BARAUNIYAR ZAUNE COMPLETE

 BARAUNIYAR ZAUNE COMPLETE 

Ya yi zuruu yana kallonta, ita kuwa sai kwasar lomar ɗumamenta take yi, jefijefi takan kai kallonta kansa, sai kuma ta kauda kai, cikin mintunan da basu gaza biyar ba ta tashi da kwanon, bayan ta suɗe ta lashe hannun, sai ta tura ma yaron kwanon “Dan Abba jeka ka cewa Indo ta zuba maka wani tunda na cinye maka wannan” Yaron ya tashi ya fice, ita kuma ta shafe guntun kukar dake hannunta bisa gashinta, ta mutsitstsike hannun, sa’annan ta warto moɗar ruwan dake gabanta ta kwankwade, ta saki gyatsa ƙyatttttt gami da faɗin “Wayyo Malam”.+

“Kirrrrrrr!”
Ƙarar ru6ar6ar wayarta ta cika d’akin, da sauri ta wawurota tana addu’ar kar ru’ba’b’ban kyauren data daura mata ya fice, asirin batirinta ya tono, sai dai duk wannan saurin kafin ta latsa kore, har kiran ya dauke alamun flashin akayi.
“Mtsss!” Ta ja dogon tsaki sa’ilin da taci karo da sunan matar ‘Hajja Salma Kilishi, ita wannan banzar Hajiyar bata son kiran mutum sai flashin, kamar ba jiya na gama fadimata banda ko kwabo cikin wayar ba’ Tayi kwafa gami da gyara d’aurin kirjinta.

“‘Dan Abba..”
Ta kwala masa kira.
“Maza tafi gurin Ɗan Kande kace ya turomin MTN na Hansin idan Babanku yazo za a bashi.
“Mama Abinci nake ci” Yaron ya bata amsa.
“Ka tashi ka tafi nace dan kwal ubanka abinda zaka ci gobe za a samo da katin.

Ta zurama wayar ido, shud’ewar wasu mintuna ‘karar masssage ya shigo.

Ta wawura da sauri game da latsa ‘kore kan sunan Matar.

“To uwar Flashin kiran namenene da uwar safiyar nan!”
Daga can 6angaren aka saki dariya gami da fad’in

“Hmm! Kedai bari Dilar Daddawa, wasu sabbin pics na samu daga India yanzu, da alamu zamu kwashi rabonmu da su.”

Ta saki dariya duk da da fari ta tsuke jin sunan da ta tsana a kirata dashi.

“Ohhh kilishin Alkhairi, kice zamu wanki gayu, amman wa kika samu a india?”

“Wata hajiya ce irin mu, amman ta nuna min akwai tabbacin indai ta turo kayan to zasu samu shiga. Dan ba kanana bane. Yanzu dai ki hau facebook na turamiki hotunan kayan ki fara tallah”

“Allah Hadamu da mai rabo” Dilar daddawa tayi saurin furtawa.
“Amin!. Kilishi ta amsa.

Ta bud’e facebook kai tsaye inbox din Kilishi ta bud’e, taci arba da hotunan ita kanta duk yawonta tsakanin wambai, sabon gari,bata ta6a cin karo da takalman yara masu kyawun wadannan ba, haka zannuwan gadon. Ta ga an rubuta mata 1500 kan kowanne takalmi guda, sa’ilin da zanin gado duk d’aya dubu 10000. ta sau murmushi lalle sunci kudinsu.

Kai tsaye group dinsu ta nufa mai suna ‘KASUWANCINKA SA’ARKA’ Ta yi postin kayan, cikin abinda bai gaza minti goma ba har an mata cmnt 20. Kowa yaba kayan yakeyi da tambayar kudin. Sai sannan tayi cmnt ta rubuta takalmi dubu 2000, zanin gado dubu 15000.

Commnet din da ya biyo bayan nata yafi kowanne d’aukan hankali. Da alamun zakuwa akai cmnt d’in.

Fadima Batool
Kai dan Allah Anty Jummai ina zan sameki, wallahi ina son zanin gadon. A Jos nake.

Ummita Asal
Ni dai takalman nake so kafa goma amman dan Allah amana discount. A kauyen Da’banow nake.

Salma Kilishi
Wai! Wai! Wai! Gaskiya sister kayan sunyi arha, matar uncle dina ta ta6a siyan zanin gadon can 30K a Dubai.

Tayi saurin mannawa Salma kilishi like gami da tuntsirewa da dariya tana kore kudan dake bin bakinta.

Bingel🤔
[8:02PM, 24/04/2016] Bingel: 🐀BARAUNIYAR ZAUNE🐀

By BINGEL MITA

2.

Ta kira Hajja Salma.
“Ke a ina kike da yan uwa masu zuwa Dubai bansani ba?” Ta kunshe dariya
“Ai kinsan sai da 6adda tunani, da kuma nuna rashin sanayya” Suka tuntsire da dariya a tare.
“Yanzu ya kukai da Hajiyar Indian ?”
“Oh tace nan da jibi kayan zasu iso, kawai agent dinta na cirowa zanje na kar6a gurinsa”

” To Allah kawosu” Amin! Suka sauke wayoyin a tare.

Ta ‘kara komawa facebook cike da fatan kar Sub dinta ya ‘kare har sai sun gama business dinnan. Kai tsaye inbox din Batool ta wuce.

Salam!
Anty Jummai ce.

Fadima Batool
Yauwa Anty, dan Allah ya za ai na samu zanin da wuri, auren kanwata za ayi satinnan mai zuwa.

Anty Jummai
Kingani karki damu su kayan fa suna kasa yanzu haka. Ki fadimin danginki dake kano sai kawai na kaimusu su bani kud’ina.

Fadima Batool
Anty bamu da kowa a kano mufa, sai dai inni zan zo na ‘kar6a.

Anty jummai
Ta nunfasa cike da godiyar Allah.
To ai wannan ba damuwa ba ne kibari kawai zan bawa motar dake zuwa can Jos d’in kai tsaye zasu kawomiki har tasha sai ki kar6a. Kuma karki biya komi zan biyasu duk cikin kudin kayan, sannan na miki ragi tunda kece, yar kanwata kibiya 12k kawai.

Fadima Batool
Cikin tsanin murna tunaninta ya manta komi sai murnar antyn nan na da mutunci.

To Antyna ajemin account number dinki, in turomiki kudin biyu yanzun nan. Nagode da kirkinki gareni.

Anty Jummai
****************(account number)
Nima nagode.

“Wannan ta kamu ta furta a ranta” sai ta doshi gurin UMMITA ASAL yar kauyen Da’6anow. Mtsss! Ni ban ma ta6ajin sunan kauyen ba. Ta furta tana rankwashin kwarkwatar kanta.

Itama nafsin abinda ya faru da Fadima Batool shi ya faru kanta, sai dai ita maimakon account number, katin waya ta ringa siya tana turomata har na 15k bayan an zare mata ragin 500 cikin kowanne takalmi guda! Kan sari. Ta kuma bata tabbacin kauyensu tsakanin Marke da Kaugama yake (Inji ni na sharo)

A wanshegarin da kayan suka zo, da sassafe taje ta sunkuyawa Malam, abinda bata saba masa ba, ya kalle ta ya watsar sai kuma ya jawo tsinke yana sakace hakoransa.

