*BARRISTER ASAAD*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
Gaisuwa na musamman zuwa Ga ‘yan group d’ina da kuma
*Fati Azland*
*Aneesa Rimi*
*Aneesa Anush*
*Baby Haneepha*
*Memxy BBC*
*Ummi Aisha*
*Anty Baraka*
*Zarah Bukar*
*Autar Hajiya*
*Mamy Aydah*
*Maryam Kaumi*
*Rookie Sadau*
*Nafee Anka*
Jambandu na
*Anty Bilkisu Zubair*
*Anty Nana Khazlim*
*Anty Halima Zubair*
*MAMEEY AYDAH*
1⃣▶5⃣
Alhaji Muhammad Ali babban Dr ne mutum ne d’an boko sosai asalinsa buzu ne amma ‘a Nigeria ya tashi Allah ya basa ilimi sosai bayan kasancewar sa Dr kuma Professor ne yanzu haka yana da asibitin kansa, matar sa d’aya ‘ya’yanta uku Ibrahim da Nabila sai kuma auta Sadiya amma suna kiranta Jalila kasancewar sunan mahaifiyarta ne da ita, Ibrahim da Sadiya sunyi karatu mai zurfin gaske gashi Allah ya basu baiwar k’wak’walwa kullum su suke d’aukan over roll students, Ibrahim yanzu haka ya kammala PHD d’insa yayi aure ‘a chan Uk kasancewar ‘a chan yayi karatunsa koda ya kammala karatunsa da first class upper ya fita shine best student of the year wannan dalilin ne yasa suka d’aukesa aiki!
Nabila kuma sai da ta kammala master’s nata tayi aure lokacin tana 20years tayi aure ita ma Allah ya bata k’wak’walwa ita ma tana lecturing ‘a ABU dan ‘a Zaria tayi aure…ita ne the most youngest Lecturer ‘a ABU English ‘a bakinta kaman me dan Slang take yi……tun tana k’arama mahaifinta da mahaifiyarta basu yi wa ‘ya’yansu Hausa sai dai English wannan dalilin ne yasa in suna speaking kaman ‘ya’yan turawa, shima mijin nata mugun d’an boko ne shine Chancellor na school d’in
Jalila ‘yar auta kam ba’a magana dan ita Allah bai had’a jininta da karatu ba kullum na 6 ko 7 take zuwa yayunta kam basu tab’a wuce first position ba, Jalila bata ji ko kad’an kullum sai an kawo k’ararta gida…Jalila sam bata ji gashi bata da mutunci ko kad’an ga rashin ji, ga rashin kunya, surutu, fitsara, fitina duk ita d’aya dan indai tana wuri sai ansan tana wuri, gashi tana da son hayaniya in tana abu wane ‘yar daba!
Duk friend’s nata maza ne shiyasa ita ma behaviour nata na maza ne
Duk zafin iyayenta sun rasa ya zasu yi da ita…dan mahaifinta yana da zafi sosai amma tunda Allah ya basa Jalila yayi sanyi gashi Allah ya d’ora masu sonta ta kad’an ba, amma basu nuna mata irin sosai d’innan saboda irin halin yaran zamani…..tana k’aunar iyayenta sosai ba kad’an ba wannan dalilin nema yasa take gudun b’acin ransu dan in ransu ya b’aci hankalinta mugun tashi yake yi koda ba ita ta b’ata masu rai ba in taga ransu ya b’aci sai ta zauna tayi ta yin kuka
yanzu she’s 16years this year zata gama secondary school, amma sai ka ranste she’s 14 dan wautanta is worst
Zaune take hannunta rik’e da littafi amma ba karatu take yi ba hankalinta na kan Tv sai taji motsi tayi pretending as if she’s reading dan ace tana karatun exams,
Mami ne ta shigo palon tare da Daddy
“Baby girl karatu ake yi?”
Fake smile tayi tana jin dad’i tace
“Yes Dad”
Girgiza kai Mami tayi tace
“Am certain she’s not reading, she’s just ptetending”
Tuni ta fara hawaye
“Mami am reading fa”
Murmushi tayi tace
“Yawwa good girl reaction naki ya nuna kina karatu da gaske good girl”
Dafa kanta Daddy yayi yace
“I promise in kika yi k’ok’ari in your Exams i’ll buy you latest iPhone da makeup kit”
Tsalle tayi ta fara yi masa godiya
Tun daga ranar Jalila ta zama serious kullum ka ganta karatu takeyi tsakaninta da Allah dama already wayanta ya lalace babu chating, kallo ma bari tayi…dan school d’insu ba’a bayar da Exco na Waec and Neco
‘A haka har suka gama Exams Jalila ta dan nustu tana karatu koda Result ya fito Jalila tayi k’ok’ari sosai daga A sai B..A sunma fi yawa dan ita ma tana da k’ok’ari kawai karatun ne bata so…the next day Daddy ya cika mata alk’awari ya saya mata Makeup kit had’e da X d’inta ranar kasa bacci tayi dan farin ciki
Tun daga lokacin labari ya chanja Jalila ta chanja friends sai masu x ne friends nata, rashin ji ko k’aruwa yayi Daddy ya kai ta training na computer kafin ‘a fara bayar da admission, Jalila kam da driver ya ijiye ta take k’arawa gaba yawo dan wannan new friends d’in nata fitinannu ne, gasu da shegen yawo kullum suna kan titi posting kam ba’a magana dan IG and Snap sun san da zaman Jalila, Modelling ma ta fara duk wasu photographers sun san da zaman ta…makeup artist duka dai hotunan ta sun gama zaga duniya
Rashin ji kam ya k’aru da kula samari dan duk wani matashin saurayi yasan da zamanta, samarinta basu irguwa….duk abinnan da take yi Daddy da Mami suna sane kawai sunyi mata shiru ne…may be they are up to something!
Zaune take ‘a kitchen ta mik’e k’afa tana yanka Alayyahu duk ta b’ata wurin wane wata mara hankali Mami ne ta shigo tsoki tayi had’e da galla mata harara tace
“Wai Jalila yaushe zaki yi hankali? Yanzu yanka alayyahun shine kika b’ata duka kitchen d’in?”
K’asa tayi da kanta tana murmushi, tsoki tayi tace
“Aurar dake zanyi na huta na wannan iskancin naki”
Turo baki tayi tace
“Ni aure ‘yar k’arama dani Allah ya kiyaye…Anty Nabila ai sai da tayi karatu aka mata aure”
Rankwashinta Mami tayi tace
“To fitsararriya ai sai ki zage ni”
“Kwarai da gaske aurar dake zamuyi ai kin sa ja’ira kawai” Taji muryar Baabaa mai aikin su tana shigowa
Murgud’a baki tayi tace
“Ai sai ki aurar d’in”
Rankwashinta Mami tayi tace
“Ohhh fitsararriya da Baabaa zaki yi?”
Murmushi Baabaa tayi dan sun saba yi da Jalila kullum sai sunyi fad’a kuma still suna shiri dan bakin Jalila bai yin shiru da sunyi fad’a zata cigaba da bama Baabaa labari in tayi banza da ita ko tana amsa mata Emm…sai ta bata hak’uri dan ta iya bayar da hak’uri ba kad’an ba
should i continue?…..
: *BARRISTER ASAAD*
Dedicated to
*Meena Parrot*
Thanks for the love and care
*Memxy BBC*
*Na gaisheku kyauta*
Maman Zainaba
Aisha Gentle
Mom Amir
Mmn Ahmad
Mai Madubi
Amatullah Bea
🔟▶1⃣1⃣
1Month aka saka bikin amma Asad ya buk’aci ‘a k’ara masa lokaci zuwa nan da 3months dan yana da buk’atar miles da yawa…dama duk abinda aka saka wa lokaci toh lokacin zai zo
Biki ya kusa saura 1Month amarya ta sha gyara sai wani glowing take yi irin na ‘yan Somalia!
Sai da ta rame duk tayi k’ashin wuya…gashi wani banzan hali data koya na rashin kula mutane da rashin shiga mutane dan yanzu ko wane lokaci ita d’aya zaka ganta daga d’aki sai d’aki koda aka kawo lefe kota kansu bata bi ba Mami tayi juyin duniya Jalila ta kalla lefe amma ina kullum cikin kuka take…
Zaune take ‘a bayan kitchen tana shan iska Khadija ta kirata
“Jalila na shigo ban ganki ba”
“Ina bayan kitchen” ta katse wayan
Ba’a fi 3mins ba sai ga Khadija kujera taja ta zauna
“Jalila mai ya same ki haka? Kin rame!”
Hawaye Jalila ta soma
“Khadija ina kika shiga haka? Ko ‘a waya ba’a samun ki?”
“Amma k’awana hope all is well?” ta soma goge mata hawayen “Ina Egypt school”
“Kinji dad’i”
“Hmmm ba wani dad’i jiya na dawo, wane school kike?”
Tsoki tayi dimple nata ya loma ta cigaba da hawaye tace
“Daddy ya tsane ni ban san laifin da nayi masa ba ya hanani zuwa university kuma auren dole za’ayi man, Kinsan Asaad ko d’an Uncle Hashim wlhy Asaad bai da mutunci ko kad’an idan kinga wulak’ancin da yake yi man sai kin yi mamaki”
Salati Khadija tayi tace
“K’awana yanzu mai solution?”
“Da na yanke shawarar ana gobe d’aurin auren na gudu”
“No kar ki gudu ran iyayenki zai b’aci d’an nasan ba k’aramin abu zai sa ya hanaki tafiya school ba d’an nasan Daddy yana son boko fiye da tunanin kowa, nasan ba k’aramin laifi kika yiwa Daddy ba, may be yasan yawo da rashin ji da kike yi shiyasa ya yanke wannan hukuncin kuma nasan duk yaransa babu wadda yake so kaman ki, kin san kawai ki kira Hajiya kaka ki fad’a mata nasan Daddy dole yaji maganar mahaifiyarsa”
“Toh shikenan zan kirata zuwa anjima”
“No ki kirata yanzu”
“Mu shiga ciki”
Tashi suka yi suka shiga ciki kiran Hajiya tayi ta soma yin kuka sai da tayi mai isan ta kana ta fad’awa Hajiya Daddy ya hanata karatu kuma yace auren dole zai yi mata
Tuni Hajiya ta kira Daddy tayi masa fad’a wurin da take shiga bata nan take fita ba, Khadija kam bata jima ba ta tafi ta bar Jalila ‘a,tarko!
Da misalin k’arfe takwas Daddy ya shigo gidan rai ‘a b’ace yasa ‘a kira masa Jalila jiki na b’ari ta saka hijab har k’asa kamar ta k’warai ta fita ‘a k’ofar palon sa ta tsaya gabanta na dukan uku-uku ta kasa shiga!
Daddy yana tsaye ya mayar da hannunsa baya fuskar sa babu annuri k’ofar ya gallawa harara though ‘a rufe k’ofan yake ta window ya hango ta
“Zaki shigo ko sai na fito?”
‘Yan hanjin cikinta ne suka kad’a ‘a hankula take taka k’asa har ta shigo tsakiyar palon!
Wanketa da mari yayi lafiyayyu gud’a uku k’asa ta zube tana kuka nunata yayi da yatsa yace
“Har kin isa ki tozarta ni? Hankalinki ya kwanta ba kin had’a ni da Hajiya ko? Yayi kyau aure an fasa school kuma zaki tafi sai dai ki sani ko sisi na bare yi kuka ba, tashi ki bani wuri”
Zatayi magana ya d’aga mata hannu ya nuna mata k’ofa ran Ya Ibrahim kam ya gaba b’aci d’akinta ya bita tana tsaye jikin bango tana kuka hijabin da yake jikinta ya ja dad’a volume d’in kukan tayi rai ‘a b’ace yace
“Gobe kije ki bama Daddy hak’uri ki ce masa kin fasa tafiya school kuma zaki aura Asaad in ba haka ba na ranste da Allah na lahira sai yafi ki jin dad’i wlhy na ranste baran yi kaffara ba”
Jawota yayi ya turata k’asa k’anta ya bugu kuka sosai tayi…’a fusace ya fita ita kam kuka tayi har ta gode Allah bacci mai nauyi ya d’auke ta ga ciwon kai mai zafi had’e da zazzab’i…da k’yar ta tashi ta sha magani sai ta tuna da bata b’atawa iyayenta rai ba su zasu saka ta ‘a gaba sai ta sha magani!
Koda gari ya waye sa 11 ta tashi da ciwon kai da k’yar ta tashi tayi wanka ko mai bata shafa ba kaya kawai ta saka ta fito koda ta gaida Mami ko kallonta bata yi ba ta amsa ciki-ciki, Daddy kam bai amsa ba dan tashi ma yayi ya bata wuri
Sai dai suka yi 5days babu mai kulata ko gaidasu tayi basu amsawa data zauna wuri tashi sukeyi su barta abinci ma Mami bata rage mata…..abin ya dameta sosai kullum sai ta shiga d’aki tayi ta yin kuka sai da tayi kwana biyu bata ci komai ba
Tafe take kaman wadda tayi wata bata da lafiya duk tayi laushi d’akin Daddy ta shiga zata gaida sa tsawa ya daka mata
“Kar ki kuma shigo man d’aki”
K’afarsa ta rik’e tana kuka mai tsuma zuciya tana basa hak’uri yayi k’ok’arin turata amma ina tak’i sakin sa sai kuka takeyi tana basa hak’uri
Ganin yak’i hak’ura yasa ta fashe da kuka numfashinta ya fara fita sama-sama dama she’s asthmatic kuma is like tana da ciwon zuciya…kafin kuce mai idanunta sun rufe tana numfashi da sauri kaman zata mutu dama in ciwon ta ya tashi tana shan wahala sosai
Da sauri ya d’auko inhaler sa ya bata dan it will take long kafin ‘a d’auko nata
Still abun bai yi ba sai ma worst da ciwo yayi hospital aka kaita within the twinkle of an eye sun isa Mami kam ita ma hankalinta ya tashi sosai haka Daddy ma oxygen aka saka mata had’e da yi mata allurai sunfi 30mins ‘a kanta da k’yar suka samu numfashinta ya dawo aka saka mata drip had’e da bata magunguna
Washe gari aka sallameta Daddy na driving Jalila kam tana bayan motar tayi shiru har suka isa bata ce komai ba sai da ta bari sun shiga ciki ta shiga har k’asa ta zube tana basu hak’uri tace ta aminci zata aura Asaad murmushi Daddy yayi ya d’ago ta ya sa mata albarka
D’akinta ta shiga tayi wanka abinci kad’an taci ta sha maganin dan zazzab’i ya rufe ta bata jima ba ta kwanta bacci mai nauyi yayi gaba da ita, koda Anty Nafeesa tazo gaidata tana bacci ta jima kana ta tafi
Tsaye yake ‘a jikin motar sa Mommy ta fito daga motar ta
“Asaad ina zuwa?”
“Mom wlcm, zan je wurin Umar”
“Okay, kasan Jalila bata da lafiya?”
Ta ke mood nasa ya chanja ya b’ata rai yace
“Ita kullum bata da lafiya! Haka zan aureta ba lafiyayya ba”
Tsoki Momi tayi tace
“Wlhy Asaad ka fiya rigima, Asthman ta ne fa ya tashi”
“Ohhh dama she’s Asthmatic ‘a haka zan aureta ta haifa man ‘ya’ya ba lafiyayyu ba bayan ciwon zuciya ga Asthma ohh ya Rabb see me through”
“Kunfi kusa, nidai ka biya ka duba jikin nata”
“Toh” Ya amsa rai ‘a b’ace
Gidansu Umar yaje ya jima suna fira…yana shirin tafiya Momi ta kirasa ta tambayesa ya duba Jalila ya fad’a mata yanzu dai zai je, kallon Umar yayi yace
“Man muje ka raka ni na duba wannan yarinyar”
“Man wai mai yarinyar nan ta maka da baka sonta haka?”
“Haka kawai, sunanta ma inna ji b’aci rai na yake yi”
Girgiza kai Umar yayi dan yasan halin abokin nasa….motar ya shiga suka tafi dai-dai wurin mai fruit Umar yace
“Man zan sayawa Umma fruit”
“Okay”
Parking yayi Umar ya saya fruit d’in 2k suka tafi gidansu Jalila
Kwance take kan cinyar Mami ‘a palo tana sanye da doguwar riga kanta babu dankwali sallamar Asad ne ya katse ta daga labarin da take bama Mami hularta taja ta saka ta dora kanta ‘a kafad’ar Mami, bayan sun gaisa da Mami Jalila tace
“Ina wuni?”
“Lafiya lau, ya jikin?”
“Alhamdulillah am feeling much better” nan ma ta gaida Umar yana ta wangale baki yana cewa matar mu basu jima ba suka tafi Umar ya ijiye fruit d’in suka fita sai da Asaad ya bari sun shiga mota yace
“Wato cin mutuncin da zaka man ka kai fruit ko? Zaka zubar man da class wannan wawiyar tayi tunanin na fara son ta”
Rik’e bak’i Umar yayi yace
“Yanzu dama wannan yarinyar ne kake wulak’antawa kyakkyawa son kowa k’in wanda ya rasa duk wanda ya sameta ‘a matsayin mata ai ya more, kaman ita tayi kanta dan kyau”
“Banza munafuki”
“Oho dai, wlhy kayi wa kanka karatun ta nutsu ka rik’e yarinyarnan hannu bibiyu, in ka rasa wannan yarinyar ai kayi babbar asara” Umar yayi maganar in a serious tone
“Mtswwww, ai had’ani da yarinyar da akayi shine asara mtswwww” Asaad yayi maganar rai ‘a b’ace
“Uhum”
Banza Asaad yayi dashi bai kuma cewa komai ba har yayi dropping d’insa gida Umar yace
“Ka dai ji na fad’a maka”
Tsoki yayi ya gallara masa harara yaja motarsa ya tafi cike da bak’in ciki…..halin Asad sai shi yanzu zaku gama wasa da dariya yanzu kuma zai iya rikid’ewa ya karta maka rashin mutunchi abun nasa kaman mai aljanu dan yanzu zaka fuskarsa ‘a sake yanzu kuma zaka ga ya sha kunu kaman wanda bai tab’a yin dariya ba
❣❣❣❣
: *BARRISTER ASAAD*
Dedicated to
*Meena Parrot*
*Nagode da Addu’o’in ku*
*Memxy BBC*
*Mom Irfan*
*Hafsa Kabir*
*Da ‘yan group d’ina*
1⃣2⃣▶1⃣4⃣
“Wannan fruit haka! ki kirasa ki masa godiya”
Tuni farincikin ta ya tafi tace
“Toh”
Tashi Mami tayi ta shiga ciki Jalila ba dan ranta yaso ba ta d’auka wayanta ta k’ira sa
Zaune yake ‘a office yanzu suka kammala shara’a wasu file ya bud’e yana dubawa wayansa ne yayi k’ara ganin mai k’iran nasa yasa bai yi picking ba sai da kusa katsewa yayi picking shiru tayi bata ce komai ba tab’e baki yayi yace
“Hello”
“Ina wuni?”
“Who’s on the line?” Yayi maganar yana duba wani file
“Kamar ya?” Tayi maganar rai ‘a b’ace
“Nace wayake magana ko baki jin turanci ne?”
“Sorry wrong number” ta kashe wayan ‘a fusace
Murmushi yayi dan yasan ranta ya b’aci…kiranta yayi da kamar barata d’auka sai kuma tayi picking
“Malam wane kai da kake kirana? Bana fad’a maka wrong number bane?”
“Calm down girl”
“Ohhh dama kasan nine shine zaka man haka?” Hawaye ta soma dan shagwab’a ne da ita
Dariya abun ya basa
“Kina nema ki fasa man kunne da k’aton muryanki”
Turo baki tayi tace
“Ni karka kuma kirana mai kat’uwar murya”
“Ke ko kashe muryan nan ma baki iya ba”
“Toni sonka nakeyi ne da zan kashe maka voice”
“Kinji dashi”
Kashe wayan yayi dan yasan inya biyeta sai ta saka masa ciwon kai tun daga ranar basu kuma yin waya ba
Bayan ta warware aka yi masu baiko, aka sa rana December amma da Inno taji tace bare yuw ba ayi bikin jikanta bata nan ba dole ‘a jirata ta dawo tana Niamey tana jiyya ita ne mahaifiyar marigayi Alhaji Hashim baban Asaad ma’ana kakar Asaad(Baban Asaad da Jalila kuma cousin’s ne)
Anty Nafeesa ta rok’a Daddy ya bar Jalila ta cigaba da karatu, babu musu ya amsa dama an bud’e sabon Private uni 3years ake yi chan Daddy ya mata reg- da kome koda Daddy ya sanarwa Jalila ya sama mata admission next week zata fara zuwa school tayi farin ciki sosai ba kad’an ba amma sai da yaja mata kunne sosai akan rashin ji da kula maza…Babaa Amadu ya wakilta shi zai na kaita school kullum kuma shi zai d’auko ta
Yau kam da wuri ta tashi ta shirya kimono ta saka tayi d’aurin turban ta fito fuskarta babu makeup, side bag nata ta d’auka d’ayan hannun nata kuma wayanta…fitowa tayi dan Mommy tana bacci waje ta fita ta sama Baba Amadu ya kai ta school ‘a wurin department nasu ya ijiye ta fitowa tayi ta shiga ta sama seat ta zauna bata fi 2mins wata tazo tace
“Are you Sadeeya Muhammad Ali?”
“Yes, hope all is well?”
“Sure, wani lecturer Mr Abdallah yana kiranki yace i should escort you to his office”
“Okay” tashi yayi suka fita zuwa office d’in nasa knocking yarinyar tayi sai da aka yi like 4mins yace
“Come in”
“Okay”
Cire takalminta tayi Jalila kam tak’i cirewa suka shiga
Tsaye yake ‘a bakin window yana waya ya juya baya, ya kai 30mins yana yin wayan ita kam ganin ta gaji yasa taja kujera ta zauna yarinyar tana yi mata alamar ta tashi amma ina Jalila bata ma san tana yi ba sai ‘yan wak’e2 da take yi ‘a hankula…koda ya gama bai bi ta kansu ba zama yayi ya kunna system d’insa…ita kam mamaki ne ya cikata mai Asaad yake yi ‘a nan is he not a Barrister? Why is he here? Tana tambayan kanta… yafi 3mins kana ya d’ago ya kalleta
“Sadiya right?”
‘A zuciyarta tace ji d’an rainin hankali
“Yes”
“Okay, wato baki da kunya ko? Baki ga ‘yar uwar ki ta ijiye shoe d’inta ‘a waje ba sai ke ko? And you sat on my chair ko? Weldone”
Takarda ya mik’a mata yace
“Write down your name”
“I don’t have biro” tayi maganar tana yin k’asa da kai tak’i tashi daga kan kujerar
Harararta yayi ya cilla mata biro yace
“Unserious element”
Bata ce komai ba ta ijiye masa yace
“OMG! Is this your handwriting! Very bad very poor, just like Nursery student”
Haushi ne ya kamata ganin babu alamar wasa ‘a idonsa yasa ta nutsu
“Wata question paper ya cilla mata yace go and do research on those schoolars, to be submitted tomorrow early in the morning”
“Okay” suka fita yarinyar tace
“Sadiya kinsan mutumin nan bashi da M ko kad’an ki kawo masa assignment d’in gobe in ba haka ba wlhy he can fail you dan yana bama assignment mahimmanci sosai…kinga ‘a department namu he’s the youngest Lecturer amma yafi kowa rashin mutunci da rules”
“Ai da ganin idonsa bai da d’igon mutunci da idonsa ‘a tsakiyar goshi”
Washe gari basu da Lecturer’s assignment ne zai kai ta school da misalin k’arfe 12 ta shiga school knocking tayi ta shiga batare da ya bata umarnin shiga ba
“Morning”
“Morning”
Ta ijiye masa assignment d’in ‘a kan table ta juya zata fita yace
“Jalila come here”
Dawowa tayi ta zuba masa ido yace
“Baran iya gane jagwalgwalon rubutun ki ba kawai send it to my email”
Turo baki tayi tace
“Wayana fa ya lalace”
“Ohhhh am happy for you, you can go”
“Ya Asaad Daddy yace na jira kayi dropping d’ina ‘a gida Baba Amadu yaje Zaria”
Harara ya watsa mata yace
“Toh ‘a nan zaki tsaya man? Sai kije ki jira 1 ya k’arasa….and koda wasa in dai ‘a cikin school ne kar ki kuskura ki nuna kin sanni”
“Toh Malam Audullahi” tayi maganar cike da rashin kunya ta fita ko ‘a jikinta
Restaurant d’in school d’in taje ta saya Shawarma da meat pie da drink dasu chocolate ‘a farar leda aka saka mata ta tafi office d’insa ko knocking bata yi ba ta shiga taja kujera ta zauna ta soma ci ganin ya d’ago kai ya kalleta yasa ta mika masa tace
“Bismillah”
Tab’e baki yayi yace
“Bana ci”
Dad’i ma taji ta cigaba da ci….tashi tayi ta bar sauran ‘a nan ta fita wajen Office d’in wani ne yazo zai wuce tayi ihu tace “Lion!” Hogging d’inta yayi cike da farin ciki suka gaisa sun kai 10mins suna gaisawa daga bisani ya wuce dan ana jiransa
Assad ne ya kira Jalila ‘a waya
“Kizo”
“Okay”
Katse wayan yayi, Jalila ta shigo harara ya watsa mata
“Wanchan k’aton wanene shi?”
“He was my secondary school friend”
“Bance kiyi man dogon bayani ba, kina da hankali da zakiyi hogging namiji daba muharramin ki ba?”
K’asa tayi da kanta yayi mata tas dan abun nata bawai yarinta kawai bane ba hada iskanci yake damunta, system d’insa da key ya mik’a mata yace ta kai masa mota
Ledar shawarmanta ta d’auka ta fita ta jima ‘a cikin motar sai da ya gadama ya fito ita kam sai video take yi ‘a snap dan motor d’in ya tafi da ita sosai range rover fari sol dark tint driver seat ta zauna koda Asaad ya bud’e motar ya ganta ‘a wurin driver yace
“Malama sai ki bani wuri”
“Ka zauna ‘a chan, i’ll drive”
“Wai Jalila ina wasa da ke?”
“Nidai ka shigo”
Kafewa tayi tace ita zata yi driving tsoki yayi ya zauna d’ayan seat d’in yana harararta ‘a zuciyarsa yace “Yanzu wannan mahaukaciyar yarinyar zan aura? Amma ba’a duban ba…yarinta ma bai yi ba da babba ne ita barata tab’a yin wanna n haukan ba”
Cike da nutsuwa take yin driving har suka kai gida tayi parking ta fito ta bar masa key d’in ‘a jikin motar ta shiga cikin gidan girgiza kai yayi yana yin mamakin wautar yarinyar nan ciki ya shiga suka gaisa da Mami ya tafi
Jalila yanzu school ya soma yi mata dad’i tayi friends sai dai bata samun sakewa sosai dan duk wani move nata yana watching ya saka mata ido sosai sai dai tana da d’aukan magana ba kad’an ba
Yau da wuri suka kammala lectures Office din Asaad taje ta samesa ‘a zaune shida wata suna yin magana ko sallama bata yi ba ta shiga bata tanka masa ba ta d’auka ruwa ta zauna
“Wace wannan?” Matar ta tambaya
“Sister na”
“Sannu ‘yammata” matar ta fad’a tana yin murmushi
Banza Jalila tayi da ita had’e dayin tsoki ta shi ta fita
Girgiza kai Asaad yayi yace
“Nadiya don’t mind her haka halinta yake”
“Babu komai” tayi yak’e
Bata jima ba ta tashi ta fita dan suna da lecture’s zata wuce taga Jalila harara ta watsa mata tace
“Ke baki da kunya ko?”
Harara Jalila ta watsa mata tace
“Ke kuma daga ina?”
“Naga alaman hauka na damunki baranyi da k’anwa na ba”
Jalila tayi mata tas ganin barata iya ba yasa ta tafi ta bar Jalila tana ta masifa
Fitowa Asaad yayi yace
“Ke zonan”
Turo baki tayi tak’i zuwa
B’ata rai yayi yace
“Wlhy Jalila in kika b’atan rai sai naki yafi nawa b’aci, daga yau kar ki kuma shigo man office”
Harararsa tayi ta k’asan ido ciki-ciki tace
“Wlhy baran bar shigowa ba”
“Repeat your statement”
“Ni bance komai ba” ta tafi
Shi ya gaji da wannan neman tsokanan nata kullum tazo office d’insa sai ta takala wani ko wata fad’a tayi ta yin tsoki da harar su, yayi mata fad’an tak’i ji….
: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
*Nagode da addu’o’in ku*
Ummu Hanan
Laila Agadaz
1⃣5⃣▶1⃣6⃣
Tsaye take tana jiran Baba Amadu yazo d’aukanta ganin bai zo ba yasa ta sama wuri ta zauna, Assad ne ya fito zai tafi yace
“Ke kizo mu tafi”
Banza tayi dashi
Ruwan da yake hannunsa ya yayyafa mata d’ago kai tayi bata ce masa komai ba ta zuba masa ido
“Tashi mu tafi”
Bata ce komai ba tabi bayansa tana tafiya kaman bata son taka k’asa har sun shiga mota yana niyar tayar da motan Nadiya tazo tace
“Mr Abdallah ga file d’in”
“Okay, Thankiu”
Murmushi tayi tace
“Wlcm, bye” ta rufe masa motar suka tafi Jalila kam tsoki tayi bata ma san ya fito ba kallonta yayi yace
“Mai tayi maki?”
“Babu komai”
Ganin motan gidansu yasa ta fita bata ce masa komai ba shi ma bai ce da ita komai ba yaja motar sa ya tafi
“Baba Amadu ka biya dani MS zan saya Pizza”
“Toh auta”
Labari ta cigaba da basa har suka isa dama shima surutu ne dashi ba kad’an ba haka suka yi ta yin surutu, shiga tayi ta saya Pizza ta fito ta shiga mota bud’e box d’in tayi tace
“Baba ai ka iya ci ko?”
“Iye! Ina ni ina cin wannan abun”
Dariya tayi tace
“Baba farin buzu sai shayi”
Shi ma dariya yayi wayanta ne yayi k’ara ganin Assad ne yasa ta b’ata rai ta d’auka jin voice d’in Safiyya ne ta k’ira yasa ta saki ranta
“Hello Besty”
“Best friend longest time”
“Wlhy, jiya na dawo daga school”
“Allah sarki, ina trying number ki not reachable”
“Wlhy Besty wayana ya lalace fa”
“Eyya”
“Kina gida ko?”
“Eh ina nan”
“Zan zo anjima”
“Dagaske? Am happy, can’t wait”
Jalila tana komawa gida d’akin Mami ta shiga tayi wanka mai ta shafa ta d’auka rigan Mami ta saka ta shiga kitchen
“Jalila sannu, wato sai kin bud’e man rigana ko”
Dariya Jalila tayi tace
“Mami kin fini kib’a fa”
“Ahhhh kin manta”
“Hhhh, Anjima Safiyyan Anty Nafisa zata zo”
“Eh ta k’irani ta d’azu”
Tuwon shinkafa da miyan taushe suka yi wa Daddy bayan sun gama Jalila tayi dambun shinkafa da kunun aya data kammala ta chanja kaya ta saka atamfa gown tayi d’aurin ture kaga tsiya sai k’amshin turare ta keyi irin na ‘yan Maiduguri
Tana jin k’arar mota ta fita Safiyya ta fito cikin mota hogging juna suka yi suka shiga ciki Mami ta gaida suka shiga cikin d’akin Jalila
Safiyya tayi murmushi tace
“Jalila haka kika yi kib’a! Cute pie”
Murmushi Jalila tayi tace
“Ai kin fini kib’a”
“Besty Besty, yanzu 17year’s kik’e ko?”
“Hahhh har kin manta? December zan shiga 16 nan da 10months”
“Kai yah still a kid”
“Ahhh kin manta”
Suka kwashe da dariya wayan Jalila ne yayi k’ara
“Hello Mami”
“Na’am kije ku gaisa da Assad yana palo”
“Toh”
Cire d’ankwalin tayi ta yafa mayafi ta samesa ‘a palo gefen hannun kujera ta zauna tace
“Ina wuni?” Batare data kallesa ba
“Lafiya lau”
Tashi tayi yace
“Ki zauna ki man fira mana”
“Ni wurin Safiyya zanje”
“Okay ai sai ki tafi, nima bari na tafi wurin budurwana”
Tab’e baki tayi ya fita ta kai wa Safiyya abinci dasu snacks da drink
“Besty na mai ya sama wayanki?”
“Lalacewa yayi 6s+ ne i don’t think zai gyaru”
“Eyyah” Drawer Jalila ta bud’e ta d’auko wani farin leda ta mik’awa Safiyya, bud’ewa Safiyya tayi taga 7+!
“La sabon waya kikayi ko bud’ewa baki yi ba ma!”
Murmushi Jalila tayi tace
“Eh sabo ne ko bud’ewa ban yi ba, Daddy aka kawo wa su shine ya bani, ki d’auka na baki”
“What? Stop kidding me”
“Wlhy da gaske na baki”
K’in karb’a tayi sai da Mami ta sa baki kana ta karb’a wayan
Hogging juna suka yi….Mami ma taji dad’i sosai dan abotan su na burgeta ba kad’an ba
Sai dare ta tafi Mami ta had’a ta da sha tara na arzik’i….Mommy tayi wa Mami da Jalila godiyan waya sosai
“Fad’a mata kikayi baki da waya?” Assad ya tambaye ta yana hararan ta
“Aah”
“Wato ga matsiyaci na kasa saya maki waya sai wata ko?”
K’asa tayi da kan ta bata ce komai ba ya gama fad’an sa ya fita tab’e baki Mommy tayi tace
“Don’t mind him ai ba rok’a kika yi ba ita ta baki, aure kuma in sha Allah babu fashi sai anyi nasan abinda yake wa fad’a kenan”
Safiyya da Jalila best friends ne sosai da sosai dan duk hutu wannan tana gidan wannan…wani hutun wannan tana gidansu wannan yanzu nema da Safiyya ta tafi boarding zumunchin ya ragu dan ba tare ake yi masu hutu ba…amma they are always in touch ‘a waya
The next day data je school bayan sun gama lectures ta shiga office d’in Assad ta same sa shida Nadiya, kallonsa tayi tace
“Ya Assad Morning”
“Morning”
Juyawa tayi zata fita yace
“Baki ga mutum ba da baraki gaida ta ba?”
Juye-juye ta fara tace
“Ni banga kowa ba” Ta harara Nadiya had’e da yin tsoki
“Wai mai nayi wa wannan yarinyar? Kullum ta ganni sai ta harare ni tayi tsoki mai na mata?, There’s nothing wrong here”
“Jalila zonan”
D’aure fuska tayi taje…fad’a sosai yayi mata bata ce komai ba ta fita…tana fita ta fashe da kuka abinku da mutum shag’wab’abb’e mai saurin kuka..A fight was the last thing she needed
Throughout week d’in bata kuma zuwa office d’insa ba ko ‘a hanya ta hangosa chanja hanya take yi!
Yau 2weeks dai-dai bata je office d’insa ba, ba laifi yayi missing dramar ta, wani student yasa yaje department nasu ya kira ta… ‘A waje yaganta tana yin waya sai da ya jira ta gama yace
“Pls nan department d’in kike?”
“Eh, wani abu?”
“Dama Mr.Abdallah Hashim ne yake k’iran Sadiya Muhammad”
“Yanzu ta fita, inta dawo i’ll tell her”
“Okay, thanks” Ya k’ara gaba
Dama sun gama lectures tafiya tayi ta sama Baba Amadu yazo tana niyar shiga motan Khalil class rep yace
“Mr Abdallah na k’iran ki”
She stared at him she saw a glimpsed what tomorrow would bring tace
“Bye i’ll catch up later, yanzu ina ciwon kai, ka fad’a masa baka ganni ba”
“Hhhhh okay” Ya tafi
“Woah,” a cool voice said as she heard footstep coming towards her
Juyawa tayi suka had’a ido da Assad d’auke kai tayi yace
“Miss are you alright?”
Shiru tayi bata ce komai ba ganin shirun yayi yawa yace
“Dan nayi maki fad’a shine kike yin gaba dani ba, good! Gobe in kin gadama kizo ki karb’a course outline na duka course naku exams is approaching”
D’aga kai tayi alaman to ta shiga mota suka tafi, Assad kam mamaki ne ya cika sa dan bai tab’a tunanin Jalila ta iya fushi ba sai yau yasan tana da saurin fushi sai dai da tayi take sauk’a amma wannan fad’an nasu ba’a magana getting to 3weeks fa!
Yau koda ta shigo school bata yi surutu sosai ba bayan sun gama Office d’in Assad ta shiga sallama tayi fuskarta babu annuri tace masa
“Ina wuni”
“Lafiya”
‘A tsaye ta tsaya ya mik’a mata takardu masu d’an yawa yace
“Kinyi man tsaye ‘a kai ko ki zauna ko kuma ki matsa”
Bata ce komai ba ta matsa yace
“Akwai course d’in ya yake baki wahala?”
“Babu” ta amsa fuska babu annuri
Nadiya ne ta shigo suka yi shaking hannu da Assad…Jalila ko takansu bata bi ba ta tafi koda ta koma gida ranta babu dad’i sai da ta samu tayi bacci kana ta sama sauk’i
Tun daga lokacin ta bar shiga harkan Assad shi ma barin shiga harkanta yayi barinma yanzu da yaga ta nuna bata son yana shiga harkanta…yanzu Nadiya take ebe masa kewa cox kusan suna tare ‘a office nasa ko wane time
Jalila kam sam ta fita harkansa sai suyi 2weeks ko fi basu had’u ba in ma sun had’u may be time d’in anzo d’aukanta ne shi ma zai tafi sai yayi kaman bai santa ba ita ma haka yanzu sam basu yin magana
‘A kwana ‘a tashi babu wuya ‘a wurin Allah su Jalila sun gama Exams d’in Level1 both first semester and second..her result was very good First Semester 8 A sai 1 B second kuma flat A guda 8…Daddy da Mami sunji dad’in ganin result d’in ba kad’an ba dan tayi karatu sosai tsakaninta da Allah…Daddy ya tsokaneta yace ashe dama tana da k’ok’ari😂…kawai tana yin karatu ne dan ta farantawa kanta dan inta ita ne she ‘ll never read…sabon waya ya chanja mata… Data koma school wulak’anci ta k’aro sai ma taga Assad ta fito da sabon wayanta dan shi IPhonex ne dashi ita kuma IPhonex maxxxxss ne da ita😂
Assad yaga result nata he was happy ita ne first class d’in department nasu…amma sam bai nuna mata ya sani ba yana ma nuna mata d’aukan mara k’ok’ari yake yi mata, this semester ya fara Lecturing nasu duk question daya tambaya Jalila sai ta amsa gashi tayi ta tambayar sa question ta k’ure sa! Tana Challenging nasa😂…dan Course outline din taje tayi research Daddy kuma yana yi mata tutorial shiyasa duk Topic da zai yi ta riga data karanta ta gane
Hy Reader’s🙋🏽♀
Here’s a flower for you💐
: *BARRISTER ASSAD*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
Nagode da addu’o’in ku
*Hamdallah*
*Maman Zainaba*
1⃣7⃣▶1⃣8⃣
Baffa Suleiman ne yazo aka sa rana dan ya gaji da halin Inno yaga alamar in aka biye mata bara’ayi bikin ba dan da bakinta ta fad’a masa bata son had’a zuri’a da Muhammad(Daddy) dama tun chan bata son sa!
Aka tsayar da rana nan da 3weeks za’ayi bikin
Already dama Jalila ta fara gyaran jiki tun 3months da suka wuce ake yi mata gyaran jiki….tun da aka sa rana Jalila ta bar zuwa school wata mai gyaran jiki daga Somalia tazo cousin d’in Mami ne matar…gyaran jiki akayi mata jikinta yayi kyau sosai tayi fresh face nata babu k’urji ko d’aya sai wani glowing da skin nata yake yi! Gashi sam bata shiga rana kullum tana cikin Ac kyanta ya k’ara fitowa sosai kaman ka sace ta
Yau Thursday gobe za’a fara event, yau za’a yi mata lalle zaune suke ‘a palon Daddy ana yi mata kunshi ita da Safiyya da sauran friends nata lallen amarya yayi kyau sosai kaman me gashi yanzu jikinta ya kama k’amshin turaren ‘yan Maiduguri koya ta gifta sai kaji k’amshi, bayan an gama ya bushe Safiyya ta taya ta wanke wa
Zaune suke ita da Safiyya ‘a d’akinta Jalila ta d’auka wayanta ta shiga IG ta goge duka post nata ta mayar account d’inta private tsoki tayi tace
“Matsalar ma kayi suna kenan yanzu mutane nasan kwalliyana kawai suke jira”
Murmushi Safiyya tace
“Haka ne fa ana sakawa Models ido ba kad’an ba amma ai kin wuce tunanin mutane”
Suka tafa
*Washe Gari*
Ya kama Kamu k’awayen amarya ankon atamfa suka yi dukan su 10 fitted gown color d’in atamfan yayi kyau sosai 15k atamfan…Safiyya kam nata gown d’in daban tayi dan d’inkin ta yafi na sauran kyau dan ita ne babbar k’awayar amarya….Amarya kam tasha kyau harta gaji ita ma peach lace ta saka aka mata buba amma ango bai je ba event d’in ba mutanen cikin wurin sunyi kyau sosai barinma Amarya kaman ka sace ta! Ali Jita yayi wasa amarya da friends nata suka chashe dama k’awayen nata suma ‘yan bidi’a ne they are social most of them ma they are Models…kunsan ‘yan Kaduna da gayu no need na fad’a maku sauran
Yau aka d’aura auren Abdallah Hashim Ali da Sadiya Muhammad Ali ‘a kan sadaki dubu dari…..da dare kuma dinner ko ‘a wurin makeup an b’ata lokaci sosai wurin tsara amarya tayi kyau sosai…Amarya kam Hudayya ta mata d’inki mai mugun kyau farin gown irin na 100k d’innan tayi mata ta fitar da ita sosai ga makeup ta sha tayi irin mugun kyau ba kad’an ba
Jalila inba an fad’a maka Buzuwane ita ba sai ka rantse she’s Indian!
Yau tayi kyau harta gaji Sai k’amshi take zubawa na musamman, Palon Daddy suka shiga ita da Safiyya Assad ya sha bak’ar suit da farar ‘yar ciki, har wani glowing shima Assad yayi…yayi kyau sosai dan haske kawai zata nuna masa ba dai kyau ba! Sajen sa ya sha gyara haka kwantacciyar suman kansa ya sha gyara lips nasa pink sai glowing yake yi…Ganin Jalila ta fito yasa ya k’arasa kusa da ita ya rik’e mata hannu yace
” ‘yammata ina Jalila?”
Murmushi tayi tace
“Baka ce nayi kyau ba, na manta munyi fad’a nake yi maka magana”
“Sorry Girl, let’s be friends for today”
“Toh, kace nayi kyau
“Kinyi kyau kaman a india”
tayi murmushi aka yi ta snapping nasu ‘a waya and camera sunyi irin mugun kyau
Mota suka shiga suka tafi wurin da za’ayi event d’in tunda suka shiga mota yake yin waya har suka isa ya fito hannu ya bata ita ma ta basa suka shiga ciki tana yi tana yi masa gulma daga tace kalla waccan sai wannan shi ma biye mata yayi suka yi ta yi, mutanen da suka zo Dinner duk manya ne da ‘ya’yan manya english gown suka saka ‘yammatan mazan kuma suit decoration d’in wurin yayi kyau sosai komai yayi kyau babu abun kushewa
Photographers k’wararru suka je Amarya da Ango sun sha pictures ba kad’an ba gashi both of them are photogenic, Friends d’in amarya da ango sunyi kyau ba kad’an ba irin wayayyun nan kud’i sunyi kuka Assad kam da Jalila babu kunya suda friends nasu suka chashe kaman babu gobe wani abunma sai da Reekado Banks yazo
Mami kam ba’a son ranta ba akayi event d’in ba dan ita bata son bid’ia cewarta albarkar auren ake so
Ranar ‘a gajiye suka dawo gida, ranar Sunday aka shirya amarya cikin lafaya aka tafi da ita gidansu Assad da k’yar aka rabata da Mami da Daddy tana kuka Mami na kuka Daddy kana sai dai yayi kuka dan sun shak’u ba kad’an ba….koda suka je gidansu Assad Safiyya nema ta rage mata kewa da yamma suka yi bud’an kai!
🌌: *BARRISTER ASSAD*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
*Wannan shafin naki ne Mom Irfan❣*
1⃣9⃣▶2⃣0⃣
Da dare ango ya wuce da amarya gida tun ‘a mota take yin kuka har suka isa, gidan amarya yayi kyau fitowa yayi yace da ita
“Ki fito”
Ganin bata da niyan fitowa yasa yayi gaba abunsa, tsoro ne ya cikata yasa ta fito da sauri d’aki ta shiga ta fad’a kan gado tayi ta yin kuka, Assad ne ya shigo yace da ita
“Tashi kice abinci”
“Ba’aci” ta cigaba da kuka koda ya maimaita bata kula sa ba takaici ne ya cika sa ya fita…kusan kwana tayi tana kuka sai wurin asuba ta samu tayi bacci
Da misalin k’arfe tara ta tashi tayi wanka ta saka sababbin kayanta maroon lace ta saka ta shafa jambaki maroon sai k’amshi take zubawa, ta fito palo jin anayin knocking yasa taje ta bud’e k’ofan ganin mai aikin Mommy ne yasa tayi murmushi tace
“Ina kwana?”
“Lafiya lau Amarya, kin tashi lafiya? Ya angon naki?”
“Lafiya”
“Hajiya tace ‘a kawo maku”
“Toh”
Ciki ta shiga ta ijiye tace
“Na wuce”
“Toh Baba Indo nagode, ‘a gaida Mommyn”
“Toh zata ji” ta fita
Jalila ta rufe k’ofan plate ta d’auka ta iba chips and egg ta soma chi sama-sama
Assad ne ya fito sanye da bak’ar shadda yanata zuba k’amshi kallo d’aya tayi masa ta kawar da idonta yau kam yayi mata kyau
“Waya kawo abinci?”
D’ago kai tayi ta kallesa da zata yi masa rashin kunya ta kasa dan yayi mata kwarji, spoon ta soma wasa dashi tace
“Baba Indo”
“Ki kaiman d’aki” ya fad’a yana niyar fita
“Naga fita kuma zaka yi?”
“Ohhh baraki kai ba? Sai kin yi man rashin kunyan da kika saba ko”
Shiru tayi bata ce komai ba
“Ohhh baraki kai man ba? Kin rainani ko?”
Tashi tayi ta kai masa d’aki wasu hotuna ta hanga ‘a kan dressing mirror d’insa wurin taje ta d’auka ta duba Assad ne da Hamida ‘a hoton wani hoton ya dafata wani sun rik’ewa juna hannu!
D’aukan hoton tayi ta yaga ta watsa su ‘a kan gadonsa ta fita d’akinta ta shiga suka gaisa da Dadi da Mami ‘a waya
Bayan ta gama palo ta dawo ta kunna Tv ta soma kallo zaman gidan duk ya isheta ita d’aya, dama ita ta saba da hayaniya ba’a jima ba sisters d’in Daddy da Mami suka zo bayan sun tafi Assad ya kira Jalila ‘a d’aki ta samesa yana zaune gefen gado harara ya watsa mata yace
“Waya baki izinin yaga wannan hotunan?”
“Nima bansani ba, zuciyana ne yace na yaga”
Kallonta yayi kusan na 5mins har sai da ta tsargu yace da ita
“Jalila kin kika raina ko?”
“Kayi hak’uri”
Tsoki yayi yace ta fita ta basa wuri fita tayi taji sallama ganin Hamida ne yasa ta zauna batare data ce da ita komai ba, murmushi tayi tace
“Amarya bakya lafiya ko kin kashe d’an masu gida”
Shiru Jalila tayi bata ce komai ba, Assad ya fito ganin Hamida yasa yayi murmushi dama muryanta yaji ya fito gefenta ya zauna yace
“Hamidooo how far?”
“Ango fine”
Tashi Jalila tayi ta shiga ciki, Assad kam ko ‘a jikinsa fira suka sha da Hamida sallamar Inno ne ya katse su…har kasa suka duk’a suka gaidata Inno tace
“Kece Sadiyan ko?”
“A’ah Mama ni sunana Hamida”
“Abokiyar aikina ne” Assad ya fad’awa Inno
Zama Inno tayi tace
“Allah sarki d’iyan arzik’i kinyi aure?”
“A’ah Mama banyi ba”
“Allah sarki Allah baki nagari”
“Amin”
K’asa ta d’uka tace da Inno ta wuce Inno ta yaba da hankalinta sosai nan kam bata san ladabin d’an kunama bane ba, kallon Assad tayi tace
“Abdallah ina matar naka?”
“Tana wanka, bari na duba kota fito” yayi mata k’arya
Har zai tashi sai ga Jalila ta shigo k’asa ta d’uka tace da Inno
“Mama ina wuni?”
Tab’e baki tayi tace
“Lafiya, Sadiya”
Tashi Jalila tayi ta zauna kan kujera tana wasa da yatsunta, Inno tace
“Ke amarya haka ake tarar bak’i ko ruwa baki san ki kawowa mutane ba, me sunan wannan Hamida take kowa tafiki hankali da mutunci”
D’ukawa k’asa tayi tace
“Mama kiyi hak’uri na bari mu gama gaisawa ne”
Tab’e baki Inno tayi Jalila ta tashi ta shiga kitchen tray ta fito dashi ta ijiye ‘a center table ta zuba mata ruwa ‘a cup d’aya, d’ayan cup d’in kuma ta zuba mata drink ta ijiye mata chin-chin da dublan da nama….
Kallonta Inno tayi tace
“Wato ke rowa ne dake ruwan ma sai kinyi k’oran sa! Allah yasa ma ki iya ma kula da mijin naki”
Shiru Jalila tayi kanta ‘a k’asa ta zauna gefen Assad…Inno ta harara Jalila ta gefen ido tace
“Ki bamu wuri zamuyi magana nida jika na”
Tashi Jalila tayi ta shiga ciki…Inno tace
“Abdallah ‘a nan zanyi wata d’aya”
“T…t..toh Inno”
“Ina d’akin saukar bak’i?”
Nuna mata yayi ta tashi ya bita ‘a baya ta suka shiga d’akin yace
“Ga dak’in ki”
Murmushi tayi tace
“Ma sha Allah gida yayi kyau sosai, gidan nada girma gaskiya bai kama ace mace d’aya bane ‘a gidannan ba”
Murmushi yayi yace
“Nikam Inno bani da ra’ayin mata biyu”
“Ohhhh wannan ta asirce ka toh ta Allah ba tasu ba” Ta turo k’ofan
Shikam mamaki ne ya cika sa da sha’anin Inno ya za’ayi ma ace tazo ta tare masu ‘a gida? Yana ta tambayar kansa
Dan tsohuwarnan halinta sai ita, kamar ya shiga d’akin Jalila sai kuma wani zuciyan yace
“Kai manta da y’ar rainin wayon, nasan inna shiga b’atan rai ma zata yi
Fita yayi ya bar gidan bai dawo ba sai da yamma koda ya dawo Inno tana kitchen tana dafa d’anwake jin motsi ‘a kitchen yasa ya shiga
“Inno? Abinci da kanki!”
“Toh tunda wannan ‘yar banzan yarinyan tak’i shiga kitchen ba dole na shiga ba”
“Amma Inno ince ana kawo abinci daga gida”
“Toh bana son wannan abincin, yau ma ya kama ta wannan yarinyan ta fara shiga kitchen”
Bai ce da ita komai ba ya fita ‘a d’aki ya sama Jalila shiru tayi tagumi
“Jalila”
“Na’am” ta d’ago ta kallesa
“Nan Inno zata zauna for a month, kinsan tsofaffi da rigima komai tace kawai kibi da ita haka”
“Toh”
“Yanzu tashi kije kitchen ki karb’eta tana dafa abinci”
“Toh”
Jiki ‘a sanyaye ta tashi ta same ta ‘a kitchen
“Sannu Mama”
Banza Inno tayi da ita ta cigaba da dafa abinci
Kusa da ita taje tace
“Mama bari na karb’e ki”
“Mtswww sai yanzu kika san zaki karb’eni? Wato munafurci ko sai da mijin naki yazo zaki ce zaki karb’eni” tayi maganar cikin fad’a… “Kikayi man tsaye zaki wuce ko sai na b’ata maki rai”
Jiki babu k’wari ta kuma bata hak’uri ganin bata da niyar amsata yasa ta fita ta sanarwa Assad ya bata hak’uri da kansa
Jalila tana kunna turaren k’amshi taji knocking bud’e k’ofan tayi taga Adda Nabila ne hogging d’in juna suka yi hannunsu rik’e da juna suka shiga palo ta gaisa da Inno da Assad suka shiga d’aki ita da Jalila kan gado suka zauna Nabila ta dafata tace
“K’anwana mai yake damunki? Naga fuskanki d’auke da damuwa, in dai kewar Daddy ne da Mami ki rage if not zai yi affecting marriage naki kinga muma ‘a haka muka saba though ba wai bamu son iyayenmu bane ba a’ah we love them morethan we do for ourselves sai dai we have no option than mu cire damuwa ‘a ranmu su kansu basu da burin da ya wuce suga sun aurar damu and we are forever than favs”
Murmushin k’arfin hali Jalila tayi tace
“Haka ne am missing my parents badly sai ‘a sannu zan saba sai dai kuma it will be very hard for me na saba dasu”
“Yes you are right nasan keda Assad bawai kuna son junan ku sosai ba with time komai zai koma normal in sha Allah”
“Adda Nabila ni yanzu abun ya had’e man ga Ya Assad ga kakarsa ita ma wlhy baki ga fitinarta ba i heard she ‘ll stay here for a month…akwai wata friend ko nace girlfriend d’in Ya Assad baki ga yadda shida kakarsa suke son ta ba”…nan ta fad’a mata duk abinda ya faru dan she’s very free with her siblings dan yanzu wannan maganar she can’t tell her parents dan bata son hankalinsu ya tashi ko kad’an amma she can tell her siblings
Shawara kala-kala Adda Nabila ta bata ‘a kan zaman aure
“Addu’a makamin mumini ne, ki kasance mai ladabi da biyayya ga mijin ki tsafta, hak’uri koda wasa kar ki kuskura ki d’aga muryanki sama dana mijinki, iya magana iya abinci, tausayin miji da yi masa uzuri da kyakkyawan zato, ki yawaita addu’an Allah baki ikon hak’uri da mijinki ki koya juriya da hak’uri ‘a zaman aure, ko wanne irin hali ne da mijinki sai kinyi hak’uri ki sawa ranki zaki iya k’ok’arin ki wurin ganin kin gyara sa don kiji dad’in zama da shi,
Duk namiji yana son macen data iya Soyayya da biyayya, Wacce ta iya magana, ta iya girki, salo na kwalliya da yarda da k’addara, Wacce take yi wa mijin ta addu’a, wacce ‘a kullum burin ta ta faran ta wa mijinta,
wacce ta iya magana da sassauk’a murya, mai yi wa iyayen miji biyayya tamkar iyayen ta, wacce in ya kalle ta sai ya ji dad’i, mai amana, mai tsafta, mai iya magana, wacce ‘a kullum tana k’ara kusan ta shi ga Allah da sunnah, Akwai tarin mazan da basu da lokacin iyalansu, Fushin zuciya bana ki bane zama mage shi ne mafutarki ki koyawa kanki zama jikinsa komai kankantar lokacin da kika samu,
Yau da gobe zaisa ki sabar masa da zarar ya fita zai ji kewar ki yau da gobe shi ma zai saba da dumin ki”
Bayan Nabila ta tafi Jalila tayi joining Assad ‘a palo suka soma kallo
“Jalila”
“Na’am”
“Ki shirya anjima zamu fita”
“Toh ina zamu je?”
“Toh sarkin tambaya wane journalist, zamu je shopping ne”
Dad’i taji atleast zata ga gari! Da dare suka fita basu dawo ba sai wurin 10..koda suka dawo Inno tayi bacci Jalila ta yar da key d’in d’akinta hawaye ta soma Assad kam abun haushi ya basa dan ya tsana kuka ita kam abun kuka bai yi mata wahala! Ranar ‘a d’akin sa ta kwana…..🙊
Haka zamansu ya cigaba da kasancewa kullum Inno sai tayi wa Jalila fad’a, fad’an safe daban na rana daban na dare daban barin ma yanzu da Assad ya koma aiki (Dama wani aiki ne aka turasa ‘a ckul d’in yanzu kuma ya gama ya bar zuwa ya koma Court) daga Inno sai Jalila ‘a gida kullum Inno cikin yi wa Jalila fad’a takeyi…Assad 8 yake fita aiki sai 8 yake dawowa dan sai ya tsaya yayi sallah ita kam Hamida ‘a week sau biyu take zuwa gaida Inno amma bata bari su had’u da Assad sai ta tabbatar ya tafi aiki Inno kam tana sonta fiye da Jalila!
: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
2⃣1⃣▶2⃣2⃣
Key ya saka ya bud’e motar sa sallamar da aka yi masa ne yasa ya juya ya kalla mutumin da yake yi masa sallamar
“Barrister Assad”
“Na’am?”
“Dama ina son muyi wani magana mai muhimmanci sai dai kuma muna da buk’atar samun wuri”
Agogon hannunsa ya kalla yace
“Yanzu gaskiya i have alot to do, sai dai in zaka bari gobe”
“Gobe is too far why not ka bani time zuwa anjima”
“Okay”
“Your address”
Card d’insa ya mik’a masa mutumin yace
“Dama Ogana ne ya aiko ni yana cikin mota if babu matsala pls kazo ku gaisa”
K’ara d’aure fuska yayi ya bud’e motarsa ya shiga ya tafi mutumin yace fad’a masa Assad yak’i zuwa murmushi mutumin yayi yace
“Babu damuwa dama ance shegen girman kai ne dashi kaman me ya fiya ji da kansa, ai mu muke neman abu ‘a wurin sa dole mu lallab’a sa ince ka karb’a number sa?”
“No bai bayar ba ya dai bayar da card d’insa”
‘Kai! Girman kansa yayi yawa sai kace d’an sarki” karb’an card d’in yayi yaga Address nasa
Haliru Dantoro creasent Malali
Yana zaune ‘a palo yana cin danbun shinkafa da vegetable soup Jalila ta fito da plate ‘a hannunta ta zauna ta soma ci kallonta yayi yace
“Wai mai had’inki da danwake? bana son warinsa”
Girgiza kai tayi dan tasan Assad da iyayi shi komai bai yi masa ba ko abu kayi baka burgesa sai ya nema yadda ya kushe
“Kawo man ruwa mara sanyi”
“Yaushe ka fara shan ruwa mara sanyi?”
“Ranar da kika fara” ya fad’a mata bak’a
Tashi tayi taje ta d’auko masa ta zauna ta soma cin d’an waken ta, Inno ta shigo
“Ke Sadiya kinyi tuwo?”
“A’ah” ta cigaba da cin abinci
“Ohhh ina yi maki magana kin mayar dani y’ar iska kika cigaba da hidiman gaban ki”
Shiru tayi bata tanka Inno ba
Assad ya d’ago kansa ya kalla Inno dan shi ya soma gajiya da ita yace
“Inno akwai damubun shinkafa kici mana”
“In banci ba to mai zanci? Tunda wannan yarinyar ta rainani abincin ma sai ta gadama take bani”
Tab’e baki yayi ya cigaba da cin abincin Inno tace
“Ina ma amfanin auren macen d’aya” tayi ya mita Assad dai bai ce komai ba Jalila ma haka shiru tayi
K’arar waya ne ya katse sa ya d’auka
“Hello Oga wani mutumi wai yana sallama, yace ace da kai mutumin d’azu ne”
“Okay ka bar sa ya shigo, ina zuwa” ya kashe wayan
Tashi yayi Jalila tace
“Ina zaka je?”
“Waje” ya bata amsa ‘a tak’aice dan ta fiya tambaya Inno kam tsoki tayi tace
“Kewai mey naki? Gulma da chan in zai fita tambayar sa kike yi ne?”
Jalila bata ce komai ba ta cigaba da cin d’an waken ta, Assad kam bai ce komai ba ya fita
‘A harabar gidan suka zauna kujerun kusa da light suka gaisa mutumin yace
“Barrister Abdallah Hashim Ali wanda akafi sani da Assad ko? Ni kuma sunana AbdulRahim Sani Gombe naji labarin ka k’ware ‘a aikin ka sosai wannan dalilin ne yasa nazo all the way from Abuja don na ganka”
Girgiza kai Assad yayi yace
“Okay, yanzu mai yake tafe da kai?”
“Yawwa anzo wurin, wani case na kawo maka”
“Okay go ahead”
“D’ana ne ya kashe wani yaron talakawa iyayen yaron sun shigar da k’ara kotu sai dai sun sama mai tsaya masu shi ne nake so muje dan ‘a Abuja za’ayi shara’ar…kud’i ba damuwa na bane ba wlhy ko nawa ne in dai har zaka kare d’ana wlhy zan biya tun daga miliyan d’aya abunda yayi sama zan iya biya”
“Okay, zan yi maka wasu tambayoyi”
“Okay”
“Wane aiki kake yi? Kuma mai silar kisan?”
“Ni d’an siyasa ne”
“Yawwa anzo wurin kaga ko wannan kawai ya isa ‘a kare d’anka dashi we can say they ‘re trying to blackmail you”
“Yawwa Barrister, abinda ya had’asu ba wani abu bane ba wata yarinya suke so ita kuma yarinyan tana son su duka shine Kabir ya kashe sa “Toh taya iyayen yaron suka san Kabir ne ya kashe sa?”
“Kawai dai sun san suna neman mace d’aya kuma Kabir yana yawan furucin sai ya kawar da yaron”
“Okay, ita yarinyar iyayenta ‘a ina suke da zama? Kuma su wane su?”
” ‘A Suleja suke da zama iyayenta dana yaron talakawa ne sosai, kasan yaran zamani kome Kabir ya gani da zai sota ma oho kawai dai yarinyar she’s extremely cute”
Jikin Assad ne yayi sanyi yace
“Babu wani abu, amma dole ka had’amu da iyayen yarinyar kaga in muka siye su shikenan”
“Yawwa Barrister na gode, gashi bamu yanka ticket da wuri ba da sai mu wuce Abuja gobe by flight”
“No ni babu damuwa mota ma is okay”
“Toh shikenan, yanzu million nawa zan fara baka? Is 10M okay? Daga baya sai na cika maka sauran ko?”
Assad ‘a zuciyar sa yace
“Kuji yadda yake k’iran kud’i just like water! Ko da yake b’arawon gov’t ne dole bare ji komai ba” ‘a fili kuma cewa yayi “Eh is okay”
Yaron da yake tsaye ‘a gefen sa ne ya mik’awa Alhajin wani box…Alhaji ya mik’awa Assad yace gashi 10M ne”
“Okay” karb’a yayi Alhajin ya wuce, tashi Assad yayi ya jima ‘a wurin yana tunani hanyar cikin gidan ya nufa Jalila ta mik’a masa waya ta fashe da kuka tace
“Dama Ya Abdallah abinda kake yi kenan? Ashe dama marasa gaskiya ne suke sayan ka? Ya Abdallah duk dukiyan daka tara ashe haram ne!”
Kallon mamaki ya bita dashi yace
“Wato dama duk abinda nake yi kina yi man lab’e!?”
“Tunda nake ban tab’a yin lab’e ba yanzu ma Mommy ne take k’iranka nazo kawo maka abubuwan da kunnena suka ji yasa k’afafuwana suka kasa d’aukan gangan jikina” Ta wuce ta bar sa ‘a nan, Mommy ya k’ira suka gaisa
Jalila toilet ta shiga ta sha kuka ta gode Allah ranar da wuri ta kwanta
Shikam Assad ranar kasa bacci yayi dan shi Case ya soma chaja masa kai!
*WASHE GARI*
Da misalin k’arfe sha d’aya ya fito cikin shirin sa ya sha shadda coffee shadda da brown hula sai kamshin turare yake yi jakar system d’insa ya d’auka da wayan sa da key ya fito lokacin Jalila ta gama gyara gida ta had’a breakfast ta fito daga kitchen ta gansa ya fito daga d’akin Inno kallo d’aya tayi masa ta d’auke kanta d’akinta ta shiga shikam ya fita ya tafi Abuja…haushi ya cika Jalila taya za’a ce ya goya bayan k’arya? Wato dama aikin da yake yi kenan? Wayanta ta d’auka ta turawa Assad message kamar haka
“What ever you did you will account for it here after, so think twice don’t commit a crime”
Yana driving yaji k’arar message wayan ya duba yaga Jalila ne ganin abinda ta rubuta ya girgiz a kai ya ijiye wayar ya cigaba da yin driving
Jalila kam duk ta damu ta rasa taya zata b’ullo masa ma hak’ura tayi kawai ta bari sai ya dawo kwanan sa d’aya ‘a Abuja ya dawo amma sam basu yi waya ba it’s like sun manta da juna
Assad ya sama abunda yake so yayi bincike sosai Alhaji kam hankalinsa ya kwanta dan Assad ya shaida masu su zasu yi wining dan ya saye iyayen yarinyar da kuma mutumin da aka yi abun ‘a gaban sa dan shi ne kawai yaga abunda ya faru!
Koda ya dawo Jalila bata kula sa ba bata ce dashi komai ba kallo ne kawai ya had’a su…yau satin su biyu da yin aure dai-dai Inno ta soma yi masa maganar k’arin aure ya nuna mata shi bai so ta ranste sai yayi aure in kuma ba haka ba duk abinda ya biyo baya shi ya saya wa kan sa
Kwance Jalila take bata jin dad’in jikinta da gudu ta tashi ta shiga toilet tayi amai, Inno ne ta shigo ganin Jalila tana yin amai yasa ta dafa k’irji tana salati magani ta d’auko ta kawo mata ta bata sai da ta tabbatar ta sha ta tafi dashi
Aure kam babu fashi dangi babu mai so amma Inno ta ranste sai anyi d’iyar wata aminiyarta ta had’a su aure cikin sati d’aya aka yi komai Assad kam bai ma san yarinyar ba dan ko gidan ma bai je ba sai da aka d’aura auren aka kawota dan k’anin Inno shine waliyyin Assad….Assad kam motar sa ko d’aya bai bayar ‘a d’auko amarya ba dangin Inno ne suka d’auko ta
Jalila tana zaune ‘a palo koda taje ganin Dr wani magani ya bata tana ta sha yanzu kam aman ya tsaya ko wanda Inno ta bata shima yayi mata aiki na gargajiya ne ta bar jin kasala da zazzab’i da amai…
Inno ta shigo palo tace
“Ke ki tashi ki gyara palon nan yau za’a kawo maki kishiya”
“Kishiya?” Tayi maganar cike da mamaki
“Eh”
” ‘A ina zata zauna?”
“Wanchan d’akin” ta nuna empty d’aki
Dariyar mugunta Jalila tayi tace
“Wlhy ba dai ‘a d’akin chan ba dan kayan ciki ubana ya saya man banga wanda ya isa ya saka wata k’atuwa ‘a d’akin chan ba”
“Toh fitsararriya mara kunya, wadda ba tayi gadon arzik’i ba” Inno tayi maganar ‘a fusace
“Ohhoo dai ko mai zaki fad’a sai dai ki fad’a amma key baran bayar ba”
“Shegiya ‘yar iska mijin ma naki ba son ki yake yi ba aka k’ak’aba masa ke”
“Dad’in abun bani na rok’esa ya aureni ba, ina da wanda suka fisa komai na amince na aure sa sabida na san darjar iyayena”
Jaraba Inno ta cigaba dayi Jalila kam ko ‘a jikinta dan earpiece ma ta saka tashi tayi ta shiga d’aki wayanta ne yayi k’ara
“Hello Mamina” Jalila ta fashe da kuka
“Jalilana mai ya same ki?” Mami tayi maganar hankali ‘a tashe
Sai da Jalila tayi kukan mai isanta ita ma Mami ma sai da tayi hawaye dan tasan irin zaman da suke yi da Inno, Mami ta mata nasiha ‘a kan zama da abokiyar zama sun jima sosai suna waya….Mami abun ya b’ata mata rai ‘ace 1month da yin auren ta za’ayi mata kishiya wannan cin mutuncin ai ya kai! Amma Mami bata nuna wa Jalila ba
Daddy ne shima ya kira ta ya kwantar mata da hankali bayan sun gama waya ya kira Assad
“Assalamu Alaikum Daddy”
“Wa’alaikumus salam Assad, ya gida?”
“Lafiya lau, Alhamdulillah”
“Dama na kira na maka Allah sa alkhairi na kuma tunatar da kai ‘a kan adalci…Jalila ‘yata ce duk duniya bani da kamanta na d’auketa na aura maka kullum cikin kewarta nake yi ina k’aunarta fiye da yadda nake k’aunar kaina amma in tayi laifi dole na nuna mata tayi ba dai- dai ba na hukunta ta ina so ka zama mai adalci ‘a tsakanin matan ka dan duk abinda kayi zaka haihu za’ayi wa ‘ya’yanka in ba’a yi masu ba kam jikokin ka za’ayi masu, ka zama mai adalci ‘a tsakanin iyalenka”
“Nagode Daddy in sha Allah zanyi adalci”
Kashe wayar Daddy yayi yace
“Amma ace biki wata d’aya zai k’ara aure! Kai namiji gaskiya bashi da tabbas nasan duk wannan kakar tasa ne ta k’ulla wannan abun”
“Kasan me? Hajiya Nafisa bata san da labarin ba sai d’azu take ji wlhy ta kirani tana bani hak’uri wlhy ita ma ranta ‘a b’ace yake…shi kansa Assad d’in ba son yarinyar yake yi ba Kakar sa ne ta k’ulla…Nafisa tace bata ma iya k’iranka dan nauyi take ji barata iya ba”
“Allah sarki ni dama nasan Nafisa babu ruwanta”…bai rufe baki ba Anty Nafisa ta turo masa text tana basa hak’uri kan auren da Assad ya k’ara bai nuna mata komai ba amma deep inside bai ji dad’in cin mutuncin da aka yi masa ba dan Inno k’iransa tayi tace bai isa ba tunda ya had’a Jalila da Assad indai tana raye barata tab’a bari Jalila taji dad’in zaman aure ba….Assad ma text ya turowa Daddy ya basa hak’uri ya shaida masa Inno ne ta had’a komai….
💐🎉
: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*Meena Parrot*
2⃣3⃣▶2⃣4⃣
Lokacin da aka kawo amarya Jalila ta riga da ta rufe d’ayan d’akin ta b’oye key d’in Inno rai ‘a b’ace ta shiga d’akin Jalila tace
“Ke Sadiya dan ubanki ubanwa yace ki rufe d’akin? Ko lokacin da Abdallah ya gina gidannan ubanki ya taimaka masa da naira d’aya?”
“A’ah ubana mai basa ko k’wandala ba amma kayan da suke cikin d’akin ubana ya saya su, sabida haka baran bayar da key ba in har kika ga na bari wata ta zauna toh an kwashe su”
Inno tayi ta zagin Jalila ganin Jalila ta mayar da ita mahaukaciya wak’a ma take yi…Inno ta fita ‘a zuciye tace ‘a shiga da ita d’akin Assad basu jima ba suka tafi amarya kam toilet ta shiga tayi wanka ta kwanta
Assad ne ya shigo Inno tace dashi
“Amarya na ciki” ta shiga d’akinta
Bai tanka ta ba ya wuce d’akin sa ganin mutum kwance ‘a gadon sa yasa yayi mamaki yace
“Yau mai ya hau kan Jalila haka!”
Sunanta ya k’ira ganin wata daban ta tashi yasa ya d’aure fuska yace
“Ke ba’a nuna maki d’akin ki ba?”
“Eh Hajiya tace na shigo nan”
Fita yayi yaje d’akin Inno yace da ita
“Inno ya zaki ce wacchan yarinyar ta shiga d’akina?”
“Eh nina ce, wacchan ‘yar iskar yarinyar ta rufe d’akin wai barata yadda ba wata ta kwanta akan gadonta”
Fita yayi bai ce komai ba, toilet ya shiga ganin ba yadda ya bar toilet d’in ba yasa yayi tsoki yasan yarinyar ta shiga ruwa da omo yasa ya wanke toilet d’in dettol sosai ya saka kana yayi wanka
Kaya ya chanja ya rufe toilet d’in da key ya d’auka system d’insa ya fito palo ya zauna ya soma aiki bayan ya gama ya kwanta ‘a palo kan kujera!
*Washe Gari*
Da asuba yayi wanka ya shirya daga masallaci bai dawo ba sai around 10am ya shigo lokacin Inno da Jalila suna drama
“Ke Jalila ki tashi ki d’ora mana abinci amarya tana jin yunwa”
“Abinci kuma Inno? Nima lokacin da nayi aurena ai da kai na nayi abinci” Ta cigaba da shan tea
“Jalila” ya k’ira sunanta
“Good Morning Sir”
“Morning Ma, had’a man tea”
“Tohm”
Cup ta d’auraye dan tana da tsafta sosai, ta had’a masa ta mik’a masa karb’a yayi ya soma sha bayan ya gama Inno tace
“Toh ai sai kasan yadda zaka yi da d’iyar mutane”
“Wake nan?”
“Khairat amarya”
“Toh Inno ai ke ya kamata ki tafi sai ta zauna d’akin”
“Ohhh korana kake ma yi? Babu wurin da zanje ina nan, ka tashi ma kaje ka duba kwanan amaryar ka”
Bai ce komai ba ya d’auko wayan sa ya k’ira ya fita….
D’akin Inno ta shiga ta kai mata Chips da soyayyen kwai da tea duk Inno ta soya
K’asa ta d’uka ta gaida Inno
“Khairat kiyi hak’uri kinji da halin mijin ki nan da wani satin zanje Sokoto wurin malami na za’ayi masa aiki dole ya soki ita kuma wacchan za’a saka masa tsanarta”
“Toh Hajiya nagode”
“In kin karya kizo d’akina kiyi wanka dan ta rufe bandakin sa”
“Toh Hajiya nagode Allah saka da alkhairi”
Sai da Inno ta fita Khairat taci abinci bayan ta gama ta tafi d’akin Inno tana jin nauyin Inno sosai da kuma kunyarta koda tayi wankan da k’yar ta fito da Inno ta kula fita tayi ta barta ta shirya dan kayan ma Inno ta d’auko mata su gown ne na material up shoulder k’irjinta duk ‘a waje gashi kayan ya d’ameta sosai hips d’inta kamar an d’ora mayafi ta yafa zata fita dan kunyar fita haka takeyi, cire mata mayafin Inno tayi tace ta fita ‘a haka ta bata wani turare mai mugun k’amshi ta shafe jikinta dashi d’aura mayafin tayi Inno tayi ta d’orata ‘a kan layi d’akin Assad ta koma ta zauna tana jin motsin sa zai shigo ta juya baya dan kar ya ganta…shigowa yayi drawer dake kusa da ita ya nufa ya bud’e ya d’auka wani abu ya juya zai fita yaji k’amshin turarenta juya wa yayi ya kalleta farinta ne kawai ya haska ta dan da black ne ita da anga muni farin ma daka gani kasan ba nata bane ba mai yayi aiki kawai dai tana da diri sosai Inno ne ta k’ira ta tashi zata fita ya k’are mata kallo bai san lokacin daya rik’e mata hannu ba ya cilla ta kan gado!….tuni suka zarce! Ta nuna masa shi ba kowa bane ba dan she’s an expert he really enjoy it…
Inno ne ta shigo ta gansu she was very happy ta fita tana habaici tana zagin Jalila
Jalila kam taji babu dad’i amma bata nuna mata ba wanka ta shiga tayi ta saka kimono da hula bayan ta kammala dafa abincin rana ta ijiye ‘a dinning ta fito d’akin Assad ta shiga yana zaune gefen gado da niker yayi gumi Khairat kuma tana kan gadon taja blanket…kallonsu tayi tace masa
“Ina son naje saloon”
“Okay” ya fad’a da k’yar
Fita tayi ta shiga d’aki toilet ta shiga tayi kuka harta gode Allah wanke fuskarta tayi ta d’auka mayafi ta fita dan wurin saloon d’in next to their house yake daga gidansu sai wurin saloon d’in shiga tayi ta zauna sun sha fira da mai wurin ita ma tazo ganin wurin kusan 2hours Jalila tayi ‘a wurin aka wanke mata kai da k’afa bayan an gama ta koma gida koda ta shiga palo babu kowa d’akinta ta shiga ta kwanta
“Khairat”
“Na’am”
“Thanks for making my day unforgettable”
Murmushi tayi ta sauk’e kanta k’asa…’a haka dai har suka soma saba wa dan duk time da yake inneed…she ‘ll never stop him yama soma manta wa da Jalila…sam yanzu bai sonta ko ganinta yayi sai ya b’ata rai abun duniya yayi mata yawa! Kuma ya hanata zuwa school
*NEXT WEEK*
“Ni zan je Sokoto sai Allah yayi man dawowa”
“Toh Allah ya kiyaye” Khairat ta d’uka k’asa…har mota suka rakata da Assad bayan ta tafi suka dawo ciki
Jalila kam tana zaune kan kujeran palo takaici ya isheta wayanta ne yayi k’ara ta d’auka Mami tayi wishing nata Happy birthday bayan sun gama Daddy ya k’irata yayi wishing nata sun jima suna yin waya bata fi 5mins da gama waya ba Mai gadi ya k’irata
“Hello Hajiya”
“Na’am”
“An kawo maki sak’o daga gidanku”
“Toh ka karb’a”
“Hajiya babban abu ne da dai kin fito”
“Okay am coming”
Ciki ta shiga ta d’auka Hijab ta fita harabar gidan taga Baba Amadu da wani mutumi
Murmushi tayi tace
“Baba Amadu an kwana lafiya?”
