BAKUWAR FUSKA CHAPTER C KARSHE

 BAKUWAR FUSKA CHAPTER C KARSHE

Kamar mahaukaciya haka take jin kanta na juya mata. Mommy ta kama ta ta zaunar, tana kallon ta cike da tausayi, ta sani an kai Mahboobah karshe ne. Ba yabon kai ba amma Mahboobah ba ta iya rashin kunya ba. Mahboobah hakuri gare ta ta kowanne fanni. A wani sashi na zuciyarta kuma, ta ji dadin amayar da maganganun da Mahboobah ta yi, ko ba komai za ta samu relief a zuciyarta.

“Ku tashi mu tafi Khalid…” Ishraq ya fada yana jin tamkar zuciyarshi za ta tsaga tsakanin kirjinshi ta bultso waje. Yana jin yadda kunya ke mamaye shi, tamkar ya bude kasa ya shiga cikinta ya boye. Ganin Khalid da Ibrahim ba su da niyyar mikewa ya sanya shi mikewa shi, “Mu je.” Ya maimaita, yana kallon Khalid da ya kasa cewa komai, sai faman jinjina maganganun Mahboobah yake yi, wanda da alama ta jima tana tara su, ranar da za ta amayar da su kawai take nema.

“Idan har ba ta ce ta yafe min ba na tabbata alhakinta ba zai daina bibiyata ba.” Ya kalli Mahboobah cikin marairaicewa, “Ki taimaka ki yafe mun…”

Hannu ta daga ma Ibrahim tana dakatar da shi. “Ka tashi ka fice mana daga gida ba na son ganin ka, ka je na yafe maka.”

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, ya mata godiya hade da mikewa shi ma.

“Ba dai zan gaji da ba ku hakuri ba. Ina fatan komai zai wuce daga wannan.” Khalid ya fada bayan ya mike tsaye.+

“Babu komai Khalid. Bayyanuwar wannan hardadden zaren ma kanshi wani abun godiya ne ga Allah. Ya wuce kawai Allah Ya kyauta gaba.”

“Ameen Mommy. Bari mu je. Mun gode kwarai da fahimta.” Suka nufi tafiya.

Tun da suka tafi Mahboobah ke kuka a wurin, Mommy ba ta ce mata komai ba, ta ba ta dama ta yi kuka, barin kashi a ciki ba ya maganin yunwa.

Sai da ta yi mai isar ta sannan don kanta ta mike ta nufi dakinta. Tana jin zuciyarta a yanayi kala biyu. Yanayi na farko zafi ne, na biyun kuma sanyi ne. Zafin na nufin tuna wahalar da ta sha a gidan Ishraq Sulaiman har zuwa kazafin da aka yi mata. Shi kuwa sanyin tsantsar jin dadin bayyanuwar gaskiyar abin da ta jima tana ma addu’a ne.

*

Tun bayan fitar su daga gidan su Mahboobah ya kifa kanshi a gaban mota. Da ma ba da motarshi suka zo ba, ta Khalid din ce. Ibrahim kuwa sun sallame shi ya tafi.

Khalid na tuki amma baki daya hankalinshi na ga Ishraq. Bai ma san ta inda zai fara bullo mishi ba. Amma dai yana da kyau ya dan tado mishi wata magana ta baya.

“Ka yi hakuri Ishraq. Ka gode ma Allah ma da gaskiya ta bayyana ba ka ci gaba da dakon alhakin yarinya ba.” Ya yi parking a gefen titi, sannan ya kama Ishraq ya tayar da shi zaune, yana kallon yadda idanuwanshi suka yi jajur, shi ba kuka yake ba amma tamkar wanda ya kwana yana kukan. “Ka tuna ranar da abun ya faru sai da na ce maka ka yi kuskuren rashin bincike? To ka ga irin ranar da ake guje mawa nan Ishraq. Bai kamata ba kawai daga jin zance ka tabbatar da haka ne har ka yanke hukunci a kai.”

Cikin wani irin yanayi mai cike da ban tausayi yake kallon Khalid, “What will happen has happened. Mai faruwa ta faruwa Khalid.”

“Then, why are you reacting like a lady in dai har ka san haka ne? Tunda dai komai ya wuce ai shi kenan sai a kiyaye gaba. Ka daina damun kanka da ma can haka Allah Ya tsara.”

“Ina jin zafin maganganun da Mahboobah ta jefe ni da su ne. Ina jin haushin kaina Khalid, ba na jin zan iya yafe ma kaina a kan kuntata wa baiwar Allah mai sona da na yi. Da gaske ina jin da na sani, da na sani mara misaltuwa. I don’t even know what to do. Da zan samu in yi kuka watakila da na sauke gagarumin nauyin da nake ji a tsakanin kirjina. Ina jin wani irin yanayi game da Mahboobah, I have never felt it before.”

STORY CONTINUES BELOW

Hannun Ishraq ya saka a cikin nashi Khalid. Yana kokarin ba shi kwarin guiwa. “Na san me kake ji likita. Na ga yadda idanuwanka suka cika da son Mahboobah…”

“What?” Ishraq ya dakatar da shi. “So? Ni? A yaushe na fada maka? Don na ce ina jin wani yanayi game da ita kuma sai ya zama So? Ka sani ko tausayi ne, ko kuma nadamar abin da na mata a baya?”

Murmushi Khalid ya yi jin maganganun da Ishraq ke yi. “Ba kai ka fada min haka ba Ishraq, ni na gani a cikin idanuwanka, kuma ba za su taba bayyana karya ba. Ko ka yarda ko kar ka yarda kana son Mahboobah. So kuma mai tsanani.”

Gyada kanshi Ishraq yake yi. In dai wannan ne So to a gaskiya abun bai zo mishi da sauki ba. A baya ya so Ameerah Muhammad amma ko kusa bai rinka jin irin wannan yanayin ba game da ita. Ita wannan, ko runtse idanuwanshi ya yi tuno yadda suka yi rayuwa a tare yake yi, tuno kyautatawarta gare shi yake yi. Ji yake zuciyarshi na bugawa tare da sunanta, kwakwalwarshi na hasko mishi hotonta. Kunnuwanshi na jiye mishi sautin kukanta. Hancinshi kamshinta yake jiyo mishi.

“Da gaske Ishraq son Mahboobah kake yi. Kuma da ma idan ba za ka manta ba akwai ranar da na taba fada maka haka, har ka karyata mu kana fadin mu psychologists makaryata ne. Ka tuna ranar?”

Guntun tsaki Ishraq ya saki. “Karya na yi ku ba makaryatan ba ne?”

“Ina kuwa muke karya tunda ga shi na maka hasashe kuma ya tabbata.” Khalid ya fada yana dariya. “Yau ga ranar da idanuwan Ishraq ke cike da damuwar rashin Mahboobah Bukar. Zuciyarshi ke cike da kaunarta.”

“Khalid…” Ya kalle shi cikin ido. “Zuciyata tana min zafi sosai. Ina tuno a yanayin da muka baro Mahboobah kar mu je wani ciwon ya tasar mata da ma dasasshiyar zuciya ce a kirjinta. Khalid idan wani abu ya samu Mahboobah ta sila ta ba zan taba yafe ma kaina ba.” Ya dafe tashi zuciyar da ya rasa yanayin da zai jefa ta a cikinshi.

“Kada ka cuci kanka Ishraq. In dai ka san son Mahboobah kake yi tun wuri ka dawo da matarka. Har yanzu lokaci bai kure ba tunda akwai sauran igiyoyi biyu a tsakaninku.”

“Ban sani ba ko son ta nake yi Khalid. Ni dai a iya sani na tausayinta ne nake ji. Ba na jin soyayyarta.”

Dafa kafadarshi Khalid ya yi. “Kusan kowa kafin ya fara jin yana son ya yi soyayya da mutum dole ne sai ya ji wannan yanayin. Shi yanayin yana nufin SO. SO ke shiga farat daya, ya sukukuta mutum, ya sauya yanayinshi, bako a abun shi zai kasa gane ko mene ne. Sai a hankali yake zaga jini da jijiyar mutum, ya zarce har cikin zuciya da kwakwalwarshi, ya sanya mishi sha’awar yin soyayya da wanda yake jin SON nashi. Don haka Ishraq abokina, babu ko tantana SON Mahboobah ne ya shige ka, soyayyarta dai ce ba ka fara ji ba, wanda na tabbata tana bisa hanya ita ma. A lokacin da ta gama shigar ka, a lokacin ne za ka gane takamaimai yanayin da zuciyarka take ciki wanda a yanzu ka ce ba ka sani ba.”

Jinjina kai yake yi yana gasgatawa da kalaman Khalid. Amma ta yaya? Me ya sa zuciyarshi za ta yi mishi haka? Me ya sa zai kamu da son halittar da ya fi tsana a duk duniyarshi?

“Ya kamata mu yi wa Mami bayani amma kafin nan kana da bukatar nutsuwa sosai ka tattauna da zuciyarka.”

“A ina ka taba ji ko ganin an yi magana da zuciya?”

Dariya ya ba Khalid. “Kai wuya ta da kai wani gwari ne. Amma ka iya kankamba kai cikakken Bahaushe ne ni kuma Kanuri. Ai ga shi nan ka kasa gane manufata.”

“Kana da matsala Khalid Zannah. Ni ban ga ta yadda mutum zai yi magana da zuciyarshi ba ne.”

Khalid ya tada mota yana hawa kan titi. “Abun nufi ka zauna kai kadai ka saurari abin da zuciyarka ta yanke maka. Idan har ka samu nutsuwa da hakan shi ke nan.”

STORY CONTINUES BELOW

“Sai yanzu na gane.” Ishraq ya fada da murmushi shimfide a saman fuskarshi. Ba karamin dadi Khalid ya ji ba ganin ko yaya ne Ishraq din ya dan samu kwanciyar hankali.

Daga nan kai tsaye gidan Mami suka wuce. Yanayin Ishraq kadai ya tabbatar mata da ba lafiya ba. Bayan sun gaisa ta dube shi tana kara karantar yanayinshi.

“Me yake faruwa da kai likita?” Ta tambaye shi idonta kyam a kanshi, tana ganin yadda idanuwanshi suka canja launi zuwa ja kamar wanda ya yi kuka.

Cikin nutsuwa Khalid ya fara labarta mata duk yadda abun ya kasance, da kuma zuwa gidan su Mahboobah da suka yi. Sai dai ya boye mata maganganun da Mahboobar ta jefi Ishraq da su.

Gyada kanta take yi tana ambatar sunan Allah. Lallai mutum mugun icce. Idan mutum ya kulla maka wani sharrin har gara ma na aljan a kan nashi.

“To ita kuwa Bilkeesu wace irin karamar zuciya ce za ta sanya ta kulla ma Mahboobah wannan tuggun? Ita ba ta ganin cewa ita ma din mace ce? Kai Allah dai Ya shirya mana zuri’a. Amma dai wallahi ba ta kyauta ba ko alama.”

Cikin sanyin murya Ishraq ya ce “Ni kaina ma ya kulle Mami. Ban ma san kalar hukuncin da ya kamata in daukar mata ba. Don sam ba ta cancanci a kyale ta ta ci bulus ba. Wallahi sai na ci mutuncinta.”

Khalid ya gyara zamanshi yana fuskantar Ishraq. “Dole bin komai za mu yi a sannu in dai har muna so mu yi nasara. Macen da ta iya kirkira wannan kalar sharrin ga baiwar Allah da ba ta ji ba ba ta gani ba, to babu wuya ka ga ta lumar da mu. Idan ba ka iya kama barawo ba tabbas shi zai kama ka.”

“Haka ne.” Mami ta jinjina kai tana dad’a al’ajabin wannan lamari. “Haka kawai yarinya ki lalata tsakanin ma’aurata, ki bata wa mace suna ba ta ji ba ba ta gani ba.”

“Ina zuwa.” Ishraq din ya fada yana dubo lambarta da take kiran shi da ita, don shi bai ma yi saving ba tsabar kiran da take mishi ne ya sa ya haddace wasu daga cikin lambobin.

Kamar tana jira ta dauka muryarta kadai za ta tabbatar da karairaiya take yi. Sannan ba karamin dadin kiran da ya yi mata ta ji ba.

“Yah Ishraq ina yini. Ya aiki? Allah dai Ya sa ka gaji ne da ja min aji ka kira ka karbi soyayyata.”

Bayyanannen tsaki ya ja wanda ya yi silar canjawar yanayinta.

“Kina ina?” Ya tambaye ta cikin takaici.

“Ina School Ya Ishraq. Za ka zo ne?”

“Idan na iso zan kira ki.” Kawai ya fada yana tsinke kiran.

“Mene ne dalilin yin hakan?” Khalid ya tambaye shi cikin mamaki.

“Zuwa zan yi in wawwanka mata mari in dawo. Ita din banza da zan bi ta a ruwan sanyi wallahi ta yi kadan. Me aka yi aka yi ta? Lallasa ta zan yi.”

Kai Mami ta gyada tana fadin “Wannan ba hanya mai billewa ba ce ba likita. Ban yarda ka daki diyar mutane ba. Idan fa wurin dukan nata tsautsayi ya gitta wani abu ya faru da ita abun Allah Ya kyauta?”

“Gaskiya ni ma dai ban goyi bayan haka ba. Amma nake ga tun da da ma yar uwarku ce, me zai hana ku tinkari iyayenta da zancen? Sam bai kamata ba a yi shiru a bar su a duhu.”

Murmushi Mami ta yi tana kallon Khalid. “Lallai ba ka san waye Alhaji Imrana ba. Ai wannan mutumin bai hada ya’yanshi da kowa ba. Ko kadan ba ya son laifinsu. Shi ne makasudin tabarbarewar rayuwarsu. Ba na tunanin a cikin yaranshi ma akwai na kirki saboda ko alama ba su samu tarbiyya mai kyau ba. Bilkeesun ce ma kadai ta kirki a gani na.”

Ishraq ya kalle ta da fadin “Kila ma gara kowa a kan Bilkeesu Mami. Babu irin binciken da ba mu yi ba a kanta shekarun baya sadda kika uzzura min a kan in tsayar da matar aure. ‘Yar kwaya ce ma.”

Mamaki sosai Mami ke yi da jin wannan zancen. “Ita Bilkeesun? Ya Salaam.” Ta hau tafa hannuwa. “Abun mamaki ba ya taba karewa. Ka ga yarinyar nan sum-sum kamar ta kwarai ashe dai ba ta kwaran ba ce. To Allah Ya shirya.”

“Ameen dai. Yanzu wannan ma ba mafita ba ne ke nan.” Khalid ya fada yana sauke ajiyar zuciya.

“Ai na fada muku ga abin da ya dace a yi amma kun dakatar da ni. Wallahi idan ba lallasa ta aka yi ba babu wata hanyar da zan bi don fanshe wannan rainin wayon nata.” Ya fada yana mikewa, takawa ya yi ya fice daga gidan. Yana jin Mami da Khalid na kwala kiran shi amma ko waigensu bai yi ba kawai ya tafi.

End of chapter

Princess Amrah

RAZ 2Ringing din wayarta ta ji, tana dubawa ta ga Muhammad ne. Ranta a bace yake, zuciyarta babu sanyin da za ta iya yin magana da kowa a yanzu. Ta kifar da wayar tana juya kanta. Gama ringing din ke da wuya ta sake ji yana kira. A wannan karon ma kin dauka ta yi tana tsinkewa ta ji karar shigowar text message…

‘Mamanmu ina wuni? Ya aka ji da fama da mu? Ina kanwata Ameerah? Ina gaishe ta. Fatan dai lafiya kuke.’

Dariya ‘Mamanmun’ da ya kira ta da shi ya ba ta. Ta saki murmushi a ranta tana jinjina barkwanci irin na Muhammad kamar ba dan gidan sarauta ba yadda ya fada mata. Don yan sarauta an san su da kamewa da shan kamshi, ga kuma miskilanci.

Ba ta mishi reply ba sai data da ta kunna tana ganin yadda sakuna ke rige-rigen shigo mata kasantuwar ta jima rabon ta da hau whatsapp, tun kafin ta fara jarabawa. Sallamar Ameerah ta ji ta daga kai ta kalle ta. Duk ta marairaice sum-sum ta zama kalar tausayi.

“Ameerah what is your problem?” Ta tambaye ta tana bude hannuwanta duka biyu alamun ta zo ta shiga jikinta. Kin zuwa ta yi Ameerah sai ma kwakkwabe baki da take yi.

“Zo mana ina wasa da ke ne?” Ta fada cikin sigar fada. Da gudu Ameerah ta shiga jikinta tana fasa kuka.

“To ya isa haka yi shiru, kin san ba na son kuka. Fada min me kike wa fushi?”

Sai da ta dago daga jikin Mahboobah sannan ta ce “Ba ke ba ce ba kike ma Daddyna fada…” Ta sake fashewa da wani kukan.+

Har ga Allah ba ta san cewa Ameerah na cikin dakin ba sadda take mayar wa da Ishraq magana. Ita dai ta ga sadda Mommy ta kore ta da wayarta ta ce ta je daki ta yi game. Amma ba ta san sadda ta dawo ba da ba ta yarda ba ta yi a gabanta, tun da halin yara akwai su da riko, kuma suna jin ciwon wani sashe daga cikin iyayensu ya kuntata ma wani sashen.

“Ameerah, abin da na ma Daddynki wallahi ko rabi-rabin wanda ya yi min a baya ban yi ba. Amma ki yi hakuri ki yafe min kin ji, ba zan kara ba.”

Murmushi Ameerar ta yi tana kara shiga jikin Mahboobah, a wannan karon rungume ta yi.

“Happy?” Mahboobah ta tambaye ta ganin ta saki.

“Yes.” Ta ba ta amsa tana daukar wayarta.

“Ammi ina son yin waya da Mamama.” Ta fada tana mika mata wayar da nufin ta kira mata Fareeda a waya, ashe mistakenly ta latsa recent call kiran Muhammad ya shiga. Kafin Mahboobah ta yi gaggawar kashewa tuni kiran ya isar ma Muhammad, da gaggawar shi sai ga shi ya kira ta.

Duk da ba ta so dauka ba amma dole ta daure ta dauka suka gaisa.

“Mamanmu ina ta kiranki in kwashi albarka amma ba ki dauka ba.”

“Muhammad Saddam.” Ta fada tana dariya. “Ba ka gajiya da tsokana. To Ameeran ma ba Mama take kira na ba ai.”

Dariyar ya yi shi ma yana jin dadin muryarta. “Okay fada mun me take kiran ki da shi?”

“Ba zan fada ba…”

“Ammi ba za ki kira mun Mamama ba ko?”

“Shi kenan ma na ji. Haba Ammi ashe ma kina tare da kanwar tawa shi ne ba za ki hada mu ba mu sada zumunci a matsayinmu na Yaya da Kanwarsa.”

STORY CONTINUES BELOW

“Allah Ya shirya ka.” Mahboobah ta fada tana kara wa Ameerah wayar. “Ungo ga Uncle ki gaishe shi.”

Cikin ladabi ta gaishe da Muhammad. Ya tambaye ta ya take ta ce lafiya lau. Da barkwanci ya yi ta jan ta har ta sake da shi suka yi ta hira har kusan minti bakwai, sannan ya ce ta ba Ammi wayar.

“Gaskiya Ammi wannan kanwar tawa barakallah akwai wayo. Haka nake son ganin yaro mai exposure. Allah Ya raya mana ita.”

Ba ta ce amin ba Mahboobah sai canja topic din da ta yi,

“Na kunna data ai yanzu na ga tarin messages dinka sai shigo mun suke ta whatsapp.”

“Eh da yake a can na fara yi miki magana, na ga ba ki da niyyar hawa shi ya sa na ga gwara in kira ki dai in isar da sakon neman abotar nan da bakina. Idan kin duba ma za ki ga har da hotunana na turo miki.”

“Me zan yi da hotonka?” Ta tambaye shi tana kallo Ameerah da ke wasa da zoben yatsarta

“Look at you. Kamar ya me za ki yi da shi? How can we be friends without knowing each other? Ni da ma dai na san ki ke ce ba ki san ni ba and you have to see my picture kafin ki dawo school.”

“Haka ne.” Ta ba shi amsa tana dorawa da “Kashe to mu ci gaba da magana a whatsapp din.”

Bayan ta shiga whatsapp ta tarar da tarin sakwannin da Muhammad Saddam ya turo mata ga kuma hotunanshi nan wasu a bisa doki, wasu tare da mai martaba Sarki, wasu kuma a London ne sadda ya je karatu. Mamaki ne ya cika ta yadda ta gan shi yaron manya ne amma yake shirme idan suna waya. Sai ta kara tabbatar da lallai ba kowanne dan gidan sarauta ba ne mai jiji da kai, ba kowanne ba ne ke da girman kai don ga shi nan ta gani a wurin Saddam.

Chatting suka yi sosai kafin daga bisani suka yi sallama ta sauka don ita da ma can ba gwanar chatting ba ce. Balle kuma yanzu da take karatu bilhakki.

*

Dari biyu ya zaro daga cikin wallet dinshi yana mika wa mai babur din da ya kawo shi. Ji yake zuciyarshi har wani zafi take yi. Wayarshi ya zaro ya kira lambar Bilkeesu bayan ta dauka yake tambayarta inda take.

“Ooops sorry Yah Ishraq dina, yanzun nan na fita daga makarantar wani babban uzuri ne ya fitar da ni. Amma why not mu hadu da kai a gida gaban Daddy? Na dai san ai maganar aure ce kake so mu yi ko?” Ta fada cikin yanga.

“You must be joking Bilkeesu. Idan ma kin dauka abin da ya kawo ni wurinki ke nan tabbas kin yaudari kanki. Ban taba sonki ba ba kuma zan fara shi ba a yanzu. Ki gode ma Allah da ban same ki ba don wallahi na yi niyyar hada miki jini da majina. Matsiyaciyar yarinya yar kwaya kawai.”

Maganar tashi ta dake ta, ta ma rasa abin da za ta fada sai dai wani irin radadi da zuciyarta ke mata.

“Munafuka asirinki ya tonu, kika hada tuggu kika shiga tsakanina da Mahboobah. To idan ma kin yi ne don in aure ki wallahi kin yi a banza. Ba zan taba aurenki ba Bilkeesu. Ko da a ce ke din ta kirki ce ba zan aure ki ba matata nake so. Balle kuma makaryaciya, mayaudariya, yar maye irinki. Wallahi ki kuka da haduwa da ni don sai na wulakanta ki. Wawuya kawai!” Ya karisa maganar da kashe wayar, yana jin haushin rashin samun ta da ya yi.

Khalid ya ji ya dafa shi, ya juya ya kalle shi. “Shi ne muka yi ta kiran ka ni da Mami ka mana banza ko. Kuma na fito nemanka har ka haye babur ka taho. Ishraq ka sassauta ma zuciyarka ka ji. Kar ka yanke ma Bilkeesu hukunci cikin gaggawa ka bari har sai mun gama tunanin matakin da ya kamata mu daukar mata.”

Banza da shi Ishraq din ya yi yana kama hanya ya isa gaban motar Khalid. Bin bayanshi ya yi Khalid, ya bude mishi motar suka shiga.

A mota kara kwantar mishi da hankali Khalid ya yi. Sosai kuma ya samu nutsuwa. Kai tsaye gida ya wuce ya kai shi sannan shi ma din ya tafi nashi gidan.

Tunda ya yi sallar maghrib ya kwanta wani irin abu mai tauri yake ji ya yi mishi tsaye a kirji. Kai tsaye ba zai ce ga abin da yake damun shi ba, ya dai san ko ma miye bai rasa nasaba da Mahboobah, tausayinta yake ji yana ratsa kowacce gab’a tashi.

Da kyar ya iya mikewa jin an kira isha ya tafi masallaci. Da ya yi ya dawo ma wani kogin tunanin ya afka. Nazartar kalaman Khalid Zannah yake yi, tun yana karya ta su har ya fara yarda da Son Mahboobah yake yi. Ji yake baki daya zuciyarshi ba ta yi mishi adalci ba. Ashe shi ya sa aka ce idan za ka so mutum ka so shi saisa-saisa, idan kuma za ka ki shi to ka ki shi saisa-saisa. Yau ga inda kiyayya ta rikide ta zama soyayya nan. Ko a mafarki bai taba hangen zai so Boobah ba, a duk duniyarshi babu macen da ya fi tsana, babu ma halittar da ya fi tsana sama da ita. Sai dai yanzu, duk tarin tsanar da ya yi mata ya tara ta, ya jefa ta a saitin Bilkeesu Imran.

So yake ya kira ta a waya amma ta yaya? Idan ya kira me zai ce mata? Bai ma san ta inda zai fara ba. Sannan a yadda ya hango idanuwan Mahboobah cike da tsanar shi, ba ya tunanin akwai sauran ko alamar soyayyarshi a tattare da ita. Da alama juyin waina aka yi wa abun, shi aka dawo wa da soyayyarta, ita kuma aka mayar mata da kiyayyarshi.

Wayarshi ya dauka ya kira Khalid. Bayan Khalid din ya dauka ya tambaye shi ko lafiya. “Khalid I’m in love, I’m in love with Mahboobah Bukar. Khalid zuciyata zafi take yi min, ban taba jin wani abu makamancin wannan ba a tattare da ni. Ban san haka ake ji ba idan ana SON mutum har sai da ka karantar da ni. Wallahi dumu-dumu na fada a kangin soyayyarta.”

Ajiyar zuciya Khalid din ya yi, yana tuna ranar da suka yi zancen Mahboobah tun farkon sanin su da ita, yana fada ma Ishraq din fa watan-wata rana zai iya son ta amma ya musa mishi. Yau ga wannan ranar ta tabbata.

“You should tell her.”

“She doesn’t love me.” Ishraq din ya ba shi amsa cikin wata irin murya mai cike da ban tausayi.

“How did you know?”

“Kamar yadda ta cikin idona ka hango Son Mahboobah da nake yi, haka ita ma din a cikin idanuwanta na hango k’i na da take yi. Khalid a can baya sadda nake aurenta, ta idanuwa take sanar da ni sirrin zuciyarta. Har ba na son na hada ido da ita don ma kar wata rana tausayinta ya shige ni. Sai dai a yanzu, akasin haka na gani a ciki Khalid. Ba ta so na, ba na tunanin ko na neme ta za ta yarda ta dawo gidana. And I need her back. I need my wife, I need my daughter too.”

“Likita.” Khalid ya kira shi yana dorawa da “Ka kwantar da hankalinka. Soyayyar da Mahboobah take maka ba za ta taba tashi a iska ba, na tabbata haushinka da take ji ne ya jawo haka amma daga zarar zuciyarta ta sanyaya za ta ci gaba da jin soyayyarka. Soyayyar ce ta daskare amma Son yana nan jibge gare ta. So abin da nake so shi ne ka daure ka kira ta ka kara ba ta hakuri, kar ka nuna mata da kudurinka, idan ka ba ta hakuri sai ka mata sallama kawai. A hankali kana dan tura mata sakon gaisuwa, ko ba ta gida kana dan lekawa ka ga Ameerah kuma ka gaishe da Mommy, in shaa Allahu sannu a hankali za ta gane ka dawo hanya mai kyau ne.”

Jinjina kanshi ya yi yana yin na’am da shawarar Khalid. Sannan suka yi sallama yana fadin ya gaishe da Junior da Ummu Salma jaririyar da ba ta fi wata shida ba da matar Khalid din ta haifa.

End of chapter

Princess Amrah

RAZ 2A gaggauce take hada kayanta saboda hutunsu ya kare a yau take son komawa Zaria. Ameerah ce ta shigo da wayarta da ke ringing a hannunta tana duba suna ta ga Ishraq ne. Kin dauka ta yi, da ya takura mata ma sai ta saka wayar a flight mode tana mayar wa da Ameerah.

“Ammi Dady ne fa.”

Wani irin wawan kallo Mahboobah ta jefi Ameerah da shi tana ci gaba da hada kayanta. Ficewa yarinyar ta yi daga dakin tana ci gaba da game din da take yi.

Tana cikin haka sai ga Fareedah ta zo. Cikin farin ciki suka rungumi juna don tun da ta zo Fareedar ba ta zo gidan ba tana ta zarya kanwar mijinta ta haihu sai yau ta samu zuwa.

“Yah Boobah ya da hada kaya kuma?” Ta fada bayan ta zauna a bakin gado.

“Bako zai yi halinshi.”

Bata rai Fareedah ta yi. “Wai da ma hutun naku dan kadan ne? Ai wallahi da na sani in yi squeezing time kafin in rinka wucewa gidan haihuwa ina dan zuwa nan mu sha hira sannan in wuce. Gaskiya ban ji dadi ba ni dai.”

Mahboobah ta sanya hannunta a cikin nata. “Kar ki ji komai kanwata ai ana tare. In shaa Allahu kina haihuwa zan zo ganin Babyna.”

“To Allah Ya sa haka.” Ta fada tana murmushi.+

“Ameen ya Allah. Ya gida, ya Abdul din?”

“Yana lafiya wallahi. Ya ce a gaishe ku yanzu yana sauri ne ya sa bai shigo ba. Sai ya zo dauka ta zai shigo a gaggaisa.”

“Eyyah Allah bai nufa za mu hadu ba ke nan.”

Ido Fareedah ta kwalalo,

“Wai Yah Boobah kina nufin yau za ki wuce? Ni fa na mayar ko sai gobe ma.”

Bayan Mahboobah ta zira bakar abayarta ta mata murmushi,

“Yanzu ma kuwa in shaa Allahu. Ba na so in yi dare ne Reedah. Na fi son isa ido na ganin ido don in kimtsa komai nawa na tabbata k’ura ta gama yin aika-aika a dakina. Ba zan so kwana a cikinta ba gaskiya.”

Kai ta jinjina Fareedah, “Haka ne kuma Yah Boobah. To Allah Ya tsare hanya Ya bada sa’ar karatu.”

“Ameen Reedahna.” Ta zira ‘yar karamar farar hijab tana daidaita zamanta. Bayan ta gama suka mike ita da Fareedah, kokarin ja mata akwatin take amma ta hana ta,

“Rufa mun asiri Fareedah da tsohon cikinki za ki ja akwati, so kike ki wahalar mun da baby ko?”

Hararar wasa Fareedah ta mata, “Ke Yah Boobah wato ba ma ta ni kike ba ko. Allah Ya bayyana gaskiya na gane idan kika samu baby tsaf za ki fifita soyayyarshi a kan tawa.”

“Fadi bata yawun baki.”

Su duka suka saka dariya suna isa falo.

Mommy suka samu zaune ita da Ishraq suna gaisawa. Mahboobah na hada ido da shi ta samu kanta da shiga wani irin matsanancin takaici. Haushin shi take ji sosai, a duk sadda za ta gan shi wutar kiyayyarshi ce take jin tana ruruwa a cikin zuciyarta.

Bata fuska ta yi bayan ta zauna kusa da Mommy.

“Ba dai har tafiya ba.” Mommyn ta fada tana kallon ta.

STORY CONTINUES BELOW

“Mommy tafiyar ce. Ba na son in yi dare ne.”

“Yah Boobah da boko. Wai daga nan zuwa Zaria tafiyar da ko awa daya ba ta kai ba shi ne kike zancen kar ki yi dare.”

Guntun tsaki ta yi Mahboobah, “na fa fada miki dalili Fareedah amma kike kara soko wani zancen.”

“To Allah Ya ba ki hakuri.” Fareedah ta furta tana jawo Ameerah a jikinta.

“Mamama yau dai zan bi ki.”

Murmushi Fareedah ta mata. “Ki je ga Daddynki can ki gaishe shi.”

Da gudunta ta koma wurin Ishraq tana shiga jikinshi.

“Mommy da ma zuwa na yi mu yi maganar shiga makarantar Ameerah, tun da dai tana da wayo sosai sai a saka ta boko da kuma Islamiyya.”

Fara’a Mommy ta fadada. “Ai kam wannan yarinyar tsufanta ya girmi shekarunta. Don ko ni nan tsaf Ameerah za ta iya kai ni kasuwa ta sayar.”

Dariya suka dauka su duka dakin har da Mahboobah. Kallon ta Ishraq ya yi yana jin dadin ganin fararen hakoranta sun bayyana. Wutar sonta ke ruruwa a zuciyarshi, yana jin idan har bai bayyana mata sakon zuciyarshi ba komai zai iya faruwa da shi.

“Kuma na ga yanzu aka koma hutu an fara daukan students. Da ma dai dalilin zuwan ke nan.”

Kamar an ce ya kai nan Mahboobah ta mike tana jan akwatinta. “Mommy ni zan wuce a mana addu’a.”

“Haba Mahboobah wai wannan wace irin gaggawa ce kike yi haka? Me ya sa ba za ki jira Aliyu ba ya zo ya kai ki tasha?”

Marairaice fuska ta yi Mahboobah, “Mommy sai ka ce dai wata ‘yar yarinya. Ko Fareedah dai ai ba za a ce dole sai an raka ta ba balle ni mai shekara ashirin da hudu.”

Gyada kai Mommy ta yi tana murmushi. “To ai sai ki tafi, Allah Ya tsare hanya Ya bada sa’a. Ki kula da kanki, ki ji tsoron Allah.”

Jinjina kai ta yi tana rataya handbag dinta. Ko kallon inda Ameerah take ba ta yi ba don kar ma ta sake hada ido da Ishraq.

“Allah Ya kiyaye hanya Ammi.” Ta jiyo muryar Ameerar ta fada.

“Au daga nan ma ba za ki zo ki mun sallama ba ko?”

Isowa ta yi gaban Mahboobah tana rungumeta.

“Allah Ya miki albarka. Idan kin fara zuwa school ki yi karatu sosai kin ji. Ban da tsokanar fada, banda kuma wasa a makaranta.”

Kai Ameerah ta jinjina tana fadin, “To Ammi. Yaushe za ki dawo?”

“Idan Mamama ta haihu in shaa Allahu zan zo Ameerah. Zan zo ganin new baby.”

Tsalle ta hau yi tana murna har Mahboobah ta fice. Bin inuwarta da kallo Ishraq ya yi yana jin ina ma, ina ma. Ai wannan ba ta ma da lokacinshi a yanzu ba ya tunanin akwai sauran ko dison soyayyarshi a zuciyarta.

***

A cikin watannin da ba su wuce bakwai ba wata irin shakuwa ta wanzu tsakanin Mahboobah da Muhammad Saddam, wanda ba sa iya yin awa biyar ba tare da sun ji muryar junansu ba. Ta dauke shi daf, ta ba shi wani irin matsayi mai girma a cikin zuciyarta. Shi din mutum ne mai kyautatawa ga kowa, mai barkwanci. Rashin sabo da kulawar namiji a rayuwarta ya sanya babu wuya ya saba mata da kanshi. Duk da bai taba furta yana son ta ba ita ma kuma haka, sai dai babu wanda zai ga mu’amalarsu bai rantse cewa masoyan gaske ba ne.

STORY CONTINUES BELOW

A nashi bangaren kuwa, zuciyarshi cike take da kaunar Mahboobah. Azalzalarshi take a kan ya isar da sirrinta ga Mahboobah sai dai ya kasa, saboda yana yawan jin yadda Mahboobar ke zagin soyayya tana kushe ta, duk da cewa a duk sadda ta yi haka yana kokarin ganin ya nuna mata da ba duka aka taru aka zama daya ba.

Tsoron shi kar ta guje shi idan ya ce yana son ta. Don kuwa a yadda ya saba da ita, ba ya jin zai iya jurar rashinta. Son ta yake da zuciyarshi daya, soyayya kuma ta tsakani da Allah.

Har wata rana mahaifiyarshi ta kira shi tana mishi zancen aure.

‘Saddam tunda dai ka kammala karatunka, kana da aikin yi, babu abin da ka nema ka rasa. Ya kamata a ce ka tsayar da matar aure haka nan.’

Murmushi kawai ya yi yana fada mata ai aure lokaci ne. Kuma wadda yake son auren ma makaranta take yi.

Fatan alkhairi mahaifiyar tashi ta yi mishi, yana barin wurin ya tafi makaranta wurin Mahboobah ya ba ta labari.

‘Fulani ta damu a kan sai na yi aure Ammi. Kuma ni na ga ban isa aure ba.’

Hararar shi Mahboobah ta yi tama kwada mishi handout din hannunta. ‘Wallahi ka ma raina mutane. Kai din ne ba ka isa aure ba ko?’

‘Eh mana.’ Ya furta yana mata dariya.

Haka rayuwarsu ke tafiye cike da faranta ma junansu rai. Duk wani abu da ya san dalibi zai bukata bai taba barin Mahboobah ta yi rashinshi ba, sai dai ta ga ya kawo mata. Tun tana kin amsa har ta gaji ta fara karba tana fada wa Mommy.

“Anya Mahboobah wannan Muhammad din ba sonki yake ba?”

Duk da a wadansu lokutan ita kanta takan ga alamun son ta yake yi amma ta kasa gasgatawa. Murmushi ta saki tana fadin,

“A’a fa Mommy, kawai dai yana da kyautatawa ne.”

Mommy ta gyada kai kawai amma ita a ranta tana gasgata lallai Saddam na son Mahboobah, soyayya kuma mai tsanani.

*

Rabon da Ishraq ya samu nutsuwa tun kafin ya saki Mahboobah, sai dai rashin nutsuwar tashi ta yanzu ta yi yawa, ta ta’azzara da har ya yi rashin walwalarshi. Tamkar zautacce haka ya koma, idan ya rufe idonshi Mahboobah yake gani. Idan ya kwanta barci ma ita yake gani. A Office ma ko aiki yake sai ya rinka yi yana soko tunaninta.

Zaune yake yau ma ya rafka tagumi sai zancen zuci yake yi. Sallamar Khalid ya ji a cikin Office din, ya sauke ajiyar zuciya yana amsa sallamar.

Bayan Khalid ya zauna ya dubi Ishraq da duk ya bi ya zama wani iri kamar ba shi ba.

“Wai kai har sai yaushe ne za ka saukaka ma zuciyarka Ishraq? Me ya sa ba za ka fitar mata da abin da yake zuciyarka ba? So kake ka illata kanka?”

Kwalla Ishraq din ya share, “Ba zan iya ba ne Khalid, ban san ta inda zan fara fada wa Mahboobah manufata ba. Allah Ya sani ina matukar jin kunyarta.”

Tausayi sosai ya ba Khalid din, yadda ya zama sukuku a yanzu kamar ba shi ba. “Daurewa za ka yi ai, ba a san namiji da tsoro ba. Ka cire komai kawai ka kira ta a waya.”

Gyada kanshi ya yi Ishraq din, “Khalid ke nan. Na kira Mahboobah ya fi a kirga amma ba ta daukar wayata. Na mata text sau uku duk babu reply.”

Shiru jim, Khalid ya yi kafin ya ce, “Ba maganar waya ba ce. Ka shirya gobe mu same ta a makaranta. Zaria. Ni zan mata magana da kaina, zan fada mata komai in shaa Allahu za ta saurare ka. Bakin da ya furta SO ko ya furta k’i karya yake yi Ishraq. Yadda Mahboobah ta so ka a baya ba na tunanin soyayyarka za ta iya ficewa a cikin shekara goma ma balle ko uku ba a yi ba har yanzu.”

Mikewa ya yi Ishraq ya cire lab court din jikinshi. “Mu tafi yanzu ma Khalid. Ina da aiki amma ba zan iya ba, ba zan iya aikata komai ba idan ba mun je mun samu Mahboobah ba.”

Dafa kafadarshi Khalid ya yi,

“A’a Ishraq rana ta yi yanzu la’asar ke neman yi. Ka yi hakurin gobe da safe sai mu je.”

Gyada kanshi Ishraq ke yi, “Dare bai yi ba Khalid, ka tashi kawai mu tafi yanzu.”

Bai da yadda zai yi Khalid din dole ya tashi suka tafi. A motar Ishraq din suka kama hanyar Zaria. Suna tafiya Khalid na karfafa wa Ishraq guiwa, amma fa shi jin shi kawai yake yi, ko kadan zuciyarshi ba ta ba shi cewa Mahboobah za ta karbi soyayyarshi. Ba ya tunanin zai yi nasarar shawo kanta.

Hudu da rabi suka isa birnin Zaria. Kai tsaye ABU suka wuce, sai da suka fara tsayawa masallacin makarantar suka yi sallar la’asar sannan suka wuce medical department. Shi Ishraq bai ma san cewa medicine take yi ba sai yanzu. Cikin mamaki ya ce,

“Da ma medicine take yi ashe.”

Murmushi Khalid ya yi. “Ai ita ce ka sanya wannan Prof din ya taimakawa mawa.”

Da mamaki Ishraq din ke kallon shi. “Shi ne kuma ka boye min?”

Ya daga kafadarshi Khalid, “A sannan ai k’in ta kake yi. Idan na fada maka ita ce ba za ka yarda ka taimaka mata ba na sani.”

Hannunshi ya sanya ya shafi fuskarshi. “Ko a sannan ina jin wannan yanayin game da ita Khalid. Tun ma kafin in rabu da ita na fara jin yanayin, sai dai na kasa gasgata wa kaina hakan ne. A lokacin da na kama Ibrahim a cikin gidana, wani irin tukukin kishi ne ya lullube ni wanda ni kaina sai da na ba kaina mamaki. Don ban ga dalilin da zai sanya ni jin kishin Mahboobah ba bayan kuma ba son ta nake yi ba. Haka bayan na rabu da ita ma, kewarta sosai na rinka yi. A wadansu lokutan har dakinta nake shiga in zauna bisa tiles ina tuna wadansu abubuwa nata. In shiga kitchen ina tuna yanayinta.”

Guntun tsaki Khalid din ya yi yana fadin, “Yanzu kuma duk ka san ka aikata wadannan abubuwan shi ne ka kasa gasgata ni da wuri? Ka ba ni wahalar yi maka bayani. Shi so ai ba ya boyuwa Ishraq.” Ya fara kokarin gano sunan Mahboobah domin ya kira ta.

Ba ta bata lokaci ba ta dauka. Ya tambaye ta tana ina ga shi nan ya kawo mata ziyara. Duk da ta yi mamaki amma hakan bai hana ta kwatanta mishi inda take ba. Babu bata lokaci suka gano wurin.

Sanye take da pink din abaya wadda ta bude sosai daga kasanta, sai ta dora lab court a kai da karamin farin hijabi ta cusa shi daga can cikin lab court din. Ita da Muhammad Saddam ne yana ta zuba mata barkwanci ita kuma tana dariya tana kallon shi.

Wani irin tukukin kishi ne ya kama Ishraq a lokacin da ya hada ido da su. A take launin idanuwanshi suka canza. Bugun zuciyarshi ya sauya. Da saurinshi ya iso gaban Muhammad din yana cin kwalarshi.

End of chapter

Dan-dan-dan-dan-dan-dan!

Ga Ishraq da cin kwalar dan Sarki😂

Ko yaya wannan harkallar za ta kare?

Ku ci gaba da bibiyar alkalamina.

Princess Amrah

RAZ 2Cike da tsana Mahboobah ke watsa mishi kallo, tana ganin yadda Khalid ke kokarin shiga tsakaninsu amma abu ya gagara, sai na Saddam duka Ishraq din yake yi.

“Wai Ishraq ba ka da hankali ne ba za ka daina dukan shi ba? Me ya yi maka? Ina ruwanka da shi kawai daga zuwa za ka hau bawan Allah da duka?” Cikin fushi Khalid Zannah ke fadin wadannan maganganun. Ishraq din kuwa sai huci yake bayan ya saki Muhammad Saddam da ke ta faman sauke ajiyar zuciya.

“Kuma wallahi duk ranar da na sake ganin ka da Matata sai na wujijjiga ka. Sai na hada maka jini da majina. Ka kiyayi shiga gonata domin kuwa ruwa ba sa’an kwando ba ne ba.”

A gabanshi Mahboobah ta matso tana mishi kallon sama da kasa, kafin cikin takaici ta ce,

“Point of correction Ishraq Sulaiman…”

Kallon mamaki yake bin ta da shi, ta yadda take ambatar sunanshi kai tsaye wanda a baya ko alama ba ta gwadawa saboda tsananin kaunarshi da take yi.

“Ni ba matarka ba ce ba, kar ka manta shekararmu biyu da wata bakwai da yankewar igiyar aurenmu. Don haka ni ba matarka ba ce ba, ba kuma zan taba zama matarka ba. A da dai da mummunar kaddara ta bibiye ni na nace ma wahaltaccen aurenka, amma banda yanzu Ishraq. Ban da wannan lokacin. Ina so ka san cewar na tsane ka, na tsani ko jin muryarka, na tsani ganin fuskarka Ishraq Sulaiman.”2

Kanshi ya dafe da hannu daya, sannan ya dafe gefen zuciyarshi da gudan hannu. Tamkar ana buga guduma a kan da zuciyar haka yake ji. Wasu irin jijiyoyi yake jin suna tasowa a saman kanshi, suna ratsa fatar kan, suna shiga ta ko’ina, suna zarcewa har cikin kwakwalwarshi.

“Idan don ‘yarka na wurina ne ya sa kake bibiyata, har kake iya ambatata da matarka to na hakura da Ameerah, ka je ka dauke ta ta koma inda kake. Ba da Ameerah na fado duniya ba, don haka da ita da babu duk daya suke a wurina, kuma zan iya rayuwa ko ba ta tare da ni.”

Gyada mata kanshi yake yi, yana jin saukar hawayen da bai san sadda suka fara fita ba. A kasa ya duke, a gabanta, ya hada hannuwanshi duka biyu alamar magiya, yana fadin,

“Don Allah ki yafe min Mahboobah, ki yafe min duk abubuwan da suka faru a baya. Na sani ni mai laifi ne, amma na tuba, na yi nadamar duk abubuwan da na aikata miki. Ki tallafi zuciyata Boobah, ki rufa wa rayuwata asiri ki dawo mu ci gaba da rayuwar aurenmu. Na yi alkawari zan shayar da ke giyar soyayya, zan kyautata mu’amularmu, zan tabbatar miki da cewa ina son ki da dukkan zuciyata. Ba don halina ba don Allah Mahboobah…” Kuka ya ci karfinshi a duken.

Tausayi sosai ya ba Khalid, ya kama shi ya mikar tsaye amma ya sake komawa gabanta ya duka. Idonta a cikin nashi ta ce,

“Na tsane ka Ishraq, ba na sha’awar komawa a karkashin inuwarka. Ban taba nadamar wani abu ba a rayuwata sama da aurenka da na yi, sama da naciyar soyayyarka. Na kasa yafe wa kaina, yadda na zama mai kaskantar da kaina a gabanka, na danne duk wata daraja ta ‘ya mace da Allah Ya ba ni, na gwada maka soyayya fiye da kowa na duniyata. Amma Ishraq ka take soyayyata, ka tattake kyautatawata, ka wofintar da darajata, sannan a karshe ka illata zuciyata. Ka fice min daga rai, a yanzu yadda nake jin ka wallahi ban taba tsanar wani mahaluki ba sama da kai Ishraq. Ka rufa ma kanka asiri ka fita daga sabgata. I hate you with all my heart.”

“Mahboobah…”

Yana son ci gaba amma ya ji an cafke shi. A zaton shi ko Khalid ne, sai ya yi kokarin fizgewa amma ya ji an kara rike shi gam. Daga kanshi da zai yi ya ga mutum hudu sanye da kaya irin na dogarawan gidan Sarki, dukkansu hannuwansu rike da sharta-shartan bulalai masu kai uku.

STORY CONTINUES BELOW

A tsorace yake bin su da kallo, idanuwanshi a bude yana mamakin dalilinsu na rike shi.

“Wallahi idan ka nemi kawo min wargi zan zabga maka wannan bulalar a gadon bayanka. Mu tafi kawai.” Wani dogari ya fada yana jan hannun Ishraq din.

“Kamar ya mu tafi…ina za ku kai ni? Me na yi Muku?” Yake jero musu tambaya yana kallon Khalid da ya kasa daina mamaki shi ma.

Gyaran murya Muhammad Saddam ya yi, ya iso gabanshi, baki daya wannan walwalar da aka san shi da ita babu. Fuskarshi babu alamun annuri, kamar ba shi ba, ya ce,

“Da karamar kwakwalwa irin taka, haka kawai daga ka same ni tare da Mahboobah ba ka san ko waye ni ba ka hau dukana. Kuma na ki biye maka amma ka kasa daina duka na, ka ki saki na. Dan uwanka na raba ka kana sake dawowa kana dukana. To ina so ka sani, sai ka yi da na sanin dukana, sai ka san cewa ka daki Muhammad Saddan d’a namiji tilo a wurin Sarkin Zazzau, Mai martaba Abubakar Saddiq na biyu. A yau za a hada maka jini da majinar da kake ikirarin za ka hada min. Ku tafi da shi.”

Zizzillewa ya hau yi, da taurin zuciya irin nashi kuma bakinshi ya gagara mutuwa. Cewa yake,

“Ban yi da na sanin dukanka ba. Kuma ko yanzu na samu nasara zan sake dukanka matukar ba ka rabu da matata ba. Mahboobah mallakina ce, ni kadai. Don ni aka yi ta ba don wani katon banza…”

Shiru ya yi sanadiyyar wata irin lafta da dogari guda ya kai mishi. Ya ji zafin dukan saboda ya shige shi sosai. Dolen shi ya yi shiru yana jin radadin dukan na shigar shi ta ko’ina.

A rude Khalid ya isa gaban Muhammad Saddam. Cikin magiya yake mishi magana,

“Don Allah ka rufa mana asiri Muhammad, ka yi hakuri ka yafe mishi. Wallahi ba a cikin hayyacinshi yake ba. Ishraq ba haka yake ba, ba halinshi ba ne ba shiga rayuwar wasu. Kaddara da soyayya ce ta mayar da shi haka. Ka yi hakuri ba don mu ba, don Allah.”

“Kar ka kara cewa ba a cikin hayyacina nake ba Khalid Zannah. Kuma ka daina ba shi hakuri an je an daka din.”

Sake lafta mishi bulalar aka yi amma duk da haka Ishraq bai yi shiru ba. Hakan ya tabbatar wa da Muhammad Saddam lallai da gaske Ishraq din ya zauce. Ya umurci dogarawan cewa su kyale shi kawai ya tafi.

“Ranka ya dade Yerima, ai da ka bari mun lallasa shi. Watakila idan ya sha kashi zai dawo hayyacinshi.” Wani dogari ya fada yana kara sakar ma Ishraq din da bulala guda daya.

“Ku rabu da shi kawai ai kuna ganin wannan kun san bai cika ba.”

Ci gaba Ishraq ya yi da faffada masa magana Khalid na toshe mishi baki. Da kyar ya ja shi ya saka a gaban mota, ya karbi makullin motar ya tada da gudu suka bar wurin.

Sai da suka nisa da tafiya sannan Khalid ya kalle shi ya ga yadda wuyanshi har zuwa hannunshi suka yi burdin bulalar da ya sha.

“Haka kawai kana zaman zamanka Ishraq ka jawo ma kanka bala’i. Yanzu duba ka ga yadda fatarka ta yi don Allah.”

Tsaki Ishraq ya yi bayyananne yana janye rigarshi ya daga ta sama. Mamaki ne ya kama Khalid ganin yadda bayan Ishraq din ya farfashe kamar wanda aka ma fin bulala goma.

“Innalillahi Ishraq ka ga bayanka kuwa?”

“Dalla mallam ka yi driving mu kar ka kada mu a mota.”

STORY CONTINUES BELOW

Tsaki ya yi shima Khalid din yana fadin, “Ba ni na kar zomon ba ai rataya aka ba ni.”

Cika yake fam Ishraq yana batsewa. “Kuma wallahi ba zan rabu da ita ba. Son ta ma yanzu na fara ni da shi shege ka fasa.”

“Tilasta mata za ka yi ta so ka?” Khalid din ya gaggauta tambayarshi cike da mamaki.

“Ko tana so ko ba ta so dolenta ta aure ni a karo na biyu. Wancan karon da take so na duk da ba na son ta ai a hakan na aure ta. Don haka sai a rama wa kura aniyarta.”

Kallon mamaki kawai Khalid ke bin shi da shi. Tamkar dai wanda ya zautu.

“Ina son ta Khalid, soyayya ba yar karama ba. Ina jin radadi a zuciyata na rashin ta a tare da ni. Ban san gaibu ba, amma matukar rayuwata ta ci gaba da tafiya a haka babu Mahboobah a cikinta to komai zai rinka zuwa da tangarda. Da gaske ina kaunarta Khalid.”

Wani irin kuka ya ci karfinshi, ga tsananin azabar bulalar da ya sha, ga kuma azabar da zuciyarshi ke yi mishi.

“Ka yi hakuri Ishraq ka sassauta ma kanka. Ba dole sai da Mahboobah ba ne za ka iya ci gaba da numfashi. Ko da ita ko babu ita za ka iya rayuwarka. Ka tumbuke ta daga zuciyarka, ka dauka tamkar ba ka taba sanin ta ba. Kamar dai yadda ka yi da soyayyar Ameerah Muhammad…”

“Ina…!” Ishraq din ya fada tamkar zai kai ma Khalid duka. “Khalid me ya sa kake magana sai ka ce dai wanda bai san SO ba? Kai ne fa a baya kake mun bayanin SO da yadda mutum yake ji idan yana SON mutum. Ta yaya kake tunanin zan iya tumbuke soyayyar halittar da zuciyata ke kwadayi da muradinta? Ka fada min Khalid ta ina zan fara?”

Dafe kanshi Khalid din ya yi, yana rasa ta inda ma zai bullo ma lamarin.

Bayan sun isa Kaduna gidan Khalid suka fara wucewa. Sai da ya ja ma Ishraq kunne a kan ya kula da tuki sannan ya ba shi makullin motarshi ya tafi. Kai tsaye gidan Mami ya wuce. Yana son yin tozali da ita, yana son dora idanuwanshi a cikin nata, watakila ganin ta zai sassauta mishi abin da yake ji a cikin zuciyarshi. Watakila jin muryarta zai iya sanyaya ruhinshi. Rarrashi da nasiharta yana tunanin za su iya yin tasiri gare shi, su janye nannauyan abin da ya yi tsaye a tsakanin kirjinshi.

Ko gyara parking bai yi ba ya fita. Bai same ta a falo ba da ma kuma ya san haka, saboda ka’idarta idan ta yi sallar maghrib ba ta fitowa har sai ta yi isha’i.

Ko sallama bai yi ba ya shiga dakin nata, da karfi ya zube a gabanta, yana fasa kuka mai sauti.

Salati Mamin ta hau yi tana tambayarshi lafiya. Cikin kuka yake gyada mata kai.

“Ba lafiya ba Mami. Na kusa mutuwa.”

A tsorace take Mamin, da rawar murya ta ce “Wannan wace irin mummunar magana ce kake yi likita? Ka fada mun me ya faru da kai?”

“Mami…idan har Mahboobah ba ta amince ta dawo gidana ba, tabbas mutuwata tana daf da ni. Wani irin radadi nake ji a kasan zuciyata Mami. Son ta nake yi da dukkan zuciya da ruhina. Ban taba jin wani abu makamancin wanda nake ji a yanzu ba Mami. Ki taimaka mun ki sanya ta ta so ni, in dai ba kya so ki yi asarar tilon danki Mami.”

Rasa ma abun fadi ta yi sai bin shi da kallo take yi, yadda yake kuka bilhakki tamkar karamin yaro. Bayanshi ta hau bubbugawa a hankali tana fadin,

“Dukkanin tsanani yana tare da sauki Ishraq. In shaa Allahu babu abin da zai same ka. Ko da Mahboobah ko babu ita a duniyarka ba za ka mutu ba har sai idan lokacinka ya yi. Ka nutsu ka yi min bayanin abin da ya faru, ji yadda duk jikinka ya yi burdi sai ka ce wanda aka zane.”

Bai san ta inda zai fara ba ta labarin abin da ya faru ba. Bai san ta yaya zai fada mata dogarawan sarkin Zazzau ba ne suka zane shi ba.

“Mami komai ya same ni a yanzu ta silar soyayyar Mahboobah ne. Ki nemo mun soyayyarta Mami idan ba haka ba kin kusa rasa ni.”

Da zarar ya yi wannan maganar sai gabanta ya fadi. Ba ta son jin haka ko kadan. “Okay Okay, ka kwantar da hankalinka, in shaa Allahu zan yi magana da ita, za ta so ka Ishraq. Soyayya ba ta faduwa kasa banza, yarinyar nan ta so ka a baya ba na tunanin a yanzu ma babu soyayyar. Za ta dawo dakinka da izinin Allah.”

*

Tun bayan tafiyar su Ishraq ta duke a wurin tana kuka, kukan da ita kanta ta rasa dalilinta na yin shi. Ta dai san ba zai rasa nasaba da tada mata tsohon tabon da ya warke mata ba. Rarrashinta sosai Muhammad Saddam ke yi, da kyar ya samu nasarar sanya ta ta yi shiru.

“Me ya sa za ki bari wani gardi can ya lalata miki mood? Kar ki sake yarda karamin abu irin haka yana canja yanayinki. Ki bar shi da haukan da ya same shi ma kadai. Kuma idan har ya zalunce ki alhakinki ba zai taba barin shi ya ji dadin rayuwa ba. Rashin sukuni ma yanzu ya fara.”

Dago rinannun idanuwanta ta yi ta kalle shi, wani irin shock ya ji ya shige shi Muhammad Saddam, ya yi gaggawar janye duban shi daga gare ta, yana neman rasa dukkan nutsuwarshi.

“Muhammad ka fada mun gaskiya mene ne a zuciyarka game da ni? Me kake ji a kaina? Mutane da dama sun sha birkita alakata da kai daga kawance zuwa can wani tunanin nasu, sai dai ina karyata hakan saboda ni dai a nawa bangaren babu komai face friendship. Amma a yanzu, ta cikin idanuwanka na hango akasin haka. Abin da nake tunani ba shi na gani ba a ciki Muhammad Saddam.”

Tun da yake a rayuwarshi bai taba soyayya ba. ‘Yanmata dai suna kawo mishi tayin kansu, amma bai taba karba ba. A kan Mahboobah ne ya fara son wata mace, soyayya kuma mai tarin yawa. Wannan dalilin ne ya sa ya ma rasa ta inda zai fara fada mata. Yana gudun kar ta bad’a mishi kasa a idanuwa. Kar ta tsane shi kamar yadda take tsanar duk wani namiji da zai ce yana son ta.

Cikin rashin kwarin guiwa yake kallon ta, so yake ya fada mata sirrin zuciyarshi, so yake ya shaida mata tarin kaunar da yake yi mata. Sai dai, bai da kwarin guiwar yin hakan, bai san ta inda zai fara ba, wani irin kwarjini take yi mishi.

“Ka fada min gaskiya Muhammad. So na kake yi ko? Tun yaushe ka fara so na?”

Dukar da kanshi ya yi kasa, yana fadin,

“Tun ba ki san ni ba, tun ranar da na fara ganin ki na ji ina son ki. Ba kawance na kira in nema a wurinki ba MB, soyayyarki na kira in nema, kika yi mini kwarjinin da dole na canja akalar ra’ayina.”

End of chapter

Hello cupcakes…ya kuke ya gida ya al’amurra? Fine in shaa Allah.

Ga labari ya nisa, ga kuma azumi ya zo.

A nan zan diga aya a labarin a yanzu, har sai bayan azumi idan Allah Ya nuna mana za mu dora.

Na gode sosai da jimirin bibiyar wannan labarin. Na gode da voting dinshi da kuke yi.

Ina mai farin cikin shaida muku cewa labarin BAKUWAR FUSKA har yanzu da sauranshi, don haka ku daure damarar ci gaba da karatu bayan azumi idan Allah Ya nuna mana.

Ina muku fatan alkhairi. Allah Ya sa mu fara azumi lafiya mu gama lafiya. Allah Ya sa mu yi karbabbiyar ibada Ya sa muna daga cikin bayin da za a ‘yanta.3

Princess Amrah

RAZ 2Gyada kanta take yi, tana jin sauyin yanayi a tattare da ita, baki daya mutuncin Muhammad Saddam take ji yana raguwa a cikin zuciyarta. Kimarshi na dunkule kanta, tana neman rabuwa a tattare da ita. Da yatsunta biyu na hannun dama take share hawayen da ke kai-komo a saman kumatunta.

“Ka yi kuskure, ka yi kuskuren fadawa tarkon soyayyata Muhammad Saddam…”

“Ban yi kuskure ba, zuciyata dai ce ta yi kuskure Mahboobah. Da a ce ina da magani da tuni ba mu kai matakin da muke a kanshi ba yanzu. Da ba za ki ma san da ni ba a duniyar nan. Da tun sadda na fara ganin ki ban bari na shiga rayuwarki ba.” Zafi yake jin zuciyarshi na mishi. Gumi yake jin yana tsatssafowa ta tsakanin matsirar gashin jikinshi. Ya ma kasa ko hada ido da Mahboobah, gani yake idan ya hada ido da ita zai iya rasa dan sauran kwarin guiwar da ya yi mishi saura.

“Ba na tunanin akwai wani namiji da zan iya so a yanzu Muhammad. Ban taba yi maka kallon masoyi ba, sai dai na girmama matsayinka a zuciyata, na martaba ka fiye da kowanne namiji. Ba zan iya soyayya da kai ba Muhammad Saddam, ka yi hakuri kawai!”

Kokarin barin wurin take amma ta ji an take mata kafar abayarta, ta juyo ta kalli Muhammad Saddam da ke durkushe a saman guiwoyinshi. Idanuwanshi sun kada sun yi jajur. Kallo guda ta yi mishi ta dauke kai, don ma kar kallon nashi ya yi tasiri gare ta.+

“Ka bar ni in tafi Muhammad.”

“Ki yi hakuri Mahboobah. Ki tallafi zuciyar da ta jima kwadaice da soyayyarki. Ki agaji zuciyar da ke bugawa cike da kaunarki. Ban taba ba, ban taba soyayya ba Mahboobah, ke ce mace ta farko wadda na fada tarkon soyayyarta, ba na jin kuma akwai wata a gaba.  Ko kina k’i na ne?” Sai a yanzu ya iya hada ido da ita, yana jin saukar hawayen da shi kanshi bai san sadda suke fitowa daga idanuwanshi ba.

Gyada kanta ta yi tana sake dauke dubanta daga gare shi. “Ba na k’in ka Muhammad, amma kuma ba na maka Son Soyayya.”

“Na yarda mu ci gaba da rayuwa a haka, na miki alkawarin sannu a hankali zan koya miki, za ki fara yi min Son Soyayya, wanda nake fatan ya kai mu ga mallakar junanmu.”

Murmushin takaici ta saki. Tana jin daf take da zame rigarta da ya take ta bar wurin.

“Zan ba ki dama Mahboobah, ki je ki yi nazari, ki yi tunani game da soyayyata. Na ba ki tun daga nan har zuwa shekaru biyar ma masu zuwa. Zan ci gaba da jiran ki har zuwa ranar da zuciyarki za ta gama yanke hukunci a kaina.” Daga haka ya mike a saman kafafuwanshi, ya taka ya bar wurin ba tare da ko waiwayenta ya sake yi ba.

Hanyar hostel ta kama, tana jin zuciyarta na mata zafi. Tana isa daki ta fada ruf da ciki, tana sakin wani irin kuka, kukan da ke fita tun daga zuciyarta yana ratsowa tsakanin idanuwanta.

Ya za ta yi da soyayyar Ishraq Sulaiman da ta taso mata sabuwa dal a yanzu? Ya za ta yi da alkawarin da ta daukar wa kanta da kuma ahalinta? Ya za ta yi da Muhammad Saddam da ya sadaukar da farin ciki da lokacinshi a kanta?

Dukka wadannan tambayoyi ne da ita kanta ba ta da amsoshinsu. Tambayoyi ne masu radadi idan ta tuno da amsoshinsu. Ya za ta yi?

Ta ji wayarta na ringing, da ta duba ganin bakuwar lamba ta yi, sai ta yi silencing wayar ta kifar da kanta tana ci gaba da kukanta.

Kamar da wasa haka Mahboobah ta kai tsakiyar dare ba tare da ko rintsawa ta yi ba. Tausayin Muhammad Saddam take ji yana ratsa duk wata kusurwa ta zuciyarta. Sai dai me, ba ta jin Son shi ko alama, ba ta jin za ta iya soyayya da Muhammad Saddam duk kuwa da tarin halaccin da ya yi a duniyarta.

STORY CONTINUES BELOW

Washe gari ta sha baccin safe saboda rashin wadatuwar na dare. Idanuwanta sun yi luhu-luhu da ta tashi. Ta duba wayarta, missed calls na lambar jiya ta gani ringis. Sai da ta yi wanka ta sha ruwan lipton sannan ta latsa kiran lambar.

Bayan an dauka ta yi sallama, Mami ta ansa mata cikin sakin fuska. Jin muryar Mami ya sanya ta jin matsanancin faduwar gaba. Ta dake ta gaishe ta.

“Ya makaranta? Ashe kin jona ABU ba mu da labari. Kin yar da ni Mahboobah.”

Murmushin karfin hali ta saki Mahboobah, tana fadin, “Ba haka ba ne Mami, yanzu ba ni da wadataccen lokaci ne kamar da. Da yake medicine ne na fara.”

“Ma shaa Allah.” Mami ta fada, tana dorawa da “Allah Ya taimaka Ya yi jagora.” Ta yi shiru, tana son ci gaba da magana amma ita kanta tana jin nauyin maganar. Sai dai kuma, idan har ba ta daure ta yi maganar a yanzu ba, rayuwar tilon danta Ishraq ke cikin garari. Ba ta fatan yadda ta ga rashin nutsuwa lullube da zuciya, ruhi, da kuma gangar jikinshi su ci gaba da yalwata. Babban burinta shi ne ta ga Ishraq a farin ciki. Ta sani shi din mutum ne mai girman laifi a rayuwar Mahboobah Bukar. Mutum ne da ya kafa shudadden tarihin da ke zaune daram a zuciyar Mahboobah. Gare ta, Ishraq, da kuma sauran mutane ne yake shudadde, amma ga Mahboobah, abu ne wanda ba zai fita da sauki daga zuciyarta ba. Lamari ne mai girman tarihin da ke da wuyar kakkabuwa daga duniyar mutum.

Ta sauke ajiyar zuciya Mami, tana runtse idonta, tana jin miyau mai daci na niyyar hana ta maganar da ta yi niyya. Da kyar ta samu ta hade shi, cikin dakiya ta ce,

“Ta yiwu kin san dalilin da ya sa na kira ki Mahboobah, ta yiwu kuma ba ki sani ba…”

Ji ta yi tamkar ta datse wayar, tamkar ba za ta iya sauraren maganganun da tsohuwar surukar tata ke da niyyar fadi ba. Sai dai, kanar yadda ba za ta iya datse wayar Mommy ba, haka ta Mami ma. Mami na da girma da darajar da har abada ba za ta taba shafe su daga rayuwarta ba. Ta daure, ta ce

“Ban san dalilin kiran ba Mami.”

“Tun bayan rabuwar aurenku da Ishraq, ban taba fadar komai ba gare ki, maganar ma ba ta taba hada mu ba. Ina so ki saurare ni Mahboobah, ki kuma yi wa maganata kyakkyawar fahimta. Na sani Ishraq mai laifi ne gare ki, mai laifi ne ga ahalinki baki daya. Amma ina so ki dauki hakan a matsayin rashin cikar shi goma ne, kamar yadda dukkan dan adam yake tara bai cika goma ba. Ki dauka cewa wannan shi ne nakasunshi.”

Ji take kamar Mami na son soko son zuciya a cikin maganar tasu. Idan ba haka ba, duk tarin abubuwan da Ishraq ya yi mata a baya amma Mami a matsayin tara ta dauki Ishraq? Idan za a tambaye ta, to da za ta ce Ishraq biyu yake a cikin goma, bai ma kai ko rabi ba ballantana a yi zancen tara.

“Ishraq ya nadama Mahboobah. Ya tuba tsakaninshi da Allah. Da dukkanin zuciyarshi yake son ki. Mahboobah na hango idanuwanshi cike da kaunarki. Na hango rashin walwala a tattare da komai nashi, ki yi hakuri ki tsamo shi daga wannan duniyar da yake cikinta. Ki dawo dakinki ki rungumi Ameerah, ku ci gaba ca hakuri da juna.”

Wani irin takaici take ji yana ratsa zuciyarta. Tunowa take da duk rayuwar da ta shiga ta kunci a gidan Ishraq Sulaiman. Tunowa take da bakin fentin da ya shafa mata. Kalmar mazinaciya da ya rinka jifarta da ita take tunawa, tana jin ba za ta iya kara rab’arshi ba har abada. Ko Ishraq ne autan maza za ta iya hakura. Ita auren ma dukka ya fice mata daga rai ne.

“Zan ba ki lokaci Mahboobah, ke ba yarinya ba ce ba ballantana a tirsasa ki dole. Sai dai kamar yadda na fada a baya, Ishraq ya nadama, ya gane kuskurenshi na baya. Ki tallafi zuciyarshi ki dawo gare shi. Ki je ki yi nazari sosai a kan haka. Forget the past Mahboobah, ki fuskanci rayuwarki ta gaba. Ba ki san kalar namijin da za ki hadu da shi ba a gaba. Komai lalacewa kin san Ishraq ya san ki. Kin san abin da yake so shi ma ya san wanda kike so. Zaman ku zai yi dadi fiye da tunaninki. Ki yi tunani. Zan kira ki bayan kwana uku.” Daga haka Mami ta tsinke wayar.

Ta rasa inda za ta sanya kanta ta samu sassauci. Zuciyarta zafi take mata ta yanda har yake hudowa a fatar jikinta. Tamkar mai zazzabi haka jikinta ya dauki zafi. Ba ta san inda za ta sa kanta ba. Muhammad Saddam ne kadai wanda ke warware mata damuwar ta, shi ne wanda ke sanya ta nishadi idan ta rasa, mai dawo da walwalarta a duk sadda ta shiga damuwa. Ga shi a yanzu har da shi cikin jiga-jigan damuwar tata. Ta rintse idonta tana tunanin mafita, kafin Mommy ta fado mata a rai. Ta latsa kiran ta, tana ci gaba da bayyanannen kuka.

Cikin kidima Mommy ke tambayarta silar kukan nata, ta kasa fadar komai sai karfafawa ma da take yi.

“Mahboobah ki yi shiru dan Allah ki yi min bayanin abin da yake damun ki.”

“Mommy…” kawai ta iya fadi, tana rasa ta inda ma za ta fara bayyana mata abin da yake faruwa.

“Mahboobah ba ki da lafiya ne? Ko ciwon zuciyar ne ya taso? Ki fada mun don Allah me yake faruwa. Kin kada mun gaba matuka, hankalina a tashe yake. Ina son sanin damuwar ki Boobahna.”

Ta yanayin maganarta kadai za a fahimci karayar da zuciyarta ta yi.

“Mommy lafiya lau nake. Amma dai ina cikin matsala, ki saka ni a addu’a.”

Jin tana lafiya ya sanya Mommy sauke nannauyar ajiyar zuciya hade da sakin hamdala a bayyane. “Ina miki addu’a a kodayaushe Mahboobah. Amma me yake faruwa da ke?”

Cikin sanyi Mahboobah ta bayyana wa Mommy kaf abubuwan da suka faru, har kiran ta da Mami ta yi, da kuma yanda suka yi.

“To ai ni ban ga wata matsala ba a nan wadda har za ta gusar miki da farin ciki Mahboobah. Abu mai sauki ne wannan. Ki shirya gobe ki zo gida weekend mu yi magana a zahiri. Amma ki kokarta ki saukaka ma kanki, ba na son wata matsala ta taso a gaba. Ki kwantar da hankalinki. In shaa Allahu komai zai zo da sauki.”

Ta share kwallarta wasu na sauko. “To in shaa Allahu Mommy.”

“Yauwa ‘yar albarka. Sai kin zo din.” Daga haka suka yanke wayoyin nasu, zukatansu cike da damuwa su duka biyun.

Washe gari tana fitowa lakcar karfe sha biyu ta hada tarkacenta a dan karamin kit ta fito, zuciyarta cike da damuwa, ga kewar Muhammad Saddam da take tsananin ji. Wani irin jiri take ta jin yana neman kwasarta, a haka dai ta daure ta fito gate, ta tari mai adaidaita ta ce ya fitar da ita kan express ta samu motar Kaduna. Bayan sun isa ta sallame shi, ya fito mata da kit dinta, ita kuma ta dauki handbag dinta ta fito, hannunta daya dafe da goshinta da take ji kamar zai tsage saboda azabar ciwon kai.

***

“Doctor ya halin mara lafiyan nan? Tun dazu na gaza samun kwanciyar hankali. Ina tsananin tausayinta.”

“Da sauki Alhamdulillah! Jininta ne ya hau sosai, shi ne ma ya yi sanadiyyar zubewar da ta yi. Kuma hawa sosai. Cututtukan zamanin nan babu babba babu yaro. A da, idan ka ga hawan jini ya sarkafi mutum to ya manyanta ne. Amma yanzu kam har kanana ma kamawa yake yi. Ta yiwu tana da wani ciwo ne wanda ya yi silar samuwar BP din. Ta iya yiwuwa kuma damuwa ce gare ta wadda har ta yi yawan da ya sanya jininta mugun hawa. Amma in sha Allahu zai sauka. Ina jira ta farka ne sai mu yi magana sosai.”

Gyada kanshi ya yi mutumin yana mika hannunshi na dama ga likitan, suka yi musabaha ya fita, a zuciyarshi yana jin tausayin matashiyar, a wani bare na zuciyarshi kuma yana jin zai iya zama warakar damuwarta.

NOOR!

Hello cupcakes! Fatan mun sallata lafiya. Ya kuke ya gida da iyali? Allah sa na same ku lafiya. Ya hakurin jiran BKF? Am back😍in shaa Allahu za mu ci gaba daga inda muka tsaya.

Masu bibiyar wannan labarin na gode sosai. Allah Ya bar zumunci.

Princess Amrah

RAZ 2Wayarta da ke hannunshi ya ji ringing dinta. Ya duba ya ga an rubuta LOML❤️. Kamar kar ya dauka da ya ga sunan, sai kuma ya ga ya kamata ya dauka din, saboda makusantanta su san halin da take ciki.

Ya dauka da sallama a bakinshi, sai ya ji muryar dattijuwar mace ta amsa sallamar. Ya gaishe ta cikin girmamawa ta amsa. Tana kokarin tambayar Mahboobah don ita a tunaninta ma ko shi ne Muhammad Saddam, ta ji ya ce

“Dazu ne a kan hanyata daga Hunkuyi zan tafi Kaduna, a kan express Zaria na ga mai wannan wayar zube a kasa, mutane kowa yana tsoron tinkararta. Shi ne na faka motata na isa inda take, na kanga kunnena na ji bugun zuciyarta. Sai na dauke ta na kai ta asibiti. Yanzu haka tana karkashin kulawar ma’aikatan lafiya ne.”

“Innalillahi wa innaa ilaihi raji’un!” Mommy ta fada cikin kidimewa. “Na gode sosai da taimako bawan Allah. Kuna wace asibiti ne? Ga mu nan zuwa in shaa Allahu.”

Cikin kwantar da hankali ya ce “Kada ki daga hankalinki Mama. Ciwon ba wani mai tsanani ba ne. Da yardar Allah ma kafin ku iso ta gama warwarewa. Yanzu ma tana barci ne. Zan tura miki text na address din asibitin.”+

Sai kuma Mommy ta samu kanta da tsorata. Idan fa wani macuci ne ya cutar mata da Mahboobarta kuma yake son hadawa da danginta? Ba ta san sadda hawaye ya hau sintiri a saman fuskarta ba. Ta ma rasa ta inda za ta bullo ma lamarin.

Fahimtar ta tsorata da ya yi ne ya sauke ajiyar zuciya, tuna cewa asibitin sanannen asibiti ne, duk wanda ya san Zaria to ya san Almadinat Hospital.

Ya tsinke wayar yana tura mata sunan asibitin hade da address dinshi.

Aliyu ta kira a waya, ta ci sa’a daidai zai shigo gida sai bai dauki wayar ba, jin muryarshi kawai ta yi yana sallama.

A tsorace ta isa gabanshi tana labarta mishi komai. Shi din ma hankalinshi ya tashi.

“Zuwa Zaria ya kama mu Aliyu.” Ta fada cikin kuka.

“Ki daina kuka Mommy in shaa Allahu za ta samu sauki. Ki dauki abin da za ki dauka mu tafi.”

Purse dinta kadai ta dauka da ma wayarta na hannunta. Suka fice daga gidan.

“Lokacin tashin Ameerah daga makaranta ya yi. Mu biya mu dauke ta Mommy?”

A yanda ta matsu ta yi tozali da Mahboobah ji take idan aka tsaya daukar Ameerah an bata lokaci. Cewa kawai ta yi ya kira Ishraq ya dauke ta sai ya wuce da ita can wurin Mami, in ya so daga baya an dawo da ita.

Hanyar Zaria suka kama, bayan sun isa ta kira lambar Mahboobah mutumin ya dauka, ta ce ga shi nan sun shigo Zaria.

“To sai kun iso Mama.” Ya fada yana komawa waje wurin parking space zaman jiran isowar su.

Da suka iso bai wahala ba wurin gane su. Ganin kamanninta da na marar lafiyar karara ya sa ya gane su ne. Ya isa gare su ya gaishe da Mommy, sannan ya mika hannunshi suka gaisa da Aliyu.

“Mun gode sosai bawan Allah. Mun gode da taimakon Mahboobah da ka yi. Allah Ya saka da alkhairi Ya biya ka dukkanin bukatunka na alkhairi. Thank you so much.”

Da murmushi a saman fuskarshi ya amsa da amin, sannan ya yi musu jagoranci zuwa dakin da Mahboobah take. Har a lokacin bacci take yi ba ta farka ba. Saboda likita ya ce har da karancin barci ne ya assasa mata ciwon kai, ciwon kan kuma ya yi silar girdewarta ta fadi.

STORY CONTINUES BELOW

Gaba gare ta Mommy ta isa, ta soka tafin hannunta a cikin nata, hawaye na sauka a saman fuskarta.

“Mahboobah kuma haka Allah Ya yi da ke? Allah Ya ba ki lafiya Ya tashi kafadunki.”

Hannunta ta kara cusawa a cikin na Mommy, kamar da ma ta san a hannun wadda take, tana ci gaba da barcinta. Mommy ta rab’a a bakin gadon ta zauna, tana ci gaba da tofa wa Mahboobah addu’a.

“Aliyu ba mu yi sallah ba fa.”

“E, ai da yake kasaru ce kanmu Mommy. Amma dai mu samu mu sauke din, kafin nan kila Mahboobah ta farka. Abokina ina ne masallaci?”

“Mu je in raka ku. Har bangaren mata ma akwai.”

“Mun gode maka sosai bawan Allah, ba dai zan gajiya ba wurin shi maka albarka. Ba ka fada mana sunanka ba.”

Ya yi murmushi yana amsawa da amin, ya dora da “Sunana Noor.”

Mommy ta saki murmushi, “Sunan kuwa ya dace da mai shi. Haske mai zuciya mai haske.”

Dariya suka yi suna bin bayanshi zuwa masallacin cikin asibitin.

*

Bayan kimanin awa biyu Mahboobah ta farka. Da sunanAllah ta bude idonta, tana jin kamar mafarki ne take yi na faruwar komai. Da sauri Mommy ta yo kanta tana mata sannu.

“Mommy…” ta fada kasa-kasa, tana dorawa da “Me ya faru da ni? Me ya kawo ni asibiti?”

“Ba na son ganin hawayen nan Mahboobah. Wannan bawan Allah’n shi ne ya gan ki kin zube a bakin hanya sai ya dauko ki ya kawo wannan asibitin. Shi da kanshi ya biya kudin komai. Da na ji ki shiru ba ki isa Kaduna ba shi ne na kira wayarki ya dauka, ya mun bayanin duk yanda abun ya kasance. Amma Alhamdulillahi tunda kin farka. Mallam Noor ko za ka je ka sanar ma likitan?”

Duk maganganun nan da Mommy ke yi bai san tana yi ba. Kallon yadda Mahboobah ke hawaye kawai yake yi. Bai san yanda aka yi ba, amma zafin fitar hawayen nata yake ji. Idonshi ya dauke daga gare ta, yana son sanin dalilin shigar ta wannan halin, domin kuwa dole da walakin goro a miya. Ba zai yiwu ba yarinya mai karanci shekaru kamar Mahboobah a ce tana dauke da cutar hawan jini.

Ganin kamar hankalinshi ba ya kansu ya sa Aliyu gaggawar fita reception, nurses station ya je ya sanar musu farkawar Mahboobah.

“Ashe da na ce ki cire damuwar nan daga ranki Boobah ba ki cire ba? Me ya sa kika bari damuwa ta miki yawan da har ta zubar da ke kasa? Uhm me ya sa da kuruciyarki kike neman takassara kanki? Namijin banza da za ki kashe kanki a kanshi! Kar in kuma ji kar kuma in gani.”

“Mommy ni ma ba da son raina ba ne…”

“Da son ranki ne mana Mahboobah! Tun jiya na taushe ki a kan ki mayar fa komai ba komai ba ki sassauta ma kanki. Lamarin soyayya ya daina gusar miki da hankali.”

Kunnuwanshi ya kasa yana sauraron tattaunawar da ke fita tsakanin uwa da diyar. A take ya fahimci daga inda matsalar take. Wato soyayya ce ta jawo mata larurin hawan jini ashe!

“Mommy na rasa yanda zan yi. Mami na can na jiran hukuncina. Ga Muhammad Saddam da ya tafi cike da damuwa. Mommy dama mutuwa ta zo ta dauke ni da na fi jin dadi.”

“Hasbunallah! Kada ki yi sabo Mahboobah. Komai ya yi tsanani maganinshi Allah. Yanzu dai ki bari har ki samu sauki sannan mu ci gaba da magana. Lafiyarki ita ce gaba da komai.”

Suna cikin haka likita ya shigo. Biye da shi nurses ne guda biyu. Bayan ya musu ya mai jiki ya hau tambayar Mahboobah me take ji yanzu?

“Kaina yana ciwo, sosai.”

Kallon ta ya yi ya ce “Kanki ba zai daina ciwo ba matukar ba ki cire tunani ba daga zuciyarki kin rinka wadataccen barci.”

Ta tsura mishi ido, ya jinjina mata kai. “Da gaske idan kika ci gaba da tufkar da ba ta da warwara kina daf da rasa baren jikinki. Matukar kina yarda irin wannan girdewar ta kama ki watarana sai dai ki ji dif barenki guda ya tsaya da aiki paralyses ya kama ki. Ba fata nake miki ba, amma tabbas zuciyarki ta yi karanta da daukar matsalolin rayuwa.”

Hawaye Mommy ta share tana kallon likitan da ke magana cike da tausayi shi ma. Ya kalli Mommy yana tabbatar da ita ce mahaifiyarta. Ya ce, “Mama, ki kwakkwafe ta, ki rage mata wannan damuwar. Mummunan hawan jini ya kama ta, har ya kai 180. At her age a ce jininta ya kai dari da tamanin gaskiya akwai babbar damuwa. Kuma duk maganin da za a ba ta matukar ba ta cire tunani ko damuwar da ke gabanta ba aikin banza ne, don ba za su yi tasiri ba.”

“In shaa Allahu likita za ta kiyaye. Thank you so much.” Mommy ta furta tana kuka.

“Ki daina kuka Mama, in shaa Allahu za ta warke in dai an bi shawarar da na bayar.”

“Muna fatan haka Doctor.”

“Ba na so in fara ba ta maganin hawan jini don kar ya bi jikinta. Zan dai rubuta mata maganin ciwon kan da jiri, sai a samu ta yawaita yin barci, in shaa Allahu za su sauka.”

Bayan ya rubuta takardar maganin Aliyu da Noor har rige-rigen karba suke yi. Noor ya ce ya bari shi zai siyo amma Mommy ta ce ya yi hakuri dai Aliyun ya siyo, ai ya yi musu kokari sosai.

“Doctor ko za a iya ba mu refer mu koma Kaduna? Don ba mu da kowa a nan kuma ba mu zo da shirin kwana ba.”

Likitan ya ce da Mommy babu damuwa. Zai ba nurse takardar ta kawo musu.

Bayan sun tafi a mota Ishraq ya kira Mommy, ya gaishe ta ya tambaye ta ya mai jiki, yana dorawa da “Na kira dazu in ji ya jikin nata sai ba a dauka ba.”

Mommy ta ce “Da sauki sosai, mun karbo refer ga mu nan kan hanyar dawowa Kaduna. Asibitin Almadina za mu je.”

“Kun kusa karisowa ne Mommy in tarbe ku a can?” Ishraq ya furta don ya matsu ya ga yanayin jikin Mahboobah.

“Da dan saura Ishraq dan ko Jaji ba mu zo ba.”

“Duk da haka dai Mommy zan jira ku a can. Tunda Aliyu ya kira ni hankalina bai kwanta ba. Na dauko Ameerah ma daga makaranta amma ta dame ni wai wurinku take so. Ga shi kuma akwai Islamiyya. Ban san yanda za a yi ba.”

“Ka zo da ita kawai Ishraq, gida zan wuce daga asibitin ni, zan kira cikin kawayenta Haneefa ko Saleemah wata ta zauna da ita.”

“To shi kenan Mommy, sai kun iso.” Daga haka suka tsinke wayoyin, Mommy na mamakin sauyuwar Ishraq, da yanda duk ya rikice saboda ciwon Mahboobah.

Princess Amrah

RAZ 2Suna isowa Almadinat Hospital na Kaduna suka iske Ishraq zaune a reception zaman jiran su. Da sauri ya sha gabansu yana kallon Mahboobah da ke jigace, Mommy da Aliyu sun tallabo ta. Ya kasa dauke kallon shi daga gare ta, ganin yadda ta yi wani irin fayau, ta rame, idanuwanta sun firfito waje, kwantaccen gashin gaban goshinta ya bayyana. Sai ta kara yi mishi kyau sosai da kwarjini.+

Da sauri Malaman jinya suka yo kansu, ganin halin da take ciki ya sa aka kai ta emergency, Aliyu kuma ya bada refer letter din, ya bar Mommy da Ishraq tare da Mahboobah. Noor kuwa tun suna shigowa Kaduna ya musu sallama, dama ya karbi lambar wayar Aliyu da ta Mommy. Ya ba su wayar Mahboobah suka rabu.

Kamar yadda likitan Zaria ya fada wa su Mommy na Kaduna ma haka ya fada musu. Saboda babban abun mamaki ne a ce yarinya mai karancin shekaru kamar Mahboobah jininta ya haura ma 180. Mommy ta masa alkawarin da yardar Allah za su kiyaye.

Sai da Saleemah da Haneefa suka zo sannan Mommy ta ce za ta koma gida. Nan fa ake yin ta, domin kuwa Ameerah cewa ta yi babu inda za ta je a bar ta wurin Amminta. Da Mommy ta takura ta a kan su tafi ma kuka ta fasa tana kama karfen gadon Mahboobah.

“Wai Ameerah ya za a yi in bar ki ku kwana asibiti kamar ni ma ke ce.” Mommy ta fada tana gyada kanta. “Aliyu maza dauko ta mu tafi gida dare na yi.”

“Wayyo Mommy ki daina yi mata tsawa.” Saleemah ta fada tana marairaice fuska.

“Kun ga masu diya su fa ba a isa a fadi laifin Ameerah ba. To ai ku da kuka iya lallaba sai ku lallaba ta, in dai Ameerah ce ba sanin mutunci ta yi ba.”

Dariya aka dauka duka dakin. Haneefa ta ce “Ta san mutunci sosai mana Mommy. Ko Ameerahna?”

Gyada kai Ameerah ta yi cikin kuka alamar a’a. Mommy me za ta yi ba dariya ba ta hau tafa hannuwa. “Ai dama na fada muku ba ta san mutunci ba ga shi nan iyayen ma ta gwasale su.”

“Mamana…ki yi hakuri ki bi Mommy ku tafi gidan kin ji. Kin ga gobe akwai makaranta.”

Ta kara noke kafada tana kallon Ishraq da ke mata maganar.

“Mommy ku tafi kawai idan ta yi barci zan kawo ta.”

“To Ishraq. Mun gode sosai sannu da kokari, Allah Ya saka da alkhairi, ka sha dawainiya.”

Kanshi kawai ta sunkuyar kasa, ko amin din ma kasa-kasa ya fada, shi a ganin shi ai yi wa kai ne, Mahboobah tashi ne don ya mata abu babu faduwa a ciki.

Bayan Mommy ta tafi Mahboobah ta farka. Ganin su Saleemah ya sanya ta sakin murmushi tana jin dadin ganin su a cikin ranta. Domin su din makusantanta ne wadanda za ta iya raba damuwarta tare da su.

Cikin azama Ishraq ya iso inda take, ya dan rusuna a gaban gadonta idonshi a cikin nata yake fadin “Sannu Madam. Ya jikin naki?”

Kauce ma haduwar idanuwansu ta yi tana kara tsuke fuska, ta amsa sannun da su Saleemah ke mata. Duk da haka bai yi zuciya ba ya kara fadin “Sannu Mahboobah. Da ma jiran farkawar ki nake sannan in tafi, ina da night consultation.”

“Da sauki.” Kawai ta fada ba tare da ko kallon shi ta yi ba, ta mika ma Ameerah hannunta ta je wurinta.

“Ammi ashe kin dawo.” Ameerah ta fada tana kokarin hawa jikin Mahboobah.

STORY CONTINUES BELOW

“Ba ni da lafiya Ameerah ki bi ni a hankali. Ba ki ga an jona mun karin ruwa ba?”

“Me ya same ki Ammi?”

“Hawan jini.”

“Wane irin hawan jini?”

“Ke ni na gaji da wannan tambayoyin naki da ba su karewa. Ina Mommy ne?”

Haneefa ce ta ba ta amsa cewa ta tafi gida ta ce sai safe za ta dawo.

“Shi ne kuma ta bar Ameerah a nan ya za mu yi da ita? Wallahi kar ma nurses su zo su sallame ku don surutun Ameerah na iya hana marassa lafiya barci.”

Harararta Haneefa da Saleemah suka yi. “Gaskiya kin ci bashi za mu rama.” Duk suka yi dariya. “Babanta zai tafi da ita yanzu.”

“Better.” Mahboobah ta fada tana kallon Saleemah da ta yi maganar.

“To ni zan tafi. Allah Ya qara lafiya. Ameerah mu je ko?”

Wani sabon darun ta saka amma Mahboobah na kallon ta ta zare mata ido tuni ta kama kanta ta shige jikin Ishraq. Kudi ya ajje musu dubu ashirin wai idan akwai wata bukata da za ta taso amma firfir Haneefa ta ce ba za su karba na, Yah Aliyu ya bar kudi wadatattu.

“Nashi daban nawa daban. Ku taimaka ku karba an kara a siyi ko fruits, ban samu na siyo musu ba.”

Saleemah mai saukin kan ita ce ta karba tana mishi godiya, ya kalli Mahboobah da ba ma ta shi take ba. “Patient Allah Ya kara lafiya. In shaa Allahu gobe da sassafe za mu zo ni da Mami.”

“Amin.” Ta fada a takaice tana kallon yanda Ameerah ta kasa ko hada ido da ita.

Yana fita Haneefa ta tabe baki. “Wai mutumin nan me yake nufi ne?”

Dariya Saleemah ta kwashe da ita. “Ga kuwa abin da yake nufi nan.” Ta kalli Mahboobah sannan ta dora da “Wallahi mugun son MB yake. Ke kin ga wani kallo da yake mata? Mu kam a daidaita ma ko za a samo ma Ameerahna kani ko kanwa.”

Harararta Mahboobah ta yi hade da sakin guntun tsaki. “Ba ki ma da hankali.”

“Ko ma dai me za ki ce na yarda. Ai dai ke ma din kina son kayanki.”

Ba ta kai da ba ta amsa ba suka ji sallamar Noor. Hannunshi rike da manyan ledoji ya ajje a kasa. Gaishe shi suka yi sannan ya tambaye su ya mai jiki.

“Ah lallai na ga alama jiki ya fara kyau, tunda ga ki nan ma a zaune. Alhamdulillah gaskiya. Allah Ya kara lafiya.”

“Ameen.” Ta fada tana mamakin yanda mutumin ya damu da ita.

“Mommy ta ce wai ciwon so kike.” Ya saki murmushi yana zama a kan kujerar da Saleemah ta sauka ta ba shi.

Murmushi Mahboobah ta saki, tana jin wani irin yanayi a tattare da ita. Kamar an ce ta daga idonta ta kalle shi. Sai ta ga shi din ma ita yake kallo, a tare suka sakan ma junansu murmushi.

“Eh mana. Ciwon so ne yake neman zautar da ke, yake son ki rasa rayuwarki. Haba Mahboobah wa ya fada miki har yanzu ana wannan? Su mazan nan da ba su da tabbas ma. Haka kawai ki kashe kanki a banza kan namiji, kafin a dauke gawarki ya fara tunanin auren wata.”

STORY CONTINUES BELOW

“Ashe ka san halinku.” Ta fada tana kawar da dubanta daga gare shi.

“Ba halinmu na sani ba Boobah, halin wasu daga cikinmu na sani. Da gaske kar ki sake irin haka. Ki sassauta ma kanki, kada damuwar kowanne namiji ta kara kwantar da ke har ta kai ki a wannan matakin. Idan yanzu ya zo da rangwame, a gaba fa, ba fata ake ba amma zai iya zuwa da tsautsayin da ya fi wannan.”

“Haka ne.” Ta fada tana jinjina karamcinshi.

“Na gode sosai da taimako. Mommy ta fada mun kai ne ka kai ni asibiti. Allah saka maka da alkhairi.”

“Ameen. Babu komai ai. Ni dai fatana Allah Ya kara miki lafiya.”

Ta yi shiru tana wasa da yatsun kafarta.

“Zuwa yaushe suka ce za su ba ki sallama…ko ba su yi zancen ba?”

“Eh.”

“Okay sannu fa. Ni bari in koma. Sai gobe in shaa Allahu zan sake dawowa. Allah Ya sawake.”

Bayan ga mike ya ma su Haneefa sallamah sannan ya fita. Har rige-rigen magana suke su duka biyun gulma na cin su.

“Mutuniyata wannan mutumin anya kuwa bai yi wuf da zuciyarki ba?”

Haneefa ta katse Saleema. “Ki ma cire anya. Ke kin ga wani kallo da suke sakar ma junansu, ta cikin ido sai aika sako suke a zukatansu.”

“Kai Innalillahi! Ni ban san me ya sa ma aka gayyato min ku ba, don ban ga yanda za a yi 2 idiots su yi jinya ba.”

“A’a gyara zancen dai hajjaju, 3 idiots dai su hadu a asibiti akwai damuwa.”

WASHE GARI

Da sassafe Mommy ta gama hada kalaci ta jera a babban kwando. Suka kama hanyar asibiti ita da Aliyu. Suna tafe Aliyu na ba ta labarin wai da kyar idan Noor ba son Mahboobah yake ba, don shi kam ya ga alama, ko jiya bayan rabuwar su sau uku yana kiran shi ya ji ya jikinta.

“Ni ma din ya kira ni da daddare. Amma ni sai na dauki hakan kawai a matsayin kulawa ce.”

“Ba wani kulawa Mommy, sai soyayya. Amma ko ma dai mene ne, idan ta yi tsami ma ji.”

Mommy ta sauke ajiyar zuciya. “Ni dai kar su haukatar min da yarinya, su bar ta ma ta ji da abin da yake damun ta.”

Daga nan ba su kara fadin komai ba har suka isa asibitin. Suna isa sai ga Fareedah ma za ta sauko daga cikin mota hannunta tallabe da Baby Hoodah. Wurin su Mommy ta isa ta ba ta yarinyar sannan ta koma ta dauko nata kwandon abincin.

Suna shiga dakin suka tarar Ishraq da Maminsa zaune. Bayan sun gaggaisa Mami ta ce bari su tafi sun cika dakin. Saleemah ta ce su yi zamansu su ma gida za su koma su yi wanka sai zuwa can anjima za su dawo. Suka musu sallama hade da ficewa.

“Ashe abin da ya faru da Mahboobah kenan. Allah ma Ya taimaka ta fada hannu na gari da shi kenan.” Mami ta fada tana jajanta wa Mommy.

“Wallahi kuwa Hajiya Mariya. Allah Ya sa yaron dan arziki ne wallahi shi da kanshi ya kai ta asibiti. Ya ce ana ta tsoron taba ta.”

“Ai haka ne da ma na Allah ba su karewa. Allah Ya kiyaye gaba Ya ba ta lafiya.”

Sallama suka ji, Aliyu ya amsa sallamar yana kallon wanda ya shigo din. Har kasa ya duka ya gaishe da ‘yan dakin, sannan ya tambaye su ya mai jiki.

Sai a sannan Ishraq ya daga kanshi ya kalle shi. Ta ina ma zai iya manta wannan fuskar? Wani irin wawan kallo ya kai wa Muhammad Saddam, yana jin tukukin kishi na taso mishi, tamkar ya shaki wuyanshi. Muhammad Saddam ya kawar da kan shi daga Ishraq, yana kallon Mahboobah.

“Assalamu alaikum…” Noor ya fada a daidai sadda yake shigowa dakin. Aliyu ne ya amsa sallamar yana ba shi izinin shigowa.

Cikin mamaki Ishraq ke kallon shi, ko ya ga motarshi a waje ne ya sa ya neme shi ya zo inda yake su gaisa?

“Ah Doctor Ish kai ne a nan?” Ya fada yana mika masa hannu hade da sallama.

“Ni ne da kaina Mr. Noor. Ka hange ni ne?”

“A’a.” Ya fada yana dorawa da “Na zo duba Mahboobah ne. Da yake ni ne na gan ta ba ta da lafiya jiya a Zaria.”

Cikin mamaki Ishraq ya dube shi. Yana son dora mishi wata tambayar kuma ya ga duk yanda idanuwa suka dawo kansu. Hakan ya saka shi sakin guntun murmushin da iyakacinshi kan lebenshi.

“Mommy an tashi lafiya? Ya mai jikin?”

“Mai jiki da sauki sosai Noor. Ga ta nan ta tashi. Ai su Haneefa sun ce ta sha barci jiya. Sallar asubah ma sai da suka tashe ta.”

“To Alhamdulillahi Mommy. Na ji dadin haka sosai wallahi.”

Muhammad Saddam da Ishraq baki dayansu shi suke kallo, Ishraq na son sanin alakarshi da Mahboobah da har yake fadin ya ji dadi da ta samu sauki. Muhammad Saddam kuma na son sanin ko shi din waye da har yake da damar fadin haka, saboda ya lura da kallon da yake bin Mahboobah da shi, da kuma wanda ita ma din take mayar masa. Wanda shi bai samu ba, tunda ya shigo kallo daya ta yi mishi ta sunkuyar da kanta kasa.

Wani abu aka ce sai iyaye. Hakika abin da babba ya hango yaro ba zai iya hango shi ba. Tuni Mommy ta gama karantar duk abin da yake wakana a tsakanin su duka mutum ukun.

“Muhammad Saddam?” Ta tambaya tana kallon shi. Kai ya jinjina mata alamar hakan ne.

“Ku je waje ku yi magana Ishraq. Ku duka.” Kallon mamaki suke bin ta da shi, musamman ma Noor da bai san madosar maganar ba. Sai dai a yanzu ya gama gane ita ce Mahboobar Ishraq, ita ce wacce yake ba shi labarin matarshi da ya rabu da ita.

Ta sake jinjina musu kai Mommy. “Ku je ku tattauna a tsakaninku. Mahboobah na maraba da duk wanda ya zama zakaran-gwajin-dafi a cikinku.”

“Mommy…” Aliyu ya dago kanshi a fusace yana kallon ta. “Me kenan Mommy?”

“Abin da kunnuwanka suka jiye maka Aliyu. Ishraq ku je.” Ita ta san abin da take yi, farin cikin Mahboobah shi take nema. To ta fahimci su duka ukun suna ranta, har Noor din da ta fara gani jiya. Ta yiwu wannan hukuncin da ta yanke ya zama mafita, sannan kuma farin cikin Mahboobah Bukar.

Babu musu su duka ukun suka fice.

End of chapter

Assalamu alaikum warahmatullah. Barkanmu da yau. Ya kuke how is every every? Fatan kowa da komai lafiya. Sannu sannu dai ga inda labarin ya kawo mu.

Ko ya wannan haduwar za ta kaya?

Mu je zuwa!

Princess Amrah

RAZ 2A cikin asibitin akwai wani fili daga can nesa, can su Ishraq suka dosa, kowannensu zuciyarshi na bugawa da sauri da sauri, suna tunanin ma ta inda za su fara ma junansu magana.

Bayan sun zauna, Muhammad Saddam ya mika ma Ishraq hannu, shi ma ya mika mishi nashi. Sannan ya mika wa Noor ma. “Sunana Muhammad Saddam, daga Zaria.” Ya fada cikin ruwan sanyi.

“Sunana Muhammad Nuraddeen Hunkuyi.”

“Ishraq Sulaiman.”

Suka gabatar da junansu. Kowannensu na neman maganar dorawa a gaba amma ya rasa.

“Ni ne mijin Mahboobah, kafin kaddara ta raba auren namu, amma har yanzu ina son matata:”

Murmushi Noor ya yi, yana tuna labarin da Ishraq din ya ba shi, cewa ba ya son Mahboobah, Maminshi ce ta tirsasa shi yin aure a lokacin shi ya sa ya aure ta.”

“Ni kuma a jiya kadai na fara ganin Mahboobah, tun kallon farko na ji ina son ta, na aminta da hakan kwarai a lokacin da na kwanta barci fir-fir ya ki dauka ta. Tunaninta ya hana ni sakat, na kuma yanke shawarar bayyana mata sakon zuciyata idan aka sallame ta daga asibiti. Aurenta nake burin yi.”

Muhammad Saddam da ke jin tukuki a zuciyarshi ya ce “Mun jima da ita amma kalmar so ba ta taba gitta tsakaninmu ba sai shekaranjiya. Na bar ta ne ta yi tunani a kan soyayyata, amma duk da haka ina bibiye da dukkan motsinta. Jiya ma sakon ciwonta bai isar min da wuri ba ne, sadda na je asibitin aka ce har an ba ta refer zuwa Almadina Kaduna, shi ne na bari yau na yi sammakon zuwa duba ta.”

Shiru suka yi daga nan, zukatansu na dokawa, kishi na sukar su su duka. Sun fi karfin minti goma magana ba ta kara gittawa ba a tsakaninsu, kafin daga baya Noor ya dubi Ishraq, ya ce,

“Ban san yanda aka yi ba ka fara son Mahboobah.”

“Kamar yanda ban san yanda aka yi ba ka fara son ta ba.” Ishraq ya ba shi amsa babu alamun annuri a fuskarshi.

Dariya Noor ya yi, yana mamakin maganar da ta fito daga bakin Ishraq din. “Mamakin me kuwa? Zuciya da So, ko in ce rai da So.”

“To kai ma mamakin me za ka yi don na ce ina son Mahboobah?”

“Gani na yi kun yi zama na fiye da shekara tare, a karkashin inuwa daya, amma duk bai sa ka so ta ba sai ma tukuicin saki da ka bi ta da shi. Sai yanzu ne za ka ce kana son ta? Ai dole in yi mamaki. Ni kuwa kowa ya san akwai irin wannan soyayyar, ta daga kallo daya. Shi Turawa ke kira da love at first sight.” Ya kara yin dariya yana kallon Ishraq da ke ciccika yana batsewa.

“Kowa ya sani soyayya na karuwa a lokacin da ma’aurata suka rabu. Ban taba sanin ina son Mahboobah ba sai bayan mun rabu da ita. Na kuma tabbata ita ma din haka…”

“Karya ne…” Muhammad Saddam ya dakatar da Ishraq. “Mahboobah ta fada mun ta tsane ka ba ta kaunarka. Ita ba a ma taba yin wanda ta tsana ba sama da kai. A gabanka a gabana ta fada. Baki daya soyayyar da take maka ta rikide izuwa kiyay…”

“Just shut up!” Ishraq ya fada tamkar zai kai wa Muhammad Saddam duka. Duk da haushin Noor da yake ji, da kuma zafin maganar da Noor ya yab’a mishi hakan bai sa ya mishi ko rabin tsanar da ya yi wa Muhammad Saddam ba. Ya tsane shi da dukkanin zuciyarshi. Hakan ba ya rasa nasaba da munanan kalaman da Mahboobah ta jefe shi da su a gaban Muhammad Saddam din, sai kuma uwa uba zanar da ya sha a wurin dogarai ta silar shi.

STORY CONTINUES BELOW

“Don’t dare shout at me (kar ka kuskura ka d’aga mun murya), ka san na san mene ne maganinka. So ka kama kanka mu yi magana a hankali.”

“And what will happen idan na daga maka muryar? Ba ya dai wuce ka hada ni da marassa imanin dogarawan nan naku ko? And so what? Soyayyar Mahboobah ce dai ba zan ajje ba, ba kuma zan bar maka ita ba. Kamar yanda muka fara rayuwar aure a baya, yanzu ma za mu koma.”

Muhammad Saddam ya yi murmushi mai ciwo. Rabon shi da walwala yau kwana biyu kenan, tun ranan da wancan abun ya faru.

“Ku bi komai a hankali. We are all matured enough (dukkanmu ba kananan yara ba ne), zai fi kyau idan muka bi komai ta cikin ruwan sanyi muka sasanta kanmu.” Cewar Noor cikin lallabarsu.

Shiru suka yi daga nan, Noor ya dora da fadin, “Ni ina ga kamar mu bari Mahboobah ta zabi wanda take so shi zai fi. Duk wani rikici da fada ba namu ba ne, mu yi ta lafiyarta ma shi ne kan gaba, kar mu kara mata wani ciwon, jininta ya kara hawa.”

Guntun tsaki Ishraq ya yi. “Kowa ai ya san ni take so. A duk cikinku wa ta taba furta ma kalmar so? Sai ni.”

Noor ya yi murmushi. “Ni dai har yanzu ban ma isar mata da sakon ta baki ba balle ta amsa. Sai dai na isar mata da shi ta idanuwa, kuma dukkan wadanda ke zaune wurin sun shaida ta karbi sakon zuciyata ta cikin nata idanuwan.”

Muhammad Saddam ya yi shiru, shi kam bai ma san me zai ce ba kuma, don ko alama bai hango soyayyarshi ba gare ta. Da gaske ba kowacce shakuwa ba ce ke zama soyayya. Akwai wadda ake gina ta sannu a hankali ta zama kakkarfar soyayya, akwai kuma wadda duk iya ginin magini ba zai iya ginata ba ta zama soyayyar. A nashi bangaren ma haka ne. Ya jima yana gina shakuwa tsakaninshi da Mahboobah. Ya jima yana son abotarsu ta rikide ta koma soyayya, sai dai abun ya faskara, ashe aikin banza yake yi. Duk yanda yake son Mahboobah zai iya hakuri da soyayyar tata, a kan ya yi son maso wani. Ya sani kafin ya iya zare soyayyarta daga zuciyarshi za a jima, ya san dole zai yi fama da jinyar so, sai dai, zai san duk yanda zai yi wurin rarrasar kanshi, yana kai kukanshi ga mahaliccin sammai da kassai, mahaliccin soyayya da kiyayya, mahaliccinshi da Mahboobah. Hannunshi ya sa yana shafe maikon da ke shimfide a kwarmin idonshi. Sai dai abin da bai sani ba shi ne, ashe ya gama malaluwa har saman kumatunshi. Kuka yake, kuka mai ciwo, kukan da tun shekaranjiya ke son fito mishi yana yakarshi, yana jin bai kamata ya zubar da hawayenshi a kan so ba, ba girmanshi ba ne yin kuka domin mace. Sai dai hakan ya gagare shi, a gaban abokan hamayyarshi kuka ya kunyata shi. Yana kokarin share hawayen wani na sauka.

Cike da tausayi Noor ya zaro hankici daga aljihunshi, ya mika ma Muhammad Saddam tare da fadin “Ka share hawayenka. Ka daina kuka, in shaa Allahu komai zai zo maka da sauki. Ka mika lamurranka ga Allah.”

Karba ya yi, yana son yi mishi godiya amma yana kasawa. Ya hau share kwallar wata na saukowa.

Abun mamaki, sai ga Ishraq da tausayin Muhammad Saddam. Ganin yanda baki daya rauni ya bayyana a saman fuskarshi. Jarumi kuma sadauki kamar Muhammad Saddam ya iya zubar da hawayenshi a gaban idonsu, lallai abun ya fi karfinshi ne. Ya kama hannunshi ya saka a cikin nashi, tausayinshi na ratsa zuciyarshi, bai ce komai ba, kamar yanda su dukka biyun ma babu wanda ya ce komai.

Bayan ya samu ya ci nasarar dakatar da hawayen, ya mika wa Noor hankicinshi, sannan ya rike hannun Noor da dayan hannun nashi, dayan kuma na rike da na Ishraq da bai sake shi ba har yanzu.

“Ku sasanta kanku, Allah Ya ba mai rabo sa’a.” Sannan ya saki hannuwan nasu, yana barin wurin. Cikin motarshi ya shiga, ya kifa kanshi da sitiyari, wani irin hawaye mai zafi na sauko mishi. Innalillahi kawai yake ambata, yana rokon Allah Ya sassauta mishi, Allah Ya kawo mishi dauki kar zuciyarshi ta buga.