“Malam kayan mu sun zo zamuje mu kai su kasuwa”

Yayi tsai yana kallonta gatanan dai kullum tace kaya sunzo, amman baita6a ganin kudin kayan ta amfana dasu ba, ita ba iyaye ba, balle yace su take kaima, ba kuma ya gani a jikinta, balle kuma a kwanonsu, hatsine na dawa kullum shi suke nad’a. Hana rantsuwa dai ta taba siyomasa Asuwaki dan Naira 20.1

Ya saki tsuka kadan gami da furta “A gaishesu” Ta mike tana juya burkotunta tana wani kada sakakken jikinta, karamin danta ya bita da kallo. Har ta isa bakin rijiyar gidan.

Da hanzari ta jawo sabulu yankan goma ta daga hammatarta tana gogawa. Malam yayi saurin kauda kai game da kara sautin radionsa. Ta goggamsa ta watsama hammatan ruwa, ta wanke wuyanta, da kafafunta. Tayi saurin shigewa daki gami da mutsikka kitsan rago. Cikin abinda bai gaza minti goma ba, sai gata ta fito cikin bugaggiyar bakar jallabiyarta zubin gidan giya. Ta maka hijabi. Gami da furta “Dan Abba zan kawo ma tsamiyar biri, sai na dawo”.2

Ka tsaye gidan Hajja Salma ta yi, cikin azalzala itama tayi nata salon, suka fito da kayansu niki niki sai kasuwa. Cikin awa biyu da shigarsu kasuwa suka rabar da kayan har ma sun kar6i fin rabin kudin.

Sai sannan Dilar daddawa ta numfasa tana kallon Hajja Salma.

“Ni wai kuwa za a samu samfurin takalman nan, da zan turama waccar yar da6anow din?”
“Za a samu mana ai bamu kewaya bane”

“To muje, ita mai bukatar zanin gado nasan yanzu zamu samu bugun garada sai mu hadata dashi, komai hotan sarkin masar ne.”

Hajja salma ta kwashe da dariya tana dubanta, ke wanan yarinyar fa ba yar gidan kananun mutane bace, gwara mu samu wadanda basu gaza 4k mu sai mata. Wane irin bugun garada kamar itace a Da’banow ? Suka tafa kana suka fara dube dube.

Can gurin masu baza kayansu a buhu ta hango takalman roba shakalin wadanda suka siyar, nan da nan tayi gurin, tashin farko yace musu 80, latsin farko ya dawo 500 nan da nan suka kwashi guda goma suka wuce.1

Haka gurin masu zannuwan gado, ba 6ata lokaci suka samu masu kyau kan dubu 4500 guda biyu, shima suka siya suka wuce.

“Ya kamata ki sai sabuwar waya yau”

Hajja salma ta fadi tana kallon Dilar daddawa, bayan sun isa gidanta.

Bingel🤔

Bata tanka mata ba illa raba kuɗin hannunta da tayi gida biyu, ta soke guda bisa haɓar zaninta, sauran kuma ta miƙawa Salma “ajemin su inda kika saba tara min”+
Hajja Salma ta karɓa tana mata wani kallo mai wuyar fassara “ina miki maganar waya fa, ya kamata ki sayi sabuwa, muje kuma a gyara miki gashin kanki ko ‘wash and set’ ne kiyi, ni duk rashin kulana bazan iya barin kaina wata uku ba wanki ba gaskiya”

“Naji ki ai! Ni yanzu abin da ke gabana zanyi tukun, gobe da sassafe nake so in tafi Takai in tako daddawata,  dan ta gurina ta ƙare, daga nan naje tashar mota naji yaya zamuyi da yaron Oga”

    Ta fad’a tana haramar wucewa.

“To ai shikenan, kindai san dole ki gyara jikinki, dan kuwa rigunnan da muka bawa mu’azu tela yace mini ya kusa kammalawa. Wallahi ba zamu je ɗaukar hoto dasu ba camera na nuna barbaɗen garin daddawa a jikinki!” Ta faɗi tana ɗauke kai.1

Ta ƙuta sosai da alama zancen nata na karshe ya taɓata. “Mtsss!” Taja tsakin da ya zama ɗabi’arta ta ce “kina wasa ne, kindai san ba gyara ba, a yanzu inna so siyan _Iphone_ ma ba wanda zai gwada mini banda abinda zan siya. Kawai tunda na ce miki ki kyaleni da NOKIA ASHAta ta fiye mini ke da malam, to kisamamin lafiya mana”

“Yo mu gani a kas mana!”  Hajja Salma tayi saurin cafewa.

To doka mata harara gami da ƙarasa ficewa daga gidan.

Hajja salma tabi kuɗin hannunta da harara “wawuya kawai”  Ta faɗi gami da tsartar da yawu jikin butar maigidanta.

“Dilar Daddawa idan an ganki anga kalwar Alheri” Ta murmusa cikin son nuna sunan baitaɓa taba “Yaron Oga samuwa ce, ta garin jos da wani Ƙauye wai shi Daɓanow”

Yayi tangal tangal kamar zai rarumeta sai kuma ya tsaya cikin rashin tazara ” To ai mai sauki ne, akwai akuri-kura mai zuwa Dabanow, sai a bashi, Jos kuma nasan yadda zanyi, ke dai kawai aje dubu 10000 kiga aiki.

Tai saurin rike ha6a gami da ja baya kadan. “A haba yaron Oga ya rashin ta ido haka kamar yau aka fara ? Ka manta na dauke ma kwanon dare, gidan Hauwa jiddah ta gujungu mai tuwan gwal ? Kawai ka karɓi biyar in yaso masu kai sakon sa farke sanda suka isa gun masu sakon, ai ka gane karatun ?”

Ya kwashe da dariya yana buga kafa ” Shege mugu yasan mafakar mugunta, duk da kin hada da gori shikenan kawo kudin da sakon kawai, ki tabbatar musu nan da jibi zasu ga sako.

Ta murmusa tana kwance haɓar zaninta, ta kirgo 5k ta bashi, ta kara masa da 500 yasha sukudayeee. Kana ta sunkucin buhun daddawarta  ta aza bisa ka, takunta kadan wani Almajiri yasha gabanta “Iya kawo na kai miki mota” Ta ɓalla masa harara gami da ƙoƙarin hankad’eshi ta wuce. ‘Yar kasuwa kamata wai yana kirana da Iya ?” Hmm! Ta yi ƙwafa.p

Ta na isa gida, wayarta ta rarumo sai facebook, ɗaya bayan ɗaya ta bisu da albishir ɗin kayansu jibi zai iso, suka dinga jibgamata ruwan godiya kanta na ƙara fasuwa.1

Cike da rashin tsoron Allah taje tayi blockin din FADIMA BATOOL da UMMITA ASAL bayan tayi removing dinsu daga group din KASUWARKA SA’ARKA.1

“Game over!” Ta furta tana sakin wata wawar mikaa.

                     Cikin farinciki ta aje wayarta bayan jin albishir din da Anty Jummai ta mata. Cike da rashin sa’ar lura da launin bakin da sunan Anty jumman ya koma, maimakon blue da aka saba gani kan kowane suna da babu katanga tsakaninku. Gaba daya ta fesawa danginsu da suka zo aure irin zanin gadon da ta saima ‘kanwarta, harda karin daga Saudiyya za a kawo mata su, masu tsada da mutunci.

              ‘Karfe goman safe a tasha ta mata, ta zauna zaman jiran awa 2 kafin taji kiran mai motar. Kai tsaye ta doshi gurin d’an motsatstsan yaron da ta gani tsaye yana yafito ta, alamun dani kike waya. Kanta a sama ta watsa masa “Sannu fa!” Ya kalleta ya maze, sai kuma ya tsuke fuska yana furta “Ga kayanki can gun ubangida, biya abinda zaki bayar a miko miki”  Ta sau murmushi cikin rashin damuwa, da tunanin yana zolayarta ne. Ta yatsine fuska irin na yan matan da suka gogu da gayu ” Okay! Nawa zan bayar to”  Da hanzari ya furta “Dubu 7K, ai kayan naki ba wani nauyi ma garesu ba”  Tayi baya da zare ido, sai kuma ta dake “Ina lefin kace 20k” Ya tsuntsure da dariya da alamun ta burgeshi ” Ah’ah kawo dai yarda na fadimiki Oga na jirana mu fasaa”

“Au wai da gaske kake?”
Ya kankance ido yana kallonta
“Ke yarinya bamasan yawa fa”
“Wai banfa gane ba ? 7K name, bayan mai kayan tace ita zata biya kudin kawowa”
“An kuma ya fada aransa” Sai kuma ya maze dan baiga dalilin tsayawa yimata bayani ba.

“Ke in kinga baki biya kawai na ware, kila biki damu da kayan bane”

Ta dubeshi cikin rashin hayyaci, sai kuma ta kewayeshi zuwa gurin direban dake zaune a mota yana kallonsu. Kantace komi ya tareta ” Duk abinda ya fadimiki haka zaki biya yarinya”   Ta yi shiruu, sai kuma ta barma ranta kan cewa kawai suna son cutartane amman Anty Jummai ta biyasu.

“To dan Allah zan biya dubu 2k
“Kinsan Allah in ba 3k ki tafi kawai”
Ta kalli jakar kayan ta hadiye yawu mukut.
To! To fadi tana kokarin zuge jakarta. A ranta kuma tana jan Allah ya isa!

          Cikin d’oki take kwarama ‘kanwarta Ladeefat Amarya kira, suka taho rududuudu kowa burinsa yaga zanin gado dan Saudiyya.

“Jar uban can” Ta kudundumuta
” Otii damii(ta cuceni)” Ta mako yarbanci
” Uwa cucenim ma” Ta hado kanuranci
Ta kara warware zanin gadon mai hotan masara, jikinta na rawa. Sai kuma ta rarumu waya. Da himmar jin ba’asi gun Anty jummai. Babu notification balle sunan anty jummai. Ta kara zaro ido, kan ta maidasu kan zanin gadon masararta.

“ㅁㄴ오ㅗㄹㅎㄷ샿너루ㅜ ” Ta daddage ta koma chinanci, sai gata ta mi’ke tana gwada ‘kushaaaa mai kutufo irin nasu Jet li, sai kuma ta zabura ta danna a guje, aka bita ana ataro! A taro!! Akwai alamun Aljaninta ‘tashi muje mu ne’  Ya diro.1

Yan biki kowa yaji labari sai ya ri’ke ha6a ? 33K at dis situation ?.

Ummita Asal.

Ta kalli takalman cike da takaicin dubu gudanta da mai akori kurah ya kar6e. “Ta kuta idanuwanta jajur wai ni za a nuna ma Birninci? Kinsan Allah Farha sai na haddasa ma matar nan yoyon fitsari ? Ta fada tana kallon kawarta dake tayata jimami. “Abin har haka yakai ?” Farha ta fadi tana zaro idanuwa. “Haba, haba kudin adashinsu Shukra ne fa na had’a nayi sarin takalman, wai danna juyasu kafin daukarsu tazo nima naci riba 15k fa ?

Farha tai saurin rike ha6a “Amman matar nan anyi shegiya, ya kamata mugano gidanta muje muyima banza dukan tsiya, amman wanann takalman 200 fa na gansu a kasuwar laraba. Wannan wace irin yaudara ce?

Ta ɓantaro goro ta wulla a baki, sai kuma tayi saurin furzarwa da alama bacin rai ya hanata jin dadinsa.

“Bari Malam balarabe ya dawo, sai na sa matarnan fitsarin 15k a gidan sirikanta, karewa ma a kwanon tsohon mijinta.1

Farha ta yi saurin sadda kai, akwai alamun batasan fidda dariyarta waje.1

Bingel🤔

Kinsan Allah wannan karon ba zamu fita gun masu hotan nan ba sai kinyi wanka. Kina wasa dani Dilar Daddawa, billahillazi ni mai ɗaukan rigunan nan ne in watsa  musu kananzir da ashana kowa ya rasa!”

  Ta zabura hannunta a kan kirji tana wara idanuwa, sai kuma ta sunkuya ta sunkuci sabulunta kore shar yankan goma, ta warci soso ta fice tana gunguni.+

“Dilar daddawa”

Taji ta sheƙa mata kira kafin kuma tasha gabanta.

“Ba ni sabulun nan ki bawa ɗan Abba Naira 40 ya siyo miki GIV kiyi wankan dashi, wai ni ke wannan wane irin jaraba kika ɗorama kanki ?”

“Likita ya hanani wanka da sabulu mai ƙamshi.”

Ta warce na hannunta tana shinshinawa.

“Shi wannan din ba gashi ƙanshin

ƙarni yake yi ba?”

“Dan Abba!” Ta kwala ma yaron kira.

“Tafi ɗakin Mamanka, ka bincika inda take aje kuɗi, ka ɗauko mini Naira 40, ai kasan ma’ajiyarta ko?”

Yaron ya kalli Mamansa yaga yadda take huci tana watsa masa harara sai ya sadda kai ƙasa.

“Ai a jikin zaninta take ƙulle kudinta, har cinikin daddawarma”

Hajja Salma ta zuba hannu a ƙirji cike da mamakin Dilar D, sai kuma ta zuge aljihun jakarta ta zaro hamsin gami da danƙawa yaron, “jeka siyo mini sabulun wanka, kace GIV”.

Yaron ya karɓa ya falla a guje, ita kuma ta dubeta “Na rantse miki da abinda zai kasheni a kuɗinki na ajiya, na fiki maƙon bala’i, amman bazan ƙi yiwa jikina ba”.

Ta zuba mata tsaki ranta na matuƙar kuna, inda abinda ta tsana  a taɓa mata bai fice kudinta na ajiya ba, kawai sai ta ɓalle gefen zanin da tai ɗaurin kirji sai ga kudi cunkus suna samamin daddawa, ta ware hamsin ta jefa mata “Gashi karki taɓamin kudina jarababbiya.” Ta sunkuya ta dauke tana murmushin mugunta. ” Da Allah in kin shinga ki wanko kanki, akwai shampoo da ake sawa a giv sabida irinku masu ci  ajikin wasu”.

