BATACCEN YANAYI
CHAPTER 1
Wasu dankararrun motoci ne guda biyu masu qirar Mercedes Benz E class suka tsaya a
yayin da wutar traffic yayi nuni da su tsaya. Daga gani dai zaka san wannan motoci na
mutum daya ne dun harta plate number dinsu ma iri daya ne, kuma customised plate ne.
Ganin sun tsaya, wata ýar yarinya me bara ta rugo da gudu ta tsaya Jikin window din daya
daga cikin motocin tana roqo. Yarinyar dai kwata kwata ba zata wuci shekara goma sha
biyar ba da haihuwa. Rigar ta duk a kode, idanunta duk sunyi yellow sun shige ciki alamar
yunwa. Da ganin yarinyar nan dai zaka gane tana cikin wani irin yanayi na yunwa da rashi.
“Oga please sir…. Help… food.. ungry.. Baba ba lafia”. Yar yarinyar nan ke ta fadi
shikuma driver din motar yayi hanzarin sauke glass din window dinsa ya daka mata tsawa.
“Gerrout of here! You filthy rag. If your parents can’t cater for you why did they bring you
into the world, pathetic beings..Ya buda baki zai sake magana aka dakatar dashi.
“Alex keep shut”.
“But boss”.
“Keep shut said!”. Glass din bayan motar aka sauke aka jeho kudi ýan dari biyar guda biyu
aka yi maza aka rufe glass din kan ýar yarinyar nan ta yi godia. Rufe window din ke da wuya
traffic light yayi nuni da su wuce Ita kuma ýar yarinya ta ruga da gudu inda Baban ta da
kaninta suke a zaune a gefen titi.
Wannan motoci basu tsaya a ko ina ba sai babban filin jirgin murtala Mohammed. Motocin
na isa wani qaton namiji me sanye da suit ya fito daga motar farko yaje ya buda kofar back
seat din mota na biyu wa boss dinsu.
“Yanzu sai yaushe?”. Amir PA ya tambaya.
“T’ll relate when i’m coming back to you in due course. Insha Allah ina gama business zan
juyo amma sai na tsaya a Egypt tukun”. Ta fadi cikin wata murya me sanyi.
“Toh Allah kiyaye hanya'”. Ba tare da ta ansa ba ta juya ta fara tafia. A hankula take takawa
kamar tana jin tausayin qasa. Sanye take da riga doguwa me tsadar gaske, idanunta kuma
ta rufe su da wasu dark shades masu kyaun gaske. A haka take takawa sannu a hankali har
ta shiga jirgi wanda yike cike da passengers zuwa qasar Australia. Wata air hostess ce me
kirki ta rige mata ýar chain bag dinta har zuwa seat dinta.
“Nagode” tayi murmushi ta anshi jakarta sannan ta zauna. Gefen ta, a kujerar da ke kusa da
ita wani namiji ne a zaune ya rufe huska da newspaper sai sharar barci yike ta yi. Abun ya
dan bata haushi har ta ja ýar tsaki saboda mutumin ya zauna a seat inda ya kamata ta
zauna, kusa da window. About 45 minutes da fara tafiyar su sai wannan bawan Allah ya
tashi.
“Hello” ya buda baki yace mata ba tare da ya jira answer dinta ba ya miqe da niyyar zuwa
ban daki. Ba da sanin sa ba ya dan taka ta ya wuce.
“Malam koh dutsen da ka taka bata ji maka ciwo ba”. Ta mai magana cikin gatse.
“Dutse kuma baiwar Allah? Koh dai shigar ki jirgin sama na farko kenan”. Ya fadi tareda
tuntsurewa da dariya abun ya qara bata mata rai ta ja tsaki shikuma ya wuce bathroom.
Kan ya dawo ta tashi ta koma seat inda yike a zaune. Shikam wannan bawan Allah na
dawowa ya ce alambaran baya yarda sai ta tashi mai amma ta qi.
Zan koh yi maganin ki’ ya fadi cikin zuciya.
Wata air hostess tazo giftawa ya kirata yace dan Allah orange juice yike so ta bashi. Cike da
murmushi taje ta kawo mai wannan orange juice din. Ya karbi cup din daga hannunta yana
mata godia. Ya sha sip din farko yana kallon abokiyar tafiyar sa wadda take sanye da
earpiece tana jin kade kade daga ipad. Ya Kalle ta ya saki murmushi yana mata tayin juice.
Yamutsa huskanta tayi alamar bata so. Can Can ba da dadewa ba aikuwa wannan mutum
ya kifar da gaba daya juice din a Jikin rigarta. Wani irin tsawa ta daka mai tare da mai wani
kallo me cike da tsana shi kam koh a jikinsa dun ya ci ma burinsa na sa ta ta tashi mai daga
seat inda yake so ya zauna. Tashin ta ke da wuya zuwa ban daki ta wanke jikinta ya tashi ya
koma kujerar ya zauna ya dau ipad dinta ya kunna waqa yana ji. Tana dawowa ta Kalle sa
wani irin baqin ciki ya rufe ta ta rasa abun da zata mai kawai sai ta kwashi kayan ta tace ita
sai dai a bata wani seat. A hanzarin sanja gun zama ta mance da ipad dinta a gunsa.
Ashe dai ta gudu bata tsira bane ba dun sabon seat inda aka bata wata mata ce zaune da
danta me kimanin shekaru biyar. Yaron baya ji gashi da surutu, a haka dai ta haqura har
jirgin su ya isa qasar Australia. Tana fita jirgi washroom din airport ta fara nufa dun ta sanja
kayanta. Ta cire wannan doguwar rigar tayi sabuwar shigar ta a cikin wani jeans wanda ya
matse ta da hoodie dinta me kalar toka. Daga nan ta ja akwatin ta zuwa arrivals lounge
inda ta hango wani bature, dan dattijo dashi riqe da wata cardboard da aka rubuta sunanta
a kai. Da hanzari ta nufi mutumin tana ýar fara’a.
“Hello mister”
“Hello ma’am. Laylah?”.
“Yes”.
“Ohhh Simon Yates. Nice to meet you”. Ya fadi yana miqo mata hannu.
“Laylah”. Ta fadi tana murmushi. Da sauri ya anshi jakarta ya cigaba da ja har zuwa inda
yayi parking din mota ya buda mata gidan baya ta shige. Shima ya shiga driver’s seat ya
rufa kofa ya hau titi. Suna tafe yana dan taba mata hira.
“Your first visit to Australia?”
“Yes sir”
“Simon… you can call me just that”. Mutumin dai daga ganinsa yana da kirki ga fara’a don
haka Laylah taji lokaci daya ya kwanta mata a rai. Tana ta kallon kyaun garin Melbourne
har suka isa wata hadaddiyar gini wanda daga duka alamu hotel ne. A nan ya sama wuri
yayi parking ya fito ya buda mata mota ta fito sannan ya buda boot ya dauko ýar akwatin ta
ya fara ja zuwa cikin hotel din bayan ya miqa wa daya daga cikin valets na hotel din key din
motar sa dun ya gyara mai parking.
Suna isa reception dun hotel din wata receptionist baturiya ta tarbe su cike da murmushi.
“How may 1 help you sir?” Ta tambaya Mr Yates.
“A reservation was booked by my boss for this beautiful miss here”
“I see, name please?”. Ta tambaya.
“Laylah”. Ta ansa a sanyaye.
2:59 PM OAO
“Surname”.
“Laylah Jaan, just that”. Laylah ta ansa da murmushi.
“Just a sec please” receptionist din ta fadi. Ta dau kaman minti biyu tana dube dube a
computer kan ta miqo masu key gami da fadi “enjoy your stay at Castle hotel”.
Bell boy Mr Yates ya samu ya hadashi da akwatin Laylah sannan ya mata sallama tare da
fadi mata saqon boss dinsa.