Noor ya kama hannun Ishraq ya rike, cikin sanyin murya ya ce “Na bar maka Mahboobah Doctor Ish. Dama matarka ce, don haka ina muku fatan alkhairi. Allah Ya kawar da sharrin shaidan a tsakaninku, Ya ba ku zaman lafiya mai dorewa.”

Mutuwar tsaye Ishraq ya yi. Bai yi zaton lamarin zai karashe da haka ba. Ya dauka wani karamin yaki zai faru da suka fito, har ya shirya makaman yakinshi tsaf. Zai yi yaki a kan So.

“Tunda ka hana ni Mahboobah dole in je in ci gaba da hakuri da Meerah.” Noor ya fada cikin zolaya, yana marerece fuska da murya.

Gam-gam Ishraq ya rike hannunshi, yana fadin “A’a dole mu nemo maka wata. Amma sai na fara nemo wa Muhammad Saddam sannan kai, don ya fi ka bukatar mace shi da bai yi auren ba ma. Kodayake na fi shi fa.” Dukkansu suka saka dariya. Daga bayansu suka ji an ce “A’a fa. Na fi ku gaskiya.” Muhammad Saddam ne ya fadi haka yana hada hannuwansu su duka ukun.

“Mu je mu fada wa Mommy mun daidaita kanmu?” Noor ya tambaye su.

“Mu je.” Muhammad Saddam ya fada yana kallon Ishraq. Duk sai Ishraq din ya samu kanshi da jin kunya. Ya kokarta kauce ma haduwar idanuwansu, ashe haka Muhammad Saddam yake da halin kirki amma ya rinka mishi wata daukar ta daban.

Suka kama hanyar amenity room 4 inda Mahboobah take. Sun tarar daga Mommy da Mami, sai kuma Mahboobah da ke rungume da Baby Hoodah. Fareedah da Aliyu sun tafi gida su dauko takardun ciwon zuciyar Mahboobah baki daya.

Da annuri suka shiga su duka ukun, hannuwansu cikin na juna. Mommy na ganin su a haka ta san lallai ta samu nasarar hukuncin da ta yanke. Ta mike tsaye tana fadin “murmushin da ke shinfide a saman fuskokinku kadai ya bayyana mini abubuwa masu tarin yawa. Kenan kun daidaita kanku?”

Muhammad Saddam ne ya fara daga mata kai. Noor ya ce “Ko gobe a mayar da auren Doctor Ish da kanwata Mahboobah. Kodayake fa sai ya biya ni kudin toshin auren kanwata ashe.”

Mami kanta wani irin dadi ta ji ya ziyarci zuciyarta. Karshen bakin cikin Ishraq dinta ya zo.

Mahboobah kuwa wani irin kuka ne ya kwace mata. Tana son Ishraq, so mai tsanani wanda ba ta tunanin akwai ranan da zai fita daga zuciya da ranta, sai dai zai iya tsayawa da gudanya, kamar yanda ya yi a baya, bayan rabuwar aurensu. Ciwon abin da ya yi mata ya sanya Soyayyarshi tsayawa cak daga gudanya a cikin zuciyarta. Amma fa son shi babu inda ya tafi, sai ma dad’a ruruwa da ya yi.

Anya hakan zai sanya ta komawa gidan Ishraq Sulaiman? Za ta iya ci gaba da rayuwar aure da mutumin da bai san darajarta ba? Gyada kanta take yi, tana jin ba za ta iya ba, ba za ta iya komawa gidan Ishraq ba.

End of chapter

Abun mamaki new update💃🏻🥰

Da wa da wa suke goyon bayan komawar Mahboobah gidan Ishraq Sulaiman? Su waye ba su goyon baya? Drop your comments, next chapter zan muku wani bayani in shaa Allah.

Thank y’all

Princess Amrah

RAZ 2Cikin azama Mommy ta isa wurin Mahboobah. Jikinta a sanyaye ganin yanda take kuka bilhakki. Hankalinta ya tashi, gudun kar a koma ‘yar gidan jiya, ga shi ta ma likita alkawarin za su kiyaye shiga yanayin damuwa da take yi.

“Boobahna me kuma ya faru?”

Gyada kanta ta yi tana kallon Mommy. “Ba zan iya sake komawa gidanshi ba, ba zan iya ba Mommy.”

Daram! Ishraq ya ji gabanshi ya fadi. A wani baren na zuciyarshi kuma tsananin tausayinta yake ji, yana tuna wahalhalun da ta sha a gidanshi, kyara, tsana da kuma tsangwanar da ya rinka nuna mata, dole ne ma Mahboobah ta ce ba za ta koma gidanshi ba.

“Ya isa haka to daina kukan kin ji. Babu wanda zai yi miki dole, in dai ba kya son shi ba za ki koma gidanshi ba. Mu da muke fatan ki samu sauki zuwa gobe a sallame ki shi ne kuma kike kuka. Kwantar da hankalinki, matukar ba kya son Ishraq to ba za ki aure shi ba. Wanda kike so shi za ki aura.” Mami ce ta yi wannan maganar, duk da a ranta tana jin babu dadi, su ga samu su ga rashi. Amma ba ta da zabin da ya wuce ta fadi haka, ba ta son zama mai son zuciya. Mahboobah abar tausayi ce, baki daya rayuwarta abun a tausaya mata ce.

“Ina son shi, amma ba zan iya komawa gidanshi ba, har yanzu ba ya so na, yanda bakinshi ya furta k’i a kaina, duk yanda ya so kiyayyar nan ta koma So ba zai yiwu ba.”

Har kasa Ishraq ya sunkuya a gabanta. Bai ko ji kunyar Mommy da Mami ba, ya share gumin da ke tsatssafowa daga goshinshi, ya ce “Tuni na karyata wannan zancen na Hausawa Mahboobah, cewar bakin da ya furta k’i ko ya furta So karya ne, to wannan zancen ba gaskiya ba ne. Ni dai na furta miki k’i a baya, ga shi kuma yanzu kaunarki ta yi kawanya a zuciyata. Babu wata mace da nake son kasancewa da ita bayan ke Boobah. Babu macen da zan iya rayuwar aure koma-bayanki. Ki amince ki share mini hawayena, na yi alkawarin share miki naki hawayen, na baya, na yanzu, da kuma na gaba wanda ba na ma fatansu, zan kokarta yaki da su ta yadda za su nisance ki, ke da hawaye sai dai na farin ciki, da izinin Ubangijin al’arshi mai girma.”2

“Ba zan iya ba Likita.” Mahboobah ta samu furtawa, cike da rauni, tana jin cewa ba gaskiya ba ne kalamanshi.

“Hajiya Mariya ina ga ko mu ba su wuri su tattauna.” Mommy ta fada, tana karbar Baby Hoodah daga hannun Mahboobah.

“Ba a yi haka ba Maman Fareedah, don Allah kar mu tauye wa yarinyar nan ‘yancinta. A bar ta da ra’ayinta.”

Mommy ta yi murmushi tana kallon Mami, “Babban ‘yancin nata shi ne mu bar su su yi magana a tsakaninsu. Ita ba yarinya ba ce, Ishraq bai isa tursasa ta ba idan ba ta yin niyya ba. Don haka mu ba su wuri din. Ku hanzarta kafin likita ya zo second roundup.”

Daga haka Mommy ta fice, Mami ma ta mara mata baya.

“To Baban soyayya sai a san yanda za a yi a shawon kan kanwata, banda kuma kalaman yaudara.” Dariya Ishraq ya yi yana kai wa Noor duka a kafada.

“Ai ni ma kanwata ce.” Ishraq din ya fada yana murmushi. Muhammad Saddam dai dauke kanshi ya yi daga gare su, wani irin kishi ke ratsa shi, yana jin ba zai iya jurar wannan lamarin ba.

“Bari in fita, zan jira ku a waje.”

Noor ya kalli Muhammad Saddam da fadin. “Ai ba za ka bar ni a nan ba ni ma, tare za mu wuce.” Suka kama hanyar fita daga dakin.

Daga gefen Mahboobah Ishraq ya zauna, yana duba karin ruwan da ke rataye, tunda ya kare wata nurse ta ce a bar ta ta huta tukunna har zuwa anjima.

STORY CONTINUES BELOW

“Wannan ai ya kamata a jona shi, har yanzu babu kuzarin kirki a tattare da ke baby.”2

Abun ta ji bambarakwai, wai namiji da suna Amrah. Yau ita ce baby a bakin Ishraq Sulaiman. Ba ta san sadda murmushin takaici ya kwace mata ba.3

“Ka manta likita, Karfen kafa ne sunan, ko kuma KK a saukake.”2

“Da kenan, kafin in zurma a kaunarki. Yanzu kam ni ne ma karfen kafar ai.” Ya fada yana dauko wata ledar drip ya jona. “Kawo in mayar miki.”

Ba musu ta mika mishi hannu, ya soka a jikin kanular. Wannan shi ne karon farko da ya taba mace ya ji sauyin yanayi a tattare da shi. Ga baki daya jijiyoyin da suke aiki a halittar jikinshi ya ji cak sun tsaya da aiki na sakan goma, kafin suka fara rige-rigen ci gaba da ayyukansu.4

Ya dago kanshi ya kalle ta, yana jin wani irin yanayi wanda ba zai iya kwatanta shi ba. Idanuwanta da ta baza a nashi kadai sun isa su saukar mishi da kasala. Hakika da akwai aure a tsakaninsu, da babu abin da zai hana shi hada jikinsu a daidai wannan lokacin, ta yiwu idan bugun zuciyoyinsu suka manne a wuri guda zai samu nutsuwar da ya jima ba ya da ita.

“Mahboobah…” Ya fada cikin wata irin murya. Haka ita ma kiran nata da ya yi ya je mata a wani irin yanayi, yanayin da ba za ta ce ga shi ba, sai dai ta sani, ba za ta ce ta taba jin dadin sunanta a bakin kowa ba kamar yau, a bakin Ishraq Sulaiman.

“Mahboobah don Allah kar ki guje ni. Na sani ni mai laifi ne gare ki, na san zai yi wuya ki yafe min abubuwan da na aikata gare ki, amma ina rokon alfarma ki ba ni dama, ki ba ni dama in kankare laifukana na baya. Na yi alkawarin shafe duk wasu zunubbaina na baya. Ki amince min mu koma mutum guda ni da ke, mu yi dashen itaciyar da ta fara fidda reshe kaddara da rashin ban-ruwa suka busar da ita, ina son ta mike da karfinta. Ta ci gaba da fidda rassa kamar yanda ta fara fitar da guda daya a baya.”

Baki daya kalaman Ishraq jin su take tamkar a mafarki. Tamkar ba Ishraq Sulaiman ba, kamar ba wannan da ta nace ma soyayyarshi yana wulakantata ba. Sai ta samu kanta da karyewar zuciya, hawaye take zubarwa masu zafi, wadanda ke fitowa tun daga zuciyarta. A bakin gadon ya jawo tissue ya nannade ta, ya hau share wa Mahboobah hawayen da take fitarwa din, yana jin kamar ya taya ta shi ma. Ba ya jin dadin wannan kukan da take yi, ko kadan.

“Ishraq…” ta runtse idonta, tana sauke su a cikin nashi da ya yi narai-narai yana jiran maganarta.

“Na amince zan koma gidanka…Ishraq idan ka cutar da ni a karo na biyu Allah Yana ganin ka, ba zai kyale ka ba.”7

Tamkar ya rungume ta haka ya ji. Ta ina ma zai cutar da Mahboobah? Macen da yake jin ta har cikin zuciyarshi? Wadda yake jin zai iya yaki da duk wanda zai cutar da ita ma?

“Alhamdulillah!” Kadai ya iya furtawa, yana tsugunnawa a kasa saitinta. “Na gode wa Azza wa Jallah. Thank you so much Booban Ishraq.” Ya gaggauta mikewa yana barin dakin, cike da farin ciki.

A duk halin da zai shiga, farin ciki ko bakin ciki yana fara raba shi ne tare da Maminshi. Wannan dalilin ne ya sa ya yi gaggawar fita domin ya shaida mata Mahboobah ta amince masa.

A bisa kujerun reception ya same su ita da Mommy, cikin farin ciki yake shaida musu, daga Mommy har Mami din sun ji dadi. Ita Mommy dama tuni ta san soyayyar Ishraq ba za ta taba ficewa daga zuciyar Mahboobah ba sai dai bacin rai, shi ya sa ta ji dadin al’amarin.

Waje Ishraq ya fito wurin su Noor, yana fitowa ya yi arba da Khaleed, suka damki hannun juna.

“Ba ka fada mun Mahboobah ba lafiya ba, sai Ameerah ce ke fada mun dazu da muka hadu na je kai Junior makaranta ita ma an je kai ta. Ta ce mun Amminta ba lafiya. Shi ne na kira Mommy ta fada mun a nan take kwance.”

STORY CONTINUES BELOW

“Hankalina ne ba a kwance ba Khaleed , shi ya sa ban sanar da kai ba. Amma dai Alhamdulillah, komai ya saukaka. Jikin Mahboobah ya yi sauki, sannan zuciyar Ishraq ma ta yi sauki.”

Kara damke masa hannu ya yi, yana fahimtar madosar maganar Ishraq. “Yanzu shi kenan komai ya daidaita tsakaninku?”

Kai Ishraq ya jinjina mishi, yana ba shi tabbacin hakan.

“Gaskiya lamarin nan ya yi mini dadi kwarai wallahi. Allah Ya tabbatar da alkhairi Ya ba ta lafiya.”

“Ameen abokina Khaleed. Ka shiga ciki su Mami na reception, akwai masu jira na a waje.” Suka saki hannun juna.

***

Bayan Aliyu da Fareedah sun dawo kai tsaye wurin likita suka wuce, saboda shi ne ya bukaci ganin takardunta baki daya, kasantuwar Mahboobar da kanta ta fada mishi ta yi fama da ciwon zuciya, yana son ganin komai saboda ya san madosar ciwon takamaimai, kar a je suna da alaka ciwon zuciyar da hawan jinin.

Takarda guda daya ce suka manta ba su cire ba ta dashen zuciyarta. Cikin mamaki likitan ya zare gilashin idonshi yana tambayar Aliyu, “Ashe har dashen zuciya aka yi mata?”

Babu halin cewa a’a, babu yanda za a yi ya musa tunda shi da kanshi ya karanta. Jinjina kai Aliyu ya yi.

“Subhanallahi! Gaskiya yarinyar tana da bukatar taka-tsan-tsan. Har dashen zuciya aka mata shi ne kuma kuke yarda jininta na mugun hawa?” Ya ci gaba da duddubawa.

“Can ya ci karo da rubutun yarjejeniyar siyan zuciyar da suka yi.” A kidime yake duddubawa, domin kuwa ya sani, kowa ma ya sani haramun ne a dokar K’asa abin da aka aikata, domin kuwa ba da izini aka yi cinikayyar ba.

“Ina da bukatar ganin Doctor Ashraf. Ashe da gaske abin da ake rade-radi a kansa? Kwanaki har case an yi ya hada shaidun karya ya kubuta, ina daga cikin masu kare shi, a gani na ba zai iya aikata haka ba. Ashe da gaske abin da yake yi kenan?”

Shiru Aliyu ya yi, gabanshi na tsananta faduwa, yana tuna alkawarin da suka daukar wa Doctor Sadeeq kan cewa wannan maganar ba za ta taba fita ba. Ga shi yau kilu na neman jan bau.

Lambar wayarshi ya latsa ya kira, bugu biyu ya dauka. Bayan sun gaisa Doctor Saleem ya hau zayyane ma Doctor Ashraf dalilin kiran nashi. Yana dorawa da “Ba na taba goyon bayan zalunci a rayuwata. Don haka ka shirya karbar sammaci. Wannan ha’inci ne kake yi, da kuma zambo cikin aminci. Shin an taba tauye maka albashinka? Ka taba yi ma gwamnati aiki ta k’i biyanka hakkinka? Me ya sa za ka aikata haka? Ka fada mun Doctor Ashraf, me ya sa kake wannan zaluncin?”

Daga inda Doctor Ashraf yake gumi kawai ke keto mishi. Ya san Doctor Saleem, ya san kafiya irin tashi. Kuma tunda ya ambaci haka ya san komai zai iya aikatawa din.

“Doctor Saleem please listen to me. Kana ina in zo mu yi magana?”

“Babu wata magana da za mu yi Doctor Ashraf. Ka sani ni ba na goyon bayan zalunci.”

“Don Allah…”

Doctor Saleem ya yanke kiran yana duban Aliyu da ya gama kidimewa.

“Me ya sa kuka biye su aka aikata wannan barnar don Allah? Shin ba ku da masaniyar cewa abin da kuka aikata ya saba ma addini da dokar K’asa? Ko ba ku san dole sai da izinin dangin mai zuciyar ba ko kuma su kuka biya kudin fansar zuciyarsu?” Shiru Aliyu ya yi yana rasa abun cewa. Suna cikin haka Mommy da ke tsaye bakin kofa tun farkon maganar tana sauraron su ta shigo. Ta zauna a kujera kusa da Aliyu cikin rashin kwarin guiwa. Ita kanta ta sani ba su aikata daidai ba, sun bi son zuciyarsu.

“Za ku hadu a kotu, idan ta kama za a nemo dangin mai zuciyar ku ba su kudin fansar zuciyar diyarsu ko dansu.”

“Doctor idan har za a iya gano su na dauki alkawarin biyansu koda a ce dukiyarmu za ta kare. Hakika duk a baya idona ne a rufe a kan ciwon Mahboobah. Wahalar da take sha a lokacin, duk ma mun riga mun cire rai da ita, Doctor Sadeeq ya ba mu shawarar dashen zuciyar.”

Jikin Doctor Saleem duk sai ya yi sanyi. Hawayen da Mommy ke yi ya rikita shi, ya tsani ganin babba na kuka, musamman kuma mace da yake girmama darajarta.

Ya dauki wayarshi ya latsa kiran Doctor Ashraf, cikin hanzari ya dauka.

“Ka zo Almadinat Hospital ku same ni, kai da Doctor Sadeeq.” Kit ya kashe wayarshi. “Ba zan boye miki komai ba Mama gaskiya kun yi kuskure. Idan ke ce yanzu sai diyarki ko danki su yi hatsarin mota ko kuma wani ciwo ya kama su har su mutu ba a gano ku ba, sai kawai wani azzalumin likita ya sayar da zuciyar dan naki ya za ki ji? Ba ma wannan ba, an bar ki cikin duhun danki na da rai ko bai da shi? A wane hali yake ciki? Duka ba ki sani ba. Mama ba a zalunce ki ba? Anya za ki iya yafe ma wanda suka aikata miki haka?”

Da sauri Mommy ta daga kai da fadin, “Tabbas an zalunce ni likita, kuma ko zan yafe sai na nuna musu kuskurensu.

Duk tunanin hakan bai zo mun ba ne. Da gaske idan an gano masu ita za mu ba su kudin zuciyar ko nawa ne, tare da rokonsu gafarar abin da muka aikata gare su.”

Ajiyar zuciya Doctor Saleem ya sauke, “Ku je zan neme ku idan sun iso.” Ya fada yana ci gaba da rubutu.

A sabule Mommy da Aliyu suka fice, suna jin nadamar abin da suka aikata.

End of chapter

Assalamu alaikum to y’all. Ya kuke ya gida da iyali? Sannu a hankali tafiyar tamu tana ta sauka. Gaskiya ne zancen Hausawa, tafiya sannu-sannu kwana nesa.

Wanda suka goyi bayan komawar Mahboobah gidan Ishraq, hakika tare muka yo hangen nan, kuma a haka na tsaro labarin tun tashin farko; haduwa, rabuwa, sai kuma haduwa.

Idan kuka duba, Muhammad Saddam dan Sarki ne, kuma saurayi. Idan har aka ce shi zai auri Mahboobah lallai za ta riski tarin kalubale, duk da hakan bai haramta ba a shari’a, amma a al’adance fa saurayi sai budurwa, budurwa sai saurayi. Musamman kuma harka ta gidan sarauta. Kwanciyar hankali Boobah ke da bukata, ba wani tarin kalubalen ba.

Sai Mr. Noor, zama da Matarshi ga Mahboobah mai sanyin hali ba abu ba ne mai sauki. Musamman kuma da larurin ya hade mata biyu a yanzu, ga dasasshiyar zuciya, ga kuma hawan jini. Mahboobah na da bukatar kulawa sosai.

Ishraq din dai🤣🤗

Princess Amrah

RAZ 2Cikakken minti talatin ba a yi ba Doctor Sadeeq da Doctor Ashraf suka bayyana a gaban Doctor Saleem. Dukkansu ana kallon su an san a rikice suke, babu wanda bai san halin Doctor Saleem ba, bai da wasa ko kadan.

Aliyu, Mommy, Fareedah, da Ishraq suka shigo Office din su ma. Mommy ta ce lallai sai Ishraq ya san halin da ake ciki, ya ba su Noor hakurin su jira shi ya dawo su yi sallama.

Hannu Doctor Saleem ya mika ma Ishraq cikin sanayya suka gaisa. Ishraq ya ce “Saleem tuzuru ashe kai ne likitan Matata.”

Doctor cikin mamaki ya ce “Kar dai Mahboobah matarka ce.”

“Eh, kuma jiya da yau duk ina nan, ba mu hadu ba.” Ishraq ya fada yana hangen ta inda zai samar wa Mommy wurin zama.

“Ina ga kamar mu je conference hall mu tattauna a can ko?” Doctor Saleem ya mike, yana musu jagoranci zuwa hall din cikin asibitin.

Bayan duk sun zazzauna, ya yi addu’ar bude taro sannan ya ce,

“Dukkanku kun san abin da ya tara mu a nan. Daga farko na ga dacewar sanar da hukuma abin da ake ciki, sai dai na tuna zancen Hausawa, cewa baki da baki idan suna haduwa rayuka ba su bace. Ku yi hakuri fa, wasu daga cikinku sun san ni, wasu kuma ba su san ni ba. Ga wadanda ba su san ni ba, haka halina yake, ina da tsauri gaskiya, musamman a kan gaskiya. Ba na goyon bayan zalunci. Don haka ga Doctor Ashraf, ga kuma Doctor Sadeeq. Ta yaya kuke tunanin gano magadan zuciyar nan ku damka musu kudin fansar zuciyarsu? Sannan fa ku sani, tare da ni za a yi komai, idan suka ce ba su yafe ba dole ku yi shari’a, gaskiya ke nan. Idan kuma ba za ku iya gano mai zuciyar ba, da Gwamnati za ku yi shari’a.”+

Hankici Doctor Ashraf ya sa ya share gumin da ke keto mishi, duk da sanyin AC da ke ratsa shi. Ya sa hannunshi cikin aljihu yana zaro ID card ya dire shi a gaban Doctor Saleem. “Wannan shi ne Identity card din da ke manne jikin gawar da aka cire zuciyar tata, tun a lokacin yana ajje cikin drawer din Office dina. Sannan na gurza kwafi dinsa ma duka na hada a cikin takardun da na ba Doctor Sadeeq.”

Ajiyar zuciya Mommy ta sauke, tana jin dadin samun ID card din, ta yiwu ta haka za su gano su, su roki gafararsu.

“Ameerah Muhammad Hunkuyi…”

A zabure Ishraq ya mike, hakan ya sa Doctor Saleem dakatawa da karantawar yana bin shi da kallon mamaki.

“Ka san ta ne?” Aliyu ya tambaye shi idanuwanshi a kan Ishraq din.

Shiru Ishraq ya yi yana komawa ya zauna, ya dafe kanshi da yake jin ya yi muguwar sara mishi. Ameerah Muhammad? Ya hau tunanin labarin da Mujaheed ya ba shi na rasuwar Ameerah, da kuma wanda ya ji a bakin Noor.

“Kudan Local Government, Kaduna State. Next of Kin Muhammadu Abubakar Hunkuyi…ga lambar waya.” Kamar a wasa Doctor Saleem ke karantowa, kafin ya jawo wayarshi ya kwafe lambar wayar jiki ya latsa kira.

Cikin rashin sa’a sai wayar ba ta shiga ba. Ya sake gwadawa amma aka ce a kashe take. Duk sai jikinshi ya yi sanyi.

Ishraq ya mike da sauri yana fadin “Ina zuwa.” Ya fice. A daidai bakin gate ya hango Noor zai fita da motarshi, ya kwala masa kira amma bai ji ba, sai da mai gadi ya taimaka masa sannan ya ji, ya daidaita tsayuwar motarshi ya fito.

“Akwai damuwa…” Ishraq ya furta, wanda ko bai fadi hakan ba tuni Noor ya hasko damuwar shimfide a saman fuskarshi.

“Mu je.” Kawai ya iya fadi, ya yi gaba Noor ya mara masa baya. Suna isa cikin hall din Ishraq ya ce,

STORY CONTINUES BELOW

“Ga wanda ya san Ameerah Muhammad na kawo muku.” Da mamaki su dukkansu suke kallon shi, shi kanshi Noor din bai san madosar zancen Ishraq din ba.

Doctor Saleem ya ce “Da gaske?” Ishraq ya jinjina kai.

“Bismillah bawan Allah.” Doctor Saleem ya gwada ma Noor kujerar kusa da shi ya zauna.

“Ka san Ameerah Muhammad Hunkuyi da gaske?”

Cikin kidima Noor ya mike idanuwa a bude, yana son yin tambaya amma ya kasa.

“Calm down…alamu sun nuna ka san ta din kenan.”

A takaice Doctor Saleem ya labarta mishi komai tun daga farko har karshe.

Hawaye Noor ya ji wanda ya kasa dakatar da su, fama mishi tsohon tabon mutuwar Ameerah aka yi, ya ji zuciyarshi na zafi. Ashe zuciyar Mahboobah ce shimfide a kirjin Mahboobah Bukar? Shi ya sa daga kallo daya ya ji kaunarta ta shige shi? Innalillahi yake maimaitawa a ranshi, yana rokon Allah Ya sassauta mishi nannauyan abin da ya yi tsaye a tsakanin kirjinshi.

“Za ka yi mana jagoranci mu je wurin iyayenta?” Mommy ta fada cikin kuka, a wani baren na zuciyarta kuma ta ji dadin hakan, ta ji dadi da ya zamanto Noor ya san yarinyar da suka ma fashin zuciya.

“Zan kai ku.” Ya fada cikin sanyin murya.

“Ina ga sai ku tashi mu rankaya yanzu, tun rana ba ta yi ba. Amma kafin nan, ga sallar azahar can ana kira, mu fara gabatar da ita sannan mu tafi.”

Dukkansu suka goyi bayan maganar Doctor Saleem.

Ko da Mommy ta koma dakin Mahboobah ta tarar daga Mami sai Fareedah ne a dakin. Yanayin yanda suka gan ta jiki a sabule duk sai suka tsorata. Fareedah da Mahboobah har rige-rigen tambayarta suke, ta share gumin goshinta, sannan ta zayyane musu komai.

Kuka Mahboobah ke yi, kukan da ita kanta ba ta san dalilin yin shi ba. Ta dai sani ta ji dadin faruwar haka, ta ji dadin sanin asalin masu zuciyar da aka dasa mata.

“To mene ne kuma abun kukan? Idan suna bukatar kudi ne ba sai a ba su ba? Yi shiru kin ji.” Mami ta hau rarrashin Mahboobah.

Fareedah cikin rarrashi ta ce “In shaa Allahu karshen damuwarki kenan Yah Boobah. Komai ya zo karshen da izinin Allah.” Ta latsa kiran Aliyu bayan ta duba lokaci. Da ya dauka ta tuna masa dauko Ameerah lokaci ya yi. Ya fada mata Hunkuyi za su tafi, amma bari ya fada wa Ishraq sai ya kira Khaleed ya dauko ta tare da Junior.

Bayan Mommy ta yi sallah Aliyu ya kira ta su tafi. Mami ma ta ce za ta bi su don bai kamata ba a ce Mommy ce kadai mace a cikinsu.

Likitocin uku suka shiga mota daya, sai kuma Noor da zai musu jagoranci. A motar Ishraq kuma Yah Aliyu, Mommy da Mami, suka rankaya sai Hunkuyi.

***

Karfe uku ta musu a can, Noor ya rinka kwatanta musu hanya har kofar gidan su Ameerah. Mommy da Mami aka ce su shiga su sanar da zuwan nasu, su kuma suka jira waje.

Cike da aminci Maman Ameerah ta tarbe su duk da cewa ba ta san su ba ba ta taba ganin su ba. Ruwan sanyi na randa ta gabatar musu da shi a cikin kwanon silver. Sannan ta zauna suka gaisa. Mommy ta ce

“Mai gidan yana nan kuwa? Tare muke da baki, kuma zuwan ba naki ne ke kadai ba, har shi.”

Cikin mamaki Mama ta ce, “Wallahi ya fita, amma na san yana daf da gida. Su shigo mana. Ku yi musu iso Hajiya…” kafin Mama ta rufe baki sai ga Baban Ameerah gaba, su Ishraq biye da shi.

STORY CONTINUES BELOW

“To Alhamdulillah ga su nan ma ai.” Mami ta fada tana kallon Mama da murmushi.

Da azama Mama ta mike, ta dauko babbar tabarma ta shimfida musu, sannan ta gaishe su cikin girmamawa, su Mommy ma suka gaishe da baban Ameerah.

“To Mallam ai ina ga a siyo musu ruwan leda ko.” Mama ta fada tana kallon Baban Ameerah. “Eh ina zuwa. Ku dan yi hakuri in siyo muku ruwa don Allah. Ba mu san da zuwan naku ba.”

Doctor Saleem ya murmusa da fadin “Wallahi da ma kun bar shi, ba wani jimawa za mu yi ba.”

“A’a ba a yi haka ba, daga ganin ku matafiya ne.” Ya fada yana zura takalminshi. “Ai ba wani nisa ne da wurin siyar da ruwan ba. Ina zuwa.” Ya fice.

Duk da gaban Mama da ke ta faduwa saboda rashin sanin su, da kuma rashin sanin dalilin zuwan nasu amma hakan bai hana ta sakar musu fuska ba. “Sannunku kun sha rana.”

Mommy ta amsa da “Aikam ba laifi ana kwala ta. Amma ku nan kamar da sauki ai, Kaduna an fi rana.”

“Au daga Kaduna kuke kenan. Gaskiya ba laifi.”

Suna cikin haka sai ga Baba ya dawo, ya ajje ruwan a gabansu yana kara yi musu sannu. Bayan duk sun sha, Doctor Saleem ya fara magana,

“Na san ba ku san mu ba, ba ku san dalilin zuwan mu ba. Amma dai kafin komai, ina farawa da yi muku ta’aziyyar Ameerah. Allah Ya ji kanta Ya gafarta mata.”

A tare Mama da Baban Ameerah suka amsa da amin.

“Sannan, akwai magana mai muhimmanci wadda ita ce dalilin zuwan namu ma baki daya…” Tun daga farko har karshe Doctor Saleem ya zayyane musu. Yana kaiwa aya Mommy ta karbe cikin kuka,

“Hakika mun san mun zalunce ku, zaluncin da idan ni aka yi ma shi zan jima ban yafe shi ba. Amma ku sani kaddara ta riga fata. A lokacin idanuwanmu ne suka rufe a kan ciwon Mahboobah, har aka hada baki aka siyi zuciyar diyarku. Ku yafe mana bayin Allah, ku yafe mana.”

Kuka sosai Maman Ameerah ke yi, yayin da Babanta ya yi shiru yana sakar zuciya, wani irin radadi yake jin zuciyarshi na mishi. Tunda suke a rayuwarsu ba su taba ganin son kai irin wannan ba.

Cikin kuka Maman Ameerah ta ce “Kun zalunce mu, kun cuce mu da ba ku bari mun ga ko gawar diyarmu ba.” Ta kara karfin kukanta, tana tuna sadda komai ya faru.

“Mun sani mun yi laifi, shi ya sa muke gurfane a gabanku muna rokon gafararku.” Ishraq ya fada cikin magiya, yana duban Maman Ameerah.

Doctor Saleem ya yi gyaran murya, “Hukuncin a hannunku yake iyayen Ameerah. Idan kun so ku shigar da kara, ni na yi alkawarin tsaya muku tare da bada shaida daidai abin da na sani. Idan kuma kun so za ku iya yafe musu amma su biya ku kudin fansar  zuciyar diyarku. Hakazalika idan kun so za ku iya yafe musu duka, sai ku ma din Allah Ya yafe muku wasu laifukanku. Sai dai kada ku manta, duk mai hakuri mai yafiya, yana da wani sakamako mai girma a wurin Allah madaukakin Sarki.”

Idanuwan Baban Ameerah sun kad’a sun yi jajur, shi bai ma san abin da zai ce ba. Sai dai a zahirin gaskiya shi kanshi ya sani ya ji haushinsu, musamman a kan son kan da suka nuna karara.

Doctor Ashraf ne ya sauke ajiyar zuciya, ya ce, “Dukkan wani abu da ya faru ba laifinsu ba ne, laifina ne. Ni ne ban kasance mai tsoron Allah ba, ni ne da zalama da son kudi. Laifina ne, ku dauki duk hukuncin da kuke ganin ya dace da ni, domin kuwa na zalunce ku, ko ba ku ba, akwai alhakin mutane da yawa a kaina.”

Duk sai ya ba su tausayi. Baban Ameerah ya gyada kai, “Babu komai, ku je kawai, duniya ce!”

“Ban fahimci nufinka ba Baban Ameerah.” Doctor Sadeeq ya fada cikin marerecewa.

“Abba ka yi magana, don Allah ku taimaka ku yi hakuri, duk garin nan kowa ya san halinku na kirki, ina so yanzu ma ku kara a kan wancan hakurin naku, ku yafe musu abin da ya faru.” Noor ne ya yi wannan maganar, cikin magiya da kankance murya.

“Babu komai…ya wuce. Allah Ya ji kan Ameerah Ya gafarta mata.”

Dukkansu suka amsa da amin, ta muryoyinsu kadai za a fahimci dadin da suka ji.

Sai da suka yi sallar la’asar sannan suka musu sallama cike da godiya, Mommy na so ta yi musu alkhairi amma tana gudun kar su dauka ko biyansu ne za ta yi, hakan ya sa ta kudura a ranta bayan sallamar Mahboobah daga asibiti za ta dauko ta da kanta su kara yi musu godiya, tare da abunuwan alkhairi masu yawa.

Har kofar gida Mama da Baban Ameerah suka rako su. Fatan sauka lafiya suka yi musu sannan suka koma gida cike da jimamin tunowa da yarinyar kirki Ameerah.

*

Suna isa Almadina Mommy ta ce a yanda suke din nan kawai su daura auren Mahboobah da Ishraq, in dai Ishraq din ya shirya, ita da Mami suka koma ciki. A take kuwa ya karbi account number din Aliyu ya zuba mishi dubu dari a matsayin sadakin Mahboobah. Saboda babu cash a hannunsa. Mutum biyar din nan da wasu daga cikin ma’aikatan asibitin suka shaida daurin auren Ishraq Sulaiman da Mahboobah Bukar.1

End of chapter

Princess Amrah

RAZ 2Sosai Mahboobah ta ji dadin yanda abubuwan suka kasance a Hukunyi, ta jinjina wa iyayen Ameerah matuka, domin kuwa ba kowa ba ne zai iya wannan halaccin da suka yi.

Mami ta mike ta musu sallama cewa za ta tafi yamma ta yi. “Hajia Mariya ba za ki jira Ishraq din ya tafi da ke ba?” Mommy ta fada cikin fara’a.

“A’a Maman Fareedah ban san ranar tafiyar wannan ba. Kuma yana iya cewa asibiti zai wuce daga nan, kar in shiga hakkinsa. Bari kawai in hau keke napep in tafi.”

Mommy ta bata rai ta ce “Gaskiya ba za ki hau keke napep ba Hajiya, bari Aliyu ya zo ya mayar da ke, na san sun kusa gamawa.”

“Me za su gama Mommy?” Fareedah ta tambaye ta.

“Idon matambayi.”

Ta kwakkwabe baki, “Wayyo Allah Mommy bakar magana ma za ki yi min ko?”

“Iyyyeeee…lallai ma Reedah. Shagwaba nake ganin kina yi fa. An dai sha kunya.” Mahboobah ce ta yi wannan maganar tana gatsine mata baki.

“Eh din ina ruwan wata, ai dai kowa ya san auta da shagwaba.” Ta fada tana kara turo baki.

“Ga dai Baby Hoodah nan na kallon ki, na tabbata a ranta cewa take su Reedah an ji kunya.”+

Dariya suka dauka su duka dakin, har da Haneefa da Saleemah da ke daidai shigowa. Suka gaishe da Mommy da Mami sannan suka tambaya ya mai jiki.

“Ni na yi fushi tunda sai yanzu za ku dawo.”

Saleemah ta hau kan gadon kusa da ita, “Afwan yarinyar kirki, ga mu nan ai mun zo.”

“Mommy ta kira Aliyu cewa ya zo ya mayar da Mami gida ya amsa da to. Fareedah da Mommy suka taka mata har gaban motar Aliyu, ta musu sallama, Mommy ta kara yi mata godiya sosai sannan Aliyu ya ja motar suka tafi.

Noor na tare da Ishraq bayan an gama daurin aure su Doctor Ashraf sun tafi aka kira shi a waya da wata lamba. Bayan ya dauka cikin tashin hankali aka shaida mishi cewa matarshi ce ta bada wannan lambar ta ce mijinta ne a kira shi, sun tafka mummunan hatsarin mota a kan hanyar Mando, yanzu haka suna General hospital ma.

A kidime Noor ke ambatan sunan Allah kafin ya yanke wayar Ishraq na tambayarshi lafiya, ya shaida masa kamar yanda aka fada masa yanzu.

Tare suka kama hanyar zuwa asibitin, suka nufi accident and emergency, a can suka tarar da Sameerah kwance jina-jina, fuskarta duk jini. Salati Noor ke yi yana kallon yanda idonta guda yake a kumbure suntum, gudan kuma a bude tana zubar da hawaye.

“Sannu Meerah, ashe tsautsayin da ya auku kenan.” Kai ta jinjina masa tana jin wata irin nadama da tsoro na lullube ta. Lallai duniyar nan abun tsoro ce, mutum ba a bakin komai yake ba. Ko kadan ba ta kasance a cikin mata masu biyyar aure ba, ba ta taba damuwa da sai ta nemi izinin mijinta ba kafin ta fita, da Noor da banza duk daya suke a wurinta. Yau ga yanda rayuwa ta yi da ita nan, kafarta karaya uku, hannunta kuwa ba a ma san adadi ba, an yi xray an dai ga karaya da yawa.

“Sameerah me ya kai ki hanyar Mando?” Ya tambaye ta yana gyada kanshi.

“Ka yi hakuri Noor…” kawai ta iya fadi da kyar, tana jin yanda hakoranta ke mata nauyi, komai nata ma jin shi take ba daidai ba, ciwo duk jikinta.

STORY CONTINUES BELOW

“Ina Ameer yake?” Ya sake jeho mata tambaya.

“Yana gida.”

“What?” Ya tambaye ta a razane yana kwalalo ido waje. “A gida kika bar Ameer din shi kadai duk da zazzabin da yake fama da shi?”

“Look…Mr. Noor. Ka yi hakuri ka bi komai a sannu. Tunda ba ta da lafiya don Allah bi ta a hankali, mai faruwa dai ta faru, sai dai Allah Ya kiyaye gaba.” Ishraq ya fada yana yi yana duba agogo. “Ina da consultation by 7pm, ga shi har 6 ta wuce. Bari in wuce, duk yanda ake ciki sai mu yi waya. Allah Ya ba ta lafiya Ya sa kaffara ne. Zan biya in dauki Ameer din in kai wa Mami shi, Ameerah ma sai a mayar da ita kafin Boobah ta wartsake. Ka kula da ita sosai Noor.” Ta juya ga Sameerah, ta yi saurin janye dubanta daga gare shi, tana jin wata irin kunya na lullube ta, tuna wulakanci da cin fuskar da ta ma Ishraq ranar da ta fara ganin shi ya zo gidanta.

“Allah Ya ba ki lafiya Meerah.” Daga haka ya juya ya fita, Noor ya mishi rakiya har bakin motarshi sannan suka yi sallama ya tafi.

“Noor ka ga yanda rayuwa ta yi da ni ko? Na tabbata alhakinka ne ke bibiya ta, shi ne ya sanya mu tafka wannan mummunan hatsarin a lokacin da muke tsaka da nishadi ni da kawayena, kuma na fita ba tare da kai kanka ka sani ba, duk da Ameer da ke kwance bai da lafiya. Ka yafe min Noor, na sani ba lallai ba ne ka iya ci gaba da rayuwa da ni, bayan rashin kyautata maka da na yi a baya, ga shi kuma yanzu na nakasa, don na san ba lallai ba ne kafafuwana su ci gaba da tafiya kamar baya, ko na ji sauki dai dole na nakasa.”

Hannunshi ya sa ya shafi fuskarshi, yana jin tausayinta a karo na farko na daga rayuwarsu. Don ba ta ga yanda fuskarta ta dame ba ne shi ya sa har take zancen kafafuwanta ba za su mike ba. Ta samu fuskar tata ma ta fara gyaruwa.

Suna cikin haka likita ya zo, ya ce dole sai an yi dinke-dinke a fuskarta saboda raunukan da suka huda fatarta.

Noor ya biya duk kudaden da suka dace aka shiga aikin da ita, sannan ya samu ya kira mahaifinta ya sanar da shi abin da yake faruwa.

Sai dai ana yin dinkin yana darewa, saboda fatar fuskarta da ta ji mayukan bleaching, an fi karfin awa biyu ana abu daya, kafin da kyar aka samu ya dan dinku sama-sama.

Ta yi kuka sosai a lokacin da likita ke fada mata dalilin wahalar da ta sha wurin dinki, tana jin da na sani na kara lullube ta, ta yanda ta bi rudin zamani ta keta hakkin aure da addininta. Hakika ta ga ishara, ta ga illar sab’awa miji, ta ga illar raina halittar da Allah Ya yi wa mutum.

*

Da dare su Mommy suka fara haramar tafiya ita da Aliyu, Fareedah dama mijinta ya zo ya dauke ta. Kafin su fita sai ga Doctor Saleem ya shigo, ya yi musu ya mai jiki cikin sakin fuska ya hau tsokanar Mahboobah wai mai ciwon soyayya.

“Doctor na ji ana kiranka da tuzuru dazu ko kuwa dai tsokanar Ishraq ce?” Mommy ta tambaye shi, tana mai yabawa da halayen kirkin likitan, samun mutum mai gaskiya da amana kamar shi a wannan lokacin yana matukar wahala.

Murmushi ya yi yana kallon Mommy, “Rabu da su kawai Mama. Ai yau din nan na samu matar aure, zan huta da sharrinsu.”

Mommy ma murmushin ta yi, “To Alhamdulillah! Ai kam ya kamata ka mallaki iyali haka nan d’ana, kana da dattako sosai da sanin ya kamata. Iyalin ne kadai ya rage maka ka karisa zama babban mutum.”

“Na same ta yau Mama, a cikin ya’yanki ma.” Ya fada yana kallon su Haneefa.

Wani irin durum! Aliyu ya ji, gabanshi ya yi mummunar faduwa kishi na tirnike shi. Shi ya sa ya ce da Haneefa ta rinka saka doguwar hijabi da niqab amma ta ki, ga shi nan yanzu wannan likitan ne neman yi mishi santatta.

STORY CONTINUES BELOW

“Ah to ma shaa Allahu, lamari ya yi kyau. Ashe haduwa asibiti alkhairi ce.” Mahboobah ta fada tana kallon yanda Aliyu ke cika fam yana batsewa.

“Doctor wannan dai matar aure ce.”

Dukkansu suka kalli Aliyu da ya yi maganar babu dariya babu murmushi a fuskarshi.

“A’a dan gidan Mama, kwantar da hankalinka ni ma ba ita na kyasa ba, wannan wacce ta fi fara’ar nake ciki, ko matata?”