              Da jaraba da nacin Hajja Salma, sai da tasa atamfa mai  dan haske cikin kayanta kafin su fita. Kai tsaye gurin mai zanen hannu suka tafi, tayi musu mai kyau, daga nan suka wuce gurin mai hotansu. Abinka da ya saba cikin abinda bai gaza awa guda ba, sai gasu sunfito Fes jikin hotan, duguwar rigarnan mai ratsin pink da baki, tayi das jikinsu, a haka zaka musu kallon matan wani kusan gwamnati ne. Da ƙyar wayar Dilar D ta kar6i USB din computer mai hoto da za a tura musu hotunan. Dan ma mai hotan ya saba da ganin wayar.

      Bayan komawarsu gida suka kafa musu, ita hajja Salma ta dage hotan Dilar D za a saka duba data fita hasken fata harma da kyawun fuska, yayin da ita kuma dilar D take tsoron ranar nadama, ranar da asiri zai tono, kar wataran taga hotanta a like a bango, kamar yadda ake lika yan takarar gwamnati, ta lumshe ido tana hango WANTED a saman hotanta, maimakon HAJIYA JUMMAI ‘YAR TAKARAR SANATA. Dan haka ta ƙara kafewa, kan itafa sai dai asa na Hajja Salma. Daga baya dai suka sulhunta , kan su hada pic mix kawai  su saka. To da wannnan shawarar hankalin kowa ya kwanta.

Ba abinda yafi daukar hankalinsu bayan saka hotun, sai cmnt din wata MATAR ENGINEER. Hajja Salma ta dafe kirji, ke kinsan kudin matar nan kuwa balle mijinta ? Itace mai gidan gonan SUYA A MASAR fa ? Dilar D ta saki dariyan farinciki, ah lalle bara kawai na mata magana cikin girmamawa. Allah sa tace guda 20 takeson rigunan. Ta garzaya inbox

Anty Jummai.

Salam Hajiya. Mai riguna ce.

Matar Engineer

Oh! Hajja jummai, ai kinga cmnt d’ina a wane gari zan sameki fa ?

Anty Jummai.

Kano nake hajiya, guda nawa kike so ?

Matar Engineer.

Kash! Ni kam kinga ina Abuja. Guda 15 nakeson rigunan, kannawa zaki bani su ?.

Anty Jummai.

Kan 7k tunda kece, a hada miki kala-kala ko ?

Matar Engineer

Ae! Zan turo miki kudin zuwa anjima, sannan akwai yarana da yawa a kano, ko gidan SUYA A MASAR kika bawa zasu kawomin har gida. Amman fa a zuba min masu inganci pls.

Story continues below

Anty jummai.

Ai dole hajiya, yanzu da kaina zanje kasuwa siyo kayan dinkinma. Ga Account Number na.

*******9

Ta nuna ma Hajja Salma hirar suka saka shewa gami da fadin ta harbu.

Ta rakata zaure sukai sallama, ita kuma ta tsaya leke kamar yarda ta saba. Adai-dai lokacin data juya da nufin barin zauren, idanuwanta suka hadu dana wata mata dake zaune acan sakon unguwar ta zuba mata ido kamar bakar mujiya.

“Aniyarki ta biki”  Ta furta gami da juyawa tana kaɗa mata mazaunanta.

         

Wanshegari da wayar Hajja Salma ta fara karin kumallo. Cike da albishir ɗin kudin mrs Engineer sun shiga account. Dan haka tayi saurin zuwa suje kasuwa dan sanin madafarsu. Cikin hanzari ta gama shirinta, dan wannan karon Malam ya tafi gaisuwa ƙauyensu.

           “Ke me kike ganin zamu siya to a madadin rigunan ? Ko kawai a sai Abaya ?” Tambayar data fara watsama Hajja Salma kenan bayan isarta.

“Haba dai Abaya ai zamu kashe kudi, ina lefin yadin landin ai shima zai yi kyau da doguwar riga”

“Jar ubancan!” Ta tare ta tana zaro idanuwa.

“Amman bantaɓa sanin rashin imaninki yakai haka ba Hajja Salma. Ai yadin landin mukanmu munyi asara kenan, tunda ko jinjiri ba za a dinka masa shi ya saka ba. Gwara dai mu sai mata yadin hijabai masu kyallin nan, kinga ana doguwar rigar sallah dama dashi.

“To da kinsan haka kike tambayata”

“Ai neman shawara ce “

“To mu tafi iyaa magana”

              Da ƙyar suka samu kan 800 ko wane yadi hudu, nan dai suka tattara suka kaima tela, da jan kunnen lalle ya musu a kwana 3, tunda dai dinkin doguwar rigane mai hade da hijabi, ba wani kayan ado bane. Daga nan kowacce ta yi hanyar gidanta. Sai dai Dilar D tana gabda shiga gida, kamar ance d’ago kanki, caraf idanuwansu suka hadu da nafsin matar nan ta rannan. Ta maka mata harara hadi da fadin da alama sabuwar almajira sukayi a anguwar, bara na aiko abaki daddawa ko kwalli 3 ce gudun ido. ” kinyi sa a ma da zan baki har daddawar Naira talatin” Ta fad’a tana mako kyauren gidanta.

            Bayan kwana uku tela ya cika alkawari. “Amman kam sun dinku. Allah har naji kyashin ta samu kamar wannan” Cewar dilar D.

Hajja salma ta kwa6e baki “To mudau d’ai-d’ai mana, inyaso sai akaimata sha uku.

“Haka za ayi ƙawata” Dilar D ta furta tana kokarin zaɓar wanda zai mata.

Wannna karon Hajja Salma ce ta tafi gidan SUYA A MASAR kai kayan, kasancewar tafi Dilar D nuna ‘Aji’  a irin guraran nan. Ita waccar din barta dai da harkar yan tasha. Ba 6ata lokaci ta sami yaron da aranar ma zai tafi Abujan. Haka dai suka rabu cike da girmama juna. Kafin kuma ta komo gida, gami da tabbatarwa Dilar D kaya sun tafi. Dan haka ta gaggauta tsige Matar Engineer daga duniyarsu ta FACEBOOK.

Matar Engineer.

Tana zaune ta harde kafa daya bisa daya. Gefenta Meesha dillaliya ce data kira dan idan an kawo kayan, kawai ta wuce dasu gun masu siye. Har bayan rabin sa’a yaron da yace gashi a garin Abuja bai karaso ba. Dan haka ta tashi tana hamma gami da fadinma Meesha D in kayan sunzo kawai ta wuce dasu duka,ba sai ta tashe ta daga barci ba. kar kuma ta manta ta siyarmata kan dubu 9 duk riga d’aya. Meesha ta kar6a da godiya, gami da furta Insha Allah Hajiya.

Durkushe take gaban Malam tayi yar kwalliyarta ba lefi, sai gaigayin 6era take masa da alama akwai abinda take so. Can dai ta nisa “Malam zani sarin daddawa Takai”

Yayi saurin maida kai gefe, shi fa inba dole ba, ba abinda zai sashi zama da matarnan. Kullum cikin tambayar kansa yake wai miyagani ne har ya aureta haka? Gayu abinda zuciyarsa ke bashi amsa kenan. Lalle kam gayu, dan kuwa a lokacin duk fadin kauyensu baya ita gurin  gayu da ilimi, kasancewar itace wacce ta kammala karatu har na secondry a wancan lokacin.

“Malam ina magana”

Yayi firgigit daga tunaninsa.

“Ba zaki ba” Ya bata amsa kai tsaye

“Haba Malam kasan fa…Durumm!” wata kakkarfar tusa ta fito, sai da hular malam ta motsa.

Malam ya  zabura yana kallonta.

“Tashi!tashi!! maza jeki a gaidasu, wallahi bazaki kasheni ba. Jummai lafiya kuwa ?”3

Ta sunkwai da kai, akwai alamun taji kunya, wai danma ba yara. Sai dai kuma tayi saurin fuskewa.

“Lafiyar kenan! Kila kokon da na gama dirka ne. NAGODE”

Ta furta gami da mikewa.

              Da tsakar rana ta isa takai, kai tsaye inda take sarin daddawarta ta nufa, sai dai danƙam da mutane, haka nan ta kukkutsa har suka gama ciniki, kasancewar akwai sanayya mai karfi tsakaninsu.

“To ai sai a wuce, iya kwarkwasa”

Wata kakkaurar mata ta furta tana hararta.

Itama ta maka mata harara gami da furta.

“Dadinta karkwasar a jinin ne, wani ya gwada mana. sarakan kauyanci kawai.

“Heee!”  Ta saki shewa tana jijjiga.

“Da dai ba a san asalin balbela bane, sai ta layan ce mana”

  

      Ta mata banza kasancewar bata jin tashancin yau. Ta sunkuya da zummar daga buhun daddawarta kenan, wata kakkarfar tusa ta fita daga jikinta, sai da mai daddawa ya hantsila yana  kokarin cafke hularsa dake kokarin arcewa. Ta dago da hanzari tana kallon matan da sukai cirko-cirko suna kallonta. Da dai ta tabbata ba ita kadai taji fitar tusar ba. Asalima bayanta yarane kanana duk sun kafa mata ido.1

Kawai sai ta fashe da kuka.Garin Abuja.*

Dillaliya ce ta shigo a harigitse tana haɗa hanya, hijabin jikinta yayi cukun-cukun alamun ko an maƙureta ko ta maƙure. Ta doka sallama gami da zubewa gaban Matar Engineer tana harararta. Mrs Engineer dake harɗe tana tsotsar ice cream ta bita da kallo ido buɗe.

“Lafiya Dillaliya?”

“Ina fa lafiya kin yaudare ni ? Ai dama wasu mutanen basu san alheri ba wallahi, dan kinga yanzu ke kina inuwa kamar ba Meron dana sani ta kauyen daɓai ba, shi ne zakiyimin sanadin barin sana’ata, ai wallahi tir! Da irin halinku na dan tsako samu kaki dangi…”

“Ke Dallah dakata” Matar engineer ta katseta a tsawace.

“Ya daga tambayarki lafiya, zaki wani tsareni da surutu kamar ru6a66ar radio ? Uban me naci na hanaki ?”+

“Ae dole ki mutsutstsike idonki da borin kunya, tunda dai bukata ta biya, zaman Abuja zai gagari Meesha! Nayi nadamar saninki. Kai Allah ya isa tsakanina dake ma” Dillaliya ta furta game da sakin kuka.

Jikin matar Engineer yayi sanyi sosai, sai ta ture daurin kanta, tana kallon D Meesha a sanyaye.

“Kiyi hakuri kawata, ni fa sam bangane abinda na miki na zafi haka ba ? Miya kawo ki hadani da Allah bayan bikimin bayanin laifina ba?”

“Ke wai karki rainamin hankali mana” D meesha ta furta a zafafe.

“Dogayen rigunan da kika bani kan dubu 9, halan ba daga hannunki suka fito ba ? Kika sa naje na hana Hajiya Saddy maman kausar karɓar kayan kowa sai nawa. Sai da na kaimata kaya, muka bude gaban dumbin mutane muka tadda  dogayen rigunane na sallah da basu gaza dari bakwai ba. Kalli nan dina kigani” Ta fad’a tana nuna mata hantsar hijabinta.

“Sha’kace da Hajja Saddy tamin, na rantse sai da na hango bangon duniya. bayan rabon shakar ma hardamin ihun kiran yan sanda tunda ni macuciya ce. Matan gurin kuma suka rakani da tofin Allah tsine.”

“Kee!” Ta katseta a firgice gami da jifa da ice cream din hannunta dabai zame ko’ina ba sai fuskar Engineer da ke kokarin shigowa falon. Tayi gunsa gadan gadan kamar shiyayi mata laifin sai kuma ta fada jikinsa gami da sakin gunjin kuka. Ita babban takaicinta sunanta da ya 6aci. Ta tabbata D mesha ta fadimusu gunta ta kar6i kayan.

“Na shiga uku”  Ta furta cikin kuka

“Dear mai ya faru ne wai, daga shigowata sai kiran uku, bayan rabon ice cream dana samu ?” Ya fadi yana dan jijjiga bayanta.

“Wata ne ta yaudareni daga sarin kaya a facebook”

“Mtsss! Yaja tsaki, kice ma ke kika 6atama kanki rai, tun yaushe na hanaki wannan sana’ar ?”

“Au haka ma zaka cemin, kana gani har ta rabani da kawata meesha”

“Ni bance ba, to yanzu ma wai mi kike so a miki”  Ya fadi yana share mata hawayen.

Ranta yayi dan sanyi, sai kuma ta sadda kai kamar tana jin kunya.

“Ni kano nike so na tafi, na daure Anty jummai gun Abokinka D.P.O”

Ya zaro ida kafin ya murmusa.

“Abin har haka ya kai, kiyi hakuri zan biya abinda aka cuceki.

“Allah ni ah’ah, nidai na nemi alfarmar nan ka barni na nuna ma matar nan, ba kowa ake cuta a kwana lafiya ba. Ta fadi a shagwa6e.

“To, to naji shikenan. Shirya ki tafi, ni kuma kamin ki isa na ta6o D.P.O din sai a shigar da case din.

Ya fadi gami da cusa hannu a aljihu, ya zaro kudi masu kauri ya mikama meesha. “Gashi hajiya aci gaba da hakuri”

Ta karɓa murna fal ranta, ko banza dai in zaman Abuja ya gagareta wannan kudin sun isheta zaman Daɓai.

              Tun a zaure tayi jifa da buhun daddawar, kafin ta isa dakin Malam da gunjin kuka. “Malam banda lafiya”  Ta furta sa’adda ta zube gabansa. Ya dangwarar da ludayin furarsa daya debo da zummar sha.