“Boss says he’ll meet you in 2 days time, i’ll come by tomorrow to transport you to his
guesthouse. For now enjoy your stay here and call me incase you need anything”. Ya fadi
tare da miqo mata wata zandareriyar waya wanda ya saka number dinsa a ciki.
“A gift from boss” ya fadi a lokacin da yike miqa mata wayar. Ta dan saki ýar murmushi kan
tayi masa sallama ya wuce. Har kofar dakin wannan bell boy din ya kai ta ya ije mata
jakarta a ciki kan ya juya ya wuce. Da gudu ta fada kan qatuwar gadon da ke bedroom din
suite din tana tsallen murna. Da hanzari ta dauko wayar da Mr Yates ya bata tayi dialling
wani number.
“Yasmeeeeeeeeeeeenah”. Ta fadi a cikin murya me qarfi.
“T’m in Australiaaaaaaaa”. Ta kuma fadi cikin murna. A haka dai suka ci gaba da hira da
wadda ta kira. Can kan ta kashe wayar sai Yasmeenah tace mata bara ta bata wani albishir.
“Albishirin ki”. Yasmeenah tace
“Goro”.
“Menene tukwuici na?”
“Duk abunda kike so”
“Kin tabbata?” Ta tambaya Laylah tace ehhh.
“Khalifa Al-Haydar is in Australia”. Ta fadi da dan karfi.
“Ki bar wasa”. Laylah ta fadi tana daka tsalle. “Yes yes! Wannan karan sai na ci ma burina'”
Ta fada cike da murna.
“Yanzu dan Allah Jaan don’t fall my hands. Make sure you get that dude”
“Trust me Yasmeenah”.
“Yanzu mu koma ga tukwuici na'”.
“Na san me zaki tambaya, let me save you the trouble. The Benz is all yours”. Ta fada. Cike
da murna suka yi sallama da Yasmeenah ta katse waya ta ta tashi ta wuce ban daki don yi
wanka. Wanka tayi ta dauro alwala. Bayan ta gama sa kaya ta shimfida sallaya ta kabbara
sallah. Ta dade a zaune tana addu’a kan ta miqe ta ninke sallayar sannan ta hau gado dun
ta huta amma duk taji ta kasa barci saboda tsananin murna.
Ta dade tana baibayar Khalifa Al-Haydar amma bata taba saa ba. A duk lokacin da aka ce
mata yana wata qasa da taje zata samu labari ya bar qasar zuwa wata sai kuma gashi yanzu
cikin sanyi ta sama kan ta a qasa daya dashi.
“Insha Allah bazan koma gida ba sai na ci ma burina. Sai na nemo Khalifa Al-Haydar, he has
to see Laylah Jaan work her charms” ta fadi afili.
********
Na san a yanzu masu karatu na cike da tambayoyi da yawa gami da rayuwar Laylah da
manufar zuwan ta Australia. Na san kuma kuna so ku san wanene Khalifa Al-Haydar. The story is boring koh? Just keep calm and follow me. I promise you’ll never regret BATACCEN YANAYI
Kiran sallan subh ne ya tayar da shi daga barcin sa. Yana tashi zaune azkhar ya fara kan ya
miqe ya nufi ban daki. Sai da yayi wanka, ya wanke baki tukun ya shimfida sallaya yayi
sallah. Yau be fita zuwa masjid ba a dalilin tafiyar da ke gaban sa. Yana idda sallah ya hau
kan arranging box inda zai yi tafia dashi. Be huta ba sai da ya gama hada komi tukun. Sake
shiri yayi cikin kaya masu kyau, ya fesa su turare da sauran su tukun ya wuce sitting room
inda ke part dinsa ya dau laptop dinsa ya hau kan danne danne.
Jim kadan sai ya ji motsin mutum ya buda kofar dakinsa ba tare da tambayar permission
ba. Kanshin turaren da ya daki hancinsa kawai ya sanar dashi waya shigo.
“And here comes the lady before my heart”. Ya fadi ba tare da ya dago kai ba daga laptop
dinsa.
“Ya akayi ka san ni ce?”. Ta tambaya bayan ta zauna kusa dashi.
“How can a son not recognise his mother?”. Yayi murmushi gami da dago da kansa ya kalli
mahaifiyar sa. Kamar yadda ta saba a Kullum, yau ma tana sanye da kaya masu kyau,
kayana alfarma gata dama da jiki me kyau. A Kullum tamkar kara kuruciya take, kwata
kwata ba alaman tsufa a tare da ita. Murmushi tayi ta jawo danta jikinta.
“Khalifatullah..” Ta kira sunansa kamar yadda ta saba kira a cikin murya me sanyi “Do you
have to have go? Ni kwata kwata hankali na be kwanta da wannan tafiyar taka ba'”.
“Look here begum, you know l’m doing this for you and I. For both of us right? I promise
zan kiraki each and every day and I’ll be back in no time. Ina gama abunda ya kaini zaki
ganni gida”
“Alkawari?”.
“Cikawa” ya fadi yana murmushi.
“Toh tashi muje kayi breakfast na kai ka airport. I know how hot headed you can be, don’t
say no”
“No begum, kema kinsan we can’t be seen together koh, i’ll take a bus”.
“Khalifatullah..” yayi saurin rufe mata baki kan ta ce komi. Yayi amfani da dayan
hannunsa ya share mata hawaye.
“Ba yaro bane ni, na san hanyar gida. Zan dawol promise”
“Shikenan, Allah yayi maka albarka da na” Ta riqe hannunsa zuwa kitchen inda tayi serving
dinsa abinci. Ta zauna ta basa da kanta a baki har sai da yace ya qoshi tukun ta daina bashi.
Zata tashi ta wanke hannun ta ya zaunar da ita.
“It’s now my turn to fulfill my obligation towards you”. Ya fara bata abinci yadda ita ma ta
basa a baki. A duk lokacin da Khalifatullah ya ciyar da ita, wani irin murna mara misaltuwa
ke rufe ta. A Kullum son dan ta kara cika mata zuciya yike ga kuma alfahari da take yi da shi
a Kullum sai dai kuma rayuwar yaron nata na matukar bata mamaki, yadda yike tafiyar da
alamuransa da kuma irin saukin kai da Allah ya basa.
Gama bata abinci yayi sannan ya kwashi plates din ya wuce dasu sink suka wanke hannun
su yace bara ya wanke plates din ta hanasa.
“You’ll miss your flight”. Ta fadi tare da tura sa zuwa dakinsa ya shirya. Wucewa yayi ya sake
kaya zuwa wani sweatpant da dan hoodie dinsa saboda yanayi weather ana dan sanyi
Bayan ya gama shiri ya fito yana jan ýar jakarsa. Yayi sallama da mamansa.
“Do give Hisham the keys to the apartment okay”. Ya fadi tare da kissing goshin maman
nasa wadda har wannan lokacin tana cikin jimamin tafiyar da dan nata zai yi.
“Beguuuuum.. Come on. Wannan fa ba shine karo na farko da nike tafia ba, i’ll be okay
promise”.”i’ll miss you son”. Ta fadi “You sure you don’t want me to drop you off at the airport?”
“Aah, i’ll be fine”. Da kyar dai Khalifatullah ya iya sallama da mamansa ya ja box nasa ya
wuce bus station inda ya sama drop na taxi har zuwa airport. Ba tare da bata lokacin ba ya
shiga queue duk ya gama formalities na airport. Yana shiga jirgi aka yi directing dinsa zuwa
seat nasa ya sama wuri kusa da window ya zauna. Can ya daga magazine da akan ije ma
passengers a jirgi ya fara dubawa har barci yayi awon gaba dashi kasancewar a daren jiya
be samu isasshen barci ba. After what seemed like forever, Khalifatullah ya farka daga
barcin da yike, hasalima fitsari da ya riqe sa ne ya tayar dashi daga barcin. A lokacin ne ya
lura har jirgin su ya daga. Juyawa da zai yi, idanuwansa suka yi ido hudu da seat mate
dinsa. Mace ce wadda a shekaru ba zata wuci shekara ashirin da hudu zuwa da biyar ba
haka. Be tsaya kallon ta ba da kyau ya dauke idanunsa a kanta. Shi ya kasance mutum ne
me matukar kunyan hada ido da mutane tun bare ma mata. Duk yadda yike da son wasa da
barkwanci, da wuya ya kalli mutum cikin ido bare ma har ya tsaya kallon mace.
“Hello” kawai ya fadi ba tare da ya kuma kallon gefen ta ba ya miqe dan ya nufi washroom
ya biya buqatan sa. Har ya dan fara tafia muryar ta ya tsayar dashi. Cikin wata murya tayi
maganan, cikin bacin rai.
“Malam koh dutsen da ka taka bata ji maka ciwo ba'”. Maganar kwarai da gaske ta dan sosa
ran sa saboda irin muryar da tayi amfani dashi ba wai dun ya gane gatsen da ta mai ba
kasancewar ba wata isasshiyar hausa yaji ba.
Even begum doesn’t use that tone on me’ ya fadi a ransa amma a fili sai ya maida mata da
ansa me cike da tsokana. “Dutse kuma baiwar Allah? Koh dai shigar kijirgin sama na farko
kenan” ya fadi gami da tuntsurewa da dariya ganin maganar ta da da bata mata rai.
Wata tsaki yaji ta saki shi kam koh a jikinsa ya wuce washroom yayi fitsarin sa ya fito sai dai
yana iso wa seat dinsa yaga hajia almasifatu ta koma seat dinsa wanda ke kusa da window
ta zauna. In zaa bi gaskia, Khalifatullah ya san seat din nata ne but shi kuma a gaskia ya fi
son window seat don haka yazo yace mata alambaran sai dai ta tashi ita kuma ta qi sai ya
rabu da ita amma a zuci ya quduri niyyar sai ya koma seat dinnan kuma true to his word,
haka aka yi. Sai da ya sa ta tashi daga seat din ta bar mai.
“What Khalifatullah wants, he gets. Ya fadi a zuci cike da murnan korar ta daga seat din baki
daya dama shi mutum ne wanda ya tsani zama kusa da mata. Kwata kwata baya so abu ya
hada sa da mata dun sha’ani dasu nada wuyan gaske kuma sai me haquri.
Da isan su qasar Australia ya shiga ya sanja kaya kafin ya fito ya nufa arrival lounge na
airport din. A lokacin ne ya tuna da ipad din seat mate dinsa a jirgi wanda yike tare dashi.
“Shit! Where the hell do I start looking for her”. Ya fadi tare da jan ýar tsaki. Nan dai ya fara
dan tafia yana sa ido koh Allah zai hadashi da ita. Yana cikin tafia ya ji an tabo sa daga baya.
A zaton sa, koh ita ce ta gansa ta biyo sa dun ta karbi ipad dinta amma yana juyawa yaga ba
ita bace.
Nawfal ne, amininsa kuma cousin brother dinsa. Kan ya ankara ya jawo sa zuwa jikinsa
yana hugging dinsa cikin murna. “Man I missed you”. Nawfal ya fadi.
‘ve missed you too”. Shima ya fadi cikin murna. Bayan gaisuwan yaushe rabo, Suka fara
takawa zuwa parking lot Nawfal na jawo dan trolley din Khalifatullah har su isa inda yayi
parking motar sa.
“Mamu doesn’t know you’re in Australia, does he?”. Nawfal ya juya ya tambaya dan
uwansa.”No, I’m here for some work. I’d love to be uncovered for a while. Zan maka bayani in na
huta'”. Ya fadi ma Nawfal wanda har ya jawo hadaddiyar motar sa me qirar chevrolet
camaro sun hayo kan titi. Can jim kadan, Khalifatullah ya fito da wannan ipad din luckily
for him kuma ipad din baya da password koh pattern dun haka swiping kawai yayi sai ya
bude. Nan da nan ya fara buga game din candy crush can kuma yaji kawai wata zuciya tana
raya mai da ya shiga gallery dinta.