BATUUL
CHAPTER 10
A hargitse ta tura k’ofan ďakin, yana kwance kan gado ya lumshe ido kamar ba shine ya shigo yanxun ba, dai dai kanshi tazo ta tsaya tana huci, ranta b’ace har wani gumi takeyi ta shiga yi masa magana, “Aliyu nifa bazan yadda da wannan abinda kuka tsira ba, wlhy ni bazan yadda da zamanta ba a cikin gidan nan, inma kai baza ka iya faďawa iyayenta baka son zamanta gidanka ba sai ka kama mata hostel ďin da kanka kawae, amma ba dai tayi ta zama min a gida ba dan dama nasan munafirci ya kawota”, sai da yaji tayi shiru tukunna ya buďe lumsassun idanunshi dake rikitata yace “tunda gidanki ne sai ki koreta”, ido ta wara tana kallonshi hawaye na bin kuncinta, cikin rashin damuwa da hawayen nata yaci gaba da cewa “tsabar rashin hankali da rashin sanin ciwon kai shine ki kaje kika tsareta a kitchen kina gaya mata maganganu koh, toh duk kika yrda ta raina ki baxa ki ji da dadi ba kuma bbu ruwana baxan kuma ce mata don me ba “, hankalinta ne ya k’ara tashi wai yau ita Abu ke k’ira mara hankali akan wata can y’ar iskar, wlhy Allah sai tasan yadda tayi da Batuul, sai ta wulak’anta ta fiyeda tunaninta, k’wafa tayi ta juya a fusace ta banko mishi k’ofar ďakin a xuciyarta tana cewa xaka rashin hankali kuwa, tabe baki yyi ya sake lumshe idanunshi ya gyara kwanciya yana shak’ar k’amshin Batuul da ya mannne mishi a kaya da yayi hugging ďinta.
+
Tana fita ďakin tayi hanyan ďakin Batuul a fusace kamar wacce zata tashi sama, kai tsaye ta tura k’ofar ďakin da Batuul ke ciki, tana zaune kan gadon a takure ta haďe kanta da guiwa, bata ďago kanta taga ko waye ba dan tasan shine ya dawo, ji tayi ance “tashi ki fita dan ubanki tunda ba ubanki ya gina min gidan ba”, a tsorace Batuul ta ďago tana kallonta da mamaki shimfiďe a fuskanta, gani tayi tana k’ara shigowa ďakin, da sauri Batuul ta mik’e tana kallonta, inda akwatinan ta ke ajiye Ajiddeh ta nufa ta ďauka tana watsarwa, a tsorace Batuul ta tsaya tana kallonta, hawaye ya taru a idonta, ita wane irin masifa ne wannan yake tunkarota ko kwana daya bata yi ba, hawayen dake k’ok’arin zubo mata ta maida ta sauk’o daga kan gadon tana ganin yadda Ajiddeh ke watsar da kayan tayi hanyan waje, wai wannan ma fa dan bata san matarsa bace ita, hanyan waje tayi zata fita daga ďakin, hannu Ajiddeh tasa ta rik’ota tana cewa “ga y’ar iska na miki magana koh, toh dan ubanki kisan inda dare yayi miki dan gidana ba gidan ajiye y’an iska karuwai bane”, ido Batuul ta rintse jin abunda Ajiddeh ta kirata dashi, zata iya rantsewa gaba ďaya rayuwanta bata tab’a jin an ambaci wannan word ďin a gidansu ba wai sai yau gashi ita ake k’ira da word ďin, hawayen dake idontane ya shiga gangarowa, hannunta tasa ta goge fuskanta, tasa hannu ta murďa k’ofan zata fita, wani irin force taji Ajiddeh ta tunkuďata dashi , ido ta rintse tana k’iran sunan Allah lkci daya ta fasa ihu tana jiran jinta a k’asa, amma ta ji akasin hka don jikin mutum ta faďa baya tayi zata faďi yayi hanzarin rikota ya rungumeta, shigewa jikinshi tayi tana boye fuskanta a kirjinsa, sai a lkcn ta fashe da kuka jikinta na rawa tsabar tsorata da tayi, kuka sosai ta shigayi tana cewa “Yaa Abu dan Allah ka maidani gida, dan Allah inaso inga Aunty, hannu yasa ya daďa haďe jikinsu dan yasan tsorata tayi ba da wasa ba, neman kukan da takeyi tayi ta rasa jin kanta faffaďan k’irjinshi, sai da yaga ta fara nutsuwa sannan ya saketa yana kallon fuskanta da hawaye ya gama wankewa, saketa yayi ya matsar da ita gefe ya zaunar da ita kan kujeran dake tsakanin ďakunan biyu, mutuwar tsaye Ajiddeh tayi ganin Aliyu ya kare Batuul, sam ba haka taso ba, taso koda Batuul bata mutu ba ta nakasa ta in yaso iyayenta suzo su ďauketa amma wannan jarababben ya taimakota, juyowa yayi ya shigo ďakin yanayinshi da ta gani ne ya sata tsorata, baice mata komai ba yasa hannu ya rik’o hannayenta tana binshi a baya kamar wata doluwa yayi ďakinshi da ita, kallonsu Batuul tayi hawaye cike idonta, ita dama tasan abin tausayi zata zama a gidan nan, duk abin nan da matarsa tayi baice mata komai ba sai ma rikota da yayi su tafi abunsu, kuka sosai ta kifa kanta kan cinyarta tanayi, sai sunan Aunty take k’ira da Baba, yana shiga ďakinshi da ita ya sake mata hannu, magana ta fara mishi cike da masifa “wllh Aliyu yarinyar nan ta barmin gidana dan…..” bai bari ta k’arasa maganan ba ya wanka mata mari lafiyayyu guda biyu, a gigice ta ďago kanta da idonta da ya rine yayi ja tana kallonshi, wani shegen murmushi ta saki tana hawaye tace “koh baka dakeni ba nasan karuwarka ce ko daga yadda ka rik’eta a jikinka, ni za a yiwa bariki a wani ce karatu tazo yi, munafiki kawai azzalumi, Kuma wlhy kaji na rantse sai na illatata, mugu kawai…..”, wani irin fixga da yayi mata yasa ta kasa k’arasa maganan da takeyi, idonshi ya sake yin jaa, yana kallonta yace “ai ke gidan na ubankine koh, dan bakida hankali kashe y’ar mutane zakiyi xa ki hankaďata hka, kinsan zaki iya barin gidan nan ita ta zauna, jahila kawai wacce bata aiki da hankalinta, kika sake min shirmen nan a gidana sai na b’ata miki yadda baki zato ba, mahaukaciya jahila”, yana kai wa nn ya jefar da ita ya fice daga ďakin, inda ya barta kan kujeran nan ya dawo ya sameta sai kuka takeyi, ce mata yayi “kukan mey kike ma mutane ke kuma har ynxu”, bata ďago ta dubeshi sai kukan da ta ci gaba dayi, cikin tsawa ranshi b’ace yace “ba magana nake yi miki ba”, rinannun idanunta ta ďago ta kalleshi cikin sanyi hawaye nata zuba tace “Yaa Abu dan girman Allah da Annabinshi ka mayar dani wajen Aunty”, hararanta yayi ya kamo hannunta, komawa tayi baya da sauri ta janye hannunta, tsayawa yayi yana kallonta yace “you thought all i was telling is lie huh, gashi nan kin fara gani tun ba aje ko ina ba, its just your first day and you have already faced soo much, sai da na faďa miki babu ruwanki da ita, mesa kika nemi magananta”, haushi ne ya cikata ta tsananta kukanta tabi ta gefenshi zata shige ďakin yayi saurin rik’ota, wayantane taji yana ringing, fixge hannunta tayi tayi ďakin, bayanta yabi a hanzarce, hannu yasa ya rigata ďaukan wayan yana kallon mai k’iran, Affan ya gani rubuce in bold da hrt emoji daga gaban, kin bata yayi har sai da wayan ta katse, batare da ya kalleta ba ya jefa wayan kan gado, tsayawa tayi tana kallonshi , Juyawa yayi yana k’arewa ďakin kallo yadda kayanta ke zube a k’asa, ce mata yayi “da kika zauna kina yiwa mutane kuka waye zai tattare miki kayan da aka zubar garin neman faďanki, kinsan baki da k’arfi kika nemi tsokananta”, bata ce mishi komai ba ta nemi waje ta zauna daga bakin gadon tare da janyo wayarta, dubawa tayi taga wa ya k’irata, ganin Affan ne ya sata ajiyan Zuciya, cikin kakkausar murya yace mata “ba magana nake yi miki ba, waye zai tattara miki kayan”, zumb’uro bakinta tayi ta juya tana gyara zamanta kan gadon tace “Ai ba ni na zubar ba, suna zamansu ta shigo ta watsar, a k’irata ta gyara mana”, da mamaki ya ke kallon yadda take mishi magana, matsowa yayi gaban gadon, da sauri ta shige cikin bargon tana cewa “nikam in ka tab’ani zan faďawa Ammah”, ce mata yayi “tashi ki tattare kayanki”, ba musu ta yaye bargon ta taso ta shiga kwashe kayan, juyawa yayi zai fita daga ďakin, har yaje bakin k’ofa ya juyo yace “kin nemi abinda zaki cin ko kuma baki gama jan maganan ba”, ganin batace mishi komai ba ya fita daga ďakin ya barta anan
1
Tana zaune ďakin har k’arfe 8 ďin dare, ga yunwa da ya addabeta, tsoron fita takeyi dan batason ko sake kallon Ajiddeh tayi, ta rasa mey zatayi kuďin wayarta ma ya k’are da ta k’ira ko su Aunty taji daďi, Affan ďinma da ya k’ira ďazu yaki k’ira har yanxu, tashi tayi ta shiga toilet tayi wanka tayi alwala ta tada sallah isha, sai da ta idar ta gama addu’anta tasha kuka ta tashi ta hau gado ta kwanta bayan ta kashe wutan, ta gwammace ta kwanta da yunwa da ta fito su haďu da Ajiddeh, jin an murďa k’ofan ďakin yasa ta k’ara tsorata, a hankali ta sauk’o daga kan gadon zata shige toilet taga haske ya gauraye duka ďakin, tsayawa tayi a tsakiyan ďakin ta kasa motsi, k’arasowa yayi cikin ďakin ya ajiye mata daya ledan dake hannunshi yace “in kin gama tsayuwan naki ga abinci ki ďauka kici, you get ready gobe by 11 zan kaiki school and mind you kina rufe k’ofar ďakinki da makulli”, wani irin ajiyar zuciya ta sauk’e jin shine, bata juyo ba har ya gama maganan da zaiyi sai ji tayi an juyo da ita, “kina jina ina magana kika min shiru, na fara wasa da ke koh”, a hankali tace “Ai naji”, saketa yayi ya juya ya fita daga ďakin tare da kashe mata wuta. Dakin Ajiddeh ya nufa rike da wani ledan ya murda kofar ya shiga, xaune ya sameta can karshen gadonta idon nn nata ya kumbura tsabar kuka, ya ajiye ledan hannunsa tare da sauke ajiyar xuciya ya nufeta, tana ganin hka ta mike da sauri xata bar wajen yyi hanxarin rikota tare da hade ta da jikinsa, ta fashe da kuka tana dukan kirjinsa tace ” let me be Aliyu, ka kyaleni, 1st thing tomorrow morning am leaving yhur goddam house, with or without my divorce prove, bna auren kuma, ae ba kai kadai bne namiji a duniya, sae ka xauna da ‘yar uwar taka…..” Ya runtse ido yace “Stop this Jiddah, yhu pushed me into behaving the way I did, meyasa baki saurarata ne wae, na gaya maki Batuul is only here for sometime, karatu ta xo yi tana gamawa xata koma Nigeria, I love yhu Jiddah bana son duk abinda xae bata maki rai, had it been we are not this close da iyayen Batuul da baxan yrda da xaman ta gu na ba coz it’s also a burden to me, plss nd plss Ajiddeh kiyi hkuri ki bar ta tayi karatun ta, her being here is nt for ever, if yhu love me do me this one favour pls babe,” tsuke fuska tayi ta kauda kai, ya marairaice yace “Plss babe!” Kuka ta fashe da tace “Shine xaka mareni Aliyu” ya kuma rungumeta yace “Ohh! Am srry babe sharrin shaidan ne plss, idan kuma baki hakura ba ki rama” shiru tayi bata ce komae ba, kissing wuyanta ya shiga yi a hnkli yace “Say something mana babe” lumshe ido tayi don kiss din Aliyu na rikitata, cikin sarkewar murya tace “Naji” bae daina abinda yake mata ba yace “kin amince ta xauna gidan ki har ta gama karatun?” Runtse ido tayi tace “Yeaa!” Yace “Promise!” Da kyar tace “I do love” Kiss din bakinta ya shiga yi passionately tana mayar masa da martani, kan kace me sae ga su kan gado.
Yana fita Batuul ta sauk’e ajiyar zuciya ta dawo kan gadon ta zauna, wayarta ta ďauka ta haska ledan da ya ajiye mata taga tambarin Mc donalds a jiki, ďan tsaki taja dan bata cika son abincin Mc donalds ba, amma tunda yunwa takeji babu yadda ta iya haka zataci, janyo ledar tayi ta shiga buďewa, kwalin chips ne a ciki sai chicken wings da dip in sauce, sai wani cup da aka sa strawberry shake da ruwa da pine apple drink, kaďan taci chips ďin, shake ďin kawai tasha da ďan yawa ta tashi ta ajiye sauran da bataci ba kan fridge, toilet ta koma tayi brush ta fito ta kwanta, tafi awa a kwance amma bacci ya k’auracewa idonta, hawaye ne ya fara zirara a idonta, she have never been this lonely gaba ďaya rayuwanta, dukda ba mai son surutu bace tafi son zama ita kaďai amma na yau ya dameta, ko ba komai a gida tana jin motsin y’an uwanta, amma yau hakan ma ya gagareta, tunanin gidane ya sata fashewa da kuka, wayanta ta janyo tana ganin hotunansu da shirmen da sukeyi, tanayi tana kuka wani kuma tayi dariya, tana nan zaune har k’arfe uku, yadda taga rana haka taga dare, gara ma da rana ta ďan samu ta rintsa, amma yanxu baccin ma ya k’aurace mata, tashi tayi taje tayo alwala, sai da tayi nafilfili tukunna tayi karatun Qur’ani a wayanta, tana nan zaune kan abin Sallah har asuba, tana idar da sllh taji wani irin bacci na fizgarta, nan kan abin Sallah ta gyara tayi kwanciyarta, tana kwanciya bacci ya kwasheta, cikin baccinta kamar a mafarki taji k’aran buďe k’ofarta, a ďan tsorace ta tashi ta zuba mishi lumsassun idanunta , k’arsowa yayi cikin ďakin yana binta da kallo, sai da ya shigo tsakiyar ďakin ya tsaya yace “wane irin bacci kikeyi anata knocking baki buďe ba”, juyawa tayi ta duba inda ta ajiye makullin ďakin taga yana nan, k’ofan ta sake kallo taga shima da makulli mak’ale a jiki, cikin tsawa yace mata “ba magana nake miki ba, ko bakiji lokacin da nace miki ki shirya zan kaiki school bane kika kwanta kina bacci”, sai lokacin ta lura da kayan jikinshi taga har ya shirya zuwa farin shirt mai stripes ďin bak’i da bak’in wando, windown ďakin ta duba taga har rana na fitowa ta kalleshi taga ita yake kallo har lkcn, ta ďauke idonta tace “ai bacci ne ya ďaukeni bansan safiya tayi ba”, ta faďa tana zumb’uro baki, k’wafa yayi yana kallonta yace “get ready and come down in the next 15mins”, daga haka ya juya ya fita daga ďakin, tab’e bakinta tayi a ranta tace masifaffe, daga haka ta cire dogon hijabin dake jikinta da rigar baccin ta shiga wanaka, ko minti biyar batayi ba ta fito daga toilet ďin bayan tayi brush, akwatinan kayanta ta buďe ta shafa mai ta ciro wata doguwar riga blue mai dogon hannu ta saka, chappette kawai ta shafa a lips ďinta ta taje gashin kanta sannan fesa turarukanta masu dadi’n k’anshi ta shafa, a hankali take sauk’owa daga stairs ďin har ta k’araso cikin palon, yana zaune kan ďaya daga kujerun palon, Ajiddeh na jikinshi sanye da wasu shegun kayan bacci da ya bayyana duk jikinta, ita ta fara hango Batuul, wani irin harara ta sakar mata kamar idonta zai zazzago ta k’ara shigewa jikin Abu dake k’ok’arin canja channel, cikin raďa tace mishi “baby i dont want you to leave”, tana yi tana kissing wuyanshi, shima janyota yayi yace mata “dont you worry, i will b back for you, kinga school zan kaita ta fara processing”, ita kam Batuul ko kallon inda suke batayi ba tazo ta wuce su zata fita waje, sai a lokacin ya ganta, da ido ya bita har ta fita daga palon sannan ya mik’e yana kallon Ajiddeh yace “Baby ki kula da kanki”, ya manna mata kiss a bakinta, hade rae tayi tace ” Babe ko gaisheni fa bata yi ba ta wuce” yace “ni din ma ae bata gaishe ni ba, kyaleni da ita” daga hka yayi waje, a bakin k’ofan palon ya tarar da ita tana tsaye, yace “Go back nd greet my wife” daga kai tayi tana kallonsa, ya hade rae yace “Do dat fast my frnd” juyawa tayi a hnkli ta koma falon, tsakiyar falon ta tsaya ba tare da ta kalli Ajiddeh ba tace “Ina kwana” a sanyaye tayi gaisuwan, Ajiddeh ta wurga mata hararan tsana tace “Da ban kwana ba kya gan ni, munafuka ‘yan maula” Juyawa Batuul tayi ta bar falon ta fita waje, har lkcn yana tsaye inda ta bar shi, ba tare da ya kalleta ba yayi wucewar shi garage ďin gidan, tana nan tsaye ya fito da wata dank’areriyar Benz, a hankali take k’arasowa inda motar take ta buďe gidan gaba ta shiga, k’anshin turarenshi ne ya cikata, juyar da kanta tayi tana kallon wajen glass, bai ce mata komai ba yaja motar ya ďau hanyar makarantan, tafiyan minti goma suka isa k’ofar makaranta sae a snn ya juya ya kalleta yace “yhu look for wat to take for breakfast a sch din,” ko kallonsa bata yi ba wani irin farin ciki ya ziyarceta ganinta a k’ofar university da kullum take mafarkin zuwa tayi karatu, batasan lokacin da murmushi ya sub’uce mata ba tana kallon yadda students kowa na aikin gabanshi, jin sautin murmushinta da yasa gefen kumatunta lotsawa ya bayyana dimple ďinta ya sashi juyowa yana kallon yadda take murna, yau ne rana ta farko da ya fara kallonta tana dariya haka, driving yake amma gaba ďaya hankalinshi na wajenta har ya iso gaban wani building yayi parking motarshi, sai a lokacin ta juyo da murmushinta ta kalleshi taga shima ita yake kallo, hararanta yayi ya buďe motar ya fito, ita dai bata fito ba dan baice mata ba, har ya fara tafiya yaga bata fito ba tana cikin motar a zaune, rai b’ace zagayo ya buďe mata k’ofan yana mata mugun kallo yace “zaman mey kikeyi da baki fito ba”, baki ta zumb’uro ta sa k’afanta a waje, ita batada lokacinshi dan ji tayi duk bak’in cikinta ya yaye, k’wafa yayi ya juya yaci gaba da tafiya, biyoshi tayi a baya har lokacin da murmushi fuskanta, har sukazo k’ofan shiga wani office sannan ya juyo yana kallonta rai a haďe, haďe dariyanta tayi ganin yadda yayi kicin kicin da fuska sannan ya tura k’ofan ya shige, a sanyaye itama ta shiga a ranta tace masifaffe kawai, nidai yau is my happy day banida time ďin kowa ta shige cikin office ďin itama, Office ďin ta k’arewa kallo, an manna hotunansu su Adam smith, Alfred Marshal, David Ricardo, J.S mills da sauran manyan economists ďin duniya, wani bature ne zaune kan kujera a office ďin, da gani shekarunshi zasu kai 60, dogo sannan yana da jiki, hannu ya mik’awa Abu yace “Mr Kyaree you are welcome”, baki ta kyab’e jin har sunanshi ya sani, juyowa yayi yana kallon Batuul yace “You can sit down madam”, yayi mata nuni da kujeran gefen Abu, kallon Abu tayi taga shima kallonta yake da lumsassun idanuwanshi, kujeran ta jawo ta zauna, tana zaune suka gama maganganun da zasuyi, mutumin ya ďago yana kallonta yace “Mrs Fatima are you single?”, question ďinne ya zo mata bazata, ta ďago tana kallon Abu dake danna wayarsa, a hankali ta ďauke kanta ta kalli mutumin da taga sunanshi Stephen xata yi magana ta ji Abuturrab yace “No! She’s nt, she’s married” kallonsa tayi sae kuma ta sunkuyar da kai, mutumin yyi murmushi yace “Dat’s Gud, yhu are welcome to London University of Economics Mrs Fatima kashim Goni” murmushi Batuul tayi jin ynda yyi pronouncing sunan nata, nan Mr Stephen ya shiga yi mata bayanin abubuwan da ya kamata, shi dae Abuturrab danna wayarsa kawae yake, sun kusa minti ashirin office din bayan ta cike wasu forms din da ya bata ta kuma yi signing kafin ya dauko ID dinta na makarantar ya bata, ya kuma yi mata maraba snn ya mika mata timetable da wasu textbuks har uku yyi directing dinta zuwa dept dinta, godiya tayi masa tana murmushi, Abuturrab ya mike ya kuma yi masa godiya mutumin ya basa hannu snn suka fita office din, bin bayansa kawae take farin ciki shimfide fuskarta, da alama ya san kan makarantar sosae ganin ynda yake tafiya with courage abunsa kuma short cut yake bi, xaro ido tayi da ta tuna ae shi ma makarantar yyi if she remembered rightly, ko kadan bata damu da ynda ya hade rae ba farin cikin da take ji a lkcn baxae ma bari ta damu da hkn ba, jefi jefi tana ganin bakaken fata kmr su suna wucewa, har gaban dept din ya kai ta, wata baturiya ce ke tafiya rungume da litattafenta, ya karasa inda take yace “Excuse me Ma’am!” D’an kallonsa tayi tace “Pardon?” Yace “Just a minute or two” Tambayarta ya shiga yi da harshen turanci ko a Dept din nn take, ta masa nodding tace “Yea!” Murmushi yyi yace “Dat’s gud Ma’am, am handing my sister over to yhu, assist her for today, yhu know! she’s new in here” Baturiyar da baxata wuce shekaru 18 ba tayi murmushi tana kallon Batuul tace “She’s welcome, she will really like it in here, from Africa I guess!” Yace “Yea! Exactly Africa! Africa Nigeria.” Karasawa gun Batuul dake kallonsu tayi ta kamo hannunta tare da shaking dinta tace “Welcm frnd, yhu will really enjoy it in here, I am Samantha Brown, yhu” Batuul tayi murmushi tace “Am Fateema kashim” k’asa pronouncing din sunan yarinyar tayi Batuul tayi dariya, yarinyar ta bude deep green eyez dinta tace “your looks are more like dat of Britney Smears a pop artiste, just dat yhu are a dark, I will cal yhu Britney! Nyc meeting yhu Britney” kallon Batuul dake dariya bakin rai Abuturrab yyi, sae ta basa dariya don bae taba ganinta cikin farin ciki haka ba, murmushi yyi yana kallon Samantha yace “Dat’s a gud start! I will take my leave now Miss Samantha, it’s nyc meeting yhu for the first time” hannu tayi masa stretching ya karba tace “Nyc meeting yhu too Mr…” Yana murmushi yace “Aliyu Ahmad” murmushin ita ma tayi tana nodding ta sake hannunsa, karban timetable din hannun Batuul yyi yana dubawa, snn ya mika mata, ya ciro 20 pound sterling hade da wayarsa d’aya ya mika mata yace “Driver xae kira ki anjima” risinawa tayi ta karba kanta a kasa tace “Nagode” bae tanka ta ba, ya ma Samantha waving ya juya ya bar su wajen.
+
Karfe biyar saura suna xaune ita da Samantha da wata Linda sae ‘yar uwarta yar Nigeria Aisha, ba karamin farin cikin haduwa da Aisha tayi ba ko ba komae ta samu ‘Yar uwa a makarantar, sae dae ita a hostel take, fitowarsu lecture knn suna ta hiransu ita kuma tana duba textbuk din hannunta, wani guy ne ya karaso inda suke yana kallonsu yace “Hi” duk suka amsa bnda Batuul da bata dago ba, xauna wa yyi daga gefenta yana kallonta yace “Assalamu alaikum!” D’agowa tayi da sauri tana kallonsa, sae a snn ta ga bahaushe ne me kyau, sunkuyar da kai tayi ta amsa masa sallamarsa, da harshen hausa yace “Ya lecture ‘yar uwa” tace “Alhmdllh tnxx” ya d’an yi murmushi jin ynda ta amsa masa yace “Am Shaheed Mukhtar by name, yhu?” Wayarta ne ya shiga ring ta mike tana kallon screen din tace “Srry Shaheed, I will be on my way ynxu” kallon Aisha dake ta kallonsu tayi tace “Plss ki d’an rakani outside gate, driver ya xo dauka na” bata jira cewar Aisha ba ta shiga yi ma su Samantha sallama, daga nn tayi gaba da sauri Aisha ta bi bayanta, binta da kallo Shaheed yyi yana murmushi, sae da suka yi nisa Aisha tace “me yasa xa ki yi masa hka Fatima, kinsan waye Shaheed kuwa, a vry popular guy a makarantar nn, he’s so intelligent, course din mu daya, nd he is in his final year, ni na yi mamakin ganinsa wllh, don bin sa ‘yan mata ke yi ba shi ke bin su ba” Batuul tayi murmushi tace “Gskya ne” tana ganin motar Abuturrab ta gane ta juya tana kallon Aisha tace “Toh sae gobe idan Allah ya kai mu, thnk for ur company frnd” murmushi Aisha ta mata ta gyada mata kai, Batuul ta juya ta nufi motar, duk a xaton ta driver ne, har xata bude baya sae kuma ta fasa ta bude gaba, ido hudu suka yi da shi, ta sunkuyar da kanta, yace “Baki ga daman d’aga call din ba knn” shiga motar tayi ta rufe ya tada motar suka bar wajen, a hnkli tace “Ina yini?” Ba tare da ya kalleta ba yace “Lfya lau” sae da suka kusa gida yace “Ya lecture” kmr an tilasta sa tambayar don can ciki yyi ta, ta kallesa tace “Alhmdllh” yana gama parking ta bude motar ta fita, sae dae bata yi gigin tafiya ba ta jira har ya fito, sae da ya shiga gaba ta bi bayansa, Ajiddeh na kwance falo ta kure Ac tana kallo sanye da kananun kaya as usual, a hnkli Batuul tace “Ina yini” Ajiddeh ta d’an saci kallon Abuturrab, ganin kallonta yake yasa tace “Lfya lau” sama Batuul ta nufa, ajiye wayarsa dake hannunta da long notes din da ta siya a makaranta tayi ta kwanta tare da lumshe ido, ta kusa minti goma kwance snn ta mike ta cire watch din hannunta da jewelry ta cire doguwar rigar jikinta xata shiga bayi tayi wanka, bude kofar dakin taji anyi ta juya a rikice suka yi ido huda da shi, xaro ido tayi ta durkushe wajen, ya dauke kai ya juya da sauri ya fice daga dakin.Yana fita ta mike da sauri ta rufe k’ofar ďakin, har lokacin jikinta b’ari yake, she wasnt expecting anyone, komawa tayi ta zauna daga bakin gadon hannunta zagaye a k’irjinta duk kunya ya isheta, tafi minti biyu a haka daga baya ta mik’e ta faďa toilet, ta daďe cikin bath tub ďin kamin ta fito, a hankali ta lek’o kanta dan tsoro takeji kamar zataga wani a ďakin, ganin babu kowa yasa ta k’arasowa cikin ďakin, akwatinta na kayan shafa dake gefe ta cicciro waďanda take buk’ata ta shafa ta maidasu cikin akwatin, gown ďin atamfa holland bak’a mai manyan patterns ďin ja da purple ta saka, bata ďaura ďankwalin ba , comb ta ciro daga cikin kayanta ta dawo gaban mirror ta shiga taje gashinta, sai da ta gama ta haďeshi in a bun, tunanin shirya kayanta dake cikin akwati a closet ďin ďakin tayi, bbu b’ata lokaci ta tashi ta buďe closet ďin, tana buďewa taga electric burner a ciki, sai da ta karkaďe k’uran wajen tukunna ta shiga jera kayayyakinta a ciki, sosai ta shiga gyaran ďakin, har bedsheet ta canja wanda ta gani a cikin closet ďin ďakin, cikin lokaci kaďan ta gama gyaran ďakin ta kunna burner ta saka sandal woods, babu abinda ďakin keyi sai k’anshi, sai da taga ďakin ya koma yadda takeso sannan tayi ajiyar zuciya , faďawa tayi kan gadon tana maida numfashi, idonta ne ya faďa kan wayarshi da ya bata dake ajiye kan bed side drawer, hannu tasa ta dauko wayar, ta d’an tabe baki ta shiga gallery duk hotunan Ajiddeh ne wayar wasu da shigar mutunci wasu kuma bbu kyan gani, k’an wani hotonsa da yyi shi kadae yana xaune office ta tsaya tana kare ma kallo, yyi mugun kyau sanye da suit blue da fadin shirt daga ciki, murmushin sa me rikita Ajiddeh yyi a hoton Lol, Batuul tayi tsaki hade da tabe baki ta wuce hoton, wani hoton ta kuma gani yana sanye da farin 3qtr da farar polo, ainahin kyansa ne ya fito a hoton, ita kanta ta san yyi kyau amma hkn bae hanata kyabe baki ba, ajiye wayar tayi ta juya abun ta ta rufe ido kmr me shirin bacci.
+
Abuturrab na fita daga ďakin dama dakinsa ya wuce, direct toilet ya shiga yayi wanka, tsakin da baisan dalili ba ya riqayi har ya fito daga toilet ďin, sweatpant grey da farar shirt ya saka, zama yayi gaban system ďinshi yana dudduba abubuwan da zaiyi, bayan wajen thirty minutes ya mik’e tare da jan ďan siririn tsaki ya fita daga ďakin dan ya fara jin yunwa, ko coffee ne zuwa zaiyi ya haďa kamin ya samarwa kanshi abinda zaici, tunda ya fito daga ďakinshi yakejin wani k’anshi mai daďi, lumshe ido yayi yana shak’ar k’anshin, sauk’a yayi k’asa yayi hanyan kitchen, Ajiddeh na kwance nan inda ya barta ta tasa bowl ďin Tacos a gaba tanaci, ďauke kanshi yayi cike da haushinta ya wuce cikin kitchen, coffee maker ya nufa ya haďa sannan ya fito, sama ya koma yayi hanyan ďakin Batuul don ce mata ta fito ta samawa kanta abinda zataci, tun kamin ya kai ga shiga ďakin yakejin k’anshin nan na daďa k’aruwa, a aljihunshi ya fiddo makulli ya buďe ďakin ya shiga, a figice ta mike daga kwancen da take dan tasan saida ta rufe k’ofarta kamin ta kwanta, lumshe ido yayi ya bude ya shiga bin ďakin da kallo ganin yadda ta gyara shi yayi kyau, abinda dakinsa bae samu daga Ajiddeh ba, tashi tayi daga kwancen da take ta zauna tana kallonshi, kyab’e baki yayi ya k’arasa shigowa cikin ďakin, gashin kanta da yasha gyara yabi da kallo, ita kam wasa ta shigayi da zoben hannunta zuciyanta na bugawa taqi ďagowa ta kalleshi, kyab’e bakinshi ya kuma yi ya ďauke idonshi daga kallonta yana daďa bin ďakin da kallo yace “abincin da zakici sai ance ki fito ki nemawa kanki?, ko dan ki samu na fađa wa Ammah cewa bana baki abinci”, bata ce mishi komai ba kuma bata ďago ta kalleshi ba, sipping coffee ďin dake hannunshi yayi yace mata “in kin gama zaman sai ki sauk’o ki nemawa kanki abinci don baki taho da Cook daga Nigeria ba”, daga nan ya juya har xae fita ya dawo ganin wayarsa gefensa ya dauka, gabanta ne ya fadi tunawa da tayi a gallery take, kunna wayar yyi ya ga hotonsa, kallonta yyi yace “Ohh hotona ma kike kallo knn,” dariya yyi yace “Lallai kina da wahala yarinya, xa ki iya kishi da matata?” Ji tayi kmr ta rusa ihu don takaici sae dae bata iya ta ce masa komae ba, yyi murmushi yace “Ae kam da kin gamu da aiki” daga hka ya fita daga ďakin, bayanshi ta bi da kallo tareda da fadawa kan gado tana kukan takaici.
Ji tayi wayanta na ringing, ta duba taga Aunty ke k’iranta, da sauri ta goge hawayenta cike da murna ta ďaga ta gaida Aunty tace “Aunty har na fara zuwa school yau, Aunty sai kinga makaranta, i couldnt believe it sai da na ganni a lecture hall, da i thought i will never get d chance to study there, but God has other plans, am just happy tun ďazu”, Aunty tayi murmushi daga ďaya b’angaren tace “Ai dama every disappointment is a blessing in disguise, kinga you were sad abt getting married, but God knows best, sai kinyi aure zaki samu kiyi fulfilling dream ďinki”, ajiyar zuciya Batuul ta sauk’e tunawa da tayi auren da tayi ne yayi silar zuwanta makaranta, jiki a sanyaye tace “Aunty its so nice, Nagode”, Aunty tayi dariya tace “godiya kuma, Allah zaki godewa ai”, tace “Ai nagode mishi sosai shima, saura Baba shima zance mishi nagode”, Aunty tayi dariya tace “toh shikenan, kayanki sun iso?”, da mamaki tace “Aunty wane kaya?”, Aunty tace “kayayyakinki mana da kuma su turaren wuta”, tace “A’ah Aunty, ni kawai wanda nazo dashine, sai turaren wutanma ďan kaďan ne”, Aunty tace mata “toh shikenan, in sun iso Abu zai kawo miki, sai ki gayamin”, tace “toh”, hira sukayi da Aunty daga nan sukayi sallama, tana ajiye wayar aka bude kofa, mikewa tayi da sauri sanin shi ne ya dawo, wani mugun kallo yake mata daga bakin kofar ta sunkuyar da kai a hankali tace “Anty ce ta kira ni” juyawa yyi ya bar kofar ta bi bayansa da sauri, downstairs ya sakko tana biye da shi a baya, xama yyi gefen Ajiddeh yana kallonta yace “Kin yi sllh babe?” Xata basa amsa idonta ya kai kan Batuul dan zaro ido tayi kafin ta mike cikin fada ta fara magana “Aliyu meye hka xata wani sakko mani falo da kwalliya hka kmr gidan mijinta? Ohh dama ita ce ta cika min gida da turare hka?” Kallon Batuul da ta k’asa ci gaba da tafiya Abuturrab yyi don shi bae ga wani kwalliya da tayi ba banda kaya da ta sa, xae yi magana Ajiddeh ta ci gaba da masifarta “Toh gskya baxan yi tolerating haka ba, cin arxiki ta xo yi gida na don hka ta bi ni a hankali, daga yau ni kar ta sake sa min turare a gida kuma kar ta kuma sakko min falon miji bbu hijab, idan ba hka ba gskya xa a ga bala’i” murmushi Abuturrab yyi ya ajiye cup din coffesn hannunsa ya kalli Batuul dake tsaye har lkcn a tsawace yace “Baxa ki bar wajen nn ba” juyawa tayi a d’an tsorace xata koma sama, yace “C’mon kin wuce kin yi abinda xa ki yi ko sae na xo kan ki” kitchen din ta nufa hawaye cike idonta, rasa abinda xata girka tayi gashi tana tsoron kar ya shigo ya ganta tsaye, bude deep freezer tayi ta ga kayan miya kala kala da nama, deciding kawae tayi ta soya Irish, tayi sauce kadan, cikin mintunan da basu wuce ashirin ba ta hada abincin ta kashe gas, kan kace me tuni kamshin d’an sauce din da tayi da hanta ya bade gidan, Ajiddeh sae wani yatsine fuska take tana kyabe baki, Abuturrab ya juya ya kalleta yace “What’s that?” Tsaki tayi bata ce komae ba, ya mike ya nufi kitchen din, goge goge ya sameta tana yi ga abincin ta ajiye gefe, juyawa tayi tana kallonsa, kmr baxae ce komae ba sae kuma yace “Iyakar girkin knn?” A hnkli tace “Um!” Tabe baki yyi har xae fita sae kuma ya karaso cikin kitchen din, plate ya dauka ba tare da ya kalleta ba ya nufi inda ta ajiye abincin ta bi sa da kallo, kadan ya dibi Irish din da sauce a gefe, ya daga kai suka hada ido, sauke idonta kasa tayi tace “ya ishe ka hka?” Juyawa yyi yace “Yea!” Snn ya fice, hade rae Ajiddeh tayi tana kallonsa har ya xauna gefenta tace “Haba babe, wnn ae xub da girma ne, maimakon ka fita ka siya ko ka aiki driver” yace “koh? In xa ki ci ki sa hannu mu ci” tsaki tayi ta dauki remote, fork ya dauka ya fara cin abincin, he was so surprise at the taste of the food, bae taba tunanin Batuul ta iya girki hka ba, lumshe ido yyi yana cin abincin, amma sbda bae son ta rainasa bae cinye potatoe din ba duk da bae ishe shi ba ya ajiye, dai dai nn Batuul ta fito bayan ta gama tsaftace kitchen din rike da plate din abincin ta, bata yi gigin kallon inda suke ba ta haura sama. Abuturrab na gama kallon program din da yake kallo ya mike ya haura sama ya bar Ajiddeh nn falon, har xae shiga dakinsa sae kuma ya nufi na Batuul, ya kusa minti biyar tsaye don bae ma san me xae kai sa dakin ba, bude kofar dakin aka yi ya koma baya da sauri duk ya daburce, kallonsa take da mamaki, ba tare da yyi wani tunani ba ya samu kansa da cewa “Tnx!” Sae kuma ya juya da sauri ya nufi dakinsa, bin sa da kallo tayi sae kuma ta kyabe baki ta sauka downstairs, dai dai lkcn da Ajiddeh ta duka ta dauki plate din potatoe’n da Abuturrab ya rage xata d’an d’ana taji taste din girkin da ya cika ma mutane gida, sae a idon Batuul, sake plate din tayi duk da har ta kai daya baki, duk ta daburce.Sunkuyar da kai Batuul tayi ta karasa sakkowa, Ajiddeh ta ji kmr ta nutse wajen don kunya, mikewa tayi tana yatsine yatsinen borin kunya ta nufi kitchen da sauri, hannu ta wanke da bakinta a sink ta shiga kakarin amai, Batuul bata san lkcn da dariya ya subuce mata ba, ta juya da sauri ta koma sama ta dinga tuntsirar dariya a corridor, bude kofa Abuturrab yyi yana kallonta da mamaki, xae yi magana sae ga Ajiddeh kmr xata tashi sama, ganin dariya Batuul take ya sa ta tsaya daga stairs tana huci, Abuturrab ya kalleta ya kalli Batuul da ta k’asa daina dariya ganin ynda Ajiddeh ke huci, a fusace Ajiddeh tayi kanta ae bata san lkcn da dariyar ta koma ciki ba tayi bayan Abuturrab a tsorace tana kiran Anty, ya hade rae yace “meye hka wae?” Lamo Batuul tayi bayansa, a fusace Ajiddeh tace “Honey ni fa take ma dariya hka kmr sa’arta fa?” Juyawa yyi yana kallon Batuul yace “kina da hankali kuwa? Dariyar me kike mata?” Batuul ta turo baki tace “Ni ba da ita nake ba fa” wani kallo ya shiga mata ya fixgo ta daga bayansa yace “ki fadi Dariyar me kike idan ba hka ba I wil slap yhu” sunkuyar da kai tayi don wani dariyar taji na taho mata, ya daka mata tsawa yace “Baxa ki yi magana ba” a hnkli tace “Kaga abincin da ka rage fa naga tana ci a falo kuma tana gani na sae ta shige kitchen ta fara amae….” Bata karasa ba ta shige bayansa ta dinga dariya har da kyakyatawa, dariyar shi ma ya fara yi yana kallon Ajiddeh da ke kikkifta ido, ganin irin dariyar da suke ya fusatar da Ajiddeh tayi bayansa da gudu xata fixgo Batuul, tura Batuul yyi bedroom dinsa da sauri shi ma ya shiga ya rufe, ae tsit kke jin Batuul don ta tsorata ssae, shi kam bae fasa dariyar da yake ba, Ajiddeh kam dakinta tayi hawayen takaici na bin kuncinta tana da ta sanin kallon potatoe’n, kallon Batuul Abuturrab yyi bayan ya gama dariyarsa ya hade rae yace “Xaki yi spelling Doom yau, ba dae dariya kike mata ba” kmr xata yi kuka tace “Wllh ni ban sani ba… Sharrin shaidan ne” sae ga hawaye na bin kuncinta, wani sabon dariyar Abuturrab ya shiga yi, Batuul ta durkushe wajen a sanyaye tana kallonsa don ita har ga Allah tsoron Ajiddeh take, ya shafa kansa yace “Ki tashi mu je ki bata hkuri idan ba hka ba ta kora ki daga gidanta yau” mikewa tayi tace “Toh” ya mike shi ma ya nufi kofa tana biye da shi a baya, yana bude kofan ya juya da sauri yace “Gata nan” a guje Batuul ta juya xata bar wajen cikin rashin sani ta take dogon gown din jikinta, ji kake tim a k’asa ta fadi, wani kara ta saki ta fashe da kuka tana kiran Anty, ya durkusa da sauri ya d’ago ta yana kallon kafarta yace “Ohh sorry!” Kuka take tana yarfe hannu don ji tayi duk jikinta na mata ciwo, ae fa nn ya rikice yana dube duben ko ta ji ciwo, gefen gado ya xaunar da ita yace “Yhu c, me ya kai ki sa kayan da ya fi ki tsayi” kukan ta kawae take bata ce komae ba idonta a runtse, ya galla mata harara yace “Ina ke maki ciwo?” Kneel dinta ta nuna masa, ya daga gown din jikinta idonsa ya sauka kan smooth fresh long leg dinta, k’asa dauke idonsa daga cinyarta yyi don har cinya ya kai rigan, ita kam jin ya daga mata riga kuma bae ce komae ba yasa ta bude ido, da sauri ta janye kafarta daga gabansa ta sauke riganta, ji yyi kmr ya nutse don kunya amma da yake gogagge ne, wayancewa yyi ya mata mugun kallo yace “Don kin samu ina tofa maki addu’a” sae kuma ya mike yace “Idan kin ga dama ki tashi mu je ki bata hkuri” a hnkli ta mike ganin ya fara tafiya ta bi bayansa, suna isa kofa ya juya yaga dingishi take, yace “Meye hka?” Kmr xata yi kuka tace “Ciwo yake min” fixgo hannunta yyi suka koma dakin ya xaunar da ita gefen gado snn ya nufi gaban mirror ya dauko man xafi ya dawo, ya wani hade rae shi a dole Lol, nan dae ya daga mata rigar kuma ya bude man ya diba, ya fara shafa mata a gwiwan, runtse ido tayi jin xafi ta dafa kafadarsa tana kiransa, kallonta kawae yake har ya gama snn ya mike ta bude idonta, ganin ya nufi kofa ta mike ita ma ta bi bayansa da sauri, a hnkli ya murda kofar Ajiddeh Batuul na boye bayansa, xaune ya sameta ta cika tayi fam tana girgixa kafa, yace “Babe!” Wani wawan kallo ta jefa masa, ya gintse dariyarsa ya juya yana kallon Batuul don yasan bata san tare suke ba, a hnkli yace “Baxa ki bata hakurin ba” Batuul kmr xata yi kuka tace “Don Allah Anty kiyi hkuri ni ba da ke nake dariya ba fa” mikewa Ajiddeh tayi da sauri tace “Ohh biyo ni daki kika yi don kin isa?” Batuul tace “A’a kiyi hkuri ni ban san xa ki ji haushin dariyar ba” Ajiddeh tace “Ae sae kin gaya min me kike ma dariya xa ki kwana gidan nn yau” shiru Batuul tayi, hkn yasa Abuturrab ya fara dariyar da yake gintsewa yace “Ta fa baki hakuri Anty” Ajiddeh ta fashe da kuka tace “Aliyu ni na gaji da wnn walakancin naka, na gaji” dariya kawae yake yace “Babe ita fa ba potatoe’n da kika ci ya bata dariya ba, aman da kika tafi kitchen kike yi shi ya sa ta dariya, ko ba hka ba Batuul” a hnkli Batuul tace “Ehh!” Ajiddeh ta kuma rushewa da kuka kmr an aiko mata da sakon mutuwa, me Abuturrab zae yi bn da dariya, dariyar da bae taba yi ba a rayuwarsa, ita kanta Batuul hadiye dariyan take tana lekan Ajiddeh Had’iye dariyarshi yayi ganin kukan da Ajiddeh keyi kamar wacce aka daka ya juyo yana kallon Batuul da tayi saurin gintse dariyarta ta sunkuyar da kai, hannunta ya kamo ya dawo da ita gaban gadon Ajiddeh ya hade rai yace “sake bata hakurin”, a hankali Batuul tace “kiyi hak’uri” jajayen Idonta da suka rine ta dago tana mata wani mugun kallo, kallon Batuul yayi yace mata “Get out”, kamar munafika ta fice daga d’akin, tana fita ya dawo bakin gadon ya zauna tareda janyo Ajiddeh jikinshi, kukan ta sake fashewa da, bayanta ya shiga bubbugawa yace “Hey babe, tace fa ba dake take ba, beside meye Na zuwa da yin amai bayan har ta ganki kinci, ai cemata zakiyi ta zubo miki ma tunda gidanki ne” ya k’arashe maganan yana murmushi, d’ago kanta tayi tana hararansa da rinannun idanuwanta a fusace tace “toh kai dariyar da kake yi ta me? Memakon kayi mata fad’an abinda tayi shine ka biye mata kuna min dariya don walakanci koh”, har lokacin yana murmushi yace “its okay yanxu ai na sata baki hakuri, i will deal with her next time she tries anything stupid thing” d’ago kanta tayi ta sake kallonshi , kai ya kad’a mata yace “i mean it wife, kin ma yi sllhn kuwa” shirun da yaji tayi yasashi gane batayi ba, yace Mata “tashi kije kiyi sllh, I will b back right away” daga haka ya mik’e ya fita
+
Batuul na fita ta wuce d’akinta, kan gado ta fad’a taci gaba da dariya, sai da tayi mai isarta tukunna ta gyara kwanciyarta kan gadon, nan bacci ya d’auketa, bata dad’e da kwanciya ba taji k’iran sllhn wayarta Na bugawa, a kasalance ta tashi dan ba isanta baccin yayi ba sannan baccin bayan la’asar ne, da k’yar ta mik’e ta kashe, ta Shiga toilet tayi alwala, abun sllh ta shimfida ta hau kai, bayan minti biyar ta tashi tayi sllh magrib, nan ta zauna har akayi Isha tayi, daga nan ta mik’e tayi shirin Kwanciya, wanka tayi ta fito ta saka kayan baccinta riga da dogon wando, snn ta koma kan gadon ta kwanta bayan ta rufe k’ofar d’akin, tafi awa d’aya kwance baccin yaqi xuwa mata, babu abinda takeyi sai tsaki, tashi tayi ta janyo system d’inta, in to the bad lands ta kunna zataci gaba da kallo, tura k’ofan d’akin akayi, a tsorace ta d’ago kanta ganin waye , mamaki ne ya kamata dan tasan ta rufe k’ofarta, toh mesa zai wani ce ta dinga rufe k’ofarta bayan yasan he have access to it, d’an murgud’a baki tayi ta sunkuyar da kanta taci gaba da kallo, shigowa yayi ba tareda yyi bother ya kunna wutan d’akin ba, a bakin gadon ya tsaya, yace “Abinci kike jira a siyo maki da baki sakko neman dinner ba, or are yhu afraid of my wife” zumb’uro baki tayi cikin duhun ganin baya ganinta, a ranta tace shi wannan mutumin ina ruwanshi ne da cin abinci na, jin tayi shiru yasa ranshi ya b’aci, a tsawace yace “ba magana nake maki ba”, tsorata tayi ba tare da ta shirya ba ta rufe system din ta mike ta yi kneel kan gadon bata ce komae ba, fixgota yyi tayi ‘yar kara ya dago ta da sauri tun kan ta kai kasa, tsayar da ita yy gabansa ya ciro wayanshi a aljihu ya haska fuskanta, a hankali tace “bana jin yunwa” d’an k’aramin bakinta dake motsawa yabi da ido, hka kawae gabansa ya shiga faduwa yana kallonta, ita kanta faduwa gabanta ke yi a lkcn, duk kamshin turarensa ya cika ta, kashe wutan wayar yyi ta juya a hnkli xata bar wajen ya fixgota ta fado kansa, runtse ido tayi a tsorace tace “Ya Abuu ni bna jin yunwaa” D’ago kanta yyi amma taki bude idonta, kallon lips dinta kawae yake cikin duhun ko kiftawa bae yi, murda kofar dakin aka yi, ya tura ta da sauri ya koma baya, ita kam rawa jikinta ya dau yi, da sauri ta haye kan gado, ya kunna fitilar wayarsa, Ajiddeh ce ta shigo ta tsaya tana kallonsa tace “Wae me kke a nn Babe?” Tana masa tambayar tana kallon Batuul da tayi kmr me bacci, Abuturrab ya juya yana kallon Ajiddeh yace “Erm dama amma ce ta kira wae a bata shine na shigo naga tana bacci” hade rai tayi tace “Toh ita bata da waya ne da sae kai xa ace ka bata” ficewa yyi daga dakin ba tare da ya tanka ta ba, sae dae tunawa da yyi ba mutunci gare ta ba yasa ya tsaya daga bakin kofa yace “Mu je” tsaki tayi ta fito daga dakin. Batuul ta sauke ajiyar xuciya ta mike ta rufe kofarta da key ta dawo ta kwanta.
Washegari Batuul na gaban mirror xaune tana shafa lotion don fitowarta daga wanka knn, taji ana bude kofar dakin, turo baki tayi ta jawo hijab da sauri ta sa, yana shigowa yyi mata kallo daya yace “Daga yau, duk safiya kika tashi kafin kiyi shirin sch ki sakko ki tsaftace gidan gaba daya, snn breakfast da dinner ke za ki dinga yi ba kuma wa cikin ki kadae ba, is dat clear?” Shiru tayi tana kallonsa a hnkli tace “Idan ina da lecture da sassafe fa?” Ya galla mata harara yace “Sae ki tashi da asuba!” Juyawa yyi ya fice, ji tayi kmr ta fara kuka, yaushe ne xata tsaya hada breakfast a gidansu tana da lecture da safe, a sanyaye ta mike ta ciro doguwar riga na kanti pink da adon blue ta sa ta fito, bbu kowa falon ta nufi kitchen, breakfast ta hada cikin kankanin lkci na fried Irish da soyayyan kwae sae ruwan Lipton, ta jerasu kan dinning, ta koma kitchen din ta wanke utensils din da ta bata ta gyara kitchen din ta fito, falo ta shiga nan ma duk ta share tayi mopping ko ina, falon ya dawo yana kyalli, dakinta ta koma, ta kuma shiryawa tayi rolling kanta da plain mayafin kayan jikinta blue, ta shafa chappette a lips dinta ta feshe jikinta da turare, ta fiddo flat shoe dinta ta sa, sannan ta dauki jakarta bayan ta sa wayarta a ciki ta fito falo, har lkcn bbu kowa falon, kallon agogo tayi taga har tara ya kusa, duk taji kmr ta rusa kuka to ta ina xata fara ce masa xata tafi suna dakinsu, ta kusa minti goma tsaye falon wata xuciyar tace kawae tayi wucewarta da kafa tunda bbu nisa sosai, amma ta kasa aikata hakan sbda tsoronsa, hawaye na ya cika idonta sanin da wuya ta samu 1st lecture, tara dai dai ta koma sama ta shige dakinta ta fada kan gado ta dinga rusa kuka kmr yarinyar, tara da minti sha biyar Abuturrab ya fito har xae sauka downstairs sae kuma ya nufi dakinta, har lkcn tana kwance tana kuka, ya karasa cikin dakin ya tsaya daga bakin gadon yana kallonta da mamaki yace “Me ya faru” kauda kanta tayi taki basa amsa, yace “Ke kina da hnkli kuwa ina maki magana kina kauda kai” wani sabon kukan ta fara, ba tare da yyi wani tunani ba ya xauna gefen gadon ya d’agota yana kallonta da mamaki yace “What’s that, what happen?” Still taki cewa komai bata kuma fasa kukan ba, ya dafa kafadunta yace “Talk to me mana, an maki wani abu ne wae?” Ganin ynda ya tsare ta da ido yasa ta shiga girgixa masa kai sae dae bata ce komae ba, jawota jikinsa yyi ya dago kanta ya hade rai yace “Idan baki bude baki kin min magana ba I will slap yhu” ta sauke idonta kasa wani sabon hawayen ya xubo idonta a hnkli tace “Am late, nayi missing 1st lecture” kallonta ya tsaya yi ko kifta wa bae yi, ya dake yace “What made yhu late?” Shiru tayi bata ce komae ba, yace “Yhu are not deaf fa, ansa me now” a hnkli tace “ko ba kai bne!” Bude idonsa yyi yace “Ni?” Kauda kanta tayi ya juyo da ita da sauri ya hade rae yace “daki daya muka kwana da xan sa ki latti? Ohh har kin kirkiro wani karyar da xa ki ma Ammah ki hada ni da ita koh, wae yhu are late! Did yhu sleep in my room ne xaki ce yhu are late or tunda kika tashi yau kin tsinana mu da wani abu ne a gidan nn, No of course u are just busy sleeping” sake kauda kanta tayi ita ma ta hade rae, ya juyo da kanta yace “Kika sake dauke min kai I will slap yhu wllh” rufe ido tayi da sauri, yyi shiru yana kallonta, sauke idonsa yyi kan lips dinta, hka kawae gabansa ya shiga faduwa, ita kanta Batuul faduwa gabanta ya shiga yi idonta rufe, without thinking twice kawae ya samu kansa da kai lips dinsa nata, a tsorace ta bude ido jin soft lips dinsa a nata, dai dai lkcn da suka ji an bude kofa, mikewa yyi da sauri ya k’asa kallonta, ya nufi kofa, suka kusan cin karo da Ajiddeh bakin kofar xata shigo, ae da sauri ya tsotse tsarabar chappette din da ya yo a lips dinsa, ta wani hade rai tace “Wae me kke dakin nn tun daxu Aliyu?” Daburcewa yyi da farko sae kuma ya wayance daga baya yace “Erm naga lkci ya wuce bata fito ba shi yasa na shiga in ga abinda take, nd nd.. I found her crying” Ajiddeh tace “Gskya idan kana son xaman lfya Aliyu ka daina shigowa dakin nn, bana so, idan tana bukatan abu ne ta jira idan muna falo ta sauko ta same mu” barin ta yyi a nn yyi ficewarsa, ta juya tana kallon Batuul ta galla mata hararan tsana tace “Munafuka kawae, ‘yan maula” daga hka tayi ficewarta, ko kadan Batuul bata san me Ajiddeh ta gama cewa ba don har lkcn gabanta bae bar faduwa ba ji take kmr lips dinsa na nata har lkcn. Ta kusa minti sha biyar xaune sae gashi ya dawo, daga bakin kofa ya tsaya ba tare da ya kalleta ba yace “Idan kin ga dama ki fito driver ya kai ki sch” daga hka ya fice, mikewa tayi a sanyaye ta dauki jakarta ta d’an gyara fuskarta kuma snn ta fito.