Dariya ya ba Mommy, har ita Saleemar ma. Wannan fa shi ne daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zak’i.

“Kanwata, ya sunan matar tawa ne?”

Ya fada yana kallon Mahboobah cikin zolaya. Mahboobah ta saki dariya tana ganin karfin hali irin na Doctor Saleem.

“Sunanta Saleemah…”

Da sauri ya ce “Shi kenan kuwa, an yi a daidai, Saleem na Saleemah.”

Duka dakin aka dauki dariya banda Aliyu da ke borin kunya.

“Kun ga mu bari mu tafi dare ke yi. Sai Allah Ya kai mu gobe.” Mommy ta fada har yanzu ba ta daina dariya ba, a wani baren na zuciyarta kuma dadi take ji, yanda ta yaba da hankalinshi, za ta so hada zuria da shi, sai dai ba ta da sauran wadda za ta hada shi da ita, sai Allah Ya sa da kanshi ya zabi Saleemah, tana fatan Allah Ya sa Saleemar ta amince, za ta fi kowa farin ciki da hakan.

“Gobe ma ba sai kun zo ba Mama, da safe za a ba ta sallama, ai ta murmure sosai, ki ga fa yanda take dariya kamar…kamar a mata refer zuwa psychiatry.”

Wata dariyar aka dauka, wannan karon har da Aliyu.

“To Alhamdulillahi ai haka ake so. Mun gode sosai Doctor Saleem, Allah Ya yi maka albarka Ya zama jagora a dukka lamurranka.”

“Ameen Mamana, da irin addu’ar nan taku ta ina mutum zai tabe? Na gode Allah da za ki zama surukata, ki yi ta saka mini wannan albarka.”

“Ba ka da dama.” Mommy ta fada tana ficewa Aliyu ya bi bayanta.

Doctor Saleem ya koma kusa da Saleemah yana fadin “Ba mara lafiya na zo dubawa ba fa dama, na ga giccinku ne na bi yo ku. Tun jiya zuciyata ta kamu da kaunarki Saleemah, ina son ki, Allah Ya sa ba a riga ni ba.”

Haneefa da Mahboobah suka tafa hannu, “Sally ku je waje tattaunawar za ta fi bada ma’ana.”

Ta harari Haneefa. “Kuna da damuwa gaskiya. 2 idiots kawai.”

Mahboobah ta sake kwashewa da dariya, “Ke kuma 1 idiot ko.”

“Ku daina fa ba na jin dadi kuna wa Matata taron dangi.” Ya fada yana kallon Saleemah da duk kunya ta gama lullube ta.

“Iyyyeee! Wannan love haka.” Haneefa da Mahboobah suka hada baki wurin fadi.

“Ba wata tattaunawa da za mu fita mu yi, yanda Mommy ta ba ni kyakkyawar shaidar nan ai gwara in karisa tabbatar mata.” Ya yi murmushi “in fara tuntubar magabatanta idan ba a yi mata miji ba an ba ni dama kun ga sai in dama.”

Haneefa ta ce “Mu ne nan maganatan nata ai, ba mu yi mata miji ba kawai ka zo mun ba ka dama.”

Da karfi Saleemah ta kai mata duka. “Ya Allah ka shiryi wadannan idots din kawayen nawa.”

“Eh mun dai ji, amaryar likita.” Mahboobah ta fada tana mata gwalo, a daidai shigowar Ishraq dakin. Suka gaishe shi, Doctor Saleem na fadin ango ka sha kamshi, amma Mahboobah ba ta gane manufarshi ba, don babu wanda ya fada mata an daura aurensu.

“Amarya da kawar amarya ku zo mu yi magana, ku bar wadannan su tattauna.” Ya fada yana dariya. Ishraq ya daki kafadarshi. “Ba ka da dama tuzurun abokina. Amma amaryar waye?”

“Amaryata mana, Saleemah matar Saleem.” Ya ba shi amsa yana nuna kanshi.

“Ahh ka ce dai tuzuru ya kusa fita daga sahun tuzurai.”

“In shaa Allahu. Yo ce maka aka yi kai kadai ne angon? Ni ma nan to be ne. Ehe!”

Da dariya ya fice, Haneefa da Saleemah suka bi bayanshi hade da tura musu kofar.

Kallo guda Mahboobah ta yi mishi ta kawar da kanta, ya matso kusa da ita yana fadin “Sannu patient.”

“Yauwa.” Ta fada a takaice.

“Ya jikin naki?”

“Na ji sauki.”

“To Allah Ya kara sauki.”

“Ameen.”

Daga haka dakin ya yi tsit, kafin ya bude ledar da ya zo da ita, ya ciro gasasshiyar kazar Hausa ya bude. “Na tabbata ba ki ci abincin dare ba. Ko?”

Ta daga masa kai, tana dorawa da “Amma na koshi.”

“Ban gane kin koshi ba Boobah. Kina nufin ina ji ina gani in bar ki ki kwana da yunwa?”

Ta daga mishi kai.

“A’a wasa kike yarinya. Bude bakinki in ba ki da kaina.”

“Ka ba ni zan ci to.”

Murmushi ya yi sannan ya mika mata takardar kazar yana bude mata lemun exotic. Kadan ta ci ta ce ta koshi, ya ba ta lemun ta sha sannan ya mika mata tissue ta goge hannunta.

Zan je toilet in wanke hannunta.” Ta fara kokarin sauka daga gadon. Da sauri ya tashi ya dafe ta. Ta dago kai tana son cewa ya sake ta, tana son tuna masa da ba muharramai ba ne shi da ita, sai dai yanda ya watsa mata idanuwa cike da kauna ya sanya ta kasa musa mishi, sai dai ta fara kokarin raba hannunshi da jikinta amma gam ya rike ta, da kanshi ya kai ta toilet din ta wanke hannunta sannan suka dawo.

“Boobahna…” Ya fada cikin wata irin murya, yana manne hannuwansu wuri guda. “I love you so much, ina son ki da dukkanin zuciyata.”

Sai mutsu-mutsu take tana kokarin kwace hannunta amma ya ki saki. Da kyar ta ce “Ka sake ni Likita, ka manta babu aure a tsakaninmu.”

Hannun nata ya saki, yana amfani da nashi wurin tallabota ya manna ga jikinshi. “Na ji dadi da babu wanda ya fada miki zancen nan, na yi matukar farin ciki da a bakina ne za ki fara jin labarin an daura mana aure dazu bayan dawowar mu daga Hunkuyi.” Yana kaiwa nan ya hada fuskarsu a wuri guda, yana soka bakinshi cikin nata, da wani irin salo yake sauke kishirwar kissing a cikin bakinta.

End of chapter

Hello cupcakes…ya kuke ya gida da iyali? Fine in shaa Allah. Tafiyar tamu dai sannu a hankali ta zo karshe saura abin da ba za a rasa ba.

Sai mu hadu a shafin karshe idan Allah Ya nuna mana.

Thank y’all.

Princess Amrah

RAZ 2A karo na barkatai kenan da Mahboobah ke kiran Ishraq amma ya k’i dauka. Zuciya mai d’arsa abubuwa, a take sai ta fara ayyana mata wadansu abubuwan da ita kanta take jin su bambarakwai gare ta. Ko ya tafi neman Ameerah Muhammad ne?

Cikin sa’a tana kan wannan tunanin sai ga shi ya shigo, biye da shi kyawawan couple ne sanye da blue din kaya, namijin da shadda, sai matar kuma atampa ce mai manyan flowers blue, ta yafa babban mayafi kalar blue shi ma.

Murmushi ta saki a lokacin da ta gane mijin, ta mike da kyar ciki na rinjayarta tana musu iso. “Sannunku da zuwa Mr. and Mrs Muhammad Saddam.”

Murmushi ita ma matar ta sakar mata tana mika mata hannu suka gaisa.

“Likita daga ina ka samo min bayin Allah’n nan da nake yawan mafarkin jin d’uriyarsu?” Ta fada tana kallon Ishraq.

“To sai ki biya ni tukuicin kawo miki su da na yi ai.” Ya fada yana gatsine mata baki.

“Ba wani tukuici sai query da za ka amsa idan sun tafi.” Ta juya ga Muhammad Saddam. “Sannunku da zuwa. Sai kawai ga ku kamar daga sama.”

“Yauwa sannu Mrs. Ish. Daga gidanku muke, a can muka samu Ishraq shi ya taho da mu, da ma mun yi da shi a can za mu hadu, mu gaisa da Mommy, sannan mu taho nan.”

“Gaskiya kun kyauta sosai. Bari in kawo muku drink. Ga shi ko girki ban yi ba ban san da zuwan naku ba.”+

“Gimbiya Amrah ce ta ce in ce da Ishraq kar ya fada miki zuwan namu. Zuwan ba zata ya fi dadi.” Muhammad Saddam ya fada yana kallon matarshi mai zubin Larabawa.2

“Ba wani dadi ni dai, da kun fada min ai da na tanadar muku wani abu. Kuma wannan Likitan ya biye ku ya ki fada min.” Ta kalle shi hade da harara ta nufi kitchen. Dariya duk suka dauka bayan tafiyarta.

A tray ta dora jugs guda biyu, gudan cike yake da zobo chapman, sai gudan kuma kunun aya ne. Dama ita ba ta rabuwa da natural drinks, ba su cika shan na zamani ba. Sai ta dora glass cups a kai, ta kawo musu.

“Ga shi ku fara da wannan, ina da frozen samosa bari in soya muku.”

“Don Allah ki bar shi Mrs Ish, wallahi mun ci abinci a gidan Mommy, ba mu ma so ba Mommyn ce ta tilasta sai da muka ci.” Gimbiya Amrah ta fada cikin fara’a.

“To alhamdulillah! Sai zaman shan hira kenan.” Mahboobah ta fada tana zama da kyar.

“Ai ba zaman hira za a yi ba Boobah, wucewa za mu yi wallahi. Daga nan ma Airport za mu wuce, Kasar za mu bari.”

Bata rai Mahboobah ta yi tana fadin “Gaskiya ni dai ban gode ba da wannan ‘yar guntuwar ziyarar. Da kun so ai wuni guda za ku zo ku yi mana.”

Hakuri suka hau ba ta ta ce ta yi, sannan suka mike ta taka musu ita da Ishraq.

Lokacin da aka gama gwagwarmayar auren Mahboobah, babu kalar tashin hankalin da Muhammad Saddam bai shiga ba, mahaifiyarshi ce ta huce masa takaici da Gimbiya Amrah, diyar Sarkin Katsina, kuma diya ga kanwarta matar Sarki. Daga farko ya so cewa ba ya son ta, sai dai ganin gatan da mahaifiyarsa ta masa ya sanya amsawa, a karshe kuwa ya ji dadin zabin, domin Amrah yarinya ce mai tarbiyya wacce ta san darajar mutane, tana kaunar talaka tana sauraron koken dukkan jama’ar da suke kasa da ita. Idan ba an fada maka ba ma ba za ka taba gane diyar Sarki ba ce ba.

*2

STORY CONTINUES BELOW

Bayan sun dawo daga rakiyar ya kama mata hannu ya zaunar da ita.

“Ina ka ajje wayarka ina ta kiran ka ka ki dauka?” Ta tambaye shi tana bata fuska.

“Ina gidan Mommy ne lokacin, ba na in dauka ki ji muryoyinsu tunda sirri ne muka yi da su.”

Ta sake bata fuska tana turo baki gaba. “To me ya hana ka fito waje ka dauka? Ba ka san yanda ka daga min hankali ba ne.”

Wasa yake da yatsunta ya ce, “To ki yi hakuri na karbi laifin. Amma to ke da me kike tunanin ya hana ni dauka?”

“Abu biyu ya zo min a rai, na farko ko ka tafi Asibiti, sai kuma na tuna yau ba ka da aiki. Na biyun kuma…” ta yi shiru tana raurau da ido. “Ban sani ba ko Ameerar taka ka tafi nema, don dama ka taba fada min ba za ka taba daina neman Ameerah Muhammad ba.”2

Fuskarshi ya shafa yana gyada kanshi. “Baby rigima. Neman Ameerah ai ya dade da karewa Boobahna. Ko da a ce ba ki amince kin dawo gare ni ba ai dolena in hakura da nemanta.”

“Me ya sa?” Ta tambaye shi cikin mamaki.

“Saboda zuciyarta ce a tsakanin kirjin Matata muradin zuciyata. Zuciyar masoyiyata Ameerah ita ce aka dasa wa masoyiyata Mahboobah Bukar.”2

Cikin mamaki ta zaro ido tana kallon shi.

“Yes…Boobahna. Ameerar nan da kuka je gidansu Hunkuyi tare da Mommy, ita ce dai yarinyar nan wacce daga kallo daya ta tafi da imanina. Kuma ita ce wacce abokina Noor ya so aure mahaifinshi ya shiga tsakanin soyayyarsu.”

“Allah Sarki!” Mahboobah ta fada tana jin hawaye na sauko mata. “Allah mai tsara lamurranSa a duk sadda ya ga dama. Ban san ta ba ban taba ganin ta ba amma ina rayuwa da zuciyarta. Allah Ya ji kanki Ameerah, Ya sada mu a gidan Aljannah.”

“Ameen.” Ishraq ya fada, yana dorawa da “Idan da hali kin yarda in aure ta gidan Aljannah?” Yana murmushi.

Ta kai mishi duka da karfi, “Ni dai gaskiya ban yarda ba. Yanda kake sonta din nan ai sai ka fifita ta a kaina.”

Dariya sosai Ishraq ke yi, “Wa ya fada miki ana kishi a Aljannah? Ai kishi a iya duniya ne kawai. Allah dai Ya sa mu yi kyakkyawan karshe.” Ta amsa da amin.

Ta mike za ta kwashe drinks din da ta kawo ma su Muhammad Saddam ke nan suka ji sallama. Ishraq ya amsa yana mikewa.

“Wani nake gani kamar Mr. Noor.”

“Ni ne da kaina, ko in ce mu ne ma. Tare nake da Meerah.”

Mahboobah ta juyo tana yi musu sannu da zuwa.

Da taimakon Noor Meerah ta dogara sandunanta a jikin bango sannan ta zauna. Da sakin fuska suka gaisa, ta gabatar musu da drinks din da za ta dauke da farko.

“Mun zo gidan wata Aunt dinta ne nan cikin Unguwan Rimi, shi ne na ce bari in biyo ta nan mu gaisa. Da yake jiya ta fara fita, muna dan zagayawa gidajen dangi ne.” Noor ya fada yana fadada murmushinshi.

“Alhamdulillah jiki ya yi kyau Maman Ameer. Wancan zuwan na karshe da muka je duba ki bai kai haka ba, ga shi yanzu sannu a hankali kina ta kara samun sauki.”

“Aikuwa dai Mahboobah. Gaskiya Alhamdulillahi muna ganin ci gaba sosai. Likita ya ce in shaa Allahu ma duka zan warware.” Sameerah ta fada tana zuba kunun aya a kofi.

STORY CONTINUES BELOW

“Gaskiya ne in dai an dage kina dan tattakawa zai yi sauki in shaa Allah. Allah Ya yaye miki.”

“Ameen” suka fada su duka.

Minti ashirin suka yi suka mike, suka raka su har bakin mota, Ishraq na ba Noor labarin Muhammad Saddam ya yi aure, ya auri cousin dinshi.

“Lallai shi ne ko gayyata babu.” Noor ya fada yana bude kofar mota.

“Duk cikin Sameerah na kwance asibiti ne shi ya sa ban fada maka ba, amma ni na je har Katsina da ni aka daura aure. Yanzu ba da jimawa ba suka bar nan ma, za su tafi Atlanta, America.

“Allah Sarki! Allah Ya kai su lafiya. Bari mu wuce Mr. and Mrs. Ishraq. Allah Ya raba lafiya.”

Godiya sosai suka yi musu sannan suka koma ciki, Mahboobah na fadin, “Wallahi na matsu in sauke wannan zundun na gabana.”

“Ni kam ban matsu ba, na fi son ganin ki a haka, kyau kike yi min.”

Ta harare shi, “Eh saboda ba kai ke fama da nauyin ba ai dole ka fadi haka. Ni damuwar ma ga bikin Sally na matsowa haka zan je ina fama da ciki ko kwalliya na yi ba zan yi kyau ba. Shi ya sa na roki Mommy a taimaka na Yah Aliyu da Hanee dai a bari har in haihu sannan.”

“Waye ya fada miki idan kin yi kwalliya ba kya kyau? Ni dai ina ganin kyan kayana.”

Ta tabe baki, “Ni kama ni in tashi. Gida ma nake son zuwa gobe.”

“Allah Ya kai mu. Dazu da na je gidan Mami take fada min wai Bilkeesu ta haukace, kwaya ta haukar da ita.”

Zaro ido Mahboobah ta yi tana fasa tashi. “Wacece ma Bilkeesu?”

“Wannan ‘yar uwar tawa da ta hada plan, silar rabuwarmu.”

Cikin mamaki ta ce

“Oh haka fa, sunanta Bilkeesu ashe. To ita dama yar kwaya ce?”

Ya jinjina kai.

“Allah Sarki har na tausaya mata. Mutane suna ji suna gani su rinka jefa kansu ga halaka. Allah Ya shirya mana zuri’a, ita kuma Allah Ya ba ta lafiya.”

*

Bayan Wata Biyu

Rigima ake ta yi da Mahboobah ta ce ita ba za ta yi taron suna ba saboda CS ne aka yi mata, amma su Fareedah sun ce dole sai ta yi, Ishraq ma ya ce yana so a yi. Ba ta da yanda za ta yi dole ta hakura aka yi din, yaro ya ci sunan Muhammad Saddam, Ishraq ne da kanshi ya zaba mishi wannan sunan, saboda sadaukarwar da Muhammad Sadddam ya yi masa, ba zai taba mantawa da shi ba a duniyarshi.

Ranar suna kuwa sun ga karamci, domin kuwa har da mahaifiyar Muhammad Saddam sai da ta hado sha tara ta arziki ta kawo ma Saddam karami, Gimbiya Amrah matarshi ma ta hado kaya na gani na fada. Saleem da Saleemah ma da nasu, haka Fareedah ma, Noor da Meerah ma da nasu, Aliyu da Haneefa da ya rage wata daya bikinsu ma ba a bar su a baya ba.

Watan Saddam karami bakwai Mahboobah ta kara samun wani cikin. Ta shiga tashin hankalin wannan ciki da goyon amma Ishraq ya kwantar mata da hankali,

“Wasu da yawa suna can suna nema amma Allah bai ba su ba. Saboda haka ki rungumi wannan kyautar da Allah Ya yi mana. Albarka kawai muke nema.”2

Haka ta ci gaba da rainon cikinta har Allah Ya sauke ta lafiya a wannan karon da kanta ta haihu ba CS ba, Ameerah  ta zaba ma yaron suna Abubakar. Ishraq ya aminta da zabin nata, ko ba komai kuma sunan mahaifin Mahboobah ne dama, suke kiran sa da Musaddiq.

Rayuwa ta yi wa wadannan mutanen dadi, duk da ba za su ce a tsawon wannan lokacin kullum cikin farin ciki suke ba, dole akwai sabani na yau da gobe wanda ka gitta tsakanin duk wadanda suke zauna tare. Sai dai kara godiya ga Allah da suke yi a kodayaushe, saboda rayuwarsu ta yi kyau, suna tsananin kaunar junansu, kowa na sha’awar soyayya da yanayin zamantakewarsu.

Babu yanda ba su yi da Mommy ba a kan ta rike Ameerah a wurinta don ta samu mai debe mata kewa tunda Yah Aliyu ma ya yi aure yanzu, amma ta ce a dai samo mata mai aiki kawai, su rike Ameerarsu ta san dole za su fi bukatarta a tare da su. Ba su da yanda za su yi dole suka samo mata dattijuwar mata suke zama tare, haka Mami ma suka samo mata.

Ishraq da Mahboobah, Aliyu da Haneefa, Saleem da Saleemah, Noor da Meerah, Muhammad Saddam da Amrah, haka suka dunkule suka zama zuri’a guda mai tsantsar hadin kai da kaunar juna. Babu wanda zai ce dukkansu babu alakar jini a tsakaninsu. Haka tsakanin yaransu ma.

Bayan Shekara Goma.

Wani matashi ne rataye da jikkar goyo, hannunshi kuma babbar jikka ce ya dauka, gudan kuma wayarshi. Idonshi kamar zai kawo ruwa yake duban ta,

“Ki rike mini amana Matar Ameer, kar ki bari soyayyar kowanne namiji ta yi tasiri a zuciyarki. Kar ki auri wani ba ni ba Ameerah. Ki kula min da kanki, ni ma na yi alkawarin zan kula da kaina, ba zan taba cin amanarki ba.”

Hawayen da ke kai-komo a saman fuskarta ta shafe,

“Na maka alkawarin kulawa da kaina Mijin Ameerah, babu soyayyar wani d’a namiji da za ta iya yin tasiri gare ni. Am going to miss you.” Ta fashe da kuka da sauri tana barin wurin, ta je ta labe. Tana kallon sadda ya shige ciki, ba ta tafi ba har sai da ta ga tashin jirginsu.

Da kuka sosai ta shiga mota, drebanta na ta rarrasarta amma ta ki shiru. Tunanin yanda za ta yi kewar Ameer dinta kawai take yi.1

(Labarin MATAR AMEER na nan zuwa sai dai ba rana ba lokaci😂🙌🏻)

The end!

Alhamdulillah!

With a heavy heart, I am finally putting down the pen😪saying farewell to BAKUWAR FUSKA after 1 beautiful year😍🙌🏻. It was an amazing journey with you all. Anyway, I just wanted to say how thankful I am for you guys🥰My loyal, beautiful, kind friends on here, and I mean all of you💕As my readers, I consider you my friends, you’all are truly amazing and cannot thank you’all enough for the love and support you give this book😍🙌🏻I can never thank you enough. I love you, all of you, never think otherwise😁❤️I try my best to show you all so much loy because you all mean the world to me. I hope to continue this journey with you to my next book, and my next and my next in shaa Allah😻🙌🏻

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *