BARIKI NA FITO CHAPTER 22

BARIKI NA FITO 
CHAPTER 22
Kuka tayi Sosai lallai Yarima shine mai Sonta na gaskiya, duk namijin da zai maka hidima 
Ba tare daya nemeka ba, shine masoyinka, mazan yanzu basa abu dan Altah sai dai in Sun miki Suma suna so kiyi musu, mata Kwadayi maza kuma shegen sha’awa, daka ya baku abu kin amsa in baice miki wani abuba toh gobe zaice dan ba’a banza yayi miki ba, wannan shi ake kira trade by barter, wani irin son Yarima yake kara shigarta, ido ta lumshe mai yasa na kasa fad’a ma Yarima gaskiya? Saboda ina tsoran in rasa Shl, saboda ina sonshl…“ D‘aukan wayanta tayi da saun‘ ta kira Layin Yarima amma still switch off, d‘an shuru tayi tana tunani kallon lokacin data kirashi tayi dazu taga wajan 39min, tace ya isa ace yakai gida yanzu don daga kaduna zuwa Zaria 30min ne, kara kira tayi amma a kashe tayi mugun shiga damuwa, mai yasa Yarima ya kashe waya Bayan yasan zata kira, sannan yasan sa’kon daya tura mata dole hankalinta zai tashi, gashi na kira yaki d’auka daga karshe ya kashe waya ….. A hankali ta furta Yarima plz ka kunna waya ina cikin damuwa…. 
Yarima Aliyu Bayan sun karasa direct masallaci yayi cikin sauri dan yin sanah isha’i, duk da sanda suka isa an idar da sallah din, direct gefenshi yayi toilet ya fad’a yayi wanka sannan ya flto yasa jallabiya, falo ya fita Inda yaga an jera Mai abinci zama yayi kuyangi suka zo suka suba Mai sannan suka barwajan, Fara ci yayi yana cikin cin abinci saiga usman d’an waziri ya shigo 
Usman zama yayi kusa da Yarima yana fad’in Wai kwana biyu Ina kake zuwa ne haka? Yarima baiko Kalli usman ba balle yasa ran samun amsa. 
Usman bai damu da hakan da Yarima yayi mishi ba dan dama yasan hali, inda Sabo ya saba, ganin Yarima bazai yi magana ba yasa yaci gaba da fadin Yarima ya kamata ka rage fita kasan Idan gimbiya tazojibi maganan Fita ya qare sai kuma Bayan aure…. 
Yarima ajiye spoon din dake hannunshi yayi tare da fad’in akan wani dalili? Usman yace domin haka shine al’adan masarautar 
Yarima yace thank god al’ada ce ba addini ba, da za’a rufe mutum a hanashi me like a prison person 
Usman murmushi yayi tare da fad’in Yarima kasan wannan masarautar bata wasa da al’ada domin an dauketa da muhimmanci, kuma ina mai baka shawara daka bi wannan al’adan Indai bason ganin fushin Mai martaba kake ba 
Yarima Aliyu tashi yayi ‘tare da fad’in nifa ban son takura a Bari inji da wannan auran da ake 
kokarin cusa min mana haba kodan Anga nayi shuru 
Usman yace shurun shine Alheri Yarima, kuma ina mai baka shawara daka girmama zabin da iyayenka suka maka, Indai kana son ganin farin cikin su, kuma kana son Kaga dakyau 
Yarima Aliyu yace naji zaka iya taf’lya 
Usman yace Allah ya huci zuciyarYarima, dama nazo ne akan kazo muje Kaga gefen ka, domin ance tunda aka fara aikin bakaje ‘ba, ya kamata kazo muje ka gani in yayi maka 
Yarima Aliyu yace basai Naje ba, komai akayi yayi dai dai Usman yace Yarima Mai martaba da kanshi yayi min magana akan muje in kaika ka gani Jin umarnin mai martaba ne yasa Yarima fad‘in muje 
Fita sukayi har zuwa gefen da akama yarima dan gajeren ginin gidan sama, tsarin ginin ya had’u falo suka fara shiga wanda yana da ginna sosai, suka gani a falon suka bude bedroom ne guda biyu a k’asa da kuma kitchen da dinning area, sai sama kuma d’aki uku ne da falo d’aya, ko wani d‘aki yana da girma Sosai gidan dai yayi kyau Sosai 
Usman yace ya Kaga gidan ina fatan yayi maka kyau Yarima yace babu laifi 
Usman yace gobe za’a zu ba kaya domin da mai martaba yasa Asa sarkin katsina yace abarshi domin shi zai saka komai, duk da Mai martaba ya nuna a barshi amma sarkin katsina yace yariga yasai komai, d’azu masu deco suka zo suka duba komai gobe zasu zosu saka kayan 
Yarima bai ce komai ba sai waje da yayi… 
Ganin haka usman ya bishi yana fad’in yarima gaba d’aya kayan da zaka saka an kammala su, ranan da gimbiya zata zo nan akwai kayan da zaka sa…. 
