BAYI MA YAYA NE COMPLETE

 BAYI MA YAYA NE COMPLETE

*BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*



Babi na 1/2



Masarautar Daborah masarauta ce dake can cikin kasar Gambia,  yankin Afrika ta gabas masarautar ta shahara a fagen Sarauta wadda ta share sama da shekara Dubu Ukku da kafuwa a cikin duniya ba inda ba'asan labarin Masarautar ba, a cikin kasar Gambia harma da kewayenta.

Masarautar kwata kwata basu san kima ko darajar bayin su ba,  sun maidasu kamar wasu dabbobi wani bima har kwara dabbobi sun fisu ƙima a cikin masarautar Daborah, kuma sunyi suna wajen tarar abokan gaba daga ko ina a cikin sassan duniya, wanda suke da tarin makayaka masu karfin gaske, labarin su ya karade kaf nahiyar wannan dalilin yasa ake shayin haye masu wannan kenan.



Duke take tana ta famar naƙuda kamar zata mutu duk tagama fita hayyacin ta,  duk yan uwanta sun zagaye kofar saboda gudun kar labarin naƙudar Binta tafita a cikin masarautar, kowa jininshi akan hakaifa yake,  sai uban zufa suke ketawa karma ace mijinta Abdulmajid hakan bakaramin tada mashi hankali yakeba, itako Binta baiwar Allah sai addu'a su Jummai ke mata ciki ikon Allah ta surbuɗo kyakkyawar yarta santaleliya jajir da ita gwanin ban shi'awa, godiya taima Allah duk da tasha wahala hakan baisa hankalin ta ya gushe yabar jikin taba, kukan da jaririyar keya hakan yasa ya fita har waje da sauri Abdulmajid ya shigo ya dauke diyar ya boyeta, sannan yasa su Jummai suka shirya su, duk baki daya hankalin su yaki kwanciya.



Ladidi ce ta shigo sai haki take a cikin Turakar bayi ta shigo dakin su Binta duk sun raina gaskiar su, kowa yabita da kallan tuhuma ko lfy? Bude baki tayi tafara magana cike da tsoro duk ya mamaye ta tace."kin bani Binta wayace ki haihu a cikin wannan Masarautar? Ko kinsan kalar hadarin da kika jefa kanki?Kin manta da matsayinki a cikin wannan masarautar?Amman kikayi wannan gangancin."!? Duk a cikin tsoro tayi wannan tambayar maida kallonta tayi ga Abdulmajid tace. "yanzun kai Abdulmajid a matsayinka na uban bayi ya zakayi da wannan matsalar."!?  Kowa ya kasa magana danko su jummai kuka kawai sukeyi sunajin tausayin Binta, karma ace yar jinjirar da batasan komai ba,  zuwan ta kenan a cikin duniyar ga baki dayanta ma, kukan da yar tasu takeyi shi yakara jefasu cikin tashin hankali hakan yasa Binta daukar diyarta tafara bata nono  kila tasamu kodan jinkai ne a wajen yarta bayan rasa su, magana Abdulmajid ya fara cikin damuwa yana cewa."Ladidi ko kinsan me kike fada, taya zamu kawar da abinda Allah ya kaddara mana, karfa kimanta munkai sama da shekaru Arba'in da aure muna neman haihuwar nan amman bamu samuba sai yanzun Allah yajikan mu yabamu sai mu yarda muce bamu so?  mukasan ko wacece wannan yarinyar nan gaba?  kisani ni Abdulmajid koda za'a sare kaina bazan taba wofintar da kyautar da ubangijina yaimani ba, bayan na bata sama da shekaru masu yawa ina nema kawai dan ina bawa sai in wulakanta wannan ni'imar mai girman gaske."? Yayi ma ladadi tambayar yana kallon kwayar idonta, girgiza kai tayi sannan tace. "Aa uban bayi ba nufina kenan ba nidai fatana Allah ya tsaremu daga sharrin makiya kuma yakare mana yar'mu." baki ɗayansu suka amsa da. "Ameen."


ita dai Binta ita kadai tasan halin da take ciki sai kuka takeyi tana addu'a Allah ya tsaremata yar'ta koda ace ba tare zasu rayuwa ba.
DOWNLOAD BOOK 1 HERE👈
DOWNLOAD BOOK 2 HERE👈

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *