ne aka sha. Kowa ya ji dadi a karshe aka watse cike da farin ciki.
Ranar asabar da safe suka tattara komai nasu suka koma gidan su Mahboobah. Karfe sha daya na safe daruruwan mutane suka shaida auren Ishraq Sulaiman da amaryarsa Mahboobah Bukar a kan sadaki naira dubu dari.
Aliyu ne ya kira Mahboobah ya shaida mata an daura aure sai ta zuba ruwa a kasa ta sha. Ba ta ko tsinke wayar ba ta saki kukan farin ciki. Sai dai a lokaci guda zuciyarta ta karye. Ta tsinci kanta a wani irin mawuyancin hali da ita kanta ba ta san yanda za ta fassara shi ba. Ba ta san a wane yanayi take ba ko na farin ciki ko bakin ciki. Ita dai abin da ta sani shi ne, ta shirya tarbar kala-kalar wulakanci daga wurin Ishraq Sulaiman.
“To shi kukan kuma na mene ne?” Haneefa ta fada a daidai shigowarta dakin. “Ki je ki yi nafila ki mika godiyarki ga Allah madaukakin Sarki tare da fatan zaman lafiya mai dorewa a rayuwar aurenki. Sannan mu ma ki roka mana ehem ehem! Ba sai na karisa ba.”
Duk yammatan da suke dakin suka dauki shewa ana cewa an gano ta. Alwalla Mahboobah ta dauro, ta saka hijabinta dogo har kasa ta kabbara sallah. Rakaa biyu ta yi, ta yi addua sosai kafin ta mike. Mai make up na zaune tana jiran ta da ma. Don haka ta kokarta saisaita kanta, hawayen da ke ta ambaliya a fuskarta ta samu ta share shi.
“Amarya idan ba ki daina kukan nan ba kwalliyarki ba za ta taba yin kyau ba.” Zinnie Smart Mai kwalliya ta fada tana kokarin bude make up kit dinta.
Murmushi kawai Mahboobah ta yi don bata san cewa har a lokacin tana hawaye ba. Wayarta ce ta yi ringing tana dubawa ta ga Ishraq. Cike da mamaki take kallon wayar tana son gasgatawa har ta tsinke.
“Ki dauka mana ba angon ba ne?”
Ajiyar zuciya ta sauke hade da dauka ta kara a kunnenta. Muryar Khaleed ta ji ya ce ga su nan zuwa tare da mai hoto a yi ma ango da amarya hotuna. Cikin dauriya ta ce “Ba a gama kwalliyar ba yanzu za a fara.”
“Eh ai mu ma din ba mu taho ba yanzu haka muna wurin reception. Na san in shaa Allahu kafin mu zo an gama. Ai dole mu jira amaryarmu a mata komai a nutse.” Ta saki murmushi bayan ta mishi sallama hade da ajje wayar.
“Wannan ango da zumudi yake.” Ta jiyo muryar wata kawarsu Zarah ta fada. “Ke ma dai kya fada Meenah. Ai angunan yanzu ba dai d’oki ba.” Rabi’atu ta fada. Duka aka dauki dariya.
Kimanin awa daya aka dauka ana kwalliyar, ba wata mai tsanani ba ce ba don ta ce simple make up take so. Amma a haka ta yi kyau sosai ta saka farar doguwar riga budaddiya sosai, aka daura mata turban shi ma fari tare da yafa mata hadadden veil silver. Jaka da takalminta duk silver ne. Nan fa aka hau tafawa ana jinjina kyawunta. Tana shirin kira ke nan sai ga shi Khaleed ya sake kiran ta da wayar Ishraq cewa ga su nan sun kariso gidan a ina za su hadu?
STORY CONTINUES BELOW

“Ku shigo ciki kawai zan turo Reedah ta kai
Ku parlon Daddy.”
Haneefa da Saleemah suka kama hannunta kai tsaye suka nufi dakin. Tare da ba sauran kawayensu hakuri cewa ba za su jima ba hotuna kawai za a ma amarya da angon.
Sun samu har angunan sun iso sun zazzauna. Ango Ishraq ya sha farar babbar riga da aka ma aiki ash. Hular kanshi ash ce da hadaddiyar Rado wristwatch silver colour. Ko kallon inda amaryar take bai yi ba, idonshi na kan wayar da yake latsawa. Cikin halin ko’inkula ya kalli Khaleed. Khalid ya gane manufarshi hakan ya sa ya ce da photographer din ya seta kayan aikinshi.
Da kyar da ma Khaleed ya lallaba shi ya yarda za a yi wannan hotunan. Sai da ya hada da sunan Mami ya san za ta yi farin ciki idan ta ga hotunan kafin ya amince.
Nan fa aka fara hotuna ba ji ba gani. Shi dai Ishraq ba ya so, sai dai bai da yanda zai yi dole ya ringa bin umurnin mai hoton yana aikata duk yanda ya ce ya yi. Duk da taba jikin Mahboobah da yake yi hakan bai sa ko dis ya ji wani abu a kanta ba. Bai taba jin alamun sonta ba hakazalika ba ya jin daidai da rana daya zai so ta. A ranshi yake ayyana zallar tashin hankalin da ta jefa kanta a ciki. Da ta sani ta daure ma soyayyar ko da hakan na nufin ajalinta. Ta debo ruwan kashe kanta don ba zai taba daina neman Ameerah Muhammad ba komai daren dadewa. Ya kuma dauki alwashin duk ranar da ya gano Ameerah a ranar zai rabu da Mahboobah ko da za ta mutu.
An gama hotuna anguna suka fara haramar tafiya. Wasu daga cikin abokan ango sai tsokanar Mahboobah suke wai ita da angon ba su jin kunyarsu sai tabe-taben junansu suke a hoto. Ita dai aikinta dariya ne Haneefa ce mai kokarin ba su amsa.
“In shaa Allahu karfe biyar na yamma motoci za su cika layin nan na daukan amarya.” Khaleed ya fada yana kallon Haneefa.
“Hmm uhmm wai ma har karfe biyar? Ni kam na dauka nan da karfe uku na rana za a kwashe ta a mika gidan Likita.”
Dariya aka sa duka dakin. “Wato kin kagara ta tafi ke nan ko?” Wani abokin ango mai suna Sultan ya fada.
“Ni dai ban fada ba kar ka hada ni da kawata.” Ta kalli Mahboobah da ke mata hararar wasa.
Sai da angunan suka fita sannan suka koma daki wurin kawayensu. Ana azahar masu kidan kwarya suka iso a lokacin Mahboobah ta canja kaya, ta saka wani coffee brown din lace mai tsada. Ta yi matukar kyau. Kawayenta suka fito da ita wurin da aka ma decoration ta zauna kan kujera. Masu kidan kwarya suka hau wasa ta. Nan fa biki ya kara armashi. An cashe sosai har zuwa karfe biyar da aka fara jin hayaniyar yan daukar amarya. Aunty Shafa ce ta je ta jawo amarya, ta kai ta ta canja kaya, doguwar rigar cotton material ce ta saka sai ta dora alkyabba black and white. Tun a nan ta fara kuka sosai fuskarta na cikin alkyabbar aka kai ta dakin Mommy. Kawayen Mommy na zaune nan fa aka hau yi ma amaryar nasiha tana kuka sosai. A karshe aka fita aka bar ta daga ita sai Mommy sai Aunty Shafa. Ido cike da hawaye Mommy ta ce
“Mahboobah.” Kyarma sosai Mahboobah ke yi tsabar kukan da take sha.
“Mahboobah ina so ki saurere ni da kunnen basira. Shi zaman aure dan hakuri ne musamman kuma wannan da kika dauko ma kanki. Ina so ki san cewa aure ya wuce duk yanda kike tsammani. Wata sabuwar rayuwa ce za ki fada mawa. Sai kin rufe idonki, kin toshe kunnuwanki sannan za ki ci ribar rayuwar aure. Yanda kika ce kin ji kin gani za ki iya, a haka za ki cika wannan alkawarin. Ki kyautata wa mijinki yi na yi bari na bari. Kyautatawa za ta sa sannu a hankali Ishraq ya so ki. Sannan ki kyautata wa mahaifiyarsa ki dauke ta tamkar yanda kika dauke ni. Za ta so ki za ta ja ki a jiki ita ma saboda zuciya tana son mai kyautata mata. Wallahi duk rashin son Ishraq gare ki ya ga yanda kike ma mahaifiyarsa dole zai ajje makaman yakinshi ya so ki. Ki rike sirrin mijinki Mahboobah. Dadi da wuya ki rike amanar aurenki. Ko da wasa kar in ji kar in ga kin aikata wani abu na rashin daidai. Matsalar aurenki ki rike ta, ke kika ji za ki iya ke kika zabe shi duk da tarin tsanarki da ya yi Boobah. Ko da wasa kar ki iso gare ni da sunan kin samu wata matsalar aure. Mun fita hakkinki mun aura miki wanda kike so, sauran aikin ya rage naki. A karshe, ina mai kara neman gafararki a karo na ba adadi, na halin da muka jefa yarintarki a ciki. Haka ni ma na yafe miki duniya da lahira Mahboobah. Ku je Allah ya bada zaman lafiya.” Ta fashe da kuka cike da rauni. Ita kanta Aunty Shafa kukan take yi, tana tausayin rayuwar da Mahboobah ta jefa kanta. Babu babbar matsala a aure sama da mace ta auri wanda ba ya son ta. Har gwara a ce shi namijin yana so macen ce ba ta so sannu a hankali zai ja raayinta. Amma wannan zama na Mahboobah akwai wuya sosai.
Sallama suka ji an yi, Hajiya Amna ce kawar Mommy ta ce ga mata biyu nan daga gidan su Ishraq sun zo tafiya da amarya. Aunty Shafa ta kama Mahboobah ta tayar suka fita. Motar Aliyu ta nufa da ita, saboda shi ne zai kai ta da kanshi. Sai ita ta zauna a gaban motar, iyayen Ishraq kuma suka zauna gefe da gefe Mahboobah a tsakiya aka rankaya Unguwar Rimi da ita, gidan mijinta.
End of chapter
Hello everyone. Ya kuke? Kwana biyu? Hope kowa lafiya. Am so sorry for keeping you waiting, uzuri na yau da gobe ne.
Finally, Mahboobah is now Mrs. Ishraq Sulaiman. Ko ya wannan zama zai kaya.
Thank you all for your love.
Princess Amrah
RAZ 2