Tsayawa yarima yayi tare da kallon usman yace akan wani dalili? Kayan da zansa ma sai an zaba min? Ni Mai yasa za‘a kawo ta jibi, a Bari sai an d’aura auren mana 
Usman yace Indai zaka auri yar gidan sarauta toh dole haka za’ayi wacce ba y’ar gidan sarauta bace za’a kawo ta Bayan an d’aura aure 
Yarima yace I don’t know why kuke d’aukan al’ada kaman addini 
Usman yace haba Yarima ai dad‘i ya kamata kaji, gimbiya cefah za’a kawo maka yarima bai kulashi ba yayi gaba abunsa 
Usman dariya yayi dan yasan Yarima baya son auren kawai dauriya yake 
yarima na shiga d‘akinshi wayanshi ya kunna, yana kunna wayan sa‘ko ne sukai ta shigowa bud’ewa yayi yaga na mutane ne Kala Kala sai kuma na princess dinshi, nata ya shiga ya 
fara karantawa ….. 
Yarima kasan hankali na a tasheyake’Ka d‘aga min hankali shine ka kashe waya dan Allah Yarima ka kunna waya bazan iya bacci ba yau har sai …… Bai karasa karanta message din ba kiranta ya shigo Murmushi yayi tare da kashewa sannan ya kira tam. 
Tana ji ya d’auka ta fashe mishi da kuka 
Yarima hankalinshi yayi mugun tashi dan jin Zainab dinshi na kuka Yace my princess what happen? Plz stop it. 
Batai magana ba sannan bata daina kukan ba 
[do ya lumshe dan baya son kukanta k0 kad’an, yace tunda ba zaki shuru ba gani nan zuwa 
yanzu 
Da sau ri tace ni karka zo, kasan zan damu shine ka kashe waya kasan tun yaushe nake cikin
damuwa dan Allah Yarima karka kararmini irin haka bazan iyajura ba Ina Sanka Yarima ban son wani abu ya sameka n…. Shuru tayi cikin jin nauyin abunda ta fad’a gashi ance magana zaran bunu 
Yarima kam jin kalmanta na karshe yasa shi jin wani irin dad’in da bai taba jiba, ina Sonka 
Yarima, ban son wani abu ya sameka, murmushi yayi tare da fadin ina jinki…. 
Kit ta kashe wayan domin wani irin kunya taji, tana kashe wayan ta Fara dukan kanta kai na kwafsa… Shuru kuma tayi tana mamaki yau itace takejin kunya dan tace Tana son wani ikon Allah ita da take tubewa tsirara gaban namiji duk bataji kunya ba sai dan tace Tana son Yarima. Kai gaskiya Yarima kai daban kake Sonka ajini na yake. 
Yarima kam jin ta kashe wayan yasa ya saki wani irin murmushi mai cike da farin ciki kaza kiranta yayi…. 
Ido ta bud’e dake lumshe tare da d‘auka bata ce mishi komai ba Yarima yace kara fadamin abunda kika ce d’azu 
Tace Mai nace ni na manta 
Yace oh I see, bari in tuna miki… 
Da sauri tace Yarima saida safe bacci nakeji 
Murmushi yayi dan yasan so take ta zille bata son ya tuna mata… Jin ana mishi nocking yasa yace ok baby good night dream about me, nd tell me tomorrow yana fad’in haka ya kashe wayan tare da tashi dan yaga Waye ke mishi nocking 
Bariki bayan ya kashe wayan, murmushi tayi tare da fad‘in ina Sonka Yarima gaba d’aya kasa na canza daka abunda na fito ina fatan kaima zaka amshi kaddara Kar kaki amsa kaman yanda akaki amsanta a baya hawaye ne ya zubo mata ….. Ganin tunanin da bata son yi yana son tayi shi yasata tashi tayi waje dan bata son tunawa da baya ko kad‘an 
Yarima bayan ya bud’e kofa sisters dinshi ya gani su duka, wani irin murmusm ya saki cikin jin dad’i tare da fad‘in saukan yaushe? 
Hafsat tace bros tun daxu suka zo, suna ta jiranka baka dawo ba Salamatu tace wai ina kaje ne
Yace Kai sis wannan tambayar ai sai ku Bari a gaisa dariya duka suka Saki tare da shiga falo din suka zauna 
Yarima kallon y’an uwanshi yake yana jin dad‘i, yau gasu su duka sun had‘u, rukkaya, salamatu, Fatima, and lil Hafsat dinshi, yarima yace shine kuka zoda wuri haka? 
Fatima tace bikin fah saura kwana biyarAini da naso inzo tun yana sati biyu Dariya Yarima yayi Sosai kaman ba shiba, yace sai kace Kece maman ango ba 
Tace ai yayar ango kaman uwa ce 
Yarima murmushi yayi
Zama sukayi suna ta flra cikin so da kauna tare da tsara irin abubuwan da za ayi duk da 
dama sun shirya komai, 
Shidai Yarimajinsu kawai yake dan baya son ana maganar bikin kwata kwata nan“ 
Katsina 
Gefen amarya wato gimbiya zinatu Anata shirye shirya Sasai musamman ma ita amaryan inda take ta gyaranjiki 
Gimbiya Zinatu ce a d’aki daka ita sai wata kawarta kallo d’aya zaka ma kawar ka gane duk suna da sarauta domin yana yin shigarta da kuma yanda ‘akeyi alaman akwai giyan sarauta akanta, y’ar sarkin bauchi ce yarinyar gimbiya Amina 
Kallonta gimbiya zinatu tayi tace my love kina ganin duk abunda na tsara zai bada matsala kuwa? 
Gimbiya Amina tace bana tunani amma ldan kika wuce gonarki zai iya bada matsala dan haka kiyi taka tsan tsan 
Murmushi gimbiya zinatu tayi tace karki damu, baza’a samu matsala ba, tare da d’aga ma gimbiya Amina gira 
Gimbiya Amina wacce take magana kaman bata son yi tace ina fatan haka, dan ldan aka sami matsala daka Wajanki toh karki ce ban fad’a miki ba 
Murmushi gimbiya zinatu tayi tace, haba haba ai ko d’aya na iya taku na 
Gimbiya Amina tace da sauranki dai domin naga kina ta rawan kai nidai ki kiyaye tana fad’in haka ta tashi tayi toilet dan tayi wanka Ganin ta shiga toilet yasa gimbiya zinatu fad‘in my love ko rigima ….. Toh fah wannan wani 
abu ne ake cewa gimbiya tayi taka tsan tsan akai???? 
“nan.“ Gaba d’aya masarautar Zazzau ta kidime wajan hidiman bikin tilon d‘anta guda d‘aya wato 
yarima Aliyu d’a d‘aya namiji a wannan masarautar mai albarka 
Yau za’a kawo gimbiya zinatu cikin wannan masarautar ita da y’an uwanta harsai Bayan an d’aura aure zasu wuce abaramarya a nan, an ware musu gefe guda . 
Yarima ne zaune akan gadon d’akinshi yana ta faman yin tsaki ga kayan da zaisa an ware Mai, gashi yana ta kiran gimbiyarshi Zainab wato bariki taki d‘auka message ya Mata tare da fad’in 
Pick my call Reply ta mishi da fad’in Sorry I can’t pick your “ now har sai bayan bikin ka karmu shiga hakkin amarya 
Yana karanta message din ya buga hannunshi biyu domin yana bala’in son jin muryanta, gashi daka yau babu inda zashi har sai an d’aura aure, nishi yayi tare da fad’in Indai bazaki d’auki wayana ba dole ln Karya wannan al’adan inje in ganki tunda ba addini bane…. 
Shuru kuma yayi ance gimbiya nan da 30min zasu karaso kuma shi zai tarbeta… Dan shuru 
yayi yana nazari d’aukan key din mota yayi daka gani shi kadai zai fita yace I have to see my princess 
Hmm

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *