BATUUL
CHAPTER 4
Suna shiga Tai solarin crescent gidansu ne na uku by the right, maza tayi ta nuna mishi dan sun kusa wucewa, dan tsaki ya ja ya danna horn aka buďe musu suka shiga lokacin 6:50, fitowa tayi daga motan ba tare da tace mishi komai ba, shima fitowa ya bi ta da kallo yace “Dake ni drivern ki ne shi sa c’mon sense din ki bae nuna maki ki bude baki kiyi godiya ba koh” bae jira cewarta ba ya nufi masallacin dake jikin gidan don yin sallahn magriba, tsaki batuul ta ja ta kama hanyar shiga gida a xuciyarta tana cewa “ae ba ni nace ka maido ni ba dae”, shi kam yana zuwa bakin gate ya haďu da k’annen Batuul sun idar da sallah xa su shigo gida, gaisheshi sukayi ya amsa musu da smile a fuskarsa ya k’arasa masallaci, Batuul na shiga ta wuce ďakin Aunty, a kan sallaya ta tarar da ita tana sallah, jiranta tayi sai da ta idar tayi azkars ďinta sannan ta juya ta dubi Batuul, ce mata tayi ” tun ďazu fa Batuul na aiki Baa Liman ya kai miki kayan shine ya fita ya dawo nace yaje yace shi ya manta ma sam da aiken, kuma Baba na nemanshi a office, yanxu nake jiran Ahmad ya shigo ya kai miki wllh”, murmushi tayi ta cewa Aunty “Ammah ce tace a kawoni dan har mai make up tazo” mik’ewa tayi tace “bari inje in ďauki kayan”, Aunty ce tace mata “mu sauk’a k’asa ai kayan ma suna can ba a hawo dasu sama ba” , k’asa suka sauk’a suka k’arasa parlour, akwati ne mai kyau purple da bak’i na victoria’s secret ajiye daga gefe, akwatin ta k’arasa ta ďauka sannan suka fito waje tare da Aunty, “Batuul banda rawan kai a wajen don Allah ki kama kanki, event ďin dare in banda ma na gama makarantane da bazan bari kije ba, kuma duk inda 10:30 tayi ku dawo gida keda Faridan, ku kula da kanku”, “In sha Allah Aunty zamu kiyaye” a tare suka fito compound ďin gidan da Anty, daga gefen gidan k’ark’ashin wani rumfa na bunu mai kyau da hasken wuta ya haska da farin florescent suka hango su Ahmad suna tennis, tsayawa Batuul tayi taga mutumin dake tare da k’annen nata ya rungume hannayensa yana kallon ynda suke buga tennis din with interest murmushi dauke fuskarsa, bata tab’a ganinshi yana murmushi ba sai yau, mamaki ne ya sata tsayawa dan tana ce ma ya tafi, Aunty ce tace “ba Abutturab bane wannan ko shi ya kawoki dama”, juyawa tayi ta dubi Aunty tace “Eh shi ya kawoni” Anty tace “Batuul shine kika barshi a waje ko ruwa ba a kawo mishi ba, ke kam wace irin yarinya ce”, cewa tayi “Aunty ban san zai tsaya ya mai dani ba”, ganin Aunty da yayi ne yasa shi k’arasowa wajensu, a nutse yace “Aunty ina wuni”, da murmushi ta amsa da “lafiya Abutturab, ya gida, mun saka aiki ko, ai bansan kana waje ba da an kawo maka ruwa”, murmushi yayi yace “a ah Aunty ba komai, ai ba aiki bane, kuma inaga bata san bn tafi ba,” ya k’arashe maganan yana kallon Batuul, k’in ďago kanta tayi sai da ya dena kallonta ta ďago, Aunty ce tace “toh maza kuje Batuul karki b’ata mishi lokaci, Allah ya kiyaye”, tafiya sukayi suka isa inda motar ke pake bayan yyi ma Anty sallama, buďewa tayi ta saka akwatin nata daga baya bayan ya buďe da controller hannunshi sannan ta koma gidan gaba ta shiga shima ya shiga ya tada suka tafi, dan tsaki ya ja can kasa a xuciyarsa yace ” Was i even suppose to wait for her” haushin kansa ya ji ssae, ko da yake wasan da kanninta ke yi ya tsaya kallo, yyi assuring kansa, babu wanda ya cewa kowa komai sai wak’an dake playing.
K’arfe 7:20 suka isa gidansu Farida, sauk’a tayi bayan yayi pakin ta zagaya ta ďauko akwatin ta, tunawa da abinda yace mata daxu yasa ta hade rae tace “Na gode” ko kallonta bae yi ba ta ja akwatin ta ta yi gaba, yadda take jan akwatin ya gani kamar ta ďauki wani abun mai girma, ďauke kanshi yayi tare da jan tsaki har yazo ya wuceta ya shiga cikin gida, bayan shiganshi da minti biyu ta shigo janye da akwatin, mai aikinsu Farida, Fanne ce ta k’araso inda take ta karb’i akwatin tace mata “sannu”, da murmushi ďauke a fuskanta tace “yawwa Fanne na gode”, sannan suka hau sama, ďakin Farida suka shiga suka sami Farida an mata kwalliya tayi kyau sosai, blue English gown ta saka da black accessories, tayi kyau ba kaďan ba kasancewarta fara, “Masha Allah kinyi kyau Riri” inji Batuul, murmushi tayi haďe da batting lashes ďinta tace “yeah i know”, bata bi ta kanta ba ta wuce toilet tana dariyan ansa da Faridan ta bata, ruwa ta watsa sharp sharp, ta fito tana tsane ruwan jikinta da towel, mai ta shafa da sauri tazo ta zauna a gaban mai makeup ďin, kayanta ta fara taimaka mata ta saka, red fench floral gown, sannan ta fara mata make up, nude matte lipstick ta shafa mata, sosai Batuul tayi kyau, sai da ta gama da fuska sannan ta saka mata accessories ďinta silver sai red agogo, gashinta ta gyara mata ya kwanto daga gefe, k’asan yayi curls, ba kaďan ba Batuul tayi kyau,
Story continues below
k’arfe takwas da sha huďu suka fito daga ďakin sukayi ďakin Ammah, tana ganinsu tace “Masha Allah kunyi kyau”, a kunyace Batuul ta amsa tace “mun gode”, k’asa suka sauk’o suna jiran mai kaisu yazo, Abutturab ne ya sauk’o daga stairs har ya canja k…
Oops! This image does not follow our content guidelines. To continue publishing, please remove it or upload a different image.
k’arfe takwas da sha huďu suka fito daga ďakin sukayi ďakin Ammah, tana ganinsu tace “Masha Allah kunyi kyau”, a kunyace Batuul ta amsa tace “mun gode”, k’asa suka sauk’o suna jiran mai kaisu yazo, Abutturab ne ya sauk’o daga stairs har ya canja kayan dake jikinsa ya saka ralph lauren shirt da blue sweats, k’afanshi sanye da slippers ďin Fenty, hanyan waje yabi zai fita ba tare da ya kalli palon ba rike da makullin motarsa, mabuďi k’ofan ya buďe zai fita yaji Ammah na cewa “Abuu, don Allah ga su Farida nan zaka ajiyesu a Tulip creek ktunda kai ma fita xaka yi, 8 ma ya kamata su tafi amma yanxu har 8:30, kuma bana so suyi driving da kansu, dare yayi”, bai juyo ba saida yaji ta gama, shi bai ma san mey zai cewa Ammah ba, amma ransa yyi mugun baci, wato dae yau shi ya xama drivern wa ennan yaran, cewa kawai yayi “toh” snn ya sa kai ya fita kmr xae tashi sama, tashi sukayi suka bi bayanshi, har bakin k’ofa Ammah ta rakasu tace musu kar suyi dare kamar yadda Aunty ta faďawa Batuul, hasken dake filin gidan ne ya haska Batuul, sai ya k’arawa accessories ďin jikinta glitters, ďago kanshi yayi zai duba ko sun fito idanunshi suka sauk’a kan Batuul, tsayawa yayi yana kallonta da gashinta da yasha gyara sosai iska na swaying ďinshi, yadda take tafiya yake kallo a hankali kamar baza ta k’araso inda motar take ba, wani takaici ya turnuke shi ya danna horn da karfi, Farida ce ta fara zuwa, shiga motan tayi ta zauna a gidan baya, ganin babu yadda Batuul ta iyane yasa ta shiga gaba dan ďazu ma ce musu yayi shi ba driver ďinsu bane, k’anshin turaren Batuul ya nuna mishi cewa ta iso, ya dubesu su biyun ya daka masu tsawa yace “ina kuke tunanin zan kaiku haka da gashi a buďe kmr wasu mahaukata, ku fice min a mota kuje ku rufe kanku kuma kar wacce ta b’ata min lokaci, it seems kuna wasa da ni ne yau, duk gidan nn a rasa Wanda xae dinga yawo da ku a mota sae ni”, Farida ce ta b’ata rai tace “Yaa Abu toh Ammah ma bata ce komai bafa, kuma ma ai baza mu daďe ba”, harara ya jefa mata ta mirror ba shiri ta bude mota ta fita da sauri, Batuul dai batace komai ba dan ranta ya gama b’aci saura kaďan tayi kuka , ta buďe k’ofa zata fita ita ma Farida tace “bari in dauko mana” hkn yasa ta koma ta xauna, kafin farida ta dawo Abuturrab ya ja tsaki fiye da sau goma, ita dae Batuul kanta na kasa sae wasa take da xoben hannunta, Farida na dawowa ta mi’kawa Batuul k’aramin jan gyale ita kuma bak’i, suna yafawa yaja motar suka tafi, hanyan Tulip suka bi, sai da ya tsayar da motan ya ce musu “duk iskancin da xa kuyi ku tabbatar by ten kun gama” Farida ta dan turo baki ta amsa mishi da “okay” suka fita daga motan suka shiga Cikin hall ďin event ďin, wajen ya haďu sosai kowane table kujerun mutum biyu ne da sunayensu a jikin kujerun, Badman bin ladin da Runtown ne akan stage suna wak’ok’insu na Mad over you da controlla, anata ihu, Affan da Farida kujeransu ďaya , kujeran Batuul ne kawai ita kaďai, sai kuma na waďanda suka je wajen rawa, suna zaune ana ta yin abubuwa har aka iso lokacin bada award, Batuul ce ta cinye cutest da most classy, Farida most beautiful, Affan kuma Ladies Man da most expesinve, bayan an gama raba sauran awards ďin ne mutane suka hau wajen rawa.
Gidansu Massa Abutturab yaje, sai da ya fara shiga cikin gida , Maman Massa ya tarar zagaye da mutane a falonta da ma’aikatan gidan, gaishe shi suka farayi tun daga bakin k’ofa, k’arasawa yayi ya tsuguna dab da k’afanta yace mata “Yaa Mera nda dubdo”(ina wuni Yaa Mera), kanshi ta shafa tace “Baanyi wushe” (lafiya Babana), ya shirye shiye”, shi ya manta ma gaba ďaya da aurenshi nan da sati uku, sai da ya tuno shirye shiryen mey take nufi sannan yace “Alhamdulillah Yaa”, “Masha Allah” tace sannan ya mik’e yace “bari in duba Massa Yaa”, tace “toh Babana, sai ka fito”, mik’ewa yayi ya tafi chamber Massa, tura k’ofar ďakin yayi ya shiga tare da sallama, su biyu ya gani a zaune suna playing game a tv, tsakin sallamar shi da basu amsa ba yayi, inda socket ďin ďakin yake ya wuce directly ya kashe, tsayawa sukayi suna kallonshi da mamakin yaushe ya shigo, Massa ne yace mishi “Man final tournament fa muke bugawa ka kashe”, bai ce mishi komai ba sai da ya samu waje a kan gado ya zauna sannan yace “sai kace yara kun rik’e controller kuna ta game, nayi sallama babu wanda yayi responding a cikinku” ya sake jan k’aramin tsaki, a tare mazan Massa da ďayan suka dubi juna suka sa dariya, dubansu yayi yaga dariyan mey sukeyi sannan yace musu “abin yi ne baku da” ya ciro wayanshi daga Aljihu, ďayan ne ya koma daga gefen Abutturab yace mishi “ai gaskiya ka faďa, mu yara ne sosai ma, kai da zaka zama ango next few weeks ai kam ka zama babba”, harara Abutturab ya jefa mishi yace ” kuyi mana kuma auren, kun zauna kuna abun yara har ana yin sallama bakwa ji”, Massa ne ya dubi wanda ke gefen Abutturab yace mishi “Abba faďa mishi ai jira muke manya su fara yi sai mu bisu a baya”, dariya ma suka bashi yace “Ku kuka sani, mu munyi gaba”, haka suka ci gaba da hira suna tsokananshi, sai 10:30 ya tuna da su Farida, mik’ewa yayi cikin hanzari yace “shit”, binshi sukayi da ido suna so ya gaya musu abunda ya faru, kallonsu yayi yaga duk shi suke kallo , ce musu yayi “wlhy su Farida na kai wajen prom kuma nace by ten ya kamata in je na manta”, Massa ne yayi maza yace “yawwa i wanted to ask you that girl, k’awar Farida ce ko, she is damn pretty, she is so densed, she is …..” , bai k’arasa ba Abutturab yace mishi “Hey meye hakan, k’awar Farida ce fa, yarinya ce fa kake cewa she is so densed, yarinyar da bata fi sixteen yrs ba, yarinyar Aunty cefa”, da ido suka bishi ganin bai tab’a shiga maganan y’an matansu ba, fita yayi daga ďakin bai ce musu komai ba
A Tulip bistro yaje yayi parking, wayanshi ya ďauko yayi dialing number Farida ba a ďauka ba, sai da ya k’ira wajen sau goma ba a ďauka ba, buďe k’ofan motan yayi ya fita daga ciki ya shiga cikin hall ďin, fuska a tamke ya shiga hall ďin ya tarar ana ta hayaniya, Farida ya hango a kan stage ita da wasu friends ďinsu suna zazzaune a zagaye sunyi round suna playing truth or dare, rasa ya zai yi ya k’irata yayi dan ko yayi ihu ma baza taji ba, Batuul ya hango daga gefe ta zaune ita kaďai a kan kujera da awards a kan table ďin da take tana danna waya, deciding yayi kawai yaje yayi mata magana ta k’ira Farida su tafi, inda take ya k’arasa ya sunkuyo daidai kunnenta zai yi mata magana dan yasan ba lallai taji ba in ya tsaya yi mata maganan kuma bayason su b’ata mishi lokaci, k’anshin turaren da taji ne ya sata saurin ďagowa , heart beat ďinta ya k’aru, waigowa tayi da sauri suka kusa cin karo, zata mik’e ya sa hannu ya maida ta, tsayawa tayi tana kallonshi a tsorace, shima fuskanta ya tsaya kallo yadda lights ďin ke haska stones ďin jikinta sai ya k’ara mata kyau, lkci daya kuma ya hade rae, hannunta ta motsa alamar ya sake mata, sake mata hannunta yayi yace mata “Go and call your friend , ina jiranku a waje”, juyawa yayi ya fita daga hall ďin, mik’ewa tayi bayan ya fita jiki a sanyaye ta isa inda Farida take tace mata “Yaa Abu na jiranmu a waje”, fita Batuul tayi bayan tayi sallama da mutane ta isa inda motar ke pake, shiga tayi ta zauna daga baya, ta ďago idonta kenan zata ce mishi Farida na fitowa suka haďa ido huďu ta mirror, maza tayi ta ďauke nata tace mishi “tana fitowa” a hankali, Tare da Affan Farida suka fito kamar ka su rabu, sallama sukayi ta shige gaba dan horn ďin da Abu ya danna, direct gida ya wuce dasu, suna shiga gida suka wuce ďakin Ammah suka ga tayi bacci, a hankali suka jawo mata k’ofan suka wuce nasu, kayan jikinsu suka cire sukayi wanka, sukayi sallah isha, bayan sun ďanyi hiran event ďin yau suka kwanta bacci
THREE WEEKS LATER
A firgice Batuul ta tashi daga baccin da take tana ambaton sunan Allah…..
THREE WEEKS LATER
A firgice Batuul ta tashi daga baccin da take tana ambaton sunan Allah (a uzu bikalimatillahi tammat, min sharri ma khalaq, bismillahi llazi la ya dduru ma’as mihi shay’un fil ard wa la fis sama’i wa huwal aliyul azim), zama tayi akan gadonta, gumin da ya tsatsaffo a fuskanta ta sa hannu ta goge, mamakin irin mafarkin da tayi yau tayi, tasan mafarkanta na tsoro basa wuce macizai amma na yau daban ne, mik’ewa tayi tabi hanyan toilet ta shiga, ruwa ta watsa tareda alwala ta fito, hijab ďinta ta ďauka ta saka sannan ta shimfiďa abun sallah ta hau ta fara nafilfili, bayan ta idar sosai tayi addu’a Allah ya kare ta daga sharrin abun ji da na gani sannan ta ďauko Quraninta daga kan bedside drawer ta karanta, sai da ta gama karanta suratul Anbiya’ da Hajj sannan ta duba agogo taga k’arfe biyar, zama tayi a kan abin sallah ta ci gaba da addu’o inta har aka tada sallah a masallaci ta mik’e tayi raka’ataynil fajr tayi sallah asuba, tana idarwa tayi azkars ďinta na safe sannan ta mik’e ta cire dogon hijab ďin dake jikinta ta ninke shi tare da abun sallah ta maidasu inda ta ďaukosu, gadonta ta koma ta kwanta, sai da tayi addu’a dan ta tsorata ďazu sosai sannan ta ja bargon ta rufe jikinta dashi ta kwanta, bata tashi ba sai sha biyu saura, ta mik’e taje tayi wanka ta saka wani riga da skirt k’arami mai kyau bata ďaura ďankwalin kayan ba sai hula kawai da ta saka a kanta, k’asa ta sauk’o bayan ta gama shafa mai, babu kowa a gidan, a ranta tace mayb mazan sun tafi ball ko tennis ďinsu na jaraba, Aunty da Yusra kuma na gidan biki, sai da taci abinci sannan ta koma palo ta ďau remote ta canja favorite tashar ta star plus, mik’ewa tayi ta koma sama dubo wayanta, missed calls uku ta gani, ďaya na Aunty biyu na Farida, Aunty ta fara k’ira, tana ďauka tace “Hello Batuul, mun fito kina bacci, ki shirya a kawoki gidan bikin , Farida ma na ta tambayanki”, sai da Aunty ta gama tace “Aunty kaina ke ciwo tun da na tashi, bana son zuwa saboda hayaniya”, da damuwa Aunty ta ce mata “kinsha magani Batuul”, “eh”, tace sannan ta ce mata “ki kula da kanki sai mun dawo, zan k’ira su Janet a waya in faďa musu suna dubaki” sannan suka katse wayan, suna gamawa tayi dialing number Farida, Farida na ďauka tace “wane irin bacci kikeyi haka har na k’ira twice bakiyi picking ba”, ce mata tayi “wayan fa yana ďaki ni kuma ina k’asa, toh meye ma na k’irana da sassafe , ke da ake hidima a gidanku”, “ai hidiman ne ya sani k’iranki, wlhy gidan ya cika da mutane , babu daďi, am coming over to your place”, kamin Batuul ta sake magana ta katse wayan,
A Protea hotel dake asokoro suke zaune, vip apartment suka kamawa abokanansu da suka zo ďaurin aure, hira suke ana ta tsokanan ango, bai ce musu komai ba, kanshi ya dafa ya rik’e da k’arfi dan wani ciwo yake mishi sosai kamar zai rabe, wayanshi ya ďaga ya k’irawo Massa dake cikin sauran abokan nasu, ďagowa Massa yayi yaga mesa yake k’iranshi bayan suna zaune a tare, ganin ya rik’e kanshi ne ya sashi tashi ya isa wajenshi, tambayanshi yayi bayan ya rik’e hannunshi da ya rik’e kan nashi dashi “Aliyu lafiya naga ka rik’e kanka, meke damunka”, a hankali yace mishi ka kaini gida kaina na ciwo”, tare da mik’ewa yayi hanyan k’ofa, binshi Massa yayi a baya yace “toh ai gidanku ma da hayaniya, muje in munga doctor sai mu wuce gidanmu ka kwanta, stress ne yayi maka yawa”, sai da suka je bakin k’ofa Abba ya ce ina “ina kuma angon zai tafi, tun ďazu yake b’ata rai yayi shiru yana ta tunani, saura fa kaďan ka k’ara hak’uri mun kusa kawo maka ita”, sauran ne suka sa dariya suka ci gaba da shak’iyancinsu, Massa ne ya dubesu yace “am sorry dan Allah zamuje mu dawo, Abba call me if ana needing wani abu”, lokacin har Abutturab ya fita shima ya bishi a baya, sai da suka biya Nisa hospital aka duba shi aka yi mishi prescribing drugs sannan suka ďau hanyan gida, a hanya Massa yace mishi “Man i told you stress ne ke damunka, these days tunaninka ya cika yawa, mey ke damunka”, Abutturab ne yace mishi “kafi kowa sanin auren nan is a compromise, yes i like her but myself being married is just out of it”, Massa bai ce mishi komai ba dan likita yace ya huta sosai so baya son ya dameshi dayawa, concentrating yayi a tuk’inshi har suka isa gida, a parlourn chamber Massa ďin ya kwanta a ďaya daga cikin dogayen kujerun, Massa ne ya mik’o mishi maganin yasha ya sake kwanciya, tambayanshi yayi “in faďawa su Ammah baka ji daďi bane ko kuma ya za ayi”, hannu ya ďaga mishi alaman a ah sannan yace mishi “yanxu Ammah zata tada hankalinta a kan ďan wannan abun, i will get better before event ďin yau”, ya sake juyawa ya kwanta ďaya bangaren nashi, wutan ďakin Massa ya rage mishi yace sannan ya fita
Story continues below
Batuul bata fi minti talatin da waya da Farida ba sai gata a gidan, mik’ewa tayi daga kwancen da take ta ce mata “woh Farida , you can be in planet Mars ke ďinnan, yaushe mukayi waya dake da har zakice min kin iso”, dariya Farida tasa tace “toh ai ni ďin kenan”, zuwa tayi ta zube a kan kujera tace, “kinga gidanmu kuwa, ba ni akewa aure ba amma nafi masu aure wahala, hatta ďakina ya zama ba nawa ba, gaba ďaya gidan ya zama wani iri, jiya ma sai a wajen Abui na kwana, bazan iya ba, ga y’an Ndjamena nan da sa mutane aiki kamar babu y’an aiki a gidan”, dariya maganan ya bawa Batuul tace “Lazy you, toh dama ai hakane if ana biki a gidanku sai kayi hak’uri, baki da k’anne da anyi suna a gidanku tun lokacin zaki gane yadda abun yake, lokacin sunan Aabid fa har cubicle ďin toilet ďina sai da aka fasa, bare naku biki, bikin ma na first child ďin gidanku ai sai hankali”, ce mata Farida tayi “as in baza ki gane ba, toh aiken kuma na meye, ni ďaurin auren nan da zasu tafi maiduguri ma ya fi min komai daďi, su tafi gidan ya koma normal”, “ai ba matan bane zasu ďaurin aure, maza ne zasuje a ďaura su dawo” inji Batuul, baki ta zumb’uro tace “ni dama auren Yaa Sadiq ne ma da sauk’i, amma Yaa Abu fa, ga matar ma ba shiri nake da ita ba, tayi ta wani girman kai, mutum babu komai sai tsayi da fari, kina ganin duk tsayin Yaa Abu fa da kaďan ya fita, ni ďazu ma kamar naji Ammah na cewa wai a dawo da boxes ďin lefen da aka kai mata tunda sunce sunyi kaďan, 40 boxes fa wai sai an k’ara musu ya zama sixty, shine Ammah ma tacewa su Aunty Amna da suka kai su dawo dashi”, girgiza kai Batuul tayi tace mata “ke dai kullum Yaa Abu, toh yanxu dai zai bar muku gidan”, da sauri Farida ta mik’e daga zaunen da take tace “Ai ni daďin da nakeji ma bayan auren da sati ďaya zasu wuce UK, life will be better, babu sa ido”, dariya Batuul tayi ta ďan dungure mata kai tace “ni tashi muje muyi alwala muyi sallah”
Wayan Farida ne yayi k’ara , dubawa tayi taga Ammah ke k’iranta, amsawa tayi tare da cewa “Hello Ammah”, katseta tayi tare da cewa “Farida kina inane tun ďazu ina nemanki, ina kika shiga”, “muna tare da Batuul ne, gidansu nazo”, ce mata tayi “ke da waye kikaje gidansu Batuul ďin”, a hankali tace “Baa Alai nasa ya kawoni”, “toh yanxu zan turoshi zaizo ya ďaukeki kuje gidan Yaa Mera, zaki karb’o min sak’o”, inji Ammah, da sauri tace “toh” dan murnan ba a yimata faďan fitan da tayi ba a sani ba, ta katse wayan, juyawa tayi ta dubi Batuul taga tana kallonta tana murmushi, ce mata tayi murmushin mey kike min haka, “ashe Ammah bata sani ba kika fito, da tayi miki faďa sosai ai”, murguďa mata baki tayi tace “yanxu ma aikena tayi, ni a gama wannan auren mu huta, ki shirya muje mu karb’o sak’on”, Batuul ce ta dube ta tace mata “in shirya muje ina?, ke ni babu inda zan fita yau, kije ki dawo”, marairaicewa Farida tayi tace “haba mana, you know i love you, you love me too, muje tare kinji, i will get you pack of twix da Raffaello pls”, dariya ma ta bawa Batuul tace “Noooo, dagaske babu inda zan fita, beside Aunty ma bata gida bare in tambayeta”, Farida bata cewa Batuul komai ba ta shiga dialing number Aunty da wayan dake hannunta, Aunty na ďaukan wayan tace “Hello Farida ya akayi”, cewa Aunty tayi, “Aunty muna tare da Batuul ne Ammah ta k’irani ta aikeni, nace ta rakani wai tace baza taje ba saboda bakya gida, Aunty kiyi hak’uri muje, gidan Yaa Mera ne, bana so in tafi ni kaďai”, dariya Farida ta bawa Aunty tace mata “kice nace ta rakaki, wani ihu Farida tasa tace “Nagode Aunty, yanxu zamuje mu dawo”, ta katse wayan, tsayawa Batuul tayi tana dubanta, ya zatayi da Farida ne a rayuwa, k’in kulata tayi ta tashi ta hau sama ta ďau wayanta ta bugawa Aunty, tana ďauka tace “Aunty kunyi waya da Farida yanxu ko”, Aunty ce tace mata “ehh yanxu ta k’irani, ki rakata Batuul kuje ku dawo”, toh kawai Batuul tace ta katse wayan, Farida ce ta biyo ta ďakin tace “zamuje ko Batuul”, hararan wasa tabita dashi, tana dariya tazo ta zauna a gefenta tace “ai nasan you cant do without me”, suna zaune har Baa Alai yazo yace mata ya iso su fito su tafi, mik’ewa sukayi, k’aramin bak’in gyale kawai Batuul ta ďauka ta yafa akan hulan dake kanta da wayanta suka fita, Batuul ce ta shiga gaba Farida ta zauna daga baya, har cikin gidan ya shigar dasu yayi parking suka fito su biyun, suna fita Batuul ta rik’ewa Farida hannu tace “Farida ya fara”, kallonta Farida tayi tace “mene ďin ya fara?”, “heart beat ďina mana, its increasing, am telling you ppl, its becoming serious”, ce mata Farida tayi “sorry anjima sai mu faďawa Aunty”, bata amsa mata ba dan ita kaďai tasan abunda take ji, tafiya sukayi mai ďan nisa tukunna suka isa cikin gidan, har ďakin Yaa mera suka isa, tana ganinsu tayi murmushi tace har kunzo, “wannan ba Batuul ba”, da mamaki Batuul tace “ehh nice” dan batasan matar ba, matar ce tace mata “Masha Allah kin girma, tun kina 2yrs rabona dake, mamanki na gidan biki ko”, da ehh Batuul ta amsa mata sannan Farida tace “Yaa, Ammah ce ta aikomu wai muz….” bata k’arasa ba tace mata “ehh kuje da Ya bawa ta nuna miki inda ake aikin kiga ko sun gama” ta haďa ta da Baiwa ďaya suka tafi, Batuul na zaune tare da Yaa mera tana tambayanta abubuwa har na makaranta, tace mata sunyi graduating yanxu university zasu shiga, wayanta take ta dannawa tana sawa a kunne sai ta cire, Batuul ta duba tace mata “Batuul”, a hankali ta ďago daga wasan da take da zoben hannunta ta dubi yaa mera tace “na’am”, “chamber ďin Massa zakije ki duba min shi inata k’iranshi baya ďauka, intercom ďinshi ma baya ďauka kuma ya shigo ďazu, ki ce mishi ina k’iranshi”, bata sa komai a ranta ba ta mik’e tace “ta ina ďakin yake”, kwatance tayi mata “tace in kin fita ki mik’e sai kin wuce dorms uku, chamber yana by the left”, ta amsa da toh ta fita, a hankali take tafiya har ta isa ďakin, knocking tayi taji ba a buďe ba, a hankali ta tura k’ofan ďakin taga babu haske, sai ďan dim light daga ciki, kai ta sa ta shiga cikin ďakin, k’anshin da taji ne ya sata jin kamar zuciyanta zai faďo dan bugawa, tsayawa tayi a spot ďin da take ta kasa gaba ta kasa baya
Tsayawa tayi tana juye juyen ina zata bi, kawai deciding tayi da ta fara sallama ko zai jiyota inma a ciki yake, sallama tayi ta yi taji ba a amsa ba, lalube ta fara ko zata ga switch ďin ďakin har ta gama lalubenta bata ga komai ba, deciding tayi toh ta k’ira sunanshi ko zai amsa, “Massa” ,shiru tayi tana jira taji ko za a amsa amma taji shiru, sau uku tana k’iran sunan taji ba a amsa ba kawai ta juya zata fita ta ga kamar mutum na kwance a kan seater, k’arasawa tayi wajen seater ta tsaya ta tabbatar mutum ne kwance a kai, broad figure ďinshi na kwance peacefully amma bata ganin fuskanahi dan ya juya mata baya, sake k’iran sunan tayi taji bai amsa ba, deciding tayi ta tab’a shi tunda baccin nashi ya kai har haka nauyi, hannu ta sa a goshinshi taji wani ďumi da laushi, maza tayi zata ďauke hannunta taji wani hannu mai laushi da faďi a kan nata, wani abu ne taji gaba ďaya yabi jikinta ga heartbeat ďin ya fara aikin nashi kamar mai shirin fitowa, idonta ya cika da hawaye tab saura k’iris ya zubo, tsayawa tayi still a wajen ta kasa ko da k’wak’waren numfashi, juyowa yayi ya jawota ta kusa faďawa kanshi tayi hanzari ta dafa kujerar, wayanshi ya ďauko daga gefenshi, flash light ya kunna ya haska yaga ko wacece, idonta ta rintse da ya haska flash light ďin a fuskanta, hawayen da ya taru a idon ne ya silalo ta ido ďaya, tsayawa yayi yana kallon cute face ďinta , k’aramin lips ďinta idonshi ya sauk’a akai, yadda hawayen ya gangaro har kan cute lips ďin yabi da ido, ita dai tana tsaye ta kasa motsi, idon ma bata buďe shi ba dan bata san ma ko waye bane, tashi yayi daga kwancen da yake ya zauna har lokacin bai sake mata hannu ba, sai da ya zauna ya fara mamakin, ya akayi tazo gidannan, kuma mey ma ya kawota har ďakin nan, k’ara janyo hannunta yayi ta fad’a k’irjinshi , a lokacin ta buďe idonta, wara idon tayi ganin wanda ke rik’e da hannunta a gabanta, ihu ta buďe baki zata kurma yayi maza ya toshe bakinta, ce mata yayi “shut up, and tell me y you are here” tare da fixgo ta ta k’arasa gabanshi, sai da yaga kyarman da jikinta keyi ya ragu sannan ya sake mata baki da hannu, mik’ewa yayi ya isa wani waje ya kunna wutan ďakin, gaba ďayanta ya duba tun daga kai har k’asa sannan ya koma ya zauna a kujerar da ya tashi, tambayanta ya sakeyi, “mey kike yi a ďakin nan har kika zo kina tab’a ni”, kasa magana tayi dan gaba ďaya ta tsorata da ganinshi, tsawa ya daka mata “yace ba magana nake miki ba kinyi shiru kina kallo na, sai da ta tuna da sunan wacce ta aikotan sannan jiki a sanyaye tace mishi “Yaa mera ce tace in zo nan chamber in k’ira mata Massa, i didnt know inace kaine Massa, kuma ďakin ne da duhu shine nace bari in tashe shi, kayi hak’uri”, gaba ďaya ta gama tsorata da ganinshi, juyawa tayi zata tafi yayi maza ya fixgota, ce mata yayi “tab’a min fuskan kuma na meye”, “innalillahi wa inna illaihi rajiun ta ambata a zuciyanta, ba ta faďa mishi tashin Massan zatayi bane kuma da duhu ita bata san ma fuska bane, cikin dakewa tace “ďakin ne da duhu, ban san fuskan ka bane” warce hannunta daga ruk’on da yayi mata tayi ta fita daga ďakin a guje, sunanta ya k’ira amma ko sauraronshi bata yi ba tayi tafiyarta, ranshi ne yayi mugun b’acin k’in amsawa da tayi, tashi yayi ya shiga toilet dake bedroom zaiyi wanka
Sai da ta iso k’ofar ďakin sannan ta tsaya ta daidaita numfashinta, ganin ta samu nutsuwa ya sata tura k’ofan ďakin a hankali, da sallama ta shiga ta zauna sannan tace “Yaa Mera , Massan baya nan” kamar kar ta faďa mata taga Abu sai kuma tace “amma naga Yaa Abu a ďakin yana bacci”, jin ance Abutturab na ďakin yasa ta cewa “ohh shi yana gida, toh dama ai dan shi nake neman Massan, yau zasuyi wushe wushen ko?”, ta tambayi Batuul, ďago kai Batuul tayi tana dubawa ko wani ake tambaya, da ta ga babu kowa a ďakin sai ita ya tabbatar mata da ita Yaa Mera ke magana, ” No, ni ban sani ba fa Yaa, bansan mey zasuyi yau ba, sai dai in Farida ta shigo mu tambayeta” inji Batuul, Yaa Mera ce ta sake cewa “ai tunda ma yana gidan bari in k’irashi yazo in ganshi muyi magana dashi”, mamakin matar takeyi kamar ba sarauniya ba, babu ruwanta, ita ko bayi ma bata ajiyewa kusa da ita gata da fara’a, ga kyau, kammansu ďaya da Ammah, Abutturab ďinma dasu yayi kama, hasken sune kawai bai ďauko ba sai yayi duhun Abui, su Farida da Sadiq ne sukayi kama da Abui amma suka ďauko hasken Ammah, tana zaune tana ta zancen zuci Farida ta shigo da plate ďin kisre da miyar kub’ewa da yaji kaji, gefen Batuul taje ta zauna ta cewa Yaa Mera “Yaa sun iya kisren sosai, kamar fa da engine sukeyi , ya burgeni yadda sukeyi shiyasa ma na ďebo kaďan, Batuul ci kiji”, Yaa Mera ce tace “shiyasa mamanku tace sai anan za ayi, yanxu ma daga nan za a kwasa akai gidansu matar Abun”, ido Farida ta wara tace “Yaa drums dayawa fa akayi, kuma duka za a kai musu, wannan matar ta Yaa Abu suna yi bada wasa ba”, dariya ta bawa Yaa Mera tace mata “al’adanmu kenan Farida, haka mukeyi in zamu aurar da yara”, cewa Farida tayi “lallai, su suka sani”, taci gaba da cin abincinta, lura tayi da Batuul bata ci tace “meye kika sani gaba, kici mana”, harara Batuul tabita dashi tayi magana a hankali yadda Yaa Mera baza taji ba “ce miki nayi inajin yunwa, ki gama mu tafi ni”, Yaa Mera ce ta ďago taga Batuul ďin bata cin kisren, ce mata tayi “Batuul bitti, beri bei” (Batuul y’ata, kici abinci), a hankali ta amsa da “toh”, sannan ta matso tasa hannu a cikin plate ďin
Story continues below
Yana fitowa daga toilet ďin bayan yayi wanka da alwalar la’asar, wayanshi ya ďaga ya k’ira Massa, yana ďagawa yace mishi ” Kana inane”, Massa ne ya amsa da “muna tare dasu Imran a Protea, ya kan naka, yayi sauk’i”, ce mishi yayi “Yeah sosai, ina jiranka kazo ka ďaukeni”, sannan ya katse k’iran, kaya ya saka cikin sabbin kayanshi da suke gidan da ya ďinka na biki, bayan ya gama ne yayi sallah la’asar, yana idarwa wayarshi tayi k’ara, ďauka yayi yasa a kunne, “salamu alaikum, Yaa Mera nda dubdo”, ehh ina gida, toh bari in sauk’o sannan ya katse wayan”, sosai yayi kyau da kaftan ďin da ya saka, ya ďaura hula akanshi sannan ya fita, side ďin Yaa Mera yayi, da shiga ya samu waje ya zauna ya sake gaisheta, Farida ma gaisheshi tayi , bayan ya amsa ne Yaa Mera ta dubeshi tace “yau ne wushe wushen naku ko”, kai ya gyaďa tare da amsa mata da “ehh”, ce mishi tayi “wane time za ayi?”, “k’arfe bakwai ne zuwa sha ďaya”, “toh yanxu kace musu su shiryata k’arfe biyar, anan za ayi mata kéla tul kamin ku wuce wajen wushe wushen, zamu tura musu mota, daga nan zamu kaita wajen, har kaya zamu bata ta saka, mun gama magana da mamanka”, cewa yayi “okay Yaa, In sha Allah zan faďa mata, sai ta faďa a gidan nasu” , sallama yayi da ita ya mik’e kenan zai yi hanyan waje yaga an buďe wani k’ofa, k’ofan yabi da kallo, Batuul ce ta fito daga ciki hannunta rik’e da hand napkin tana gogewa, ta cire gyalen dake yafe akanta ďazu sai hular kawai, idonta dake kan abinda ke hannunta ta ďago suka yi ido huďu, wani irin abu taji gaba ďayanta, shima tsayawa yayi kallonta, idonta ta ďauke daga kanshi shima yayi k’wafa ya fita daga ďakin
k’iran Massa ne ya shigo wayanshi, recieving yayi yace mishi “ka iso ne?, toh gani nan fitowa”, motar da Massa ke ciki yaje ya buďe ya zauna , Massa ne ya tambayeshi “ya jikin dai Man, wannan rashin lafiyan ai sai ya bari ba dai akwanakin nan ba, kai da kake shirin zama ango da dai ya isa wani wajen, yayi wrong timing gashi da yake ka fishi k’wari kayi fighting ďinshi”, kallon Massa yayi da ďan murmushi a fuskanshi ya girgiza kai yaci gaba da danna wayarsa, “Hello”, yace bayan ya an ďauki wayar da ya buga ďin, amsa akayi da “Hello baby, am missing you over here, ya gajiya dan ni gaba ďaya na gaji so nake kawai a ďaura auren nan mu tafi mu huta dan ba k’aramar gajiya nakeji ba a jikina, yanxu ma a ďaki nake ni kaďai wai za a min gyara….”, yasan idan ya barta taci gaba da magana sai ya manta dalilin da yasa ya k’irata, katseta yayi yace “gajiya Alhamdulillah, ki faďawa su Mum za ayi miki kéla tul before a tafi wushe wushen a gidan Aunty ďina, kuma kayan wushe wushen ma daga can zaki sa, zan aiko mota by 5, you should be ready”, ce mishi tayi “Aliyu gaskiya waďannan abubuwan naku na al’ada na gaji dasu, tunfa last week ake ta yi, kuma kayan ma mum ta riga da tasa an siyomin a turkey, ni gaskiya a bar wannan ďin kawai, ai anyi sauran, kuma ma its too late yaushe zan faďa musu su shirya”, ranshi ne ya fara b’aci, cikin dakewa yace “wani shiri zakuyi, ce miki nayi zan aiko mota ki taho ke kaďai, kuma in kin faďawa mum ďin nasan ba hanaki zatayi ba”, tsaki yaja dan ranshi daďa baci yayi yace “in na aiko da motar kar kizo” ya kashe wayan , Massa ne ya dubeshi yaga ranshi ya b’aci yace “lafiya naga kana tsaki”, tsakin ya kuma ja yace mishi “yarinyar nan , tun last few days nayi observing that duk abinda na faďa sai ta canja, ce mata fa nayi yanxu zan turo driver a kaita gidan Yaa, take cemin ita baza taje ba”, bai ci gaba ba Massa ya dafa kafadmďanshi yace mishi “Man its okay, zata dena in sha Allah”, da haka suka canja hira, hotel ďin sukaje yaga abokananshi dayawa sun sake k’aruwa, sai da ya ďan huta yake tambayan Massa, “gobe what time za a tafi ďaurin auren Maiduguri”, “sunce flight ďin goben k’arfe huďu ne , so muna da time da in mutane suka k’aru za a yi musu booking tunda da yamma ne”, “okay” kawai yace mishi suka shiga cikin abokanan
Ganin ya katse wayan ne ta tsaya ta k’urawa wayan ido kamar wanda sukayi wayan dashi ďin zai fito, Mesa Aliyu yake min hakane take tambayar kanta, jibi nefa ďaurin aurensu amma kawai dan ta faďi magana ya katse mata waya harda cewa in ya turo motar kar tazo, ai gaskiya ta faďa tun kwananki suke ta yi musu abubuwa wai al’ada, shi kuma kawai sai ya ďau fushi, a ranta take cewa “dan yaga inasonshi ne yake wasu abubuwan”, k’wafa tayi ta cewa mai yi mata gyaran jikin zata je ta dawo, matar tace mata babu komai sai kin dawo, fita tayi daga ďakin, tun daga bakin k’ofa gidan cike yake da y’an uwa d abokan arziki, matane kyawawa, farare da gashi kowa taci kwalliya an zuba gwalagwalai, ďaďďaya zaka bak’i a gidan nan, tana tafiya mutane na ta gaisheta wasu ta gaishesu cikin yarensu shuwa, wani ďaki ta buďe ta shiga, ďakin babba ne mai kyan gaske, babu mutane a ciki sosai, daga Mum , sai wata mata da zatayi sa’ar Mum sai Yaa zee, k’arasawa tayi ta zauana daga gefen mom, matar kawai tace wa “Jainaba inta afe”, matar ce tace mata “afe selai Ajiddeh, ya shirye shirye, da gajiya”, tace gashinan fa na gaji sosai, ina su Attutu, Abba Mahammad da Adum”, ce mata tayi “suna gida bamuzo tare ba anjima za a kawosu”, juyawa tayi ta dubi mum da ke jiranta ta gama ta faďa mata dalilinta na fitiwa ana mata gyaran jiki, ce mata tayi “Mum yanxu Aliyu ya k’irani wai zai turo a ďaukeni k’arfe biyar a kaini gidan k’anwar mamanshi, wai akwai wani abu da zasu yi min daga can zamu wuce wajen wushe wushen, kuma ma wai kayan da zan saka ma su zasu bani”, cikin ďaga murya Mum ta fara magana “nifa Abun nan nasu Hajiya Bilqees ya isheni, wace al’adarsu ce bamu gani ba fara bikin nan, ni sanin da nayiwa Hajiya Bilqees ma ba kanuriya bace amma gaba ďaya dan tana auren kanuri ta canja gaba ďaya, a ina ake wani kéla tul a Ndjamena, kuma da suke cewa su zasu baki kayan kisa ai ganin kasawarsu ne yasa muka ce zamuyi miki , ko ďari mukace muna so ai yaci a kawo miki, kinfi k’arfin akwatuna arba’in, ba dan Babanku yace a bari ba kuma zai sab’awa duk wanda ya tada maganan wlhy da sai an maida musu tunda dama cewa tayi a dawo dashi in muka k’i karb’a”, Yaa zee ce tace “Mum ai ita tabi ta liqewa yaron kamar babu wani namiji a duniya sai shi, ni gaba ďayanshi bai min, sai girman kai da uake dashi kamar mutumin da”, matar da aka k’ira da Jainaba ce tace “toh ku yanxu menene na tada jijiyoyin wuya, ai damu suke zancen , ku bari kawai a gama bikin zasu shigo hannu, tayi yadda yace ďin, anjima in ya turo driver kije, tashi kije a gama miki gyaran kamin lokacin yayi”, da haka ta mik’e ta koma ďakin, tana zama ta k’irashi, ansawa yayi shiru yana jiran yaji mai zata ce mai zata ce mishi, cewa tayi “Hello baby, toh mey na kashe wayan, in ka shirya ka turo motan na faďwa su Mum sunce inje”, ce mata yayi “okay yayi kyau, by five zaizo”, ya katse wayan
K’arfe shida na yamma Aunty ta dawo gida lokacin har Batuul sundawo, a palo ta zauna ta k’irawo wayan Batuul tace mata ta dawo, sauk’owa tayi mata sannu da zuwa, zama tayi daga gefenta tace “Aunty ya gidan bikin”, ce mata tayi “lafiya Batuul, masha Allah , gobe zasuje Maiduguri ďaurin aure, har Baba ma zaije, amma shi sai ranan ďaurin auren, jibi kenan”, baki Batuul ta tab’e tace Allah ya basu zaman lafiya”, “Amin” tace sannan tace mata tace “yaushe kuka dawo ne”, “tun three thirty suka sauk’eni a gida ita kuma Farida ta wuce gida”, ta sake cewa “Aunty maganan admission ďin nawa kunyi da Baban, time yana wucewa”, Aunty ce tace “ni na manta ma Batuul amma yau zamuyi maganan in sha Allah , Allah dai yasa kar in manta, “Amin ta amsa da sannan suka mik’e a tare sukaje yin sallah dan an fara k’ira, Batuul na ďaki bayan ta idar da sallah ta zauna tana game a Macbook ďinta, Yusra ce ta shigo tace mata “Yaa Batuul, Mama tana k’iranki tana ďakinta”, cemata tayi “kice ina zuwa”, ta juya ta fita, tana fita ta ďauke Macbook ďin akan cinyarta ta mayar gefe, mik’ewa tayi tabi bayan Yusra, da sallama ta shiga ta tarar Aunty tana duba abu a closet ďin kayanta, k’arasawa tayi cikin ďakin tare da sallama ta zauna aka makeken gadon ďakin, cewa tayi “Aunty gani”, sai da gama dubo kayan da take nema sannan tace wa Batuul “kije ki shirya zamu tafi wushe wushen Aliyu, k’arfe 8 zamu fita, kije maza ki shirya”, da sauri Batuul ta ďago kanta tana kallon Aunty, ganin Aunty ko noticing kallon da take mata ma batayi ba yasa ta cewa “Aunty wushe wushe kuma, nifa bazan je ba , tun ďazu ma na faďawa Farida, kuma ma ban shirya bafa”, ba tare da Aunty ta kalleta ba tace “ki tashi kije shirya, jama’a sai tambayana ina kike akeyi, wasu ma cewa suke ni ke hanaki fitowa bayan halinki ne na k’in jama’a yake hanaki shiga taro, ki tashi kije ki shirya” tana faďa mata tana warware laffayan da ta ďauko, baki Batuul ta zumb’uro ranta a b’ace ta mik’e ta fita, ďakinta ta isa ta zauna akan gado gaba ďaya ranta a dagule, toh ita wane kaya ma zata sa , bayan angon ma ba son mutane yake ba shine za ace wani sai anje bikinshi, mik’ewa tayi ta shiga toilet ta watsa ruwa ta fito, zama tayi shafe jikinta da mai sannan ta isa closet ďin kayanta ta ciro abaya ďaya a hanga na Al layl mai kyau da purple crystals a jiki ta sa, gashinta ta taje ta k’ara parking ďinshi sannan ta shafa powder ta saka kwalli a idonta da chappete a bakinta, turarenta masu k’anshi ta fesa ta sauk’o k’asa tana jiran Aunty, Aunty na sauk’o zata cewa ďaya daga cikin masu aikin ya k’ira mata Batuul ta ganta zaune a palo, ce mata tayi “Batuul bana son iskanci, kina jina, ince kije ki shirya shine zakije ki wani sako min doguwar bak’ar riga, dama naga ranki bai so ba shiyasa dole ki b’ata min rai ko?, toh ki wuce kije ki canza su kuma karki b’ata min lokaci, mik’ewa Batuul tayi tace “Aunty bansan kayan da zan saka bane”, “duk kayanki kice min kin rasa na sawa, ba wushe wushe bane, ai kina da dongashua da zaki saka, ki wuce kije ki canja ki dena b’ata min lokaci”, rafiya tayi ta haura sama ,kaya ta canja ta saka shadda duck mai blue da bak’i, ďinkin riga robe da straight skirt, ta ďauko k’aramin jan gyale ta yafa, ta saka sark’a da ďan kunne suma ja da abun hannunsu, shoe Rack ďinta ta nufa ta ďauki slippers ďinta louis vuitton mai ja da bak’i ta saka, tayi kyau sosai har ta fi da, sauk’owa tayi, Aunty batace mata komai ba tayi hanyan waje, Batuul ma ta bita a baya, mota Aunty ta buďe ta shiga, Batuul ma ta shiga gidan gaba, Fa’iza da ke rike da Aabid suka zauna a baya itada Yusra, Aunty ke tuk’a motan suka ďau hanyan inda za ayi event ďin, parking sukayi a wajen parking ďin motoci , suna fitowa daga mota, sautin kiďa ke tashi a wajen, tana fitowa daga mota wata rolls royce ta danno kanta wajen, daidai fuskan Batuul motan ya haska, tsayawa tayi mai motan ya gama iskancinshi na haske mata ido sai ta tafi dan bata gani, su Aunty har sunyi gaba sun barta, k’ofan motan aka buďe, iska ne ya buso mata k’anshi turaren, kanta ta ďago dan tasan mai turaren, kashen wutan motar akayi tana ďaga ido, fuskan Abutturab idonta ya sauk’a akai, ba kaďan ba yayi kyau, kaftan sky blue ya saka, yayi kyau sosai, shades ďin ray ban ne mak’ale a idonshi, gani tayi yana tahowa hanyanta, tsayawa tayi ta kasa motsi sai bugun da zuciya ya fara
Aunty(Mama) haka k’annen Batuul ke k’iranta
Ganin yana nufota ne tayi maza ra rik’e rigan cikinta, ray ban glass ďin dake fuskanshi ya cire , ido huďu sukayi da Batuul, kasa ďauke idonta tayi daga kallonshi shima hakan bai ďauke nashi ba, sai da ya iso har inda take sannan ya tsaya, idonta ta ďauke daga kallonshi shi kuma yaci gaba da kallon nata, a hankali ta sake rik’on da tayiwa riganta, ya buďe baki kenan zaiyi mata magana ta juya a guje ta bar wajen, ranshi ne yayi bala’in b’aci ya daka mata tsawa, ” *Batuul*”, ko juyowa batayi ba taci gaba da gudunta, sosai ranshi ya b’aci, ba sau ďaya ba yanxu tana mishi irin haka sai yana mata magana ta gudu, tunawa yayi da ranan da ya fara ganinta ranan idi, haka ya buďe baki kenan zai ce mata ta gyara gyalen kanta, gashinta na a waje tak’i ko da tsayawa jin mey zai ce mata ta gudu, ko ďazu ma haka tayi mishi ta gudu daga ďakin yana k’wala mata k’ira, inda tabi ya kafawa ido yana daga tsaye, ji yayi an dafashi ta baya, Massa ne ya zagayo gabanshi yace mishi “Yanxu amarya ta k’irani wai suna ciki tun ďazu, sun jiramu bamu zo shine suka shiga”, juyowa yayi ya dubi Massan sannan yace “toh mu shiga”, shi da tawagar sauran abokanshi da kana ganinsu kasan dagaske suke suja k’arasa ciki, fili ne babba zagaye da canopies sai kujeru daga ciki biyu aka kasa wajen, side ďin amarya da gefensu, k’awayenta da dangi, sun sha ankon atamfa maroon, sunyi kyau sosai kasancewarsu farare, ďayan side ďin dangin ango ne suma da ankonsu na irin kayan da Batuul ta saka, daga gefe side ďin amarya ne da ango anyi musu rumfan fulawa da kujeru biyu, mutanene cike a wajen wasu na zaune wasu na kai kawo, Kamal da Mansur ne daga tsakiya rik’e da mic suna ta rero wak’a, ganin ango da abokansa sun shigo ya sa mawak’an k’ara kaimin wak’arsu, k’anshin turaren wuta ke tashi ta ko wane angle,tuni wajen ya kaure da hayaniya, k’awayen amarya aka fara k’ira suyi rawa da danginta, sun shiga sun tattaka rawa sosai sannan aka k’ira Family ďin ango, Batuul na zaune ita da Farida duk ranta a b’ace, gaba ďaya bata so Aunty ta sata zuwa wajen nan ba, ta k’agara ayi abinda za ayi ita ta koma gida, k’iran y’an uwan angi ne ya sa Farida mik’ewa zata shiga wajen rawa tare da janyo hannun Batuul, warce hannunta tayi daga rik’on da Farida tayi mata tace “mey haka kike jana, mey zan tashi inyi miki”, “rawa mana baki ji an k’iramu bane, ai ni komin rashin shirinmu da Yaa Abu sai nayi rawa, ba namu bama munyi bare na gida”, ta faďa tana dariya, “A dawo lafiya”, inji Batuul ta sunkuyar da kanta taci gaba da dannan wayanta, Farida ganin dagaske Batuul take ya sata juyawa ta shiga filin rawa, rawa sosai su Farida sukayi da sauran family, sai da suka gama lokacin aka k’ira ango da amarya su fito suyi rawa, mik’ewa sukayi a tare shi da Ajiddeh, sosai tayi kyau, bak’in lace ta saka da blue laffaya, anyi mata kéla yaskè(kitson gaba) da aka bi akayi mishi ado da gold sai ya k’ara mata kyau, ko ina a jikinta gold ne , har anklet sai da ta saka na gold da nose ring, hannayensu mak’ale cikin na juna suka tasi suka isa filin rawar, mutane ne suka shigo ana ta yi musu lik’i, abokan ango dollars, Euros suke zubawa amarya, sau ďaya Batuul ta ďago kanta ta kallesu ta mayar, wayanta ne taga yana ringing, Aunty ke k’iranta, jutawa tayi ta dubi inda Aunty ke zaune taga tana mata alama da tazo da hannu, tashi tayi ta isa inda Aunty ke zaune, sai da ta zauna a empty kujeran dake gefen Aunty sannan tace “Aunty gani”, jakanta ta ďauko sannan ta ciro bandir ďin 1000 sabbi dal ta mik’awa Batuul, da ido Batuul tabi kuďin tana jira taji na meye na “Kije kiyiwa ango da amarya lik’i, ni bana son tashi saboda da Aabidĺ, Batuul gaba ďaya bata yi zaton abinda Aunty zata sata yi ba kenan, ranta ya b’aci amma ba tayi musu ba dan bata son b’atawa Aunty rai kamar ďazu, kuďin ta ansa sannan ta mik’e Kamar mai shirin yin kuka rai b’ace ta isa inda suke, y’an dubu dubun nan ta rik’a cirowa tana yiwa amarya lik’i dashi, wani mugun harara Ajiddeh tabi Batuul da, daga k’arshe ma barin wajen tayi ta koma daga gefe wajen danginta, Batuul bata sanma tana yi ba, kuďin da yake hannunta tabi da ido, ko rabi bata lik’a ba, juyawa tayi ta dubi Abutturab taga idonshi na kanta, sauri tayi ta ďauke nata idon, Aunty ta sake waigawa ta duba a inda take zaune taga tana kallon wajensu, babu daman ta bar wajen, kawai kuďin ta fara zara tana yiwa Abutturab lik’i da, ido ya kafa mata yana kallon yadda tayi kicin kicin da fuska tana b’ata rai, Massa ne ya hango Batuul tana yiwa Abutturab lik’i, zuwa yayi inda take ya fara mata ruwan dollars a kanta, gaba ďaya sauran abokan ango ma hankalinsu kan Batuul, lik’i suka dinga yi mata kamar itace amaryar, ba k’aramin haushi Ajiddeh taji ba, ji take kamar ta shak’e yarinyar nan ta huta, gaba ďaya bata sonta , hankalinta sam bai ďauki Batuul ba, wani irin b’ata fuska Abutturab ya rik’a yi ganin yadda abokansa ke yiwa Batuul lik’i bayan ga amaryar basu yi mata ba, niyya yayi yaje yace su dena wannan shirmen, A guje Batuul ta sake kuďin hannunta a jikin Abutturab ta fice daga filin dan ta tsorata sosai da yadda dukkansu ke mata lik’i ita da bama rawa tayi ba, wajen zamanta ta k’arasa ta zauna, tana zama Massa ya bita shima ya zauna a kujerar Farida dake gefen nata, wani irin murmushi yayi mata yace “Fatima ko”, kai ta gyaďa mishi ba tare da ta ďago ta dubeshi ba, k’anshin turarenshi duk ya cikata har yana neman sa mata murya, juyawa tayi ta dubi inda Aunty take taga hankalinta baya ma wajensu, ita masu rawa take kallo, “masha Allah”, yace sannan yace “ranan grads ďinku i wanted talking to you sai kuma ban samu chance ba, you know kin burgeni, ni ban tab’a sanin Su Baba nada yarinya babba haka ba sai ranan graduation ďin da naji sunanki, kin tab’a sanin Aunty ce ta yayemu ni da Aliyu, ina zaki sani ai ba a haifeki bama lokacin”, ďagowa tayi ta dubeshi , toh ita mey ruwanta da Aunty ta yayesu, ina ruwanta ma in a gidansu aka haifeshi shi da Aliyun, juyar da kanta zatayi taga idon Abutturab a kansu rai a b’ace, ďauke idonta tayi taci gaba da wasa da awarwaron hannunta, “Cutie, it seems your mind is totally not here, mayb you should share your contact with me, sai muyi magana anjima, nima ďin yanxu am busy”, dariya ne ya kusan kufce mata na sunan da ya k’irata dashi wai cutie, da har zata bashi number ta na da sai kuma ta tuna ai zai iya tambayan Farida ma ta bashi, deciding tayi da ta bashi natan , ai ba lallai ne in ya k’ira ta ďauka ba, karanto mishi tayi numbers ďin ya rubuta a wayanshi, mik’ewa yayi tareda kai hannun zai shafi fuskanta rayi maza ta matsa da baya, idon Abutturab akansu duk abunda sukeyi yana kallonsu sai ma harara da yake binsu da, tashi yayi zai fita daga filin ranshi b’ace, Massa ne ya hango shi zai fita yayi maza ya cewa Batuul “Aii cutie we will talk later”, yayi maza yabi bayan Abutturab yaji lafiya zai fita ana cikin event, daga waje ya tarar da shi wajen da sukayi parking motoci, zuwa yayi yacewa Abutturab”Ya ka fito ka bar amaryarka a ciki, ana ta event, wato halinka ko a ina sai ka nun…..”, bai k’arasa ba ya katse shi da “Mustapha what is wrong with you, for Gods kaga abinda kuka dinga yi a wajen nan, duk kun wani juya kuna yiwa yarinya lik’i bayan amaryar ma baku yi mata wanda kukayiwa yarinyan nan ba, kuma da ta bar wajen ka wani bita a baya , wannan ai neman raini ne a wajen yara, mey zaka nema a wajen Batuul yarinya k’arama, k’annenmu nefa, y’ar Aunty ce inma baka sani ba toh ka sani, k’anwar kace”, kasake Massa yayi yana kallonshi, wannan faďa da yake yi kuma na meye haka, ce mishi yayi “toh menene in k’anwata ce ko kuma y’ar Aunty ce, ai nan nema zanyi yadda nakeso ko akwai inda aka hanani nemanta, kuma right from day one na faďa muku ni k’aramar yarinya zan aura, manyan mata wannan sai ku, kuma Batuul is d right choice for me saboda abinda ya fara min tarbiya shi yayi mata tarbiya dan haka ana gama bikinka zan kai nawa maganan gaba sai dai in itace tace bata sona” ya faďa yana maida numfashi, wani irin kallo Abutturab ya bishi dashi ya rasa mey zai ce mishi, tsaki yaja ya koma cikin wajen Massa ya bishi a baya
Story continues below
Yana barin wajenta ta sauk’e ajiyar zuciya, ďazu a wajen lik’in nan taji an k’irashi da Massa, da ma shine, tab’e baki tayi a ranta tace toh wannan ne prince , ai surutunshi yayi yawa, dama Abutturab ďin ne prince zai fi dan shi yafi ji da kai, ku kuka sani dai, dama sune take ganin pictures ďinsu a album ďin gidansu suna yara , baki ta tab’e tace ku kuka sani dai,
Mik’ewa tayi daga indactake zaune ta isa wajen Aunty, marairaicewa tayi kamar zatayi kuka tace “Aunty, ciwon kan ďazun fa ya dawo, insaso in je gida”, dubanta Aunty tayi sannan tace “baki sha magani bane ďazu”, da sauri ta kaďa kai, “nasha, mayb effect ďinshi ne ya sakeni, inaso in sake shan wani”, Aunty bata sake cewa komai ba ta ďaga waya ta k’ira Ahmad, yana amsawa tace “ga Batuul nan zaka kaita gida, kanta na ciwo”, bayan ta katse wayan ta cewa Batuul “ki tashi ku tafi, Allah ya sauwak’a, in kuma zaki iya ku bi ta asibiti Dr zaka ya dubaki”, cewa tayi “toh Aunty bari muga idan na sha na yau ďin bai yi ba sai mu tafi gobe ya dubani”, da haka ta mik’e tayi hanyan waje, a bakin k’ofa tazo zata fita shi kuma zai shigo suka kusa bugewa, matsawa tayi da sauri kar ya bugeta dan taga ranshi duk a b’ace, tsayawa yayi kallonta har sai da ta wuce, Massa ne da ya ganta ya fara smiling, “Cutie ia zuwa”, sunan da yaji ya k’irata dashine yasa shi saurin juyowa, tsayawa yayi yaji mey zatace, a hankali kamar mai raďa ta ce mishi “kaina ne yake ciwo za a mayar dani gida”, baiji mai tace ba, haushi ya sake turnuk’e shi yaja tsaki ya shiga ciki, tsakinshine ya jawo hankalinsu suka dubeshi, su sunace ma ya tafi, da damuwa Massa ya dubeta “let me drop you mana”, “No brother na yana jirana shi zai kaini, nagode” tace ta juya ta bar wajen bata sake ce mishi komai ba, a mota ta tarar da Ahmad yana jiranta, buďewa tayi ta shiga ta zauna, with concern yace mata “sannu Yaa Batuul”, ta amsa da “yawwa muje”, dan so take ta bar area nan gaba ďaya, rage Ac motar yayi sanan ya tada suka tafi
A kujera ya tarar da Ajiddeh ta cika tayi fam, yana zama ta dubeshi tace “Aliyu dama wushe wushen naku kenan, muzo a wulak’anta mu”, tunda ta fara magana bai ce mata komai ba sai da yaji ta ambaci wulak’anci, katseta yayi tareda da tambayanta “wulak’anci mey aka yi muku”, “ehh mana wulak’anci mana , dubi fa yadda abokanka da yan uwanka suka dinga yiwa bak’ar yarinyar nan lik’i kamar itace amaryar, da kunsan ita kuke son yiwa lik’in kaje ka aureni, ai da an aura maka ita sai kuji daďin yi mata lik’in da kyau, wani kallo ya bita dashi da ya sata haďiye magananta da sauri, “mey ke damun kankine wai, wa yace miki ana faďa min ko wane irin magana, ba ni ba ko mutum dake kusa dani bana yadda a faďa mishi magana anyhow bare ni da kaina, da kike cewa a aura min ita ai da naso tare za a haďa min dake akai min ku ko kuma in fasa nakin in aureta, sai ki rik’a yin magana kamar yarinya, jibi ne ďaurin aurenmu inma zaki gyara tun wuri ki gyara dan bazan yi tolerating shit ďinnan a gidana ba, you have change”, ya faďa yana mai kallon agogon hannunshi, duk maganan da sukeyi a hankali suke yin shi kamar masu yiwa junansu hiran soyayya
Batuul na isa gida ta hau sama, wipes ta ďauka ta goge abinda ke fuskanta sannan ta shiga tayi wanka tayo alwalar isha ta hau abin sallah, tana idarwa ta cire hijabin jikinta ta ninke shi ta ajiye a gefe, ko hula bata ďaura akanta ba ta sauk’o k’asa dinning dan yunwa takeji, kwanukan wajen ta shiga buďewa, plate ta jawo ta ďebi white rice da stew sai potato salad, ďakinta ta tafi da abincin sannan ta zauna taci a a nutse, tana gamawa ta buďe fridge ďinta ta ďauki ruwa tasha, sai da ta gama abubuwan da zatayi tahau gado ta yi addua ta kwanta, bacci nebmai nauyiya ďauketa, can cikin bacci wajen k’arfe goma sha ďaya ta jiyo murya kaman na Farida, a hankali ta buďe idonta taga Farida tsaue kanta da wannan wide smile ďin nata tana kallonta, ta kunna hasken wutan, Aunty ce ta shigo ďaki tana tambayan Farida “tayi bacci ko, watak’ila kan ne ya ďan saketa”, ganin Batuul ta farka ne ya sata cewa “ya kan Batuul, yayi sauk’i”, a hankali tana goge ido tace “ehh Aunty yayi sauk’i nasha analgesic “, da Masha Allah ta ta amsa sannan tace mata “Allah ya k’ara lafiya” tayi musu sai da safe ta fita, kallon Farida Batuul ta tsaya yi, “You didnt tell me you were coming over”, baki Farida ta buďe da mamaki tace “toh ko in koma ne, wannan tambaya haka da ake jeho min”, bata cewa mata komai ba taja bargonta ta rufe kanta ta kashe wutan daga gefen gadonta, Dariya Farida tayi bata ce mata komai ba sai da taje tayi wanka tayi sallah ta canja kayan bacci, wutan ďakin ta sake kunnuwa tayi tsalle ta hau gadon, Mik’ewa Batuul tayi ta dubi Farida tace mata “meye matsalanki wai”, tashi Farida tayi daga kwance da take tace “my problem is i love you so much”, tsaki Batuul taja zata koma ta kwanta ta farida ta janyota “kinsan na faďa miki dama gida ya isheni, wait ma, keh da na barki kina yiwa ango lik’i sai nemanki nayi na rasa, Allah kinga yadda kika yi kyau a wajen kamar kece amaryar sai lik’i ake miki , ko amarya ma ba ayi mata ba, Yaa Massa ne ya fara miki ai ko sunace kece amarya har Pounds an zuba miki, mehn i enjoyed that part”, “Allah Farida ke ko, yanxu dan wannan kika tada ni, Allah ya shiryaki”, wayanta ta jawo ta k’ira Affan, yana ďagawa kamin yace komai tace “Bestfriend com and carry your girl, tun ďazu take damuna ta hanani bacci”, ce mata yayi “bata wayan, mik’awa Farida yayi, zama tayi tana jira ta gama wayan, amma har bayan minti talatin basu gama ba, da taga basu da ranan gamawa ne ta jawo bargonta ta kwanta
K’iran Ajiddeh ne ya fara shigowa wayanshi, ansawa yayi tare da yi mata sallama, “salamu alaiki zawjati”, tare da wani irin murna takeji kamar ta ganta a gabanshi, wani murmushi ta saki haďe da cewa “baby an ďaura, am officially yours now”, murmushi yayi tareda girgiza kanshi yana mamakin Ajiddeh ko kaďan bata jin nauyinshi ko kunya, “In sha Allah forever” yace, zata sake magana kenan yace wasu mutane suka zo yi mishi murna, ce mata yayi “hold on wife, zamuyi magana anjima, am busy over here”, da murnan sunayen da ya k’irata yau ta katse wayan, gaisawa yayi da mutanen dake gabanshi, jama’a sai k’aruwa sukeyi suna mishi murna tare da yi mishi fatan alheri a rayuwan aurenshi, walima suka wuce daga wajen ďaurin auren a state hotel, k’arfe ďaya suka gama walimarsu suka wuce airport daga nan, a airport sukayi azahar gaba ďayannsu, 1:45 sukayi boarding plane, k’arfe uku dai dai sukayi landing a Nnamdi azikiwe international airport dake Abuja, basu isa gida ba sai biyar saura, a gajiye ya shiga bayan an gama kai mutane masaukinsu,
Bayan su Batuul sun gama cin abinci, wajen k’arfe uku Aunty ta ce su shirya suje gidan Ammah, ita yau baza ta samu zuwa ba, in sunje su gaisheta kuma zasuyi waya, dan gudun magana Batuul ko attempting saka abaya ma batayi ba, wani peplum blouse da skirt na atamfa ta saka, ta samu k’aramin pearl pebdant ďinta da stud masu kyau suma ta saka, ta ďauki k’aramin mayafi ta yana a kanta, Addua take a gama bikin nan ko zata huta da yawo, Baa Liman suka sa ya kaisu, k’arfe huďu suka isa gidan, gidan a cike yake da mutane kowa nata hidima, gaishesu suka rik’a har suka isa ďakin Ammah, basu sameta ba a ďakin ba, ďakin Farida sukaje , da sauri Farida ta janyo k’ofar dan kamar ba ďakinta ba, side ďin Abui ta jawo hannun Batuul sukayi tana cewa Batuul “ni in zanyi aure baza a zauna a gida ba, dubi fa gidan kamar ba shi ba kuma fa masu aiki na ta gyara amma kamar basayi”, “dama haka taro yake, sai an kwana biyu zakiga gidan ya koma daidai”, suna isa side ďin Farida ta murďa k’ofan ta shiga, Ammah ta tarar ita da Aunty Amna suna zaune a ďakin bak’i na side ďin Abui tana yi mata bayanin wani abu, ga robobi nan manya manya a gabansu cike da kaji da snacks, k’arasawa sukayi daga ciki, Farida ce ta fara gaida Ammah da Aunty Amna, sai Batuul, bayan ta amsa gaisuwan ne tacewa Batuul “Bitti sai yau na ganki tunda aka fara bikin nan, lafiya bakya zuwa”, kai ta sunkuyar sannan tace mata “Ammah ina zuwa, shekaran jiya ma naje wushe wushe”, ” toh yayi , madallah, ďazu tela ma ya kawo kayanku na dinner na sa a ďinka muku, sai kuyi shiri anjima kuje kunji”, toh kawai Batuul tace amma ba wai dan ta saka zuwan a ranta ba, suna zaune su Ammah kuma nata bayanin yadda za a kai kayan nan gidan amarya, mik’ewa Farida tayi ta fita, shigowa tayi ita da wata yarinya ďauke da plates a hannayensu na abinci, ajiyewa tayi ta zauna yarinyar kuma ta fita, cewa Batuul tayi ta taso suci abinci, mik’ewa Batuul tayi tazo kusa da ita ta zauna, ďan kwalin dake kanta ta cire ta ajiye daga gefen gadon sannan suka fara cin abinci, sallama akayi a k’ofa, Sadiq ne ya shigo ďakin , sai da ya gaida Ammah da Aunty Amna sannan ya zauna, Ammah ce ta dubeshi tace “kun dawo Sadiq, ya hanya, anyi lafiya babu matsala dai ko”, kai ya girgiza tare da cewa “Alhamdulillah Ammah kunyi k’ok’ari mutane kamar turo su akayi a wajen ďaurin auren nan, komai ya tafi lafiya”, cewa tayi “Alhamdulillah , dama haka nake son ji, Allah ya sanya Alheri, Allah ya basu zaman lafiya” dukkansu suka amsa da Amin, Farida ce tace “Yaa Sadiq shikenan yanxu Yaa Abu zai bar zama a gidanmu, shikenan daga nan sai kai gidanmu zai zama daga Abui sai Ammah sai ni, zanyi abinda nakeso”, dariya ma ta bashi yace mata “zama gadin gidan zakiyi ashe, ai nima sai kin rigani barin gidan nan, waye ma zai barki ki zauna, next year kema by now munje maiduguri har mun dawo”, b’ata rai tayi tare da zumb’uro baki tace “Ammah kin ga Yaa Sadiq ko”, kamar ba ita ta fara hiran ba, “Sadiq ka dena damun ta tana cin abinci”, mik’ewa yayi yace “Ammah bari inje in dawo”, tace “okay sai ka dawo”, Batuul ji tayi sun birgeta, inama tana da yaya itama, amma irin Sadiq ba iri Yaa Abu ba dashi bama a ganin dariyanshi, Sadiq na fita yayi hanyan su ya haďu da ango, tsaidashi yayi yace “Abui ya shigo gidane naganka a side ďunshi, ce mishi yayi “No Ammah na ciki, daga wajenta nake, yace “okay let me get to her”, k’ofan falon Abui ya buďe, yana saka k’afa Batuul dake ciki taji gaba ďaya ta zama restless, bugun zuciyan ya fara, a hankali ta rik’a tauna abincin dake bakinta, k’ofar ďakin da suke ya tura ya shigo, cak komai ya tsayawa Batuul dan batayi expecting ďinshi ba at this time, k’anshin turarenshi ya cika ko ina na ďakin, da sallama ya k’araso ďakin ya zauna a gefen gado, Gaisheda Ammah yayi sannan ya gaida Aunty Amna tana ta yi tsokananshi, Farida ce ta gaisheshi , ba yabo ba fallasa ya amsa mata, sau ďaya ya kalli inda Batuul take ya ďauke kanshi, ita dai bata ce mishi komai ba gashi nan dab da ita ya zauna, xame hannunta tayi daga plate ďin ta cewa Farida ta k’oshi, ccewa Ammah yayi “Ammah béri manyin, (Ammah inason abinci) banyi breakfast ba yau throughout bare inci lunch ga yamma tayi”, Aunty Amna ce tace “wannan duk ďokin zama angon ne ya hanaka cin abinci” tana dariya, bai ce mata komai ba dan ya saba da tsokanar Aunty Amna, shi bai tab’a haďuwa da Aunty ďinshi mai tsokana kamar ita ba, Ammah ce ta dubi inda su Farida ke cin abinci ta lura da Batuul bata cin abincin, tambayanta tayi “bitti ya akayine bakya cin abincin”, murmushi Batuul ta k’irk’ira tacewa Ammah “Na k’oshi Ammah”, ce mata tayi “Bitti ďauko wa Abu abincinshi a palo, yana nan na shirya akan tray”, a sanyaye ta mik’e tare da cewa toh, ida ta ajiye ďankwalinta ta duba zata ďauka taga akai ya zauna, bata ce mishi komai ba tayi hanyan palo, binta yayi da kallo har ta b’ace sannan ya ďauke idonshi a ranshi yace batason rufe kanta,dan yasha ganin gashinta on several occasions , mik’ewa Ammah da Aunty Amna sukayi suka fita dan sun gama abinda zasuyi, turowa kawai zasuyi a zo a ďauki kayan, inda Farida take zaune ya duba yaga tana ta faman dambe da k’ashi, ďauke kanshi zaiyi daga kallonta, sake dubanta zaiyi yaga abinda takeyi still kenan, tsayawa yayi yana kallonta yaga baza ta dena ba bayan ga wasu a plate ďin, harara ya zabga mata yace “ke in baza ki ci abinci nan ba tashi ki fita, kin zauna kina ta kokuwa da k’ashi ko ina zaki kai na cikin plate ďin” zumb’uro baki tayi tareda kinkiman plate ďin abincinta tayi waje a ranta tana faďin “ohh masifaffe, mutum ran aurenshi ma sai yayi masifa”, ta fice abinta
Story continues below
Bayan few minutes Batuul ta shigo ďakin kinkime da babban tray, saura kaďan ta sake tray ďin , wani irin faďuwa gabanta yayi ganin shi kaďai ne a ďakin, kanshi ya ďago ya ganta tsaye, ďauke kanshi yayi yaci gaba da abinds yakeyi, ganin ta fara gajiya da tsayuwan ne ya sata k’arasawa jiki a sanyaye ta shigo, a gabanshi ta sunkuya ta ajiye tray ďin , shi kuma gashin kanta da tayi parking in a messy bun yake kallo, yadda sukayi curls wasu na lilo ya zubawa ido, ďagowa tayi daga tsugunnen ta mik’e tsaye, tsayawa tayi a kanshi tana so tace yana zaune a kan ďankwalinta zata ďauka, binta yayi da kalli yace “wa zai zuba min abincin kin ajiye kin nemi waje kin tsaya kina kallona”, bata kulashi ba ta tsuguna ta ďauki plate da serving spoon tace mishi “mey zan zuba maka”, ba tare da ya kalleya ba yace “anything”, gima ta zuba mishi a plate ďin, daga gefe ta saka mishi scrambled potato mai cheese sai sai kémoniye a wani saucer, ce mishi tayi ta gama , sunkuyawa yayi ya ďauka ya fara ci, ďagowa yayi da kanshi ya ganta tsaye tana fidgeting yatsunta kamar zatayi magana, kallonta shima ya tsayi, sosai yarinyar is tiny, k’aramace ya faďa a ranshi, ce mata yayi “get me a bottle of water”, ba musu taje ta ďauko mishi ta mik’o mishi, hannu yasa zai karb’a hannunshi ya gogi nata, maza tayi ta sake ruwan ya faďi a k’asa, kallonta yayi tare da ďan k’aramin tsaki ya ďauki ruwanshi, ganin ta kasa mishi maganan ďankwalinta ne ya sata kawai ta fita haka, juyawan da tayi zata bar wajen kawai ta bige tumbler dake wajen , a take suka tarwatse a wajen, k’afa ta ďaga zata matsa daga wajen ta tak’a ďaya daga cikin broken glass ďin , wani k’ara ta saki ta tsuguna a wajen, dubanta yayi ya ďauke kanshi, sai da yaga jini daga gefe ne ya sashi ajiye abincin a gefe , tunawa yayi lokacin da yake k’arami suna London, Aunty na koya mishi homework ďinshi ya ďauki blade ya yanke hannunshi dashi, rudewa tayi sosai har idonta sai da yacika da hawaye tayi mishi treating hannun, har sai da ya warke tukunna ta fara barinshi yana yin abu da kanshi, tashi yayi ya isa inda take, tsugunawa yayi dab da ita har tana iya jiyo numfashinshi a fuskanta, ga k’anshin turarenshi ita tayi mata yawa, hannun yasa zai janyo k’afarta tayi maza ta janye, tsaki yayi tare sa janyo k’afan yana dubawa, glass ďin da ya mak’ale a k’afan ya sa hannu ya cire, wani ihu tasa tare da k’ank’ame shi, shiru yayi yaji yadda heartbeat ďinta ke bugawa da k’arfe, idonta ta buďe da taji zafin ya ďanyin sauk’i, da sauri ta sakeshi ta matsa baya ganinta kwance a jikinshi, tashi yayi ya koma gefen gadon ya zauna, yunk’urin tashi tayi itama zata tafi ta kasa, wani k’ara ta sake sawa, tasowa yayi ya dawo gabanta ya mik’a mata hannun alamun ta rik’e ya mik’ar da ita, nok’e hannayenta tayi, mamakinta ya tsaya yi, mutumin da bazai iya rashi ba an mik’a mishi hannunshine yake nok’ewa, haushi ne ya sashi sunkuyowa ya ďauketa cak, ido ta wara ganin abinda yayi , k’ok’arin sauk’a ta farayi daga hannunshi, idonshi masu kama da na masu jin bacci ya zuba mata, hawayen nan suna nan a idonta suna shirin zubowa, ce mata yayi “stay still, ciwo kikaji bazaki iya tafiya ba, am helping, ki tsaya in gama”, shiru tayi ta dena k’ok’arin sauk’an da take, toilet ďin ďakin ya shiga da ita ya ajiyeta a bakin bathtub , shower ya janyo ya kunna ruwa yana zubawa a wajen tare da sa hannu yana wanke jinin da ya fara bushewa a wajen, rintse ido tayi sabida zafin da wajen keyi, sai da ya gama ya sake ďaukanta cak ya fito da ita ďakin, a kan kujera ya kwantar da ita , ďakin Abui ya shiga ya ďauko first aid kit, dab da k’afanta ya zauna ya kamo k’afan ya shiga gogewa da spirit, ido ta rintse tsabar azaba ta rik’e hannunshi da sauri, hannunta da ta rik’eshi dashi yabi da ido, ďauke hannun yayi daga jikinshi yaci gaba da abinda yakeyi, zafin ne yayi yawa tace mishi “Yaa Abu dan Allah ya isa haka, akwai zafi”, dubanta yayi yaga hawayen sun zubo ,ce mata yayi “clean your face and close your eyes, it wont hurt”, hakan tayi ta rik’e mishi riga har sai da ya gama dressing ciwon , tashi yayi daga wajen ya gyara mata k’afan ta kwanta comfortably, juyawa yayi zai fita tace mishi “Yaa Abu zansha ruwa”, tsayawa yayi cak ba tare da ya juyo ba jin ta k’ira sunanshi sai da yaji abinda take buk’ata, ba tare da ya juyo ba yaje ya ďauko mata ruwa sai da ya buďe ya mik’a mata, tashi tayi ta zauna sannan ta karb’a ta sha, fita zaiyi daga ďakin kenan Farida ta shigo tana ihun “Batuul mey kika tsaya yi tun ďazu ina jiranki kizo kiga kayan da akayi mana, its f**ki…..” bata k’arasa ba tayi maza ta rik’e baki ganin Yaa Abu a tsaye, murmushi Batuul tayi ganin yadda ta haďiye maganan, a sanyaye ta k’arasa wajen Batuul tace “mey ya sameki, ya akayi kika ji ciwo har haka daga fitana”, Farida ya k’ira yace mata “clean this mess and help her situp”, ya sa kai ya fita, ko ta kan abincin bata bi, yana fita Farida ta dubeta tace “shi ya ji miki ciwon ko, ai nasani, kuma in yaga mutum yaji ciwo yafi kowa damuwa”, kai Batuhl ta girgiza tace mata “Ba shine fa ya ji min ciwo ba, nice na fasa tumbler da na ajiye, dama ance everybody will b d first victim of his own corruption, gashi nan ni ya fara ji wa ciwo”, tausaya mata Farida tayi tace “sannu”, tambayanta Batuul tayi “mey kike faďa ne da kika shigo har da su f**king” ta k’arashe maganan tana mata dariya, “kayanmu ne na dinner, yayi kyau sosai, both d material and d style sunyi kyau sosai, sai ma mun saka tukunna”, ce mata tayi “Dinner sai ku, ni yanxu ina naga k’afan zuwa dinner” a ranta kuwa hamdala tayi dan dama bata son zuwa, Farida ce tace “tih nima bazanje ba tunda bazaki ba”, ido Batuul ta wara ta buďe baki tace “kinsan mey kike faďa , dan bazanje ba kema bazaki ba, ai sai in sa Ammah ta turaki dole, bare da ita ma zara ai dole kije”, dariya Farida tasa tace “I wont miss it for the world wasa ma nakeyi, zanje kema kuma zakije”, kamin ta bata amsa Ammah ta shigo ďakin, ganin Batuul a kwance yasata hanzarin k’arasowa inda suke, tambayanta ta shiga yi yadda akayi taji ciwo, faďa mata gaba ďaya, sai da ta gama tace mata “Toh yanxu ina Abutturab ďin, shine dan bak’in hali ya fita ya barki ke kaďai Kuma bai zo ya sanar dani kinji ciwo ba”, “yanxun nan ya fita Ammah”, Batuul ta faďa mata, taimaka mata sukayi ta tashi, har toilet sukaje da Farida tayi alwala ta fito, kaďan kaďan take ďingisawa, side ďin Ammah suka koma sukayi sallah suka fara shirin zuwa dinner dan Ammah tace babu abinda zai hanata zuwa