Murmushi yayi yace
“Alhamdulillah ‘yata” key ya mik’a mata yace “Gashi inji Alhaji” wata leda ya mik’a mata “wannan kuma Mami”…d’ayan mutumin ya mik’a mata farar leda yace
“Gashi wannan inji Maman Assad”
Baba Amadu ya nuna mata wata sabuwar mota fara sol tasha tint daka ganta kaga sabuwa rik’e baki tayi ta soma kukan farinciki tukwici ta basu da k’yar suka karb’a tayi parking motar ‘a parking space ta shiga ciki Ledar Mami ta bud’e taga sak’arne mai kyau da wrist watch ga tarin su chocolate, k’iransu waya tayi…ta masu godiya sosai da sosai…palo ta fito lokacin Assad zai fita Khairat ta rako sa
“Ya Assad Daddy ya bani car as a birthday gift, motan yana waje muje na nuna maka na Mami….bai kula ta ba sai da ta maimaita yace
“Malami naji motanma da in banda yawo mai zaki yi mtsww” Ya fita
Khairat kam kaman ta hadiya zuciya ta mutu ko Allah sa alkhairi bata mata ba…ranar suka raba girki..though kowa nasa yake yi babu mai cin na kowa amma ranar aikin su suna yiwa mijin su da mai gadi…Khairat kam bata iya abinci ba sai dai abinda ba’a rasawa Assad ma ranar girkinta ‘a restaurant yake sayen abinci dan bare iya cin jagwalgwalonta ba
Kwanan Inno hud’u ta dawo d’aki ta k’ira Khairat ta bata magunguna tayi mata bayani yadda zata yi amfani dasu….
Jalila na kwance ‘a d’aki tana zazzab’i ya rufe ta ganin throughout yau bata fito ba Assad ya shiga ganinta ‘a kwance ta rufa yasa yace
“Da ita Jalila mai yake damunki?”
“Zazzab’i”
“Mtsww ai sai ki tashi muje asibiti”
Da k’yar ta tashi ta saka hijab suka tafi
Dr ya gama ‘yan gwaje-gwajen sa yace
“Ammm is she your wife?”
“Wani abu?”
“Yes, dama tana d’auke da cikin 2weeks sai dai tayi using pills na zubar da ciki yanzu ya zube, kuma it’s like mahaifanta ya sama matsala ma”
“Innalillahi wa’inna’ilaihir raji’un! Jalila abinda kika yi man kenan? Kin kyauta wato har kinsan ki zubar da ciki kan ki kika yiwa keda Allah sauk’in ma ba kene kawai matana ba” Tashi yayi ya fita rai ‘a b’ace Jalila goge hawayenta tayi ta tashi ta fita ko kallon Assad bata yi ba ta fita ta hau adaidaita ta kaiwa police report ‘a kan magananin da wani Dr ya bata shima ‘a chan asibitin yake aiki ta koma gida police d’in suka ce zasu k’irata…tana shiga palo Assad ya wanketa da mari ya cilla mata maganin daya d’auko ‘a drawer yayi ta zaginta Inno ma zagin Jalila tayi sosai Khairat kam tana jikin Assad tana yiwa Jalila dariya tace
“Dear ka bar damuwa in dai Baby kake so ‘ll give you”
“Thanks my Love”
Ganin cin mutuncin ya isa yasa Jalila tace
“Duk wanda ya kuma cewa na zubar da ciki Allah ya isa kuma sai anyi mana shara’a”
“Kin zubar da baki zubar ba ai Dr bare yi maki k’arya ba kuma ‘a magani an gani ‘a d’akin ki” Khairat tayi maganar cike da rashin kunya
Jalila ta chakumo ta da k’yar Assad ya raba su dan Jalila k’arfi ne da ita da an bar su sai ta ji mata ciwo…Zaginta Assad ya cigaba dayi Jalila kam da tayi zuciya wayarsa ta d’auka ta bugata da k’asa ta fashe! Gashi Samsung ne dama screen d’in shine waya kusan 100+ ake gyaran screen d’in dan latest Sm ne…salati Khairat da Inno suka fara belt ya cire ta soma dukanta ta ko ina Inno tana k’ara mata sai da taji jiki sosai ya barta ya fita.. suka yi ta yi mata dariya bata ce dasu komai ba ta tashi ta shiga d’aki tasha kuka har ta gode Allah bacci mai nauyi ya d’auketa bayan ta tashi ta gasa jikinta
*WASHE GARI*
Koda ta tashi bata tanka kowa na gidan ba abinci ma bata yi ba ta fita, Police ya kirata ta samesu ‘a chan police station an kama Dr d’in an tambayesa waya sa ya bata maganin daya ga wuya yace Inno ce!
Tare suka tafi da Police da Jalila da Dr. lokacin Assad yana zaune ‘a palo Jalila ta shigo tace da Inno
“Ashe dama Inno tsanar da kika yi man ya kai haka?!”
“Uwar mai nayi maki?”
“Come in” Jalila tace dasu
Police da Dr….Dr ya kunna system ya dama akwai cctv camera ‘a office d’insa suka ga lokacin da Inno taje tace dashi ya bama Jalila maganin zubar da ciki inta zo asibitin duk abinda ta k’ulla suka gani….tace dasu “you can go” suka tafi
Assad yayi wa Inno kallon tuhuma yace
“Yanzu Inno ke kika ce Dr ya bata maganin zubar da ciki?! Ke kika kashe man ‘yata ko d’ana!” salati yayi…Inno ta fara kukan munafurci wai sharrin shaid’an ne, kallon Jalila yayi dan bai san ma taya zai soma bata hak’uri ba faahewa tayi da kuka ta shiga d’aki ta rufe kanta wuni tayi kuka ta kira ta fad’awa Mami…tuni hankalin Mami ya tashi tace karta fad’awa Daddy dan yau in ya sani rayuka zasu b’aci Mami tayi wa ‘yarta addu’a sosai
Yunwa ne ya fito da ita zata shiga kitchen ya Khairat ta bangajeta ta wuce jawota Jalila tayi tace
“Baki ga kin buge mutum ba?”
“Mtswwww aikin banza”
Jalila dama jiranta kawai takeyi dan dariyan da tayi mata na jiya ta k’ulu marinta Jalila tayi Khairat ta zube kasa tana ihu wai Khairat tayi mata dukan tsiya Inno tana ji tak’i fitowa dan tana jin tsoron had’uwa da Assad!
Assad ya fito ‘a gigice yana tambayarta abunda ya faru tayi k’ara wai Jalila ne tayi ta dukanta!
“Ke na gaji, baran iya ba ki tattara kayanki ki tafi gidan ku”
D’aki ta shiga ta tattara kayanta ta d’auka babban akwati duk abinda tasan zata buk’ata ta d’auka cikin daren ta tafi tayi driving zuwa gidan su har sun rufe mai gadi ya bud’e mata ta shiga dan 10 d’in dare!
Ciki ta shiga tana yin kuka da Daddy suka ci karo ya rik’eta yana tambayar ta lafiya?…ta fad’a masa Assad ne yace ta dawo gida ta kuma fad’a masa abinda Inno tayi mata na magani duk abinda ake yi mata ‘a gidan ta fad’a masa….shida Mami ransu ya b’aci ba kad’an ba
: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
2⃣5⃣▶2⃣6⃣
Bayan kwana biyu ta cigaba da zuwa school ta saka damuwa ‘a ranta ba kad’an ba dan yanzu karatun ma kawai tana yin sa ne dan yanzu ba wani ganewa take yi ba tana yi ne kawai ‘a wuce wurin, kullum cikin tunani take yi abun na damun iyayenta ma…sannu ‘a hankula tana shiga cikin friends d’inta yasa ta soma mantawa da Assad amma barata tab’a mantawa da cin mutuncin da yayi mata ba yanzu haka tayi deleting pictures d’insa kayan lefen da yayi mata kansu ‘a chan gidansa ta barsu duk kayan da take sakawa wanda iyayenta suka yi mata ne duk wani abu data san yana da dangantaka da Assad ta yar dan bata san abinda zai tuna mata da shi….yanzu ma tayi joining school na koyan snacks har ma da abinci yanzu kam ta zama expert ta soma sayar da birthday cake kuma ana saya
Zaune take ita da Fadila suna yin labari dan sun jima basu had’u ba kasancewa Fadila ‘a Maiduguri take tazo kawo wa aminiyarta Invitation d’in bikinta da anko ‘a gidansu ta kwana
“Jalila Model”
Murmushi tayi tace
“Na bar maki ai”
Fadila ma murmushi tayi tace
“Kinsan almost 4months nida Ammi bamu da waya”
“Haba ni dai kona ce lokacin da zanyi aure na k’ira ki not reachable number Ammi ma haka”
Kallon mamaki Fadila ta bita dashi tace
“K’awa dama kinyi aure? Shine koki fad’a man ai in da amana ko baki sameni ‘a waya ba zaki iya zuwa Maiduguri…nida na damu dake tunda ga chan nazo Kaduna”
Tab’e baki Jalila tayi tace
“Fadila ke kanki kin san baran tab’a mantawa dake ba, you mean alot to me…kin san kawai in aka aura maka wanda baka so zaki ga abubuwa basu tafiya dai-dai”
“Allah sarki aminiya, ya akayi haka ya faru?”
“Kin san brother d’in Daddy Uncle Hashim wanda ya rasu wai shi ya bar wasiyya…wlhy baki ga wanda aka aura man ba bai da mutunci ko kad’an tsanar da yayi man bai misaltuwa”…ta kwashe labari kaf ta bata
Gumin dole Fadila tayi ta bata hak’uri ta kuma fad’a mata kalamai masu dad’i had’e da cewa Innallaha ma’assabirin
Washe gari ta tafi…Jalila kam bata sha wahala ba wurin iyayenta suka barta taje bikin Fadila dama tana da Anty ‘a chan kuma Daddy ya san iyayen Fadila kwanan ta hud’u ta dawo Kaduna bayan sunyi hutu ta tafi Niger wurin k’anwar Daddy mai suna Hajja Fatuma
Assad kam harkan gabansa yake yi hankalinsa ‘a kwance
Khairat na zaune tayi crossing leg tana kallo sai karkad’a k’afa take yi Inno ta shigo
“Khairat ina abinci na?”
Tab’e baki tayi ta mata kallon banza tace
“Ban dafa dake ba”
“Iyeeee?” Inno ta rik’e baki
“Abinda kunnuwanki suka ji ne”
Kasa mostawa tayi, Khairat tayi tsoki ta tashi ta bar palon ta shiga d’aki ta kwanta
Tun bayan tafiyar Jalila komai ya chanja yanzu abinci kansa Khairat bata dafawa da Inno da maigadi kanta kaiwa take dafawa sai Assad dan yanzu ta d’an iya abinci…magani ya gama yin aiki yanzu kam Khairat ta mallake Assad ita da uwar ta mugun bin malamai sukeyi yanzu sai yadda Khairat tayi da Assad, rabon sa da Mommy har ya manta ko ‘a waya kud’in sa kam duk ta gama kwashewa kullum cikin kawo masa matsala take kuma bai isa yace bareyi ba! Inno kam taga rayuwa dan yanzu rashin kunya sosai Khairat take yi mata har zaginta tana yi…gidan duk ya k’azance ko ina datti sai tayi sati bata share gidan ba jikinta kawai take gyarawa…rashin kunyar ta ya kai in Inno tana zaune Khairat ta saka tsintsiya ta share mata k’afafuwa! zaman gidan ma ya gagare ta tuni ta had’a kaya zata koma Sokoto ta fito da k’ullin kayanta Khairat ta bita da kallon banza tace
“Keee malama kwashe man wannan tsumman kayan naki na share palona”
“Wai Khairat kin manta ko ni wace? Ko kin manta dangantaka na da maigidan? Ko kin manta da halaccin da nayi maki?”
Tsoki Khairat tayi tace
“Keeee dakata wannan kuma ba matsalana bane ba in zaki kwashe kayanki ki kwashe ko sai na bugeki”
“Iyeee! Wato ni kike fad’awa haka? Lallai ne duniya juyi-juyi” Inno tabi gefenta zata shiga cikin d’akin Assad dan suyi bankwana, Khairat ta tura ta saura kad’an ta fad’i kuka Inno ta soma tana kwashewa Khairat albarka!
Khairat ta balbaleta da masifa Inno taga she can’t take it ita ma ta cigaba da zaginta Khairat ta turata k’asa Inno ta tashi itama ta turata Khairat ta chakumeta suka fara kokuwa jin hayaniya yayi yawa yasa Assad ya fito tashin sa daga bacci kenan
“Khairat kina da hankali?”
“Bansani ba”
Jin salati ne yasa suka juya Mommy ne take shigowa tace
“Ke ki cikata”
“Baran cikata ba”
“Keee kinsan wace? She’s my Mom” Yayi mata tsawa
“It doesn’t concern me, wlhy inka b’ata man rai yau zan bar maka gidanka” tayi maganar ‘a fusace
Rik’ota yayi yana bata hak’uri Mommy tana k’iransa Khairat ta jasa suka shiga ciki haushi da takaici yasa ta tafi…Inno ma ta tafi Sokoto….dama ance duk tsuntsun daya ja ruwa shi ruwa ka doka
D’akin Jalilla Mommy ta duba taga ‘a rufe ta fita bakin gate tace da Driver d’inta ya tsaya zata yi wa Mai gadi magana
“Sannu”
“Yawwa barka Hajiya an fito”
“Eh, Jalila ta fita ko?”
“Ai Hajiya Jalila bata gidannan kusan 2months rabonta da gidannan wannan matar da mai gida ya aura tasa ya koreta”
“Kora!” ranta ya gama b’aci number Jalila ta k’ira ‘a kashe,
Cikin gidan ta koma ta balbale Assad tashi Khairat tayi ta shiga dashi d’aki ta rufe d’akin Mommy ta k’ulu ba kad’an ba, fita tayi gidansu Jalila tace da Driver d’inta ya kaita
Bayan sunyi parking ta shiga ciki ‘a babban palo ta same su an gyara ko ina tsaf sai k’amshi yake yi ga sanyin Ac, zama tayi suka gaisa lafiya lau Mommy tace
“Gida naje duba Jalila dan kusan 2months ko ‘a waya naji wani zance mara dad’i wai Abdallah yace da ita ta dawo gida wlhy ‘a bakin mai gadi nake ji dan Assad ko kallona bai yi ba wlhy”
Gyaran murya Daddy yayi yace
“Ayya, wlhy kam abunda ya faru kenan”
Mami kam shiru tayi dan ta kasa magana
Rantsewa Mommy tayi tace
“Ita wlhy bata ma sani ba…dan shi kansa Assad rabonta dashi tunda yayi aure! ta basu hak’uri sosai kuma ta fad’a masu abinda suka yi mata yau dan taga ba zancen b’oye-b’oye ‘a tsakanin su d’an uwa ya wuce wasa
Daddy ne yayi jugum.. yace
“Anya yarinyar nan bata yi masa magani ba? Dan abunnan ya wuce tunani ko mene ma Allah ya fita kuma in sha Allah with time asirinta zai tonu”
“In sha Allahu asirinta yana daf da fallasa, dan Allah kuyi hak’uri da cin mutuncin da Assad yayi wa Jalila”
Nan suka nuna mata babu komai dan bada saninta ba
“Yanzu ina Jalila? Nayi kewanta, i want to see her”
“Allah sarki Jalila tayi tafiya amma if she’s back zata zo ta gaidaki”
“Allah ya dawo da ita lafiya”
“Amin”
Hak’uri ta kuma basu dan ta damu sosai kana ta tafi
“Haba Jalila wai baraki bar saka damuwa ‘a ranki ba sai kinje kin kamu da ciwo haba Jalila”
Hawaye ta soma sai da tayi kuka mai isan ta tace
“Anty ina son na manta amma i can’t shiyasa aka ce is better to stay long than to marry wrong, ace 1month da 2week’s da aure na mijina ya sake ni am too young, am just 17 fa” kan cinyar Anty ta kwanta ta fashe da kuka da k’yar Anty ta rarrasheta
Key Anty ta d’auko suka fita suka sha iska suka d’an zaga garin kana suka dawo…’a hankula Jalila ta soma sabawa da ‘ya’yan Anty Fatuma kafin kace mai sun saba sai dai har yanzu akwai ciwon da take ji ‘a zuciyarta wanda yayi sanadiyar kwantar da ita asibiti ya haifar mata da ciwon zuciya! Yanzu haka magani take sha!
Bayan ta sama sauk’i aka yi bikin d’iyar Anty Jalila kam ita ne kan gaba gata ga amarya tuni pictures nata suka zaga all over media dan sai ka ranste amarya ne ita sunyi picture’s da ‘yan gidan…yayan amarya mai suna Hammad yasha kaftan da babbar riga da hula Jalila ma ta sha lace color d’in kusan same ne da, nasa coffee nata brown ta d’aura ashoke kaman amarya suka yi hoto tare in ka gansu sai ka ranste amare ne su sun dace sosai sai dai kuma kaman su yayi yawa kawai shi ya fita haske ‘a IG tayi posting ‘a page nata ta saka “Alhamdulillah best moment ever, the best feeling in the world is to be with someone who loves you deeply” tayi posting with heart emoji…ranar yayi masu dad’i sosai dan sunyi making fun ba kad’an ba
Zaune yake ‘a office ya kammala aiki dan har yau ank’i zama shara’ar da Assad zai kare d’an Alhaji tsawon 4months kenan,
Data ya kunna ya shiga IG dan ya rabu da shiga sosai yanzun ma dan he have nothing to do yasa ya shiga post d’in daya gani ne yasa ya dafe k’irji yace
“Kar kuce Jalila tayi aure!, no it can’t be barata iya auren wani ba beside me…amma kuma couples ne kawai za suyi dressing haka and abunda ta rubuta ya nuna ta auresa! Innalillahi wa’inna’ilahir raji’un” different pages sai posting hoton Jalila da Hammad suka yi ake yi ana cewa HML kishi ne ya cika ta ya kashe datar ya ijiye wayan cike da jin haushi ko time d’in tashi bai yi ba ya tashi ya fita zuciyarsa na yi masa k’una
Mota ya shiga da k’yar yayi driving zuwa gida ‘a kan kujerar palo ya kwanta bacci yayi gaba dashi, Khairat ta fito ta samesa yana yin bacci ruwan sanyi da zuba masa zubawar wulak’anci ‘a firgice ya tashi yana k’iran sunan Jalila sauran ruwan ya zuba masa duka ‘a jiki gashi cup ‘a cikie!
Harara ta watsa masa tace
“Taliya ya k’are ka kawo na bayar ‘a saya”
Cike da takaicin abinda tayi masa yace
“Khairat kinfi kowa sanin bani da kud’i”
“Tohhh uban mai zamu ci?”
“Ba akwai shinkafa ba?”
“Ban sani ba” tayi tsoki ta shiga ciki tun daga lokacin data ga kud’insa sunyi k’asa raini ya shiga tsakanin su sosai kuma haka zata ci bashi son ranta in anyi salary ta kwashe kud’in…kuma yanzu ‘yammata kala-kala suke shigowa gidan dan in Asaad ya tafi wurin aiki basu tafiya sai ya kusa dawowa su biyu kullum sai sunzo in yau wannan tazo gobe wannan tazo….yanzu ma abin yayi gaba ita ma kullum fita takeyi bata dawowa sai wurin 11, gashi business take yi sosai yanzu kam tayi kud’i dan tama fi Assad kud’i yanzu shikam ya rasa ina take samun kud’i haka zaka ji ta shiga meeting da wannan babban da wanchan babban! Yanzu ko mayafi bata yawo dashi ga shigar banza da take yi shi kam Assad bai iya yi mata magana dan da yayi mata zata balbale sa kuma sai ta juya masa baya kusan fin sati shiyasa yake bin ta ‘a hankula dan ta gama mallake sa…pills take sha na hana d’aukar ciki dan ta ranste barata haihu dashi ba barinma yanzu data ga ya tsiyace
💐💐💐💐💐💐
: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
Typing error? Don’t mind cox this page is not edited
2⃣7⃣▶2⃣8⃣
Zaune yake ya rasa abinda yake yi masa dad’i gashi gobe zai wuce Abuja za’ayi shara’ar kisan yaron da d’an Alhaji yayi, tashi Assad yayi ya fita ya saya abinci yaci bayan ya gama ya zaga gari kana ya dawo Khairat kam bata nan ita ne bata dawo ba sai 12 koda ya k’ira ta she didn’t pick
“Daga ina kike?”
“Yaushe muka fara haka da kai?”
“Khairat wato kin mayar dani dan iska ace yau Sunday ni ina gida ke kin fita sai 12 zaki dawo”
Tab’e baki tayi tace
“Sau nawa zan fad’a maka business nake yi?”
“Wane irin Business ne haka?”
“Wai yaushe kayi baki? Lallai ne wato har kana da bakin da zaka tambayeni toh saye da siyarwa nake yi”
“Ba haka bane ba amma ga duk namiji mai kishin iyalensa ya zama dole yayi tambaya”
“Toh tunda ka zama wawa baraka iya bani enough kud’i ba ya zama dole naje na nema” tayi maganar tana shiga d’aki ko ‘a jikinsa yau kam ta kai sa bango dan ya gaji da yawon da take yi
Ranar basu kula junan su ba washe gari da asuba ya tafi Abuja
Ya fito daga mota suka had’u da Alhaji murmushi Alhaji yayi yace
“Pls Brr.Assad kayi mana k’ok’ari”
Girgiza kai Assad yayi ya had’a girar sama da k’asa dan miskilanci nasa ya motsa brief case ya d’auko ya mik’awa Alhaji…Alhaji yace
“What is this? Ba kai na bama ba?”
“I don’t have to say alot, bani da lokacin b’ata lokaci am sorry to say Alhaji baran iya goyon bayan k’arya ba tunda nake ban tab’a ba kuma in sha Allah i’ll never…nasan zaka yi mamaki na karb’a da farko yanzu na dawo maka dashi it’s a trap kai ne mutum na farko dana tab’a playing and kai ne na k’arshe sorry” ya wuce ya bar wurin
Alhaji ran sa ya gama b’aci ‘a lokacin ya sa aka nemo masa wata ya biyata kud’i zata kare d’ansa!
Alhaji yanata mamaki yadda Assad yayi playing d’insa dama tun farko ba wai ya yarda da Assad zai goya masa baya ba….Assad ba kowa bane ba yasa ya fasa face wa’azin da Jalila tayi masa dama bai tab’a karb’an cin hanci ba sai ‘a kan Alhaji!…tun ranar ya kasa tab’a kud’in ko 1naira bai tab’a ba yadda aka bashi haka suke
K’arfe goma aka yi shara’ar bayan sun tashi sun gabatar da kansu kaman haka
“I am Barrister Abdallah Hashim Ali” d’ayar ta tashi ta gabar da kanta Barrister Khaleesat Hadi Hassan….tashi Assad ya buk’aci Alkali ya basa izini yayiwa wanda ake tuhuma tambayoyi..Alkali ya masa izini Assad ya matsa kusa da Kabir yayi masa tambayoyi kamar haka
“Kotu zata so taji sunanka”
“Sunana Kabir”
“Shekarunka nawa?”
“24”
“Mai dangantakar dake tsakaninka da wanda ake tuhuma ka kashe?”
“B…b….bbbb…ba komai”
“Kar kaji tsoro, kayiwa kotu bayani”
“Yana son yarinyar da nake so”
“Okay, amma mai yasa mutane suke tunanin kai ka kashe ta?”
“Nima ban sani ba”
“A’ah ka fad’awa kotu gaskiya”
“Suna jin haushi na sabida ubana d’an siyasa ne shi kuma nasa uban ba kowa bane”
“Sabida mai zasu ji haushin matsayin mahaifinka? “
Shiru Kabir yayi d’ayar matar ta tashi ta nema alkali ya bata dama
kusa dashi taje tace
“Malam Kabir ka fad’awa kotu duk abinda ka sani, ranar da abin ya faru ka tafi Cyprus ko ba haka ba?”
“Eh haka ne”
“Idan kotu ta bani dama zan so na gabatar da shaidu”
“Kotu ta baki dama”
Wasu ta k’ira suka zo gaban kotu suka shaidawa kotu ranar Kabir yana Cyprus har visa aka nunawa kotu…Alhaji yaga alaman zasu yi nasara sai dad’i yake ji
Tashi Assad yayi ya buk’aci kotu ta basa damar gabatar da nasa shaidun yace
“Muhammad Kalu”
Muhd ne ya fito Assad yace masa
“Muhammad zamu so ka fad’a mana abinda ka sani”
“Kabir da Musbahu basu shan inuwa d’aya kullum sai sunje fira wurin Fatima kuma sai sunyi fad’a kullum ni nake rabasu dan Fatima tafison Misbahu shi Kabir yana yi mata dolene though iyayenta sun fi son ta da Kabir, ranar da abun zai faru sunyi fad’a kacha-kacha Kabir da Misbahu ‘a kan idona Kabir ya luma masa wuk’a ganin mutane sun fara fitowa yasa ya gudu”
“Yayi, ko zaka iya fad’a mana mutanen da suka gani?”
“Eh dukkansu suna cikin kotunnan, akwai iyayen yarinyar da kuma Ibrahim, Faruk”
“Kotu tana da buk’atar ganin mahaifin Fatima”
Fitowa yayi Assad yace
“Ko zaka fad’awa kotu yadda abin ya faru?”
“A’ah ni ban sani ba kawai k’arya yake yi…ni banga komai ba”
“Malam Kamala gara ka fad’a gaskiya dan in kotu ta gano you are lying…zaka gane kuran ka”
“Ni babu abinda na gani”
“Yayi”
Mahaifiyar Fatima aka k’ira ita ma same abu tace bata sani ba…sauran mutum biyun suka shaidawa kotu da gaske ne…anso ‘a d’aga shara’ar amma Assad yayi k’ok’ari sosai har za’a tashi Fatima ta shigo tana yin kuka tace
“Kabir ne ya kashe man Misbahu Mama Baba bai kama ta ‘a saye ku da kud’i ba don kubi bayan k’arya”
Tashi suka yi suka ce eh haka ne Assad kam murna ya rufe sa at-least he won…mutane sai albarka suke saka masa koda aka tashi ran Alhaji ‘a b’ace ya harara Assad yace dashi
“Kaje zaka gani, u’ll regrets what you did”
Girgiza kai Assad yayi yace
“Zanga alkhairi in sha Allah” ya tafi
Driving yake yi amma duk jinsa yake yi kaman mara lafiya ya kusa shiga Kaduna wasu mutane suka harbe tayar motar…kwace wa motar tayi ya buga wani tree he had a trible accident da k’yar aka ciro sa cikin motar lokacin kaman bai yin numfashi jini ta ko ina ‘a jikin sa in kaga yadda motor d’in yayi damaged bara ka yi tunanin an fitar da mutum ba ba’a ma san wurin da za’a kaisa ba gefen titi aka ijiye sa ba’a jima ba motar asibiti yazo ya d’auke sa…emergency aka kai sa bullet d’in da aka harbesa aka cire masa kana aka soma yi masa d’inki dan yaji ciwo sosai ‘a jikin sa bayan an gama ne Dr.Safwan ya k’ira mahaifiyar Assad tuni ta rud’e duk laifin da Assad yayi mata ta manta ‘a rud’e ta tashi driver ya kawo ta asibiti kuka sosai tayi dan sai da aka janye ta
“Daddy nikam wane year ne kakana ya rasu?” Jalila ta tambaya Daddy
“Kai Jalila an dad’e ba kad’an ba lokacin ko aure banyi ba ya rasu i think i was 7 lokacin daya rasu, bayan rasuwan sa aka turo mu makarantar allo nida Hashim (mahaifin Assad) kuma kar kice mahaifinmu he’s poor…yana da kud’i dan ‘a zamanin sune masu kud’in garin mu…bayan ya rasu dangi suka saka mu ‘a gaba kowa ya tsanemu babu mai son mu gadon da aka bar mana ‘yan uwa suka cinye makarantar boko ma cire mu aka yi abinci kam sau biyu ake bamu ‘a rana shi ma kad’an mun sha wahala ba kad’an ba, muna shekara tara aka kawo mu Nigeria makarantar almajirai tunda suka tafi babu wanda ya kuma neman mu…wahalan rayuwa babu wanda bamu sha ba kinga munyi tallar goro, mun sayar da ruwa, mun yi achab’a, munyi kondastan mota, munyi carpenter, munyi gyaran mota, munyi gini, munyi gadi ‘a makarantu rayuwa fa babu wacce bamu gani ba ‘a haka da dad’i babu dad’i muke zuwa makaranta, abinci da tufafi ba’a magana dan kullum da k’yar muke samun gari kaya kam Kala biyu ne kullum su muke maimaitawa wlhy Jalila da zan fad’a maki irin wahalar da muka sha sai kinyi hawaye amma yanzu gashi ya zama labari shiyasa nake takura maku kuyi karatu shine babban gatan da zan baku…kinga yanzu da nayi karatu ga matsayin da Allah ya kaini shiyasa aka ce kaga mutum kawai baka san baiwar da Allah yayi masa ba kinga yanzu da Allah ya azurtamu ‘yan uwan da suka gujemu yanzu wai sune suke son mu, tsoron Allah da rik’o da gaskiya da neman halal shi ne kan gaba da juriya su suka kaimu ga wannan matsayin nida d’an uwana sai gashi Allah ya d’auka ransa…Jalila kinga Ibrahim da Nabila da ‘ya’yan Hashim baki da kamar su duk duniya” ya kalla Mami yace “Anty Sadiya Allah yayi maki albarka, tun bani da komai ta amince ta aureni though mahaifinta yana da kud’i ta amince ta aure ni lokacin ko gidan kai na bani da amma ta amince ta aureni lokacin ina aikin kondastan mota”
Murmushi tayi tace
“Amin Mijina”
Ajiyar zuciya tayi ta sauk’e numfashi tace
“Allah sarki swt Dad, Allah ya k’ara budi”
“Amin ‘yar Mami da Daddy”
Murmushi dukan su suka yi
Wayar Daddy ne yayi k’ara ganin Nafisa yasa ya d’aga yace
“Hajiya Nafisa”
“Na’am” ta amsa tana kuka
Salati yayi yace
“Lafiya?”
“Wlhy Assad ne aka harba kuma yayi accident”
“Innalillahi wa’inna’ilahir raj’iun, yanzu kuna wane asibitin?”
Ta fad’a masa cikin kuka kashe wayan yayi yace
“An harba Assad kuma yayi accident”
Jalila dafe k’irjinta tayi..da k’yar ta iya tashi ta d’auko Hijab suka tafi asibitin
Zuba masa ido Jalila tayi an saka mass oxygen gashi jikinsa duk anyi d’inki har yanzu bai farfad’o ba sun jima kana suka tafi Khairat kam tana chan yawon ta koda ‘a k’irata aka fad’a mata ko ‘a jikinta sai washe gari taje ta duba sa ko gaida Mommy bata yi ba ce mata kawai tayi sannu ta duba jikinsa ta fita dan tunda ya farfad’o jiya bai samu bacci ba sai yau da safe bacci ya d’auke sa tun asuba yau ma Daddy da Mami….Jalila kuma tana school dan tana da Exams…koda suka zo duba jikin sa yana yin bacci Daddy ‘a nan ya bar Mami sai 9d’in dare Daddy yazo d’aukanta Assad kam magana ma da k’yar yake yi dan ya bugu ba kad’an ba
: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
*Not edited*
2⃣9⃣▶3⃣0⃣
“Jalila how was the Exams?” Mami ta tambaye ta
Ajiyar zuciya tayi ta zauna k’asan carpet ta zubar da books d’in hannunta da Bag d’inta tace
“Wlhy Mami Exams d’in yau yayi wahala ba kad’an ba sai addu’a”
“Allah ya bada sa’a, Exams dama haka yake babu abinda yafi k’arfin add’ua”
“Mami mai aka dafa?”
“Macroni ne”
Food falsk d’in ta bud’e ta d’auka plate ta zuba abincin kad’an taci dan yunwa yaci ya cinyeta! Dan yau sun sha wahala kuma ita haka halinta yake in dai sunayin exams bata iya cin abinci ‘a school tashi tayi ta bar books d’in ta shiga d’aki tayi wanka…girgiza kai Mami ta d’auke books d’in ta d’ora su kan kujera dan Jalila she’s careless
Bayan ta fito wanka kaya ta saka ta fito palo ta zauna kusa da Mami
“Jalila d’azu Daddynki yace in kin dawo kije ki duba jikin Assad, gashi baki dawo da wuri ba”
Kalan tausayi tayi tace
“Ai dare yayi Mami yanzu 6:23 fa”
“Eh fah, nima ban jima da dawowa ba”
Kafin ta rufe baki Daddy ya shigo barka da dawowa suka yi masa kana ya zauna ya kalla Jalila yace
“Daddy’s pet how was your Exams?”
“Alhamdulillah”
“Daddy include me in your du’a, Exams yanzu wahala yake yi man”
“Allah bada sa’a dama final level yafi wahala keep on trying your best, read and pray”
“In sha Allah Daddy”
Kallonsa ya mayar ga Mami yace da ita
“Mami ashe kin dawo? nayi trying number ki network was awful, naje na duba jikin Assad he’s in poor health har yanzu bai gane mutane”
“Ai abun sai add’ua, jikin ma kaman is getting worst”
“Allah dai ya basa lafiya” Daddy yayi maganar ‘a sanyaye
“Ameen, kasan tunda abun ya faru sau d’aya matarsa taje ta duba sa abu har tsawon 1week”
“Allah yasa mu dace” yayi maganar ya gyara zama yace
“Jalila ki shirya anjima around 8pm zamu je mu duba jikin Assad tunda aka kwanatar dashi sau d’aya kika gansa ko?”
“Eh Daddy, toh” tashi tayi ta shiga d’aki dan ranta bai so ba ita ko sunan sa ma bata son taji sai dai ranar da suka je asibiti dubasa ya bata tausayi sosai amma yanzu kuma she don’t want to think of him anymore, yanzu ma ranta ya b’aci da Daddy yace ta shirya suje su gaida sa
8:00pm
Daddy yayi driving d’insu zuwa asibitin…suna shiga asibitin Jalila ta d’aure fuska koda suka shiga d’akin kanta na k’asa kusa da Anty Nafisa taje ta gaidata ta tambayeta mai jiki…Jalila kam ko kallon Inno bata yi ba ta tsaya, Safiyya ne ta shigo ganin Jalila yasa tayi murmushi suka gaisa dan ita ma jiya ta dawo daga school Uni Maid tana rik’e da wata yarinya kusa da Jalila yarinyar taje tana wasa da hannunta, murmushi Jalila tayi ta d’auke ta tace
“Baby what’s your name?”
“My name ishh Aman”
“Wow nice name”
Murmushi yarinyar tayi, Jalila ta kalla Safiyya tace
“Who’s Baby?”
“Babyn Ya Saeeda” (Babbar Yayar su)
“Ma sha Allah, where is she?”
“Taje gida ta dawo”
“Ayyah”
Sai 10 suka tafi
“Jalila mu tafi ko?”
“Toh”
Jalila ta kalla Aman Tack
“Baby zan tafi sauk’o ko?”
“A’ah ni zan biki” Yarinyar ta soma yin kuka
Da k’yar Aman ta sauk’a tana ta kuka Jalia ta dafata tace
“Baby gobe zanzo na tafi dake kinji?”
Da k’yar Aman ta hak’ura su Jalila suka tafi
2week’s later
Tun ranar Jalila bata kuma zuwa duba Assad ba sai yau ta shirya cikin black abaya ta yafa veil d’in suka tafi tare da Mami
Zaune kan gado yana cin abinci an fara samun improvement dan yanzu har fira ana yi dashi, abinci ne dai har yanzu bai fiya ci sosai ba kuma bai iya yin tafiya sai da chroches, su Mami ne suka shigo Jalila na gefenta ta rik’ewa Mami hannu yana ganinsu yaji fad’uwar gaba tuni wulak’ancin da yayi wa Jalila ya dawo masa ‘a kai…kunya ne ys rufe sa yayi k’asa da kansa
“Mami ina wuni?”
“Lafiya Assad, ya jikin? Naga jiki yayi kyau sosai”
“Alhamdulillah”
Had’a ido suka yi da Jalila ta d’auke kanta bayan Mami sun gama gaisawa da Mommy Jalila tace da ita
“Mommy ina wuni?”
“Lafiya lau, Jalila ya gida”
“Alhamdulillah”
“Ya school fa? Ance you guy’s are writing exams, all the best”
“Amin Mommy”
Inno ne ta shigo ganin su Mami ne yasa jikinta yayi sanyi duk sai taji babu dad’i
“Hajiya Sadiya ce”
D’ago kai Mami tayi tace
“Mama Ina wuni?”
“Lafiya qlau, ya iyali?”
“Lafiya lau”
Inno ne ta kalla Jalila tace
“Jalila babu gaisuwa?”
D’auke kanta Jalila tayi ta b’ata rai tace
“Ina wuni?”
“Lafiya lau”
Tashi Jalila tayi zata fita Mami tace
“Baby ina zuwa?”
“Mamina ana k’irana ‘a waya ne”
“Okay in kin gama let me know sai mu tafi”
“Toh” ta fita dama key d’in motar su is with her bud’e motar tayi ta shiga ta zauna tafi 30mins Mami ta k’irata
“Jalila har yanzu baki gama ba?”
“Mami na gama yanzu nake shirin k’iran ki”
“Okay, where are you?”
“Am in the car”
“Okay ina zuwa’
Mami bata jima ba ta fito tayi driving suka tafi
“Abdallah lafiya naga yanayinka ya chanja?” Inno ta tambaya
D’auke fuskar sa yayi bai tanka ta ba…tsoki tayi tace
“Kaji da bak’in halinka baka lafiya amma bak’in halinka baka bari ba”
B’ata rai yayi bai ce komai ba…Dr ya shigo yace da Assad
“Abdallah mun auna vp naka ya hau sosai gaskiya in dai kana so ka sama lafiya sai ka rage tunani”
Assad dai bai ce komai ba Dr yayi masa bayanin yadda zai sha magungunan nasa Dr na fita Inno tace
“Kai kam yaro da kai amma kana da hawan jini”
Ya gama k’uluwa wani irin kallo yayi mata yace
“Ai kene sanadiyyar hawan jinina”
Dafe k’irji tayi tace
“Ai dama nasan abinda zaka fad’a kenan wato baka tawakkali duk abinda ya sameka daga Allah ne”
“Eh na san wannan karatun amma kene sila”
“Ai sai kayi hak’uri”
“To in banyi hak’uri bama mai zanyi”
Mommy ne ta kallesa tace
“Haba Assad she’s your GrandMa fa”
‘A sanyaye Inno tace
“Ni wlhy kunyar Hajiya Sadiya nake ji ban san ma taya zan fara bata hak’uri ba amma ya zama dole na tara ku da Muhammad duk ‘a yafewq juna….Jalila nasan da k’yar ta yafe man dan kallon da tayi man d’azu ya bani tsoro” Inno tayi maganar ‘a sanyaye
Mommy kam girgiza kai tayi…
“Shege ubanwa ma yace kace Jalila ta tafi gidan su” Inno tayi masa d’akuwa
Hararar Inno yayi yace
“Da baki aura man wannan yarinyar ba da duk haka bai faru ba, ai laifin duk naki ne”
“Mtswww kayi man shiru naji da abinda ya dameni”
Inno tayi ta yin surutu Assad yayi banza da ita
*WASHE GARI*
Inno tazo gidan su Jalila ta bama Daddy da Mami hak’uri Jalila kam ba wai ta hak’ura ba, daga k’arshe ma tashi tayi ta shiga d’aki har Inno ta fita Jalila bata fito ba sai bayan 1hour Jalila ta fito lokacin Daddy na zaune ‘a palo yana cin abinci ganin Jalila ta fito yasa yayi murmushi yace
“Babyn Daddy”
“Na’am Daddy”
“Babyn Daddy ki manta da komai kinji?”
“Toh Daddy….dan ka saka baki shiyasa na hak’ura”
Murmushi yayi ya saka mata albarka
Kwance take yanzu ya gama shan magani yana jin bacci Khairat ta shigo ta sha ado ko Momi bata kalla ba ta tsaya ‘a kan Assad tana chewing gum
“Daga ina kike? Sai yau kika gadamar zuwa dubani?”
“Daga yawo nake kar kayi tunanin duba ka nazo yi” wayanta ne yayi k’ara ta d’auka
Bin ta da kallo yayi
“Hello ina zuwa”
Kashe wayar tayi tace
“Assad bani takardar saki”
“Saki!” Ya maimaita
Drip d’in da yake hannunsa ta cire da k’arfi shi kansa yaji zafi
“In ka cika kai d’an halal ne ka sakeki”
Wanketa da mari yayi
Mommy ne ta tashi dan hayaniya suka soma…Khairat tayi tw zaginsa Assad yace
“Na sakeki saki d’aya, kije duniya ne Allah yayi maki abinda kikayi kan…maciya amana kawai ba dai yawon iskanci kika saka ‘a gaba ba? Kije gaki ga duniya”
Tsoki tayi tana wak’a ta juya zata fita yace
“Na sakeki saki d’aya” making two!
Cigaba da tafiya tayi sai da ya bari taje bakin k’ofa yace
“Na sakeki saki d’aya, ya cika uku”
Dummm taji duk sai taji jikinta yayi sanyi dan bata tab’a tunanin zai yi mata saki uku ba…fita tayi gwiwa babu k’wari sai da taje wurin Alhaji ya k’ara mata k’arfafa mata gwiwa
Mommy tace
“Komai ya faru da bakayi mata saki uku ba”
Inno ta shigo taga hannunsa yana fitar da jini tace
“Abdallah ya akayi naga drip ‘a k’asa hannunka kuma jini?”
Takaici ne ya rufe sa dan he can’t talk Mommy ne ta fad’a mata abinda ya faru rik’e baki Inno tayi tace
“Gwara da kayi mata saki uku da ana yin dari da dari kayi wa ‘yar iskar mara tarbiya yarinyar da ko hannu aka saka mata ‘a baki barata ciza ba amma yanzu ta zama gogaggiyar ‘yar iska taje zata gani” ranar wuni Inno tayi tana yin mita mai sa Assad bai buge Khairat ba😂…shikam ko takanta bai bi ba yayi banza da ita
: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
*Wannan shafin naku ne babbar yaya, Aneesa Abubakar Rimi&Mamie Hamma*
3⃣1⃣▶3⃣2⃣
“Adda Nabeela nikam na maki wani tambaya?”
Ijiye wayan Nabeela tayi tace
“Ina jinki Jalila”
“Nikam wai ance bayan anyi aure babu sauran soyayya tsakanin mata da miji in yana k’iranki Dear zai dawo k’iranki ma with your real name?”
“Who said so? Kawai dai is not comparable da soyayyar ku before ki shiga kinga ‘a waje ke kike juya sa har da jan aji ma amma in an shiga babu zancen jan aji ko kad’an kuma shi zai juyaki, ai true love never dies…in kina yi masa abinda yake so kina yi masa ladabi da biyayya yi nayi bari na bari, kina kuma rik’e sirrin sa ai Alhmdlh…kinsan duk abinda aka ce ibadah dole sai ka had’a da hak’uri”
Murmushi Jalila tayi tace
” ‘A media nake gani abun sai yayi ta tayar man da hankali in kika ji tashin hankalin da suke fuskanta ‘a gidansu sai kin zubarwa wasu da hawaye”
Nabeela ta gyara zama tace
“Haka ne kowa da k’addarar sa, kinga shiyasa ‘a lamarin aure ake son auren miji mai addini wanda ya san menene aure, wani zaki ga yayi auren amma bai san addinin sa ba ko kad’an kawai anyi auren ne bai ma san menene auren ba..amma in da addinin komai zai zo da sauk’i tsoron Allah ma zai hanasa aikata wani abun ma matar sa”
Labari suka sha ranar sai wurin 3 Nabeela ta bar Kaduna sabida is not that far to Zaria
Yau Sunday babu kowa ‘a gida sai Jalila sarkin tsoro ta rufe k’ofan palo dana kitchen tana ta bacci kusan 10missed call aka yi mata sai ‘a na 11 d’in ta tashi d’aukan wayan tayi taga missed call na Mami
“Hello Mami naga missed call naki i was sleeping”
“Sarkin bacci dama zan fad’a maki har yanzu bamu gama ba, Mama Hafsatu tazo?”
“Bari naje na duba”
“Okay, inta zo kice tayi abinci ta kai asibiti, anjima kuma su Ibrahim zasu zo”
Dad’i Jalila taji dan tana ji da babban yayanta kaman yadda yake ji da ita
Ta shi tayi ta d’auka wayarta ta fita key ta d’auka ta bud’e k’ofan shiga kitchen ta cikin palo
“Mama Hafsatu ashe kin shigo, ina kwana”
“Lafiya lau, tun d’azu na shigo nasan kina bacci”
Hamma tayi tace
“Yanzu na tashi, Mami ta k’ira tace na fad’a maki ki kai abinci asibiti, anjima su Ya Ibrahim zasu zo”
“Toh, mai za’a dafa wa ‘yan asibitin?”
“Kawai kiyi masu something simple da baraki wahala ba, ni zanyi abincin rana dan Ya Ibrahim da Anty Sumayya zasu zo”
Murmushi Mama Hafsatu tayi tace
“Allah ya kawo su lafiya”
“Amin”
“Ki bari kawai zanyi”
“Toh shikenan” fita tayi ta koma d’aki tayi wanka ta shirya tsaf ta saka atamfa riga da skirt ta fito palo kallo ta kunna ta kai Zee tv da tana son Indian series ba kad’an ba
Sai 1 ta tashi taje tayi sallah ta dawo palo, chocolate ta d’auko ta sha son ranta dan tasan in Mami tana nan barata barta ta sha zak’i haka ba…ita in da zak’i toh babu maganar abinci shiyasa gashi kullum kib’a take yi
K’arar horn yasa ta tashi ta lek’a window ganin motar Ya Ibrahim yasa ta fita da murmushi ‘a fuskarsa tayi hogging Anty Sumayya Ya Ibrahim ya mik’a mata hannu suka gaisa ta karb’a Amal takwararta ‘a hannun ya Ibrahim suka shiga ciki, zama suka yi bayan sun gaisa ta k’ira Mama Hafsatu tazo suka gaisa ta kawo masu ruwa da drink kafin abincin ya k’arasa
Amal na hannun Jalila tana yi mata wasa Ya Ibrahim yace
“Jalila ya school?”
“Alhamdulillah” ta kalla Anty Sumayya tace
“Anty Sumayya ina Safina?” (Sister d’inta)
“Tana gida, ita ma kullum in muka had’u sai tace na gaidaki”
“Allah sarki, ai zan karb’a number ta”
“Garin nan naku zafi” Ya Ibrahim yayi maganar
Murmushi Jalila tayi tace
“Ya Ibrahim Kaduna ma ai babu zafi, yafi Abj sanyi”
“Hmmm” tashi yayi yace “bari na lek’a Uncle Mahmud” neighbour d’insu
“Toh” Sumayya ta tashi ta rak’a sa k’ofa kana ta dawo Jalila kam abin nema ya samu dan tana da son yara, sai wasa take yi wa Amal…bayan sun ci abinci sun huta Ya Ibrahim ya tashi dan har yanzu su Mami basu dawo ba ita da Daddy suka fita
Ya Ibrahim yace da Sumayya
“Beauty muje ko?” Kallon Jalila yayi yace da ita
“Babyn Daddy zaki je ko?”
“Toh Ya Ibrahim” mayafi ta d’auko suka fita asibitin suka je sallama suka yi suka shiga Amal na hannun Jalila
Mommy tace
” ‘Yammata zo” sauk’a tayi dan bata da k’iwa taje Mommy ta d’auke ta bata jima ba ta fara alaman zata sauk’a wasa tayi ta yi tana zaga d’akin lokacin Assad yana bacci taje tana tab’a masa fuska tashi yayi ya ganta, Jalila taje zata d’auko ta rik’e hannun Amal yayi yace
“Ki barta, d’ora man ita kan gado”
D’ora masa ita tayi tana rashin ji yana wasa da sumar kan sa…bayan sun gaisa da Ibrahim yace
“Amal baki jin magana, zonan”
“A’ah ‘a barta”
Sai fira take yi masa dan sak surutun Jalila babu abinda ta bari sun jima kana Jalila taje zata d’auketa ta fara kuka ita barata je ba sai da Ibrahim ya sa baki ta yadda Jalila ta d’auke ta suka tafi…har sun shiga mota Ya Ibrahim ya tuna da fruit d’in da suka sayawa Assad girgiza kai yayi yace
“Beauty kinga mun manta da fruits d’in ko, Baby pls d’auka ki kai”
Ranta bai so ba amma bata nuna masa ba ta d’auka ta shiga ciki ta jima ‘a bakin k’ofar sai da taji mosti alamar za’a fito ta murd’a k’ofar ta shiga ta bama Mommy ta fita
Mommy ta kalla Assad tace
“Nikam Assad mai zai hana ka mayar da matar ka?” Mommy tayi maganar cike da damuwa
Shiru yayi na 1min kana yace
“Mommy koda nace zan mayar da ita nasan wani war d’in zai faru dan wlhy baki ga kallon da Jalila take yi man ba nasan ta tsane ni”
“Kar ka sama damuwa inka warke ka sama sauk’i zanyi magana da iyayenta, yarinyar tana da hankali ga ladabi da biyayya”
Shiru yayi bai ce komai ba…dan ya tsana yaji ana yabon wani ba shi ba lol.
Suna zaune Ya Ibrahim da Daddy ‘a palon suna yin fira Ya Ibrahim yace
“Nikam Daddy wai Babyn ka barata koma gidan Assad ba?”