“Miya sameki Jummai”

“Malam ciwon tusa ya matsamin, bayan wacce nayi gabanka, nayi wata a gaban mai daddawa. Babu wacce tafi dagamin hankali sai wacce na saki a cikin Bus gani ga Direba  har sau biyu Malam. Dan Allah muje asibiti”

Ya bita da kallo ganin yarda duk ta firgice yau d’aya. Jummai da ta tsani a mata zancen Asibiti. Amman yau itace ke kiran aje. Lalle abun mai girmane. Sai dai ya fuske yana shafa gemonsa. “Shikenan ki dau Indo ku tafi. Allah ya baki lafiya. Ni dai kam banda ko sisin da zan baki.”

Ta mike ita ba damuwarta kudin ba dama, tadai dauka zai rakatane ko kuma yana da wani abin taimakon da zai mata, amman tunda ya nuna suje can din ai shikenan.

Ta kai dakalin kofar sa kenan wata tusar ta kara fita Tuss!. Kawai ta karasa ficewa da hanzari tana sharar kwalla.

Yar yaloluwar likitar ce zaune bisa kujera me juyawa. Gefenta Dilar D ce tana ta raba idanuwa. Bayan nazari na wasu sakannai sai ta dubeta.

“Ya sunanki”

“Tundazu nace muku Jummai Malam”

“Me ke damunki to ?”

“Ciwon tu….6usss!” wata arniyar tusa ta fita ta fi kowacce karfi da razani.”

“Af ! Gama ciwonnan ya tona kansa” Ta fadi tana duban likitar da karan tusar yasa glass din idonta faduwa ƙasa ya fashe.1

“Tashi maza-maza ki fice  nan ba muda maganin sakarkaru, jeki nemi Orange ko ki jika kanwa kina sha.”  Likitan ta furta tana sharce gomin wahala.

*

“Jummai anya ba Iska bane ?” Malam ya furta bayan ya gamajin bayanin da jummai ta gama kora masa na abnda ya faru a asibiti.

Ta watsa ma Malam harara kafin kuma ta sadda kai ganin bata da ta cewa.

“Yo ai naga yanayin ciwon naki ne, wannan tusar kam tafi ta mutum. Kila garin tako daddawarkine kika tako musu tasu daddawar. Amman bari gobe zanma Ustazu jazuli magana sai yazo ya miki Rukya ko za a dace.”

“Allah ya kaimu”  Abinda ta furta kenan bayan ta gama jin ciwon zancensa.

Wanshegari Ustaz ya iso, kallo ɗaya zaka yi masa kasan cewa ba ƙaramin ruɗaɗɗe bane. Ya watsama Jummai ido, kafin ya maida kansa ɓañgaren Malam.

“Gaskiya kam Aljanu gareta yallaɓai. Ƙila ma su ɗan mitsili ne kasan su akwai fitina, amman bari muyi rukiyaar mu gani”  Ya fada yana zaro wata shafceciyar bulala daga aljihunsa. Jummai tayi baya a tsorace tana dafe kirji. Ustaz ya kalleta yana murmushi.

“karki damu ba ke zamu daka ba, su zamu buga”

Ta sauke ajiyar zuciya, kafin taji kakkarfan hannunsa bisa goshinta yana karatu.

Ya jawo Nas, ya koma falq, yaja wattaba’u ya koma Ayatul kursiyyu, duka tsit! Kake ji. Can dai Ustaz ya nisa sai ya koma Suratul Saffat. Aiko wani razanann ihu data saki, sai da ɗan Abba ya sume. Ustaz ya jawo tsumagiya gami da sakar mata guda a baya yana fadin “ka fita! shege mai taurin kai”  Jummai ta kara sakin ihu wanan karon da muryarta. “Malam ni kake duka fa” Ina ustaz bai jiba, sai da ya mata biyar masu kyau kafin ya saketa yana nunfarfashi.2

“To tunda ka gama bugunta ai sai mu zanta” Aljanin ya furta da ƙaraji.

“Miya hada ku da baiwar Allahn nan” cewar ustaz

“Goɗiyarmu ta taɓa”

“Wacece goɗiyarku? Mai kuma ta mata da zafi hakada har kuke wahalar da ita.”

“Goɗiyarmu Rufaida ‘Yar laɓe ta taɓa, abinda ta mata kuma uban wani ya sakamu mu faɗa.” Aljanin ya furta a tsiwace”

Ustaz ya danƙo goshinta gami da jawo wata aya a saffat. Aljanin ya kwala ihu kafin yace zan faɗa malam.

“To ina jinka”

“Cinikin banten mata suka yi (pant)😂 shine jumman ta cinye ma goɗiyata kudinta ta sakata a damuwa”

“To ai wannan ba abune mai girma ba.”

“Agurin kane baida girman”

“To naji ka fita”

“Bazan fita ba, kozan fita sai dai na fita ta keya, bayan na mata a jiyar kusumbi a baya”

Bingel🤔Kai musulmine kuwa?” Cewar ustaz.

“Babana ma shi ne limamin kwankwanbilo, kuma silar kyautar daddawar da ta yiwa uwata yasa ban kai ta garinmu ba tun shekaranjiya”.

“To in hakane na gama ka da girman Allah ka fita, ta amsa laifinta za kuma ta baku haƙuri.

“Malam ban fa yarda ba sai dai muyi wa’ad da kai”

“Wa’ad name sarakan ƙarya?” Cewar ustaz,

Aljanin ya yi banza bai kara tankawa ba. sai dai Ustaz kamar ance ɗaga idonka  ya hangi gadon bayan Dilar D yana  kumbura kamar an cusa balam-balam. Yaja baya a tsorace yana kallo, sai kuma ya matsa da sauri gami da cafkar goshinta ya fara jan ƙarshen Ayatulkursiyyu. Aljanin ya saki wani razanannan ƙara, kafin kuma dariya ta biyo baya.+

“Ai da ka ci gaba da cemin maƙaryacin, har kaima sai ka samu rabon ajiyar. Karka damu da gadon gonar kakata zan ma ajiyar.

Ustaz ya zaro ido kafin kuma yasha kunu.

“Nace ma Alƙawari name ? Na goge ƙaryar dana ƙara maka.

“Ko kaifa, alqawarin ba wani mai girma bane. Kawai muna buƙatar taje ta bawa goɗiyarmu Rufaida yar laɓe haƙuri, ta kuma ninka mata dan kamfen da ta damfareta.

“To ai wannan mai sauƙi ne, za taje tayin, yanzu ka fita ta baki.”

“Zan fita ai ba kai zaka nuna min hanyar da ta dace ba” Aljanin ya furta gami da sakin zazzafar hamma, daga bisani bayan Jummai ya fara sacewa, sai kuma ta bingire da barci.

Ustaz ya ɗago ya sharce zufar fuskarsa, kafin kuma ya farga da waɗanda ke tsaye a bayansa.

“Ya tafi ko ? Idan ya tafi mijinta ya kinkimeta zuwa cikin motarmu dake kofar gidansa”.

Cewar wani kakkauran ɗan sanda mai baƙin leɓe sai zuba muzurai yake.

Ustaz yayi yake bayan ya fahimci abinda ke faruwa, sai kuma ya maida kallonsa kan  Malam da ya fara sharce gumi tun lokacin da yaji ana ya kinkimi jummai ya kaita mota, yo shi ai ko a zamanin yarinta bai iya ɗaukarta balle yanzu. Ganin da ya yi Ustaz na kallonsa yasa ya yafitoshi.

“Na sani yallaɓai, amman kasan Allah banda abinda zan baka indai ba jummai ce ta farfado ba” cewar malam bayan ya gamajin ladan aikin da ustaz ke bida.

Ustaz ya murmusa kafin ya furta “Ai ba komi tunda kusa ake, Allah dai ya fito da ita lafiya ta bani hakkina.” Malam yace; Amin! Kafin ya maida kallonsa kan yan sandan dake binsa da muzurai.

“To ai saiku turo yaranku mata su dagata ku tafi, ni kam babu ni a wannan wahalar tunda bani na tura Jummai nemo magana ba”

“Amman ai kaima kaci rabonka ko ?” Cewar wani figaggen ɗan sanda mai zubin dolaye.

“Ah’ah Sajen Tanko! Ogaa bai ce mana mu tsaya maida martani ba, Mu dagata kawai. Maimuna DG!”

Kan ya haɗa muryasa. Mulmulalliyar matar ta bayyana gabansa  tana ta muzarai hannunta dauke da gora. Tayi saurin saramasa kafin ta kame.

“Ki dagota mu wuce”

Ta watsama jummai dake sharar barci harara kafin kuma ta karasa gurin ta.

“Kin tabbata itace wannan ko ?” D.P.O ya fad’i yana kallon Matar Engineer.

“Eh itace Yallaɓai. Bara ma na tasheta” Ta fada gami da tsiyaya mata sassanyen ruwan robar dake hannunta.

“To yanzu abinda nike so dake, kije dandanlin naku na facebook can inda matar ke harkokinta, kiyi shelar cewa lalle gobe ana bukatar duk wanda yasan wanan matar taci kudinsa to ya hallara a farfajiyar gurinnan, domin abi masa hakkinsa, akuma tauna tsakuwa dan aya taji tsoro. D.P.O ya fadi gami da murza gashin bakinsa.

Matar Engineer ta sakarmasa murmushi mai aji kafin ta tashi ta fice daga gurin. Bayan ta watsamasa kalmar godiya.

Matar Engineer tunda tayi shelar an kama Anty jummai, ana kuma bukatar kowa yaje can inda aka kaita, bayan ta aje adireshi da komi na gurin. Yan gulma da gutsiri tsoma, hardasu tambaya, su fadi ba a tambayeka ba, suka sha alwashin sai sunje. Ciki harda wadanda jummai bata taɓa cin karo dako sunansu ba, balle sisinsu.

Wanshegari tun 12:00pm aka fara dururwar zuwa police station. kan a farga mata sama da ashirin sun hallara, kowacce kuma taci ado na kece raini, sai watsama bakaken yan sanda kallon hadarin kaji suke.

D.P.O ya shigo bayan ya harde kan Kujerarsa, ya umarci da ajere matannan kan layi, kowacce tazo ta fadi iya abinda Jummai ta cinye mata. A kuma ji tsoron Allah a fadi gaakiya, lalle idan wani mahaluki baya ganinka to mahaliccinka yasan har gaban abinda ka ɓoye a qalbinka. Dan haka Aji Tsoron ALLAH! Jikin mata da yawa yayi sanyi, nan da nan yan gulma suka ware kansu kusan su 15, akabar mutane 15 dake da hakikanin shaidarsu.

D.P.O ya kai kallonsa ga wacce ke layin gaba.

Gatanan dai doguwa samɓal, sai dai ta yi kalar matsorata. Ya watsa mata tambaya “Baiwar Allah fadi sunanki da abinda ya hadaki da Jummai?”

Ta sadda kai tana juya azurfar hannunta kafin ta fara.

“Malam Sunana Shatutu yareema. Abinda ya hadani kuwa da ita, kayan mata na siya gurinta bayan ta bani tabbacin masu kyau ne har na dubu 5, sai da nazo amfani dasu bayan na gama saidama mutane, na tadda ashe dakakken kashin awakine.” Ta fada gami da share kwalla. Akwai alamun har yanxu abin na mata zafi.

Mutanen gurin suka dauki salallami, wata yar tsagal dake amsa sunan Mrs Jiddah tayi saurin shan gabanta tana rike haɓa “Kuma yanzu sauran mutanen da kika saidama sun cusa a gurin ko ?”

Shatutu ta sadda kai gami da furta “Har taruwa sukai sukai min dukan tsiya Jiddah”

D.P.O yayi saurin daka tsawa gami da fadin ayi shiru kafin ya maida kallonsa gata biyu. Ke fa ?

Matar mai zubin yan Nijar ta dago tana goge ido, da alama kiris take jira ta fashe.

“Sunana Husnah ‘Yarbaiwa, abinda ya hadani da ita kuwa shi ne; Atamfa ta nunamin mai zubin babbar atamfa wata Java kan dubu 10, ashe Karamr atamfa ce ta dubu 2500, yallaɓai in takaice maka na sari atamfar nan har dozin 3, akarshe dai bayan na rabama mutane nima cikin rashin sani. ‘yan daban unguwarmu sukayimin asarar hakorana guda biyu, kaganni na zama wawulo” Ta furta tana budemasa bakinta, kafin kuma ta rushe da kuka.

Haka dai ya dinga binsu har akazo kansu Batool aka koma kansu Asal, aka maimaita na matar injiniya. Kafin kowa yayi shiru yana sauraran hukuncin d.p.o.

Ya bude baki da zummar magana kenan wasu mutum biyu suka fado suna haki.

“Yallaɓai wannan tsinanniyar tafi cutarmu kan kowa” Babbar mai zubin masifaffu ta furta.

“D.P.O ya dubesu kafin yace muna jinku.

Gudar mai zubin miskinai ta numfasa kafin ta fara.

“Wannan kawatace sunanta Hibbah tare muke kasuwancinmu, ni kuma sunana Kyautah, Mun hadu da Jummai a facebook. Bayan tayi postin na wasu Teddy’s masu kalar macijai da damisa. Mukai ciniki kan dubu 100 guda 20, yalla6ai in takaicemaka dai da aka kawo mana Teddy’s,  maimakon muga macijai da damisa, sai muka ga yar babyn kashi, wannan dai ‘kashin na SA da kakaninmu ke yin Yar tsana dasu a masu lalle. Ta jera mana su a kwali gami da yimusu kwalliyar atamfa.” D.P.O yayi saurin sunkwi da kai da kokarin shanye dariyarsa.

Kafin yaji muryar HIBBAH kuma ta ratsa su, harda bugun kirji.

“Ai kawai ni ka bani shegiya in yi mata Askin kwalba” Ta furta tana fiddo wata mikakkiyar kwalba daga jakarta.

Jummai  dake la6e cikin cell ta kurma Ihu, bayan da taji zancen Hibbah.

