BATUUL
CHAPTER 6
A YEAR AFTER
K’aran Alarm ne ya cika dakin gaba ďaya, kwance take tana bacci har sai da K’aran ya kusa katsewa tukunna taja tsaki, ta Janyo wayar da k’afarta, ko kallon fuskar wayar bata yi ba ta saka hannu ta katse karan tukunna ta maida wayan, duk abin nan da tayi bata bude ido ba, sai da ta mike ta zauna daga bakin gadon tukunna ta buďe idonta a hankali wayar ta sake ďauka taga 7:09, tafi minti biyar a zaune daga bisani ta mik’e tana fadin “mutum da kanshi zai saka abinda zai dameshi”, gashinta ta tattare ta haďe su waje ďaya, ta isa inda bathrobe dinta ke rataye ta cire kayan baccin dake jikinta ta saka bathrobe din ta shige toilet, sai da tayi brush tukunna tayi wanka, gaban mirror ta zauna bayan ta fito daga wanka ta shafe duk jikinta da mai,ta fesa body spray tukunna ta je saka kaya, closet dinta ta buďe ta ciro wata coffee abaya mai Babban hannu da adon milk daga jiki, sai da ta saka kayanta tukunna tayi inda jakunkunanta ke rataye ta jawo d’aya daga ciki ta zuba tarkacenta a ciki sannan ta yafa gyalen abayar a kanta sannan taje ta saka slippers din Laura Ahman shima milk, har ta fita ta tuna da key ď in mota da wayarta ta koma cikin hanzari ta ďauko lokacin 8am daidai, k’asa ta sauk’o babu kowa a gidan shiru, ta tasan kowa ya tafi makaranta, Aunty da Baba kuma mayb suna bacci, ta nufi dinning area, sai da ta bubbuďe duk kwanun dake dinning din tukunna ta ďauki soviet ta ďauki sandwich ďaya a cikin wani transparent bowl, ta ďauki disposable cup ta tsiyayi fresh orange juice a juice dispenser, har ta zauna zata fara ci taga time zai k’ure maza ta mik’e ta yi hanyan waje , sai da ta taje dab bakin k’ofa zata fita Taji muryan Aunty a zaune a parlour tana ce mata “sannu Batuul , kin kyauta , cin abinci a waje ko ? Nasha fada miki banaso babu kyau shine kika wani ďauki sandwich a paper kamar wacce ta rok’o toh yayi miki daidai”, sai da Aunty ta gama maganan da takeyi tukunna ta juyo da murmushi a fuskanta ta dubi Aunty tana k’arasowa cikin parlour ta ce “Aunty Nda wattu, nifa banma San kin tashi ba, Ina kwana” ta sake maimaitawa bayan ta zauna kusa da Aunty, Da lafiya Aunty ta amsa mata sannan tace “Batuul ba kya Jin magana ko” Da sauri Batuul ta girgiza kai tace “Aunty ba haka bane fa, har na zauna zanci naga time ya kusa k’urewa zanyi latti shinefa zanje mota dashi , bama a layi zanci ba fa” ta gama maganan tana sadda kanta k’asa dan tasan Aunty ta hanata, Sai da Aunty ta dubi hannunta taga ma abinda ta ďauka din tukunna tace “mota ba layi bane ko ? Ai cikin gidane, kuma waye ya hanaki tashi da wuri har kika kusa lattin ke da ba sllh kike ba bare ace baccin asuba kika koma kika makara, kin wani ďauko Sandwich ďaya kamar wacce ta rok’o” ganin faďan baya k’arewa kawai ta fara cin Sandwich ď in tana tunkud’awa, haka ta gama ci tana kurb’an juice ď in har ta gama, mik’e wa tayi zataje ta ajiye sauran juice da ta rage, dama tunda ta fara cin abincin Aunty bata kalleta ba sai da ta gama ta mike tukunna ta dubeta tace “sauran Juice din kuma fa? wa kika ragewa” marairaicewa tayi tare da da juyowa tace “Aunty na koshine zanje in ajiye”, “Da kinsan bazaki iya shanyewa ba kika ďebo dayawa, dawo ki zauna ki shanyewa shi”, haka ta dawo ta zauna ta shanye a ranta tana addu’a Allah yasa bata yi latti ba, bayan ta gama shanyewa a dustbin ta jefa cup din da tissue ta dawo tace “Aunty zan tafi” ďagowa tayi ta kalli Batuul tace “A dawo lafiya, Allah ya bada sa’a” ta amsa da Amin ta wuce, har taje bakin k’ofa Aunty ta sake k’iranta “Batuul”, juyowa tayi tare da cewa “Na’am Aunty”, “What time zaki gama lectures” Aunty ta tambayeta, “10:30 zan gama, class ďaya dani yau, by 11am zan dawo”, “okay in kin gama inaso kije ki gaida Ammah, jiya munyi waya tana tambayana ke, so ki wuce daga can sai ki dawo da yamma” toh kawai tace ta fita, Parking area ta nufa taga ďaya daga cikin masu aikin gidan na goge motar, farar BMW, k’arasawa tayi wajen motan tana laluben makulli daga cikin jakan, ďagowa tayi bayan ta samu makullin ta amsa gaisuwan da mai aikin ke mata “Yauwa Friday sannu da aiki” ta danna button din motar, kamar jira yake dama tana dannawa ya buďe mata, sai da ta shiga ta zauna tukunna ta ciro ďari biyar ta mik’a mika mishi, murna ya dinga yi yana mata godiya, murmushi kawai tayi ta jawo motar ta ta tafi, a bakin gate ma sai da ta mik’awa masu gadin ďari biyar biyar tukunna ta fita daga gidan, a wajen wani traffic ta tsaya tana jira a basu hannu su wuce, wani super tint AMG ce ta tsaya daga gefenta nata, bata kalli motar ba saima wayarta da ta ďauko daga ďayan kujeran zata duba time, jiya tayi kamar ana kallon ta ta gefe, a hankali ta juya ta dubi gefenta, k’irjinta ne taji yayi dam , wani mugun faďuwa gabanta yayi, sosai ta tsorata da mutumin dake cikin motar dan wani irin kallo ya tsaya yana yi mata, sunan Allah ta shiga jerowa tare da fatan traffic ď in ya basu daman wucewa ta wuce, bata sake k’ok’arin kallon gefen ba, a haka traffic ď in yayi signalling ďinsu da su wuce, a guje ta figi motar kamar mai shirin tashi, Sai da tayi nisa sosai tukunna ta ďago ta rear mirror ta duba ko mutumin na binta a baya amma bata ga alaman motanshi ba, wani ajiyan zuciya tayi tare da faďin Alhamdulillah a fili, 8:34 daidai ta isa school, dpt dinsu taje tayi parking sannan ta fito tayi hanyan class ďinsu, a tare da lecturer ďinsu dai dai suka iso, ta k’ofan baya ta shiga ta samu waje ta zauna , nutsuwa kowa yayi a ajin har malaminsu ya fara lecture, 10:30 dai dai ya gama ya fita suma suka mik’e suka fito, sai da ta ďan gaggaisa da y’an ajinsu da ta sani tukunna tayi hanyan motan ta , bata tsaya yin komai ba ta shige ta wuce abinta, hanyan gidansu Farida tabi, a hanya tana driving tana tambayana k’iran number Farida tasan duk yadda akayi dai ta tashi daga bacci yanzu dan can gari yanxu 2 biyu tayi, sau biyu tana k’ira bata ďauka ba, cikin minti 18 ta isa, har cikin gida ta shiga tayi parking , da sallama ta shiga parlour babu kowa a ciki sai kanshi da yake tashi, hanyan stairs tabi zata hau sama wata mai aiki ta fito daga kitchen ta gaisheta sannan ta tambayeta Ammah na gida, Ce mata tayi ehh tana sama, godiya tayi mata ta k’arasa hawa Saman, a hankali ta buďe k’ofan ďakin Ammah tare da sallama, su biyu ta tarar a zaune, da gudu Farida ta taso ta rungume Batuul tana ce mata “dullop head I missed you, you didn’t tell me zakizo” murmushi Batuul tayi tace “ai yanzun ma ba wajenki nazo ba” bata rai Farida tayi tace “Really? well am not hurt, nasan zaki dawo ki nemenin nima” ido Batuul ta juya tare da mata gwalo tace “not in this life” Ammah na daga zaune tayi murmushi ta girgiza kai, gaban Ammah Batuul taje ta zauna tace mata “Nda dubdo Ammah” , “Lafiya kalau Bitti, ya gida ya Aunty, ya kuma karatu, ana dai yi lafiya ko’? kai ta gyaďa mata tare da cewa “Alhamdulillah Ammah , duk lafiya ” dubanta Ammah tayi tace “kin buya Bitti, sam ba a ganinki ko kuma makaranta ne? ” Da sauri ta sadda kanta k’asa dan tasan bata kyauta ba, rabonta da gidan ta kai wata biyar, kuma kullum suna haďuwa da Farida a school, jiki a sanyaye ta girgiza kai tace ” Ammah, zan rika zuwa yanxu” Ammah tace “toh yayi kyau, ai Faridan ma ďazu da asuba suka iso, ni yanxu zan shiga in kwanta dan yau ban samu nayi bacci ba tunda Farida ta iso ta isheni da surutu” ta faďa tare da mik’e wa zata kwanta , da ido Batuul ta bita ganin yadda maganan Ammah yayi sanyi gashi har ta ďan rame, ganin zata juyo ne ya sata tayi maza ta ďauke idonta daga duban ta, Ce musu ta sakeyi ” Farida in kun sauk’a ki turomin Yaa Bawa” tare suka amsa da toh dukkansu biyun, tana shigewa Batuul ta Janyo hannun Farida tana tambayanta “Ke da muka turaki Uk kiyi wata ďaya shine ko sati ďaya baki cika ba kika dawo ” Suna fita suka haďu da Yaa Bawa ta tattaro kaya zatayi k’asa suka ce mata Ammah na nemanta sannan suka shige ďakin Farida “Batuul ce ta sake tambayanta “wai meye inata magana kinyi min shiru” tsaki Farida taja tace “ai ni da dan ta nice wlhy ko kwana ďaya banyi a kasar nn, dama can ba so nake ba Ammah ta sani dole inje, wlhy saura kaďan in mutu dan baqin ciki, dama sai da kika tayi min dariyan mugunta har da wani rakani airport bakiga ko waya banyi nace miki zan dawo ba, ni nan gaba ko meye za a bani ba zanje gidan ya Abuu ba, toh meye ma yayi zafi, ni dai ban k’ara zuwa, gidan Yaa Abu bai yi ba, shi zafin kai matarsa y’ar duniya mara mutunci, gaba ďaya ta gama da Yaa Abu, Dan tausayi ma yake bani ” tsaya Batuul tayi tana kallonta har sai da tayi shiru tukunna tace “tun ďazu kike surutu, tell me exactly what happened da kika dawo before time ” tsaki Farida taja tace “kina son spoiling mood ďina ko, toh tunda baki ganeba, gidan ne babu daďi, tunda nayi stepping k’afa na a cikin gidan maganan arziki bai tab’a haďani da Ajiddeh ba, kai tun lokacin da na shigo gidan tana hakimce a parlour ita da wasu y’an uwanta ko k’awayenta ne oho taqi amsamin sallama ban sake bi ta kanta ba, shima Yaa Abun da ya dawo gida da yamma naje zan fara mishi complain cewa yayi wai shi fa baya son K’ananan maganganu , wai haka matar tashi take I shud let her be, ni nake dafawa kaina abinci, shima ďin sae dae Cook suyi ya ci, gara ma da naje ne take ďan sani in dafa mishi wani abun, kuma baya iya ce mata komai duk iskancin da takeyi, daga ta ganni zata fara wani shan magani tana habaice habaice, har da cewa rannan wai aikin banza, ai mun riga da mun makara daga ni har iyayena tunda har muka bari ta aureshi, toh shine shekaran jiya da naga iskancin nata kaďan ne da ta saka Ammah jiya na tashi na bita har ďaki bayan y’an iskan y’an uwan nata sun tafi nace wlhy in ta kuma faďin wani abu akan iyaye na sai na lakaďa mata dukan tsiya, kuma in daki banza babu mai ce min komai, da yake k’aramar y’ar iska ce bata ce min komai ba….” Ido Batuul ta wara ta riko hannun Farida tace “Dan Allah dagaske kike, duka fa kikace zakiyi mata har ďakinta kuma, ta girmemu fa sosai farida” hannunta ta Janye tace “Ni ina ruwana da girman ta, ai bata rike ba, y’ar rainin hankali ai da ta sake faďin wani abun wlhy da sai ta raina kanta, sai na kusa illatata, Dan ko banida karfi sai na samu wani abin na bigeta dashi, shine fa bayan Yaa Abu ya dawo, yana shigowa ta fashe da kukan munafurci wai yau wuni nayi ina zaginta har dasu dungure mata kai, dukana kadae ne bae yi ba in gaya maki, shine fa yayi maza yayi min booking flight na dawo yau, har ce min yayi fa wai hutun ya isa haka in koma dama shi bai nemeni ba bare inzo ina tayarwa matarsa hankali, Dan bakin ciki ma ko tsayawa banyi na mishi explaining komai ba na juya naje haďa kayana, a parlour ma na kwana shi kuma ya jata sukayi sama , da asuba ya sauk’o ya tulo min kuďi masu Uban yawa kamar su aka ce mishi nazo nema, ya haďani da John Driver ďinshi ya kawoni airport, da ya rakani bakin k’ofa nidai sai da na mishi magana nace mishi wlhy Hakkin su Ammah bazai barshi ba, tunda yayi aure sau ďaya ya tab’a zuwa ya dubasu waya kam ba a xancen sa don baya kira, kuma fa ba wai baya shigowa Nigeria ba, yana shigowa Dan ko randa naje a jiyan shi ya dawo, sai da naga jikinshi yayi sanyi tukunna na fita na bar mishi gidanshi, yau da asuba muka k’araso, kinji yadda akayi na dawo banyi wata ďaya ba, tagumi Batuul tayi tana kallonta cike da tausayin Ammah, shi yasa duk bata da sukuni knn ta ga ta rame, gskya ya Abuu bae kyauta ba.
K’arfe biyar suka sauk’o k’asa ita da Farida zatayi wa Ammah sallama ta wuce , a kitchen suka tarar da Ammah ita da wasu y’an aiki tana masu magana, ganin Batuul da shirin tafiya tace “Bitti ba dai tafiya bako, ko Baa Alai din yazo ne, in baizoba ki bari anjima ko Sadiq ne ya mayarda dake”, murmushi Batuul tayi tare tareda da girgiza kai tace “Ammah da kaina nazo, kuma Aunty tace in dena zama a waje har six, shine nakeso in koma gida kamin shida ” tace “toh shikenan yayi kyau bitti, yanxu driving din yayi kyau sosai ko” tace “Ehhh Ammah muna trying”, tace yayi kyau toh, Allah ya taimaka,muje parlour bari in hau sama in dawo ” haks suka koma daga parlour suna jiran Ammah , suna zaune ta sauk’o rike da Babban farin leda a hannun ta, a tare suka mik’e suka isketa, Batuul ta mik’awa ledan tace “gashi bitti, useki kinji, nagode sosai, ga wannan kinji nakine”, gaba ďaya sai taji wani irin da yadda Ammah ke mata magana, hawayene ya taru a idonta, kamar tayi laifi haka ta rik’a ji’, maza tayi ta maida hawayen dake shirin zubo mata ta karb’i ledan daga hannun Ammah, jiki a sanyaye tace “nagode Ammah” , “Babu komai Bitti, ki rik’a zuwa akai akai kinji, ki gaida Aunty in kin koma da sauran yaran kinji” kasa motsawa tayi daga wajen har sai da taga Ammah ta haura bene tukunna ta juya a sanyaye tayi waje dama Farida ta dade da fita, a cikin mota ta tarar da Farida zaune ta k’ure wak’ar Ed sheeran ta shape of you a motar tana ta rawa, sau uku tana k’iran sunanta bata ji ba, har sai da ta zauna tukunna tace “Dadin abin ke da Affan ďin duk halinku ďaya da ya wahala sosai ” juya ido tayi tace “ai inma ba ďaya ba haka zai hak’ura dani, babu yadda ya iya” tana ďaga gira ta k’arashe maganan, Sai da Batuul ta tada mota tukunna tace “Alhamdulillahi ma da halin naku ya zamo ďaya”, dariya Farida tasa ta fita a motan tace ‘toh ni dai ban shiga school this week , sai next week, Yauwa I forgot to tell you, Guess? Ta tambayi Batuul tareda daga mata gira ďaya, “kinsan I always get it wrong when I guess, so just tell me, time is going” Farida tace “toh naji, Mrs, Yaa Massa is getting married, ďazu Ammah ke faďamin wai da na tafi, y’ar Sultan ďin Sokoto zai aura wai sunanta Rahama” sai da ta gama Batuul tace “Allah sarki Yaa Massa, ashe……” , bata gama faďan abinda zatace ba Farida ta katse ta “wani irin Allah sarki, ke da kika k’ishi kememe kice baki sonshi shine harda wani tausayinshi, shima ďin nei dai ya barki , ai da nice shi Allah straight away Baba zanje in samu, sai dai kawai kiji ance an ďaura miki aure, wai shi tunda baki sonshi zai hak’ura da azo ayi abinda za azo ana magana daga baya , ni haushi ma yake bani , he was very lenient on you ke kuma kikayi ta gwara shi ,muna nan dai muna jiran Jin wanda zaki aura, Kai Allah yasa ma Baba ya badake Sadaka tunda ke kowa bai yi miki ba” Dariya maganan ya bawa Batuul tace ” toh muguwa haba dai sadaka, that is not happening , not with me, ni kinga tafiya zanyi before Aunty ta faramin waya” , dariya Farida ma tasa tace “zaki sanine bari mu gaji dake Kiga ikon Allah ” Sai da tayi reverse tukunna ta cewa Farida “Dan Allah turomin number shi Yaa Massa inyi congratulating ďinshi dan tun lokacin da yake ta damuna nayi deleting sai kuma number shi ta Germany shi kuma bazai yi Amfani ba”, juyawa Farida tayi tana komawa ciki tace “fadi gaskiya dai Dan yanxu yana da matarshi , Dariya sukayi a tare kowannensu na dariya Batuul tayi sallama da Farida ta koma gida.
Daidai ana k’iran magrib ta isa, A cikin gida da taje parking taga kamar motan ďazun nan ne pake, sanin babu yadda za ayi yazo gidansu kawai ta tab’e baki ta shige cikin gida, Aunty na alwala Batuul ta shigo da Sallama tace “Aunty na dawo “, Aunty tayi mata sannu da zuwa, ta juya zata koma ďakinta Aunty ta tsayar da ita ta hanyan cewa “in kin idar da Sallah kinada bako , ji tayi k’irjinta ya bada sauti Dam! Ita?, bako kuma? , toh shi waye ?, ita dai babu wanda yace mata zaizo wajen ta ko a y’an ajinsu , maza maza hankalinta ya tuna da motar dan ta gani pake , toh in shine bakon ni ina na sanshi ta ďan ja siririn tsaki, da sauri tace “Aunty ba wajena yazo ba, ni ban sanshi ba, “matsar min daga k’ofan toilet in wuce ni, waje na yazo tunda nice Batuul ” marairaicewa tayi tana girgiza kai tace “Aunty dagaske fa ni ban sanshi ba “, bayan Aunty ta saka hijab zata tada Sallah tace mata “toh naji baki sanshi ba, wuce kije kiyi Sallah”, jiki a sanyaye ta fita tayi ďakinta, tana tafiya tana ta sak’e sak’e a ranta “toh shi wannan mutumin what does he want with from me, ni ban sanshi bama gaba ďaya inba da na ganshi ba ďazu a traffic, am not even sure ko shi ďin ne bama” Alwala tayi ta tada Sallah, tana idarwa ta tub’e kayan jikinta ta shiga wanka, wani dogon riga mara nauyi ta kuma maidawa mai hula purple, ta ďan fesa turarenta mai sanyin k’anshi, kamin ta sauk’o Mahir ya shigo yace “Yaa Batuul Mama tace kizo”, K’aramin gyale ta yafa bak’i tace “muje toh ” tare suka isa ďakin Aunty dashi , da sallama ta shiga tace “Na’am Aunty” , ďagowa tayi ta dubeta tace “kije Guest room, bak’on naki na can na faďawa su Janet su kai mishi drinks kuma bana son gardama” tsayawa tayi bayan Aunty ta gama ta kasa tafiya, dubanta ta sakeyi tace “baza ki wuce ba, mutum na jiranki tun ďazu ” kamar mai shirin kuka tace “Aunty Allah ban sanshi ba, maybe ma mistake ne bama ni yake nema ba”, Hararan da Aunty ta sakar mata ne ya sata yin shiru ta juya zata tafi, tafi minti uku tsaye bakin k’ofan ďakin ta kasa shiga daga k’arshe dai ta ďaga labulen tare da sallama tasa kai ciki, bata ďago kai ko sau ďaya taga mutumin dake zaune ba, kujeran dake nesa dashi taje ta zauna tareda da sadda kanta k’asa, shiru ďakin yayi babu wanda yayi magana, tunda ta shigo ya k’ura mata ido yake kallonta, ita bata ma San yanayi ba, ji tayi ya k’ira sunanta daga inda yake zaune “Batuul “, bata amsa ba kuma bata ďago ba sai ma mamakin da take na yaushe yasan sunanta, Sai da ya k’ira a karo na biyu tukunna ta amsa ba tare da ta kalleshin ba, murmushi ta bashi ta k’ara burgeshi dan komai na Batuul na burgeshi, from d very first time he set his eyes on her , cikin nutsuwa ya fara mata magana “Well it seems you are not ready to respond, okay then ni…..” , ďagowa tayi ta kalleshi , mutumin nan ne na ďazu a traffic kuwa “Hasbunallahu Wa ni’imal wakil “, dama haka yake, k’yak’yawa ne sosai ba kaďan ba , kuma fari ne sosai. …..”, katse mata tunani yayi ta hanyan ci gaba da maganan shi ” Ni sunana Abdallah , I know baki sanni ba but though may be you have seen me once, that is ďazu kenan if you could remember, I can’t deny the fact that am in love with you, shiyasa I did all possible things to get to you today, Am praying and hoping that babu wanda ya rigani, ita gaba ďaya mutumin nan ya sata Jin wani iri , da k’yar ta samu ta ďago tace mishi “okay i will think about it ” ta mik’e, gabanta yazo ya tsaya yace “toh tsaya mana, kamar wacce ake Kora, in kika tafi a ina zaki sameni in kinyi tunanin, kinga yanxu ki bani number ki, then anjima sai we will talk Dan naga you are not comfortable ” Da sauri ta kaďa mishi kanta har sai da ta saka shi yin murmushi, a lokacin ta karanto mishi ta juya ta tafi, da ido ya bita a ranshi yana faďin “Alhamdulillahi yayi mata, yau zai faďawa Mummy wannan great News ďin dai ta daďe tana jira” , Murna fal ranshi shima ya fita daga ďakin
Ranta b’ace ta shigo cikin gida, ignoring kowa tayi zata haura sama Aunty tace “zo nan Batuul” , dawowa tayi ta zauna daga gefe kanta a k’asa, “kikace baki sanshi ba, ya akayi yasan sunanki, har parlour ya shigo ya sameni yace min Batuul yake nema ” , “Aunty nima ban san ya akayi yasan sunana ba , ni ban sanshi ba ” ido Aunty ta k’ura mata da taga taqi magana tace mata “tashi kije” ranta gaba ďaya a dagule, ta rasa mey ya hanata cewa mutumin bata sonshi, ko dan ta ganshi matured ne not like the other guys da suke binta, alwala sallah Isha tayi ta tada Sallah, tana idarwa ta kwanta, tunanin abubuwan da suka faru a yau ta rik’a yi, abinda ke damun Ammah ne ya dawo mata, mesa Yaa Abu zaiyi haka, shi ko tsoron hakkinsu baya ji gashi har yasa Ammah a damuwa matar da take very jovial and authoritative ta zama very silent just because of Abu, tsaki taja tareda juyawa ďayan gefenta, dama can mugu ne shi ita ta dade da sanin haka, haka taci gaba da tunane tunanenta har bacci ya ďauketa, cikin bacci taji kamar wayarta na ringing , tashi tayi ta zauna ta duba screen ďin wayar, sai sabuwar number ta gani, har ya katse bata ďauka ba sai da aka sake k’iranta , ďagawa tayi bayan tare da tace komai ba, daga ďaya b’angaren taji ance ” salamu alaiki Noor ” cire wayan tayi daga kunnenta ta sakr duba number, cikin muryan bacci tace “ba Noor bace, it’s a wrong number ” zata ajiye wayan taji ya sake cewa “toh ai ke ďin Haske ce shiyasa na saka miki suna Noor ” , cikin kosawa da surutun da yake mata tace “who are you ” , murmushi yayi daga cikin wayan har tana jiyowa yace “It’s Abdallah, tunda kin kasa ganewa let me tell you, well as it is, nakasa bacci because of tunanin ki na kasa bacci ” ita dai bata ce komai ba sai shiru da tayi tana sauraronshi, “baza kiyi min magana inji muryan ki mai dadi ba Noor ” a hankali tace “bacci nakeji yanxu bazan iya doguwar magana ba, am sorry you should call me tomorrow ” , murmushi ya sakeyi yace “Alright Noor, it’s okay kiyi bacci but gobe zan kiraki kuma zakiyi min magana but for now you should go to bed , okay? ” a hankali ta amsa mishi da “toh” , yace mata “good night sleep tight” ya katse wayan, mamaki ta rik’a yi mesa shi wannan mutumin baya bata haushi kamar sauran mazan dake cewa suna sonta, ganin babu mai bata amsa yasa ta kwanta ta koma bacci
B.A flight ne ya iso Nigeria K’arfe 6 na yamma, cikin mutanen dake fito fitowa daga ciki harda Abutturab da matarsa Ajiddeh, tafiya suke cike da nutsuwa, sunyi kyau sosai, kanta kwance yake kafaďanshi gashin nan da yasha gyara an barshi iska sai kaďawa yake , wani mutum ne yazo cikin hanzari ya karb’i Jakar dake hannun Abutturab yace “Sir this way please, the car is parked down there” bayan mutumin nan suka bi har wajen motar da zata kaisu, bayan ya buďe musu sun shiga sun zauna ne Ajiddeh tace “Babe, bana so muje gidanmu saboda y’an sa ido, kar aje ana cewa mun shigo gari, we should lodge in a hotel, kuma ma tunda babu wanda yasan muna hanya sai y’an gidanmu Mum da Yaa Zee kaga it will take time before a gyaggyara kuma ma ai ba daďewa zamuyi ba ana gama bikin nan zamu koma, so we should stay in the Hotel ” gefen fuskanta ya shafa yace ” alright then, hakan ma zaifi” Hotel ďin dai suke so su sauk’a suka faďawa mai tukin motar, ba b’ata lokaci ya juya yayi hanyan Hotel ďin da aka faďa mishi , suna isa bayan sun kama ďaki tayi ordering abinci taci tayi wanka tasa aka turo mata driver daga gidansu, Ce mishi tayi ya tashi su tafi yace mata “No he is exhausted, bazai iya zuwa ba , amma zaije dinner ” ganin kaman ranta ya fara b’aci yayi maza ya taso ya rungumeta tare da mata peck yace “baby na gaji ne yanxu; I can’t come but anjima zanzo dinner da za ayi I promise, kuma zan baki what you asked for ” sai a sannan ta sake fuska tace “toh zaka K’aramin akan na da” yace “yeah , everything for you ” juyawa tayi ta fita daga ďakin, da ido ya bita a ranshi yasan something is not right but ya kasa ganewa ko menene, ya rasa gane mesa baya iya yiwa Ajiddeh faďa akan abubuwan da takeyi , yanxu ko kayan jikinta ma bai kamata tana matar aure ta rik’a fita babu ďan kwali ba amma bazai iya ce mata komai ba, kan gadon ya koma ya zauna tareda da dare kanshi Dan mugun Sara mishi ya fara.
Tana fita ta wuce gidansu daga hotel din, cike gidan yake da mutane da suka zo biki, wucewa takeyi tana ta daga kai ita a dole matar mai kuďi, matan dake zaune sai gaidata suke wasu kuma suyi gulmarta, ďakin da tasan zata samu Mum straight ta wuce, ba ko sallama ta saka kai cikin ďakin, Mummy na ganinta ta taso cike da murna ta rungumeta tana faďin “Yar albarka baki min waya kince kun iso ba ” ta fadi tana K’arewa Ajiddeh kallo ganin yadda ta canja lokaci kaďan, ga wani kyau da ta k’ara dama can Masha Allah, Hannunta ta jawo bayan ta saketa daga rungumar da tayi mata taja hannunta suka shiga bedroom, Junaiba dake zaune ce ta bisu cikin ďakin, a tsakiya suka sa Ajiddeh, Mummy ce ta fara ce mata “Ajiddeh kinga yadda kika canja , lalalala Masha Allah, kin zama matar manya, duk komai yana tafiya yadda muka shirya ko? , Jainaba ce tayi maza ta karb’e maganan da cewa ” Mummy ai ko baki tambaya ba gashi kin gani, yarinya zata cuci kanta, ana so a ayi miki abin kirki a taimakeki kina ke mijinki, kefa kina sonshi, toh da mun barki haka da yanxu duk ba haka bane, yanxu faďa mana muji inda matsala mu san yadda zamu b’ullowa matsalar mu magance ta” , tunda suke surutun su bata ce komai ba sai danna waya da take tayi , sai da ta gama ta ďago tana kaďa hannu tace “Mummy ai Aliyu sai abinda nace, tun farkon aurenmu da ya fara min masifa kullum ni k’azama ce, na faye son jiki, bbu abinda na iya, gashi da bak’in halin jaraba sam ba a zama ayi hira dashi , amma tun bayan nayi muku complain ďinnnan da kukace in turo kuďi , everything have been fine since then, kuma sam baya tambayan mutum mey zakayi da kuďi komi yawansu bayarwa yakeyi shiyasa bamu samu matsala ba, maganan da nakeyi muku yanxu haka Mummy tunda mukayi aure sau ďaya yaje gida, waya kam dama babu magana, ai na gaya muku wannan watan sun turo k’anwarshi tazo, itama ďin dai bata daďe ba Nasa ya maidata , wannan zuwan ma da zamuyi ban yadda mun zauna a gidanmu ba saboda Kar ma susan da zuwanmu ” “Jainaba ce tace “ai hakan ma yayi daidai da kikayi, toh ya akayi da wancan abinda nace miki na abincin shi ne, wannan na naman, tunda cewa kikayi ba kya girki, ko kinyi bayaci” , dariya tasa tace “Jainaba kenan, ai in yasan wata baisan wata ba, shi yake dafawa kanshi abinci ko kuma ya siyo, toh watarana yakan ajiye na dare da safe yayi warming yaci, ni dama bana bi ta kanshi, kuma dama ba iya dafawa nayi ba, sai dai kullum in rik’a ordering don of recent ya sallami cook din gidan” , Mik’e wa tayi tana dariya tace “Mummy ,Jainaba, ku bari mu dawo daga dinner in mun nutsu zan faďa muku duk yadda ake ciki, ni sam ban maje naga Amarya ba, tunda aka saka ranan nan ya ďaga mun hankali wai sai nayiwa Ufa magana ayi bikin aurenta a gidannan saboda bata sn y’an uwan mijinta su rainata ” , Mummy ce tace “ai da gaskiyarta, Ina zata yadda da raini, gara da ta bar gidansu tazo nan ďin ayi komai a gama, ko ba komai itama tana da y’an uwanta masu akwai ” Da haka suka fita daga ďakin, Mummy da Jainaba suka tsaya daga falo Ajiddeh taje side ďin da Amarya da k’awayenta suke.
Babu abinda ke tashi a wajen nan sai sautin kiďa, Hall ne mai girma da aka yiwa ado sosai na gani na faďa dan da gani kasan yaci Naira, Tun daga mota Abutturab yake k’iran number Ajiddeh amma bata receiving, fitowa yayi daga cikin motan yayi heading cikin hall, mata ne tare da maza kowa yana displaying talent ďinshi na rawa, Ajiddeh ya hango daga cikin y’an rawa sai kaďa waist takeyi, ranshi ba K’aramin b’aci yayi ba ganinta cikin maza tana rawa ga wasu shegun kaya da ta saka duk bayan ta a buďe, ji yakeyi kamar yaje ya fincikota amma babu hali, waje yaje ya samu ya zauna daga gefe yana jiran lokacin da zata gama, sai da suka gama tik’a rawansu tukunna bayan Dj ya k’are suka bar filin rawar, tana juyowa idonta ya sauk’a kan Abutturab, haďe rai tayi kamar ba ita ke dariya ba yanxu, k’arasowa tayi inda yake zaune ta tsaya mishi a ka k’erere tana ďan karkaďa k’afa, ďagowa yayi ya dubeta tare da cewa mata “Babe har kun gama rawan ne? ” wani Harara ta sakar mishi tace “Kai fa ka cika wulak’anci, tun ďazu muyi da kai zaka zo shine sai yanxu ka wani ďebo k’afa kazo, y’an uwana sai tambaya sukeyi ina kake, kowa yazo da mijin shi sai ni kaďai ce babu mijina, ni tun farkon nasan wulakantani kaso yi dama bada son ranka muka zo ba…..” katse mata maganan yayi tareda kamo hannunta ya zauna da ita kan kujeran dake kallon nashi, magana ya fara yace “Babe c’mon, tun ďazu fa nake wajen nan ina k’iran wayanki baki ďauka, da na shigo kuma na ganki you guys were busy dancing” , a ranshi yana son yi mata maganan cewa ita matar aurece, bai kamata tana irin wannan shigar ba har tana Cuďanya da maza, amma bazai iya ba, kawar da zancen yayi yaci gaba da cewa “so bana so in dameki shiyasa na bari sai kin gama tukunna sai ki ……” bai k’arasa ba yaga ta warce hannunta daga rik’on da yayi mata ta bishi da harara ta juya daga wajen ta nufi tsakiyar hall ďin Jin an ambaci cewa y’an uwan Amarya suzo ayi hoto da ita, wani irin bak’in ciki yaji a ranshi wai shi Ajiddeh ke yiwa abubuwan nan da takeyi haka “toh meye ke damuna ne? ” ya tambayi kanshi, inda tabi shima yabi da ido ya ganta ita da sauran y’an uwanta maza sun sata a tsakiya cameras nata haskasu sai washe baki takeyi yana cikin tunani yaji an da dafashi daga baya, a ďan firgice ya juya yaga ko waye, kanshi ne yaji yayi dammm tare da zaro ido ganin mutumin da yake expecting gani least a wajen, zagayowa yayi ya zauna daga ďayan kujeran murmushi ďauke a fuskanshi yace “Ashe kana gari, Well i can see you are surprised to see me here ko bro? , bai bashi ansan tambayan da yayi mishi ba sai ma jifanshi da yayi da nashi tambayan shima “What brought you here Sadiq? Mey kazo yi?” Shima bai bashi amsa ba sai ce mishi da yayi “Answer me first bro, ni na fara tambayanka kuma your question is irrelevant, yaushe ka shigo Nigeria, ko da shike dama ance mana kana shigowa mune dai bama ganin ka ” ďagowa yayi da sauri ya dubi Sadiq Jin abinda Sadiq ďin yake faďi , cikin rashin Jin daďin abinda Sadiq ya faďa mishi yace “ance muku ina zuwa Nigeria? Su waye ke faďa muku cewar ina zuwa” murmushin takaici Sadiq ya saki yace “Allah sarki these doesn’t matter now, Ni auren Abokina Muhsin nazo, shine angon, so banma jima da shigowa ba, but tunda na shigo na ganka wani xuciyar ke cemin ba kai bane, I thought ma gizo kake yimin ba kai bane cus I wasn’t expecting you ” , sai da yayi shiru tukunna Abutturab yace mishi “Ai Amaryar k’anwar Ajiddeh ce, so shine muka zo Dan kusan Ajiddeh ce tayi sponsoring biki saboda mamar yarinyar ai ta rasu” kai Sadiq ya kaďa yace “Ohhh , that’s nice then, toh yau ďin zakaje gidane ko kuwa zaka koma ba tare da kaje ka gaida Ammah ba ” jikinshi ne yaji ya daďa sanyi Jin an ambaci sunan Ammah, ba tare da ya yadda sun haďa ido da Sadiq ba yace “toh shikenan bari in faďawa Ajiddeh zamuje yanxu, k’ar inje kuma bata sani ba hankalinta ya tashi ” , da tausayin ďan uwan shi a ranshi yace “gaskiya hakan ma yayi kyau, kaga kar tazo tana ta nema ai babu daďi” , yace “Ehhh shine yanxu zan k’irata, naga ma she is so busy yau ďinnan” , yaci gaba da dialling ďin number ta, da k’yar aka samu ta ďauki wayan bayan ya k’ira kamar sau bakwai , tana ďauka tace mishi “baby wai meye haka, baka ganin am busy ne ? Kasan fa ni nayi komai na auren nan kuma na daďe ban haďu da y’an uwana ba ai sai ka barni in huta, da ka k’ira kaji ban ďauka ba ae sai ka hak’ura, amma ka ta wani k’irana sai kace ladan a masallachi” , sai da ta gama ya kwantar da murya yace “sorry Babe, something came , zanje wajen su Ammah ne in duba su, ya daďe da na gansu, I will go briefly and come back ” , batasan lokacin da ta mik’e daga zaunen da take ba, gumi ne taji gaba ďaya ya fara tsatsaffo mata, Ce mishi “Aliyu ba muyi haka dakai ba, mu da zamu koma gobe mey zakaje yi, toh ni dai bana son zuwanka, kuma baxa kaje ba ” , samun kanshi yayi da katse wayarta, har sai da yayi mamakin kanshi shima, mik’e wa yayi ya cewa Sadiq “muje ko? ” kallon mamaki yabi Abutturab dashi wai wannan shine yayanshi da yake takawa maza ma birki amma yau shine da kanshi mace ke mishi tsawa har yana ji a waya, ji yayi hawaye na son zubo mishi yayi maza ya maidasu yace “Yaa Abu muje” , ya shige gaba Abutturab na binshi daga baya,
Wani ihu ta saka tare da fashewa da kuka, hankalin su Mummy yayi kanta a tashe, tambayanta suka shiga yi lafiya take ta ihu haka amma tak’i magana, Yaa Zee ce tace mata ” a k’ira miki mijin nakine ko wani abin ne ya sami mijinki”, wani irin kallo ta Watso mata tace “Da wani abun ne ya same shi ai duk mai sauk’ine akan abinda yake shirin faruwa” taci gaba da kurma ihunta, su Mummy ganin tana Janyo hankalin mutane kansu tayi maza tasa su tafi da ita gida, har suka isa gida tana kuka suko sun sata gaba suna kallonta suna jiran Jin meye ke damunta, sai da tayi shiru tukunna tace ” Mummy Aliyu ya tafi gidansu, duk k’ok’arina na kar yaje sai da yaje kuma gashi malamin nan sai da yace indai nayi mishi toh ko kar in yadda ya haďu da ďan gidansu ko ďaya in ba haka ba Babban Al’amarine zai biyo baya, Mummy ni ban san meye Al’amarin ba amma duk yadda akayi ba mai kyau bane, gashi kuma ya tafi, Mummy ya tafi na shiga uku, bige mata baki Mummy tayi tace “akan wannan abin kika ďagawa kanki hankali, mu inane bamu shiga, ai in yasan wata baisan wata ba, ki kwantar da hankalin ki ba gobe zaku koma ba, toh babu abunda zai sameku daga ke har shi ďin ” a haka dai suka ci gaba da bata hak’uri da baki har suka samu tayi shiru amma ba Dan hankalinta ya kwanta ba, Dan gaba ďayansu basu san waye Aliyu ba, ita tasan yadda ta wahala a hannunshi farkon aurensu , tasan idan asirin nan ya karye toh nata ya k’are
Tafiya sukeyi babu wanda yace da wani komai, Abutturab ne ya ďago ya dubi Sadiq yace “Farida ma last month taje wajena ai, amma kai ko sau ďaya baka nemana ko? ” wani siririn dariya Sadiq yayi, yasan yayanshi is feeling guilty of himself shiyasa baisanma mey zaice ba, Sadiq yace “No Yaa Abu, abubuwa ne sukayi min yawa, ga hidiman Ammah, Abui da kuma na wasu shiyasa, amma in kuka koma har can zanzo , In shaa Allah” , jikin Abu ne ya kuma yin sanyi yace “Allah ya yadda ” a ranshi yana tunanin mey zai fara cewa su Ammah, sai yanxu yake sake ganin rashin kyautuwar abinda yayi, a haka suka isa gida suna hira jefi jefi, a k’ofar gida Sadiq ya tsai da motar tare da yiwa masu gadin horn, da sauri saurinsu suka taso suka buďe, ba K’aramin mamaki sukayi ba ganin Abutturab, da sauri suka faďaďa fara’arsu suna “Alhaji K’arami sannu da zuwa , an sha hanya to ya iyali , fitowa yayi daga motan ya mik’a musu hannu suka gaisa , sai murnan dawowanshi suke dan yana da kyauta sosai duk rashin dariyarsa, wucewa Sadiq yayi tukunna Abutturab yabi bayanshi, a hankali yasa kai cikin falon har wani faďuwa gabanshi yakeyi, Farida ce ta fito daga kitchen da tray a hannun ta, to abin ka da jini batasan lokacin data ajiye trayn ba tazo da gudu ta rungume shi ba, har da hawaye a idonta bayan ta sassauta rik’on da tayi mishi ta kalleshi tace “Yaa Abu ashe za kazo, Dan Allah kana zuwa gun mu kaji” Janyota ya sakeyi jikinshi yace zan rik’a zuwa kullum kinji Autan Abui” Dariya tasa ta goge guntun hawayen dake idonta tace “yawwa Yaa Abu, gidanmu babu daďi da baka nan, gaba ďaya abinda yayi mata da taje wajenshi last month ya rik’a tunawa, sae yaji bai kyauta ba, duk rashin shirin su da Farida amma cikin k’annenshi yafi sonta, haka itama tafi sonshi, masifanshi ne kawai bataso, juyawa tayi tace “bari in kira Ammah ya Abuu tana daki” k’asa cewa komae yyi sae bin ta da kallo da yyi, dai dai nn Ammah ta shiga sakkowa daga stairs.
Dawowa yayi yabi stairs ďin da kallo, da sauri ya ďauke idonshi daga wajen dan bazai iya kallon Ammah ba , falon k’asa tazo ta zauna ba tare da ta kalli inda Abutturab yake ba, jikinshi ne ya k’ara yin sanyi har sai da Sadiq ya lura dafa kafaďanshi yace mishi “it will be okay, just pray and be optimistic, a hankali ya ďaga k’afanshi kamar k’afan na mishi ciwo, har cikin falon shima ya k’arasa, ya samu waje a k’asa ya zauna ďan nesa da Ammah, cikin sanyin murya yace mata “Ammah ina wuni ” ba tareda ta kalleshi ba a tak’aice tace “lafiya” daga hka yyi shiru don ya rasa abun cewa, Abui ne ya shigo daga waje, da sauri Abutturab ya mike ya isa wajen Abui, cikeda girmamawa yace “Abui barka da gajiya, sannu da dawowa gida ” , kallon mamaki Abui ya shiga yi masa daga sama xuwa k’asa snn a takaice yace “sannu na gode , ashe ka shigo gari ” inji Abui yana me dubansa har lkcn, Kai Abutturab ya gyaďa tareda cewa “Ehhh Abui, ďazu na shigo ” , yace “madallah toh yayi kyau ” , bai sake bi ta kanshi ba yayi hanyan stairs, Ammah ce ta tashi tabi bayanshi suka haura tare tana mishi sannu da dawowa gida, Juayawa yayi ya dubi Sadiq a sanyaye , kai Sadiq ya girgiza mishi alamar assuringly, kamar yasa ihu haka ya rik’a ji a wajen, idonshi ne yaji yana kawo hawaye, tambayan kanshi ya fara “mesa na zama haka ne? , akwae randa su Ammah xa su ki murnan ganina bayan tsawon watanni, yana cikin tunanin yaji wayanshi na ringing, hawayen dake idonshi yayi maza ya goge ya ciro wayar daga aljihu, sunan da yayiwa Ajiddeh saving ya gani a screen ďin, sai da ya kusa katsewa tukunna yayi receiving yasa a kunne, Sadiq kam juyawa yayi ya bar wajen, jiki a sanyaye yace “Hello” , “Aliyu wai meye haka ne, har yanxu baka fito ba wai , tun ďazu fa nake zaman jiranka, daga cewa kaje gidanku yanxu zaka dawo shine zaka zauna ka shanya ni, ni da ina nan ma Wllh bazan bari ka tafi ba, kuma Hotel ďin kake son naje ni kaďai?” wani irin tsawa da ya daka mata ne ya sata yin shiru ba shiri, gaba ďaya jikinta sai da ya ďau rawa har gumi sai da ya tsatsaffo mata a goshinta , “bana son rashin hankali kina Jina ko, kin manta inda nace miki zanje ne, gidan iyayena naje kuma da kike cewa ke kaďai zaki kwana a hotel yau kika fara kwana a hotel ke kaďai ne , kuma ba dawowa zanyi ba so kar ki koma hotel ďinnan ki wuce gidanku ki kwana a can” gaba ďaya ta tsorata dashi, a hankali ta buďi baki tace “toh sai da safe” , wani iska mai zafi ya furzar daga bakinshi ya maida wayar aljihu, ďakin shi ya nufa, tsaf ďakin yake kamar yadda ya tafi ya barshi , babu abunda aka canja sai ďan k’uran da yayi, sai da yayi karkaďe k’uran tukunna yayi wanka ya kwanta, gaba ďaya bacci ya k’aurace mishi, sai yanxu abubuwan da yayi suka fara tariyo mishi, sai yanxu yake sake ganin rashin kyautuwar abinda yayi wa iyayensa, kusan kwana yayi yana tunani, ganin babu abunda tunani zai mishi ne yasa ya mik’e yaje ya ďauro alwala ya fara Nafila, haka ya kwana yana addu’a yana rok’on Allah ya huci zuciyar su Ammah, yana zaune kan sallaya har aka k’ira sallah asuba, Tashi yayi ya tafi masallaci, a nan ya haďu da Sadiq da Abui, tunda Abui ya amsa gaisuwan shi bai sake ce mishi komai ba, ba K’aramin tashi hankalinshi ya daďa yi ba, babu abunda yak’i irin ganin b’acin ran iyayenshi, Sadiq ne yaci gaba da kwantar mishi da hankali har suka shiga gida kowa yayi ďakinshi, zaman jiran gari ya waye yayi yaje ya samu Ammah, yasan in Ammah ta hak’ura toh Abui bashi da matsala, bakwai saura ya kasa hak’ura ya tashi yayi ďakin Ammah, yasan bata bacci war haka, yafi minti uku tsaye bakin k’ofar ďaki ya kasa shiga, a hankali yayi knocking k’ofar ďakin, muryan Ammah yaji tace bismillah, a hankali ya tura k’ofar ďakin ya shigo, Ammah na zaune daga bakin gado casbah a hannunta, da sallama ya shigo kanshi a k’asa ya zauna dab da k’afanta , cikin sanyin murya yace “Ammah Nda wattu” sai da ta ďauki seconds ba tare da kallon inda yake ba ta amsa mishi da “Lafiya” hankalinshi ne ya sake tashi yasan Ammah ba K’aramin fushi tayi ba , ko da wasa bata so tayiwa mutum kanuri yayi mata hausa, amma gashi yau ita da kanta tayi mishi hausa, shiru yayi ya rasa mey zaice can da yaga shirun baya zuwa ko ina yace “Ammah Dan Allah kuyi hakuri, wlhy ban san meye ya yazo kaina ba , Ina sha Allah bazan sakeyi ba, ku yafe min pls ” cikin kanuri yyi mata maganar, duk maganan da yakeyi ko sau ďaya bata juyo ta dubeshi, jiki a sanyaye ya sake matsawa kusa da k’afanta yace “Ammah fishinki na ďaga mun hankali fiyeda komai, nayi alk’awarin hakan bazai sake faruwa, kuyi hakuri ku yafe min, fishinku a kaina na Janyo min fishin ubangijina, Am so sorry Ammah ” , Hannunta yaje ya rik’a cikin nashi cikin sark’e war murya yace “Ammah kiyi min aikin gafara ko zan samu kwanciyar hankali, Ammah nasan na b’ata muku ……” , bata bari ya k’arasa ba ta Janye hannunta daga rik’on da yayiwa hannunta tace mishi ” hakurin mey kake bani wai, ni nace maka kayi min laifi ne, I thought you did what you think is right ko, then you should let me be ka dena damuna da hakuri, bance kayi min komai ba”, kanshi ya kifa a cin y’anta ya fashe da kuka yana girgiza kai, ya kai 1min kwance kai bata ďaga shi ba, tausayin dan nata ya cikata don tasan of course ba yin kansa bne, ta sa hannu a hankali ta ďauke kanshi daga cinyarta tace “you can go, am okay bakayi min komai ba , rasa mey ya ke mishi daďi yayi ya dubeta da idonshi da suka rine sukayi ja yace ‘Ammah pls forgive me, am promising you it won’t happen again, Ni gaba ďaya garin ma bazan sake bari ba, I will resign daga aiki a can, you should forgive me Ammah ” ce mishi tayi “Aliyu tashi kaje, bana so kazo kana damuna kaji , you should leave ” , kallonta yayi zai sake magana tace ” I said leave”, jiki ba k’wari ya mik’e ya fita, da ido tabi bayanshi cike da tausayin ďan nata, waje ya fita daga ďakin kanshi na Sara mishi, ďakinshi ya koma ya kwanta ya runtse ido hawaye na bin kun cin shi, wayar ya Janyo yayi receiving saboda K’aran da take, a kunnenshi ya saka tareda yin shiru, Ajiddeh ce tayi magana daga ďaya b’angaren tace “Aliyu har yanxu baza ka dawo ba , yaufa zamu wuce, kuma ma…..” katseta yayi yace “Look here free me, in baza ki iya zama ba toh ni kinga rabu dani, you should just go back am busy over here, xa ki iya tafiyar ki” ya katse wayan, hankalinta yafi na kullum tashi, shikenan ta shiga uku ta dinga nanatawa ta faďa kan kujera, baya fitowa daga ďakin sai in zai zo bawa Ammah da Abui hakuri amma duk da haka babu progress, hka yyi ta neman fuskar iyayen nasa amma bae samu ba, Farida da Sadiq ne ke shigowa wajenshi suna tausanshi tareda bashi baki, ranan kwana uku da yaje ya samu Abui, a ranan Abba ya nuna masa komae ya wuce ya hak’ura, murna fal cikin ransa ya fita tareda yiwa Abui alk’awarin hakan bazai sake faruwa ba, Ammah kam har yanxu tak’i hakuri tana nan kan bakanta
A ranan da ya cika kwana huďu a gida, da yamma ya fito falo ganin babu kowa kuma he is bored of zama a ďakinshi shi daya, ďaya daga cikin dogayen kujerun falon yaje ya kwanta a kai tareda lumshe ido kamar mai Jin bacci, Batuul ce ta shigo gidan ďauke da royal Food flask mai shegen kyau sai kuma leda a ďaya hannun Aunty ta aikota, mutum ta gani kwance kan kujera duk tunaninta Sadiq ne, da yake suna dan ďasawa dashi cikin sanďa ta tako tazo inda kujerar take , daidai fuskanshi ta tsuguna tare da yin k’ara, mik’ewa yayi xaune da sauri don har ya fara bacci rike da remote a hannu, ya juya don ganin wane isasshen ne hka , sai da hanjin cikinta suka kaďa ta xaro ido a tsorace don she wasn’t expecting him ko kaďan, da sauri ta koma baya Dan gaba ďaya ta gama tsorata da ganinsa, kallonta yayi tsaya yi ko kyaftawa baya yi, juyawa tayi zata bar wajen da sauri ya daka mata tsawa yace “Dawo nan ” , tsorata ta sakeyi ba kaďan ba ta sake ledan dake hannunta dama tun farko ta ajiye food flask ďin ta haura sama a guje ta shige ďakin Ammah, Ammah na ganinta ta shigo a guje ta mik’e tace “Subhanallah bitti, ke da waye haka? Wa ke binki ” , ba shiri ta k’irk’iri murmushi tace “Ammah ba komai” tare da k’ara faďaďa murmushinta, komawa Ammah tayi ta zauna tace “Bitti sak’on fa” , tace “yana falo Ammah, bari in taje in ďauko , bata k’arasa rufe bakinta ba ya shigo da Sallama rik’e da ledan a hannunshi, sai da ya ajiye tukunna ya sami waje ya zauna, shi da kanshi ya rasa mey ya hanashi komawa Dan yasan ba magana Ammah zata yi mishi ba, itama Ammah duk da ta fara tausaya mishi ta kuma ajiye fushinta kansa gaba daya ganin yanda ya rame har ya ďan k’ara duhu kuma tasan ba yin kanshi bane amma sam bata nunawa, Ammah tace “Bitti bakiga Yayanki ba” , pretending tayi tareda murmushi tace “ai mun gaisa a falo” , Mik’e wa tayi tace “Ammah zan tafi, Aunty tace kar in zauna muna da aiki, Dan taxi ma nazo da, motana ya samu problem kuma su Ahmad basa gida, Baa Alai da Baba kuma sun tafi Kaduna” , ta gyara gyalen kanta bayan ta gama maganan, Ammah ce tace “Taxi kuma, No baza ki koma a taxi ba, bari ďaya daga cikin drivers ďinnan yazo ya kaiki ” ta Janyo intercom zatayi waya ďaya ya maida Batuul gida, Abutturab ne cikin sanyin murya kamar mara gaskiya yace “Ammah drivers ďinfa ďaya yana office tareda Baba, ďayan kuma na aikeshi, bata kalleshi ba tace “bari in k’ira miki Sadiq ya kaiki kinji , nasan baiyi nisa ba” ta ďauki wayanta zata k’ira Sadiq Abutturab ya mike yace “Ammah zan kai tace tunda ina nan ” , a firgice Batuul ta kalleshi ta gefen ido, ďaure fuska Ammah tayi tace “Allah ya kiyaye, kuma daga nan ka tabbata ka shiga ka gaida Aunty “toh” yace ya juya yana yiwa Batuul wani irin kallo ya fita zuwa ďakinsa ďauko makulli, Batuul na ganin haka ta mik’e tareda k’irk’iro murmushi tayiwa Ammah sallama tace zata jira shi a k’asa ta fice a ďakin cikin sauri, da gudu ta sauk’o daga sama ta fita gidan gaba ďaya, waige waige takeyi tana sauri har ta iso bakin titi, tana zuwa ta samu taxi ta shige ta faďa mishi inda zai kaita, Ammah kam tun bayan fitan Batuul tayi tagumi tayi shiru zuciyarta na raya mata dama tun farko Batuul suka aurawa Abu da yanxu basu shiga bak’in cikin nan da suke ciki ba, wata zuciyar ce tace mata ai yanxu ma ba b’aci yayi ba, still zasu iya hadasu, a haka ma sai su k’ara k’arfin bond ďin dake tsakanin family, ji tayi zuciyarta tayi Na’am da zancen, take wani murmushi ya shimfiďu fuskarta, ta samu kanta cikin farin cikin da ta daďe bata ji irinshi ba, zama tayi kawai tana jiran Abui ta faďa masa wannan zancen taji mey zai ce.
Yana fitowa daga ďakinshi bayan ya ďauko makullin ya dawo ďakin Amma, dubanshi tayi tace mishi “baku tafi ba wai, mey kake jira”, cewa yayi “Eh ita nazo k’ira ta fito mu tafi”, ďauke Idonta tayi daga kallonshi tace mishi “tana palo k’asa ae tana jiranka”, juyawa yayi ya fita daga ďakin jin abinda Ammah ta faďa mishi, sakkowa falon yyi, yyi murmushi ganin bata nn ya fita compound, nan ma sai da ya dudduba bai ganta ba, masu gadi yaje ya samu ya tambayesu suka ce mishi ai ta wuce, bai sake ce musu komai ba ya koma wajen motarsa ya hau ya bar gidan, hanyan gidansu ya ďauka , dai dai tana isa ta sauk’a zata bawa driver taxi kuďi shima yayi parking motarsa gaban gate ďin gidansu saboda yayi beating traffic ďin cikin gari, su ko sai da suka bi ta ciki, gaba ďaya hankalinta ya gama tashi ganin motarsa, kasa tsayawa tayi ta karb’i canjinta tayi maza ta nufi cikin gida, yana ganin haka shima ya buďe motanshi ya fito cikin sauri yabi bayanta, dai dai k’ofan palo ya cimmata tareda da fizgota, gaba ďaya ta gama tsorata dashi har kyarma jikinta yakeyi, kuka ta fashe mishi da, rintse idonshi yayi ganin ta fara mishi kuka a ranshi yana cewa “she will neva change”,lkci daya ya buďe ido ya hade rae tare da k’ara janyota har jikinsu na tab’a juna, yana mata mugun kallo ya fara mata magana “wato rainin nan naki yana nan har ynxu ko?, yaushe na zama sa’an wasanki, I mean yaushe na fara miki wasa da zaki min kara a kai ki gudu, kuma kukan da kikeyi sai ki faďa min na meye, wato ke har yanxu baza ki canja ba ko?”, shiru tayi tana saurarenshi har tana jiyo heartbeat ďinshi, sai da taji yayi shiru tukunna ba tareda da ta ďago kanta ba ta fixge jikinta daga rik’on da yayi mata ta shige palo da sauri, inda tayi yabi da ido, da kamar zai koma sai kuma ya fasa ya tura k’ofan palon, dai dai nan Aunty ta fito daga kitchen, da mamaki a fuskanta ta buďe baki tace “Lalala, wa nake gani kamar Abutturab”, murmushi yayi tareda sunkuyar da kai k’asa ya k’arasa shigowa cikin palon,sai da ya zauna tukunna ya gaisheta, ta amsa da fara’a ta shigo falon ta xauna tana tambayarsa yaushe ya shigo gari, hira sosai sukayi da Aunty , Janet Aunty ta k’ira tace ta k’ira mata Batuul, dawowa tayi tace tana zuwa, sai da ta canja kaya ta saka straight skirt baqi da peplum blouse peach, ta sauk’o, kanta da ta taje take tattarewa ta sauk’o ba tare da sanin yana gidan ba, turus ta tsaya ganin mutum zaune yana hira da Aunty a gidansu, ita a zatonta ya wuce tun ďazu, ta hade rae a hankali ta karaso wajen Aunty tace “Na’am Aunty, Janet tace min kina k’irana”, cewa Aunty tayi “Ehhh, kitchen nakeso ki shiga kiyi Assisting su Esther ku k’arasa mana abinci, mik’ewa tayi daga hannun kujeran da take tayi hanyan kitchen, ya bi ta da kallo, Aunty ce tace mata “Batuul ya haka, bakya ganin Yayanki ne zaune baki gaidashi ba” juyowa tayi tace “Aunty mun gaisa, shi ya dawo dani gida ma fa”, ta faďa ba tareda ta bari sun haďa ido ba ta juya ta ci gaba da tafiyanta, har ta shige kitchen bae daina kallonta ba, a gidan ya zauna har akayi sallahn magriba sukaje suka dawo, suna ta hira shida k’annenta dan yana da son yara, Batuul kam duk aikin da takeyi ranta a b’ace yake , kwata kwata she is not comfortable don da ta fito kitchen sae sun hada ido, dama ga wannan masifan heartbeat ďin nata da ya fara dawowa bayan tsawon lokaci, gaba ďaya ya sata ta sake takura, k’ara b’ata rai tayi ta fito tana jera abincin da suka girka a dinning, suna haďa ido ya sakar mata harara, ďauke kanta tayi bata sake kallon inda yake ba, tana gamawa ta haura sama bata sake sauk’owa ba har ya bar gidan bayan Aunty ta tilasta shi cin abinci har tana ce mishi ko dai sabawa da yayi ne da girkin Ajiddeh yasa baya jin daďin wani abincin sai nata, murumushi yayi a ranshi dan shi baisan ma ya taste đin abincin Ajiddeh yake ba dan ba iyawa tayi ba, haka ya hak’ura ya zauna yaci dan babu yadda ya iya, bazai iya yiwa Aunty musu ba
Bayan anyi sallahn Isha Abui ya shigo gida, dama Ammah duk ta matsu ya dawo ta faďa mishi abinda ke ranta, bayan ya dawo saida ya sauk’o palon k’asa tukunna Ammah ta kawo mishi abincinshi har palon, sai da tayi serving ďinshi yana ci tukunna ta fara magana, shima dama ya lura da magana a bakinta, cewa tayi “Abul Aliyu”, ďagowa yayi bayan ya cinye spoon ďin abinci da ya saka a bakinshi yace “Na’am Umm Aliyu”, ya tsaya yana kallonta yana jiran yaji mey zatace, sai da tyi ajiyan zuciya tukunna tace “dama wani shawara nayi đazu akan yaran nan namu, kuma ina ganin its beneficial to both families, mey zai hana mu nemawa Abutturab auren yarinyan nan Batuul, yarinyar nutsatsiyace sosai kuma gidan da ta fito nan aka fara yiwa Abutturab tarbiya, a gidan ya fara koyon komai na rayuwanshi, kuma ko babu komai in suna tare a can , toh nasan lallai zata na watching moves ďinshi dan tana da lura da sanin ya kamata, xa kuma tana nuna masa what’s right nd wrong, gata kuma da hankali, kaga inma shi ya tafi yaqi dawowa toh ita ba yadda zatayi tayi ta zama babu ganin gida dole sai ta dawo, toh ,kaga a haka zai biyota su dawo ko dan kunyanmu”, tunda ta fara magana ya maida spoon ďin abincin cikin plate ďin, murmushi ďauke a fuskanshi yace “Masha Allah, wannan ai abin farin ciki ne sosai kuma nima zanfi kowa murnan ganin wannan al’amari ya faru, kamar Farida haka nake jin Batuul a raina, gobe in Allah ya kaimu zanje in tuntub’i mahaifinta akan zancen muji in babu matsala ko kuma da akwai wanda takeso “, Ammah tace”Abul Aliyu in sun yadda ma kawai a ďaura auren su tafi in yaso daga baya ayi biki , sai taci gaba da karatunta a can,”, yace “okay duk zanyi trying inji, Allah dai ya taimaka” haka dai sukayi ta zancen haďa Abutturab da Batuul aure har Ammah na cewa ai da tun farko ma sunyi tunanin nan da duk yanxu basa cikin matsala
Washe gari ranan juma’a bayan an idar da Sallah a masallaci Abui ya haďu da Baba, bayan sun gaisa Baba yace “Alhaji mu dai bama tab’a haďuwa dan kanmu sai dai ko masallaci ko kuma meeting”,dariya Abui yayi yace “rayuwan kenan Alhaji, in mukace zamu zauna gida abin bazai yi kyau ba, da shike ma yanxu girma yazo, mun kusa sauk’a mu huta ai”, duk su biyun suka sa dariya, Abui ne yacewa Baba ” *Alai wa office lan gèrezain, dai fatoro iske kèla kwamnyen* , Alai ana jirana office yanxu, amma anjima zanzo gida, there is this issue i want to discuss with you”, da haka sukayi sallama, da yamma wajen k’arfe biyar Abui na tashi daga office yayi gidansu Batuul ko gida bai je ba, lokacin Baba na gida saboda its a short day duk sun tashi aiki da wuri, fitowan Batuul kenan daga backyard đin gidansu, tayi mamakin ganin Abui a gidansu, har k’asa taje ta tsuguna ta gaisheshi sannan ta tashi da taje tayi serving ďinsu drinks da snacks, bayan ta ajiye zata mik’e Abui yake tamabayanta ya makaranta, tace Alhmdllh, nn yayi ta sa mata albarka har sai da taji kunyanshi sosai , bayan ta tafine Abui ya fara magana , sai da ya gama baynin abinda ya kawoshi tukunna Baba ya fa’da’da murmushin fuskarsa yace “Alai nidai b’angarena babu matsala dan babu abinda zaka nema matsawar inada iko akan abun in hanaka, kuma ma ai Abutturab yaron kirki ne sosai, dama dai akwai wani yaro da naga ya fara zuwa wajenta tun wancan watan amma bansan ko sunyi maganan aure ba, kuma tunda ga na gida da aka san halinshi ai yafi da a bawa na waje da ba’a san halinshi ba, dan ma dai naga yaron nada hankali amma zamu bashi hak’uri, yanzu dai ni zanje inyi shawara da y’an uwana da manya na sai mu san abin yi dan Yayya ma ta matsa tafi kowa son a aurar da Batuul sai gashi Allah ya taimakeni akai”, godiya sosai Abui yayiwa Baba daga nan suka shiga hirar politics da matsalolin dake damun Nigeria.
Batuul na kwance kan gado wajen k’arfe 8 na dare bayan tayi sallah isha, kayan bacci ne jikinta dogon wando da y’ar riga, kan gadon duk ta baje takaddu sai Macbook ďinta daga gefe, chocolate bowl ta janyo ta ďau twix ďaya ta b’are ta jefa a bakinta tukunna taci gaba da duba takaddan, tana ci taji wayanta na ringing, tashi tayi ta ciro wayan daga caji, Recieving tayi tareda komawa kan gadon ta kwanta, kamin tayi magana daga ďaya b’angaren akayi sallama tareda da faďin “Ranki ya daďe Habibty, i cant imagine life without you”, murmushi tayi har ana jiyo sautin daga ďaya b’angaren tace “tareda naka, you can live normally mana tunda ai da can ma baka sanni ba and you were living”, dariya yasa yace “that was then, amma ai yanzu tunda na sanki, life is gonna be hard without you, promise you wont leave me”, ji tayi gaba ďaya ya gama bata tausayi, ita tasan ba sonshi takeba but tana respecting ďinshi sosai, avoiding promise ďin da yace tayi mishi tayi tace “Ya jikin Mummy, ta k’ara samun sauk’i ko?”, da sauri ya tareta yace “Ba kinqi zuwa in kaiki wajenta ba, kullum sai ta tambayeni yaushe zan kawo mata kene, har banaso tana tambayana dan bansan mey zance mata ya hanaki zuwa ba”, kai ta girgiza kamar yana gabanta tace “No fa ba naqi zuwa bane, we have time , kuma i dont think its right muje gidanku tun yanzu , i will come when its time”, tambayanta yayi mey takeyi dan yaga mind đinta is not with him, tace mishi assignment takeyi, da haka ya barta tace they will talk ltr
Bayan Abui ya tafi, Aunty ce ta sauk’o k’asa ta sami Baba zaune yana kallon CNN channel, daga gefenshi ta samu waje ta Zauna tayi mishi sannu da gajiya tareda ajiye. abinda ke hannunta, volume ya rage ya juyo ya dubeta ya faďa mata yadda sukayi da Abui, ita gaba ďaya bata expecting haka, ta k’asa daina kallon mai gidan nata, hankalinta ba k’aramin tashi yayi ba jin xancen Baba kuma tasan babu yadda za ayi yaqi bawa Abutturab Batuul tunda har gida Babanshi yazo nema mishi aurenta, ajiyan zuciya tayi cike da damuwa tace “Uncle Batuul ďin kuma, shi da yayi aure ko shekara bai wuce ba, ai sai ya bari ko matar tasa in ta haihu ne sai ya fara zancen k’arin aure amma ba daga aure ya bijiro da sabo ba”, ta faďa tana jiran jin mey Baba zaice, cewa yayi “indai zai kula dasu duka biyu ai bamu da matsala, kuma ai ba sanin matsalarshi mukayi ba na son k’ara aure, kuma ma dai yaron nan ďanki ne, kinfi kowa sanin halinshi, ya kamata kifi kowa murnan kasancewar wannan al’amari, kinsan ko shekaran jiya kina zaune kina ji sai da Yayya ta k’irani akan Batuul, toh yanxu mafitar addu’an da nayi na samu, nasan Aliyu yaron kirki ne zai kula da Batuul in sha Allah”, ido kawai Aunty ta zubawa Baba yana magana hankalinta na dađa tashi, Batuul tayi yarinya da auren mai mata, barema irin su Ajiddeh, cutan Batuul kawai za ayi indai ta zauna a gidan nan a matsayin matar Abutturab, dan tasan yadda familyn Ajiddeh suke akan kishiya, mik’ewa kawai tayi ba tareda ta sake cewa komai ba ta haura sama don bata jin xata amince da wnn batun at all, idonta ya kaďa har ya canja kala.