“Nima nayi wannan tunanin, so nake ya sama sauk’i sai muyi maganar”
“Gaskiya ya kamata dan k’aramar yarinya ace ta zama bazawara ai babu dad’i mutane kansu zasu sama abin fad’a kamata yayi ta koma cikin satinnan Daddy”
“Gobe zan wuce Lagos, kafin na wuce zamu tattauna da Hajiya Nafisa
‘A b’angaren Mami kuma suna palonta suna yin fira,
Da wuri Jalila ta tashi tayi wa su Ya Ibrahim breakfast dan da wuri zasu tafi…Jalila kam sai da tayi kuka dama kullum in yazo in zai tafi sai tayi hawaye dafata yayi yace
“Haba Lil sis in kina yin kuka nima ai sai kisa nayi kuka” Ya goge mata hawayen..kana suka tafi ta rik’e hannun Mami suka shiga ciki
“Kinga ga farar leda ‘a gefen gadona d’auko”
“Toh Mamina” tashi tayi ta d’auko ta mik’awa Mami..Mami tace
“Baby ai naki ne Ibrahim ya saya maki, ni kuma kinga sark’ar da Sumayya ta kawo man Ibrahim kuma ya kawo man lace biyu da atamfa uku, laa kinga na manta Sumayya ma ta baki cosmetics ledar na kan dressing mirror”
Murmurshi tayi ta bud’a ledar English wears ne masu kyau set shida…ta duba cosmetics d’in tayi murmushi waya ta d’auka ta k’irasa
“Ya Ibrahim”
“Babyn Daddy”
“Na’am ya hanya?”
“Alhamdhlillah”
“Naga kaya meyetti, Allah ya k’ara bud’i”
“Amin Lil sis”
“Bye”
“Okay bye”
Anty Sumayya ta k’ira tayi mata godiya bayan sun gama Mami tace
“Baby pls kije wurin Zainaba ki karb’o man jaka”
“Toh Mamina” tashi Jalila tayi ta d’auka hijab d’in Mami ta saka ta fita dan inda sabo Mami ta saba Hijab,Mayafi, Takalmi duk na Mami take saka wa kuma tana da nata….’a harabar gida taga Daddy da abokin sa wurin da suke zaune taje ta gaida abokin nasa Daddy yace
“Babyna ina zuwa?”
“Mami ta aikeni wurin Anty Zainaba”
” ‘A dawo lafiya”
“Amin Daddy na”
Ta fita ‘a palo ta sama Anty Zainaba tace
“Anty Zainaba ina wuni?”
“Lafiya lau, ya gida”
“Lafiya, Ya Maminki da Daddynki?”
“Sunanan lafiya”
Zama tayi Saleem yace
“Ke baki iya gaisuwa ba?”
“Hahhahaha, blacky blacky ka bar saka man baki”
“Tohhh tsohuwa”
Chapter suka sha kana ta shiga wurin Anty Sajida suks sha fira
“Nikam Alaji Muhammad da zaka amince da mun had’a Sadiya da d’ana aure” mutumin ya d’auka cup yayi sipping drink
Gyara zama Daddu yayi yace
“Tana da aure”
“Ahhhh haba! Allah sarki amma baka yi man adalci ba ace anyi bikin d’iyarmu banji ba”
“Wlhy lokacin ne i was running outta time, yaron wajen Hashim ta aura”
“Allah sarki, Allah basu zaman lafiya”
“Amin”
Fira suka cigaba dayi…haka dai kullum duk friend d’in Daddy da zai zo in yaga Jalila sai yace yana son had’asu aure da d’ansa!
“Babyn Daddy”
“Na’am Daddy”
“Kinji yau aka sallama Assad?”
“D’azu na k’ira Mommy ta fad’a man”
“Baby har yanzu kina son Assad?”
Shiru tayi ta sauk’e kanta k’asa Daddy ya cigaba da cewa
“Baby Jalila baran maki dole ba ‘a karo na biyu in kin amince toh in baki amince ba kar ki cuci kan ki, pls be sincere…ki fad’a man abinda yake cikin zuciyar ki”
“Daddy na amince zan koma”
“Kin tabbata”
“Eh” idonta yayi ja hawaye sun taru
“Allah yayi maki albarka in sha Allah baraki tab’a ganin duhu ‘a rayuwan ki ba”
“Amin Daddy”
“Toh ki shirya kayan ki anjima zai biyo ya d’auke ki”
“To”
Ta shi tayi ta shiga d’akinta tayi kuka mai isanta jin motsi yasa tayi sauri ta tashi ta shiga toilet tayi wanka…koda ta fito ta sama Mami tana had’a mata kayanta cikin akwati gefen gado ta zauna ta soma shafa mai
“Mami da kin bari zan had’a”
“A’ah babu komai”
Cigaba da shafa tayi Mami tace
“Kunyi magana da Daddynki ko?”
“Eh munyi” tana k’ok’arin hadiye kuka
“Allah yayi maki albarka”
“Amin”
Fita Mami tayi…bayan Jalila ta gama shafan kaya ta saka ta fito ta shiga d’akin Mami ta nufa dressing mirror ta soma duba turare kusan kala hud’u ta d’auka tace
“Mami na d’auka perfume, kin bani?”
“Toh Baby in ban baki ba wa zan bama ki d’auka mana”
“Nagode Mamina”
Murmushi Mami tayi Jalila ta fita ta had’a sauran kayan ‘a handbag nata, ta shiga d’akin Daddy shima yana shirin fita
“Daddy pls abu nake so”
“Toh Baby mai sunan abun?”
“Perfume” tayi maganar kalan tausayi
Murmushi yayi yace
“Babyn Daddy kenan, Allah sa akwai wanda kike so duba ki gani”
“Toh Daddy”
Dubawa tayi ta sama wanda take so babba ne sosai irin Arabian perfume ta d’auka tayi masa godiya ta b’oye
“Yanzu mutumiyar ka ta nunaman turaren ka ta d’auka” Mami tayi maganar tana shigowa
Murmushi yayi Mami tace
“Ai ni yanzu in dai naji Jalila zata zo toh b’oye turarena zanna yi dan Jalila da son turare take” tayi maganar tana yin dariya…murmushi Daddy yayi
*30mins later*
Assad ne zaune ‘a palo shida Daddy da Mami bayan sun gama gaisawa tashi Mami tayi ta shiga d’akin Jalila
“Baby ki fito Assad yazo, ki kai masa ruwa yana palon Daddy”
“Toh” ta amsa jiki ‘a sanyaye
Ta shi tayi ta shiga kitchen ta d’auka tray ta zuba ruwa da drink ta fito da k’yar take tafiya dan duk ji take yi kaman ba ita ba! Gashi gabanta sai fad’uwa yake yi sallama tayi ta shiga palon lokacin shi ne kawai ‘a palon kan center table ta ijiye tace
“Ina wuni?”
“Lafiya”
Ruwa ya zuba ‘a cup ya sha, kallonta yayi yace
“Mu tafi ko?”
“Toh” ta amsa ba tare data kallesa ba, fita tayi ta shiga d’akinta ta d’auko handbag d’inta da akwatinta suka fito da chroches taga yana tafiya dan ba’a kunce masa d’inkin k’afafuwansa ba kallo ta bisa dashi trolley d’in hannunta yasa hannu zai karb’a ya jaye boot ta bud’e ta saka su Mami da Daddy suka fito nan ma wani sabon kukan ta soma da k’yar tayi shiru suka tafi driver na gaba yana driving Assad da Jalila suna baya
Tunda suka shiga ko A bata ce ba idonta da hankalinta na window…titin ya kuje motan yayi shaking Jalila ta buge Assad yace
“Ouch!”
‘A tsorace ta kallesa bata ce dashi komai ba har suka isa, fitowa tayi ta d’auka trolleynta da handbag nata ta shiga gidan ko ina tsaf an gyara an share sai k’amshi yake yi dining kuma ga flask uku ne da plate spoon and so on ‘a ijiye, d’akin tayi sallama ta shiga kan gado ta fad’a tana yin hawaye jin motsi ‘a bayanta yasa ta juya….
: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
#Thanks a bunch for the love and care…comment, and support 1luv#
3⃣3⃣▶3⃣4⃣
Mama Hafsatu ne ta shigo tace
“Jalila ni zan wuce”
“Ashe kina nan”
“Eh nina gyara gidan, abinci na kan dining”
“Okay, thanks”
“Sai anjima” ta fita
Jalila duk taji duniyar yayi mata wani iri dan yanzu ta shiga wani rayuwa na daban ba irin na gidansu ba komai zai chanja, tashi tayi ta fito dining ta nufa ta zuba abinci ta koma d’aki ta zauna taci bayan ta gama ta fito da plate ta shiga kitchen ta wanke kana ta fito ‘a palo ta same sa ya zuba abinci yana k’ok’arin d’auka amma bai san ya zaiyi ba sabida chroches da yake amfani da, tausayi ya bata taje ta d’auka masa hanyar d’akin sa ta nufa yace
“Jalila iye man ‘a palo kawai”
Bata ce komai ba ta ijiye masa ta shiga d’akinta ta kwanta
Bayan ya gama tashi yayi ya shiga d’akin sa ya kwanta cike da tunani
*WASHE GARI*
Da wuri ta tashi ta share gidan though babu datti sai da ta share ta goge ko ina ta kunna turaren k’amshi wanka ta shiga bayan ta fito tayi shafa turaren Daddy dana Mami ta fesa k’amshin sai ya had’e, riga da jeans ta saka anyi mata kitso mai kyau k’anana ya zubo baya, ko hula bata saka ba ta fito ta shiga kitchen wani takarda taga an manna dubawa tayi taga time table ne ta abinci from monday to sunday breakfast, lunch and dinner tab’e baki tayi tace ta duba na yau abinda ta gani tayi bayan ta gama ta iba nata dama yau Saturday ana yin wani series TV ta kunna ta zauna ta jima kafin ta gama ci dan ta bama kallon full attention
Tana gani ya fito bata ce dashi komai ba shi ma bai ce da ita komai ba ya zauna flask ya bud’e ‘a zuciyarsa yace “lallai tayi abun arzik’i tunda har tayi abinda ta gani” zuba abincin yayi yaci bayan ya kammala cikin palon yazo yace da ita
“Anjima zanje asibiti kar kiyi abincin rana dani”
D’aga kanta tayi alamar toh, d’aki ya shiga yayi wanka bayan ya kammala ya fito zai tafi tace
“Zanje asibitin ina son naga Dr”
“Okay, muje” fita yayi ita kuma ta d’auko dogon hijab har k’asa ta fito, Driver yaja suka tafi Assad na gefe Jalila kuma tana baya ita d’aya wayanta ta d’auko ta kunna Data ta soma chatting
Ciki suka shiga Dr ya soma kwance masa bandage d’in k’afarsa aka soma yi masa dressing zafi sosai yake ji tun yana jurewa har ya soma rik’e hannun Dr yana rufe ido alamar zafi
“Dr kayi masa ‘a hankula man” Bata ma san lokacin data fad’a ba
Shi kansa Assad mamaki ne ya cika sa juyawa yayi ya kalleta ganin yana kallonta yasa ta juyar da fuskarta bayan an gama Dr yace
“Ciwon ma Alhmdlh ya kusa warkewa amma kuma Hajiya sai kin takura masa da shan magani dan bai son magani kinga kuma yanzu yadda yaji ciwon nan in bai shan magani wani cutan zai iya shigan sa”
Shiru tayi na 3secs kana tace
“Toh zan kula”
“Ammm tace bata da lafiya zaka dubata” Assad yayi maganar yana kallon Dr
“Okay, Hajiya mai yake damunki?”
Kallon Assad tayi taga shima ita yake kallo d’auke kanta tayi tace
“Ni Dr kawai nake son gani”
“Tabbb aikam babu wurin da zanje, if you can’t tell him now sai dai ki tashi mu tafi”
Shiru tayi bata ce komai ba
“Mu tafi?”
Tashi tayi ta fita wurin wata dan ita kunyansa take ji wurrin Dr ta mace taje bayan sun gaisa tace
“Dr dama i need your help”
“Okay, i can hear you”
“Dama 2months back wani Dr ya bani maganin zubar da ciki ba tare da sanina ba shine nake son ki dubani kiga in mahaifana ya sama matsala”
“Ke kam garin ya kika sha baki karanta ba?”
Jalila ta fad’a mata abinda ya faru
“Allah sarki, Allah kiyaye gaba”
“Amin”
Dubata aka yi bayan an gama Dr.Mommyn Irfan tace
“Mene tukuicina?” Tayi maganar tana yin murmushi
“Dr ki fara fad’a man dan nasan matsayina”
Gyara zaman glass d’inta tayi tace
“Alhamdulillah babu abinda ya sama mahaifan ki sai dai yaso ya shafa babyn da kike d’auke dashi yanzu zan d’oraki kan wasu magunguna”
Zaro ido Jalila tayi dan she’s speechless and totally outta word’s! Kafin kace mai? Ta soma hawayen farin ciki tace
“You mean am pregnant?”
“Yea, ga takardan ki duba babyn ki..you are 1months 3weeks pregnant”
Karb’a tayi ta duba tana murmushi cike da farinciki tace
“Dr. what do you want?”
Murmushi Mom Irfan tayi tace
“I want nothing but a pray”
Tashi Jalila tayi…tayi hopping Mom Irfan suka yi sallama ta fito…wayanta ne yayi k’ara
“Jalila kina ina? Tun d’azu muna cikin mota muna jiranki and av been calling you, u didn’t pick”
“Am on my way”
Kashe wayan yayi…ta samesu ‘a mota suka tafi
D’akinsa direct ya shiga binsa tayi bayan ya zauna ta mik’a masa takardar zama yayi ya duba kallon mamaki ya bita dashi yace
“Amma mai sa baki tsaya Dr ya dubaki ‘a gabana ba”
“Kunya nake ji”
“Kunya! Ba Dr.Haleem yace cikin ya zube ba?”
“Toh ni dai abinda aka bani kenan”
“Muje”
“Ina?”
“Wani asibitin”
Batayi musu ba tunda ta san tana da gaskiya ‘a mota ta samesa da kansa yayi driving dan karanbani ne dashi kallon yadda yake yiwa k’afar tayi alamar yana jin zafi tace
“Let me drive”
“Na fad’a maki baran iya ba?”
“Allah baka hak’uri” bata kuma cewa komai ba har suka isa aka dubata asibiti uku suka je amma same result aka basu…k’afan yana dan yi masa zafi yace da Jalila
“Pls kiyi driving k’afana na yi man zafi”
“Ai tun farko nace ka bari sabida taurin kai kak’i” tayi maganar ciki-ciki bata yi tunanin yaji ba yace
“Taurin kai ba ‘a wurin ki nayi gado”
bata ce komai ba ta shiga driving tayi suka je asibitin da Dr.Haleem yake aiki basu fita ba Assad ya k’irasa bayan ya fito suka gaisa da Assad Jalila kam ko kallonsa bata yi ba, Assad ya tambaye sa dalilin daya sa yace cikin Jalila ya zube bayan k’wararrun Doctors sun shaida masa cikinta bai zube ba sai dai maganin yaso affecting nata amma Allah ya taimaka Dr.Haleem ya fad’a masa Inno ne ta sa ya fad’a haka tsoki ‘a fusace Assad yace
“Amma ka bani kunya da kai za’a had’a baki ‘a cuceni Allah ya isa” ya rufe glass d’in motar Jalila taja motar da k’arfi ta tayar da k’ura ya b’atawa Dr.Haleem fararen kayansa
Suna shiga gida ta fita ko key d’in bata cire ba ta fita d’akinta ta shiga ta zube kan gado tana kuka
“Jalila mene na kuka kuma! I think the game the over ba? Yanzu lokaci ne da ya kamata ki gode Allah tunda babynki is in good health”
Tashi tayi ta shiga toilet ya bita da kallo dan ta chanja sosai kamar ba Jalilar daya sani ba mai shegen surutu da k’iriniya amma yanzu babu ko d’aya tashi yayi ya fita, sai da taji motsin rufe k’ofa ta fito kitchen ta shiga ta dafa abincin dare.. Dama ita in dai tana yin abinci bata had’asa da komai kamar chatting kallo duk batta yi ‘a kitchen take tsayawa har sai ta gama, bayan ta kammala abinci taci ta sha magani ta fito palo ta zauna sai wurin 11 ta tashi sai ‘a lokacin ta tuna bata ga fitowar Assad ba tun bayan dawowarsu, d’akinsa ta shiga tayi sallama fitila ‘a kashe…kunna fitilar tayi yana kwance amma ba bacci yake yi ba, k’arasawa tayi ciki ta zauna gefen gadon tace masa
“Naga baka ci abinci ba am certain baka sha maganin ka bama”
‘A gajiye yace
“I can’t eat, sai anjima”
“Maganin kuma fa?”
“Zan sha anjima”
Tashi tayi ta fita bata jima ba ta dawo da plate ‘a hannunta
Zama tayi ta mik’a masa
“Ka tashi kaci”
Babu musu ya zauna ya karb’a kad’an yaci, maganin ta ciro da bottle d’in ruwa ta mik’a masa ‘a zuciyarta tace “wai babba da kai magani ma sai an baka baka ji rashin lafiya bane” sai kuma tayi tunani dan gaban goshin Mommy ne komai yi masa takeyi dan tana ji dashi ba kad’an ba kasancewar shine kawai d’anta namiji ta riga ta sabar masa komai ita take yi masa
Tashi Jalila tayi tace
“Sai da safe”
“Allah ya kaimu”
“Amin” ta kashe masa wutar ta fita
*BAYAN SATI BIYU*
Haka rayuwa ya cigaba da kasancewa Jalila da Assad har yau basu saba da juna ba, kullum da wuri take tashi ta gyara gida tayi wanka ta kuma dafa abinci…kullum daga kwanciya sai kallo, gidan kullum shiru baka tab’a cewa da mutum ‘a gidan dan gaisuwa ne kawai yake had’a su sai kuma in zata tuna masa shan magani kaman yaro!
Har yau sun kasa sakin jiki da junansu dan ko ‘a palo suke zaune suna yin kallo babu mai yi wa kowa magana sai dai suyi ta satar kallon juna
“Jalila ki shirya muje mu gaida Mami dasu Mommy”
“Toh”
Tashi tayi ta shirya ‘a palo ta same sa yana saka bottle d’in hannu dan yanzu ya sama lafiya ya bar amfani da chroches, taimaka masa tayi ta saka masa ya danyi smiln yace
“Thanks”
“DM”
“I really don ger u”
“Toh don’t mention”
“Nace ki fad’a ne? Tun kafin ‘a haifake na sani” Yayi maganar in a play tone
Tab’e baki tayi suka fita waya ta k’ira Mami bayan sun gaisa tace
“Mami kina gida?”
“A’ah tare muka tafi Gombe da Daddynki”
“Laaaa na manta jiya kin fad’a man zaku je, kun isa lafiya?”
“Alhamdulillah, ya gida ina Assad?”
“Duk lafiya Mami, da zamu zo ne”
“Ayyah sai dai in mun dawo, ki gaida man Assad d’in”
“Toh Mami bye”
“Bye”
Jingina kanta tayi jikin seat d’in motar tace
“Mami bata nan”
“Okay”
Lokacin da suka shiga palo Mommy tana d’aki zama Jalila tayi, Assad kuma ya nufa hanyar d’akinta lokacin tana fitowa da alama yanzu ta idar da sallah dan ko hijab bata cire ba hogging juna suka yi…palon suka zo suka zauna kusa da ita ya zauna, Jalila tana zaune ‘a k’asa ta gaida Mommy…Mommy cike da murna tace
“Jalila ya gida?”
Kanta ‘a k’asa tace
“Lafiya lau”
Bayan sun gama gaisawa Assad ya gaida Mommy…tashi tayi ta shiga kitchen, Assad ya kalla Jalila yace
“Madam ki koma kan kujera”
D’agowa tayi ta kallesa bata ce komai ba
“Madam baki ji?”
“Nan is okay”
“Ahhh Jalila ki koma kan kujera mana” Mommy tayi maganar tana fitowa
Murmushi Jalila tayi tace
“A’ah Mommy nan yayi”
“Haba Jalila kamar bak’uwa”
Murmushi tayi ta tashi ta zauna Mommy ta zauna mai aikinta ta kawo masu abin sha dana ci
Ruwa ya d’auka ya sha yace
“Mommy kin san mai?”
“A’ah sai ka fad’a”
Kallon Jalila yayi yace
“Mommy Jalila tana..”
Minstininsa tayi ya kalla Jalila yayi murmushi yace
“Mun kusa samun k’aruwa ‘a gidan mu, she’s 2months pregnant”
Murmushi Mommy tayi ta masu fatan alkhairi Jalila kam kunya ya rufe ta, Assad ya fad’awa Mommy ashe Inno tace ace cikin ya zube!
Sai da Magrib suka tafi, koda suka shiga mota bata ce masa komai ba…kallonta yayi had’e da yin murmushi yace
“Mai kike kumbura fuska? Baki san masu kyau in suka b’ata rai basu yin kyau ba?”
“Ni ka barni” Tayi maganar kaman zata yi kuka
“Toh mai ciki” Yayi maganar yana kallon titi
“Uhm uhum ni bana so” ta soma kuka
“Lallai ‘yammata hawaye sunyi maki yawa”
Koda suka je gida bata yi masa magana ba ita tayi fushi d’aki ta wuce…kamar an jefota ta fito palo ta zauna kusa da Assad tace
“Ya Assad bari na nuna maka wani abu”
Kallonta yayi yace
“Surutu ya dawo kenan”
Turo baki tayi ta tashi tace
“Na manta mun b’ata”
: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
3⃣5⃣▶3⃣6⃣
Kallonta yayi ta k’asan ido yace
“Ai mun shirya”
Girgiza kai tayi tace
“Ni ka bar yi man magana”
Tashi yayi yace
“Tunda munyi fad’a shikenan nima na tafi wurin friend d’ina”
Rigarsa ta rik’e tace
“Ni baran zauna gida ni d’aya ba dare yayi”
“Toh sarkin tsoro sai ki tashi mu tafi amma daga chan zanje wurin girlfriend d’ina”
B’ata rai tayi ta tashi ta shiga d’aki ta buga k’ofan da k’arfi “hmm” yace ya fita zuwa wurin friend d’insa, parking yayi ya jira friend d’in nasa ya fito ‘a mota ya samesa
“D’an Audu how far?”
“Umaru Faruku”
“Ya garin?”
“Fine”
“Ina amarya fa?”
Tab’e baki yayi yace
“Sarkin fitina kenan tana gida”
“Ai dad’in auren yarinya kenan tayi ta maka shagwab’a”
Girgiza kai yayi yace
“Kai problem d’ina da kai kenan wallahi”
“Kodai problem d’ina da kai? Mutum sai son girma haba! Ya kamata kasan kayi aure fa duk wannan abun ka ijiye sa gefe ka kama matarka hannu bibiyu..that’s if you don’t want to loss her”
“Toh shege wa’azi zaka yi man”
Dafe kansa yayi yace
“Ai kaji matsalar ka”
“Kai ka sani”
“Ni tashi ka tafi matar ka na jiranka”
“Ohhh korana kakeyi?”
“Ai gaskiya ne”
“Fitar man ‘a mota”
“Banza koba kace na fita ba..zan tafi” Fita Umar yayi zai rufe k’ofar Assad yace
“Abokina sai da safe”
Umar bai ce komai ba ya tafi inda sabo sun saba dan kusan kullum in suka had’u sai sunyi fad’a!(Abotar kenan)
Jan motarsa yayi ya koma gida, ‘a palo ya sameta tana yin kallo zama yayi bai ce komai ba yana b’ata rai, kallonsa tayi tace
“Ya Assad namiji bak’i in ya d’aure fuska muni yake k’ara yi”
Dariya abin ya basa pillow ya cilla mata tana yin dariya tace
“Wai mai sa kake d’aure fuska? Frankly bai yi maka kyau”
Zuba mata ido yayi yace
“Jalilu kike ko Jalila”
“Ahhh ba Jalilu ba Jalaluddeen”
“Dan Allah kiyi shiru ban shirya yin surutu da tsohon daren nan ba”
“Hahhh, ina abokin naka?”
“Ohooo masa”
Dariya tayi hada hawaye ganin abun nata ba mai k’arewa bane ba yace
“In kin gama ki kawo man abinci” ya shiga d’aki
Tashi tayi ta had’a komai ‘a tray ta d’auka ta kai masa ‘a kan side drawer ta zauna ta kunna wak’a ‘a wayanta tana bi, 1spoon yayi ya kalleta yace
“Waya koya maki abinci?”
“Yayi dad’i?”
“A’ah”
D’aukan plate d’in tayi ta b’oye ‘a bayanta tace
“Bai yi dad’i ba ko toh ka k’oshi”
“I was kidding you fa”
“Toh sai kace you love me”
Kallon mamaki ya bita dashi ganin she’s nay joking yasa yace
“Toh ki fara fad’a”
“An fad’a maka ina son ka ne?”
“Nima an fad’a maki ina sonki ne?”
Murmushi tayi ta ijiye plate d’in tayi clapping hannunta ta zauna kusa dashi tace
“Ya Assad kasan mai?”
Girgiza kai yayi, tace
“Kaga ban tab’ayin soyayya ba sai mu fara daga yau ko? Dating zamu fara yi”
Dariya ta basa amma bai yi ba…shiru yayi tace masa
“Ya Assad kaji?”
“Anty Jalila naji” Dariya abun ya bata
“Yace toh shikenan lemme have my phone”
k’in mik’a masa tayi ta chanja sunanta daga Jalila zuwa Swthrt❤🔐 da love emoji ita ma chanja masa zuwa tayi daga Ya Assad zuwa Veryown❤🔐 ta basa wayan…tashi tayi ta fita tace dashi
“Good night”
“Allah ya kaimu”
“Amin” Ta fita
D’akinta ta shiga tayi wanka ta kwanta wayanta ta d’auka tayi dialling number Assad
“Hello Veryown good day”
“Swthrt kina lafiya?”
“Yes am fine and you?”
“Same”
“Dama i just call to say Hy”
“Thankiu swthrt, good night”
“Dream at me”
Murmushi yayi yace
“Baki da matsala”
Kashe wayan tayi tana yin dariya juyawar da zata yi taga Assad yayi folding hannunsa yace
“Madam you are no more my girl friend”
Dariya tayi tace
“Tabbb ai mai rabaki da kai sai Allah”
Murmushi yayi yaja mata k’ofa
Kwance yake ‘a d’akinsa yana tunanin shirmen Jalila yana murmushi shi d’aya yace “yanzu in ba yarinta ba mai na cewa muyi dating” ya cigaba da yin dariya zuciyarsa tace “toh ai kaima yaron ne tunda ka biyeta” kasa d’aure fuska yayi dan daya tuna sai yayi murmushi
Kwance yake yana yin bacci Jalila bata ji mostin fitar sa masallaci ba, bayan ta idar da sallah ta shiga d’akinsa torch d’in wayarta ta kunna ta haska dan d’akin duhu ‘a kwance ta gansa yana yin bacci gefensa ta zauna ta soma yi masa magana ‘a hankula cikin kunne ganin yak’i tashi ta soma yi masa tafiyar tsutsa ‘a k’afa cikin bacci ya tashi
“Boyfriend yau baka yin sallah ne?”
Zaro ido yayi yace
“OMG! what happened to me today”
Sauko da k’afan yayi k’asa ya kunna fitilar d’akin yana lumshe ido
“Boyfriend ka tashi mana”
Mik’a yayi ya tashi yayi alwala ya tafi masallaci, lokacin daya dawo ‘a palo ya same ta tana kallo, kallonta yayi yace
“Kayyihh! Jalila wai baki gajiya da kallo? Sai rana yayi kiyi ta yiwa mutane bacci…sai dare yayi ki hana mutane bacci”
Ido ta bisa da, kusa da ita yazo yayi kneeling yace da ita
“Hope my baby is in good health?”
Murmushi tayi dama k’aramar shirt ne ‘a jikinta d’aga shirt d’in yayi ya shafa cikin nata ya jima kana ya tashi ya shiga d’aki yayi wanka dan yau zai koma aiki
*7:00am*
Ya fito cikin shirin sa ya saka arsh Suit lokacin Jalila ta gama had’a breakfast an kai masa mota, d’akinta ya shiga lokacin tana yin bacci duk’awa yayi ya shafa cikinta ya kai 2mins kafin ya tashi kamar an mintsineta ta tashi ta ga zai fita
“Ya Assad morning”
“Morning”
“Wait lemme show you something” Tashi tayi ta samesa hannunsa d’aya ta rik’e tana kallon fuskarsa tace
“Tie d’inka ba dai-dai yake ba” gyara masa tayi tace “yawwa yayi kaganka kaman wani sabon ango”
Murmushi yayi yace
“Ai very soon zanje neman auren yarinya ‘yar 14year’s”
Turo baki tayi ‘a zuciye ta koma ciki ta kwanta murmushi yayi ya tafi
Bayan ta gama bacci sallah ne kawai yake tashinta sai 5 ta tashi ta kuma yin wanka ta dad’a gyara gidan kana ta shiga kitchen ta dafa abincin dare tuwon semo da miyar kub’ewa ta had’a komai ‘a dining kunun aya ta had’a ta zuba ‘a jug ta saka ‘a fridge, wayanta ne yayi k’ara ganin Assad ne yasa ta turo baki ta zauna
“Hello Girlfriend”
Turo baki tayi tace
“Ni mun b’ata”
“Haba Girlfriend mana”
“Uhum uhum”
“Ki fito waje ki tayani d’aukar abu”
“Toh” tashi tayi ta d’auka mayafi ta fesa turare ta fita ‘a mota ta same sa ‘a zaune bud’ewa tayi ta shiga tana kallon sa
“Girlfriend kinyi kyau”
Smiln tayi tace ina kayan?
Girgiza kai yayi yace
“Fira nazo, i mean zance ake k’iransa ba”
Wani irin kallon yayi mata jikinta yayi sanyi yace
“Girlfriend say something mana”
“Ka dawo daga wurin girlfriend d’inka zaka man dad’in baki”
“Haba mana, kin san kene kawai girly d’ina am sorry babe was kidding you”
“Uhum”
Leda ya mik’a mata yace
“Girly na gashi na saya maki nasan mai ciki da kwad’ayi”
Rufe face d’inta tayi alamar taji kunya, karb’a tayi suka fita ya rufe motar dafa mata kafad’a yayi suka shiga ciki, wanka yayi bayan ya fito ta zuba masa abinci kallonta yayi yace
“An fad’a maki zan iya cinye wannan abincin?”
“Zaka iya mana, kaci mana” tayi maganar tana cin shawarma…kallon cikinta tayi tace
“Ya Allah wannan babbyn nawa yana saka ni naci abinci da yawa” tayi maganar kaman zata yi kuka
Tab’e baki yayi yace
“Ba wani Babyna kene dai mai cin”
Turo baki tayi tace
“Dama ba sona kakeyi ba”
“Eh” ya cigaba da cin abinci
Kuka ta soma yi ‘a tunaninsa ma wasa takeyi dan ta saba, bayan ya gama wayansa ya d’auka zai tashi yaga tana yin hawaye kusa da ita ya matsa hannunsa ya d’ora kan fuskanta ya shafa gashinta yace
“Girlfriend am sorry kinji? Kin hak’ura?”
Cigaba tayi da kuka, hanky ya d’auko ya goge mata hawaye ya rungumeta yana buga mata baya yace
“Sorry kinji?”
Ajiyar zuciya tayi tace
“Na hak’ura”
“Yawwa my girl ko kefa”
Tashi muje ki huta”
“Ni ban gaji ba”
“To muje”
Hannu ya rik’e mata ta cigaba da yin kuka, kallonta yayi yace
“Jalila mene kuma?”
“Ni gashina zafi baran iya kuncewa ba”
“Muje na tayaki”
Kibiya da cumb ta d’auko ‘a kan cinyarsa ta kwanta yace
“Jalila to ya zanyi maki ‘a haka?”
“Ni haka nake so”
“To ai shikenan” kibiya ya d’auka ya soma kunce mata kitson tsaf ya kunce mata cumb ya d’auka zai taje ta soma hawaye tace
“Zan taje”
“A’ah ni zanyi maki”
“Ni zanyi”
Hannunta ya buge yace
“Bana son gardama” hawaye ta soma bai bi ta kanta ba ya taje mata ya shafa mata mai, tashi tayi tana matsar k’walla b’ata rai yayi yace
“Ni tashi ki bani wuri, komai naki kuka ‘a haka zaki zama Mom!”
Tashi tayi ta shiga d’aki tana hawaye…ji tayi an rungumeta ta baya k’amshin turarensa ne ya daki hancinta, juyowa tayi ta rik’e wuyansa da duka hannunta biyu goge mata hawaye yayi yace
“Girlfriend ban san mesa kuka bai yi man wahala ba, pls ki bari”
“Toh na bari” sakin sa tayi ya juya zai fita ta hau bayansa tana yin dariya
Da k’yar ya samu ta sauk’a zama yayi ta kwanta kan cinyarsa, yatsunta ya rik’e yace
“Girlfriend haka kike tara farce!”
Shiru tayi tana kallonsa abun yanke yatsu ya d’auka ya yanke mata tas…..!
*🧕🏼BABY GEH🧕🏼*
: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
*Idan baki girmama mijinki ba, Alama ne da ke nuni da cewa baki ga mahaifiyar ki tana girmama mahaifinki ba*
3⃣7⃣▶3⃣8⃣
Kwance take ‘a kan gado shikam har yayi wanka yana shirin fita yana d’aura agogo ya kalleta yace
“Ashe kin tashi”
Murmushi tayi tace
“Sai ka dawo zaka yi breakfast ko?”
“Eh, baran jima ba”
Wayanta ne yayi k’ara tab’e baki tayi tace
“Who’s on earth calling me this early morning”
Kallonta yayi yace
“Kin tambaye ni”
Ganin bata san number ba kaman barata yi picking ba sai kuma ta d’auka tayi shiru
“Hello Jalila”
“Na’am, kina lafiya?”
“Fine ya gida?”
“Wlhy fine”
“Nasan baki gane mai magana ba?”
“Haka fa”
“Amina Jabir Matawalle Gombe”
“Laaaa Meena JB! Where have you been all this long?”
“Wlhy muna Ibadan kusan 5year’s da dawowarmu”
“Allah sarki, ina kika sama number na?”
“Fauziyya Ali Baba ta bani number ki”
“Allah sarki! I missed you fa”
“Same here, guess what? Ina Kd gobe zamu wuce zan shigo gidanki anjima”
“Really! Amma nayi murna wlhy can’t wait to see you”
Bayan ta gama wayar kallon Assad tayi tace
“Ya Assad baka wuce ba”
Taje kansa yayi ya ijiye cumb d’in kallonta yayi yace
“Yanzu dai zan wuce”
Tashi tayi ta rak’a sa k’ofa, dak’i ta shiga tayi wanka bayan ta shirya kitchen ta shiga ta had’a masu breakfast
*11:25am*
Ya dawo gida dama wasu file ya kai welcoming nasa tayi tace
“Boyfriend ka dawo!”
“Eh, hope breakfast is ready?”
“Yp, muje”
“Am damn tired just bring it here”
“Toh” kayan breakfast d’in ta had’a ta kai ta ijiye ta zuba masa ‘a plate suka ci tare, bayan sun gama kwashe kayan tayi ta kai kitchen ta soma wankewa shigowa yayi ya karb’a sponge d’in hannunta kallonsa tayi cike da shagwab’a tace
“Ya Assad ka bani mana”
“Ni zan wanke” yayi irin magananta
“O’ooo ni zan wanke”
“Tohm shikenan in kina da k’arfi sai ki karb’a”
Zageye kitchen d’in suka yi ta yi sai dai ta hak’ura ta bar sa, wanke plate d’in yayi ita kuma ta d’auraye bayan sun gama ‘a d’aki suka shiga tana gyara wardrobe kusa da ita ya zauna yana taya ta gyarawa tana basa labari
Wayanta ne yayi k’ara
“Hello Meena”
“Na’am, tun d’azu nazo ina ta knocking shiru”
“Okay, ina zuwa”
Kallon Assad tayi tace
“Ya Assad friend d’in nawa tazo”
“Okay”
Dankwali ta d’aura ta fita ta bud’e k’ofar Amina ta shigo hogging juna suka yi kana suka zauna bayan sun gaisa Jalila ta kawo mata abin sha sharp-sharp ta dafa taliya da vegetable sauce ta kawo mata
D’aki ta shiga ya sha kaftan zai fita yana fesa turare kallon sa tayi tace
“Ya Assad ina zuwa haka?”
Ijiye turaren yayi ya d’auka key d’in motar sa yace
“Zanje na gaida Mami daga chan zan wuce wurin Mommy”
“Okay ka gaida su”
“Zasu ji”
Rik’e mata hannu yayi suka fito shi yama manta da tayi bak’uwa gaidasa Amina tayi batare daya kalleta ba yace
“Lafiya” ya fita Jalila ta rak’a sa ta dawo
Zama tayi Amina ta kalleta tace
“Amma d’an uwanki ne ko? Dan naga you guy’s look alike kawai shi bai da haske”
“He’s my cousin”
“Ayya, ai naji kaman ance auren had’i ne ko?”
Murmushi Jalila tayi Amina tace
“Nikam ina wani friend d’inki d’an sarkin Niamey?”
“Wama ya san masa”
“Iye! Nifa i thought shi zaki aura”
“Kin san matar mutum k’abarinsa kema kinsan ni ban tab’a yin soyayya ba though ance babu aboki namiji at the end zai furta yana sonki amma ni ban basu fuska friendship ne kawai”
Tab’e baki Amina tayi tace
“Eh haka ne, amma ya akayi kika aura wannan dan naji labarin ba shahararren mai kud’i bane ba”
Rik’e baki Jalila tayi ta kasa yin magana
Amina tace
“Nayi tunanin zanga mijinki irin mugun don haka kuma mai irin shegen kyau amma sai na gansa dai-dai, kuma naji ance kamar ma’aikacin gov’t ne bayan haka babu wani abu da yake yi, kuma ya kamata ace gidan da kike yafi haka had’uwa ace da irin pool garden haka…ya kamata ace yafi gidanku kyau nesa ba kusa ba”
Gyara zama Jalila tayi tace
“Ai shi so babu ruwan sa da kyau ko muk’ami ke kanki kin san ni namiji fari bai burgeni and maganar kud’i da kikeyi Assad yafi man kowa ina son sa fiye da yadda nake son kai na…bari kiji zama attajiri bawai yana nufin yafi komai ba wani zaki ga yana da bala’in kud’i amma sam bai da lokacin iyalinsa ya kamata ki sani kud’i basu bane kwanciyar hankali ba burina kullum mijina ya ciyar dani halal ya tufatar dani halal…ina mamakin ‘yammatan yanzu suce su sai mai kud’i zasu aura shiyasa auren yanzu bai yin lasting tunda soyayyar ba dan Allah akeyi ba kawai anayi ne sabida kud’i, kyau, muk’ami…’yammatan yanzu basu damu da Halal ba su ko Haram ne in dai da kud’i shikenan, Alhamdulillah mijina yana tufatar dani halal ya ciyar dani halal, ya shayar dani halal ko sau d’aya ban tab’a raina arzik’in mijina ba dan Allah tashi ki barman gida…ai banga wanda ya isa yazo har gidana ba ya zagar man mijina ba’a haifesa ba” hanya ta nuna mata alamar ta fita ganin zatayi yi magana yasa ta tashi ta turata sai da ta kai ta har k’ofa kana ta juyo zata shiga taji an rik’e mata hannu, mari zata kai taji an rik’e hannun taga Assad ne duk ‘a tunaninta Amina ne, hogging d’insa tayi shi ma yayi hogging d’inta back tana hawaye
“Jalila kiyi shiru” Zama suka yi yana rungume da ita yace
“In kina yin kuka kan ki zai yi ciwo ki bari kinji?”
“Toh” ajiyar zuciya tayi kallonta yayi yace
“Jalila inna tambayeki wani abu zaki fad’a man gaskiya?”
“I promise”
“Kina sona?”
Kallonsa tayi idon ta cikin nasa for 1mins kana tayi k’asa da idonta tace
“I do love you”
“Really?”
Ta d’aga masa kai
“Thankiu i love you too, Jalila tun kina k’arama nake sonki sai dai ban tab’a furta maki ko nuna maki ba sakamakon halinki…sai dai yanzu Jalilana ta chanja sosai ba kamar da ba…Jalila ina sonki fiye da tunanin ki, i promise you my life, my love infact my everything”
Hawaye ta soma tace
“You are such a darling” ta kwanta kan jikin sa tana yin hawaye
Hannunta ya rik’e yace
“Jalila naji duk abinda ya faru cox i forget to carry my phone na dawo zan shigo naji duk abinda ya faru thankiu very much Jalila yau na tabbata kina sona nayi alk’awarin in sha Allah baran tab’a saka ki kuka ba in sha Allahu”
Murmushi tayi ta lumshe idanunta tace
“Ya Assad kayi alk’awarin kula dani tskani da Allah?” Ta tambayesa tana zubar da hawaye
Shafa fuskarta yayi yace
“In sha Allah Jalila zan kula dake”
“Ya Assad abinda yasa na tambayeki sabida ina ganin halin bak’in ciki da mutane suke shiga bayan sunyi aure, shiyasa aka ce kar kasa ran soyayyar da kayi da namiji shi zakayi ‘a cikin gida dan mostly maza da anyi aure suke chanjawa wani ma baki isa ya zauna yayi fira dake ba koda he’s free sai dai ya d’auka wayarsa! Wallahi halin mazan yanzu yana bani tsoro” ta fashe da kuka
Rarrashinta ya soma yi yace
“Jalila kar ki manta ko wane namiji da irin nasa halin kuma kullum in kinyi add’ua ki rok’a Allah ya baki zaman lafiya da mijin ki kuma ki rok’a Allah ya had’a kanki da mijinki”
“In sha Allah, Ya Assad akwai wata neighbour d’inmu sunyi soyayya for almost 5year’s har ya kai su ga aure 1week kawai suka yi na jin dad’in aure amma tunda ga nan mijinta ya chanja sam bai kula ta daya ganta ma sai yake bone face, bai da time d’inta sam gaisuwa kawai yake had’a su dan sai yayi 2week’s bai yi mata magana ba ko palo ta samesa tayi joining dinsa wlhy fad’a zai hauta da ya tashi ya bata wuri sam basu shan inuwa d’aya ko fa bai fita aiki ba yana gida bata isa ya zauna yayi fira da ita ba wlhy inka ga wahalar da take sha sai ka zubar mata da hawaye…dare ne kawai yake had’a su shima daya gama zai k’ara gaba imagine auren soyayya fa! Wlhy yarinyar kar ka ce wai ‘yar iska ne ita wlhy ko kad’an dan duk unguwar mu babu kamilar mace kamar ta mutuncinta har gidan auren su ta kai masa..amma da yake namiji ba d’an goyo bane ba ya juya mata baya, 12months suka yi ya saketa da tsohon ciki, wlhy lokacin har tsoron aure na fara shiyasa da aka ce za’ayi man aure na tayar da fitina sabida ina tsoron fad’awa irin halin yarinyar nan dan yanzu mostly aure da anyi an rabu gidan aure babu dad’i ko kad’an wurin daya kamata ace ka sama nutsuwa chan ne ma wurin tashin hankali! Ai zamanin nan bai yi ba, iyayenmu they wasn’t like that shiyasa har yanzu suna tare da mazan su kuma suna samun kwanciyar hankali”
Shi kan sa yarinyar ta basa tausayi yace
“Jalila wlhy ni kai na halin wasu mazan na bani haushi, if you are not prepared to spend time with your wife why did you get married? If you don’t want to talk to her correctly why did you marry her and waste her life? Why did you take someones child? You would have said so from the beginning…wlhy duk abinda mutum yayi he ‘ll account for it here after kuma duk abinda kayiwa d’an wani toh wlhy kai ma sai anyi wa naka d’an ko jikan ka…in alkhairi ka shuka zai dawo maka in sharri nema zai dawo maka”
Jalila bata tab’a tunanin haka Assad ma yake da sani ba sai yau
*Wlhy mazan yanzu sai addu’a zaku sha soyayya ‘a waje kaman baraku iya yin 1mins ba tare da juna ba, amma bayan aure wani namijin ko kallo baki ishe sa ba wata ma first week d’in da aka kaita ne kawai taje jin dad’in aure amma bayan lokacin babu sauran soyayya koda d’igo ne! Wata ita da kwanciyar hankali ‘a gidan aurenta har ‘a bada, wani mijin baki isa ya zauna yayi fira dake ba komai kika yi sai ya kushe kuma ke kina iya k’ok’arinki ki faranta masa amma shi ko sau d’aya bare faranta maki ba, mutanen waje yana wasa da dariya dasu sai ya shigo gida ya bone fuska haba haba! Bafa baiwa aka kawo maka ba, duk cutarwar da kayi wa matar ka zai dawo maka Allah zai iya jarabtar ka da d’a ko ‘ya fitinanne…wlhy maza kuji tsoron Allah akwai hisabi, danka aureta bawai yana nufin ka cutar da ita ba..kuma haka yana faruwa da yawa sabida k’aranchin ilimin addin, Allah yasa mu dace*
*Allah ya bamu mazaje na gari wanda zasu somu har bayan rayuwarmu, masu aure kuma Allah ya k’ara d’ankon soyayya wanda kuma suke cikin matsala Allah ya kawo masu mafita Amin*
*🧕🏼UMMEETA🧕🏼*
🌌: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
*Jama’a ina kuke? Duk wanda bai karanta littafin Billyn Abdul CIKI DA GASKIYA an bar sa ‘a baya dan littafi wollah ya tsaru ba kad’an ba…kar ku bari ‘a baku labari*
4⃣0⃣
Wurin Umar yaje suka gaisa dan ko cikin gidan bai shiga ba ‘a cikin mota suka zauna
“Man ya garin?”
“Normal”
“Wai lafiyan ka? Naganka duk kayi wani iri” Umar yayi maganar yana kallon aminin nasa
Cire space d’in fuskar sa yayi yace
“Aboki na wlhy kwana biyunnan bana jin dad’in garin”
“Ko muje mu duba Dr?”
“No, bama wannan ba Ibrahim brother Jalila yazo man da wani magana”
“Ina jinka”
“Wai yana so na dawo Companyn sa da aiki ni kuma ina ganin kaman hakan zai jawo raini”
Dafe kai Umar yayi yace
“Ohhhhnii Umar! Yanzu aikin shine raini? Wlhy Assad girman kai babu wurin da zai kai ka”
“Umar kafi kowa sanin bana son raini, duk abinda zai sa ayi man gori wani rana bana so ko kad’an kaga yanzu abin Allah kyauta zamu iya samun sab’ani da Jalila tunda duk mutum ajazini ba fata ba amma kasan zata iya man gori yayanta ma kaga raini zai iya shiga tsakanin mu tunda taga ina aiki ‘a k’ark’ashin yayanta, amma what’s your view?”
“Assad gaskiya da nine zan sauk’e girman kai na karb’a aikin nan, Assad na tabbata zaka ji dad’in aiki da Ibrahim Khaleel sabida mutum ne adali haka kaima zai ji dad’in aiki da kai sabida rik’on amana, and batun raini babu shi har gida aka zo aka gayyaceka kuma kar ka manta kai kanka ka shaida man Jalila bata wulak’anta d’an Adam ko man talauchin ka barata ji k’yank’yamin ka ba, komai tayi maka barata tab’a goranta maka ba sabida bata tashi taga anayi ‘a gidansu ba”
Robar ruwa ya bud’e yasha yace
“Haka ne shikenan zan fad’a masa na amince”
“Yawwa ko kai fa, amma mai Mommy tace?”
“Mommy kasan bata da matsala”
Dukan Umar ya kai masa yana dariya yace
“Saraki ai ne mai matsalar ai”
“Hahahh, bari na wuce”
“Ahhhh lallai ne dole ka wuce wato yanzu sam baka shigowa ka gaida Umma”
Rik’e baki Assad yayi yace
“Tsakanin ka ga Allah yaushe rabona da zuwa?”
“Shege haka zaka fad’a yanzu ai kayi aure ka bar zuwa shan miyar tsohuwa”
Duka Assad ya kai masa ya kauce, fitowa suka yi suka shiga ciki k’asan carpet Assad ya zauna Umar ya kallesa yace
“Su o’o kaman da gaske”
Buge masa k’afa Assad yayi yace
“Shege baraka tab’a chanjawa ba”…
“Ahhh maraba, wa nake gani kaman Abdullahi?”
Murmushi Assad yayi yace
“Umma ina wuni?”
“Lafiya lau Abdullahi, Ya Amarya?”
K’asa yayi da kansa Umar ya tab’o sa yace
“Kana ji ana cewa ya Amarya? Ba sai kace lafiyarta klau ba?”
Dak’uwa Umma tayi masa tana murmushi tace
“Sai aka fad’a maka shi irin kane? Maras kunya kawai”
Dariya Umar yayi yace
“Allah yaja da ran tsohuwa mai ran k’arfe”
“Kaga tsohuwa ‘a gidanku ba dai ni ba”
“Tsohuwas matar Audullahi ta kusa sauk’a fa”
“Wane kuma Audullahi Umar ba dai jan magana ba yanzu wannan tsohuwar ce zata haihu”
Dariya yayi yace
“Kunji tsufar ko bafa matar Baffa ba Assad fa”
“Ahhh haba? Allah ya sauketa lafiya”
“Amin”
“Tuzurun kawai”
“Nifa Umma ba tuzuru bane ba na kusa angon cewa”
“Mara kunya”
Tashi Assad yayi Umar ya rak’a sa mota
“Toh ni zan wuce”
“Toh my regards to Amarya”
“Zata ji, yaushe rabonka da gidana? Ya kama ta gobe ka shigo mana yawon juma’a ko zaka sama 10 naira”
“Hahhhhhh wlhy Audu kaga wurin kwanana”
“Umaru na nawa kuma”
Sallama suka yi Assad ya tafi gida sai da ya tsaya ya saya Grilled chicken mayo&Gherkin sandwic….. Guava ya gani ya tsaya ya saya
Zaune take ta mik’e k’afa dan yau ta tashi ciwon k’afa dan kusan 3months da suka wuce take fama da ciwo, bayan Assad ya fita kasa tashi tayi wayanta ne yayi ringing ganin Anty Ramla ne ke k’ira yasa ta d’auka tace
“Assalamu Alaikum”
“Wa’alaikums salam Jalila ya nauyin jikin?”
“Alhamdulillah Anty Ramla, yasu Nuwair?”
“All fine, ya maigidan naki”
“Lafiya lau”
“Ki gaida sa tunda shi bai k’irana”
“Anty Ramla wayansa ya sama matsala ne amma naga jiya ya saya k’aramar waya”
“Tohm ki gaidasa”
“Zaiji”
Sallama suka yi ta kashe wayan dan Anty Ramla tana son wanda ya damu da ita sabida Jalila akwai zumunchi tana yawan k’iran y’an uwa da abokan arzik’i su gaisa tana da zumunchi
Sallama yayi ya shigo wurin daya barta d’azu nan ya same ta, ledar Guava ya ijiye mata ‘a gefenta da sauran abun daya saya mata…Guava d’aya ta d’auka zata kai baki ya karb’a yace
“Dirty Babe, baki wanke ba”
Jingina kanta tayi jikin kujera ta dafa cikin ta tace
“Baran iya tashi ba”
D’auka yayi ya wanke ya kawo mata, wayarta da ke wak’ar *MOTIGBANA* ya d’auka ya kashe yace
“Koman dad’in kid’a shiru ya fisa dama karatun Qur’ani kika saka da yafi ni kar ma ki haifa man mawak’a ache duk wani latest update na music kin sani kuma kin iya haba! Think twice”
Shiru tayi bata ce komai ba ta soma cin Guava tace
“Anty Ramla na gaishe ki”
“Tazo ne?”
“Nope muyi waya ne, tace baka k’iranta na mata k’arya wayan ka ya lalace day before yesterday ya saya wani”
Lumshe ido yayi ya jingina kansa jikin kujera yace
“Allah yayi maki albarka”
“Amin, Amma pls kana k’iranta time to time kuna gaisawa Anty Ramla tana da zumunchi”
“Toh zage ni wato ni bani da zumunchi ko?”
“Ba haka bane ba kawai dai naga duk duniya mutum bai da kamar ‘yan uwa”
“Allah ma yasa ‘yan uwa ne”
“Allah huci zuciyarka”
“Amin”
Ganin shirun yayi yawa yasa yace
“Ki gama mu fita exercise ki zaga gidannan”
Sauk’e numfashi tayi tace
“Dear baran iya ba”
“Ohhh aikam dole ne”
“K’afufuwa na sunyi man nauyi”
“Ai sai kiyi sai fa mun fita”
Murmushi kawai tayi dan ita bata da damuwa ga hak’uri Allah ya bata shi kuma Assad bai da hak’uri ko kad’an dama Allah bai fiya had’a duka ba, suna yawan fad’a sai dai they can’t live without each other in d’aya yana cikin damuwa to d’ayan ma zai kasance cikin damuwa…amma kamar Tom and Jerry suke in dai suna wuri sai sunyi fad’a kuma suna yi zasu shirya😂, dan inka shiga tsakanin su kai ne da jin kunya
“Yawwa Ya Ibrahim ya bani sak’o pls ka amince masa kuyi aiki tare”
Ransa ne ya b’ace amma dannewa yayi ‘a zuciyarsa yace “wato mutumin nan talla ma yake yi dani” ‘a fili kuma cewa yayi
“I’ll think about it”
“Pls Dear”
“Amma fa gaskiya ina son aikina bana jin zan iya bari”
“Ya Assad aikinku akwai hatsari sosai pls ka amincewa Ya Ibrahim”
Shiru yayi bai kuma cewa komai ba dan bai tunanin zai aiki under yayan matarsa dan yana gani kamar raini zai shiga
Bayan sun gama fad’an cewa dole sai taje exercise ita kuma tace barata je ba, share juna suka yi suka k’urawa TV ido bayan hankalin su sam bai kan kallon, time to time suna satar kallon junan su
Tashi yayi ya shiga kitchen 2 plate ya d’auka d’aya ya saka Grilled chicken the other one kuma Gherkin Sandwich sai kuma empty plate da spoon da knife sandwich ya yanka ya saka ‘a plate d’in da fork ya d’auko ya matsa kusa da ita
“Haaa” yace da ita
K’in bud’e baki tayi ta fara matsar kwalla
“Haba Baby bud’e bakin mana, haba Jalilan Abdul”
Ya mata chakulkula tayi murmushi ta bud’e bakin bata ci sosai ba kazar kam taci ba kad’an ba sai da ya gama bata ya soma yi ta tayar masa da rigima dole ita zata basa haka suka yi ta yin drama duk ta b’ata masa fuska
Taimaka mata yayi ta tashi ta shiga d’aki amai ya soma tashi mata da gudu ta shiga toilet tana amai Assad ya shigo bayan ta gama wanke mata baki yayi ya watsa wa zink Omo mai k’amshi sabida kar yayi k’arni, d’aki ya taimaka mata suka fito ta kwanta dan samun hutu
Muryar Inno suka tsinto ‘a palo da take ta sallama tashi yayi ya same ta ‘a palo zama yayi Inno tace
“Ohhh ni ina nan ina ta rafka sallama kuna chan kuna shan soyayyya, ohni ‘ya’yan zamani”
Tab’e baki yayi yace
” ‘Yar tsohuwa yaushe kika zo garin?”
“D’azu nazo, Ina Jalilan?”
“Tana d’aki k’afanta ciwo yake yi mata”
“Ohni kai mata na shan wahala”
Tashi yayi suka shiga d’akin Jalila, da k’yar ta tashi ta zauna tana murmushi suka gaisa
“Ya nauyin jikin?”
“Alhamdulillah”
“Allah ya sauk’eki lafiya”
Dukan su suka amsa da Amin
Numfashinta ya soma fita sama-sama ganin alamun haihuwa ne yasa Inno tace Assad ya d’auko key d’in motar sa…akayi rashin sa’a an tafi da motar wanki harma dana Jalila yana wurin wanke ganin yadda tace fitar da numfashi tayi gumi sosai Assad ya mugun tausaya mata waya ya k’ira Dr ba’a fi 10mins ba tazo ita da Nurse ganin haihuwa yazo gadan-gadan Dr ta buk’aci Assad ya fita sam yace bare fita ba dan bare iya barin Jalila cikin wannan mayuwacin halin ba, hannunsa Jalila ta rik’e duk taji masa ciwo tafi 1hour ana abu d’aya addu’a yayi ta yi mata da addu’ar da ake bama masu ciki cikin ikon Allah ta haifa d’anta santalele amma ta sha wahala kafin ‘a bata ruwan add’uar duk ta fita hayyacinta
Bayan ta sauk’a lafiya aka shirya Baby tsaf aka mik’awa Assad fuskarsa d’auke da murna maras misaltuwa kud’i da bai san adadinsu ba ya mik’awa Dr ‘a matsayin tukiuci godiya suka yi masa suka tafi Inno kam murna baki har baka mai aikin gidan Mama Hafsatu tayi murna sosai ta had’awa Jalila ruwa mai zafi sosai suka shiga ta gasata Jalila cike da kunyar Mama Hafsa sauk’in ma tun gida sun saba in tana ganinta tana rage mata kewar iyayenta tunda tun tana k’arama ‘a gidansu take yin aiki har yanzu
Assad kam d’akin sa ya shiga da Babbyn ya kashe Ac ya zauna gefen gado yayi wa Babyn addu’a wayarsa ya d’auko ya k’ira Mommy
“Hello Mommy”
“Assad ya gida? Ya jikin Jalila?”
“Komai lafiya Mommy kin sama jika from your only son”
“Alhamdulillah, kai am very happy Allah ya raya pls send his pic”
“Mommy baraki zo ba? Inno ma tana nan”
Murmushi Mommy tayi tace
“Ka manta bana gari? Amma In sha Allah gobe da wuri zan dawo sabida Baby”
Bayan sun gama hoto ya shiga d’aukan Baby suna kama sosai da Assad komai nasa ne kaman yayi kaki ya tofar sabida tsananin kama hasken ne kawai na Jalila dan duk hasken Jalila Babyn ya fita nesa ba kusa ba…..
Bayan sun gama Inno ta shigo d’akin Assad tace
“Oga ai sai ka kawosa ‘a shayar dashi”
Mik’a mata shi yayi dama kuka yake yi, D’akin Jalila ya shiga lokacin tayi wanka ta saka kaya hogging d’inta yayi yace
“Congrats Baby, Allah yayi maku akbarka”
Murmushi tayi itama tayi hogging d’insa bag…sun kai 2mins ‘a haka kafin ya sake ta Inno ta shigo tana murmushi tana yi wa Baby wasa tace
“Wai wane suna za’a saka masa?”
Kafe Inno yayi da ido yace
“Hajiya Inno sunanki za’a saka masa”
D’akuwa tayi masa tana yin dariya peck yayi wa Jalila ‘a kumatu ya fita Inno ta rufe idonta dan abun ya girma idonta😂…Jalila kam duk kunya ya kama ta
Toh ko sunan wa za’a saka wa Baby ohoo?!
Kun san dai Assad da tsattsauran ra’ayin Gashi tunda Inno ta sama labarin Jalila nada ciki tace in dai namiji aka haifa ‘a saka sunan mahaifinta…In kuma ta mace ta bar masa zab’i
Toh mai zai faru?
Ga sunan Mahaifinsa
Ga kuma na d’an uwan sa babban yayansu wanda ya rasu shekaru da suka shud’e
*Ya Allah ka biya mana buk’atunmu na alkhairi, Allah ka k’ara d’aga darjar musulunchi, Ya Allah ka kare musulmi ‘a ko ina yake daga sharrin masu sharri, Allah yasa muyi kyakkyawan k’arshe, Allah kasa mu cika da kyau da imani, Ya Allah kasa kalamar mu na k’arshe ya zama kalmar shahada, Wanda kuma suka rigamu gidan gaskiya Allah ka kyautata makwanccin su Allah ka haskaka k’abarin su ‘Amin’*
: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
*Rashin hak’uri da hangen na wani shi yake kai ka ga halaka*
4⃣1⃣
Sallamar Safiyya ne ya katse su ta shigo d’akin da gudu dan ita ma hankalin da sauk’i lol, hogging d’in Jalila tayi cike da murna sai da suka zauna ta kula da Assad murmushi tayi tace
“Ya Assad ina wuni?”
“Ohhh sai yanzu kika ganni”
Murmushi tayi ta mik’a hannu zata d’auka Baby Assad yace
“Wai mai sa baki da nutsuwa? Sai kin karya masa hannu”
“Kai Ya Assad”
Tsoki yayi ya fita Inno tana dariya tace
“Kai ni banga ranar da mutuminnan zai chanja ba, mutum sai bak’in hali nan gaba ma babu wanda zaka gani ‘a gidanka kawai zaka ci albarkacin matarka tana da mutunci da son mutane”
Jalila kam bata ce komai ba dan tasan halin Inno ba mutunci ne da ita ba, sallama tayi masu ta tafi Safiyya ta kalla Babyn tace
“Jalila Babyn nan hasken ki ya d’auko amma fuskarsa na Ya Assad ne”
Murmushi Jalila tayi tace
“Aikam carbon copy nasa ne”
Fira sosai suka sha Safiyya ta shiga Kitchen ta dafa ruwan zafi ta saka ‘a flask ta kai wa Jalila
“Safiyya pls ki kaiwa Ya Assad Flask d’in da Cup with spoon”
“Toh” Tashi tayi ta d’auko cup da spoon ‘a kitchen ta kai masa yana zaune kan gefen gado yana yin aiki ‘a system
“Ya Assad gashi”
D’agowa yayi ya kalla abinda ta ijiye masa ya dalla mata harara yace
“Tunda aka haifeki kin tab’a ganin na sha tea? Mumu kawai”
Sai ‘a lokacin ma ta tuna tace
“Ya Assad na manta ne”
“Allah yasa baki manta karatu i pray one day kar ki manta how to spell your name”
Murmushi tayi ta d’auka madara da milo ta bar masa coffee zata fita yace
“Gidan uwar wa zaki fita da Sugar?”
Dawowa tayi ta ijiye tace
“Wlhy mantawa nayi”
Tsoki yayi ya soma had’awa har ta kai k’ofa yace
“Auta zonan”
Ranta bai soba dan tasan Assad da saka aiki ba kad’an ba shiyasa ma sai ta jima bata zo ba, dawowa tayi ya nuna mata wuri alamar ta zauna
“Kin fitar da miji?”
Gabanta ne ya fad’i cike da tsoro tace
“E…h…Eh….a’ah”
“Wane irin iskanci ne zaki ce dani Eh Aah wato rainin har ya kai haka?”
“Kayi hak’uri”
“Tashi ki bani wuri”
Tashi tayi ta fita ta fad’awa Jalila yadda sukayi da Assad kallonta Jalila tayi tace
“Amma kina da wanda kike so?”
“Eh”
“Mai sa baki fad’a masa ba?”
“Kinsan halin Ya Assad yanzu zai iya yi man tas dan tun farkon sanina da abokinsa sai da yaja man kunne kar na kuskura nayi soyayya da abokin sa..kawai sabida bai san raini ya shiga tsakanin mu”
“Yanzu wa kuke soyayya dashi?”
“Best friend d’insa Ya Umar”
“Aikam Umar mutumin kirki ne, kawai ki sanarwa Ya Assad nasan zai yi farinciki”
Rik’e baki Safiyya tayi tace
“Rufan asiri in na fad’a masa haka sai ya fasan baki”
“Karki damu zan fad’a masa in sha Allah zai amince”
“Thankiu, amma ki bari sai bayan suna yadda kafin ya ganni ma da aiki”
Murmushi Jalila tayi wurin 9 Safiyya ta tafi
Kwance suke Baby na tsakiyar su Jalila tace
“Dear d’azu kunyi maganar Safiyya kota fitar da miji ko?”
“Eh”
“Ta fitar sai dai kasan mata da alkunya barata iya fad’a maka ba”
Rik’e baki yayi yace
“Wannan yarinyar mai ido ‘a tsakiyyar goshi ne take jin kunya”
Murmushi Jalila tayi ta rik’e yatsun hannun sa tace
“Koman rashin kunyar mace in dai aka zo maganar aure koya sai jikinta yayi la’asar”
“Uhum, tama k’i fad’a man wanda take so”
“Da amininka Umar yake sonta”
“Mai tace masa?”
“Ta amince”
Mood d’insa ne ya chanja yace
“Wato munafurcin da zasu yi man kenan? Ahhh lallai toh basu isa ba Safiyya dama ba kunya ya isheta tana ganin ta aura aminina ai iskancin sai yafi haka”
Tashi Jalila tayi ta d’auka Cup dispenser ta nufa ta iba masa ruwa mai sanyi ta mik’a masa tace
“Ka sha”
“Bana jin k….”
“Pls mana”
Babu musu ya karb’a ya sha sauran ta karb’a ta k’arasa sha ta zauna gefensa tace
“Ya Assad kar ka manta da Safiyya jininka kace farin cikin ka shine farin cikinta Ya Assad kai ne uba ‘a gareta inta aura Umar zata sama kwanciyar hankali da farin ciki dawwamamme in sha Allah”
Zai yi magana tace
“Pls mana Ya Assad dan girman Allah ka amince”
“Shikenan na amince”
Dad’i sosai taji ta masa godiya, Babyn ya d’auka yayi ta yiwa wasa sai da dare yayi sosai Assad ya tofa masu addu’a ya fita sabida bare iya kwana babu Fan babu Ac ba kuma nan an kashe shiyasa ya tafi d’akin sa
*Washe Gari*
Yana dawowa masallaci d’akin Jalila ya shiga ya d’auka Baby yana masa wasa bayan gari yayi haske Mama Hafsa ta karb’e sa tayi masa wanka Jalila ma tayi wanka breakfast tayi shi kuma ya sha Coffee suka tafi ganin Dr dan ‘a duba lafiyar mai jego da Babynta
Bayan sun kammala da asibitin gidan Mommy suka je dan bata fi 10mins da dawowa ba, Mommy tayi murna sosai sai dai kuma kamar yadda Jalila tayi k’asa da kanta tana jin kunya haka Mommy ma dan dattijuwa ne ita mai kunya addu’a tayi wa Babbyn suka tafi gida Mommy cike da murna ta k’ira ‘yan uwa da abokan arzik’i ta shaida masu matar Abba ta haihu dan ‘yan uwanta da Abba suke k’iransa kasancewar Abdallah sunan mahaifin Mommy ne
Kullum gidan cike yake da mutane ‘yan barka ana gobe suna ‘yan uwa suka zo suka yi ta aikace-aikace Assad kam ran sa bai so ba taron mutanen dan shi bai so ayi masa taron suna ‘a gida ba tattara kayan sa yayi ya tafi gidan Mommy dan bare iya da hayaniyar mutane ba
*Washe Gari*
Bayan an saka wa jinjiri suna Muhammad Ali gida ya shiga ya k’ira Jalila ‘a waya tazo ta same sa
“Ya Assad ina kwana?”
“Lafiya lau, kin san sunan Baby?”
“A’ah yanzu dai nake son na tambaye ka”
Murmushi yayi ya shafa sumar jinjirin ya dad’a tofe sa da addu’a yace
“Sunan Baba na saka masa?”
“Baba kuma?”
“Eh Daddy”
“Allah sarki Allah raya sa Allah yayi wa rayuwarsa albarka”
“Amin, a tunanin ki wane Daddyn?”
“Daddynka mana”
Murmushi yayi yace
“A’ah sunan Daddynki na saka”
“Kana nufin Muhammad Ali?”
“Eh mana”
Bata san lokacin da tayi hogging d’in sa ba sun jima tare daga bisani ya fita ta rufe d’akin sa ta tafi da key d’in d’akinta
“Nikam ina Assad?”
“Yanzu kam ya fita”
Kafin Nabeela ta rufe baki k’iran Assad ya shigo
“Hello Assad”
“Na’am Ya Nabeela ina wuni?”
“Lafiya lau Baban Baby”
Murmushi yayi yace
“Ai munyi fishi shiru sai yau kika zo”
“Wlhy Assad takwaran ka ne babu lafiya”
“Ayyah, ya jikin nasa?”
“Jiki yayi sauk’i Alhamdulillah, kamar kam kasan yanzu na gama tambayar ka”
“Hmmm, na d’an fita ne amma inna dawo zan shigo na mik’a gaisuwa wurin babbar Yaya”
Murmushi tayi bayan sun gama wayar Jalila ‘a ranta tace
“Lallai Ya Assad in yana yi da kai ya yi in kuma bai yi bai yi”…dama tun chan Assad da Nabeela suna shiri sosai
“Wai mai sunan Babyn ma?”
“Sunan Daddy, Muhammad Ali” tayi maganar idonta cike da hawaye…Nabeela ma hawaye ta soma tuni mutuwar iyayensu ya zama masu sabo kuka sosai suka yi Sister’s d’in Daddy dana Mommy suka saka su ‘a gaba,suka yi masu nasiha Nabeela tayi shiru amma Jalila ta kasa yin shiru da k’yar aka rarrasheta dan Naberla Assad ta k’ira ta fad’a masa hankali ‘a tashe yace ‘a bata wayar yayi mata nasiha mai ratsa jijiyoyin jiki kana tayi shiru….’yan suna kam Alhamdulillah kowa ya bayar da abinda Allah ya sauwak’e masa…Ya Ibrahim kam yayi k’ok’ari sosai Dan akwati d’aya ya had’awa Baby da mahaifiyar sa matar sa kuma turare dasu pampers ta bayar ya Nabeela ma tayi k’ok’ari sosai
Rago biyu aka yanka washe gari aka soya aka raba mutane duk ranar suka watse ya rage daga Nabeela sai Sumayya suma da suke shirin tafiya nasiha sosai suka k’ara yi mata suka bata wasu turarukan gida dana jiki da dai sauran su
Mayafi Jalila ta yafa ta rako su Baby yana wurin Mama Hafsa, Ya Ibrahim ne ya shigo da motar sa Jalila da murmushinta ta bud’e ma sa tace
“Big Bro mai kake nufi baraka fito ba? Gaskiya sai ka fito kaci abinci da kai na fa na dafa maka”
Murmushi yayi yace
“I promise next time lil kinga yanzu kafin muje Abuja will take long”
“Haba Ya Ibrahim just 5mins fa”
Assad ne ya shigo ya nufo su yace
“Ba dai tafiya ba”
“Wlhy kam”
“Nayi-nayi yaci abinci ma yak’i ci”
“Haba Babban Yaya ka fito man ko kad’an ne kaci”
Murmushi yayi ya fito suka shiga ciki yaci abinci bayan sun gama suka tafi gida cike da kewar su ta dawo cike tare da mijinta
: *BARRISTER ASSAD*
*©UMMEE HAMBALI*
Dedicated to
*MEENA PARROT*
4⃣2⃣
Zaune Assad yake ‘a palon Mommy suna yin fira Inno ta shigo Assad ya gaidata amma ciki-ciki ta amsa zama tayi
“Inno babu lafiya ne?”
“Mai kuma ka gani?”
“Naganki ba yadda na saba ganinki ba”
Ba dole ba, ya muka yi da kai? Kace zaka sakawa yaro sunan mahaifina ka saka sunan Muhammadu”
Dariya ma abun ya basa yace
“Haba Inno na”
Banza tayi dashi ganin bata da shirin hak’ura yasa ya tashi ya tafi…Mommy ta kwantarwa Inno da hankali
“Inno kiyi hak’uri kin san halin Abdullahin naki”
Tsoki Inno tayi tace
“Shegen yaro sai taurin kai da tsattsauran ra’ayi, bai biyo halin mai sunan ba”
Murmushi Inno tayi tace
“Inno dan Allah kiyi hak’uri”
“Toh ba dole ba, ai nama gode Allah ba shine kawai jikina ba”
Ranar wuni Inno tayi tana mita ta shirya kayanta dan gobe zata tafi Sokoto wurin dangin ta
Bayan Assad ya koma gida Mommy ta aiko wa Jalila da Sultan kaya da sauran su…Jalila ta k’ira Mommy tayi mata godiya sosai
Knocking ne ya katse su daga labarin da Jalila take basa tashi yayi ya bud’e k’ofar ganin Umar yasa ya saki murmushi had’e da rungume aminin nasa suka shigo ciki, bayan sun gama gaisawa Jalila ta kawo wa Umar ruwa da drink da spring roll da meat pie
“Man wannan beta haka” ya nuna tray
Girgiza kai Assad yayi had’e da yin murmushi yace
“Mai hali dai bai chanjawa”
“Ina fa, ai dole na zage nayi aure”
Dariya Assad yayi ya zuba ruwa ‘a cup ya sha kad’an ya ijiye sauran ya kalla aminin nasa
“Ya kama ta ai, amma baka da mutunci”
“Man mai nayi?” Umar yayi maganar yana cin snacks abun sa
“Kayi mata ‘a gidanmu shine baka fad’an ba”
“Hmmm, babban Yaya dama zuwan nan da nayi nazo na fad’a maka ne”
Assad yaji dad’i dan koba komai zumunchin su zai dad’u sosai
“Allah ya sa alkhairi’
“Amin Amin Amin Amin”
Murmushi Assad yayi yace
“Ohhh ni Abdullahi! Kaga ango mara kunya”
Dariya dukan su suka yi dan Umar irin mutane ne masu barkonci ranar da kuka had’u ranar zaku saba
*1year later with some months*
Sultan yana wurin Mommy yaye yana samun kula na musamman wurin kakarsa yayi k’iba yayi kyau dan yaron bai wasa da cikin sa, sai dai akwai k’iriniya da surutu amma ko kad’an bata tab’a k’osawa da jikin nata ba sabida soyayyar da take yi wa mahaifinsa
*YEARS LATER*
Suna zaune suna breakfast familyn abin burgewa komai suna yin sa ne cikin nutsuwa da k’aunar juna dan ‘a babban tray suka zuba abincin suna ci su duka….
Yanzu ‘ya’yansu 6 Sultan ne babba shekarar sa 10 sai mata twins d’aya sunan Mommy d’aya Mami shekararsu 8, sai Al-Hashim mai sunan baban Assad suna k’iran sa Khaleefa shekarar sa 5, sai auta Ibrahim suna k’iransa Khaleel yayan Jalila Ibrahim aka yi wa takwara shekarar sa 2….
Familyn komai nasu abin burgewa yanzu kam Jalila tayi hankali sosai dama ance aure da haihuwa masu chanja mutum, gashi business yana tafiya dai-dai sabida dukan su sun rik’e gaskiya da amana gashi yanzu sun shak’u kamar ciki d’aya suka fito
Mommy ma tana son jikokinta ba kad’an ba duk weekend friday to sunday take sa akai mata su
Sun fito daga shopping yana d’auke da Khaleel d’ayan hannunsa kuma yana rik’e da hannun matarsa suna niyar shiga mota sai ga wata mata kamar almajira ta nufo su jaka Jalila ta bud’e zata bata sadaka matar tace
“Assad, Jalila”
K’are mata kallo yayi ya nuna ta yace
“Khairat?!”
“N…n…na’am” tayi maganar tana hawaye tana kallon sa dan yanzu ya chanja sosai ya k’ara kyau da jiki da alama yana samun kwanciyar hankali dan ya zama wani Alaji
Mota ya bud’e zai shiga Khairat tace
“Dan Allah ku yafe man abinda nayi maku”
Shiru yayi ita kam kuka takeyi sosai Khairat ne tayi k’arfin halin cewa
“Allah ya yafe mana”
Assad da Khairat suka amsa da amin kud’i ta ciro ta mik’a mata tana ta godiya da kuka Assad kam ko kallonta bai yi ba yaja motar suka tafi yayi shiru yana Driving tace
“Kai duniya kenan wlhy ta bani tausayi”
“Bata bani tausayi ko kad’an ba ai in mutum ya cutar da wani Allah ai Allah bare bar sa ba, kuma in kace yawon duniya zaka saka ‘a gaba wata rana duniyar zata juya maka baya…’yammatan yanxu suna yin kuskure babba suna d’aukar yawon duniya wani abu eh lokacin da akeyi dake ana yi dake amma lokacin da duniya zai juya maka baya bola ma yafi ka darja”
“Haka ne, Allah yasa mufi k’arfin zuciyoyin mu”
“Amin Habibty”
The End
Nagode sosai da so da k’aunar da kuke nuna man i love y’all❣