“Yalla6ai wallahi Allah shaidana bani kadai bace ke harkar nan harda kawata Salma kuma ita ta fara nunamin hanyar. ASALIMA duk wani kudi nawa sama da dubu dari 5 yana gurinta na bata ajiya”

D.P.O ya daka mata tsawa kan yace “Bamu adireshin Salman aje akawota.

Nan da nan ta rattabamasa.

Ya shigo gami da kamewa kallonsa nakan D.P.O

“Oga munje gidan fa”

“Ina jinka Sajen Tanko ya a kai tana ina ?”

“Oga ai ina ganin sata ta saci sata fa”

D.P.O ya dago gami da kafa masa ido.

“Gidan a kulle muka taddashi da kwado, akwai tabbacin wai safiyar yau ta daga kasar China.”1

BINGEL😏Abinka da haihuwar fari har hajiya ta fara sakin ihu tana kiran wata kishiyar kakarta Ngozi. Cikin Hanzari matar engineer ta matso gurinta ita da  Asal suka ciccibi Amat zuwa cikin mota, mata sun d’uru kowa na fadin Albarkacin bakinsa. Su Batool ke fadin “Salati zaki yi Hajiya. Ngozin koda tana gurinnan babu abinda zata iya miki sai ido.”

       Bayan an natsa su Asal sun dawo daga asibiti. Hankalin D.P.O ya dawo kan taron matan dake gabansa, a hankali kuma yakai kallonsa ga Sajen Tanko da ya gama rubutu komi, Ya dan dubi gefensa inda Sifeto Isyaku ke zaune. Kamar ya bashi umarni yayi saurin mikewa gami da wucewa gurin Jummai, kai tsaye ya fiddota daga cell gami da dangwararta gaban D.P.O tukunna shima ya zauna da nufin fara aikinsa. Ya kalleta yana murza gashin bakinsa, kafin kuma ya watso mata tambayar.

“Zaki biyasu dukkan abinda kika karɓe musu, ko kawai a wuce kotu dake ?” “A’a yallaɓai zan biya sun dai, bana son batun kotun nan” Ta fad’i da kyar da alamun wahala. “To a yanzu muke bukata ki biye, ke duk da haka ma akwai bukatar ke leka gidan kaso ko na wata 2 ne”  Ta fashe da kuka kafin ta kara dukar da kai. “Amin Afuwa yallaɓai wlh na tuba. Na kara da Alkawarin har abada ma bazan sake yin fesbuk ba, dama duk Hajja salma ta dora ni a hanya. Ni har na baro kauyenmu ban masan akwai wata duniya a cikin wayar hannu ba.” 

Yakai kallonsa ga matar Engineer tayi saurin kifta masa ido.

  “To yanzu fadimana inda kika aje kudin jama’ah aje a kwaso. Idan ya fice awa daya zakijiki a kotu daga ke har mijinki.  “Yalla6ai na rantse ma da Allah dukkan dukiyata suna gurin Hajja Salma. Sai buhun daddawata guda daya shi ya ragemin a zaure.  ‘Kushhhh! Wani zazzafamna rankwashi ya ziyarci kanta, tayi saurin dagowa tana kallon zainabu bararo sai huci take.  “Haba yalla6ai a bamu ita mu kwata da karfinmu, kun tsaya sai lalla6ata kukeyi” “Eh! wlh zainabu abamu ita  a  hannunmu” cewar sauran matan.  D.P.O ya daka musu tsawa gami da zarema zainabu ido.  “Ke bama bukatar kauyanci anan duk ba sokancinku yaja muku ba” Zenabu tayi shiru tana kunkuni.  Sifeto yaci gaba da aikinsa.  “Yanzu sanin inda Hajja Salma take ai yana gurinki Hajiya ɓera. Sai ki fadimana inda take muje mu samota kafin cikar awa guda.”  Tayi shiru kirjinta na bugawa da alamun tashin hankali ya tsananta gareta. Wani zafi take ji a zuciyarta, bata taɓa zaton Hajja Salma zata yaudareta ba. Zuciyarta ta bushe idanuwanta sun kafe babu ko digon hawaye. Sai tururin nadama dake bibiyarta. Akwai alamun ɓoyeyyen duhun ramuwa a zuciyarta. Ta dago ido cikin ido tana kallon sifeto.  “Hajja Salma ba tada gurin zuwa banda china. Wannan shi kadaine sirrin da na sani game da ita. Dan haka na yarda akaini kotun a kuma yankemin dukkan hukuncin da ya rataya akaina. Dan bani da wani abu a duniya da zan iya biyamusu dukkan abinda muka samu daga garesu ni da ‘kawata. Sai dai ina neman Alfarmar da a kyale mijina sabida shi bashida hakki ko guda cikin zancennan. Asalima banda Asuwakin Naira 20 bai ta6acin ko sisi ba cikin abinda nake samu. “

      D.P.O ya bita da kallo ido bude. Sa’ilin da can cikin zuciyarshi wani tausayi ke kokarin lullu6eshi lalle akwai alamun rashin wayo a tare da Matar nan.  A hankali ya furta “Shikenan Allah ya kaimu kotun”. 

‘Karshe!    

+

🐀🐀🐀🐀🐀🐀🐀🐀🐀🐀🐀

*SANWARWA/SHAWARA/GARGADI.*

Wannan labarin ba ayishi dan cin zarafin wata ko wani ba. Asalima an yishine ta sigar nishadi da kuma tauna tsakuwa dan aya taji tsoro. Masu online business daku nake bawai kuma ance dukanku halin 6ERAYE gareku ba. Ah’ah ana nufin acikinku akwai 6ata gari. Wadan suke 6atamuku kasuwanci da cin amana da kuma cin hakkin bayin Allah. Wanda asalima cin riba anyi hani dashi. Balle akai ga kar6ar kudin mutane babu biya sai ma kwamashon blocking da mutum zai samu.  AJI TSORON ALLAH. Wallahi idan babu kamun Mutum ko kamun ALJANI kayi ciniki da aljana baka sani ba, sai ka cimyemata kudi danginka kaf su shiga uku. To wallahi akwai kamun Allah. Kamun da wataran zaka tashi ka dau Naira 20 da nufin siyo Ashana, kiga Naira 20 ta koma kullin Sabara ko wannan koren maganin da ake sawa a koko yama sunanshi ?🤔.ko kuma wata masifar daban (Allah ya kiyashemu.)Bakasan dawa kake tare ba, bakasan kuma irin bakinshi ba. Haka baku tsoron cin hakki. Bakasani ba ko marayane. Kuyi ciniki kabi ka lamushe masa kudi. Shi kuma ya bika da addu a. Haba jama’a!  Wallah daga gareni ko kallon banza mutum yafiye yimin tsorata nake yi. Balle kuma akai ga Allah ya isa! Ta6di!   Adaiji tsoron Allah. Anayi ana tuna rayuwar nan fa mai karewace. Haka dukkan abinda ka shuka shi zaka girba a inda babu Ummu wala abbu wala akh wala Ukhty.  Fatana Allah yasa masu Halinnnan zasu daina. Zasuna yin hakuri da abimda Allah ya horemu su.  Na gaisheku kawayena da yan uwana da duk wanda ke sona. 

Bingel🤔  Slow Typing.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *